Wednesday, 3 October 2018

CANJIN RAYUWA Kashi Na 1 (Shafi 16-20) - ISMAIL SANI

CANJIN RAYUWA
[Kashi na 1]
(Shafi 16-20) Tare da -
Halima K. Mashi
Post By ISMAIL SANI

Ya tafi malumfashi sai gobe zai dawo. MIMI ta zaro idanu yaya dady zai min haka ya tafi ya bar ni,ta kalli hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta ce,hajiya don allah ina waya ta?hajiya ta ce,sai za ku tafi zan baki,don ni ba za kiyi mani chatin din naki ba a nan,ki karya ki je ki yi wanka,in malamin su hussai ya zo zaki bisu, ki je daukar karatu a gurinsa.ina sa ran ma alhaji ba zai tafi da ke ba,nan zai bar ki sai kin san addininki za ki tafi, ko da zaki cinye hutun ki a nan. cikin sauri MIMI ta koma daki cikin kuka sai da tayi me isarta ta shiga wanka,a fili kuwa fili kuwa fadi ta ke, Allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani zuwa katsinan nan.dolenta ta saka atamfa riga da siket,a cikin durowarta ta ciro don tana da kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wasu usaina sai an yi mata. ta shirya tsaf ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi. amma ko ta halin kaka baza ta zauna cikin irin takurar ba. can ta hango wayar hasana kan durowar ta.cikin sauri ta tashi ta dauko, layin dad ta kira wanda ta san in ta kira zai dauka da sauri,cikin kuka ta soma magana,bayan ya daga dad kaga hajiya ta dauke min waya ta,kuma wai ba zan tafi ba,ni dai dad wallahi bazan zauna ba.ya ce,ya shiru uwata kar ki damu ba zan barki ba ni ma,yanzu me kike so? ta ce,phone di na,ya ce,shikenan zan ce ta ba ki,kin ci abinci? ta ce,aa ya ce,to kije ki ci zan sata baki wayarki kin ji?

Ta na zaune a kan dining ta hada shayi tana sha da cokali cikin hankali don ita sam bata da hanzari,tana kallo lokacin da hussaina ta kawo ma hajiya waya ta ce,dady ya kira,ta daga.ta na jin lokacin da hajiyar take cewa,tsaya kaji alhaji, sai kuma tayi shiru,da alama ya katse ta ne,ya hana ta magana,don taga hajiya tayi shiru,amma ranta a bace yake.sai kuma tace to alhaji naji zan bata, amma bana son chatin din nan data keyi. MIMI ta yi murna,a ranta tace dady na kenan,ta nufi daki da murna,alhaji ya ce,kar ki damu sauda,’yarki mai kamu kai ce.ita da kowa ya shaida ko saurayi ba.

Shi yasa nike dubawa don in samo mata miji wanda zai kimanta min ita,ya bata kulawa fiye da wanda take samu a guri na.

Hajiya ta ce umm!allah ya taimaka,ai ni dana zaci ma baza ka iya auradda ita ba(cikin gatse tayi maganar)ya ce,kash kin ji ki da wata magana kuma sauda,in ban aurar da ita ba ai kuma na cuce ta.ina maki kaga an taba haka?ke dai kiyi mana addua,ta ce,allah ya taimaka,kun gama ganawar ne? ya ce,eh,yanzu haka muna hanyar malumfashi sai na dawo ta ce,allah ya tsare,ka dawo lafiya,ya ce, amin,ga dai uwata nan amana naba ki,katse wayar yayi ba tare da ya jira jin amsa daga bakinta ba.ga zaton MIMI tana aje wayar alhaji zata zo taba ta tata,amma sai taji shiru. ta sake fitowa falo nufin ta kila hajiya ta ganta ta tuna,idan ta manta ne, amma sai taga hajiya ta ci gaba da lamuranta. yaran duk suka yi wanka suka fito,husna da hasina suka shiga falo da gudu suna cewa,ga malam nan yazo.ga mamakin MIMI sai ta ga duk yara sun rude, wasu  sun dauko alkur’anin su suna karantawa da sauran littafai da yake masu.a ranta ta ce ni ko bari in ga wanene malamin ,kai har naji na tsane shi tun kafin in ganshi.a zaton ta nan zai shigo sai ta ga abdullahi da umar da aminu da sadik sun soma fitowa bayan dawowansu sai zainab da hasana da hussaina suka fita.

Hasina da husna kuma sun dukufa suna ta karbarma juna hadda,kafin a zo kansu.MIMI ta tabe baki tare da cewa,wahalar da kai,basu dade ba suka dawo.su hasana sun mike kenan hajiya ta fito daga daki ta ce,ke ma tashi kije, ta nuna MIMI ta hada rai,sai dai bata da damar yin musu,don babu alhajin da zai tare mata.hasana ta ce. yaya MIMI sai kin sako hijabi fa,ta banka harara,ban dauko ba,ina wasa da ke ne?in ki ka kara yi min magana sai na mare ki. Suka yi shiru suka wuce,ta warware dan kwalin kayanta ta yafa,tana biye da su har falo baki,kafin su shiga sai da suka kara gyara hijabansu suka yi sallama suka shiga,ta tsaya tana mamaki wai malami ne suke yi ma bare-baren, malamin ma wai na lslamiyya,ita malami ko na boko bata dauke shi wani abu ba,face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da ba zata iya, Face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da baza ta iya bambamce shi da maigadi ko mai sharan gidansu,kosawa ma ta yi ta shiga ta gani wane gaja ne?

Hausa-Katsina Post
CANJIN RAYUWA [Kashi na 1] -Tare da Halima K. Mashi (Shafi 16-20)


Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

LITATTAFAN HAUSA December 17, 2016 Author
CANJIN RAYUWA [Kashi na 1] -Tare da Halima K. Mashi (Shafi 16-20)
0 0
00
MORE 
NOW VIEWING


Ya tafi malumfashi sai gobe zai dawo. MIMI ta zaro idanu yaya dady zai min haka ya tafi ya bar ni,ta kalli hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta ce,hajiya don allah ina waya ta?hajiya ta ce,sai za ku tafi zan baki,don ni ba za kiyi mani chatin din naki ba a nan,ki karya ki je ki yi wanka,in malamin su hussai ya zo zaki bisu, ki je daukar karatu a gurinsa.ina sa ran ma alhaji ba zai tafi da ke ba,nan zai bar ki sai kin san addininki za ki tafi, ko da zaki cinye hutun ki a nan. cikin sauri MIMI ta koma daki cikin kuka sai da tayi me isarta ta shiga wanka,a fili kuwa fili kuwa fadi ta ke, Allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani zuwa katsinan nan.dolenta ta saka atamfa riga da siket,a cikin durowarta ta ciro don tana da kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wasu usaina sai an yi mata. ta shirya tsaf ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi. amma ko ta halin kaka baza ta zauna cikin irin takurar ba. can ta hango wayar hasana kan durowar ta.cikin sauri ta tashi ta dauko, layin dad ta kira wanda ta san in ta kira zai dauka da sauri,cikin kuka ta soma magana,bayan ya daga dad kaga hajiya ta dauke min waya ta,kuma wai ba zan tafi ba,ni dai dad wallahi bazan zauna ba.ya ce,ya shiru uwata kar ki damu ba zan barki ba ni ma,yanzu me kike so? ta ce,phone di na,ya ce,shikenan zan ce ta ba ki,kin ci abinci? ta ce,aa ya ce,to kije ki ci zan sata baki wayarki kin ji?


Ta na zaune a kan dining ta hada shayi tana sha da cokali cikin hankali don ita sam bata da hanzari,tana kallo lokacin da hussaina ta kawo ma hajiya waya ta ce,dady ya kira,ta daga.ta na jin lokacin da hajiyar take cewa,tsaya kaji alhaji, sai kuma tayi shiru,da alama ya katse ta ne,ya hana ta magana,don taga hajiya tayi shiru,amma ranta a bace yake.sai kuma tace to alhaji naji zan bata, amma bana son chatin din nan data keyi. MIMI ta yi murna,a ranta tace dady na kenan,ta nufi daki da murna,alhaji ya ce,kar ki damu sauda,’yarki mai kamu kai ce.ita da kowa ya shaida ko saurayi ba.

Shi yasa nike dubawa don in samo mata miji wanda zai kimanta min ita,ya bata kulawa fiye da wanda take samu a guri na.

Hajiya ta ce umm!allah ya taimaka,ai ni dana zaci ma baza ka iya auradda ita ba(cikin gatse tayi maganar)ya ce,kash kin ji ki da wata magana kuma sauda,in ban aurar da ita ba ai kuma na cuce ta.ina maki kaga an taba haka?ke dai kiyi mana addua,ta ce,allah ya taimaka,kun gama ganawar ne? ya ce,eh,yanzu haka muna hanyar malumfashi sai na dawo ta ce,allah ya tsare,ka dawo lafiya,ya ce, amin,ga dai uwata nan amana naba ki,katse wayar yayi ba tare da ya jira jin amsa daga bakinta ba.ga zaton MIMI tana aje wayar alhaji zata zo taba ta tata,amma sai taji shiru. ta sake fitowa falo nufin ta kila hajiya ta ganta ta tuna,idan ta manta ne, amma sai taga hajiya ta ci gaba da lamuranta. yaran duk suka yi wanka suka fito,husna da hasina suka shiga falo da gudu suna cewa,ga malam nan yazo.ga mamakin MIMI sai ta ga duk yara sun rude, wasu  sun dauko alkur’anin su suna karantawa da sauran littafai da yake masu.a ranta ta ce ni ko bari in ga wanene malamin ,kai har naji na tsane shi tun kafin in ganshi.a zaton ta nan zai shigo sai ta ga abdullahi da umar da aminu da sadik sun soma fitowa bayan dawowansu sai zainab da hasana da hussaina suka fita.

Hasina da husna kuma sun dukufa suna ta karbarma juna hadda,kafin a zo kansu.MIMI ta tabe baki tare da cewa,wahalar da kai,basu dade ba suka dawo.su hasana sun mike kenan hajiya ta fito daga daki ta ce,ke ma tashi kije, ta nuna MIMI ta hada rai,sai dai bata da damar yin musu,don babu alhajin da zai tare mata.hasana ta ce. yaya MIMI sai kin sako hijabi fa,ta banka harara,ban dauko ba,ina wasa da ke ne?in ki ka kara yi min magana sai na mare ki. Suka yi shiru suka wuce,ta warware dan kwalin kayanta ta yafa,tana biye da su har falo baki,kafin su shiga sai da suka kara gyara hijabansu suka yi sallama suka shiga,ta tsaya tana mamaki wai malami ne suke yi ma bare-baren, malamin ma wai na lslamiyya,ita malami ko na boko bata dauke shi wani abu ba,face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da ba zata iya, Face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da baza ta iya bambamce shi da maigadi ko mai sharan gidansu,kosawa ma ta yi ta shiga ta gani wane gaja ne?


Ta jingina da kofar,sannan ta kai kallonta gurin shi,yana zaune kan kujeran zaman mutum daya sanye yake da jallabiya mai ruwan madara mai dogon hannu da maballi a hannu,tare da kwala a wuyarta.ga wani dan ado da zare mai ruwan kasa da aka yi a wuyar da hannun rigar,bata kai can kasa ba,irin dai shiga ta sunna,hular kanshi baka ce irin wanda ake kira minista. ya na rike da alkurani yana bude inda suke.su kuma su hussaina suna zaune a kasa kan kafet a gabanshi duk suna rike da alkuraninsu,MIMI ta tabe baki tare da harde hannuwanta a kirjinta,tana kare masu kallo.a ranta ta ce,tabdi,ai ba a yi mutumin da zai zo gidan ubanta ta zauna a kasa yana kan kujera ba.malam lsmail ya dago ya kalli bakin kofa da kyawawan idanunsa,duhun mutum ya gani,ya sa shi kallon gurin ya kalli MIMI da ke tsaye ta watso masa wani kallo da ba zai iya fassarashi ba. ya mayar da kanshi ga abinda yake yi.su hussaina suka ci gaba da kawo masa hadda yana yi masu ‘yan gyare-gyare, suka kamalla,sannan suka soma sauran littafai. Ta shiga ta zauna tare da daukan rimote ta kunna tv, ya dago ya dube ta, tamkar zai yi magana,amma sai ya fasa. ya san da gadara tazo, bayan su hussaina sun kamalla,sai hussaina tace, yaya kizo mun gama,ta kalle su cikin harara,ku fita mana, suka fita suka je suka sanar da hajiya ko mai. ita kam suna fita ta mike tana tafiyar nan tata, ta isa kan kujerar gefen shi ta zauna. ya dago ya dube ta,ya mike tare da tattara littafansa,ya nufi fita,a bakin kofa suka ci karo da hajiya zata shigo,ya dakata ta kara so suka gaisa,ta ce, har ka mata karatun? ya ce, wace kenan?ta ce, MIMI, bangan ta ba ai,hajiya ta ce aa ta shigo ciki falon, ta ce gata nan fa,ya dawo cikin falo,ok!wannan ce? na ganta amma ban zaci karatu za ayi mata ba.ita kuma bata fada min ba. hajiya ta ce,ai ba zata fada maka, Saboda ba son karatun ta ke yi ba.ka soma mata daga fatiha don ba na zaton ta iya,don allah malam lsmail kar kayi mata da sauki.lsmail ya ce, ba komai hajiya.amma ta saka hijabi ta ce,to ba komai bari in sasu hasana su kawo mata,in ta ki yi ka dake ta ko ka kira ni.

Hajiya ta fita shi kuma ya kai duban shi gare ta, MIMI ta cika tayi tam.ya na zama hasana tana shigowa da sallama,shine ya amsa,ta ce,yaya ga shi, harara ta watso mata,ta ki amsa,hasana ta aje a hannun kujeraq da take zaune ta fita. Ya kalle ta,malama ki saka hijabinki mana,cikin sauri ta dago kai ta dube shi duban tsana mai tsanani,domin ba a taba ci mata mutunci kamar yau ba a gaban kaskantacce irin wannan.ba a taba rena mata wayo ba kamar yadda shi din ya yi mata,ya ganta sarai,amma ya ce,bai ganta ba.abin yayi mata ciwo fiye da abinda hajiya tayi mata.ta harare shi sama da kasa sannan taja tsaki, malam baya daukar reni,sabi da haka sai ya hada rai tare da rufe alkuranin shi. Ta ce kai waye suna da ake kiranka? ina son ka sani na wuce ka rena min wayo kuma kai baka isa ka koya min karatu ba.ya daga hannu tare da katse ta da cewa ke.ba ki da ladabi ne? gaskiya ba tarbiyyar nan gidan ba ce,domin yaran gidan nan mazansu da matansu nayi shedar su guri ladabi game da sanin darajar mutane,ke ma ina yi maki nasiha ki canza.kuma ina son ki sani karatun nan in kin yi kin ma kanki ne bani ba,don haka ka da allah yasa ki yi,ya mike ya fita abinsa.             yana jiyo tsakinta gami da cewa, talakan banza kana ci a karkashin mahaifi na ka nuna ni da yatsa,to bari ka gani lokacin barin ka aiki yayi. Har ya tafi ya dawo ke ma dukiyar daki ke takama ba taki ba ce,ta mahaifin ki ce,ina son ki sani ba keki ka dauke ni aiki ba bare ki sallame ni.ba kuma maula nake zuwa yi a gidanku ba,ina son ki san wannan.kafin ta sake yin wata magana ya wuce ya barta cikin takaici,lallai sai nayi maganin sa,shine mutum na farko a tun tasowar ta da ya taba fada mata abinda ya ke so,

(Zan ci gaba)..

IP

Friday, 28 September 2018

CANJIN RAYUWA Kashi Na 1 (Shafi 11-15) - ISMAIL SANI

*CANJIN RAYUWA*
*[Kashi na 1]*
*(Shafi 11-15) Tare da -* _Halima K. Mashi_
Post By *ISMAIL SANI*

Yakan kai sha biyu bai shigo gida ba zai yi ta gaisawa da mutane, abokai zuwa ‘yanuwa suka ji cewa ya shigo gari. don haka ita ma hajiya bata fito ba sai bayan sallah isha,ta shiga daki alhaji don sake kalailai ce shi,tare da kunna turarukan kamshim daki,ta fitar ma da alhaji kayan barci,ta dama masa fura,ta nufi dakin yaranta don ta tabbatar suna cikin koshin lafiya. daki maza ta fara shiga, umar da aminu suna ta yin home work, abdullahi yana kwance kan gado, sadik yana buga game a tv. ta ce,sarkin game kai ka yi home work dinka? ya ce, eh nayi hajiya ta kalli abdullahi,kai fa bawan allah yau da wuri zaka yi barci kenan? ya tashi zaune kaina ke ciwo hajiya shi yasa ki kaji na ce dad ya bari sai gobe mu je super maket din.don ba zan iya kula da su ba.
Ta ce,ba sai kun yi haka ba,ya ce,kin shiga daki lokacin ta ce,to ka sha magani?ya ce eh!ta ce to allah ya sawwake,ya ce ameen. ta ce,sadik tashi ka kulle muku kofar ku sai da safe,suka ce,to ta ce,kar fa ku manta da yin addua lokacin barci,suka ce to.ta nufi dakin su husna da hasana da kuma zainab yar gidan hajiya binta, wace ta ki komawa wajen uwarta,tun lokacin da alhaji ya saki hajiya binta,ya kwaso yaran ya kawo su nan.hajiya sauda tace sam ba zai yiwu ba,lallai ya mayar da ita,ta rike kayanta. domin ita kanta ba zata sa araba ta da ‘ya’yanta ba.shine da ya dawo da ita ya mayar mata da yaran amma ban da zainab,don kuwa ta kekashe ba9a ta bi su ba.      lta ta fi son zama a nan, hajiya sauda ta rike ta,ta hada da ‘ya’yanta guda goma sha biyu da ta haifa suka zama sha uku.su kam sun fara barci. don haka ta shigo ta yi masu addua tare da kulle masu kofar dakinsu. hasana suna zaune suna kara ma juna haddar alkur’ani mai girma, ita kuwa ‘yar gwal,wato MIMI tana kishigide kan gado.tana ta chatin,kai tsaye gurinta hajiya ta nufa ta fisge wayar da sauri MIMI ta dubi wayar cikin bacin rai.tana ganin hajiya sai ta yi kasa da kai kamar munafuka,kin yi sallar ne? cikin tsawa ta ji maganar MIMI, MIMI ta yi shiru, ta ce,ba ki ji niba ne?ta girgiza kai tare da fadin banyi ba. hajiya ta rufe ta da fada bangane ba kiyi ba?

Anya ma kina yin sallar na kuwa? ta kalli hajiya cikin sauri tare da fadin ina yi mana,hajiya tace,karya ne kalli agogonki karfe nawa ne yanzu?da har zuwa yanzu baki yi ko sallar magariba ba bare lsha.in na lura musulunci ba ya birge ki,lslamiyya kin daina,duk wani abu da lslam yazo da shi,komi na addini kin mayar da shi kauyanci,ke ga ‘yar boko ko?MIMI dai bata dago kai ba,hajiya ta ce,na san ko zaa kashe ki yanzu da kyar in zaki iya kawo mini fatiha cikakkiya. kin zauna kina ta danne-dannen waya,in ba ki sani ba ne gara ki sani,kina cutar kanki ne.rayuwar daki ka daukar wa kanki ba mai dorewa ba ce,don haka ba ta dace da ke ba.ki ta shi ki yi sallar yanzun nan, sakarya marar hankali. simi-simi MIMI ta tashi ta nufi bandaki,hajiya ta ce,tunda abin naki ya soma nisa haka,wayewar taki har ta kai ki da gudu salla,to nan gida za ki kare hutunki.ki dau karatu gurin malamin yaran nan,ki koyi salla tun da bani da tabbacin kin na yi.bari baban naku ya shigo,ta juya ta fita da wayar a hannunta. MIMI daga cikin bandaki,kuka wiwi ta dinga yi,ita kam baza ta iya zam har ta gama hutu cikin takurar ba. a silent hajiya ta saka wayar MIMI ta ja durowa ta jefa.MIMI tana kuka ta yi sallar,su hussaina suna kallonta,ta idar ta fada kan gado ta ci gaba da kuka.don ita amshe mata wayar da hajiya ta yi,ya fi bata mata rai fiye da fadan,don jin ta take tamkar an raba ta da ranta, sam bata nisa da wayarta. misalin shabiyu saura alhaji ya shigo,tuntuni yake ta neman layin ‘yar lelanshi,amma sai tayi ta ruri har ta yanke ba a daga ba. hajiya ta shiga ta same shi tana cikin shirin barci,ya kalle ta da wayansa a hannu,MIMI fa? ta kalle shi,in kira maka ita ne? ya lura cikin gatse ta yi masa maganar,don haka sai ya ce,aa dama in ji ko ta yi barci ne,saboda ina ta kiran wayarta bata dauka ba.cikin jin haushi hajiya ta ce oho..
Hausa-Katsina Post
CANJIN RAYUWA [Kashi na 1] -Tare da Halima K. Mashi (Shafi 11-15)
Daukar Nauyi: Funtua Mandate Promoters

LITATTAFAN HAUSA December 11, 2016Author
CANJIN RAYUWA [Kashi na 1] -Tare da Halima K. Mashi (Shafi 11-15)
0 0
84
MORE 
NOW VIEWING

Yakan kai sha biyu bai shigo gida ba zai yi ta gaisawa da mutane, abokai zuwa ‘yanuwa suka ji cewa ya shigo gari. don haka ita ma hajiya bata fito ba sai bayan sallah isha,ta shiga daki alhaji don sake kalailai ce shi,tare da kunna turarukan kamshim daki,ta fitar ma da alhaji kayan barci,ta dama masa fura,ta nufi dakin yaranta don ta tabbatar suna cikin koshin lafiya. daki maza ta fara shiga, umar da aminu suna ta yin home work, abdullahi yana kwance kan gado, sadik yana buga game a tv. ta ce,sarkin game kai ka yi home work dinka? ya ce, eh nayi hajiya ta kalli abdullahi,kai fa bawan allah yau da wuri zaka yi barci kenan? ya tashi zaune kaina ke ciwo hajiya shi yasa ki kaji na ce dad ya bari sai gobe mu je super maket din.don ba zan iya kula da su ba.

Ta ce,ba sai kun yi haka ba,ya ce,kin shiga daki lokacin ta ce,to ka sha magani?ya ce eh!ta ce to allah ya sawwake,ya ce ameen. ta ce,sadik tashi ka kulle muku kofar ku sai da safe,suka ce,to ta ce,kar fa ku manta da yin addua lokacin barci,suka ce to.ta nufi dakin su husna da hasana da kuma zainab yar gidan hajiya binta, wace ta ki komawa wajen uwarta,tun lokacin da alhaji ya saki hajiya binta,ya kwaso yaran ya kawo su nan.hajiya sauda tace sam ba zai yiwu ba,lallai ya mayar da ita,ta rike kayanta. domin ita kanta ba zata sa araba ta da ‘ya’yanta ba.shine da ya dawo da ita ya mayar mata da yaran amma ban da zainab,don kuwa ta kekashe ba9a ta bi su ba.      lta ta fi son zama a nan, hajiya sauda ta rike ta,ta hada da ‘ya’yanta guda goma sha biyu da ta haifa suka zama sha uku.su kam sun fara barci. don haka ta shigo ta yi masu addua tare da kulle masu kofar dakinsu. hasana suna zaune suna kara ma juna haddar alkur’ani mai girma, ita kuwa ‘yar gwal,wato MIMI tana kishigide kan gado.tana ta chatin,kai tsaye gurinta hajiya ta nufa ta fisge wayar da sauri MIMI ta dubi wayar cikin bacin rai.tana ganin hajiya sai ta yi kasa da kai kamar munafuka,kin yi sallar ne? cikin tsawa ta ji maganar MIMI, MIMI ta yi shiru, ta ce,ba ki ji niba ne?ta girgiza kai tare da fadin banyi ba. hajiya ta rufe ta da fada bangane ba kiyi ba?

Anya ma kina yin sallar na kuwa? ta kalli hajiya cikin sauri tare da fadin ina yi mana,hajiya tace,karya ne kalli agogonki karfe nawa ne yanzu?da har zuwa yanzu baki yi ko sallar magariba ba bare lsha.in na lura musulunci ba ya birge ki,lslamiyya kin daina,duk wani abu da lslam yazo da shi,komi na addini kin mayar da shi kauyanci,ke ga ‘yar boko ko?MIMI dai bata dago kai ba,hajiya ta ce,na san ko zaa kashe ki yanzu da kyar in zaki iya kawo mini fatiha cikakkiya. kin zauna kina ta danne-dannen waya,in ba ki sani ba ne gara ki sani,kina cutar kanki ne.rayuwar daki ka daukar wa kanki ba mai dorewa ba ce,don haka ba ta dace da ke ba.ki ta shi ki yi sallar yanzun nan, sakarya marar hankali. simi-simi MIMI ta tashi ta nufi bandaki,hajiya ta ce,tunda abin naki ya soma nisa haka,wayewar taki har ta kai ki da gudu salla,to nan gida za ki kare hutunki.ki dau karatu gurin malamin yaran nan,ki koyi salla tun da bani da tabbacin kin na yi.bari baban naku ya shigo,ta juya ta fita da wayar a hannunta. MIMI daga cikin bandaki,kuka wiwi ta dinga yi,ita kam baza ta iya zam har ta gama hutu cikin takurar ba. a silent hajiya ta saka wayar MIMI ta ja durowa ta jefa.MIMI tana kuka ta yi sallar,su hussaina suna kallonta,ta idar ta fada kan gado ta ci gaba da kuka.don ita amshe mata wayar da hajiya ta yi,ya fi bata mata rai fiye da fadan,don jin ta take tamkar an raba ta da ranta, sam bata nisa da wayarta. misalin shabiyu saura alhaji ya shigo,tuntuni yake ta neman layin ‘yar lelanshi,amma sai tayi ta ruri har ta yanke ba a daga ba. hajiya ta shiga ta same shi tana cikin shirin barci,ya kalle ta da wayansa a hannu,MIMI fa? ta kalle shi,in kira maka ita ne? ya lura cikin gatse ta yi masa maganar,don haka sai ya ce,aa dama in ji ko ta yi barci ne,saboda ina ta kiran wayarta bata dauka ba.cikin jin haushi hajiya ta ce oho..

Na zata ita ma nan zamu kwana tare don kar wani abu ya cinye ta. ya mike tare da kama hannunta,sauda kin canza sani na ba haka kike ba.yanzu kin zama mai saurin fushi.ta kalli fuskarsa,kai da ‘yarka kuka canza ni. ya ja hannunta, to zo mu zauna in ji mai zan samu.ya basar da wancan zancen.ita ma sai ta biye masa da cewa,duk abinda kake so.ya tallabe fuskarta kin san mene ne sauda?ta girgiza kai kullum na kalli fuskarki.rana mai tarihi a guri na.hajiya sauda ta ce, ikon allah ni kan da a ce kalmar karatu ce,da sai in ce,tuni na haddace ta,tun muna da kananan shekaru.      ya yi ‘yar dariya ina jin dadin tuna baya,wani lokacin sai in ji tamkar in mai do lokaci.ta lumshe ido, ai alhaji kuruciya cike ta ke da shirme,in ta wuce sai ayi ta kewarta,

Ni kaina ina son tuna baya,rayuwa tana da sauri,duk da haka in muna tare,sai in rika jin kaina tamkar ‘yar kasa da shekara ashirin.yayi dariya,a haka ni ke kallon ki sauda, kullum na kan ce, lokacin na sauri.ta kwantar da kanta a kafadarsa.allah ya kara mana tsaw rai da rayuwa mai amfani.a kunne ya rada mata amin.da ma an ce soyaya bata tsufa, sai dai masoya su tsufa, allah ka yi mana mai kyau. karfe bakwai alhaji bashir yana ta shiri cikin sauri,hajiya tana taimaka masa gurin saka kaya, rokonsa take yi ya dan sa wani abinci a bakinsa,ta ce don kai nasa a yi kunun gyada da kosai,saboda na san kana so.ya kalle ta,ta na saka masa liks a hannun riga ya ce,ki yi hakuri mata ta,ba komai,na yi alkawarin zan gana da wani mutum ne,wanda na fi wata guda ina neman damar ganinsa.

Ta ce,duk da haka ka karya zai fi.ya ce sai na dawo,domin in na samu damar da nike nema a gare shi,kasuwanci na zai ninka,in ko haka ta samu yaya kika gani?ta ce, umm! kai dai da ma kullum saurin ka bai wuce kasuwanci,a kasuwanci ina ne ba a sanka ba,duk fadin afirka ina ne sunanka bai kai ba! wane irin kudi ne baka mallaka ba kullum cikin samun riba ka ke. ta mika masa hularsa,me ya kamata ka nema kuma alhaji?yanzu baya ga aljanna? murmushi ya yi,ba tare da yaba ta amsar duk tambayoyin da ta jero masa ba.ta ci gaba, ni dai ba zan gaji da baka shawarar cewa,kamata yayi zuwa yanzu kayi murabus ka bar abba da mukhtar su jagoranci kasuwancinka.ya ce,ni kuma fa ta ce,ka zo mu zauna mu huta,mu karasa rayuwarmu,’yan kananan yaranmu su shaku da kai.ya saki dariya tare da cewa,sauda kenan.in ki ka fadi wata magana sai ki tuna mimi tadinmu na farko da ke.ta ce au!kana nufi maganar ma dana fada shirme ce?ya ce,kusan haka,kina cewa in bar ma su abba ragamar kasuwanci,ki na tsammanin za su yi jarumtar kasuwanci kamar ni?            bai jira amsa ba, ya ci gaba da cewa,da ma MIMI ce babba,ko da tana mace na san za ta iya.amma su abba shirme kenan,shi yasa kika,
Ga ko shawara ce na fi son yi da ita koyaushe ta na bani shawara ta musamman yadda ake fadada kasuwanci a duniya ta cikin yanar gizo. su kuwa su abba bakin ku daya.kullum in takaita kasuwanci a iya gida nijeriya,ni kuma na wuce nan tuni. ta ce,ka fahimce ni ba muna cewa kar kayi kasuwanci da waje ba ne aa,ai bunkasar ka ta isa ka yi kasuwanci da waje.harkar shigo da magunguna ne muka ce ka daina,tunda ana yawan zargin kana shigo da haramtattun magunguna da kuma miyagun kwayoyi. ya gyara zaman hularsa,ya sa hannu ya shafi kumatun ta, ki ci gaba da yi min addua sauda,ke ce kurum ki ke fada min son ranki in ji ban ji haushi ba.ya cire takalminsa tana fesa masa turare ya ce,ban sani ba ko zamu gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko yaya ne dai daga can zan wuce malumfashi. in duba su binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba. inda lokaci zan shiga masari can ma na jima ban je ba.kin ga sai na kwana kenan,gobe zan dawo in dauki uwata mu koma inda muka fi wayo.ta ce,allah ya tsare sai ka dawo din amma batun tafiya da MIMI ne nake tunani a kai.ya kalle ta, kamar yaya?ta ce,sai ka dawo dai allah ya tsare,ya dan tabe baki amin.suna fitowa falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da gaishe shi,ya amsa da daidai,ya kalli usaina,MIMI fa?ta ce tana kwance dady,ya ce,shikenan zamu yi waya.hajiya ta raka shi har mota,ba sabon abu bane,haka ta saba tun suna da kuruciya. falo ya kacame,yaran suna ta karin kumallo,sai hayaniyarsu da karar kofuna.

MIMI ta fito sanye ciki riga da wando masu dan kauri na barci. sauri ta ke yi,tare da fatan allah ya sa dad dinta bai fita ba,don ba za ta taba bari ya fita ya bar ta ba.ta iso gurin hajiya,fuskar ta babu annuri ta ce,ina kwana hajiya?ba tare da ta dube ta bata ce,lafiya lau.MIMI tayi tsaye shiru,tana son yin magana amma tana tsoro.hajiya ta dago ta dube ta,ga kayan shayi can a kan dining,na san ba kya shan kunu,ta ce tam!ehemm!da ma zan gaida dady ne,yana ciki ne? hajiya ta ce a’a.

(Zan ci gaba)…

*IP*

Tuesday, 25 September 2018

CANJIN RAYUWA Kashi na 1 Shafi 6-10 - ISMAIL SANI

CANJIN RAYUWA
[Kashi na 1]
(Shafi 6-10) Tare da -
Halima K. Mashi
Post By ISMAIL SANI

Hajiya ce ta janyo masa kujera ya zauna,ya kalli MIMI zauna mana uwata. Ya mayar da kallon shi ga hajiya sauda, an yi mata farfesun kifin? hajiya ta kalli MIMI cikin daurewan fuska,sannan ta ce,an yi,MIMI ta turo baki tare da hada rai. Hajiya tana zuba masu dan waken cikin plate tare da colslow,ta janyo wani plate din tana zuba masa farfesun kafar sa,ta tura gabansa tana fadin alhaji ba ka tambayi yaran gidan ba? ya kalle ta cikin ‘yar zolaya yace,duk ganin ki ne ya mantar dani. ko da dai na san zuwa yanzu suna lslamiyya ko? ta ce eh,yau kam ma da murna suka fita,don na gaya masu cewa kana tafe,ya ce ga shi ban riko masu tsaraba ba. amma bari in sa direba ya sayo masu,ta ce aa zai fi kyau ka fita dasu don yaran nan basa samun kulawarka,kamar fa sam basu shaku da kai ba.


Ya kalli MIMI wacce ta jibga tagumi,ya ce zan gani ko da lokacin,kin san fako a can ba samu zama nake yi ba.shiru tayi don ta san kome za tace ba fahimtar ta zai yi ba,ta jima tana yi mishi nacin cewa,ya dinga baiwa yaran ko da awa daya ne a cikin lokacinsa, amma sam ya ki.ko su da suke matansa basa ganin shi a kan lokaci,sai yayi wata ko sati uku in kuma yazo kwana biyu yake yi, nan guri ta ya kwana daya ya je malumfashi wajen hajiya binta ya kwana daya  tunaninta ya katse lokacin da ta ji yana tambayar MIMI menene uwata? na ga duk kin bata ranki?ki ci kifinki mamana. Ya kalli hajiya sauda ina kifinta?hajiya ta nuna kular da cokali,ga kular kifin nan gabanta?ta dauka mana ko a baki zan bata? MIMI ta sake tura baki tare da kallon mahaifiyarta,ni na koshi,hajiya sauda ta ce, karyarki dubu wallahi kin yi kadan ki ce a dafa miki abin, yanzu ki ce baza ki ci ba,saboda bakin raini ai na lura da ke tunda ku ka shigo gidan nan na san baki so zuwa ba, ko katsinar ce baki so zuwa ba oho miki, amma bakin ranki ya kare miki can.

Sauda! Alhaji ya katse ta tare da daga hannu, gaskiya ni bana son abinda ki keyi,a ce ke da ‘yarki ta cikinki amma ba ki kaunarta?….

Hajiya tace, ba kaunarta bane bana yi, halinta ne bana so.kuma in har ta ga mun zauna inuwa daya da ita to ta tabbatar ta canza halinta,in ko ba ta canza ba to sai dai ta nemi wata uwar ko da yake tana da ita ma.                   ya tausasa murya ai ba maganar fada bane, amma gaskiya ba zan iya kallo kina mata irin kalaman ba, kullum tana yi mini korafin ba ki sonta,ita in fada mata gaskiya ko dai bake ce ki ka haife ta ba?ya aje cokalin hannunshi,na rasa me take miki,ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba.sai ta zo hutu irin haka,amma sam ba kya ko yin kewar ta. hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba,wanda ta hada masa,a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce,halin ta kawai zata canza,in dai tana son soyayyata. yanzu baka kalli shigar da tayi ba? tun daga abuja ka sako ta gaba har katsina, kana mahaifinta ga shi kanta a waje,kayar jikinta duk sun dame ta,wai ita dole ta waye.
Ya kalli MIMI sannan ya kalli sauda, da dan murmushi,ina laifin kwalliyarta,ni ban ga aibun ta ba,haka ‘yan mata matasa irin ta ke yi.ya kalli MIMI,ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?tsaki hajiya ta yi ta nufi dakinta.sai lokacin MIMI ta samu damar yin mita,kaga ko dad,sai da nace ka barni can in gama hutu na,ka ce aa sai na zo, ni daman na san hajiya ba za ta taba so na ba. Ta mike tsaye tare da kallon jikinta,shiga tafa, mene ne aibunta?ya kalle ta cikin sigar lallashi yace, ban ga laifi ba.ita hajiya wai sai tace,sai na saka hijabi da atamfa,ni kuma ba zan iya sa iri wannan kayan zafin ba.na yi karatu na waye ni ba irin su usaina ba ce kauyawa.yayi murmushi,shgwabarta tana burge shi. kallon ta ya ke yi tamkar ‘yar shekara biyu. ya mike ya zagayo wajen ta ya dafa kafadarta,kar ki damu uwata. mamanki tana sonki,na san ta ga nafi damuwa da kene cikin ‘ya’ya na,kin san don ita ce ta haife ki,shi ya sa fa.in da a ce kamar hajiya binta ce ko nafisa da tuni na sallame su,kin manta na taba kora hajiya binta saboda ke?ta ce na tuna Dad, Ya ce to kar ki damu ina son mahaifiyarki ko da bata haifamin ke ba, bare ta haife ki.  kina son a ce mahaifanki biyu ba su tare?ta ce ba zan so ba dad.amma ka yi mata magana ta daina matsa min,ya ce zan yi mata, amma ke ma ina son cikin kwana biyun nan ki canza kaya sawarki,ki rinka saka irin wadanda take so.ta ce zanyi in dai za ta bar ni in yi abinda na ke so,ya ce za ta barki mana kin ji,ki dai na kuka.ya yi ta lallashinta har ta daina kuka.

Suna cikin cin abinci hajiya ta sake fitowa daidai lokacin yara suka dawo daga lslamiyya da sallama suka shigo, ita ce ta amsa sallamar,husna da hasina ne a gaba,suka ce sannu da gida hajiya ta ce yawwa sannunku da dawowa yara na.ina sauran? kafin suba ta amsa sai ga su suna ta yin sallama,da hannu ta nuna masu gurin dining,ga dadin ku,suka nufi gurin suna gaida shi da daidaya.ya dafa kan husna da hasina, su ne kanana a gidan, yana ta amsa masu.MIMI ta hada rai ita ba ta son hayaniya. dady ya ce,ba ku gaida sista MIMI ba.suka kalle ta don suna tsoron ta,sannu yaya MIMI,cikin daure fuska ta ce,yawwa,na amsa duka ne ba sai kowanne ya gaishe ni daya bayan daya ba.hasana da usaina sune ‘yan matan da suke bi MIMI a haihuwa.dad ya kale su ku shirya da kannen ku, yau yazo ya kai ku super market ku sayo tsarabarku, don ban riko komai ba, kowa ya je ya zabo abinda ranshi ke so.

Yara suka shiga murna hasana da hussaina suka ce dad,mu kam ba zamu je ba.ya ce,saboda me?suka ce,muna da karatun hadda gobe,malamin mu zai zo, bin abdulrahaman. hajiya ta ce,tabbas ba ku da halin fita, in ba haka ba zaku sha dukan tsiya gurin shi.duka kuma?in ji dad dinsu,hajiya tace sun wuce duka kenan?karatu sai da zare ido. abdulkarim ya yi sallam, ya shigo falo suka amsa,ya iso gurin dadin shima ya gaida alhajin.MIMI tana ta chatin dinta ba ta dago kai ba,shima bai ko kalle ta ba. ya dubi su hasana ya ce, kun dawo?suka ce eh! yaya sannu da zuwa, dazun hajiya ta fada mana zuwan ka. mun je dakin ku kana wanka, Kuma lokacin lslamiyya ya yi dole muka tafi.ya ce,na ji shigowar ai, ya ya zauna,usaina na fadin,lslamiyya lafiya,munyi murajaa ne yanzun. ya ce, kun kusa fara jarabawa kenan suka ce eh! hasana ta ce,yawwa yaya don allah ka amsar mana hadda in anjima mun yi magariba, gobe da safe muna da malamin gida bin abdulrahaman. abdulkarim cikin sigar tsokana ya ce, bani da lokaci,ku ce gobe zanyi kallon duka. usaina ta ce agaji yaya abdul, bulalarshi akwai zafi,suka sa dariya tare.ya ce,bari mu yi sallah sai in karbar maku,suka ce,yawwa yayanmu mun gode.
MIMI daga wurin da take zaune tana jin su tana kuma kallon su,sai ta soma mita,ni na san duk ‘yan gidan nan ba sa so na,dole kawai suke gani na,kalli yaya abdul,ko kallo na bai yi ba.alhaji yace,kai! abdulkrim,ya ce naam,ya zo ga ni dad.ya ce baka ga MIMI ba ne?ran abdulkarim ya baci,nan a take fuskarsa ta nuna,cikin wata murya marar dadi ya ce,na ganta mana dadi.shine ba za ka yi mata magana ba? Kafin ya yi magana hajiya ta amsa da cewa, in duniya da gaskiya ita da shi wanene gaba?shine ya kamata ya gaida ta,ko ita ce ya da ce ta gaishe shi?. alhaji ya ce,amma ita bakuwa ce.bayan haka kuma yaushe rabonsa da ganinta?a kalla ya nu na kewarsa gare ta ko?kan abdul yana kasa tamkar ya sa kuka don haushi da takaici.hajiya ta ce,bai gaishe ta din ba.tafi abinka abdulkarim,cikin sauri ya wuce.su hasana ma suka yi dakinsu ita ma hajiya ta juya zuwa dakinta,MIMI ta kalli dad,kawai mu koma kalli fa duk yanda suka watse suka barmu,ya dafa ta karki damu ina zuwa. baki gado hajiya sauda ta zauna ta zabga tagumi,wannan abin ya ci mata rai,a ce mutum kamar alhaji ya dinga irin wannan abu sai ka ce yaro.kirikiri yana gani garkiya sai ya runtse ido saboda son zuciya,bai san cewa haka zai sa kan ‘ya’yansa ya rabu ba ne?sallamar shi ce ta katse ta,ta dago ta dube shi,shima ya iso ya zauna bakin gadon.haba hajiya ki sakarwa ‘yarki fuska mana?ke ba abin faharin ki bane a ce nafi son ‘yarki,duk cikin ‘ya’ya na?

Ya kama hannunta cikin sigar lallashi ya ce,haba sauda kin fa san ina tsananin sonki, sonki ne fa ya shafe ta ko baki lura ba?ta daga ido ta kalle shi,ban musa ba,na san kana so na,amma ni burin na shine ka yi adalci tsakanin yaranka alhaji, ko don gudu rarrabuwar kansu. ya ce,menene na yi mata wanda ban yi masu ba?ta kalli cikin idon shi,ai ba za su kirgu ba,banda nuna tsantsar kulawa a fili, duk cikin yaranka wanene ka kai kasa wajen karatu bayan ita?to indan wannan ne,karatun na su na gida ya fina ta cin kudi sauda. umm, haka dai za ka ce,tunda kana son kare kanka,ya ce, ni dai ina neman alfarma ki sakar mata fuska ki dan ja ta a jikin ki har mu tafi.ta kalle shi,ta rasa me zata ce masa,sai kurum ta ce to. don tana son kawo karshen zancan, ya shafi kumatun ta,na gode,ya matso da bakin shi saitin kunnuwanta,ina son a kyuatata shimfida ta anjima. don na iso da muradin hakan.

Ta sake murmushi tare da kallon shi,wai alhaji yaushe zaa girma ne?ta yi tambayar cikin sigar wasa. ya janyo ta jikin shi,wa ya ce miki ana girma da lada? sai dai in mutuwa ce ta dauka.suka sa dariya tare, daidai lokacin aka yi kiran sallar.suka mike, ta ce lokacin sallah yayi bari in fita ‘yan mazan nan sai nayi fama sannan su wuce masallaci.tare suka fita ya nufi dakin shi,har lokacin MIMI tana zaune a falo.sai dai lokacin ta koma kan kujerar zaman mutum biyu tana ta chatin. Alhaji ya nufe ta yana cewa,mamana kina hutawa ne?ba tare data dago ba,ta ce eh dady.ya ce da kyau.ya wuce dakinsa. hajiya sauda ta dube ta,ki tashi kiyi sallah,ta dago ta kalli hajiyar ta ga fuskarta a daure,ta zabga mata harara na ce,ki tashi ki yi sallah.tsam ta mike ta nufi dakin su usaina inda nan ne take sauka in ta zo,kayan tama cikin suke.sai dai ita bata sm hakan saboda a abuja sasanta dabam, amma a nan hajiya ta hana a yi mata dakinta dabam.ta sami su hasana suna sallah, ta fadi kan gado ta ci gaba da chatin dinta. Ga al’ada alhaji in ya fita sallah (Zan cigaba)…

IP

Thursday, 13 September 2018

Canjin Rayuwa Kashi Na Daya Shafi 1-5 - ISMAIL SANI

CANJIN RAYUWA [Kashi na 1] -
Tare da Halima K. Mashi
(Shafi 1-5)

Hajiya saudat tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, ‘yar kimanin shekaru arba’in da bakwai zuwa da takwas,amma ba ta yi kama da shekarunta ba saboda kyan jikinta da kuma hutu. In an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya, kyakyawa ce mai cikar mutunci. Wayarta da ke gefe samfurin Nokia tayi ruri, cikin natsuwa ta kai hannu ta dauka tare da kallon fuskar wayar.

Kamar yadda ta za ta, maigidan ne domin duk yinin yau ba ta samu kiransa ba. Sallama ya yi,ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce, hajiya ki karbi bakuncin mu anjima. Cikin taushin murya tace, shine ba ka fada mini ba tun safe? Cikin lallashi ya ce, na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce, da ka nemi ta su usaina, kila network ne domin waya ta kunne ta ke, ya dan murmusa, ba mamaki zan iso da yunwa fa, don haka a tarbe ni, ta yi ‘yar dariya, wace irin yunwa? Shi ma yayi ‘yar dariyarsu ta manya, duk wata yunwa ta, da ita zan zo,ta ce, kar ka damu Allah ya kawo ka lafiya,ya ce,amin.

Ki sa a yi wa uwata farfesun kifi tare za mu zo,take ta hade fuska, tamkar yana kallon ta, ta ce alhaji don allah kar ka zo min da mimi. Ya ce, saboda me? Ta ce, ka san komai, alhaji MIMI in ta zo gidan ba, ba maaikatan gidan ba. Ta sani, na fada mata kar in sake ganinta a gidana matsawar ba ta canza halin ta ba, ba na bukatar ta.yayi shiru domin ranshi ya baci, kusan minti daya duk sun yi shiru.

Sannan ya ce,sauda, ba zan gaji da fada miki cewa ban jin dadin abinda kike yi wa MIMI ba gaskiya, zai fi kyau ki fito fili ki zage ni sai ya fi min sauki maimakon aibanta MIMI. allah! In ji hajiya saudatu,ta sake tausasa muryarta,ban san lokacin da za ka fahimce ni ba alhaji,amma kayi hakuri. in dai don mu zaka zo, to ka zo kai daya zan fi so haka. cikin dan zafi ya ce, sauda muna hanya kar ki manta da abincin ta na yau da kullum, ki fada ma duk ‘yan gidan wanda bai son ganin ta zai iya barin gida har sai ta tafi sannan ya kashe wayarsa.
Ta dan ciji lebe tare da lumshe ido cikin takaici, ba ta da zabin da ya wuce yin abinda mijin ta ke so. A fili ta ce ni kan bana son zaman MIMI garin nan,na tsani halin ta,a ce yarinya karama a bar ta tana yin yadda ta ke so.ta mike tana nunke sallaya.

Abdulkarim ya yi sallama, ta amsa fuskar ta daure,sannan ta yi tsaki, abdulkarim ya ce,lafiya hajiya?alhaji ne ya kira ni wai suna tafe shi da MIMI. abdulkarim ya ja tsaki,don jin ambaci sunan MIMI, sannan yace,ashe yanzu zan juya a kan sawuna mu gaisa kawai hajiya in sabi jaka ta,ai a wannan sati bani da darasi kamar yau,sai na sake dawo wa. hajiya sauda ta yi yar dariya tare da fadin haba abdul,ka taho tun daga zariya har katsina sannan ka ce mu gaisa kawai ka wuce saboda MIMI? Ta ci gaba da fadin ba zai yiwu ba.dauki jakarka kawai ka wuce sashin ku,ka watsa ruwa.barin in sa mutuniyarka tabawa ta kawo maka abinci na san yanzu sun gama na rana.ya ce,ai ni bana son rainin wayonta ne hajiya, a ce yarinya karama kanwar bayanka ta zo tana kawo maka rainin wayo, ba dama ka yi magana. Ni kuma kin sanni da zuciya sai in doke ta. hajiya tace,aa kar ka soma, ka san halin alhaji. ina fatan baka manta da yadda yayanka abbas suka kwashe ba,in ka tuna zungure mata kai kurum yayi,amma ta inda alhaji yake shiga bata nan yake fita ba.tsawon wata shida yaki ams gaisuwar abbas.sai da biki shi sannan alhaji ya sauko,shima sai da abokan abbas suka taro abokan alhajin aka hadu ana taba shi baki, sannan ya hakura da kyar da dokoki a kan ‘yarsa. Abdulkarim yayi ajiyar zuciya cikin takaici,sannan ya ce,ban manta ba.hajiya shi yasa nace, zan koma,tace ka hakura da harkanta.yace, gaskiya alhaji ba yayi mana adalci,a ce cikin ‘ya’yansa mu ishirin da biyu,amma ya zabi daya rak yace,ita ce star don kawai tana da sunan mahaifiyarsa.allah hajiya abin yana damu na, kanwarmu ce fa,amma ko shawara da ita sai abinda ta ce a family.
hajiya sauda ta ce,ku yi ta hakuri, dadin abin ita dai ta mace ce,duk abinta ai dole ta yi aure ko? abdulkarim ya ce, tabdi, wannan ‘yar jin kan? ya zauna a kujera, sannan ya ce,allah ya sa ta saurari wani. hajiya ta ce, ayya abdulkarim dole tayi aure. ba dai mace ba ce?shi kanshi zai so a bar masa ita a gabansa? abdul’ ya yi ‘yar dariya,sannan yace, kila ya ce mijin ya dinga biyo ta nan gidansa. hajiya ta ce, oho mishi su dai suka sani, suka yi ‘yar dariya,ta ce ba su lokaci kawai.ni dai ina ta fada ma allah,ku da ma na haifa ciki daya kuna jin takaici da haushinta, bare wadanda ba ni ce na haife su ba. Abdul ya mike tare da saba jakarsa,bari ni kan na isa dakinmu, hajiya ta ce, to ni ma bari in je babban kicin.   hajiya sauda ta tafi gefen babban kicin,ka san cewar gidan babban gida ne mai tsari,tun daga waje za ka san cewa mamallakin gidan ya tara abin duniya ba kadan ba.ta isa babban kicin din,mata uku ta samu a ciki suna ta aiki,suka maido da hankalinsu gurinta tare da yin mata sannu da shigowa,ta amsa da sannunku da aiki cikin girmamawa,ta kalli tsohuwar cikinsu ta ce,baba tabawa me aka yi da rana? tsohuwar tace,taliya ce ke kan layi da rana,da dare kuma zamu yi tuwon masara da miyar danye kubewa,ga taliyar nan ma yanzu na sauke.

hajiya tace to,a canza na dare a yi mana dan waken gari dawa sannan ayi shi da wuri.baba tabawa tace,maigida yana nan shigowa kenan?hajiya tace eh,suna tafe,suka hada baki guri cewa,allah ya kawo su lafiya.hajiya tace amin.sannan ta kalli jummai muna da kifin ruwa ko?jummai ta ce eh,hajiya ta ce yawwa ki dafa kadan kar ki cika yaji kuma kar ki sa tafannuwa.

sannan ki kula kar ya dagargaje na MIMI ne. dukkan su suka hada baki gurin tambayar har da MIMI ne za a zo?jummai ta ce, allah ya fishe ni yin kuskure. hajiya tace kar ki damu, sannan abinda kawai zan fada maku in tazo,ku kawar da kai duk abinda za tayi kun ji ko?cikin karyayyar murya suka ce to shikenan,tabawa ta kalli jummai kar ki sa mata tafannuwa, Wancan zuwan da ta yi maman sani daga sa tafannuwa shikenan ya zama sanadin korarta. jummai tace,zan kula insha allah. hajiya ta kalli ramma tace,da safe me muke da shi?ramma ta ce, shayi ne,hajiya tace,to a canza zuwa kosai da kunun gyada,ta ce to hajiya. tabawa tace akwai kafar safa ko wannan karon ba zaayi ma alhaji ba?hajiya tace,a dora zan dinga zuwa ina dubawa,na zata babu ne,tabawa mutumin ki fa yazo abdul,a kai masa abinci,ina magajiya?tabawa ta ce allah sarki abdul ne yazo zan kai masa ma da kaina maigida sukutum.hajiya ta juya tana dariya tare da fadin kowa ya duba abinda babu sai yazo ya fada min.

Da kanta ta nufi wajen me wankinsu yana ta gugar kayan yara,ta ce masa ka je ka fadawa mai gadi da mai kula da fulawa cewa MIMI za tazo anjima,sannan yau direba ya same ni a falo.ta sake cewa,danladi na fada maku ne don ku kiyaye bana son ana korar min ku,danladi yace,zan fada masu.ya nufi gurin mai gadi,ya turo mata direba ya sanar da su zuwan MIMI nan suka dinga tattauna rashin mutuncin MIMI,ya same ta tana duba nono a cikin firiji.domin tasan aladan shi ta sha furan dare.


Direba yayi sallama cikin girmamawa,hajiya ta amsa,ya gaida ta sannan yace,ga ni tace,malam yau da ma ina son sanar da kai ne,yau MIMI zata zo na san ba ka santa ba.amma ka samu labarinta?cikin in’ina yace eh naji gurin su danladi.tace to ka tafi filin jirgi tun misalin hudu da rabi,gara ka jira su,domin da jiran da suka yine wancan direban namu shine sanadiyyar korar shi da MIMI ta sa alhaji yayi.ya ce zan kiyaye insha allah.

Tun hudu yau ya nufi filin jirgin,jiran zai fi masa sauki da haduwa da fushin MIMI. biyar da minti talatin suka iso,Alhaji bashir aliyu masari ya fito daga cikin jirgi,MIMI tana biye da shi, sanye cikin riga da wando masu kalar pink sun dame ta tsam.sai after diress baka mai sheki,sannan ta gaba an ratsa pink hakanan rigar ba ta kai kasa ba.don haka ana ganin wandonta, dan siririn mayafinta ba shi da girma, Shima pink bai rufe dogon gashinta ba.          Kafarta sanye cikin takalmi shima pink dinne,da ratsin baki marar tudu mai igiyoyi,purse din hannunta da wayoyin ta kirar nakia duk kalar pink ne.can sama goshinta zaka iya kallon wani katon gilashi irin wanda wayayyun ‘yan mata masu jin kansu suke sakawa.da gudu yau ya nufe su domin duk da bai san MIMI ba ya san maigida na su.cikin ladabi ya yi masu sannu da zuwa,ya amshi jakar hannun alhaji, alhaji ne kawai ya amsa, MIMI kan ko kallon shi ba ta yi ba. ya bude kofofin motar sannan ya sa jakar alhaji a kujerar gaba,bayan sun fito daga filin yana hawa titi zai raraka da gudu,alhaji ya ce tafi a natsuwa MIMI bata son gudu,yau yace,to ranka ya dade.  shi kanshi mai gadi a waje ya tsaya yana jiran zuwan su,yana hangosu da gudu ya nufi ciki ya wangale get din,kamar yanda MIMI ke so,don bata son jira.ko da direba ya tsaya ya bude masu sannan ya cire jakar ya bi bayan su MIMI ta kalli gidan sannan tace,Dad gidan nan yana son fenti yayi datti,ya yi ‘yan kalle-kalle,yace,na lura da haka za a sabun ta shi da fenti.direban ya ajiye jakar a kujera sannan ya kalli alhaji Alhaji, na barku lafiya ya fita.Alhaji yaso ma kiran hajiyata-hajiyata,ta fito,dankwali a hannun ta,domin lokacin ta gama saka kayan,ta yi adonta cikin super kalar blue da ratsin yellow sai kamshin turare take yi.

Ta kalli mijinta, sannu da zuwa alhaji,ya ce,yawwa sauda ta dubi MIMI wadda tunda suka shigo falo ta natsu saboda duk iya-shegenta tana tsoron uwarta,ta san hajiya sam bata daukar reni.ta dago ido cikin fargaba ta kalli mahaifiyarta sauda tace, sannu hajiya,ta amsa yawwa,ya mominku nafisa da kuma sauran kannenku?ta ce kowa lafiya,hajiya ta ce,masha allah,ta dauki hular alhaji da jakarsa da kuma malun-malun dinsa ta nufi dakinsa tana fadin za a hada ruwan wanka ko? aa rabona da abinci tun safe shima ba wani abinci na ci mai nauyi ba coffee ne,ta karasa dakin ta aje kayan hannunta ta fito tana fadin mu je Dining.

#ISMAIL SANI

Sunday, 8 July 2018

BAYAN WUYA SAI…… Page 5 & 6 By Ramlat Y Salis


✨🌟✨BAYAN WUYA SAI……✨🌟✨



             ✨NA ✨
    RAMLERT  y salis ✨✨✨✨✨✨

  🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝📚



DA SUNAN ALLAH ……...YA ALLAH KANUNA MANA GASKIYA ,GASKIYA CE KABAMU IKON BINTA .KANUNA MANA KARYA,KARYA CE KABAMU IKON GUJEMATA.

 ✨ Wannan page nakane ya mustynahsadaukar wace agareka ✨





✨page 5💲6✨
Soyayyahce ta shiga tsakaninmu mai karfi,muna son juna sosai afifah mahaifinki dan kanin babanane,tun lokacin damuka hadu dashi bayan dawowarsa daga karatu,nadena kula kowane saurayi a family domin nasa a raina shine zai zama mijina.

   Akwai wani dan kanin babana shine likitan family dinmu,duk wani rashin lafiya daza'yi ko wata matsala data shafi lafiya shi ake sawa saboda babban likita ne,ninasan akwai mutunci a tsakaninmu ammah bansan yana sonaba,kuma akwai shakuwa sosai atsakaninmu.amma banTaba sanin yana sonaba sai da babanki ya dawo muka fara soyayyah, har manya sukashiga tsakani,yanemi soyayyahta alokacin danikuma babanki nake so hakuri nabashi ammah yaki hakura wai ai tunkagin nasan babanki shinafara sani kuma nasan yana sona,sosai abun yaso yaxamamin matsala dan akwai mutunci sosai a tsakaninmu banason muyi rabuwar rashin kyautawa.ammah fir yaki saurarata waishi dole sai najanye daga kula mahaifinki shibayaso,kuma shi auranmu nankusa yakeso bazai iya jira har sai shekara ta
Zagayoba sannan ayiba,

  nashiga damuwa sosai akan,lamarin dannarasa taya zan rabu dashi batare da ansamu matsala a zumuncinmu ba,Ana hk su babana suka kirani akan zancen mahaifinki,ban6ata mudu lokaci ba na amsa cewa ina sonsa.babana yayi farinciki sosai hakama baban mahaifinki har aka yimana baiko bansan waye ya sanar dasu muna soyayyah ba.

  Watarana da yamma ina zaune a falo a part dinmu,sai ga dan kanin babanmu yashigo a birkice wato likitan family din,gabana yazo ya tsaya Yana huci,inna kulama kamar hawayene afuskar shi da yatsansa yanuna ni yana cewa "nizaki yaudara menayi miki meyesa zakimin haka kinsan yadda nake sonki basai nafadamiki ba,ammah wai naji anyi baikonku jiya da wannan banza.tsawon wane lokaci muke tare dake ammah baifi wata daya da dawowarsa ba zaki zabe shi akaina mena miki haka"jikina rawa ya fara nayi zaton dukana zaiyi sai kuma yatsugunna yarike kafata yana kuka yanacewa"ki taimakeni karki barni dan Allah kicemusu kinfasa wlh bazan iya rayuwa  babu keba,nasan nayi kuskuren kin fadamiki ammah nayi tunanin kinsanine kin fahimci inda na dosa,bawanda yasan da irin son danake miki sai mahaifiyata kiyi hakuri karki barni"
 Afifah nashiga rudani alokacin sosai nafarko naji tausayinsa sosai sai naji konajenye ammah dana tuna irin son danakewa babanki sai naji bazan iyaba yin abinda yaceba,na dai samu na rarrasheshi tsawon kwana biyu. Kullum muna wasan yar buyadaga karshe mukayi wata haduwa a school bansan yana binaba har na isa,fadamasa
Gaskiya nayi sosai mukayi rigima muka rabu kancewa "bazai bari na auri kowaba inbashi ba sai dai muyita zama haka dagani har shi"ni dai kawai najishine ammah gani nake bai isaba,haka suka kulla gaba da babanki ko gaisawa basayi.

  Ana saura sati daya bikinmu nida mahaifinki,duk wanda za'a aurar a shekarar muka hadu a babban falon babana yayimana nasiha,sannan yace dukkan mu za'amana gwajin jini dan a tabbatar kowa na lafiya kuma asan matsayin jinin kowa kamar yadda akasaba.
Dahaka aka fara gwaJi har akazo kanmu nida babanki likitan damun hada ido sai yayi murmushin mugunta niduk ban kawo komai araina ba,Afifah ashe akwai abinda yake shiryawa,wannan mutumin shine silar shiga matsalarmu domin shine ya hadamu da iyayen mu.
 Daya gwada jininmu sai yace wasu babanmu ai akwai matsala,"cewa in mukayi aure dani da babanki jininmu zai bada sikila wato zamuna haifar yara masu cutar sikila"dafari bamu dauki abun dawata matsalaba sai damukaji irin illar sikila.
 sosai iyayen mu sukayi bakinci Suka cemasa meye to mafita sai yace"Ai bawata mafita gaskiya sai dai muhakura inkuma bamu hakura ba to zamuna samun yara marasa lafiya"kowa ya girgiza da zancen sa shima sai yanuna kamar abun bai masa dadiba.
 Haka aka tashi daga taron kowa jikinsa a sanyaye,nikam har da kuka, nida babanki aka kiramu bayan  munje su babanmu suka cemana to su dai da ana haifar yara ba lafiya kuma abun zaiyi yawa tunda munsan auren family akeyi gara mu hakura da juna,sai kowa a canza masa abokin zama.
Tashin hankali mukashiga sosai,mun rokesu akan su barmu amma sam sukaki haka har aka tashi daga taron.
  Acikin kwana uku na zabge sosai nayi rama duk nazama wata iri,bani da aiki sai kuka narasa ina zansa raina,hakama babanki kullum yana cikin damuwa.
shawara babanki yazomin da ita kancewa "shifa bai yarda da abun da likita ya fadaba akan gwajin jininmu yafadane dan yana son yasameni"sai daya fada sannan nima nayarda hakan zai iya kasancewar.

 Asibiti muka tafi mukaje gurin wani babban likita Yasake yimana gwaji anan ya tabbatar mana bamu dawata matsala ajininmu zamu iya yin aure.
 mamaki mukayi sosai dajin abinda yafadamana,Anan muka tabbatar abinda likita yafadawa su baba karyane yayine dan a rabamu da babanki.
Da murna muka koma gida muka nunawa su babanmu ammah sai sukace karya mukeyi zuwa mukayi akayimana result din karya dan su amince mana kuma ma ai likita bazai mana karyaba.
 ina kuka ina musu rantsuwa ammah basu sauraremu ba,kowa kin yarda yayi da zancen.
 likita nasamu
Narinka rokonsa akan yayi hakuri yafadawa su babanmu gaskiya ammah sai cewa yayi "aishi yafadamin baxai iya kallon na auri wani bashiba"
Bawanda bamuje gurinsa yarokesu  suyardaba ammah abun yaki yiwuwa,kullum saina kira babban yayana ina masa kuka har garashi shiyana rarrashina sosai yamin nasiha akan nayi yadda sukace.
Babana sosai ya tausayamin ganin yadda nakoma,haka zai zauna yana rarrashina yanatamin nasiha inyi hakuri inyi yadda suka umarceni saboda gujewa shiga matsala kar azo asamu yara Marasa lafiya,kuma in yace zai barni na aureshi yan'uwansa zasuga kamar yayi son kai saboda ni 'yarsace ya gwammace akawo musu matsala cikin family,duk dacewa shine babban su ammah suma sunada hakkin yake hukunci akan yaransa,kuma bantaba neman abu agurin sa narasa ba to shima yau yanason nayi masa wannan alfarmar nanemi abu yabarni na auri wanda nake so ammah bai barniba na daure nayimasa wannan alfarmar"wannan itace maganar da mahaifina yake fadamin duk sanda naje masa ina kuka.
 mahaifiyata Itama tana bani baki sosai,itama tashiga damuwa ganin yadda nakoma.kowa bani baki yakeyi gara nahakura akan nasa yaran dazan haifa a matsala.
    
   Dahaka na hakura,inaji inagani karyace aka mana, ammah nasamu mahaifina nace masa duk mijin dazasu canjamin karsubani likita,ya tambayeni meyesa bance masa sharrine gwajin dayayi manaba,kawai cemasa nayi ba komai.
Alkawari yamin akaro na biyu zai bani duk wanda nake inhar ba irin waccan matsalar,amince masa nayi yabani duk wanda yakeso ammah banda Likita domin zan iya zama da kowa banda wanda yayi silar rabani da babanki.
wani daban,aka bani wanda zan aura,shina mahaifinki aka basa wacce zai aura.alokacin har nafi mahaifinki dauriya domin sai da aka kwantar dashi a asibiti yana rashin lafiya sosai,
  Ana gobe za'a fara biki,kwanwar su babanmu ta ido da duk yan'uwa wanda ba a kasar sukeba.har babban yayana da matarsa.
 Da kwanwarsu babanmu taje asibiti duba babanki sosai hankalinta ya tashi ganin yadda yake,nima danaje dubashi asume aka
Dawo dani,hakan yakara tayar da hankalinta.
Su babanmu tasamu tace tazo da shawara "ita a ganinta su barmu mu auri JUNA tunda kowannenmu na cikin damuwa"basu yarda da zancen taba, sai datasa wani sharadi nacewa"duk dan dazan haifa bazan shayar dashi nono ba aranar dana huihu za'a dauke yaron har sai ya girma,tunda bai sha nonoba ba'abunda zai sameshi"duk da haka basu amince mataba,sai data tsugunna akan gwuiwowinta har hawaye nazuba afuskar  tace"tun tasowata nake karkashin umarninku amatsayinkuNa yayuna,ina da wanda nake so ammah kukace nima auren gida zakuyimin ba yadda na'iya haka nabi umarninku dan kawai inmuku biyayya ba dan banason saurayinba,ko bayan aurena duk abinda kukace haka nakeyi dai dai da rana daya bantaba sa6awa umarninkuba har zuwa yau danake durkushe a gabanku.ashe nima kenan baxan iya kawo shawara ku daukaba bazan iya yankewa yayanku hukunci ba kenan.ko bayan ranku dolene na rungumesu domin nima tamkar yaran cikinane,yadda suke nunawa junansu soyayyah koda an aurar
Dasu ga wasu daban,bakwa tsoron sukasa rabuwa da juna kowannensu da aure kansa ammah suna bibiyar juna,in har aka rabata da dan dazata haifa bai sha nonontaba ba'abinda zai samu yaronta tunda dama duk wani abu ta nono yara  suke sha,da wannan nake neman afuwarku ku duba sannan ku yanke hukunci .

  Anan suka yanke hukunci akan shawararta cewa sun amince da sharadin aranar dana  haihu zasu dauke dan ko 'yar su kaimata dan inhar zasu bar dan a kasar nan zami iya zuwa.
wasu sunyi murna wasu kuma ba
Suyiba,dan suna ganin araba uwa da danta data haifa aranar bakaramin damuwa bane.
Dani da babanki farinciki muka shiga,sosai mara misaltuwa,wasu na gargadina kar nasake nayarda ace daga na haihu za'dauke dan gara na auri wani daban,Nikuma jinsu kawai nakeyi dan gani nake gara hakan sosai da'arabamu,shima babanki haka yace gara haka sau dubu da a rabamu.
Afifah biki akayi wanda ba'ata6a irin saba a family,mu shida  aka aurar mata uku maza uku.babanki shine auta agun iyayensa nikuma nikadaice mace Dan haka akayi 6arin naira sosai,afifah inkinga gidana acikin family hause zakiyi mamaki domin ankashe kudi sosai wanda hankali da tunani bazasu iya daukaba.
Daga kayan danasa ranar kamu zuwa ranar party,ranar budan,kai har ran daurin aure,afifah kudinsu baxai dauki hankaliba mahaifiyata da babban yayana sune da wannan aikin, abunda zan iya tunawa iya sarkokin danayi amfani dasu abikin zasu kai millions arba'in,takalma da jakunkuna sun kai millions saba'in,haka wasu agoguna da mahaifiyata tasiye Su da dadewa bansa nita ajiyewa ba suma sunkai millions biyar.komai nawa danasa abikin makudan kudine suka siyesu,har abin yafara zama surutu a family sai da'akaje gidanama akafara surutu masu mamaki nayi masu gulma haka,afifah dakin ganni alokacin zaki dauka wata sarauniyarce zata gasar kyau,ranar daza'akaini babana yamin nasiha da mahaifiyata da yayunama nayi kuka sosai duk da acikin gidanne naji radadin rabuwa dasu.


 Alokacin da akakaini part din kakarki tawajen uba,wata abaya tadauko wacce Akayimata ado da gwal wacce ta,kai millions dari har dawani abu ta nadamin da kanta,kowa mamaki yayi sosai wasu na guda cewa tayi kowama ya dena mamaki dan da a lefe zatasa ammah saitaga gara sai nazo dan haka yanzu nazama autarta tunda nazama matar auta,haka take cewa babanki.

    Rayuwa mukayi da babanki cikin kwanciyar hankali ga dumbin soyayyar damukewa juna,kyau nakara sosai nayi giba.babana sosai yakejin dadi duk sanda naje gaisheshi hakama mahaifiyata take koyamin business irin nata.
Hakama surukata tana kula dani sosai inada masu yimin komai tamkar diyar sarki.

 Rayiwatamin dadi soyayyah muke da mijina sosai,ana haka har nasamu ciki ananma na fara samun wata kulawa ta musamman ammah damun tuna za'a dauke abunda zan haifa abin sai yafara damunmu.

 Aranar dana haihu na haifu yarana yan biyu duka maza,kowa yayi farinciki babanki yayi kuka har dana murna, kowa na murna aranar.

 aranarne kanwarsu babanmu ta sauka a kasar,sai kuma nashiga damuwa ganin da gaske za'adauke minYarana kuka nayi sosai sanda za'atafi dasu hakama babanki.kakarkice take ta rarrashina ammah gani nake duk abanza ace na haihu yarana badu dan dani nono naba kuma a daukesu.
kullum ina cikin damuwa har nagama wankan jego asatin dana gama babanki yamana biza muka tafi ganin yaranmu.

 sun danyi wayo,dukkan du da babanki suke kama sai dai babban farine sol karamin kuma ruwan tarwatsane inaji ina gani na baro yarana muka dawo gida.
 tun muna damuwa har mukadaine,mahaifiyata nabani hakuri sosai haka Ma surukata.mun koma rayuwar mu kamar da kamar ban haihuba,cikin so da kauna.


 Ana haka nakuma samun ciki na haifi 'yata mace mai kyau itama kamat babanku ruwan tarwatsane fatar ta.
 afifah haka itama aka rabani da ita hakan yadame mu sosai nida babanki har zuwa mukayi muka samu likita muka rokeshi akan yaje ya fadamusu gaskiya ammah ko saurararmu baiyi ba.
 Bayan shekara biyu sai na kuma samun ciki,dana fadawa babanki sai yace kar infadawa kowadanshi yagaji bazai iya kara bari arabamu da dan
Dazan kuma haifaba.

  Aiki ya nema a saudia kuma akayi sa'a yasamu kuma zasu bashi gida da motar hawa.fadamin yayi cewa"zamu gudu mubar mudu kasar bazai kara bada dansaba,bazamu dawoba har sai abinda zan haifa ya girma sunga bawata cuta dayasamu daya sha nonona".nima sosai nayi farinciki da shawararsa,kuma ba wanda zamu fadawa inda muke.
Wannan shine babban kuskuren damuka aikata,sai tasaki kuka mai ban tausayi ta rungume afifah tana kuka tana cewa"kece muka haifa afifah damuka gudu saudia"
Aranar dazamu tafi sai damukaje gidan kowa da kowa muna musu sallama bayate dasusaniba,

 Nayi kuka sosai dan zanbar iyayena da 'yan'uwana babankine yaita bani baki har nadena.
abinda yasa nakasa manta saudia saboda nasan canne ake aikin haji,inna tuna wannan sai ingane saudia muka gudu.12:00pm jirginmu zai tashi aranar,kuma aranar ne kanwarsu babanmu taxo wai ta kawo 'yan biyu wai ta yaye kanwarsune tafara cin abinci,'yan biyu kuma alokacin suna tafiya ko inaabin sha'awa kamar yaran turawa.
 Ba abinda muka dauka sai bizanmu da wani abun hotuna bikinmu wanda babban yayana yamin,abun security akesamasa bamai budewa sai wanda yasan sunan da'aka saka kums sunnan,babban yayana nasa akan abun mai kama da karamar tibi,afifah abun yana gida yanzu haka sai dai bawanda zai tunamin sunan yayana da yabude kinga hotunan family mu baki daya.


lokacin dazamu tafi goman dare tawuce 'yan biyu suna part dimu alokacin karamin ne yake kuka sai babanki yasa aka maidashi gurin mai renonsa dan yana da
Kiwiya sosai,
babban kuma yana hannun babanki har muka fito harabar gidan,mahaifinki yace bazaima maida sshiba dashi zamu tafi.kin yarda nayi nace bai kamata arabashi da dan'uwansaba,haka muka fito dashi har muka isa airport ina kuka.


  

 Damuka isa babanki ya kira gida a waya yafadamusu sudena neman yaron yana gurinmu,dukace masa ina mukaje bamu kwana agida ba,cemusu yayi munbar kasar har saina haihu zamu dawo.fada sukayi masa sosai kuma akancewa mudawo aranar,ammah mukacire layin wayarma mu
 Ashe kusan wayarmu ta karshe  kenan,munzalinci kanmu mun manta rayuwar mu ba'a hannun mu takeba.

     karamar yarkoyo RAMLERT y salis  ✍🏻  inajin dadin addu'oinku da encouraging dinku ALLAH yabar zumuncin KAUNA masoya.