Tuesday, 13 March 2018

'YAR KWALLIYA Page 31-35



'YAR KWALLIYA Page 31-35
.
Amal tace beyi karya ba ai shi gayu ne kukuma haukane  Abu tace Binta gyara kiga da alama harda ita zamu hada tintini nakeso na koya miki hankali kunyar hajiya nakeji shiyasa nake shiru  Yace Dan Allah ki bari na kirawo gidan mahaukata ina tantaman hankalin su wlh  Abu da Binta sukayi kukan kura sukayi kan malam bashiri Muta nan gurin suka rike Abu da Binta  Abu tace bakomai muna nan ai zaka kuma fadan wani abin mara dadi kaga yanda zamuyi dakai  ke kuma zamu koma gida  Allah ya kaimu nima so nake na koya muku hankali kucakai kawai        Amal ta koma ta zauna                    Abu da Binta suka zauna suma suna huci  Malam dayayi karatu saiya juyo ya kalle su sukuma kwafa kawai sukeyi Abu na Sosa hannu Amal rai a hade hararar su abu da binta take ta yi  Amal ta jiyo wata a bayan su tana cewa basuda hankali inba hakaba mezesa suyi yinkurin dukan namiji   Ta kusa da ita tace yan qauye ne bakiga shigar suba ba hankali bansan abinda zasu daukaba da waccan ta taho dasu ta nuna Amal  Amal tace ba laifinku bane laifin sune da basu kama Kansu ba har mata marasa  aji irinku kuke gaya musu magana cemiki akayi bamu san komai ba mekalan dangi irinki  Ke banyi dakeba in banda shisshigi meye naki nasa baki dake nayi ni da yan qauyan can nake qucakai dasu nake kalan dangi kuma iyawane watama tayi mu gani  Amal ta girriza kai "a'a bada niba Wannan saiku dadinta nidai a gidan ubana nake ba wankewanke da shara nake yiba  Yarin yar ta fashe da kuka yanzu nizaki yiwa gori dan kinsan mahaifinki nadashi muma aibamu muka dorawa   kanmu talau Ciba dadinta ba a gidanku nake wanke wanke da sharaba balle kifada min magana   Abu da binta suka baro inda suke suka dawo kusada Amal dansu tabbatar da abinda sukaji  Amal tace Niban fada miki maganaba nadai tinatar dake ne idan kin manta koke wace shine kawai   Yarin yar tace wlh saigin gane koni wace da zaki fada min magana zakiga gatan me wanke wanke da shara  Abu tace Alhamdulillah naji dadin haka Wannan magana tamin dadi Amal matsa dan Allah kije ki turo duk wanda kika ga dama amma gashe da ki nuna mishi   Abu da Binta suka rufeta da duka duka bana wasa saida suka tara mata gajiya sannan suka barta  Malamin bita yayi iya yinshi akansu rabu basu rabuba saida suka gadama  Abu tasa i hu tace naji dadi wlh da wacce takeso itama mu Nada mata na jakine ko da wacca zata shigar mata   Kowa yace a'a  Binta tace shegu sunji tsoro dagun shigar mata  dakun ga danyan kai  
.
Yarin yar ta dago tana kuka tace ni kika yiwa haka ko bakomai kamar ni kucakan nan zasuwa haka gaskiya na fado idan bandau mata kiba  Abu tace dama dukan be ishe niba dan Allah kidau mataki ni zan iya sugun nawa akan kidau mataki  Base kin tsogun naba nariga nayi niya kuma sai nayi ta Ciro waya tana yauki jiki yayi tsami takira kannen ta tace su daho ta kashe waya  Malam dai abi mamaki yake gani "Allah yasa bani yaran nan zasu yiwa hakaba da an samu matsala ke ya nuna Amal yace zo  Amal taze            Yace wayan can yaran anyafe musu bita base sun zoba subari in anfara koyawa sazo  Amal ta jinjina maganar "nafada musu komai bazasu yarda su zauna agidaba indai ni ina zuwa karka damu hakan baze sake faruwa ba  Yace Nasani indai ta maganar ki zanbi amma sudinne kalli fa ki gani sun rabamin aji2 wancan nacan wancan nacan   kutsiri tsoma kawai sukeyi memakon su maida hankali a abinda ya kawo su kinga hakan be dace ba ko  Eh zan musu magana hakan baze sake faruwaba   Yauwa nagode meye sunan ki  Amal  Suna me dadi  Nagode Amal ta fada taje ta zauna   Abu da Binta sunsa 'yar mutane a tsakiya da tayi magana saisu dungure mata kai har aka tashi   Suna fita suka ga yan uwan yarin yar sunzo Abu ta kare musu kallo  A yasine "ni na dauka zanga wasu manya manyan mutane shine zaki turo min wayan nan da basufi nasa bulala na Zane suba  Yarin yar tace kibar rainasu barga ninsu sirara karfine dasu bana wasaba shiyasa na kira wosu  Binta tabisu da kallo 1bayan1 tazaga yesu ta tofar da yawu " nina dauka zanga rin dina guda shine zaki aiko saura yan nan   guda3 tomu maza ma 5 sun mana kadan a duka balle Wannan abin ta nuna kannenta mata da suka zo  Ke karki sake ki zage mu jikufa niba zan hada jiki da kuba Balle Ku goga min halin qauye da bulalana nazo na Zane ku  Gaskiya kin kyauta da kika rage mana aiki kika tahoda abinda zamu zaneki dashi cewar Amal  Yarin yar tace waime kuke jira Ku Dakar minsu indai kun cika kannena nane ku ciki1 muka fito daku kuramamin dan na tab batar da haka  Yaran sukayi kan su Amal Abu Binta         Abu da Binta tuni sukayi kukan kura suka rufar musu bayan sun gama dasu suka hada da yayar tasu Wannan karan harda Amal a dukan su   Abu tace Ku dena raina qauye duk abinda kuke takama dashi Akwai a qauye nasan ba zuwa wanke wanke da shara harna tsawon sati  Binta tace ba fita kice amuku ruwan zafi idan ba aso kujima a gida dan kar a kore Ku daga aiki  Suka je suka shiga mota suna dariya suka barsu a kwance   Haka suka jera sati1 suna zuwa bita wataran ayi dadi wataran kuma ba dadi dan kuwa su Abu ne suke nemo   fada wataran Amal ta tayasu wataran kuma tabarsu su cika aiki da kansu sun gama bita zasu shiga koya gadan gadan
.
  Suka shirya tsaf dan tafiya Kaya iri1 suka saka   Abu tace nakagu naga munfara KWALLIYA kinga KWALLIYAR da nagani a wayar yar ajinmu irin na amaren nan yamin kyau sosai sai lokacin nasan asheni ba KWALLIYA nake yiba  Amal tace Alhamdulillah Gwanda da Allah yasa kika gane yanzu kya dena KWALLIYAR Aljanu ta bakin yaya Aqeel  Waaaa ba abinda zan dena harse na iya waccan tukun na kalan nayi saki na dafe Allah sarki nunar rana gidan ba dadi da basa nan wlh   Hmm yaya yace a siya muku waya ze tema kamuku sosai na fadawa daddy yace ze siya muku  Binta tace da naji dadi wlh dankuwa wayata cika zeyi da hotu nan abinci iri iri  Kura kyaci da Gashi sudai bazasu ciyuba saidai ki kalla da ido ki hadiyi yawu shine kawai  Amal ta fada tana dariya  Amal kenan lokacine da kanki zaki dena cemin kura niyanzu hanka lina ya kuma school wlh jibi zamu fara Exam   Abu ta zaro ido "hakane fa ni harna manta wlh idan mun dawo sai muyi karatu  Amal kallon su kawai take tana dariya "kaji student Allah ya te maka yasa Ku fito da saka mako me kyau   Suka ce Ameen  Binta tace mutafi karmu makara dan naga matar nan hakona kawai takeyi   Meyasa take ha konki baki ce mata tsaka ninki da abinci Akwai amana ba da zata ce miki haka Binta  Binta tace yauwa *point of correction* sunana *Fatima* ba Binta ba idan ya miki tsawo kice min *tima baby* zan amsa inata so na fada miki mantawa nakeyi  Amal ta zare ido ta saki baki ta zube kasa tana kallon binta " menake ji Binta kicemin bake kika fadi hakaba nidai banida matsalar kunne fa  Abu tace kunnan ki lafiyarsa kalau nima daga yau karki sake cemin Abu sunana *zainab* idan kuma zainab yamiki tsawo kice min *zee baby* duk1 ne Amal karkiyi  mamaki *levels don change*   *Oh my God what a surprise* amma kun shammaceni  Amal ta bisu da ido cikin mamaki           
.
   Abu tace Shammata ba batun Shammata  Anan makaranta fa muke zuwa taya zaki dinga gaya mana wani suna mara dadi ga namu na yanka  Binta tace Kalan yan ajinmu suji sufara kiran mu dashi ga yan makaranta da tsokana  Amal tace tab A she daddy beyi asarar kudin ba kukara kokari kufi haka Allah ya te maka    Suka ce Ameen mutafi   harlokacin Amal kallon su takeyi cikeda birgewa harsuka je suka dawo Abu baki falda maganganu taci Sa a hajiya na falo da sauri ta karasa gurin ta  Mommy kinsan me fuska nashan wuya Anan wlh kinga irin abinda A kanuna mana kuma wai duk a fuska ake amfani dashi   Binta tace kut fuska nashan wuya ko abinci nashan wuya mommy kinga irin kakalan da akewa abinci kuma idan angama ya tafi ciki  Abu tace injiwa kinga kayan KWALLIYAR da ta nuna nana ne shine zakice wani abinci karki damu idan aka siya min zaki gani  Binta tace ba wani nan ke kinga kayan banzan da aka zuba wa a girkin da mukayi yau ne tin ina fahinta harna dena saida aka gama naci tukunna na gane komai  Hajiya da Amal Suka sheke da dariya   Hajiya tace Allah binta da fatan dai yayi dadi  Sosai ma mommy zanmuku shi amma ba yauba   Amal tace harna kagu naga girkin daya tafi dake Binta saidai kinsan me yanzu kika fara ganin girke-girke iri-iri   
.
Binta tace da naji dadi kinsan yanda nake son kirgin karyan nan kuwa idan na gama koya babban gidan abinci zan Bude fa kuma kuma zan koya muku  Abu tace nikuma gidan KWALLIYA kekuma Amal gurin dinki zaki bude amma muna kusa da juna kowa zekoyi abinda kowa ya iya  Hajiya tace insha Allah kumai da hankali a abinda kuke koya banda fada baruwanku da kowa      Suka ce to mommy   Abu tace mommy ai munyi sanyi sosai ma tambayi Amal a sati befi muyi fada da mutum 2 ko 3 ba aikin ga da sauki ko  Amal tace sosai ma yanzu dai gobe kushirya mu shiga kasuwa kowa ya siyo abinda akace musiyo naji kunyi shiru ko ba a ce Ku siya bane  Binta tace tafada mana yanzu na keso na fadawa mommy  Hajiya tace Amal idan kudin gurinki baze kaiba ki fada min na kara muku Abu Binta kuje kuyi karatu gobe jara bawa  Abu tace hakane bari muje   Amal tace kujirani muje kunayi ina jinku  Taho to suka tafi suna wasa da dariya hajiya ta kalle su tayi murmushi "Allah ya raya minku    
.
Abu da Binta suka jera sati1 suna zuwa zana jara bawa sai su raba dare suna karatu Amal dakinsu ta dawo da kwana tana   temaka musu saboda ita jami'a take zuwa hankan yasa su Abu da binta suke fahintar abinda suke karan tawa hakan   besa sun dena zuwa koyan KWALLIYA da girkiba sun bawa komai lokacin shi jiran ranar da za a basu hutu da saka   makonsu suke jira duk sunbi sun hana Amal sakat daga sun tuno saisu ce mata na nawa zamuzo sai tace musu na 1  Binta tace Amal ni saina ga kamar ba gaskiya kike fada manaba  Amal tace ban fa himtaba kodai duk irin karatun da mukeyi yatashi abanza   Abu tace kamarya yatashi a banza bam fahim taba   Kin fahimta hankali kawai zaku raina min woto idan munyi karatu idan kunje makaranta sai kuyi wasa ko    Binta tace injiwa bakiga yanda muke cika paper ba  To idan hakane karku sake damuna kusa a ranku cewa zaku fito da saka mako me kyau kunga ne ko  To munji    Yau zamu gama namu jara bawar natafi   Saikin dawo Allah ya bada Sa a  Ameen nagode muku   Tashirya ta fita Amal na fita suka shirya zasu tafi makaranta dakin hajiya suka je suka sanar da ita tai musu addu'a Suka wuce makaranta  Suna shiga aji yan ajin suka Sa dariya Abu da Binta suka kule suka basar suka samu guri suka zauna duk wanda ya juyo ya kalle su saiyasa dariya abinya ishi Abu    me kuke nufi da mune dazaku kalle mu kusa dariya ko kungamu da wata makusa ne hannune daku muma muna dashi kuna da kafafu muma muna dashi to meye na dariya  Binta tace Rabi dasu DA alama sai mun dagargaza bakin su tukunna zasu gane naga dan rainin hankalin da ze kuma dariya Anan inbamu koya mishi hanka liba  Tana gama fada suka Sa dariya  A zuciye Abu da Binta suka yi Kansu zasu daka  Malamin su yace karku fara kutsaya tukun na   Binta tace amma malam tinda muka shigo suke ta mana dariya dube mufa kaga meye abin dariya a jikin mu  Yace kume yasa kuke musu dariya            Yan ajin basu ce komai ba sai dariya da sukeyi  Hakan ya kara konawa Abu da Binta rai  Malam matsa kar jini ya tabaka dan cikin ajin nan yau ba wanda ze fita cewar Abu  Yace meyasa kukeda saurin fishi ya fada yana dariya  Binta tace harda Wannan abin a kara bata mana rai Abu me muke jirane   Yace A'a ku Tsaya ni da kaina zan fada muku da lili an hada dika aji 2 a nan ne saboda wani abu   Meye shi ayi a fada mana hannuna na kai kayi wlh zan fasa baki cewar Abu  Yace Bakinwa dafatan dai ba nawaba a ss1A zainab kece kika dauki na1 A ss1B kuma Fatima kece ta 1     Yana gama fada yan haji suka tafa musu "suka ce Wannan shine abinda yasa muke muku dariya murna muke tayaku        Abu da Binta baki harkeya suka koma suka zauna  Yace ga result dinku kukai gida   Suka ansa suna murna baki yaki rufuwa     Ana tashi me mota ya daukesu ya maida su gida yana a jiyesu suka fella da gudu suka shiga gida suna shiga   suka samu hajiya da Amal a falo sai kuma suka canza fuskar jiki a mace suka zauna   Amal tace meya faru kardai kuce min kunfadi a jara bawa   Hajiya tace Ku kwantar min da hankali mana Abu Binta Ku fada min meya faru  Abu tace gaskiya mun tabbata marasa kokari mune mukazo na karshe a aji shine kawai  Amal tace karya ne duk irin karatun da kukayi magudine Wannan anyi cuta wlh naga saka makon naku  Suka mika mata   Amal na budewa ta fashe da dariya ta run gumesu "nidai nasani cewa kuzakuzo na 1 indai ba ayi magudiba  Hajiya cikin farin ciki tace Allah ya temaka kukara dagewa wajan karatu yanzu ss2 zaku idan ankoma hutu ko   Eh   Hajiya tace Da kyau Alhaji ya dawo daga tafiya fitayayi ba dadewa zedawo yana dawo wa nizan fara fada mishi Zeji dadi sosai na sani    Abu da binta suka ce Muzamu shiga ciki sai anjimanku   Amal tace kujirani ina zuwa mutafi tare      Tabisu suka tafi koda dare yayi hajiya taje dakin Alhaji a zaune ta same shi   Tai sallama               Ya amsa        Tasamu guri ta zauna " Alhaji wata magana na keso muyi da kai   Ina jinki fada min  Alhaji bansan yanda zaka dauki maganar ba amma ya dace na fada  Ba komai koma meye ki fada min ina jinki  Alhaji cewa nayi meyasa baza mu hada Abu Binta da Aqeel Arif aure ba kaga su Arif haryanzu basu fitar da matan   da zasu auraba su Binta kuma yanzu ss2 zasu shiga za a iya daura aure idan sun gama makaranta saisu tare yaran   Nada kokari sosai saboda karatun da ake musu a gida suna zuwa makaranta a kasasu a ss1 susu kazo na 1 a aji  Murmushi Alhaji yayi "naji dadin maganar da kika fada nima nayi Wannan tinanin saidai amincewar yaran shine  Zasu amince Wannan ba matsala bane Alhaji basa kula samari koda sun musu maga shiyasa nakeda tabbacin cewa bazasu kiba  Alhamdulillah Wannan ba matsala bane   Sunyi hutufa Alhaji shine nace kar a Ja abin meze hana muje DARAUDAU mu sanar dasu a dauro auren daga can mudawo  Kemafa kin kawo shawara bakomai dama kuma zanjima kafin na koma jiya nayi wayada mahaifin Abu yadawo yana gida yanzu haka ki sanar dasu hajiya kisa rana sai muje  Aini ko gobe idan mukaje ba komai Alhaji bakasan yanda na damuda Wannan hadinba dama sunjima basu jeba bari naje na sanar dasu su shirya gobe muje  Hajiya kina maganar shirya wa su Aqeel Arif kin sanar dasu ne  Zan sanar dasu kuma koda anyi musu aure baza suyi maganaba Allah yasani munbasu dama amma haryanzu ba lbr   To shikenan Allah ya basu zaman lpy   Ameen Bari naje gurin su         Tana fita taje ta samesu suna ta hira basuda niyar yin bacci  Sannun Ku da hutawa  Mommy yaushe kika shigo bamuga shigowar kibafa cewar Amal  Hakane kuna hira baza Ku saniba Abu Binta kushirya gobe muna *DARAUDAU*   A tare Abu da Binta sukace muyi me a *DARAUDAU*   Hajiya cikin mamaki tace mekuke nufi inna  Nura da Umma kum manta dasu kenan ko yaya  Abu ta zumbura baki tace badan na ajiye su a canba ba abinda ze kaini *DARAUDAU*   Lallai Abu ma haifar taki cewar Amal  Binta tace itafa bazaku gane bane mu baza mu iya zama a canba yanzu tinda muka saba da nan Allah da*      
.
   Idan munje a can zamu zauna ba dawowa cewar hajiya  Saikun dawo mudai ba inda zamu cewar Abu da Binta  Amal dariya take ta yi "bantaba ganin mutum yaki komawa inda ya fitoba zuwa kamar anje Ehhhe nima inaso naje *DARAUDAU*   Girgiza kai binta tayi "Kita zuwa mudai ba inda zamu saidai idan ta karfi za a mana bazaki ganeba Amal nagode Allah cewa dake zasuje zakika komai da idanki idan kin dawo kya bamu lbr  Kun isa kafata kafar Ku zamuje *DARAUDAU*   Abu tafashe da kuka " Nifa idan aka kira sunan garin tahin zuciya yake sani idan aka kuma fada kuma zan iya amai  Hajiya tace Kyama dena dan idan muje zamu dan jima kafin mudawo  Binta tace mommy kinga Ku musu kudin mota su suzo badai mu muje ba   Nifa na gama magana kushirya gobe muna *DARAUDAU* cewar hajiya           Tana gama fada tayi fice warta  Amal tace hartsawan sati2 zamu zauna a gida ba inda zamu zamu iya zuwa idan mun dawo kuma sai muyi bikin gama koyan dinki KWALLIYA girki natafi yara kuyi murna saida safen Ku   Bintasu kayi da kallo rai a bace  Itafa waccan murna kawai takeyi cewar Abu   Binta tace tinda naji ance *DARAUDAU* yanda kika san karna kwanta bacci dankar safiya tayi a ce mu fito mutafi  Ya muka iya kayan aro baya rufe katara dole mu hakura muyi addu'a kar Allah yasa idan munje su baromu  Binta tace bazasu baro muba idan suka baromu karatun mu fa Waze mana   Hakane kuma hakuri kwai zamuyi mu kwanta bacci saida safe   Allah ya kaimu    Kwanciya sukayi badan suna jin bacci ba a kunne su aka kira sallar Asiba suka tashi sukayi sallah saiga Amal ta shigo  Tinjiya na gama shirya kayana yan mata sai tafiya kufa   Binta ta kalle ta "tsirara zamu   Amal tayi dariya "Allah ya Baku hakuri daddy ya tafi masallaci yana dawowa sai tafiya shine nazo na fada muku  Abu tayi tsaki "shine me ko kuka zamuyi saboda kin fada mana haka   Bazan so kuyi kukaba kuyi farin ciki kuda zaku DARAUDAU kuga wayanda kuka jima Baku ganiba kuje dandali kokum mantane   Abu ta kalli binta            Suka kama hannun Amal suka fitar da ita daga dakin suka rufe     Bakomai dai zamu hado a motar zuwa DARAUDAU  Kinsan meyasa take mana haka saboda ta gane cewa ba masan zuwa daga yanzu mununa cewa munaso aje cewar Binta  Bazan iyaba wlh saidai tai tayi ko a jikina  
.
Ai shi kenan sai kishiga Kiyi wanka kifito nima nayi cewar Binta  Wai yanzu da gaske dai za a je Cewar Abu  Gashi kuwa waccan kwandar tace tashirya harda hada Kaya ma  Bakomai Allah gamu gareka         Tashiga wanka ta fito Binta tayi ta fito      Suka saka Kaya iri1   Sai ga Amal ta dawo   Nazo naga wana irin KWALLIYA zakuyi   Abu tace Ya akai kika shigo  Makullin dakin ku yana gurina shiyasa bansha wahalaba  kai kayama iri1 mukasa kai abin mamaki   Ita kadai taita magana basu kulataba harsuka gama shiryawa ita ta daukar musu kayan da zasu tafi dashi dakin   hajiya sukaje suka gaidata suna fitowa suka ga Alhaji shima suka gaida shi  suka zauna a falo suna jiran fito   warsu bajimawa suka fito suna karyawa suka shiga mota suka dauki hanyar tafiya DARAUDAU sunyi tafiya me tsawo kafin suka isa garin   suna zuwa yara suka zagaye motar a kofar gidan su abu suka yi parking din mota koya ya fito banda Abu da Binta  Saida hajiya tayi dagaske kafin suka fito dan cewa sukayi a kirasu suzo su gaisa sai su koma basai sun shiga ba suna fitowa      Amal tace yara Baku gane su bane Abu da binta ne    yaran suka shiga kiran sunan Abu da Binta sukuma suka hade rai Amal dariya take tayi cikin gidan suka shiga inna   ta shimfida musu tabar ma Suka zauna Abu da binta na tsaye  sunki zu zauna  Inna tace Abu Binta Wannan wana sabon salone kuma haka  Abu tace inna karki damu yanzu zamu koma base mun zauna ba   Abu da Binta suka gaida inna          Ta amsa cikin mamaki "lallai yaran nan sun shiryu yau kune kuka gaisheni mariya nagode naji yanzu ba kanshin gado sundena KWALLIYAR haukan nan amma naji dadi  Binta tace inna ina yaya Nura ban ganshiba    Dashi da baban Ku suna can wajan daurin aure yanzu zasu dawo  Abu tace umma fa   Tace gatanan zuwa dan nasan lbr yasameta cewa kunzo yanzu zata shigo  Koda suka gaji da tsayuwa suka samu guri suka zauna   Nan fa inna ta shiga gaisawa da Alhaji hajiya da Amal bayan sun gama gaisawa   A tare malam munzali Nura da umma suka shigo   Abu da binta sukasa ihu da tsalle Suka Tsaya a gaban Nura  Yace na sani ai baza Ku taba gyaruwa ba ko ina kukaje yanzu Wannan ihun na me Nene kuma   Farin ciki mana Tsaya ma tukun na baka farin cike da ka ganmu ne ko yaya kaga dama ba dadewa zamuyiba yanzu zamu koma kwantar da hanka linka cewar Binta  Yace yazance bana farin ciki da ganin Ku babu wanda ya kaini farin ciki nayi kewarku sosai da kyar na iya jure rashinku wlh  Sukace Allah sarki yayan mu           Umma suka gani a gefe tana kallon su tana dariya  Suka Sa ihu sukayi ganta cikin farin ciki da so da qauna ta rungumeso Amal na ganin haka tagane cewa mahaifiyar Binta ce    Umma harda hawayan farin ciki ganin yarta tayi fari tayi kyau tana cikin koshin lpy  Amal ta taso ta sunkuya a gabanta ta gaidata umma ta amsa gaisuwar tareda dago Amal umma ta samu guri ta zauna suka gaisa dasu hajiya tai musu godiya malam munzali ma gaisawa sukayi   Abu da Binta sukace munganku kuna lpy mu zamu tafi daddy mommy Amal kutaso mu tafi  Kudai kutafi mukuma muna nan bazamu koma gida ba cewar Amal  Abu tace to ai shi kenan mu zamu shiga gari bazamu dadeba zamu dawo Amal taho muje kiga DARAUDAU   Amal tace To muntafi   Nura yace Ku Tsaya mu tafi tare dan yaran nan ba nutsuwa sukaiba suna iya zuwa wani ya tsokanesu sukuma su daka tatashi suhau fada   Yaya nura we are not a kid's she kararmu 17 mun wuce yara ko   Hakane bakiyi karyaba Amal mutafi          Suka fita gaba 1 su  wato sun hakura sun yarda suna karatu a can kenan   Amal tace Eh yanzu ss2 zasu shiga  Ss2 kuma dawana kanzasu shiga amma sunyi sauri yaranda basu iya karatu ba  Sanin da kamusu yanzu ba haka suke ba susukazo na1 a ajinsu   Tab amma kunyi babban yaki kafin su fara zuwa makaranta ko  Wannan yazama lbr yanzu dan Gashi suna jin dadin makarantar tasu    Koda yaran suka fita ya rage saura iyayan  
.
Alhaji Nasir yayi gyara murya "wata maganace take tafe damu nanya sanar dasu abinda suka yanke akan yaran nasu  Malam munzali yace Wannan ba matsala bace kunfi karfin haka a wajan mu saidai ga mahaifiyar Binta bari muji daga bakinta  Umma tace bakomai wlh ni banida matsala idan yaran sun yarda shi kenan  Allah ya musu Albarka ya basu zaman lpy  Alhamdulillah tinda munfahimci juna yaushe kuka zaba dan a daura auren nasu cewar munzali  Alhaji Nasir yace munfi so a daura auren nasu Anan sai kusa rana munana har a gama komai na bikin a musu komai kamar yanda a keyi   Bakomai Wannan ba matsala bane yau laraba mu bari ranar juma'a sai a daura musu aure Wannan ba matsala bane cewar munzali  Inna tace ni kuma zanyi magana da su Abu da Binta nasan zasu a min ce   To Bakomai Allah ya kaimu da rai da lpy  Su Abu na cikin tafiya wani ya Tsaya a gaban su da redio irin nada yana jin waka   Abu tace Wannan rashin hanka linfa zaka wani zo gaban mutane ahaka  Yace kuyi min uziri san kune ya makantar dani tin kafin Ku tafi birni nake dawai niya da sanku banaci bana sha koda na samu lbr zuwanku nayi murna sosai shine nazo na sanar daku kafin kumin nisa  Abu da Binta suka kalli juna suka tafa   Binta tace a haka kake sonmu dubi kayan jikin ka Riga daban wando daban hula a yahe kuma dan idonka da kwalli shine zakace kana sonmu  Abu tace maza wayanda suka fika a birni saudubo ko kulasu bama yi shine dan munzo nan zamu kulaka kabace a gaban mu komu gyara maka zama    ×

1 comment: