CANJIN RAYUWA
[Kashi na 1]
(Shafi 6-10) Tare da -
Halima K. Mashi
Post By ISMAIL SANI
Hajiya ce ta janyo masa kujera ya zauna,ya kalli MIMI zauna mana uwata. Ya mayar da kallon shi ga hajiya sauda, an yi mata farfesun kifin? hajiya ta kalli MIMI cikin daurewan fuska,sannan ta ce,an yi,MIMI ta turo baki tare da hada rai. Hajiya tana zuba masu dan waken cikin plate tare da colslow,ta janyo wani plate din tana zuba masa farfesun kafar sa,ta tura gabansa tana fadin alhaji ba ka tambayi yaran gidan ba? ya kalle ta cikin ‘yar zolaya yace,duk ganin ki ne ya mantar dani. ko da dai na san zuwa yanzu suna lslamiyya ko? ta ce eh,yau kam ma da murna suka fita,don na gaya masu cewa kana tafe,ya ce ga shi ban riko masu tsaraba ba. amma bari in sa direba ya sayo masu,ta ce aa zai fi kyau ka fita dasu don yaran nan basa samun kulawarka,kamar fa sam basu shaku da kai ba.
Ya kalli MIMI wacce ta jibga tagumi,ya ce zan gani ko da lokacin,kin san fako a can ba samu zama nake yi ba.shiru tayi don ta san kome za tace ba fahimtar ta zai yi ba,ta jima tana yi mishi nacin cewa,ya dinga baiwa yaran ko da awa daya ne a cikin lokacinsa, amma sam ya ki.ko su da suke matansa basa ganin shi a kan lokaci,sai yayi wata ko sati uku in kuma yazo kwana biyu yake yi, nan guri ta ya kwana daya ya je malumfashi wajen hajiya binta ya kwana daya tunaninta ya katse lokacin da ta ji yana tambayar MIMI menene uwata? na ga duk kin bata ranki?ki ci kifinki mamana. Ya kalli hajiya sauda ina kifinta?hajiya ta nuna kular da cokali,ga kular kifin nan gabanta?ta dauka mana ko a baki zan bata? MIMI ta sake tura baki tare da kallon mahaifiyarta,ni na koshi,hajiya sauda ta ce, karyarki dubu wallahi kin yi kadan ki ce a dafa miki abin, yanzu ki ce baza ki ci ba,saboda bakin raini ai na lura da ke tunda ku ka shigo gidan nan na san baki so zuwa ba, ko katsinar ce baki so zuwa ba oho miki, amma bakin ranki ya kare miki can.
Sauda! Alhaji ya katse ta tare da daga hannu, gaskiya ni bana son abinda ki keyi,a ce ke da ‘yarki ta cikinki amma ba ki kaunarta?….
Hajiya tace, ba kaunarta bane bana yi, halinta ne bana so.kuma in har ta ga mun zauna inuwa daya da ita to ta tabbatar ta canza halinta,in ko ba ta canza ba to sai dai ta nemi wata uwar ko da yake tana da ita ma. ya tausasa murya ai ba maganar fada bane, amma gaskiya ba zan iya kallo kina mata irin kalaman ba, kullum tana yi mini korafin ba ki sonta,ita in fada mata gaskiya ko dai bake ce ki ka haife ta ba?ya aje cokalin hannunshi,na rasa me take miki,ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba.sai ta zo hutu irin haka,amma sam ba kya ko yin kewar ta. hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba,wanda ta hada masa,a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce,halin ta kawai zata canza,in dai tana son soyayyata. yanzu baka kalli shigar da tayi ba? tun daga abuja ka sako ta gaba har katsina, kana mahaifinta ga shi kanta a waje,kayar jikinta duk sun dame ta,wai ita dole ta waye.
Ya kalli MIMI sannan ya kalli sauda, da dan murmushi,ina laifin kwalliyarta,ni ban ga aibun ta ba,haka ‘yan mata matasa irin ta ke yi.ya kalli MIMI,ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?tsaki hajiya ta yi ta nufi dakinta.sai lokacin MIMI ta samu damar yin mita,kaga ko dad,sai da nace ka barni can in gama hutu na,ka ce aa sai na zo, ni daman na san hajiya ba za ta taba so na ba. Ta mike tsaye tare da kallon jikinta,shiga tafa, mene ne aibunta?ya kalle ta cikin sigar lallashi yace, ban ga laifi ba.ita hajiya wai sai tace,sai na saka hijabi da atamfa,ni kuma ba zan iya sa iri wannan kayan zafin ba.na yi karatu na waye ni ba irin su usaina ba ce kauyawa.yayi murmushi,shgwabarta tana burge shi. kallon ta ya ke yi tamkar ‘yar shekara biyu. ya mike ya zagayo wajen ta ya dafa kafadarta,kar ki damu uwata. mamanki tana sonki,na san ta ga nafi damuwa da kene cikin ‘ya’ya na,kin san don ita ce ta haife ki,shi ya sa fa.in da a ce kamar hajiya binta ce ko nafisa da tuni na sallame su,kin manta na taba kora hajiya binta saboda ke?ta ce na tuna Dad, Ya ce to kar ki damu ina son mahaifiyarki ko da bata haifamin ke ba, bare ta haife ki. kina son a ce mahaifanki biyu ba su tare?ta ce ba zan so ba dad.amma ka yi mata magana ta daina matsa min,ya ce zan yi mata, amma ke ma ina son cikin kwana biyun nan ki canza kaya sawarki,ki rinka saka irin wadanda take so.ta ce zanyi in dai za ta bar ni in yi abinda na ke so,ya ce za ta barki mana kin ji,ki dai na kuka.ya yi ta lallashinta har ta daina kuka.
Suna cikin cin abinci hajiya ta sake fitowa daidai lokacin yara suka dawo daga lslamiyya da sallama suka shigo, ita ce ta amsa sallamar,husna da hasina ne a gaba,suka ce sannu da gida hajiya ta ce yawwa sannunku da dawowa yara na.ina sauran? kafin suba ta amsa sai ga su suna ta yin sallama,da hannu ta nuna masu gurin dining,ga dadin ku,suka nufi gurin suna gaida shi da daidaya.ya dafa kan husna da hasina, su ne kanana a gidan, yana ta amsa masu.MIMI ta hada rai ita ba ta son hayaniya. dady ya ce,ba ku gaida sista MIMI ba.suka kalle ta don suna tsoron ta,sannu yaya MIMI,cikin daure fuska ta ce,yawwa,na amsa duka ne ba sai kowanne ya gaishe ni daya bayan daya ba.hasana da usaina sune ‘yan matan da suke bi MIMI a haihuwa.dad ya kale su ku shirya da kannen ku, yau yazo ya kai ku super market ku sayo tsarabarku, don ban riko komai ba, kowa ya je ya zabo abinda ranshi ke so.
Yara suka shiga murna hasana da hussaina suka ce dad,mu kam ba zamu je ba.ya ce,saboda me?suka ce,muna da karatun hadda gobe,malamin mu zai zo, bin abdulrahaman. hajiya ta ce,tabbas ba ku da halin fita, in ba haka ba zaku sha dukan tsiya gurin shi.duka kuma?in ji dad dinsu,hajiya tace sun wuce duka kenan?karatu sai da zare ido. abdulkarim ya yi sallam, ya shigo falo suka amsa,ya iso gurin dadin shima ya gaida alhajin.MIMI tana ta chatin dinta ba ta dago kai ba,shima bai ko kalle ta ba. ya dubi su hasana ya ce, kun dawo?suka ce eh! yaya sannu da zuwa, dazun hajiya ta fada mana zuwan ka. mun je dakin ku kana wanka, Kuma lokacin lslamiyya ya yi dole muka tafi.ya ce,na ji shigowar ai, ya ya zauna,usaina na fadin,lslamiyya lafiya,munyi murajaa ne yanzun. ya ce, kun kusa fara jarabawa kenan suka ce eh! hasana ta ce,yawwa yaya don allah ka amsar mana hadda in anjima mun yi magariba, gobe da safe muna da malamin gida bin abdulrahaman. abdulkarim cikin sigar tsokana ya ce, bani da lokaci,ku ce gobe zanyi kallon duka. usaina ta ce agaji yaya abdul, bulalarshi akwai zafi,suka sa dariya tare.ya ce,bari mu yi sallah sai in karbar maku,suka ce,yawwa yayanmu mun gode.
MIMI daga wurin da take zaune tana jin su tana kuma kallon su,sai ta soma mita,ni na san duk ‘yan gidan nan ba sa so na,dole kawai suke gani na,kalli yaya abdul,ko kallo na bai yi ba.alhaji yace,kai! abdulkrim,ya ce naam,ya zo ga ni dad.ya ce baka ga MIMI ba ne?ran abdulkarim ya baci,nan a take fuskarsa ta nuna,cikin wata murya marar dadi ya ce,na ganta mana dadi.shine ba za ka yi mata magana ba? Kafin ya yi magana hajiya ta amsa da cewa, in duniya da gaskiya ita da shi wanene gaba?shine ya kamata ya gaida ta,ko ita ce ya da ce ta gaishe shi?. alhaji ya ce,amma ita bakuwa ce.bayan haka kuma yaushe rabonsa da ganinta?a kalla ya nu na kewarsa gare ta ko?kan abdul yana kasa tamkar ya sa kuka don haushi da takaici.hajiya ta ce,bai gaishe ta din ba.tafi abinka abdulkarim,cikin sauri ya wuce.su hasana ma suka yi dakinsu ita ma hajiya ta juya zuwa dakinta,MIMI ta kalli dad,kawai mu koma kalli fa duk yanda suka watse suka barmu,ya dafa ta karki damu ina zuwa. baki gado hajiya sauda ta zauna ta zabga tagumi,wannan abin ya ci mata rai,a ce mutum kamar alhaji ya dinga irin wannan abu sai ka ce yaro.kirikiri yana gani garkiya sai ya runtse ido saboda son zuciya,bai san cewa haka zai sa kan ‘ya’yansa ya rabu ba ne?sallamar shi ce ta katse ta,ta dago ta dube shi,shima ya iso ya zauna bakin gadon.haba hajiya ki sakarwa ‘yarki fuska mana?ke ba abin faharin ki bane a ce nafi son ‘yarki,duk cikin ‘ya’ya na?
Ya kama hannunta cikin sigar lallashi ya ce,haba sauda kin fa san ina tsananin sonki, sonki ne fa ya shafe ta ko baki lura ba?ta daga ido ta kalle shi,ban musa ba,na san kana so na,amma ni burin na shine ka yi adalci tsakanin yaranka alhaji, ko don gudu rarrabuwar kansu. ya ce,menene na yi mata wanda ban yi masu ba?ta kalli cikin idon shi,ai ba za su kirgu ba,banda nuna tsantsar kulawa a fili, duk cikin yaranka wanene ka kai kasa wajen karatu bayan ita?to indan wannan ne,karatun na su na gida ya fina ta cin kudi sauda. umm, haka dai za ka ce,tunda kana son kare kanka,ya ce, ni dai ina neman alfarma ki sakar mata fuska ki dan ja ta a jikin ki har mu tafi.ta kalle shi,ta rasa me zata ce masa,sai kurum ta ce to. don tana son kawo karshen zancan, ya shafi kumatun ta,na gode,ya matso da bakin shi saitin kunnuwanta,ina son a kyuatata shimfida ta anjima. don na iso da muradin hakan.
Ta sake murmushi tare da kallon shi,wai alhaji yaushe zaa girma ne?ta yi tambayar cikin sigar wasa. ya janyo ta jikin shi,wa ya ce miki ana girma da lada? sai dai in mutuwa ce ta dauka.suka sa dariya tare, daidai lokacin aka yi kiran sallar.suka mike, ta ce lokacin sallah yayi bari in fita ‘yan mazan nan sai nayi fama sannan su wuce masallaci.tare suka fita ya nufi dakin shi,har lokacin MIMI tana zaune a falo.sai dai lokacin ta koma kan kujerar zaman mutum biyu tana ta chatin. Alhaji ya nufe ta yana cewa,mamana kina hutawa ne?ba tare data dago ba,ta ce eh dady.ya ce da kyau.ya wuce dakinsa. hajiya sauda ta dube ta,ki tashi kiyi sallah,ta dago ta kalli hajiyar ta ga fuskarta a daure,ta zabga mata harara na ce,ki tashi ki yi sallah.tsam ta mike ta nufi dakin su usaina inda nan ne take sauka in ta zo,kayan tama cikin suke.sai dai ita bata sm hakan saboda a abuja sasanta dabam, amma a nan hajiya ta hana a yi mata dakinta dabam.ta sami su hasana suna sallah, ta fadi kan gado ta ci gaba da chatin dinta. Ga al’ada alhaji in ya fita sallah (Zan cigaba)…
IP
0 comments:
Post a Comment