Sunday, 17 December 2017

'Yar Fulani Part 30-35 (The end) Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YAR FULANI Part 31-35 (The end)
.
Yau dai ta samu qafar da Dan sauqi har ta fito babban parlor ana Dan taba hira da ita Zubaida Na zaune daga gefenta duk mgnar da suke akan shirye shiryen auren zubai danne da Na Amir tun dazu Hassan ya shigo bayan gaisawa da sukayi bai sake cewa komai ba sai dai ya qurawa matarsa ido in ta kalleshi ya danyi murmushi  ya murza manyan idanunshi da sukayi ja suka qanaqce sai ya Dan kwanta jikin kujera ya shafa kwanceccen sajenshi ya Dan leshi lips 
inshi sarai ta gane damuwarsa sai dai tayi kamar bata ganeba can ya danyi miqa da  Hussain ya kalleshi cikin wasa yace kai doctor naga dai ba aikin dare kaiba jiya da zaka xo kai ta mana  ya dan harareshi yace to sarkin Sa ido can dai dabara ta fado mai ya dauki phone enshi ya tura mata message kamar haka (ayyah Habibati ban sanki da hakaba bafa plzz ki tausa yawa Hammanki wlh Na kasa daurewa Na kasa sarrafa kaina ki ji tausayin mijinki kar nashiga wani hali ) ta karanta ta kalleshi ta share ya sake tura mata wani sai taqi karan tawama can dai sai ya miqe yace toh nikam sai da safe Dan ina da aikin safe ya kalleta ya danyi dry mugunta yace Fateema kizo muje ki bani pakalana Dan ina da buqatarsa yanxu aikinshi zanje nai ya qarisa mgn yana tsareta da ido tace ni kuma bata qarisaba ya katseta taso sauri nake Umma tace jeki bashi sai ki kwanta ki huta haka ta tashi da qyar take takawa tana shiga dakin 
.
Ya jawota jikinshi ya mannamata kiss a lips enta ta Dan tureshi ta zauna bakin gado ya maso a hankali ya kai bakinshi cikin kunnenta ya rinqa huramata iska yana Dan mgn cikin rarrashi ayyah Habibati kiyi haquri wlh Na kasa sarrafa kai nane ki tausa yamin wata 2 fa ai nayi haquri a haka dai yaita mata zaqin baki har ya sameta ya kauda buqatarsa shi ya taimaka mata tai wonka ya shiryata sab sannan ya fita mama ta shigo Dan tunda cikin ya tsufa ta dawo gunta.. sun danyi hira da mama  har mama tai bacci itama ta kwanta
Tana Sa kanta kan pillow taji wani irin Abu ya tsikari ququnta da qafafunta ta Dan cije baki ta kwanta ajima kadan taji abin ya sake tsikarinta sai kuma taji ya Dan lafa har taji wani irin bacci mai dadi inko in ya tsikareta a firgice zata farka haka tai ta fama har zuwa 4:Am sai lkcin kuma ta rinqa jin wani irin fitsari da baya qarewa taje yanxu tana fitowa zata sakeji anyi kiran Assalatu ta shiga Dan tai fitsarin ta kuma yi alwala sai taga Dan jini kadan a jikinta a take taji wani irin sarawa da ququnta da cinyarta keyi ga wani irin amai da ya taho mata   cikin bacci mama taji kakarinta da sauri ta shiga toilet en ta taddata a ronqofe sai amai take da qyar tasamu ya Dan lfa mama tai sallah itako tana zaune tana ta faman jin azaba sai zufa keta keto mata tako ina mama Na idarwa ganin ta cikin yanayin naquda gadan gadan yasa ta fita da sauri taje ta sheidawa su Umma aiko a take suka nufi hospital Amir ke jansu sai mama da Umma tana tsakiyatsu Ammi kuma ta kira Hassan da su nazir ta sheida musu 
.
A asibitin tun tuni doctors ke ta zirya a kanta ga naquda kama kama Amman aihuwa ta faskara ga aman da yaqi tsayawa ciwon qugu da qafafu kuma abin yaci tura Hassan kam al,amarin ya zarta tunaninsa
Yanxu qarfe 4:pm Amman har yanxu bata aihuba 
Dr Halima ta fito cikin yanayin tausayi tace a gsky dr Hassan sai anyiwa dr Fateema c,s, Dan yanxu kam ga aihuwa tazo ita kuma qarfinta ya qare bata iya nishi gashi cikin ya fara haurawa Saman qirjinta Sa hannunka kawai muke so cikin rudani ya rinqa girgiza kanshi yana cewa a a insha Allahu baza a mata c,s, ba zata aihu da kanta gaba daya ya fita haiyacinsa ya rame lkci daya ya kasa koda shan ruwane idanshi yayi zuru zuru Dan firgita da tsoron halin da Habibatinshi zata kasance Umma ta kalleshi tace haba Hassan ai ko ba komai ma tausaya mata qarfinta ya qare kasa hannu a ceci rayuwarta insha Allahu ba abin da zai sameta Hussain ya karbi takaddar yada hannu yace dr Halima muje muyi aikinmu suka juya suka tf gaba daya sun gama shirin yimata aikin saura su fara kawai Hassan ya shiga tana ganinshi ta kamo hannunshi cikin murza kai tace Hammana kaga abin da nake gayamaka ko cikinan zai kasheni bazan iya haifarshiba.   da sauri ya rufe bakinta yace daina fadin haka insha Allahu zaki aihu lfy ba abinda zai sameki inaji ajikina ba abinda zai rabamu ta qara matse hannunshi tace Hamma a kiramin bappana xai bata amsa Dr Halima ta katsesu da cewan ya gyara za amata allurar da zai kashe zafi za,afara aikin ya qara sunkuyowa kanta daidai lkcin taji wani irin azabar da bata taba jiba sai amai ba qaqqautawa duk ta fita haiyacinta  gaba daya doctors en sukayi kanta cikin azaba taji wani irin nishi ta rinqa nishi ta qanqame Hassan ta mai wani irin riko su gaba daya basu lura da nishin da takeba sai jin kukan baby sukayi
Gaba daya suka xuba mata ido cikin mmk shi kuma Hassan tuni ya koma qasanta ya dauko baby ya macece fara tas bata da wani girma ya yanke cibiya ya miqawa Dr Halima ta fara gyara yar bayan baifi minti 15 sai ko amai kam ya dawo sabo fil yi take tana nishi sai ga wani Dan ta maida kanta kan pillow tana maida numfashi gaba daya suka dauki hamdala Hussain shine ya fita  ya yiwa su Umma albishir kan kace kobo zuriyar saraki sun cika da farin ciki Amir ya kira Ammi ya gaya mata sai Alhamdulillah take ta fadi tai alwala tai nfl ta godewa rabbi mai kyau ta da qari a can banqaren kuma har yaxu mahaifa taqi samuwa duk sunyi iya yinsu abin yaci tura Hassan kam gaba daya hankalinshi ya tashi Sam ko yaran bai samu damar ganinsuba duk ta fara birki cewa Dan sai wani sabon ciwo ya taso dr Halima ta maso Dan tayi dabarunsu Na likitoci ta fidda mahaifar tana dan tabata ta dago da sauri tace dr yarima harfa yanxu akwai wani babyn a cikinta sabon naquda take. gaba daya sun cika da mmk saiko ga naguda kam gadan gadan amai sabo ya taso yi take ba qaqqautawa ga baby ta kawo kai ita kuma uwa qarfi ya qare sai ta fara nishi sai tace Hamma nagaji bazan iyaba ya koma ta kanta ya rinqa shafa kanta dr Halima kuma Na shirn karbar baby cikin qarfafa mata guiwa suke cewa kiyi nishi ki daure sai ta danyi sai kuma ta maida kai tace bazan iyaba can ta Dan qara nishin har kan baby ya fito gaba daya sai kuma idanunta sukayi luuu ta maida kai cikin gajiya tace Hamma Ku ciremin xai kasheni ya Dan kalleta cikin kidima a ransa yace dole sai Na yimiki abinda baba so yasa Dan babbar yatsarsa ya danna bayan kunneta sai ga wata atishawa mai qarfi baby da mahaifar duk tare suka fado dr Halima tace Alhamudulallah komai yayi normal Hassan yace a a Halima ai ita a sume take bani ruwa da sauri ya fesa mata ruwan ta farfado cikin nitsuwa    cikin sauki aka gyara yaran da mahaifiyarsu aka kaisu inda zasu huta Hassan kam yaga gata da soyeyya agun yan uwansu farin cikin su bai misaltuwa gaba daya ma,aikatan asibitin sukaita tururuwar mishi barka a Daren sarki dasu waziri suka xo Ammi ma ta zo duk yan uwa sunyi hamdala ita  kam maijego  bacci gajiya kawai take da yan tagwayenta bata san abinda akeba
Jinjinata a gareki qaunari sadidan a raina Anty Hafsat matar sherif.
.
D'akin cike yake da y'an uwa da abokan arziqi da sukazo musu murnar samun qaruwa da ganin yan 3 Hassan dake zaune a gefenta runqume da ya macen daya dan kuma Umma Na riqe dashi sai daya da suka liqawa Fateema tana tirjewa ita a barta ta huta sai kusan karfe 10 aka dan watse saura Hassan ya bawa Amir key en motarsa yace yaje ya dauko mai wata yar roba mai cike da dabino mai kyau yaje ya dauko Hassan ya karba ya miqaqa Fateema yana klonta da qauna mai zurfi yace karbi tauna duk ki basu ruwan a bakinsu ta zura mai ido tace ni fa bacci nakeji kai ka basu mana....Umma tace a a Fateema karbi ki bawa yayanki hakan yana da fa,ida sosai kece uwa anfi bukatar ki basu domin bakin uwa kuma bayarwan yana da amfani Dan da izin Allah da zai kasance mai jin mgnar uwa  hakazali ka likitocin zamani sunyi ittifaqi duk abinci da Dan Adam keci sai yabi jini yabi jijiya kafin yaje ga qoqolwa Amman shi dabino kai tsaya qoqolwa yake tafiya kuma yanasa yara kaifin basira haqiqa da yawa iyaye suna sakaci da bama jarirensu ruwan dabino da zasu tauna da bakinsu.
Hassan yace gsky ne Umma ya miqamata ta karba ta tauna zata bawa Dan da yake hannuta din yace a a da babbar za,a fara haka kuma akayi duk ta basu Umma ta kalleta tace Fateema ki basu mama su fara tsotso Dan zai taimaka wurin jawo ruwa ta dago da sauri da zare tace tab Umma ni dai inajin tsoro Hassan yace babbar mgn me kike sonyi kenan tace a basu madara nifa bazan iya basu ba sunyi yawa 
Abu kamar wasa taqi basu nono har aka sallamesu suka koma gida nanma anyi taqi fir innartama tazo Bappa ma yazo yaga yan jikokinshi inna kam tananan an hanata kowa ance ta haqura tai ko kwana 5 inyaso ta koma tunda ba kowa a gida.****
.
Yau kwanasu 3 Amman har yanxu basu samu nonon mahaifiyarsuba sai suita kuka sai dai a basu ruwan dumi in innarta tai kanta da fada sai su Umma su hanata a cewasu zata basu in nonunan suka isheta da nauyi da kukan yaran 
Qarfe 4 dai dai su Hussaini da Nazir da Hassan en suka shigo dakin su samu Umma nata faman rarrashin yara suna ta tsala kuka inna nata fada ita ko tana zaune tai luf a kan gado ta Dan tura bakinta Hussaini ya karbi daya Dan Nazir ma ya karbi dayan shi kuma Hassan ya dauki ya macen sukai ta Dan jijjigasu Amman Sam sunqi shiru Hassan ya kalleta a raunane cikin lallashi yace Dan Allah kiyi haquri ki shayarda yayanki ki gafa yadda suke buqatar mamansu yunwa Na damunsu ta Dan kalleshi tace nifa wlh Hamma tsoro nakeji jiyama da inna tasa Na Dan samata a baki ita da ta fiye rakin wlh ta jamin da qarfi zafi kamar zanyi  inna tace ai kema da haka aka shayarda ke ta fita tana ta fada
maxan kam sun danyi bacci Amman ita macen sai kuka take Hassan ya tashi ya nufi dakin Amminshi ya shiga da slm tana zaune kan sallaya tana riqe da carbi yazo kusa da ita ya zauna runqume da babyn ya gaida Ammi ta kalleshi a nitse tace lfy kuwa meke damunta ya kalleta a raunane yace Ammi mamansu taqi ta basu nono yunwa sukeji Dan Allah Ammi muje ki mata mgn ya qarisa mgn cikin damuwa fuska a raunane ta danyi dry tace kai yaran zamani kai Sam baka jin kunyar yaran toh ai ita Fateema kunyace ke qara sata hakan ya kalli Ammi ya lonqobar da kai yace gsky Ammi bazan yardaba zata cutarmi da yara da kunyarta ta Fulani da mutanen daa ni dai muje ki mata mgn
Ammi tai Dan murmushi tace toh ni meruwana badai Ku kunci abincin ba ya kalleta cikin sauri Dan yau dai Ammi ta nuna shi a matsayin danta mafi soyuwa har tana indai shi yaci ba matsala tanaiwa yayansa wasa yai dry cikin jin dadi yace muje dai Ammina suka futo a tare suna dry a parlor sukaci karo dasu Hassan Hussain ya kwashe da dry yace tab su Ammi manya yau hira ake da Dan fari harda dry Ammi tai sauri harararsa sukuma duk sukai dry
A dakin Ammi tai ta lallaba Fateema har ta yarda tace toh zan basu Amman kadan kadan zasu Sha cikin sauri Hassan yace eh mun yarda sai kuma ta noqe Ammi tace jeki wanke bakin nonon nanma ta noqe cikin fulakun Ammi ta gane kunyarta takeji sai ta fita ta ja musu qofar
Aiko da sauri ya matso gunta ya zuge zip din dake manne a gaban rigarta su 2 ko wanne yana kan saitin nono da kanshi yasa hannunshi ya fito da nonon ya dan kalleta cikin rarrashi yace qyara ki bata bakin nononma a wonke yake ba matsala ta qarbi yar ta Dan talla bota ta Dan sunkuyo ta miqa mata nono itako baby sai neman nonon take tanata raruma ta kasa bata ta kama Dan nonon sunan das dasu ba alamun kwanciya ta kalleshi fuska a shogobe tace Hamma kaga taki karba ko ni zan maida abina ya kalleta ido cikin ido da tsantasr qauna yace kiyi haquri bari Na koya miki ya Dan kara matsota yasa hannunshi ya kamo nono ya samata a baki aiko ta cabke ta fara zuqa dama nono ya ciko tab itako tai dan zillo tana yarfa hannu tace Hamma zafi zata ciremin bakin nono ya Dan hadata da baby ya runqumosu yace sorry my Habibati tinda dai Abbanta bai cire bakin a baya ba toh itama bazata cireba ya fada cikin wasa da zoleya ta rufe idanta Dan kunya haka yasa ta tabasu duka cikin hikima ya kuma yiwa yayansa huduba  kuma a ranan sarki ya shedawa Hassan da dukkan yan uwa cewa ran suna za,a nada wa Hassan sarautarsa...........
Taro yayi taro ran sunan kuma ran nadin sarautar yara sunci sunan Abba da Bappa sai Ammi ya macen Aysha Ammin kenan sai Aliyu Hydar sai Bappa abubakar Abii  duk yan uwa da abokan arziqi sun xo su Adda Mina mutan daura harda su maitamacy ikon rabbi ga kanawan dabo duk sunzo ga hajiyar SA Fiji itama tazo mutanen garin yabani ma sun zo yara sun sha kyautar garken shanaye da raquma da dawa kai fulle Yola kam bamu da iyaka mun biyo Farida dasu Yaya Bashir su Zubaida Amare da matar Amir sun tare a gidan tunda akai aihuwar Fulb'e gembu ma an faso yara sunsha suturu da kyaututuka little Ammi kam abin ba,a mgn Dan sonta azimun tasha yan kunnayen zinari da azurfa An watse taro lfy
Bayan 40 mai jego ta koma gidanta..
*************"""""""""""""**********
Bayan shekara   7 Nima Aysha sai yau Na dawo jihar Gombe misalin qarfe 4 motarmu ta shigo cikin garin bubayero gaba daya a gajiye nake Dan tfya ce mai nisa Na yi tun daga jihar Taraba tarabanma can cikin garin gembu tunda muka kama hanya ban bude data naba sai yanxu da muka iso cikin Gombe Na danja phone ena Na bude data Na a take naji saqonnin Na shigomin tako ina ina budewa ko Na samu qorafe qorafe mansu karatun yar Fulani ne sukafi yawa a cikin sakonnin kan cewa Na daina typing a yadda sukeso cewar ina jinkiri typing nandai naita basu haquri da kuma gayamusu uzurina Na kuma yi alqawarin yau dai zan leqa gidan sarki Hassan Dan sarki Aliyu jikan sarki abubakar naga wacce wainar ake toyawa toh masu karu Ku biyoni mu ganewa idanmu,,,,,,
Ina shiga gidan naji hayaniyar yara da Dan sowarsu da sauri Na qarisa cikin parlor da yasha gyara da kayan qawa da alatun da kayayyakin more rayuwa Parlor ne babba daga can gefe kuma dining table ne qawatacce cangefen dining en naga wata yar duma duma mata yar das da ita tana cikin sutura ta alfarma da ka ganta kaga jin dadi a fili   komai a jikinta das sai da Na zubamata  sosai Na gano cewa Fateema ce  ga yan yara su 6 dayar yar babba kadan ita zata kai 8 year's sai wasu su 3 Kansu daya sunsha gyara sai saura biyun bazasu wuce 4 year  ba gaba daya sun kaceme sun rikita gun da hayaniya Duk sai zagaye parlor suke Abii nabin Ammi shi dai wlh sai ya rama shiko hydar ya kame sai murtuqe fuska yake da hancini Afreen kuma taya Ammi fadan take tana Ammi ki gudu kije gun mami zasu dokeki Ammi ta Dan tura baki tace Anty Afreen ko naje gun mami dukana zatayi cewa take Na fiye kaudi da masifa gashi Abbana bai shigoba kiyi sauri kizo mu gudu gun Ummi Afreen ta jawo hannuta zasu gudu kenan Abii ya tare gabansu yace hydar kazo mu rama aiko Ammi ta daddage ta tureshi ta gudu ta koma bayan Fateema maminsu kenan Hassan da tun dazu ya shigo yanata kallonsu sai murmushi yake aransa yace aha Ammina ko bananan zaki kwaci kanki Fateema ta kalli Ammi cikin tsawa tace Allah sai kin tsaya sun rama kaji fitinenniyar yarinya kin iya kalen mgn kuma kice kar a taba jikinki tace maza Abii zoka rama ta kalli Ammi tace kinsan shi kam sarkin miskilanci wlh in hydar ya kamaki zaki gane sai yanxu Hassan yai mgn yace maza Ammina gudo kizo gun Abbanki aiko ta kwaso a guje ya sunkuyo daidai tsawonta tasa hannu ta maqale wuyanshi ya tashi ya miqida ita ya kamo hannun Afreen yace yaki Ummana nasan ke zaki fadan gsky me ya hadasu ya dirata kan kujera ya zauna gefenta ya jawo Afreen yace Abii kuxo nan kunji duk suka taho tsakiyar parlon Fateema ta zauna gefe ta zuba musu ido tasan dai sai dai su Abii su hakura kawai Amir karami da Jaafar sukuma suka maqale jikin Fateema jafar Dan Na,ima ce matar Nazir sai Amir qarami shi kuma Dan da Zainab matar Hussain ta kuma aihuwane Fateema kam shiru bata kuma aihuwaba tun kan yan 3  
Hassan ya kalli Afreen yace Ummana me ya hadasu fadan ? cikin sanyi da nitsuwarta tace Abba su suka tsokaneta fa Fateema tace kai Afreen fadi gsky fa ta Dan kalli Fateema tace Allako mami su sukayi tsokana ta juya gun Hassan tace Abba ka gani ko ta ture hular kanta da Na Ammi yan qananan kitson Kansu suka zubo kan kafadunsu sai sheqi gashin yake tace Ummi Na ta min kitso shine tace inje in kira Ammi itama a mata, toh ina kasan Ammi ita yarinyace tana kukan kitso ? ta fada da alamun tabbaya yace mata ehh sai kuma akai yaya,? Taci gaba da cewa shine da muka je su Abii suka bimu ana mata kitso suna ta mata dry hydar harda cewa wai ita raguwace ba abinda ta iya sai sokanci da kaudi Ummi tai ta musu fada subari sukaqi shine ita kuma da ta tashi ta watsa musu ruwa muka gudu gun momyn jafar Na,ima kenan.Ammi tai maza ta daga yan sawayenta masu kama dana Fateema sak tace Abbana kalli momy kuma ta mana qunshi ya Dan kalli qafansu ita da Afreen yace gsky kunyi kyau Ummi da momy sun kyauta toh mami kuma maita muku ya fada yana kallon Fateema ya Dan kashemata ido ya kwntar da kai yana furza numfashi Ammi ta katseshi a tafiyar da yafara nisa cikin buqatar matarsa,,,,,, tace cikin shogoba tab mami kam wonka ta mana kuma ni kam Abbana kumfa ta samin a idona shine Dan nayi ihu ta dirkamin dundu abaya kamar zata karyani su hydar suka min dry niko Na rama a kansu *** Hassan ya danyi dry cikin nishadi da tsantsar qaunar yayansu gaba daya Fateema ta Dan kalleshi cikin salon  kana son kai yace kiyi mgn mana kinyi shiru ni dai nasan Ammina bata Neman tsokana  ta miqe cikin Dan fushi ta nufi gunsu zata cabko Ammi tana cewa kaji yarinya ina zaune zaki min sharri ganin haka Ammi tace wayyo Abbanna mami ta karyani ya danyi dry mai sauti yace kai Ammina batama isomu bafa ya sauqeta ta bayan kujerar da yake zaune yace maza duk Ku gudu gun babanku Hussain kenan zai kaiku garin yabani aiko duk sukayi waye a guje Ammi Na cewa nice zan zauna agaba hydar yace kaji maiyar mota da son zama a gaba sai son yawo kamar kaza, tace oho dai ba,arama ba,,,,,,,
Suna fita ya jawo Habibatinshi jikinshi ya runqumeta yayi ajiyar zuciya ya dago kanta ya zuba mata ido yace,,,,,
.
Yace Habibati kinyi shiru ta Dan dago ta kalleshi tace gsky Hammana kana son kai kana nuna babbanci komai Adai tai bata laifi su Abii ko sune da gsky baka basu gsky yarsu yarinya ga shegen kaudi batajin mgn ni gsky zan shiga ramawa bayin Allah ya dan kamota ya rungume abarsa yace kai Fatima ai ya kamata ki gane itafa Ammi itace babba kuma ita macece Mae rauni ce ita su mazane dole in koyamusu haquri da mace kuma dole in nuna musu mace uwace yar a lallaba kuma mace mae raunice abin a tausayawa dole in godamusu wahala a kan mace karsu girma basu San wahala a kan mace ba su zo suna horuwa da girmansu kamar yadda Abbana ya horani a kanki Fatina ta Dan kalleshi cikin salon so da qauna tace gsky Hammana duk da haka kafi son Ammi wlh ya Dan kara mannata jikinshi ya rinqa shafa gadon bayanta a hankali ya sake daqo ganta ya daura hancishi kan nata yana Dan gogawa a hankali ya Dan lumshe idonsa ya bude a hankali atake idonsa suka rine sukai jaa ya Dan zaro harshenshi ya Dan lashi lips enta cikin sarqewar murya da jinta kasan pakala yake buqata yace Ammina Ammina Fateema dole naso Ammina fiye da sauran 'yayana Ammina ita Na fara fitarwa daga jikina Na baki kika rainama Na ita Ammina ita Na fara gani a duniya a matsayin gudan jininah Ammina ita ce mai sunan mahaifiyata Ammina itace take gwadamin yarintarki a baya da ban ganiba fuskar Amina fuskarkice jikinta irin naki sak qafarta irin taki tafiyarta mgnarta sakalcinta shogobarta kaudinta da tsiwarta sak irin taki ta yarinta Fateema kin manta yarintarki ko toh ni ban manta ba bazan kuma manta ba kin manta wata rana da yamma a kan hanyar dadin kowa kin mata tsiwar da kikamin ta Dan tsune kanta a girjinshi alamar  ya tallabo kanta yace  i love you my baby Zahra ta Dan dago tace cikin kasala Dan muryarsa da Solon yadda yake mgn da yadda yake mata itama tuni ta fara darso pakala a ranta kai Hamma wai baby da girmana  ya Dan yin kissing inta a habarta ya sunkuyo ya dagota tsaf ya nufi daki da ita yana cewa girma ai sai dai su Hydar suga girmanki Amman banda Abbabsu kam Dan nikam har abada a yarinya danya caraf nake ganinki dai dai lokacin ya direta kan gado ya jawo blanket ya Dan rufesu ya Dan ronqofo kanta yace cikin tsantsar qaunar ta kin manta wasu darare guda biyu da suka wuce kin manta abin da nai miki a dakin nan da kuma can bedroom ena kin manta nine Na karbi quruciyarki kin manta a hannuna kika girma ni Na maidaki cikekkiyar mace cikin sanyin murya tace ya isa haka Na tuna cikin hikima ya zira harshenshi cikin bakinta ya rinqa sarra fata sai bayan wani Dan lokaci ya Dan samu ya iya furta mgn yace Fateema kiyi Addu,a Allah yasa yau zan samawa Ammina qanwa  ta Dan narke a jikinshi tace Hammana zaka tayani naqudane yadanyi murmushi lokacin da ya jamusu borgo yace kiyi shiru kar Garkuwa ta jiki kinsan ta da son ganin qoqof Dan naga yauma daga gembu ta dawo ko suwa ta leqo kuma oho cikin muryar rada tace su yaya Ahmad da Hamma Yusuf da yaya Adam dasu Aysha sai Amira ta leko kuma kwananan zata turawa masu karatu,,,,,,,,,,,
Alhamdulillah ala kulli halin.... - ISMAIL SANI
.
WhatsApp
08038655307

0 comments:

Post a Comment