Sunday, 17 December 2017

'Yar Fulani Part 6-10 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YAR FULANI Part 6-10
.
Ta cikamu su randunan duka taje ta juye wanda tadawo dashi yenzun a bandaki cikin wani Abu kamar daro saidai shidinma Na tabone ta hada daruwan zafi tayi wanka tafito tana tsane gashin kanta.ta tajeshi gashin har gadon bayan ta gashi bakikkirin gashi da santsin da sheki.taje bakin kitchen tace inna kizo kiyimin kitso.tajuyo tana cemata yau baxaki bisu kiwon bane?tace a a zanje mana inna kiyi sauri kizo kimin.to zama zasuyi sujiraki kenan tace a a basu ma fara kucce shanunba fa. inna tace to dauko kifiya.
Ki kawo suka fara duk yawan gashinan kitson kwaya 5 akayi 2 akazubo su gaban goshita 2kuma akayi baya dasu guda 1 kuma tufkeshi akayi atsakiyar kayin.Na gabannan har kan girjinta suke kwace.
Tasa kayanta irin nasu Na fulani rigar yar guntuwa bata karisa  rufemata cibiyarta bama ta daura zani  tasa takal minsunnan Na kiwo. da sauri sauri tasha madaran nono.ta dauki Dan sandanta tace inna midilli.inna tace allah yaba da Sa.a yakare ku.tace amen ta fita suka tfi.
Sungama fita cikin forest din sundauki hanyar hawa kandan wani dutse.gaini mai kiwo yace mata to bimbi kiyi sauri kitafi karki makara adakeki.tace to saikun juyo ko...jaaeh yace kedai tafi.tajuya ta gangara ta kasan dutsen naga tashiga kwadam ta nufi makarantasu ta yan mata tanazuwa tasamu duk sun shiga class tatsaya tabakin window tana lekensu tana tunanin shiga tasan wannan malamin mugune shi bashida tausayi..
Taji andafata tajuyo arazane sai taga yaya Sulaiman ne tace yawwa yaya shiga nake sonyi kuma inatsoron malaminnan yacemata kishiga bazai miki komaiba tace to taje tashiga.
Mutumin da yake tsaye kusa da Sulaiman yace wlh nikam mamaki nakeyi..sulaiman yace namefa.yace na yedda akayi iyayen yarinyar nansuka yerda takeyin karatun boko.kasanfa ba abida fulaninnan suka tsana kamar karatun boko.sufa gani suke bokon kafurcine..mutanneda ko hausa kayi saisuce maka kado.
Sulaiman yayi dry yace ai iyayenta basu san tana zuwaba.tace indai babanta yasan tana zuwa saiya kusan yankata..Adamu yace tokai asuwa kasata makaranta.yace amusulmi Dan uwan musulmi.yaci gaba dacewa.yarinyar tana da ra ayin yin karatun kuma tana da saurin fahimta..lokacin da tafara zuwanan.kullum insun fito kiwo sai tazo ta tsaya a window aji tanajin abinda akeyi.wata rana nakirata nace kekuma fillo me kikeyi anan sai tai dry tace karatun nake son koya.nace to kicewa baban ki ya kawaki mana ta zare ido ta buga hannu agirji tace ai den xaiyankani nacema ta tokeda suwaye kike zuwa?. Tace nida yayunane inzamuje kiwo sai in ce musu xanzo nakoyi krt.sukuma basa hanani kuma duk abinda akayi suma inakoya musu.shine nacemata kin iyane tace min eh.nace to fadamin abinda kika koya.
Hakika nayi mamaki lakacin da naji yariyarnan tana zaiya namin duk abi da ake koyawa yan pramary 6 gashi tana da ilimin addini sosai.to nikuma daga ranar nasata a school din.itakuma bata fashin xuwa kullum zata sallami iyayenta da zummar zata tafi kiwo.suna zuwa nan saita shigo tayi karatunta sukuma sutafi kiwo.garfe daya da rabi ake tashi.sukuma masu kiwon tun 1: suke juyowa..sai sutafi cikin forest dincan suci gaba da kiwonsu. Gashi yenzu har tana a s s3 sune masu gamawa bana kuma tunda ta shiga take daukan no 1 a ajinsu...
Adamu yace to menene sunanta.Sulaiman yyi dry yace nidai tacemin bimbi Amman da yar fillo ake kirantan.Adam yace gskya kasamu lada tunda karabata da jahilci..Sulaiman yace ai daman can ita ba jahila bace.tunda tana da ilimi Arabic.Adam yace gaskiya ne....
Toh muji lbrn bimbi bari mukoma muga ya doctor yerima Hassan Aliyu yake ciki......
.
Yau Sunday ana hutu shiyasa tunda akayi sallar asuba hassan yakoma bacci bai tashiba sai karfe 9:yana tashi yaga Hussain bayanan ya shiga toilet yayi wanka yana ftwa ya shirya cikin wani wando 3 quarter d wta yar Riga ma ra hannu mai hade da hula ya maida hular bayanshi ya kwanta kan kafadadunsa yadan fesa turare ya zira takal mansa.ya dauki key dinsa da lap top dinsa sai phone dinsa ya nufi gdan su yana shiga ya gaida Umma.tace kiyi breakfast kuwa yace sai anjima..yce ya baba tace ai yana tare da baki yace to bari Na gaida ammi.tace to.
Sau 3  yana sallam ba amsaba.parlor shiru bakowa sai yashiga kawai ya kwanta ka kujera ya dora laptop dishi kan cikinshi yanata danne danne..ammi tafito ta sameshi yana kwance.tace kaikuma yaushe kaxo yace daxu.tce o yagaishe to.daga nan ba wanda ya kara mgna a hankali ammi ta kira xubaida tace jeki hadamin tea tce to tajuya ta tafi Hussain yashugo tare da sallama suka gaisa da ammi.hassan yace brother INA kaje da sassafennan?.yace wlh babane ya aikeni inkira mai waxiri akwai taron gaggawan da xasuyi.kumafa harda su yaya Bashir kai dukan muma..hassan yace to Allah dai yasa lfy ammi tace amen.Zubaida nakawo tea din Hussain ya karbi cop din ya fara sha..tace yaya ammi nefa tace inkawo mata yace to hadomata wani harta tafi ya kirata yace .wai nikam Zubaida ban hanaki Sa kanana kayan nanbane? Tace kahana yce OK rashi tarbiya ce kenan tasa kike sawa tace a a kayi haquri baxan sakeba..hassan yace Dan Allah malam kabar yarinya tasake kai saishegen iyayi..ammi tace ai dama xakace haka tunda kaima bakada wata shiga sai ta kananan kaya.Abu ko tsari babu kafa sandal sandal awoje.yace ammi ai shan isakane..tce shan iska ko iskanci ba.tasake kawo tea din hassan ya karba yafara sha.xubaida ta tura baki tace wlh nikam Na gji ammi..Hussain yace da kikayi me oya jeki hadomata wani shayin .taju ta tafi tana qunquni. Hassan yace ammi tuwan shinkafa d miyar kubewa da man shanu nake so.tace ka gayawa mama.yace nidai kenake son kiyimin innace baxan yibafa yace xakiyima  ammina....
Parlon yayi shiru bayan gaishe gaishen da skyi sarki yfra bayani kamar hka.yce Na gdwa Allah daya nunamin wannar ranar kuma ayau dinnan nakson insheda muku cewar zanyi murabus daga kan sarautar nan kuma zanbawa Babba danane mulkin.Bashir ya dgo kansa d sauri yce baba nikuma yace eh kai bashiru..yce baba Ku gafarceni wlh nikam banaso inda mai so acikin kannena to abashi.. Ibrahim yayi maza yce tonima dai bana buqata sai daiko in fawaz..fawaz din yyi dry yace kuji sonkai fa nikuma maiye hadini da sarauta ina sojo ina soja ina sarauta
Sarkin ransa yabaci sosai yace to nafisa kindai ji abin da yayanki sukace.wato ban isa inbasu umurniba.ko. ahankali waziri da galadima suka riqa bawa sarki hqri hardai ya Dan huce. ammi tace a gskya Bashir baka kyeuta minba ai babban wa shine magajin uba.don haka kyi hqri ka karbi wannanr sarutar.yce wlh ammi mulki baya ckin tsarin rywta..Umma tace Aysha barshi a yau da shikadai aka haifa a gdnna da sai muji haushi Amman ai suna da yawa..
Taci gba dcwa kai hassan inna neman alfarma daka zama mgjin ma haifinku.hassan ya dago kansa d sauri yce Umma nikuma tace eh kaifa hassan don wlh ninasan ba wanda zai iya riqe wannan sarautar sai kai Nina dade da sanin  hakan..yce don Allah baba kaci gaba da riqe sarautarka inkuma ka gaji kbwa Bappa Ibrahim .sarki yce shima yaqi kuma kunqi ai duk randa Na mutu sai kusayar da sarautar ko.waziri yce baxa ayi hakaba haqiqa nafisa maganar gskyace tabbas  hassan shine sarki kuma kaima kasan haka mai martaba don duk lkcin da akayi istihar inuwr hassan ke giftawa. Sarki yce to ke Aysha mkkace?ammi tce a gaskiya wannan tsarin baiyiba shidai Bashir din xa abawa.Bashir yce ammi kyi hqri wlh mulkinnan Na hassan ne.. Waziri yce Aysha ke muke sauraro fa..tce duk abinda kuka yanke ai shekennan Umma tce Na gode Aysha d kka fhimce mu.
Sarki yace to hassan nan da wata1 kafitar da mata don so nke randa xancika shekara 40 akan karagar mulki inyi murabus kuma randa za a nadaka aranar za adaura aurenka Kay da Hussain da naziru tunda shima naziru zaidawo cikin makonnan sai yanzu Hussain yyi mgna yce to baba nikuma me yahadani da yin aure.Umma tayi dry tce to haka xaku tabbata bakuyi auren bane? Hassan Wanda ya gama cika da takaici yce to ni wama nasan zan cewa xanyi aure nidinnan dai ace xanyi wani aure ai sai arei nani yacigaba dacewa haka kawai ya Bashir kasa xa ahadamin zafi 2 lkci 1 gskya ni baxan yi aureba.ammi tce tofa kunji irin tunanin da yakeyi kuma wai ahaka kuke son   bashi shugabanci jiha gaba daya mutumin da bai masan abu mai kyeu ba..ahaka dai akayita masu fada da nasiha ..andai tashi taron da sharadin dukansu su fidda mata.fawaz yace tofa sarki hassan sai arege jin kai atsaya anemi aure.inko miskilancin ka ya hanaka wlh za ajajubo maka wata a hadaku kuma kasan gidanmu ba yaji bare saki.Ibrahim yce gayamsa dai Fawax.aka rufe taro da addu.a........
.
Yau kwana 3 kenan bimbi bataje makarantaba sabida Bappa bashida lfy yana fama da ciwan kai mai tsanani har ya  kwantar da shi hatta yawunsa iya tofar sai suga yakoma jini bimbi d hari sun rude sosai.to shiyasa bata samun damar binsu gaini kiwo sai dai taje lambu tadanyi aiyukan da Bappa yakeyi kamar dibo kwan xabbi d ciro banana da dai sauran yayan itatuwan.yau kam tayi niyar xuwa makarantar don haka tana xuwa labbun tayi abinda yakamata tayi da sauri sauri ta wuce school din. tana zuwa uncle  Sulaiman yace yar fillo meya hanaki xuwa kwana 2 cikin sanyi murya ta gaya mishi abinda yake damun Bappanta ta qarisa maganar tana goge qwallah a idonta cikin tausayawa yce kun kashi asibiti ne tace a a yace to ko gobe kukaishi asibitin aduba kan nashi asan meyake damunshi kar abari ciwon yyita qaruwa.tce to xamu kawoshi ko wancan asibitin tanuna wani Dan karamin asibitin.yce a a Ku kaishi babban asibitin cikin gari don acan xa.afi gane meke damushi.tce to ai bamu san wurinba.yce to xan rubuta miki adireshin asibitin saikuje ko. Ya rubuta mata yabata yana dada jadda mata akansuje fa.tace to ta karba ta tafi gida 
Haka kuwa sukayi washe gari ran jumma.a suka tafi cikin gombe .qarfe 9 dai dai tasame su cikin asibitin suka sayi kati sukaje suka kama layi ganin Dr itace take bin layin Bappa kam yana kwance kan benci.har layi ya iso Kansu wata Norse ta leqo tace ardo yabani Buba yashiga...lkcin kuma Bappa yasamu baci ya saceshi.sai ta tashi ita zataje tashiga tamusu bayin ciwan nappan nata to daga bude qofar tarasa yedda xata bude kawai sai tahau turawa da iya karfinta tayi tayi qofa taqi budawa kawai  saita kama bugawa tana cewa kuzo kubu demini.cikin jin haushi da hatsala Dr ya dakawa Norse din tsawa yace ke Hafsat kije kiga wane Dan issakanne yake shirin ballamin qofar office tace sorry ser taje ta budemata qofar dai lkcin da shikuma Dr yerima hassan Aliyu yake cewa ai dama irin wannan bugun qofar sai masu suna ardo da jauro ne xasuyishi mutane kullum basa taba wayewa.yadago idonsa dai dai lkcin da ta xauna kan kujerar da aka tanada Dan majin yata da sauri yasake kallonta sama da qasa....
.
Suna cikin mota ya juyo ya kalleta yace qanwata me sunanki.tce bimbi cikin mmki yce bimbi kuma tace eh yce to sabida me ake kiranki bimbi don dai nasan ba shine sunanki Na gaskiya ba.tce eh sunana fateema ana kirana bimbine don an ayfeni da safe yyi dry yce to wannan kitsonfa me sunansa tace kumbo bobini.yce to mesunasa da Hausa tce bansani ba nima
Dai dai  lkcin suka shigo hospital ya bude mata ta fito ya dauki wasu kayan itama ta dauki wasu suka shiga.suna tafiya suka hadu da wata Norse tace oga a ina kasamu wannar kyekkyewar yariyar yce qanwata ce suna shiga ya ajiye kayan hannunsa yce to Bappa bari naje nayi sallah gashi yau jumma.a Bappa yamishi gdy.shikuma yce to Fatima sai nazo anjima ko ga Abicinku yana cikin ledanna ko tce to yayana mun gd sai kzo.
Bayan suntaso dga mallacin ya wuce gda suna zaune a parlor yce ammi adafa min abinci mai Dan sauqi zan kaiwa wasu  Fulani tce INA yan uwasu.yace inaga dga nesa suke tace to....hassan da yake kwance yana kallon kwallo shida nazir a laptop dinsa yce hum ammi dama kin hutar da knanki wa ennan mezasu iya ci in banda nono duk inda suka shiga sai yayi qarnin nono.
Hussain yce ammi kiga pic din yarinyar ya miqamata woyarsa tce kai yarinya kyakkyawa fara Sol kamar bala rabiya.nazir yce ammi bani ingani yana karbar woyar yce lahh ammi itace yarinyar da hassan yyi fada da ita muna dwwa cardi Hussain yce haba dai nazir yce wlh itace ko hassan? Ya tabe baki yce oho nikar kusani cikin hirarku.duk sukayi dry. Ammi tce mutum ko ina inya je saiya Nuna baqin hli
Da safe suna xuwa asibitin Hussein yce xomuje iduba wani abokina hassan yce to yabishi skje sna shiga yaga fatima yja tsaki ya harareta.yadai gaida Bappa ba yebo ba fallasa.Hussain yce Bappa wannan dan uwanane Bappa yce Ku tagwaye ne yce eh ya ajiye musu abincin yace Fatima ya kke tce lfy.mungode yayana kaikam kana da hankali.da tausayi.. hassan yce to waye mara hankali d tausayin?. Tace oho aishikam yasan Kansa mara imani kawai hassan ya yce kaji shegiyar yarinya nitake cewa  mara imani da tausayi.da yake a hankili yyi maganar Bappa baijiba Amman ita taji kuma Hussain ma yace mutafi to ya jashi suka fita hassan yai ta fada kamar zai doki Hussain shidai dry ma suka bashi mutane kamar kishiyoyi dasun hadu sai fada.sunan kamar wuta d auduga
Da daddere hussain tare da su ammi yazo suka gaida Bappa Umma tce babansu yace agaishe ka da zamuzo dashi to sai yayi baqi Bappa yayita gdy Umma ta jawo Fatima tace Aysha ga rinyar nan kekkewa da ita ammi tace wlh nika yarinyar ta kwanta min Umma tyi dry tce ai dama kekam kinaso 'yaya mata.sukayi musu saida safe suka koma gda 
Washe gri aka sallami su Fatima Hussain da kanshi yce zaikaisu tashan dukku su shiga mota suna shirin fta yce Bappa xomuje kuyi slm da dan uwana.itakam Fatima badon tasoba tashiga ya gaida bappa amutunce sukayi slm Bappa ya fta fatima Na qoqarin fita ya jawo hannuta d qarfi yce to uwar reshin kunya wlh kinci Sa.a Bappa yana nan da sai Na karyamiki hannu wannan shegen bakin in pasashi Kuma innaxo miki dinki indinke bakin duka inga taya zakiyi fitsarar ya murder hannun nata saida tayi qara.Hussain yce kaifa mugune brother xaka karyata fa yce ai dama sonake inkaryata din.ahaka dai suka tafi ya kaisu tasha suka shiga motar kwadam suka tfi....
.
Cikin tsawa yace mata ke mahaukaciyar inane waya baki damar shigo min office ko ancemiki nanma jejine da zaki shigomin kaitsaye ubban me xanmiki ni yau maza nake dubawa ba mataba ko kece ardo yabanin?ya sake dannamata harara yace kallekifa saikace shanu qafa duk tabo kindebo shi acan dajin naku kin kawaminshi office dina don rainin wayoko.tomaza fita kibani wuri yagadei tana tsaye yace ke kauce karna dakaki kin tsaya kintsuramin ido kamar mayya to kya ci kanki ko kici jakunan rigarku.yce ke Hafsat maxa fitarmi da ita tace to ta kamo hannu bimbi ta nufi kofar fita suna isa bakin qofar ana turo qokar za ashigo qofar tabugeta sainda ta fadi qasa.
Da sauri ya shigo yana cewa subahanallahi kiyi hqr wlh bansan da mutumba awuri ba ya kamota ya tada ita yana cewa qanwata bakiji ciwo bako.itako sai baya baya takeyi tajuya ta klin hassan takuma juyowa tkli Hussain cikin yanayin jintsoro.Hafsat ce tace oga tsorofa kuke bata kaga yedda jikinta ke bari a hankali Hussain yamatso kusa da ita yariqo hannunta yce karkiji tsoro qanwata mu yan uwane shi yayanane uwa daya uba daya.hassan yce do Allah can malam ni kafitar minda ita daga nan hussan yace bazata fitaba ya zaunar da ita yajuya gun hassan yce.
Brother anfa kawo wata mata aihuwa kuma dole sai an mata tiyata.sai kaje kayimata yace to kaifa me aikinka Hussain yyi murmushi yace xanduba sauran marasa lfyn da kake dubawa hassan yace to naxir fa? Yace shikuma naxir ankawo wasu samari sunyi hatsari yana daure musu karaya..Hassan yace wato kaikuma Dan xaman banxa ko?Hussain yce Kaidai jeka kayi tiyata.
Hassan din ya tashi yana qoqarin fita yana cemusu kuma kayi maza kafitar min da wannar bororiyar daga nan inyaso kwayi hirar awoje dai dai lkcin da yazo kusa da ita ya danna mata wani mugun raqqoshi saida tayi kara shikuma yafi.
Hussain yace kiyi hqri kijiko qanwata tayi shiru yace kece mara lfy tace a a Bappa nane kuma yana woje yce to jekishigo dashi.
Bayan ya duddubashi yce Bappa ciwan kai ne kawai bakada bp Amman za abaka gado.Bappa yace to yaro kuma gashi banxo da namiji ba sai bimbi Hussain yace karka damu Bappa zanlura da kai ai nima kazama banana.
Da kanshi ya kaisu dakin daxasu kwanta yabashi magunguna.yace to Bappa bari muje mu saya maka buta da bokati d taburma da dai sauran abinda xaku bukata.Bappa yace da bimbi xakaje yace eh da ita xanje karka damu xandawo maka da ita cikin lfy bppa yace Na yerda da kai yaro bakayi kama da ma hainci ba....
.
Yau Sunday kuma tunda yadawo masallaci ya shiga wonka yfto ya shirya cikin qananan kaya ya dauki key din Sa da woyarsa ya nufi gidansu yau gaba dayan su suna hade a parlon sunata hirar yaushe gamo don jiya da dare su Hajja Babba da Alh Babba suka dawo umra kakannisu hassan kenan kuma sun dawo tare da amir kannisu hassan wonnada yake karatu a Jami.atul Madina ya gama digiri dinsa"
yashiga tare da slm amir yatashi da sauri yaje ya rungumi hassan yana cewa yaya nayi missing dinku all yyi murmushi yace muma haka yai masa murnar gama karatusa amir yce gsky yaya yafa kamata musamu anutys dukansu sukayi dry" Hajja  tce mishikili kafi mahaukaci ban haushi ya Dan yamutsa fuska yce kundawo lfy tce lfy lau ya halinka..Alh yce sai abida ya karu  halikam ai bazai canjaba" .Hussain da yake yankewa ammi farce yce nifa yunwa nakeji..amir yace to yaya biri inkawo mana abici yje ya kawo musu hassan da yketa hira da ya Bashir da fawas yce yaya ku sauqo muciko.suka sauqo gaba daya suka hadu suna ci ..Hussain ya gama yanke ammi farce ya juya ya dauki cokali zai faraci....
Hassan yce kai malam dakata kaifa wlh ka iya qaxanta saikace ba Dr ba..duk suka tsaya suna kollonshi. Umma tace meyiyi Na qaxanta" yce kalifa Umma yanxu ygma yanke farce kuma bai wanke hannunsa ba zaici abu ..
Ammi tace ikon Allah ni Aysha Na haifi abin Al ajabi yenxu farcen nawa kake qyema to kai baka dashi ne...amir yyi dry yce lah ase dama ammi kekika haifesu kuma kike wani sharesu don su yan farine 
Tce kaci gidanku amir duk sukayita dry ammi dai kunya tasata tabar palon
Sarki yce ku dai barsu suci abincisu..
Sungama cin abinci..suna tahira.
Alh Babba yce to Aliyu lkci yyi da su hassan xasuyi aure..sarki ya gyera zama ya gayawa mahaifimsa yadda sukayi da yaransa kwanakin baya ya Dora dacewa kuma 
Yenxu saura wata daya Amman dukansu ba wanda yaseke maganar.' Alh yce toni ina da xabin da nayimusu..
Hussain yce wadin nidinnan dai da ajina da hankalina ka xabamin mata toh nikama inada wacce zan aura sai dai ko Dan uwana xaku xabawa.
Hassan yce bana buqata yana fadar haka yatashi ya tf rai abace yafita kenan ko awa 1 baiyi da fitaba nazir ya qira Hussain yace Hussein kayi maza kazo asibinmu yce lfy kam?
Nazir yace kaidai kaxo cikin rawar murya yakewa hussani maganar
Arikice Hussain ya gywa iyayen nasu bari yaje asibiti 'ya Bashir yce lfy kuwa.yce nima bai gayamin komaiba ya Bashir yce to muje.. amir yce nima xanje 
Lkcin da suka isa.naxir yaja hannu ya Bashir ya shiga dashi wani room su amir Na biye dasu abaya.
Hassan ne kwance cikin jini gaba da kafafa funsa sun karye hannu Sa 1 ya karye gashi ya suma tunda yayi hatsarin bai farfadoba kusan awa 3 kenan Amman haryenxu bae dawo hayyacinsa ba dukansu sai salati sukeyi Hussain da amir d nazir kuka wai wai sukeyi kamar yara ya Bashir ne mai dan qarfin zuciya shiyake musu fada suyi shiru....
.
Yau kwana 5 dayin hasarin hassan Amman har yau bai farfado ba..
Ya Bashir ne da Ameer suke gunshi kullum mai martaba d Umma sai sunje sau 3 haka kuma su hajja.
Amman ammi ko sau daya bata jeba.ya Ibrahim ne yaketa cukucun fitar da dasu qasar India yaune 
Yagama hada musu komai Na tfya..qarfe 9 Na deren yaune✈ zai tashi
Hussain zaune gaban ammi yanata.kuka 
Tace kukan namene...cikin shesheqar kuka yce
Ammi don Allah kije kiduba dan uwana kafin mutafi kowa yaje saikece ba kijeba ammi memuka yimiki mai tsanani haka dayasa baki damu da Al amuranmuba ko lfyarmu bata damunki .cikin dakewa tce to in naje xanbashi lfy ne
xubaida tace a a ammi Amman kinsan ke ma haifiyar sace inkinje kinmishi addu.a Allah xai karba tace to tashimu tfi
Lkcin da ammi taga halin da danta yake ciki batasan lkcin da ta fara kukaba 
Tana ya Allah ka rufamin asiri katashi wannan dannawa Allah kabashi lfy.Allah kana gani wannan dan nawa bai taba bata min raiba.kuma ko ya  bataminma Na yafe masa duniya da lahira ammi kuka ya Bashir dakanshi sai da yayi kuka.......
Qarfe 8  daidai suna cikin asibitin har anbasu gado doctor s suka duqufa wurin ceto ran hassan kowa Na iya qoqarinsa Amman abin yaci tura Dr sai zirga zirga sukeyi da dagon turanci suna kan hassan har qarfe12 Na dere sanna babba su ya fito yce wa Bashir gsky sai dai kuyi hqri harzuwa gobe da safe muci 
Gaba da aikin amma yanzukam. Bai farfadoba..
Ahaka sukaci gaba da xama a india har tsawo kwana8 Amman hassan bai farfadoba saidai wannan Dr ya leqa wanncan ma ya leqa 
Da sarki yaga haka sai yace sukoma saudi 
Cikin kwana 2 suka koma saudi.
Suma likitocinsu sun yi iya bakin qoqarinsu amma INA Allah bai nufa ya farka ba.
Su Umma d ya fawas d adda Mina dasu Hajja duk sunje dubashi..
watan su 1 acan Hussain yazo Nigeria don ya dauki iyayen amminsa suje tare.
Ya je asibitinsu atsatsaye har xai tafi nazir.yce Hussain
Nifa akwai wani abokina da ya kwatatamin wani mutum mai maganin gargajiya yce min shi mutumin koda mutum yakai wata 5 ne asume yana farfado da mutum kuma kareya koda takai ga qashin mutum ya faffashe yaku watse akan titi to yana iya gyerawa.
To shine nace ko xamu gwada kawo hassan gunshi.
Hussain yce kaiya nazir abinda bature baiyiba baqin fata zaiyine? yce to ai kowa da irin baiwarsa kuma dama na gayawa babana waxiri kenan kuma yce min ya gayawa sarki
Sarkin kuma ya yerda harma yacewa su yaya Bashir sutaso yau dinnan su dawo...
Muje xuwa masu krtu waishin wayene mutuminnan mai gyeran karaya?.
.
Bayan sallahn isha suka iso.
Suna sauka a airport ko gida basu jeba suka wce gidan mai maganin su 6 ne harda hassan din Hussain d yaya Bashir amota daya ya Bashir yana ruqqume da hassan  Hussain kuma yana drive daya motar kuma nazir ne d ameer sai Saminu dayake nuna musu hanyar..
Tafiya kadan sukayi suka isa cikin Forest Saminu yace yauwa ka shiga nan ya nunawa nazir wata yar qaramar hanya..
Suna Dan fitowa fili kadan nazir ya tsaya yce to Saminu wirinna fa gaba daya dabbobi nake hange babu ta inda mota xata wuce.
Saminu yce eh ka fito muje.yaya Bashir yace yadai kuka tsaya sukace hanyar ta qare daganan saidai muqarisa da qafa.
Bashir yace to muje Saminu.
Suna tfy suna tsallaka shanu har suka isa inda suke hango hasken wuta.Saminu yyi slm ya gaisa da samarin wurin yce wurin. Ardo yabani mukaxo ko yananan sukace eh yana can kuje.
Suka gaisa da ardo .
Bashir yamasa bayanin abida ke tafe dasu.
Ardo yakira gaini yce maxa kaje can bakin garke xaka ga baqi da mota sai kanuna musu hanyar baya suqara so yce to yaje ya nunamu su hanyar ameer ya shiga motarsu Hussain yaja suka qariso wurin.
Ardo yace maza aje akawo masa fitila.
Ameer yace a a ardo ga haske ya kunna wani lontor gaba daya wurin ya dauki haske saikace rana..Bashir yayiwa ardo bayanin lkcin da abinya dauka yaci gaba d cewa kanaga xaka iya.ardon yyi dry yace da ixinin Allah yau dinnan zai dawo haiyacinsa.cikin jin garfin guiwa Hussain ya dago kansa yce Allah ko ardo..alkcin shima ya dgo kansa yce lah hussani kaine garinmu cikin mamaki yce nine Bappa dama kaine kuma kaine mai maganin yce eh nine Amman shidin kam bani zanmasa ba.Amman karka damu muma munsamu damar yimaka hallacin d kayi mana.
Suka shiga cikin gidan .part 3 ne a gidan 2 Na majinyata ne da yake ajiyewa  1 Na mata 1 kuma Na maxa 1 dayan kuma yana can ciki shine Nasu ardo.da iyalansa
Ya kaisu wani Dan daki yana da Dan girma katifa biyune aciki sai wurin sallah dakin tsaf tsaf dashi suka kwantar da shi kan katifar.
Ardo ya tafi cikin gida yncwa bimbi ga wannan yron d ytaima kamana abirni tce.Bappa yayana yce eh shifa ya kawo mara fly kuma ma tashine kinga kenan kexakiyi aikin tace to.
Yce yauwa kekuma hari hada msu abincin nan da za akai gun masu karatu akaiwa baqin tace to malam.
Shida kansa ya kai musu yce kuci kuyi sallah tukunnan sai axo afara aikin...
.
Ardo Na gaba fateema Na baya tana rike da kwariyar magunguna da allon qarfe sukayi slm suka shiga
Ardo yaji ddi sosai yada sukaci abunci hatta ameer mai yawan qenqeni ma yaci xabin Dan yaga suna da tsafta sosai.
Fateema ta gaida Hussain cikin fara a ta gaida sauranma tacewa naxir kai mai kashe nagge in dan uwan kamasifefe yace ayya fullo ai shine bashi d lfy.
Tab tace aradu Bappa bazan mishi aikiba.Bappa yce kina haukane to maza matso kiyi aikinki Hussain yce kiyi haquri kiyi don ni Dan uwanane fa da qer dai aka lallabata ardo kuma yana ta fada shimam ameer yaji yarinyar ta burgeshi.
Ta dauki allon tayi rutu ta wanke tace yayana karbi kabashi yasha.Hussain yce ai baya iya shan komai tace mishi xaisha da ikon Allah.ya karba ya bashi shi dai baiga alamar ya hadiye ba itakuma tce abinda ya hadiye zaiyi aiki ta dan lakuci wani mai ta shafa masa a fiska..tce to sai da safe .Bashir yce iya maganin kenan kuma kukace zai farka tce eh karka dmu yaya.
Ardo yace zanzo kafin ayi kiran sallah asuba.
Sukace to ya tfi..sudai gaba dayan su babu wanda yyi bacci Bashir yana ruggume da hassan tunda aka bashi rubutu Hussain Na xaune agefe naxir d ameer d Saminu sukuma suna kan daya katifar.
Can kusan asuba bacci ya kwashesu sai ya Bashir ne kadai baiyiba...yana xaune ya qurawa qaninshi ido..
Kamar a mafarki yaga hassan ya bude ido yana bin dakin da kallo.ya juyo gun yaya Bashir dinsa yanata kallonsa..
Cikin tsananin farin ciki Bashir yace alhamdulillahi.. hassan hassan yaita kiran sunan sa da qarfi.
Dukansu suka tashi afirgice suna cewa yadai yaya Bashir. Yce ya farfado.gaba dayansu sukayi kanshi sunata hamdalah Hussain harda kukan farin ciki..suna cikin haka ardo ya shigo yce ya farka ko? sukace eh amma baya magana.yce to 
Ga wannan rubutun in naje ina kiran sallah ku kuma sai kuna bashi kuma .kuna 
Kiran sallah harzuwa kan kalmar shahada.
Haka kuwa sukayi"suna xuwa wurin yin kalmar shahada..saigashi shima yana binsu suna rufe bakinsu
Yce yaya Bashir inane nan yce wurin maganine yce o.
Su Hussein sukayi ta murana..da safe fateema ta dauko kayan aikinta tana shiga yce kekuma me ya kawoki nan tce kodai kai meya kawokaba nankam gidanmune ba asibitin kaba. bashir yce kayi shiru kawai kabarta tayi aikinta..
,
Ta zauna.'tce kawo kafan naka ko.intafi harkar.gabana" Ta dauki. Wani dan.mai tarinqa'bin duk. Inda karayan yake tana.shafawa"atake wuraren sukayi.jajawur'cikin jin radadi. Da a xaba'hassan ya.rinqa" cije lips.dinsa yana murxa.kanshi.yasa. hannu shi.ya.damaqi yaya Bashir da yake riqe.dashi.idanunsan.. sukayi jawur.jijiyoyon kanshi.suka taso sama." Fateema.ta kalleshi tyi dryar mugunta"Tce malam.infa kasan"kai.regone.toka shiyar ihu.kuma wlh.qarti xansa"su danne .minkai" cikin"wahala.da masifa"yce wlh.kekam baki isa kiyimin abinda."xaisani ihuba...tace shikenan."
Tasake'shafamar.wani farin mai.ta qara.woni akai.kamar man shunu.'a.take yaji wani.irin sanyi.kamar ba wurinne.yake ciwo yanxuba.wani" bacci.mai ddi ya dau keshi.
Tace"yana farkawa xai.tashi'ya tsaya da.izinin Allah." Sukace.to mungode"
Garfe 9 su sarki. Suka iso'shi da iyyensa da matansa' lkci.da ardo.yazo.suka.gaisa..."fateema.kuma ta ajiye .abincin da takowo musu"ta gaishesu.cikin fulatanci ta juya ta tfi.sukuma sukaci gaba "da hirasu"ta.manya!
Alh Babba. Yce" haqiqa. Akoi wani haske atattere da.wannan"xuwan.namu .ardo yce nima.naji dadin 'samun nasaran wannan.aiki da.akayi.Alh yyi.dry irintasu ta manya.yagyera.xama'yce."ni Usman. Ina Neman.alfarman".kyautar.'ya agareka.ardo' ya dago kansa.ya kallesa"cikin' rashin.fahimta"yce.bangane nufinkaba."Alh. Yce.abinda' nake nufi.INA nemawa jikana"auren'yarka.fati'yci.gaba.da cewa.haqiqa.Na dde.ina'yiwa jikokina.istihara.akan.nema'musu'mata.ko...yaushe in akayiwa. Hassan inuwar.yarka"fateema ke.baiyana.cikin yanayin.haske"to kaga.saiyau"Allah ya.nunamin'ita!
Ardo yyi.shiru"nadan.wani lkci'sannan.yadago...".kansa"yce.kuyi hqri .nrga .da Na.mata"miji.dama jira.nake' tacika.shekara"14. Sai ayi bikin.cikin yanayin neman alfarma.sarki."yace tabbas.nima duk'lkcin danayi istihara inuwar.fateema.ke.......gilmawa cikin.wannar shigartata.ta Fulani.kayi hqri.ardo" kabawa.Dana auren.ta.waxiri. yce.Muna.
Neman wannan alfarma.don Allah dakuma.albarkacin annabi.' Da fulakun.dake.tsanin mu.
Ardo yce.to" barina kira.muku mai bada ita.duk'abinda'yce.........shikenan.ya aika.aka.kiramasu.  jawro' yazo .suka gaisa.cikin karamci.waxiri.yamishi' bayanin dllin kiransa.yyi dry.yce."ai dama hassan.shine.Mijin." fateema.nikuma: nabashi.aurenta' duk.randa kuka.shirya"kuxo a daura.musu.aure"
Cikin tsananin .frin.ciki suka.rinqa"gdya.
Suka.ajiye"cewa duk'randa.xa.asallami."hassan rannane.xa'a.dauramusu auren..
Su Hussain. Da suketa hira.dasu ammi.a gindin. wata. bishiyar.mangoro. umma.tace.su.Alh kam wacce maganace".sukeyi  .da taqi qarewa.ammi.tce.Allah dai .yasa alkharine" yaya Bashir daya fito dakin.yanxu.kuma" yasan Duk.maganar da akayi"yyi'dry.yce. alkhairin nema" Babba.kuwa.hassan" daya samu yadan jingina da pillow.cikin murya irin ta majin yata.yce nidai naji ajikina  bawani alkhari.
Sukayi"dry.ammi.tce"  ai kuma kayi sauqi bakinka.yabudu.sai
bakin baki zakatayiwa.mutane. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment