'YAR JAMI'A Part 9 (THE END) .
Kome aka sa wa lokaci toh alal hak'ik'a sai yazo,yau take asabar wanda shirye-shiryen tafiya tsaf sun gama had'uwa,a inda dady yayi musu jagoranci,ali driver ya kai su airport suka wuce abuja,ko da suka isa can sameer ne yayi wa dadynsa waya aka zo aka d'auke su,sai dai ummah tuni ta gama tsara inda zasu sauka gidan babbar aminiyarta inda a can ne 'yan uwanta da abokan arzik'i zasu taru,dole ba don yaso rabuwa da beauty ba sameer ya sauke su acan kafin ya wuce gida,bayan isarsa gida ne sameer ya iske ameenu da tun ranar litinin ya taho don ya shirya masa yadda dinner zata kasance,wanda ya tarar tuni an gama komai lokaci kawai ake jira! . _8:00p.m(na dare)_ . Dandazon motoci ne na alfarma kana ganinsu kaga zallar ajiyar naira aciki ke ta faman tururuwar shigowa gidan can tsakiyarsu wata doguwar mota ce bak'a tasha wanki sai kyalli take wanda da alama ango ne aciki,haka suka jero suka yada zango a tsakar gidan,yadda abokansa ke fitowa daga motoci cikin kaya na alfarma wanda suma dai sukai ankon shadda blue wanda ita kad'ai zai gaya maka cewa bikin manya ne,hira da dariya kawai kake iya jiyowa ta kowane yanki,sameer dake cikin mota zaune ne ya fito a tare wani irin ihu suka sake ganin ango yasha wanka na had'uwa shadda black ce sanye jikinshi tasha zubin aiki golden colour d'an senegal,sai hula da takalminsa duka baki,hannun nan sanye da agogo itama golden,tattare a lallausar farar fata irin ta sameer abin dai ba'a cewa komai,zagaye shi suka zo sukayi kowa da irin tashi salon tsokanar can ameenu ya lek'o ta cikin mota da yake shi ya tuk'o sameer yace ango lokaci na tafiya fa akira amarya ko naje na fito da ita!wani kallo sameer ya wurga masa sai kuma can yace toh ai sai kaje ta fito da ita mu gani,gaba d'aya waje aka sa dariya wasu na fad'in jealousy!! Abin shina sai ya dawo yana bashi dariya dole ya zura hannu cikin aljihu ya fiddo waya ya shiga laluben lambarta,bugu biyu ta d'auka nan ya shaida mata zuwansu,ko me ta fad'a daga d'aya b'angaren ya bata amsa da ok my princess;da haka ya kashe wayar aka ci gaba da hira ana jiran k'arasowarsu! . Wani lokaci kad'an bayan wannan hayaniya ce ta 'yan mata had'e da gud'a kake jiyowa wanda duk dangin ummah ne na yola da ta sanar dasu bikin suka xo sai kuma 'yammatan gidan da suka fito ga wani k'amshin turare daya lullub'e gidan tun bayan fara fitowarsu,inda 'yan matan amarya suka sanya beauty a tsakiyarsu duk kan ninsu sanye da anko,baka iya hango komai daga shigarta,tafiya suka shiga yi basu zame ko ina ba sai jikin motar sameer inda suka zagaya suka shigar da ita sannan suma suka nufi sauran motocin suka shiga,duk wani zumud'i da rikicewa sameer ya gama yinshi burinsa kawai yayi ido hud'u da gimbiyar tasa don haka cikin sauri shima ya bud'e motar ya shiga" watabarakallahu ahsanal khaliqeen"abinda sameer ya iya fad'a kenan jikinsa na kyarma ya matso daf da beauty ya kai hannayensa biyu ya d'ago ta daga sunkwi da kai da tayi,karaf suka had'a ido wani shu'umin kallo suka shiga jefar junansu dashi inda ko wannensu baki d'auke da murmushi na farin ciki" a haka ameenu ya ja motar saura na biye dashi suka bar gidan,yayin da a hankali beauty ta maida dubanta k'asa tace ni kam ka bar kallo na haka"daga k'asan zuciyarsa ya sako wata dariyar had'e da k'ara matsowa sosai ya matse jikinta da nashi,shinshina k'amshin jikinta ya shigayi,yanda yake bin wuyanta da shinshina yasata fara janye jikinta tana tureshi taji can kamar mai rad'a yana fad'in ki barni naji k'amshin matata ko kuma yanzu labari ya canja,ya zatayi da sameer ta san halinsa idan ya fad'i magana dole ba dan taso ba ta barshi ya ci gaba da abinda yake inda sak'onsa ke ziyartar kwakwalwarta tana karb'a! . Karya kwanar da akai ne aka shiga wani k'aya taccen hotel ya tabbatar da beauty da an k'araso wajen inda cincirindo na motoci suka rigaya suka cika wajen,a bakin event hall d'in ameenu ya tsaida motar a inda sameer ya fito ya zagayo ya bud'e waa beauty k'ofa ya rik'o hannunta k'am kamar wacce za'a kwace masa take masu nan da nan aka fara ruwan d'aukar hoto sai alokacin sameer ya iya k'are mata kallo wanda ita ma dai doguwar bridal gown ta saka bak'i wuluk ta bi jikin nan nata,sai head d'in ta golden da takalminta,sosai beauty tayi kyau,don duk yawancin hotunan sameer na kallonta ake yi,lura da haka yasa ta d'an b'ata fuska tanai masa rad'a ka kalli mai camera mana !shima ya rad'a mata nak'i wayon!dariya suka sa a tare kamar daga sama taji ana mata magana ta baya inda akace amarya ta sha k'amshi,muryar data doki kunnenta yasa ta saurin juyawa don tabbatar da zargin da zuciyarta ke yi mata,nan tayi tozali da zee-zee dake tsaye cikin ankon da ita kanta bata san dashi ba don ta lura kusan kowa yayi ankon,a d'an rikice ta kira sunanta tana nunata da yatsa,cike da jin dad'i zee-zee ta matso tace mata juya bayan dinner mayi magana,haka beauty ta juya sameer ya k'ara manna hannayensu suka nufi ciki! . Sabon kid'a aka saki inda jama'a kowa ya mik'e don tarbar ango da amarya a nutsu suka nufi ciki k'awaye da abokai na take musu baya har suka k'arasa mazauninsu daga nan ne kuma shagalin biki ya fara a yanayinda kake iya hango abokan ango da danginsa suna zubar kud'i sam babu k'anshin tausayin naira tare da su,haka daga b'angaren dady da ummah kowa ya baje kwanintarsu ga 'ya d'aya tilo da suka mallaka a duniya,taro yayi taro can ummah ta hango dady na kwaso shoki na kud'i yana sauke wa a goshin 'yar tashi,dariya kawai ta saki cike da jin dad'i don in da sabo ummah ta saba da halin mutanen nata biyu,jama'ar waje kowa ya gani dariya yake,haka shagali ya ci gaba har kusan 11:na dare inda daga haka jama'a suka shiga watsewa,shima ango ya rik'o amaryarsa suka shiga mota zee-zee na biye da su!hira akai tayi cikin motar ana maida zancem dinner haka har suka k'araso gida nan ne zee-zee tai sallama da ameenu itama dai haka sukai sallama da sameer har ta juya zata tafi ya kira sunanta murya a k'ank'ance yace pls kar ki late bacci nake ji" a kunyace beauty ta shige gida da gudu zee-zee ta bi bayanta,a tare suka saki wata irin dariya sameer da ameenu ganin abinda ya faru da haka suka shige mota suka fita a gidan! . Tun bayan shigar beauty gida basu zame ko ina ba sai d'akin da aka ware mata inda ta shigar da zee-zee ta kuma kullo k'ofar,saman kujera suka zauna beauty duk ta gama d'okin ta ji labarin,sai kuma ta ji zee-zee tayi shiru tab'o ta tayi da hannu tace wai ke dilla ki fara bani labarin mana,murmushi zee-zee ta saki sannan ta gyara zamanta sosai tace,toj sarkin son labari bud'e kunnenki kiji da farko dai kamar yadda na labarta miki a waya nayi sabon saurayi mai kayan harka,toh wannan yaron kusan shine silar duk wani abu daya faru domin kuwa bayan sati da had'uwarmu ya min kyautar mota ta azo a gani dole na je inda nake aje waccan tsohuwar motar wacce nace miki itama bani akai amma ba wanda ya sani a gida bayan mama,na had'a su biyu yau na hau wannan gobe na hau waccan,fantamawa kawai abuna nake har ta kai a unguwa kowa yasan da sake mota ta,ana haka kwatsam na dawo daga jami'a wata rana ina shiga ma'ajiyar motar kwatsam muka ci karo da baba wanda nasan ba makawa ni yake zaman jira,ranar nan k'arshen danasani sai da nayi ta,don dukan da nasha ranar kamar bazanyi rai ba ga horo mai tsanani na ya cireni daga jami'a babu inda nake zuwa kullum ina gida zaune,na tak'aice miki labari mai kai bolar gidan mu wato almajirin layi ya fini daraja a gidan nan,ba anan abin ya tsaya ba har mama sai da ya shafa gida baba ya turata a karo na farko azamantakewarsu halin yanxu dai bai jima da dawo da ita ba,maganar bikinki kuma lamba na gani an kira ni a waya koda naji namiji ne da kamar bazan magana ba saboda 'yar jami'a na wahala....kul kar ki sake ce min 'yar jami'a kirani da sunana hajara,beauty ta katseta!dariya zee-zee ta saki tace shegiyar gari wato kin ji jiki ai na samu labarin komai ke dai bari na gama miki,haka taci gaba da cewa bayan na amsa wayar ne ya labarta min komai cewa shi abokim sameer ne wanda zai aure ki kuma yana da buk'atar mu had'u da yake hajara na shiryu sam banji nauyin b'oye masa komai nawaba don kar yaga na hana sa gamuwa dani yayi zaton ko wulak'anci ne bayan ya gama ji ne yace ma bashi lambar baba,duk da ina gudun yim wani laifin amma daya matsa dole na bashi,da haka mukai sallama! tun lokacin ban sake jin shiba sai lahadin data wuce ina zaune tsakar gida ina wankin kayan yara naji shigowar baba kallo d'aya yayi min ya kauda kai sai ji nayi yace kiji waje da bak'o zakuyi magana,wani rass gaba ya fad'i sanin cewa bazai wuce cikin abokan baba yake son had'ani da wani don ya zama horo a gareni ashe abin ba haka bane sai dana fita muka gaisa naga saurayine kuma ba laifi kallo d'aya na yaba dashi amma dana ji shine ameenu da mukai waya a baya sai na saki jiki mukai magana ya kuam shaida min da baba ya amince kuma akan gobe litinin tare zamu taho anan abuja na yi wasu shirye-shiryen biki,da yake had'uwar farko ce sai na kasa sakewa dashi sai da muna kan hanya zuwa nan yake shaida min cewa ya nemi aure nane a wajen baba duk da bai ganni ba amma ya yarda da nadamar da yaji daga gareni,tuni na shiga godiya ga mahalicci na hajara na k'ara yadda cewa Allah na tare da mai tuba yayin laifi,toh tun daga haka kawo yanzu wani son shi nake ji har bana son naji bana tare dashi,ai kin gane,k'arashe maganar zee-zee tayi tana kashe mata ido na wasa haka suka wkashe da dariya a tare,suna haka suka ji ana bugun k'ofa beauty ce tace waye?can suka ji muryar yarinya tace wai aunty hajara ke zo d'akin sama ana nemanki!toh kawai beauty ta amsa da sannan ta mik'e tace ina zuwa da haka ta nufi hanyar fita! . . D'aki ne cike da iyaye mata hira sosai suke yi haka beauty tayi sallama ta shiga can tsakiyarsu ta hango ummah don haka ta nufe ta,ummah gani ta fad'a kanta a k'asa,kafin ummah tayi magana Aunty balaraba tace tashi ki shiga bayi gani nan zuwa"toh kawai tace nan ta mik'e ta nufi bayi,waje ta samu a ciki ta tsaya tana 'yan dube-dubenta ciki taji shigowar aunty,wankan magarya tare dana turaren mata aunty tayi mata duk wan sak'o da lungu na jikin beauty sai data tabbatar data wanke shi tas sannan ya samh turare, bayan sun gama ta rik'o hannunta suka fito wani k'aramin labule da ke sak'ale a d'akin suka nufa suka shige ba wani abu cikin banda kayan mata da turaruka ga wata drawer can ta kaya nan ta ciro mata kayan da ummah ta tanada mata lace ne dark blue tasaka sannan ta d'aura mata alkebba d'inta bak'i a sama,k'arshen kyau beauty tayi shi ita kanta dubin kanta amadubi ta hau yi,sai data gama shirya caf bayan kayan shaye-shayen data bata,kafin nan suka fito,gud'a tsofaffin gurin suka hau yi ummah dake zaune tabi 'yar tata da kallo don sosai tayi kyau tankar ba ita ba,tasan cewa tabbas yanda taso ta aurar da 'yarta hakan ya kasance, tsakiyar d'akin aunty balaraba ta zaunar da ita sannan ta samu waje itama ta zauna,nasiha da fad'a haka mutanen nan suka shiga yi mata tun tana iya jure hawayenta har suka fi k'arfinta,suna haka suka ji alamar bud'e k'ofa wanda hakan ya tabbatar musu cewa dady ne ya dawo tare da mijin aunty balaraba,kuka ne ya k'ara ciyo beauty sanincewa dady ne da kansa yace zai kai ta d'akinta,mik'ewa tayi da gudunta ta fad'a jikin ummah ta shiga rero wani sabon kukan,tsintar kansu sukai daga ita har ummah cikin kuka,can aunty taga wannan kukan nasu ba mai k'arewa bane dole ta rabo beauty da ummah tayo waje da ita,a bakin motar dady beauty ta iske zee-zee na ta kukan rabuwa da k'awar tata nan itama ta k'ara kecewa da wani kukan dady dake gaban mota zaune tuni ya fara matsar kwalla jin rurin kukar 'yar tasa,da haka tana kuka tana ihu aka sata mota suka tafi! . A tsadadden gidanta wanda a hak'ik'anin gaskiya sameer yayi k'ok'ari matuk'a wajen tsara shi dady ya kai beauty har d'akinta sai dai sam ya kasa ko kwakwkwaran magana sai kuka da suka d'unguma sunayi rarrashin duniya mijin aunty yayi amma ina sam sun k'i ji dole ya kamo hannj dady tare da rufo mata k'ofa suka fito! Sameer dake sashensa zaune shin da ameenu da jin k'ugin tashin motar su dady wani tsalle ya doka yana fad'in yes ta shigo gidana!tuni ya soma sauri yana shiryawa,wanka yayo har da d'oro alwalarsa sannan ya fito shadda brown colour ya saka ya feshe jikinsa da turare sannan ya d'ago kai yace da ameenu ya ka gani?jinjina da hannu ameenu yayi masa sannan yace gaskiya mutumin ba k'arya yau zaka koya wa 'yar jami'a hankali,wani mugun kallo sameer ya watso masa,take ameenu ya saki dariya yace sorry aboki mantawa nayi princess,mik'ewa tsaye yayi daga zaman daya ke yace to ni dai baru na wuce tunda an kawo mana ita but pls kabi ta a hankali kasan ita fa yarinya ce kar la sauke mata nauyi,wani wawan duka sameer ya buga masa a baya har yana duk'adda da baya ameenu yana dariyar mugunta yayi waje yana fad'in sai mun had'u gobe, bai amsa shi ba sameer sai ma wata nannauyar ajiyar xuciya daya sauke ya k'ara duban kansa a madubi sosai sannan ya fito ya nufi sashen beauty! . Ko da ya isa bakin k'ofa sameer turowa yayi ya shiga inda ya sameta can zaune tsakiyar gado ta had'a kai da gwiwa da alamun kuka take,sallama yayi sannan ya k'arasa ciki saman gadon ya nufi a hankali ya shiga yaye mata alkebbar daga fuskanta,d'ago fuskanta yayi cike da tausayi ga kuma wani sonta da yake fizgarsa a halin yanxu ya shiga share mata hawaye yana manna ta a jikinshi,sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya d'ago fuskarta ya sakar mata murmushi,a daddafe itama ta mayar masa sannan yace my princess yau bani da sauran magana tunda Allah ya mallaka min ke don haka tashi muje mu fara gabatar da sunnah sai mu dawo nan,ba musu ya rik'o hannunta suka tashi bayi ya shigar da ita tayo alwala sannan suka gabatar da sallah,gaban kanta ya kama kamar yadda yake yayi mata addu'a sannan ya mik'e ya fita bai jima ba sai gashi ya dawo rik'e da tray na kayan tab'a wa a baki,ba wani sosai ta ci ba haka ya d'auke kayan yana mai ce mata ki shirin bacci bara na kai kayan waje,yana fad'in haka ya fice! Tashi tayi beauty ta shiga cire kayan jikinta zuwa na barci kamar yadda aunty ta nuna mata night gown d'in da zata saka wata light pink iyakar gwiwa haka ta janyota ta saka hannu ta saka tana d'an janyo rigar k'asa amma ina tak'i sauka,beauty take taji duk kunya ta gama kamata can kuma ta tuna da wani abu da sauri ta nufi wata k'aramar jakarta dake nan ta fiddo wani k'ulli neman ruwa tayi ta rasa nan ta bud'e k'aramin fridge da ke d'akin ta janyo ta zuba a cup,k'ullin maganin da baba yagana ta bata ne ta tuna don haka ta d'akko ta kad'a a cikin ruwan ta shanye,haka kuma cikin sauri ta maida ta ajiye ta nufi gado,bargon dake linke a saman gadon ta shiga yaye shi kwanciya tayi ta rufa ruf har kanta! . Tana kwance har bacci ya d'an fara fizgarta taji alamun bud'e k'ofa shigowa sameer yayi amma ganin har ta kwanta yasa shi laluben madannin wutar ya rage hasken d'akin, kafin ya wuce can d'ayan gefen gadon ya kwanta,koda ya kwanta sunanta ya kira amma da mamaki yaji shiru,jim ya d'anyi sanin cewa ba bacci take ba yasa shi murginawa a hankali har inda yake,hannu ya kai ya sak'alo bayanta dashi take ya sauke ajiyar zuciya"jin har lokacin babu alamar zata motsa yasa ya maida hannunsa saman kanta,hular dake sanye akanta ya zame take ya hau shafar suman kanta a hankali uwa mai neman wani abu aciki! Yadda yake wasa da gashin kanta sosai take jin tsigar jikinta tayi yarr ta tashi,saurin kai hannunta tayi saman nashi tajanye,ya sameer ka bannj ni bacci zanyi,haka ta fad'a tana maganar uwa wacce ta fara bacci,k'ara matsowa sameer yayi sosai har yana iya jiyo saukar lumfashinta haka ya kara bakinsa saitin kunnenta ya fara magana yana ci gaba da shafar gashin nata,my princess bazan hanaki bacci na kinji amma yana da kyau ki min abinda zanyi marking dix night as my best night ever kinji,na son kina so na kuma zaki iya sadaukar da komai naki domin ni pls baby ki bari ko tab'a jikin ki nayi na samu relief,kin ji?em em ni ka rabu dani ya sameer bacci zanyi?beauty ta fad'a har lokacin tana k'ok'arin raba jikinta da nashi amma ta gaza hakan,can ya nisa yace ok naji but atleast tell me something pls,nan ya matso da kunensa saitin bakinta yace all ears dear?duk a takure beauty take jinta yadda ya ke shige mata se take jin duk ba dad'i haka ta rad'a masa in na fad'a zaka sake ni nayi bacci na? Da sauri ya bata amsa da yes dear had'e da ci gaba da shafan kanta! Da jin haka a hanakali beauty ta shiga juya harshenta tana fad'in: _To night i feel so happy,i feel that i have not reached any where in my lyf,i have not made my goals,my dreams,i feel that i was just born again,that i have to start over,and it makes me a little scared bcox i have never comes across such moment in my lyf till now,and i have never thought i would feel this way;you have showed me all over wit ur luv and carez thanks yuh so so much my prince!_ Wani wawan hugging sameer ya kai mata yayinda ya k'ara manne jikinta da nashi sosai yana fad'in . _My angel u must be a fantastic runner bcox now u are always running in my mind before i neva thought sameer will fall this way but now i do so for dat pls permit me 2 know more of u!_ . Yanayin da sameer ke maganar kad'ai ya wadatar ya gama kashe wa beauty jiki take ya fara aika mata wasu irin zafafan sak'onni tun tana kauda kai tana janye jikinshi daga nata har ya kai ta fara karb'a tana maida martani,take jikin sameer ya hau kyarma yamda yake jin beautu sosai tare da shi,labari ya soma canja wa laluben jikinta ta ko ina yake har ya cimma burinsa,kuka da ihu babu irin wanda beauty batai tun kana iya juyo sautin kukanta har muryar ta ya dishe dan azaba sosai sameer ya shigeta,haka daren sababbin amaren biyu ya zama cike da jin dad'i! . Bayan da sameer ya dawo daga sallar asuba ne ya shigo d'akin wanda har lokacin beauty kwance tale tana maida baccin wahala,gabanta sameer ya je ya zauna tare da yaye bargon da take rufe da shi can kuma wata zuciyar ta shiga raya masa abinda ya wakana daren jiya k'arar kukan beauty kawai yale tinowa yana dariya summ haka ya rungumota jikin nan nata gaba d'aya ya gama d'aukar zafi ya shiga fad'in thanks yuh so much my princess u make me feel morethan my expectation!k'ara matseta yayi gam jikinsa kamar wacce za'a kwace masa ya fad'a da k'arfi;wallahi alhaji beauty tayi ba kad'an ba ni da ita kuma mutu ka raba!k'ara k'are mata kallo yayi kafin yakai mata hot kiss a baki yace i luv yuh *'YAR JAMI'A* bayan nan ne kuma ya tashe ta domain sallah wanda haka rayuwarsu ta ci gaba cikin so da girmama juna! *TAMMAT BI HAMDULLAH!* - ISMAIL SANI
Saturday, 30 December 2017
Home »
'Yar Jami'a Complete
» 'Yar Jami'a Part 9 (END) Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI
https://mynovels.com.ng/jiki-na-yake-so-complete-hausa-novel/
ReplyDelete