Tuesday, 16 January 2018

NI A.Y.S NAKE SO Page 26-30

NI A.Y.S NAKE SO Page 26-30
.
WRITEN BY Princess Eshat Aysm
.
In Dedication to *ABDULLAHI YAHYA SA'AD ZARIYA*
A.Y.S
.
Ba musu ta mik'e fuska a ?aure, da gani taji haushi, sai kuma yaji ba da?i, haka ya?au keys yayi gaba.
da suka isa ko kallonshi batayi ba tawuce, kifa kanshi yayi yanajin wani iri, wunin ranar cikin kasala yayi ta, gashi yakasa zuwa ya bata amsar tambayar datasa ta fushin, tayi masa kyau sosai fiye da kullum, fuskarta yayi ta hangowa a zuciyarshi, ana idar da Sallar magriba ya koma gida yayi wanka, coffe kawai ya ha?a yasha ya koma Asibitin.
Tana cikin rera karatu Lidia tana gabanta tana sauraro ya shigo, gefen Sallayar ya zauna yana kallon Qur'anin, yana ?aya daga cikin abunda yasa take burgeshi, ko kallonshi batayi ba harta gama karanta shafin, hanu ta ?aga tana addua duk da baya ji haka yayi ta cewa Ameen.
Lidia ma Ameen ta ce sannan tajuya tana gaida dashi, ba yabo ba fallasa ya amsa, takaddan hanunshi ya mik'a mata yace "kimun typng".
kar?a tayi ta fita da hanzarinta, kai idonshi yayi kan Aisha ya ce "Ashe kema kin iya fushi ne"?
Harara ta watsa masa ta kauda kai, ya ki?eme ya ce "me kikeso yanzu"
Zun?ura baki tayi ta ce "Gida zaka kaini".
wani malalacin murmushi yayi ya ce "nifa bani na kawoki ba, idan wata uku tayi nasan Abbahn ki zaizo dubaki, tunda kin warke kinga sai kibishi basai kinyi wata shida ba".
"yanzu watana nawane"?
ya ce "watanki biyu". yamutsa fuska tayi ta ce "Allah ya kaimu".
Zata mik'e ya rik'o hanunta ya ce "ina neman alfarma, kidaina fushinnan kinsa kaina ya fara ciwo".
dara daran idanuwanta ta sauk'e akanshi ta ce "nadaina, amma nima kadaina mun haka".
murmushi yayi ya ce "nadaina".
duk da baisan me take nufi ba.
Hancinshi taja tana dariya, dariya shima yayi yace "kin ramane"?
Ka?a mishi ido tayi ta ce "kanaso na ramane"?
girgiza kai yayi yana dariya, ba k'aramin kwanciyar hankali ya samu ba, yarasa me yake damunshi game da ita, itakam jin da?inta yafi a misalta, tunda ta gane Ays ?inta ne, takejin kamar sonshi zai huda k'irjinta.
.
.
.
.
NIGER
"Unaisa badake nake magana ba, wani irin amai kikeyi kwana biyunnan, gaba ?aya kin canza, da anyi maganar asibiti kifara zun?ura baki".
Zun?ura bakin tayi ta ce "Mama nifa nakejin ciwonnan, idan naga ban warkeba ai dole na tafi asibitin".
"to ai shikenan jiki magayi".
Sallamar Kareema ce ta katsesu, da dariya tagaida Maman suka shige ?aki.
Ko zama batayi ba ta ce "ke nazo da wani zance kuma naga kin wani rame kin k'ara fari".
Unaisa ta ce "fa?an zancen naji".
"ba zama nazoyi ba rakani zakiyi wajen Malamin nan".
Kareema ta ?ata fuska tace "nifa ba inda zani, bana fa?a miki abunda yamunba, kuma haryanzu babu wani bayani".
Kareema ta sauk'e ajiyar zuciya ta ce "kinga sai mu fa?a masa, nifa yanzu gaba ?aya Yazeed ya canzamun, jiya har dukana yayi".
Unaisa ta ce "duka? Yazeed ?in? Bamuci ta zama ba".
Da sauri tashirya suka tafi, ko nisa basuyi ba ta fara kwarara amai, ba k'aramin ru?ewa kareema tayi ba, ta ce "k'awata haka kike amai dama, mu wuce asibiti kawai".
Jiki ba k'wari Unaisa ta mik'e, ba musu suka nufi asibitin, gwajin farko aka fa?a mata tana ?auke da ciki, tun a wajen ta fara rusa kuka, tanayi Kareema tana taya ta, a haka suka nufi gidan Malamin nasu.
basu samu kowa a gunba don haka suka shiga kai tsaye, yana ganinsu ya fara dariya, ganin suna kuka yasa ya tsagaita yashiga tambayarsu, sanar mishi sukayi Unaisa tanada juna 2, me makon ya ?ata rai sai ya wani washe baki, yasan cikinsa ne tunda shi ya ?are ta, kallonsu yayi ya ce "me sauk'ine ai, basai a cire ba".
Da sauri Kareema tace "yauwa a taimaka mana a cire".
Wani dariyar yayi ya ce "aljanin dare zai  cire, sannan ina miki albishir nanda sati biyu za'a ?aura aurenki da Faruq".
Wani bak'in cikine ya kamata ta ce "nidai damuwata yanzu a cire cikin, wazai aureni da cikine ma".
Jaddada mata dole sai ta kwana yayi sannan a cire, dole ta amince babu yanda ta iya.
Koda Kareema ta fa?i matsalarta wani maganin yabata, ta tafi tabar k'awarta tana godiya, daren ranar Malam yasha aiki akan Unaisa? ko ran farko batasha wahala haka, tunda yagane tanada da?i yakasa barinta, kwana yayi yana abu ?aya, washegari tanaji tana gani ya hanata tafiya, daren ranarma ta ciyu, tun tanajin abun da zafi harta yafara mata da?i, dazai kaita yayi mata wanka da ruwan magani, na toshen bakin iyayenta kada su tambayeta ina taje, ku?i ya tula mata ya ce duk abunda takeson ci taci, bayan sati cikin zai zube.
.
Wasa2 Dr Abdul yayi nisa a soyayyar Aisha duk tunaninshi ?an zaman da sukayi ne yasa suka shak'u, tana ?ebe masa kewar Raliya k'anwarsa, musamman wajen neman fa?anta, kullum cikin lissafin kwanakin da yarage mata yakeyi, babu wani hujjar dazaisa ta ci gaba da zama a wajen, tana zaune a gabanshi tanashan maganin da yabata, sai yamutsa fuska takeyi, idonshi nakanta yana murmushi k'asa2, wayarshi ne tahau ruri ya ?auka, Dr Mansur yagani, yayi dariya ya ?aga, kafin yayi magana Dr Mansur ya ce "kazo ka?aukeni mun iso".
Kashe wayar kawai yayi, mik'ewa yayi tare da fa?in "kina gama sha ki tabbatar kinci abinci".
?ata rai tayi ta ce "zanbika".
"ba nisa zanyi ba".
Kuka zata farayi ya ce "ke kuma, kuka?
taso mutafi".
Da sauri ta tashi suka tafi.
Dr Mansur yana zaune ata gefe ya hango motar Abdul, da hanzari ya mik'e ya nufi wajen, da tsananin farinciki Abdul ya fita suka rungume juna, Abdul ya ce "ina shirin bada cikiyarka kenan".
Duka Mansur ya kai mishi ya ce "na da?e da dawowa ina zaria".
Murmushi sukayi suka nufi motar, mamaki ne ya kama Mansur ganin Aisha, ya sake baki ya ce "wacece wannan yau a motarka".
Ha?e rai Abdul yayi ya ce "idon matambayi ne".
Ta?e baki yayi ya ce "kai kasani".
Dole baya yashiga yana mamaki, ?an satan kallon Mansur tayi ta mudubi tayi masa sannu da dawowa, a dak'ile ya amsa ya kauda kai, hakan ya tabbatar masa da ta warke, tunani yafara yi, wani irin abune a tsak'aninsu haka, yasan Abdul baya yadda yayi ko magana da wata a wajen balle shiga wajenda yake, Addu'a yafarayi a ranshi Allah yasa ba soyayya suka fara ba.
Bawanda yayi magana har suka isa gidan nasu, ganin sunfita yasa itama tasa k'afa zata fita, sunkuyawa yayi dai dai kunnenta ya ce "ina zakije, gidan da babu mata a ciki".
murmushi tayi kawai ta koma ta zauna, shima murmushin yayi yaja hancinta sukayi dariya, Mansur ya ta?e baki yashige da sauri, bin bayanshi yayi yana ?aga mata hanu, ajiyar zuciya ta sauk'e me k'arfi, "Allah kabani Abdul yazamto abokin rayuwata ta har abada".
ta fa?a a ranta.
.
Suna shiga Mansur ya ce "yaushe kazama haka"?
cikin ko inkula ya ce "rayuwace ta canza, zan kaita, kasameni acan, idan ka huta saimu gaisa".
Mansur yayi shek'ek'e ya ce "wai kana nufin ta warkene".
?aga mishi kai yayi ya ce "ina tunanin haka".
"shine saboda iskanci kake yawo da ita".
runtse ido yayi ya ce "nifa banson tambaya, cewa tayi zata biyo ni".
da mamaki Mansur yace "dama tasaba binka kenan"?
tsaki yayi ya ce "ko kotu naje iya tambayoyin da zasuyi kenan".
Binshi da harara Mansur yayi ya ce "mutum kamar mutum amma...
Shiru yayi ganin ya fita bai saurareshi ba.
Wani irin fa?uwar gaba yaji ganin murfin motar a bu?e kuma bata ciki, lek'a ko ina yayi babu alamarta, da sauri ya koma ciki yana k'walawa Mansur k'ira, har yafara wanka yasa riga ya fito, a ki?ime shima yashiga tambayar sa lafiya yake masa irin wannan k'ira,
"Banganta ba".
abunda ya iya fa?a kenan yana zare ido, Dr Mansur yayi tsaki ya ce "shine kabi ka futa a hankalinka".
wani kallo ya watsa masa ya ce "idan ta ?ata wa za'a kama"?
shiru yayi yanufi hanyar futa, da sauri ya bishi a baya, duba gidan suka shigayi amma babu ko alamunta, shi kanshi Mansur har wani zufa yakeyi, da sauri ya nufi Gate ?in gidan, a zaune a jikin bishiyar kwakwan dake k'ofar gidan ya hangota, wani farin mutum dogo yana  zaune kusa da ita, da gani tanajin da?in maganar tasa, fuskarta cike da murmushi tana ka?a wayarsa a hannun ta, wani malolon bak'inciki ne ya tsikari Abdul, idanuwanshi har wani canza kala sukayi lokaci guda, Mansur kam tsayawa yayi yana dariya, ya ce "tasa hankalinmu ya tashi a banza, ka?auke ta kutafi tun kafin taja mana magana".
ko kallonshi Abdul baiyi ba ya nufeta, wani irin zafi zuciyarshi takeyi, da iya k'arfinshi ya fizgo ta, wayar dake hannunta ya kar?a ya kwa?a da k'asa, cikin tsantsan isa ya ce "wani irin iskanci ne daga zuwa waje zaki jaji?o wani".
mamaki ya kamata, bawai maganar ne yabata mamaki ba, yanda ya canzane ya bata mamaki, sunkuyar dakai tayi zata fara kuka mutumin dayayi mutuwar tsaye ya k'araso, a hankali ya ce "bai kamata...
wani uban harara ya watsa masa dayasa yaja bakinsa yayi shiru, jawota yayi da k'arfi yayi cikin gidan da ita, har lokacin zuciyarshi bai daina tafasa ba, jefata cikin motar yayi yazaga zai shiga Mansur yayi saurin tareshi, cikin kunnensa yayi masa magana "nasanka da kishi akan abunda kakeso, ina umurtarka dakayi a hankali akan 'yar mutane kada kayi mata illah, tamkar amana take a wajenka, watak'ilma zurfincikin ka bai bari kafa?a mata kana sonta ba amma kake nuna irin wannan kishin, kayi a hankali".
Binshi da kallo Abdul yayi harya shige, dawo da kallonsa kan Aisha yayi lokacin har tafara kukannan nata, kauda kai yayi yashiga ya tada motar, maganar Mansur  sai yawo yake masa a kunne.
ya lumshe da ido yana kallonta ta gefen ido, zuciyarshi ce tafara fa?a mishi zafinda kaji a zuciyarka lallai shine SO, Runtse ido yayi yafara girgiza kai, wata zuciyar ta ce "tunda ka rasa ESHA bazaka sake son wata ba".
Haka yayi ta tunani, kukanta ne yadawo dashi, tsaida motar yayi ya kifa kanshi, wani sabon kukan tasake ?arkewa dashi, a hankali ya k'ira sunan ta, jin tak'i ta amsa yace "zamuyi ta zama anan har sai kinyi shiru, kukannan naki sam banason ji, kiyi hak'uri ki daina".
Kamar k'ara mata yayi, ?wani iri yakeji har cikin kanshi, hannunshi yasa ya kamo nata batareda ya ?ago ba, wani irin abune ya tsikaresu, zata janye hanun yasake matsewa, cikin kuka ta ce kasakeni ba kyau fa".
Murmushi ne ya su?uce mishi ya ce "to kidaina kukan".
Dainawa tayi tana sauk'e ajiyar zuciya, ya ce "meyasa kika zauna da wani har kina masa dariya"?
Zun?uro bakin tayi
.
Ta ce "cemun yayi Dr Abdul mutumin kirki ne shine naji da?i".
?agowa yayi yana kallonta, wani gefen ya?anji kunya meyasa ma yayi haka, ya ce "meyasa kikaji da?i"?
Kallonshi tayi kafin ta ce "haka kawai".
Kamar me ra?a yace "Zaki iya rayuwa dani Aisha"?
Waro ido tayi tana mamaki, shi kanshi baisan yayi maganarba, "na rayu dakai tayaya".
Tayi tambayar yayinda ta tsareshi da ido, suman kanshi ya baza ya ce "kiyi hak'uri, mantawa nayi".
Batace mishi komai ba ta kauda kai, "bazan ta?a nuna maka nice Aisharka ba, dole nasan zaka soni, saboda don ni akayi ka, nima saboda kai akayi ni, a duk inda numfashin mu ya ha?u sai munji alama ajikinmu".
Ita ka?ai take magana a ranta, kallonshi tashiga yi tana murmushi, murmushin nata ba k'aramin tsumashi yakeyi ba, a kasalance yaja motar suka tafi.
.
.
.
Momi tayi matuk'ar farinciki jin cewa Abbah ya ce yanemi Sadiya, ta jinjina wa Abba sosai da karamci irin nashi, ita kanta saida taja Allah ya isa mawanda yashiga tsak'aninshi da Aisha, k'warin gwiwa ta bashi akan ko bayason Sadiya ya tilastawa ranshi sonta, bazaiyiyu ya watsa musu k'asa a gwiwa ba.
Shidai harga Allah baya wani sonta, amma a hankali suka fara sabawa, tun tana ganin rashin dacewar abun har tazo tafara sonshi, dama suna sonshi tun a dama, soyayyah suka fara sosai da yasanya iyayensu samun kwanciyar hankali, tunaninsu ?aya Aisha, Ammi tana tsoron Aisha tadawo ta tadda wannan abun, saidai sun tanadi uzurin da zasu ?aurata akai.
Aure nufine na Allah, kana naka Allah yana nashi, matar mutum tabbas itace kabarinsa.
Sati biyu akasa bikin Faruq da Sadiya.
Fatan Allah yakaimu lokacin.
.
Ranar wata talata da daddare, yayi daidai da saura kwana 2 Aisha ta cika wata uku, tana kwance idonta yana lumshe kamar me bacci, wani iri takeji kamar zuciyarta tana bugawa, ba abunda yake damunta sai tunanin wani irin rayuwa zatayi idan ta rabu da AYS, taya zatayi ya gane itace Aishar sa, a hankali hawaye ya fara sauk'o mata, tasan idan har tabar garin bai ganeba ta rasashi kenan har abada, wayar Lidia ne taji yafara ruri, tsaki taja ya katse mata tunani, harya tsinke aka sake k'ira, sauk'a tayi a hankali ta isa inda Lidia take ta fara tashinta, a firgice ta tashi tana zare ido, batace mata komaiba sai nuni da ta mata da wayarta, da bacci cike a idonta ta isa wajen wayar ta ?auka, ganin sunan ne yasa ta zaro ido tana mamaki, bata daina mamaki ba har k'iran yasake katsewa, a karo na uku a ka sake k'ira, ?auka tayi tana baza hanci kamar ta wajen zataji maganar, Aisha dai ta tsura mata ido, dariya ta bata sosai ganin yadda take magagin bacci, da sauri taga Lidia ta nufo wajen ta, tana mik'a mata ta ce "oga yana magana dake".
ita kanta mamaki ya gama kamata, ganin Lidia ta koma baccinta yasa tayi ajiyan zuciya tasa wayar a kunnenta, cikin wani irin kasallaliyar muryan da bazata ta?a Mantawa dashi ba taji yana k'iran sunanta, har hawaye ta farayi, yau ta da?a yadda shine Ays ?inta, muryanda tayi rayuwa dashi na k'ank'anin lokaci, ya zauna a zuciyarta na tsawon shekaru.
"_Aisha bakijine"
Nutsuwarta ta saita ta ?oye mamakinta tace "bacci nakeyi".
murmushi yayi ya ce "ESHA nakasa bacci".
Da damuwa ta ce "meke damunka".
numfashi ya sauk'e a hankali kamar me ra?a ya ce "tunaninki".
waro ido waje tayi ta ce "kafa?amun".
shiru yayi na tsawon lokaci kafin ya ce "ina zuwa yanzu".
Zatayi magana ya kashe k'iran.
,
Tananan zaune cike da tunani kala2, ko minti 10 ba'ayi ba ya sake k'ira, "kifito kisameni a mota".
haka kawai ya fa?a ya kashe, tsura wa wayar ido tayi, ko bakomai taji da?i zata ganshi kamar sun juma da rabuwa, hijab ?inta kawai tasaka ta fice, dai2 inda yake ajiye motar ta hangoshi, cikin nutsuwarta ta k'arasa, tunda ya hangota yaji wani sabon farinciki, tabbas rayuwarshi zata zama wani iri idan ta tafi, minti tayi bata kusa dashi yakanji duniyar tayi masa zafi, shikam yana mamakin wannan al'amari.
Murfin motar ta bu?e ta shiga, idanuwa ta zuba masa tana murmushi, kafin ta ce "Ashe lafiyarka lau".
Lumshe ido yayi ya ce "haka kika gani, inaso ki nutsu sosai, duk maganar dazamuyi yanzu babu wasa aciki, inaso nasan ke wacece, sannan nafi matsuwa nasan waye FARUQ a rayuwarki, naso barin komai a cikina amma bazan iya ba, inaso zumuncinmu ya ?aure na har abada".
Taji da?in magar tasa, wannan ya nuna alamar tana cikin rayuwarsa kuma baya fata ta fita, a hankali tashiga kwararo masa labarin Aurenta da Faruq, amma ko ka?an batayi gigin sanar dashi tayi rayuwa da wani AYS ba, tadai fa?a mishi bata wani sonshi aka aura mata wani takeso, sannan tafa?a mishi irin dukan daya mata da sakin daya mata, ajiyan zuciya ya sauk'e me k'arfi, da lumsassun idanuwanshi yake kallonta sannan yace "wanene wanda kike so ?in, a ina yake".
Shiru tayi can tace "yayi mun nisa, a halin yanzu na manta dashi".
Hancinta yaja ya ce "ashe ke bazawara ce"?
Sunkuyar dakai tayi tana murmushi a ranta tanajin haushin sunan.
D'aure fuska yayi alamar babu wasa, da wani irin yanayi ya ce "?ago ki kalli cikin idona, wani irin k'warjini yayi mata, ta sunkuyar dakanta da sauri, ?ago ha?arta yayi da hannunshi ya ce "ki kalleni Aisha, inaso ki ganemun menene a ciki"?
A hankali ta kalleshi, runtse ido tayi da sauri wani abu na mata yawo a kanta, a hankali ya ce "zaki rayu dani"?
Dukda tambayar ta daki zuciyar ta, ta daure ta ce "wani irin rayuwa kuma"?
hancinta yaja ya ce "rayuwar da kika sani".
.
Kallon rashin fahimta tayi mishi, ya ce "Aisha, inasonki, inaso na rayu dake, nasan so, nasan shi nake miki, a yanzu bana gane komai sai ina tare dake, idan naganki a kusa dani kuwa, nakanji zuciyata kamar zata fashe, saboda tsan2 so, nasan masifar so tun akan ESHATA, haka nake jinki a raina, zaki rayu dani".
Tunda yafara maganar take kallonshi bako k'yaftawa, ji takeyi kamar mafarki takeyi, ganin shima ya tsura mata idone yasa ta sunkuyar da ?kanta, jan hancinta yayi yace "kallonnan naki yana tsumani".
da?a sunkuyar dakai tayi tanajin sanyi a ranta, ganin bazatayi maganaba yasa ya ce "Babu wani lokaci Aisha, kidaina tunanin komai ni nasan zan zame miki gata a rayuwarki, ni nadace dake, ina tunanin iyayenki suzo a jibi su rabani dake ban fa?a miki abunda yake raina ba, idan kin amince, idan sunzo tare dani zamu tafi ayi maganar aurenmu".
Da?ine ya ratsata jin maganarsa, fuskarta ta ?oye cikin hijabi ta ce "nifa bazawara ne".
Wani irin fa?uwar gaba yaji har cikin kanshi, bayaso ya tuna cewa wani ya ta?a ra?arta, wani kallo yayi mata dukda kanta na cikin hijabi ya ce "to menene, abunda nasani kawai shine inasonki, bazan iya rayuwa babu ke ba, ki manta da cewa kin ta?a aure, nima zan manta da haka, banaso na sakejin kin fa?a".
?aga mishi kai tayi, yayi murmushi ya ce "nagode".
Ranar dukkaninsu kwanan cikin farinciki sukayi, musamman da Abdul daya kwana yana adduar Allah yasa ta zamto alkairi a gareshi, koda yafa?awa Mansur yayi masa fatan alkairi, a ramshi ya ce "gara da banyi kato?ara ba, don farkon ganinta yaji ta kwanta masa arai, Aisha irin matannan ne da kallo ?aya namiji zai musu yaji yana sonsu saboda k'warjini bawai tsantsan kyau ba, Mamsur ya tayashi murna sosai, suka tsayarda magana akan idan iyayenta sunzo zai bisu su tafi tare.
.
Anyi Auren Faruq da Sadiya satin da yagabata, zuwa yanzu son juna sukeyi sosai, sai a lokacin Faruq yasan menene auren, a baya soyayyar Aisha ta hanashi gane menene fari menene bak'i, rayuwa sukeyi me cike da kulawa, dukkansu jefi2 sukan tuna Aisha daga baya su rarrashi juna, itakam momi kullum takan godewa Muhammad mesaje bisa karamcimsa garesu, don haka ta rik'e Sadiyar kamar 'yarta, dukda wani gefe na zuciyarta tafi k'aunar Aisha, tanason yarinyar sosai, to Sadiyar ma batada laifi, tafi Aisha sakewa da wayewa, idan tana zuba mata hira kai kace ba surkuwarta bane, hakan yana burge Faruq matuk'a, kullum sai momi tayi sadaka Allah ya baiwa Aisha Lafiya.
.Ohhh *Abunda yafi k'arfin kuka sai salati, don Allah waye ya bu?e account da sunana a fcbk???, Princess Eshat Aysm biyu ne a fcbk kuma duk nice, yanzu kuma naga sun zama uku????*
*Grup ?in da ake bu?ewa da sunana a wtsp sam baya damuna, amma wannan kam naji haushi????? don Allah wacce ta bu?e ko ya bu?e kumin magana??*
.
Momin Faruq tunda taji ranar Juma'a za'aje duba Aisha ta ce "ita zataje, da kanta taje ta samu Abbah ta ce "ita zataje, shima bai matsa sai yajeba saboda Dr daya turasu ya k'irashi ya fa?a mishi ta warke idan sunje tare zasu taho, Farinciki a wajensu baya misaltuwa, hatta k'awayenta saida Hajara ta tarosu ta fa?a musu Yau Aisha zatawo, gida kam ya cika fal tun kafin lokaci yayi nisa, dayake jirgin safe tabi zuwa 10 ta isa, address ?in da Abbah ya bata dashi tayi amfani yakaita har asibitin da Aisha take.
Tana zaune a gefen Dr Abdul yana duba wata duk yagama gajiya, dak'yar yasamu yashawo kan lamarin, lumshe ido yayi yajingina yana kallon Aisha, murmushi tayi masa tace "sannu".
Shima murmushin yayi yace "banyadda da wannan sannun ba".
?an shagwa?e fuska tayi ta ce "zanyi wanka na shirya, katashi mutafi".
"waye ya fa?a miki zaki tafi, sai kincika wata shida".
Da wasa yayi maganar itakam ta ?auka da gaskene, wani irin kuka ta fashe dashi tana bubbuga k'afa, kama baki yayi yana kallonta, can kuma yafara mata dariya, kukan tafara da iya k'arfinta, tsagaita dariyar yayi ya ce "kin kasa gane kin girma yarinyarnan, abu ka?an sai kuka".
Cuno bakin tayi ta ce "nadai ji, katashi mutafi".
a gajiye ya mik'e yanufi kusa da ita, ?an sunkuyawa yayi ya sumbaci goshin ta ya ce "har murna kikeyi zaki daina ganina ko, to bazan yadda ba tare zamu tafi".
wani irin murmushi tayi masa dayasa tsik'an jikinsa tashi, ta ce "inaso naga kowa da kowa, koda na?an lokacine, kai kuma nafiso nazauna dakai na tsawon rayuwata".
waro ido yayi yana kallon ta, yaji da?in kalamin nata, a hankali ya ce "abunda kika fa?a gaskiya"?
Cike da kunya ta ce "Eh".murmushi yayi yaja hanunta suka tafi.
.
A gaggauce tayi wanka ta shirya cikin wata dogon riga milk colour, ru?i biyune ?ayan ru?in bak'ine da wani zanen flower me kalan golden ajiki, kwalliya tayi sosai, mayafin nashi me ?an girma ta yafa, Lidia ta sake baki da hanci ta ce "yau kinfi kullum kyau, ina zuwa yau kuma"?
Murmushi tayi mata kafin ta ce "inasa ran zuwan iyayena yau, kuma tare zamu tafi".
Sosai Lidia taji babu da?i, jiki a sanyaye ta ce "inaso muyi wata magana kuwa....
Sallamar da akayi shi ya katsesu, Momi ce tashigo tare da Dr Mansur, fuskarta ?auke da Farinciki, da saurari Aisha ta fa?a jikin ta, sai kuma ta fashe da kuka, ?an buga bayanta Momi tashigayi tana rarrashinta duk da batasan dalilin kukan ba, ?an tsawon lokaci ta saketa suka zauna, tanata jira taga ta ina Ammi da Abba zasu ?ullo amma shiru, jiki a sanyaye suka gaisa da Momi ta tambaye ta ya jikin, sai binta da kallo Momi takeyi ganin ta murmure sosai tafi da cika da kyau, kamar ba jinya aka kawota ba, Dr Mansur ya ce "yau dai zaki koma gida, fitina ya k'are".
ya k'arasa yana dariya, zun?ura baki tayi batace komai ba, ita jira takeyi taga ta ina Abbah zasu shigo.
Wani gefen zuciyarta tana jiran Abdul, ?an abun ta?awa Lidia ta kawo wa Momi, ka?an taci, ta kalli Aisha taga tayi kicin kicin da fuska, saura ka?an ta fara kuka, Murmushi Momi tayi kamar tasan abunda yake ranta ta ce "matso kusa dani 'yata, ni dakaina na rok'i alfarmar a barni naje na taho da ?iyata, idan kin shirya ki taso mu wuce".
da?ine ya kamata, kaya ko kala ?aya bata ?auka ba, duk tabarwa Lidia su, jiki a sanyaye ta ce "ina Dr Abdul".
Cikin zolaya Mansur ya ce "yatafi zaria ?azu...
Bai k'arasa ba tafashe da kuka, Momi tayi shek'ek'e tana ganin ikon Allah, a ranta tace "anya ta warke kuwa".
Kuka takeyi sosai, Lidia ta jinjina kai tana dariya, ganin da gaske take kukan Mansur ya ce "Momi ko zaki barmana ita ina tunanin bata gama warkewa ba".
Murmushi Momi tayi don tagane tsokanarta yakeyi.
Sallamar sa ne yasa ta sauk'e ajiyar zuciya me k'arfi, da sauri ya k'arasa cikin ?akin, fuskarsa a ?aure yafara tambayar waya sata kuka.
Nuna mishi Mansur tayi da baki, cike da Masifa ya juya, sai asannan yaga Momi, da sauri ya tsuguna ya gaishe ta fuska a sake, tace "ina fata zamu iya tafiya da ita"?
Kallon Aishar yayi yaga itama shi take kallo, tun a lokacin kewarta ta fara kamashi, ya susa kai ya ce "bari nadubata, idan babu wata matsala sai ku tafi".
Kallon Aisha yayi da ni?imammun idanuwansa ya ce "muje".
ba musu tabi bayansa, har office ?inshi suka shiga, key yasaka yajuya yana fuskantar ta, izuwa lokacin idanuwansa sunyi jaa sosai, matsawa daf da ita yayi ya ce "Aisha, inaji kamar bazan iya bari ki tafi ba, kinga ba Abbah bane yazo bal?e nayi masa bayanin kaina, don Allah kizauna wallahi zan iya shiga wani hali idan kika barni".
Waro ido tayi ta ce "gaskiya na matsu naga iyayena, karka damu, kabimu mutafi kamar yadda muka tsara".
tsura mata ido yayi kafin ya rik'o hannunta, ya?an matsa yatsunta ya ce "idan naje bazan dawo ba sai an auramun ke".
Murmushi tayi ta sunkuyar dakai, yaja hancinta ya ce "wacece wannan ?in, jikina bai bani Ammi bace".
?ago ido tayi tana kallonshi, sannan tayi murmushi ta ce "Mahaifiyar Faruq ne".
Wani kallo yayi mata cikeda kishi ya ce "ok tazo biko ko, to bazaki bita ba...
fa?a yashiga yi sosai, itadai tana mamakin kishi irin nashi, gaba ?aya futa a burki yayi, saida yagama surutunsa sannan ta ce "ana bikon zaki uku ashe"?
susa k'asan sumanshi yayi ya ce "abu me sauk'ine ai".
dariya tayi taja hancinsa ta ce "inason wannan kishin, bawani wanda zai sake rabani da farincikina...
sai kuma tayi shiru, Ido ya lumshe yanajin inda sonta yake ratsashi, abun har tsoro yake bashi, idonshi yana ?lumshe yajawo ta da k'arfi ta fa?a jikin shi, hannuwa yasa zai rungumeta tayi saurin bige hanun ta matsa gefe, numfashi ya sauk'e a hankali ya ce "Ina sonki Esha, ha?uwata dake tayimun da?i, zan rik'eki da amana, murmushin ki shiya fara tsumani naji ina ra'ayinki...
Buga k'ofar dayaji anayi ne yasashi yin shiru, ko ba'a fa?a ba yasan waye zai masa wannan iskancin, da?a mik'ewa yayi ya kwanta idonshi na lumshe, itakam inbanda ido babu abunda ta zuba mishi, a hankali ta isa ta bu?e k'ofar, tun kafin yashiga ya fara binsu da kallo, baki Ya ta?e ya ce "wannan kuma wani salon iskancine, ni nasan babu wani abunda zaka bincika, idan zaka bata yarinya su tafi ka bata".
Ko bu?e ido baiyi ba balle yayi magana, yanaji Mansur yanata ?a?atu k'arshema yadaina sauraran me yake fa?a.
Jiki a sanyaye Aisha ta nufi k'ofa da niyyar fita, wani tsawa ya daka mata yace "ina zakije"?
Baki bu?e ta tsaya tana kallonshi, tsaki yaja ya watsawa Mansur harara sannan yajata suka fita, ta?e baki Mansur yayi ya ce "kaji dashi, mutum sam bayabin So a hankali, wataran sai kanka ya kunce".
Ko kallonshi Abdul beyi ba suka tafi.
Cewa Momi yayi akwai abunda zaifa?awa Abbah dole su tafi tare..
Sai yamma lis suka isa garin Bauchi..
Sai kunjini anjuma..
.
Kai tsaye gidan Momi suka wuce, Aisha dai taso su sauk'a a gidansu amma bayanda ta iya dole suka bi Momin, tana shiga taji gabanta yana fa?uwa, abubuwa da yawa sun canza a gidan, angyara shi kamar sabo, a falonta ta sauk'esu, rayuwar datayi na shekaru uku yazamo mata sabo, haka kawai taji tanaso taga Faruq.
Da hanzari Momi tawuce ?aki tana cewa "ina zuwa".
Dr Abdul ya sauk'e ajiyan zuciya a hankali ya ce "matso kiji".
Nok'ewa tayi ta ce "gulma ba kyau".
D'an murmushi yayi yana shafa kai ya ce "kamar kinsan kuwa shi zanmiki".
Murmushi kawai tayi don tasan fitinane kawai.
Ya sha'afa da kallonta Momi ta fito, wayarta ta ?auka tafara k'ira, ana ?auka ta ce "nadawo, amma ina tare da bak'i, a kawo musu abinci".
Dr Abdul ya mik'e yace "naga masallaci ajikin gidannan, zanje nayi Sallah".
Momi ta ce "to Dr, ka?anyi hanzari saboda mu wuce, kaga iyayenta sun fara k'ira".
Russunawa yayi kafin yafita, da kallo Aisha tabishi har ya ?ace, wani ajiyan zuciya ta sauk'e tana murmushi, ganin komai takeyi kamar a mafarki.
Momi ta zauna kusa da ita jiki a sanyaye ta ce "wannan Doctorn kamar na ta?a ganinshi nake nagani".
Aisha ta sunkuyar dakai tace "hala ko kamane".
Shiru Momi tayi kamar me tunani..
.
Basu ankara ba sukaji an shigo da gudu cike da murna, kai tasaye kan Momi ta fa?a tana "Oyoyo momina".
ita sam bata lura da wacce take zaune ba, baki sake Aisha ta mik'e cike da mamaki, da Sauri ta ce SADIYA".
Itama Sadiyar da sauri ta juyo jin muryan Aisha, tana ganinta ta sake Momi ta k'ank'ame Aisha, rungume juna sukayi suna dariya, wani gefen zuciyar Aisha ya cika da mamaki, itakam Sadiya farinciki fal ranta ta ce "Aunty munyi missn ?inki wallahi, Allah yasa kin warke muci gabada rayuwar mu, me zakici na kawo miki".
Daidai lokacin Faruq ya shigo, baki a zun?ure ya fara magana, "Mom shina da kika dawo baki k'irani ba kika k'irata ko, ni inaganin wariya a gidannan".
shi baima lura da Aisha ba, a hankali Aisha ta zame jikinta ana Sadiya, ko ba'a fa?a ba tasan Sadiya ta zama matar Faruq, mamakinta k'aruwa yayi tana tunanin taya akayi haka ta faru, duk sunsha jinin jikinsu sun dawo hankalinsu, Faruq baki bu?e yake kallon Aisha ko k!yaftawa bayayi, Abdul ne ya shigo da sallamarsa, ganinsu cirko cirko yasa yabisu da kallo, ganin kallon da Faruq yakewa Aisha yasa kishin nasa ta motsa, a zafafe yaja hanunta suka bar falon.
Ajiyan zuciya Mom ta sauk'e ta ?auko mayafinta ta ce "zamu k'arasa, saina dawo".
jikin Faruq duk yayi sanyi yakasa cewa komai, Sadiyace tafara borin zata bita tace tabari sai gobe.
bataso ba haka ta hak'ura.
.
Abdul daya jata suka fita ko nisa basuyi da falon ba ta fashe da kuka, tsayawa yayi yana kallonta, ranshi a ?ace ya ce "saboda kinga tsohon mijinki kike ?are baki, sai ki koma kiyi ta kallonshi".
hanunta ya zare ya fara tafiya ya nufi wajenda ya ajiye motarsa, zuciyar shi har k'una takeyi, baiyi tunanin komaiba yanufi motar zai shiga, da gudu ta k'arasa ta rungume shi ta baya ta saki kuka mara sauti, runtse ido yayi yana fa?in Innalillahi, duk wani tsikan jikinshi saida suka tashi, a hankali ya jiyo da ita tagabanshi yafara share mata hawayen, ganin bazasu k'areba yasa ya zuba mata ido, shi haushin gidanma yafara ji...
Momi ce ta nufosu da saurinta, yana hangota ya janye Aisha  a jikinsa ya koma gefe, ko kallonsu batayi ba tashiga sit ?in baya tana cewa muje ko".
haka suka shiga suka nufi anguwarsu Aisha kowa da abunda yake sak'awa a ranshi.
lokacin k'arfe 8 saura na dare, duk duhun daya rufe garin bai hana Abdul gane wannan anguwar ba, bugun zuciyarsa bai tsaya ba har suka isa k'ofar gidansu Aisha, da matsanancin mamaki yabita da kallo, ji yake kamar ya fito da zuciyarshi waje ko zata daina harbawa, jin tsayuwar mota yasa Abbah yafito rik'e da carbi a hannunshi, ta cikin glass Abdul yabi Abbah da kallo, da sauri ya dubi Aisha, lokacin Momi harta shige cikin gidan.
"Aisha wannan ne mahaifin naki"?
kafi ta bashi amsa Abbah ya k'araso wajen, cike da murna ya bu?e ta gefen da ya tabbatar tana wajen, itama da sauri ta rungume Abbah tana kukan Farinciki, tayi kewarsu sosai.

0 comments:

Post a Comment