Wednesday, 31 January 2018

PHERTY Part 16-20

PHERTY PART 16-20
.
A dai-dai wannan lokacin pherty na kwance tana barci tun bayan gama wayarsu da abdool ta kwanta akan ta huta kafin ta tashi tamai girkin da yake sow tasan baxai wucce minti talatin ba barci takeyi mai nauyi koda ummie aysha ta shigo ta ganta tana barcin murmushi tayi tare da cewa almira kwanan ki nawa rabonki da barcin rana. Mama ma da ta shigo tashin ta fasawa tayi dan taga da alama barci ya mata dad`i mama ce tayi girkin.
.
Cikin firgici Abba ya shigo gidan hankalinshi tashe mama naganin haka tasan ba lafiya tace abbansu meya faru yace ina pherty mama tace tana barci yace alhamdulillah sanninta ne kawaii babban tashin hankalin xuri'ar mu. Mama tace meke faruwa wacce irin magana kake yace AISHA bai tab`a kiranta da sunanta ba sai yau cikin kid`ima ta ke kallonshi yace Allah yayi ma abdallah rasuwa yanxu a hanyar shi ta dawowa gida daga abuja. Yana juyowa yaganta kwance ta suma tashin hankalI wanda ba'a samashi rana kafin yayi wani yunk`uri dady ya shigo bai lura da mama dake kwance k`asa ba yace mustapha ina phertymerh yace tana barci sai lokacin ya kula da mama dake k`asa kwance fidge ya nufa tana farfadowa suka nufi gidansu abdool. Koda suka shigo gidan sun tarar da gawar har ankawo ummie aysha da momy nata kuka kamar ransu xai fita momy tace ina pherty akace tana barci cikin kuka tace Ku gaggauta kimtsashi akaishi makwancin shi tun kafin ta tashi.
.
Dai-dai wannan lokacin ta tashi tana tashi agogo ta kallah cikin sauri tayi wanka Tasha kwalliya amman sai taji gidansu shiru kamar ba kowa a gidan aranta tace kila ma yah abdool ya shigo suna gidan cikin sauri ta gama shiryawa farar shadda ta saka tasha aiki pink ta yafa pink din gyale sai kuma taji gabanta na fad`uwa ba k`ak`autawa. Har takai k`ofa xata fita kuma bugun k`irjinta ya tsananta cikin ranta tace k`ila ma yah abdool ne ya dawo tunda duk lokacin da yayi tafiya inajin irin haka in ya dawo but na yau dai ya tsananta. Gidansu abdool ta nufa tana shiga harabar gidan bata ga mai gadi a k`ofa ba tace yau baba ko ina akayi d`aga kan da xatayi sai taga ABULACE a harabar gidan ga mutane sunata alwallah nan take taji gabanta ya sake fad`uwa. Tana kaiwa k`ofar falon taji dady nacewa indai har aka kai gawar abdool pherty bata saniba ba'ayi Mata adalci ba yaseer jeka ka taho da ita taga gawar sah ko addu'a tayi mai d`agowar da yaseer xayyi yaga pherty tsaye tana kallonsu. Fuskar nan tayi wani iri ba annuri haka ta k`arasa shigowa falon momy ta nufa tare da cewa momy ina yah abdool ya iso ina barci ko? Kasa bata amsa tayi sai kuka juyawa tayi gun ummie tace ummie da gaske ne wai abinda naji dady na fad`a da gaske yah abdool ya rasu nan ma bata samu amsa ba gun Abba ta nufa tace Abbah yah abdool ya mutu da gaske cikin dauriya da nuna jarimta Yayi Mata nuni da bayanshi tare da cewa ya rasu phertymerh ga gawarshi nan je kima masoyinki addu'a. Cikin sauri ta isa gaban gawar tana budewa sai taga kamar yana murmushi kawaii sai taga abin kamar a mafarki ta fara karanta Mashi suratul yasin tayi mai addu'o'i sosai tana gamawa, Dady yaxo ya Kama kafad`unta tare da mik`ar da ita tsaye kusa da momy ya xaunar da ita har lokacin bata gasgata yah abdool ya rasu ba kamar an tsikareta ta tashi ta nufi gawar abbah ya rik`eta ta fusge tana isa gun ta yaye likafanin tana shafa fuskarshi.
.
Tace yah abdool tashi ka fada musu mafarki nakeyi kamar daga sama taji yaseer na cewa miemie ba mafarki kike ba abdool ne ya rasu da gaske bai rufe baki ba saiga hakeem cikin kuka kamar yaro pherty na mik`ewa taji k`afarta bata daukarta sai lokacin kuka yaxo Mata mai tsuma xuciya tare da cewa, Haba yah abdool ya xakamin haka ya xa'ayi ka tafi ka barni bayan kasan baxan iya rayuwa babu kai ba kowa na falon sai da ya xubar mata da hawaye cikin sauri ta goge hawayen fuskarta tare da tashi tsaye ta gyara gyalenta tace yah abdool tashi mu tafi nasan baka mutu ba Juyawa tayi tace Ku dena kuka wallahi abdool dina bai mutu ba yanxu ne ma dai`dai lokacin dawowarshi ni wllh mijina bai mutu ba kowa na falon kuka yake abba yace ku dauke shi Ku kaishi masaukin shi cikin hargowar pherty tace wanne makwanci wllh Abba bai mutu ba dak`ar su momy suka rik`eta aka fita da gawar tana gani aka fita dashi. Cikiin kururuwa take cewa dady karku tafi dashi ban sake ganinshi ba sake rik`eta su momy sukayi wani k`arfi ne yaxo Mata ta fusge kanta daga hannunsu tafi su Abba da gudu dady ne Yayi mata kyakyawan ruk`o a kunnenta ya rad`a Mata kiyi hak`uri pherty nasan kinyi rashin masoyi ya kamata ki sakama xuciyarki dangana duk da nasan xayyi wuya hakan. Abdool bai cancanci kuka daga gareki ba addu'a xakiyi maii bai gama maganar ba yaji ta sulale k`asa a sume cikin sauri yace mama ku taimaka mana da ruwa cikin sauri suka runk`a xuba mata ruwan sanyi amman ba alamar rai a tare da ita....
.
Sai da aka xuba mata roba d`aya na ruwa sannan ta farfad`o wanda yayi dai-dai da lokacin da aka ida fita da gawar abdool daga cikin falo wani irin kuka ta saka mai tsuma xuciya wanda yasa kowa na falon kuka tare da cewa ya xakamin haka yah abdool bai dace ka tafi ka barni ba. Juyawa tayi tare da kallon momy tace momy dan Allah kice karsu tafi dashi wallahi bai mutu ba baxai iya tafiya ya barni ba momy saboda yasan numfashina tare yake tafiya da nashi cikin kunnenta momy tace ya kamata ki yarda da k`addara da irin jarabbatar da Allah ya miki ta rashin masoyi ki ringa yima abdool addu'a kuma kisani abdool ya amsa kiran ubangiji kuma xaki rayu......
.
bata k`arasa ba pherty ta saki wani ihun da ya rikita kowa tare da cewa ki dena momy bana sow. Can kuma tayi lamo tare da rufe ido kamar tana barci wanda yayi dai-dai da gama yima gawar sallah (Allahu Akbar) suna fita da gawar kamar an mitsini pherty ta xabura ta tashi xaune tare da fara surutai, Reality ya xakamin haka ka tafi ka barni? Haba yah abdool ba haka mukayi dakai ba kada kamin haka cikin kuka tace ma mutanen falon dan Allah kuce su dawo dashi wllh xai tashi. Kukane yaci k`arfinta amman duk da haka bata fasa surutun ba. Dan darajar Allah kuce su dawo dashi wane hali kake tunanin xanshi ga in na rasaka yah abdool nasan kana jina. Kalamai take wad`anda duk wanda ya ji xai san mutuwar ba k`aramin tab`a ta tayi ba dan ko iyayensu basuji mutuwar kamar yarda take jinta ba duk wanda yaji kalaman da takeyi yasan ba k`aramar kauna ke tsakaninsu ba. Cikin kuka ummie aysha tace kiyi hak`uri pherty kiyima yah abdool addu'ar samun rahama cikin masifa da kuka tace uban waye yace miki yah abdool ya mutu sai kuma ta fashe da kuka wallahi ummie mijina bai mutu ba wayyo Allah yah abdool.
.
A hankali taji an dafa kafad`arta tare da rufe mata baki tayi shiru amman a xuciyarta tana tunanin duk Wanda ya rufe mata baki bai yi mata adalci ba yarda ya hanata ambatar sunan GUDAN JININ TA danme xa'a rufe mata baki bayan ansan tayi babban rashin jigon rayuwarta. Cikin sauri ta jiyo tare da buge hannun da aka rufe Mata baki dashi juyowa tayi cikin sauri mamaki ne ya lullub`eta duk da k`arancin muhallin hakan a wannan lokaci Halimcy ce tsaye fuskarta cike da hawaye sakin baki pherty tayi sai hawaye dake xuba daga idonta cikin rawar murya take magana muyi hakuri pherty wannan babban rashi ne mukayi kiyi hak'uri Allah ya jik`an abdool. Kalma mafi d`aci kenan da pherty ta tsani a fad`a mata kawaii sai taga raunin sown da Halimcy ke abdool rasa kome xata cema halimcy tayi sai Kama hannunta da tashi ta sauke shi daga kafad`arta guri ta samu ta xauna bata sake magana ba haka hawayen idonta sun k`afe har maxan suka dawo tana xaune kan gadon abdool (da yake can aka mayar da ita) Dady ne yace ma yah yaseer yaje ya taho mashi da ita yana shiga ya sameta da wayarta a hannun tana kallon hotunan da ummie tayi masu daren da xai tafi dubai hawaye ne ke xuba a idonta amman fuskarta murmushi takeyi. Gabanta yaseer yaje ya tsaya tare da cewa meimei da sauri ta d'ago kanta suna had`a ido ta tashi da gudu ta rugume shi tare da cewa daman nace musu baka mutu ba yah abdool amman sunata yimin musu ni nasan masoyina bai mutu ba..
.
Kusa da ita ya sake matsowa sosai kallonshi ta ringa yi gaba daya ya rikid`e mata ya koma mata abdool da sauri ta karaso gabanshi. Fad`awa tayi jikinshi tayi mai kyakyawar runguma har yana jin laushin dukiyar fulanin ta na take yaji jikinshi yayi sanyi tare dajin wani irin abu ya tsarga shi cikin kuka take cewa daman nace musu baka mutu ba yah abdool hakanan akamin musu, Cikin sanyi jiki ya d`ago hab`arta tare da cewa miemie abdool fa ya rasu ya kamata ki fuskanci rayuwa hawaye ne ke xuba a idanuwan ta tana girgixa kai tace nidaii aah wllh I missed ur yah abdool cikin sauri ta sake fad`awa k`irjin shi. Wani shock yaji ya kamashi dan wannan karon kab k`irjinta ya baje a jikinshi dandanan ta rikitashi har fuskarshi ta fara sauyawa hannu yasa yayi mata wata kyakyawar rugumar da sai da ta saki wata yar k`ara. Hannunshi ta kama cikin sauri har tana sark`ewa take cewa xo muje yah abdool muje gun dady nidai a d`aura mana aure yanxu. Kallonta kawaii yake dan ta riga ta gama kashe mai jiki gaba d`aya ta rikita mar lissafi a haka ta jashi har falon dady cikin murmushin da suka dad`e basu ganta dashi ba take magana.
.
Dady munxo a daura mana aure ne wallahi ina sown shi cikin mamaki dady ke kallonta ya dad`e yana kallonta sannan ya fara kallon yaseer bai ga alamar komai a tare dashi ba sai dai reaction dinsa daya sauya wani murmushi dady ya daki tare da cewa to Alhamdulillah. Wayarshi ya dauka ya kira abbanta yayi mashi bayani tare da cewa yanxu in muka fita sallahr axahar sai a daura auren gobe yaseer din xai wucce sai ya tafi da matarshi tunda Allah ya kawo mana saukin wannan abun. 02:30 aka d`aura auren phertymerh da yaseer Allah sarki pherty matar mutum kabarin sah tana lik`e da yaseer tunda ya dawo daga d`aurin auren tana kwance kan k`irjinshi tana barci. Shikau duk lokacin da ta tab`a jikinshi wani mugun shock yakeji a jikinshi har yana tunanin Ashe haka abdool keji shiyasa kullum yake lik`e da ita Ashe haka jikinta yake matsalar d`aya ce abdool ya rigashi ga komai a gunta dandanan fuskarshi ta sauya A ranshi yace abdool ya fini sanin dad`in jikinki kenan meyasa na amince da wannan auren bayan nasan yarinyar nan saura ce sauran ma ta k`anina duk sown da nake miki dole in barki miemie. Cikin d`aga murya yake magana meke shirin faruwa dani yarinyar da nake sow kamar in mutu gata yau a matsayin matata but baxan iya rayuwa dake ba phertymerh sai dai kiyi hak`uri cikin sauri ya xameta daga jikinshi tare da fita daga d`akin. Part dinshi ya nufa ya fara had`a kayanshi cikin yan mintuna ya gama had`a kayan ko sallama baima kowa ba yayi tafiyar shi .
.
TOFA MASU KARATU MEKE SHIRIN FARUWA DA PHERTY NE ???
.
Yana fita ya d`au hanyar abuja cikin awa ukku ya isa birnin tarayya kayanshi ya had`a yaje yayi baking jirgi xuwa u.s gab da xai tashi ya kira Abba a waya tare da ce mashi wata tafiya ta kamashi yanxu xuwa u.s haka ya kira dady sukai mashi fatan sauka lafiya Ba tare da sunsa shi kadai ya tafi ba wanda mamansu pherty kawaii ta sani dan ita dashi tunanin su d`aya suna tsammanin ta ba abdool kanta. Tana kwance a inda ya barta tana ta barcinta cikin kwanciyar hankali tana mafarkin abdool d`inta. Kamar an mintsineta ta tashi tare da juyawa a iya tsawon rayuwarta bata taba shigowa part din nan ba nan ta fara tambayarta to meya kawoni nan kallon falon ta fara yi tana wani naxari ta sake juyawa, Gani takeyi kamar tasan falon tak`amemen hoton yaseer ne ya bata amsar abinda take nema da kakinshi na soja fuskar nan a d`aure kamar ba hoto xa'ai mai ba. Hakanan kawaii taga ya burgeta matsawa tayi kusa da hoton tana kaiwa kusa da gadon ta buge wani abu durk`usawa tayi da niyar d`auke ko miye abinda ta gani ne yasa ta daskarewa gun tare da tunanin meya kawota d`akin nan ma?
.
Wani photo ne tagani ita da yaseer da mutum yaga hoton xayyi tunanin tare sukayi shi hoton Yayi bala'en kyau kuma dukkansu dariya sukeyi a jikin hoton gani tayi ma dariyar batayi mar kyau ba d`auke hoton tayi tare da fitowa. Tana fitowa dady nayin parking din motarshi binta da kallon yake cike da mamaki dandanan fuskar shi ta sauya tare da cewa wato ni yaseer xai toxarta kenan in d`aura mashi aure da yarinya gudu, Sannan saboda tsabar raini ya kirani yacemin wai tafiya ta kamashi lallai yaseer..... Pherty ce ta katse mai tunanin shi tace dady sannu da xuwa tare da kamo hannun shi da d`ayan hannunta sukayi cikin gida. Babu Wanda ya sake maganar yaseer tunda Abba yaba dady hak`uri tare da cewa yayi mashi uxiri tunda da amincewar sa aka d`aura auren badan dady yaso ba yayi shiru ita kam hajiya pherty batama damu ba kawai daii tasan tana like din yaseer saboda kamannin shi da abdool. Kuma kullum yana kiranta a waya suna gaisawa wata ranar har su d`anyi firar karatunta sabo mai tsanani ne ya Shiga tsakaninsu dan har ta saba da lokacin kiranta yayi xata xo gaban wayar ta xauna. .
.
AGURGUJE BAYAN WATA UKKU
Pherty na kwance tayi lamo kamar tana barci waya takeyi inba ka kasa kunnenka kusa da bakinta ba baxaka ji abinda take cewa ba amman da gani tana cikin nishadi wanda koni bansan dalilin shi ba (amman xanje gulma) Murmushi tayi tare da cewa nidai aa yah yaseer ban girma ba fa kaga yah abdool baimin irin maganar......
.
cikin d`aga murya da tsawa yace stop it miemie ya isheki hak......kafin ya k`arasa maganar ta kashe wayar tare da dafe k`irji. A ranta tace d`an bala'en mutum wannan bala'en baxaka saukeshi a kaina ba ka rasa da wanda xakayi kishi sai mattace kuma d`an uwanka ni baxan iya jarabar nan ba sa'a kaci dan yah abdool yamin magana a mafarki da tuni na kashe auren nan. Sake kiranta yayi tana gani tak`i picking message ya turo mata taki dubawa kuma tayi delete yaji shiru ya sake kira nan ma shiru Wani dogon tsoki yaja mtswwww tare da cewa yarinyar nan na neman rainani yau ko saina koma gida banda yarda xanyi da aurenta tunda ina sownta baxan iya rabuwa da ita ba xan rayu da ita amman ba rayuwar aure ba baxan iya kusantar ta ba. Cos baxan iya rayuwar aure da wacce k`anina ya sani ba duk sown da nake mata am so sowrie miemie and i luv u so much. Cikin sauri ya had`a koma tsanshi sai katsinan dukko tudu garin d`an marna ta malamai da gid`ad`o.
.
Fitowar ta daga wanka kenan tana goge jikinta da towel bata lura da mutum ba. Tana zama gaban madubi tana sharce kai tahango mutum zaune da kakin sojoji. Zaro ido tayi arude ta bude baki zatai ihu ya balla mata harara tareda daura hanunshi akan lebenta alamun tamai shiru. Kama bakinta tayi gam jikinta na mugun rawa. Ya taso cikeda tafiyar kasaita ya tsaya a gabanta haryanajin bugawan kirjinta yace"uban wa kika share?bakiga kirana ba kikaki dauka? Ta girgiza mai kai tana hawaye takasa magana. Fisgota ya sake yi ta fad`awa jikinshi ya rugumeta sosai tare da d`ago fuskarta halshen shi ya saka ya Fara lashe hawayen da ke fuskarta har ya gangaro bakinta nan take ya fara bata hot kiss ko motsi kasa yi tayi hannunshi nata yawo tsakiyar bayanta can kuma taji yana Neman xame towel din jikinta da k`ar ta fusge bakinta cikin sark`ewar murya ta fara magana. _plx yah abdool ka dena bana sow....._ bata k`arasa ba taji ya jefata kan gado da k`arfi.
.
#admin

0 comments:

Post a Comment