Wednesday, 31 January 2018

PHERTY Part 6-10

PHERTY PART 6-10
.
ASALINSU Alhaji suleiman aliyu karad`uwa da dan uwanshi alhaji mustapha aliyu karad`uwa alhaji Suleiman ne babba iyayensu daya uwarsu d`aya ubansu d`aya ma biyi da ma biyi ne su kadai iyayensu suka haifa yan asalin garin katsina ne a wani local government karad`uwa iyayensu nan da rai amman suna garinsu wato karad`uwa Alhaji suleiman ne babba wato mahaifinsu abdool dan siyasa ne dashi gwamnati ke damawa domin kuwa shine kakakin majalisar dattawa na garin katsina wato (speaker) sab`anin dan uwansa alhaji mustapha wato mahaifinsu pherty da yake cikakken dan kasuwa yana da gidajen mai sunfi a k`irga da plaxer da kuma super market.
.
Matar alhaji suleiman daya sunanta phertymerh yaransu ukku yaseer, abdool, ummie aysha.
.
Yaseer ne babba soja ne yana aiki ah kaduna amman yafi xama england yana wani cos ne a can basu shiri da pherty kokaran duk da tana da sunan mum dinshi kuma miemie yake ce mata duk in suka hadu sai ya daketa sbd pherty surutun tsiya ne da ita ga iyayi shi kuma duk baya sown wadan nan abu buwan shiyasa baya shiri da ita duk da yafi shakuwa da ita akan ummie aysha. Abdool ko yagama digree bautar kasa yake a inda aka turashi makarantarsu pherty komai pherty keyi yana burgeshi bata tab`a b`ata mashi rai ba hasalima komi tayi ganinshi yakeyi dai-dai dan shi pherty bata laifi shi kuma mami yake ce mata Abdool na sown pherty sosai dan shi irin maxan nan ne masu sown mata ba kamar in yaga mace yar gayuce haka xalika mata na rububinshi duk inda ya shiga sai yayi budurwa sama da d`aya hakan ke sa yanmatanshi kullum cikin fada suke amma ta dalilin pherty duk ya watsar da yan matanshi sbd baya sown bacin ranta ko kadan duk ya shagwabar da ita indai yana nan bata tab`a neman abu ta rasa ko miye xai nemo mata shi kab xuri'ar su sunsan da soyayya da shakuwa mai tsanani a tsakaninsu Yana da wata budurwa mai suna halima ana cemata halimcy a uguwarsu layinsu daya sun sow juna kamar su mutu duk sown da yake mata sai dai sown da yake ma pherty ya taka nata saboda pherty ya hakura da ita ko magana baya mata itakam kullum sai ta xo gidansu hakan ne kadai ke hadashi fada da pherty Ko tafiya yayi sai tayi ciwo shima haka wannan dalilin yasa babu inda yake xuwa ya tattaro kayanshi ya dawo part din yayanta hakeem. Ummie aysha ce k`aramarsu kuma ita hakeem xai aura iyayensu na alfahari da wannan soyayyar da ta k`ulu tsakanin yaransu tana karatun ah jami'ar ummaru musa yar'adua dake cikin garin katsina tana karantar biology education ajinta biyu.
.
Shima alhaji mustapha matar shi d`aya sunanta maryam yaranshi biyu abdulhakeem da pherty hakeem ne babba sai pherty Hakeem ya gama karatun shi yana aiki EFCC abuja bai cika xama katsina ba sai in yana hutu Alhaji mustapha naji da pherty sosai bai had`ata da kowa ba haka ita ma dan ko shawara batayi da mamanta ko Ummie aysha daga abbanta sai yah abdool ita kuma mamansu tafi shiri da yaseer da ummie aysha saboda miskilancin su shiyasa idan tana ma pherty abu kamar bata sownta abbanta ke fada Hakeem kam daman dan gidan momy ne shiya ba ruwansa da abubuwan nan nasu.
,
Yau cikin nishad`i pherty ta tashi da sauri take shirinta na xuwa makaranta kuma tana sown ganin abdool dan ta hucce da fushin da ake dashi na kwana biyu doguwar riga ta saka (gown)pink ce da ratsin blue-green ansha powder da pink din jambaki ta shafa kwalli sai tayi wani irin kyau abinka da farar fata gyalen rigar tayi rawling dashi. (da yake qawar tawa akwai sown wannan shigar shiyasa take girmamata duk ranar da xatayi shigar cikin farin ciki take.) Fitowa tayi daga dakinta kitchen ta nufa tea ta hada tana fitowa taci karo da mama aikau tea din ya xube mata a jiki tana dagowa ta kalli mama sai hawaye sharrr hararar ta mama tayi tare da cewa kinmin b`arna kuma kina tsaye kina kallo na halan baki iya gaisuwa ba takaici ne yasa pherty kuka tare da cewa Yanxu mamah saboda Allah kinsan haw many hours na b`ata gun kwalliyar nan wllh nasan baxan sake mai kyanta ba buge mata baki taji anki aiko ta fasa ihu mama tace rufemin baki tun kafin in fasa miki wannan fitsararren bakin naki marar kunyar banxa dan danan ta hadiye kukan tare da wucewa dakinta Har ta fara shawarar cire kayan ta sake sai kuma aka fasa toilet ta nufa ta sakama rigar ruwa tare da fitowa hand bag dinta ta dauka da wayarta tayo waje tako tarar da mutumin nata har ya fito yasha farar shadda da black din hula sai kamshi ke tashi aranta tace ( annabi ma yace
mafi kyawun sutura fari ).
.
.Bata san lokacin da ta saki wani irin murmushi ta saki wanda yasa kyanta ya bayyana abdool ma murmushi yayi dan yasan ta sauko kuma yasan tana bala'in sown shigar da yayi bai lura da rigarta a jik`e take ba sai da taxo gab dashi yace Mami meya jik`e miki kaya tace fitsari nayi murmushi yayi har hakoran shi suka fito tare da kad`a kaii yace to muje kinsan lecture safe xan muku 9to10 kuma mun makara k`in bude motar tayi ta shiga har sai da yafito ya bude mata tare da cewa HUKUMA murmushi tayi tare da cewa kaine ka sabamin shiyasa bana sown xuwa uguwa in baka kusa saboda bude mota kada kai yayi saida ya shiga sannan yace In ban kusa ba tace sai na fasa xuwa uguwar sai ka dawo. Yace in na mutu fa dandanan ta hade rai ta bata fuska har suka isa makaranta bata kalleshi ba koda yayi parking inda ya saba sai ga Halimcy tsaye agun da alama xuwanta kenan ta hango su ta fito daga motar ta. Kwata-kwata pherty bata ganta ba shikam ya hango ta da sauri ya kalli pherty yaga batama kula da ita wata siririyar ajiyar xuciya yayi. Pherty tana fitowa sukayi ido hud`u da halimcy ta dauke kanta xata wucce gefen halimcy ta rik`e mata gefen riga tana juyowa ta wanka mata mari ji kake tassss.
.
Wani kallon raini tayi mata tare da fusge rigarta tayi gaba abinya nan ta barshi tsaye da ita wani kallo yayima halimcy kallonshi tayi kamar xatayi mgn kuma sai ta fasa ta shiga motarta tafi bin motar da harara yayi tare dayin tsoki mtsww. Ko da pherty ta shiga hall ta iske ya cika mak`il da mutane tana shiga suka xubo mata ido kowa ya natsu dan sunsan mr.abdool bai da M kuma sunsan tare suke shigowa da pherty wannan dalilin ne yasa kowa yayi shiru sai kuma sukaga bai shigo ba harta xauna sannan ya shigo hall din. Yana gama musu lecture din ya shiga hangen inda xai ganta can tsakiya ya hangota da wayarta a hannunta da alama game takeyi baisan lokacin da ya saki murmushi ba wanda sai da duk yammatan dake hall din suka k`yasa dan wani irin kyanshi ya bayyana hade da kwarjini ya daga murya tare da cewa Mami kin d`agowa tayi duk da tasan da ita yake ya sake cewa mami tukun ta d`ago idanuwanta cikin yanga da bacin raii dtashi anunta har sunyi jaa sbd tsabar kishi.
.
( in banda abin qawata miye na bacin rai tunda har ta kaii mari). Yace xo yana gama fadar haka ya fita kab idanuwa suka dawo kanta ana jiran aga tashinta (kunsan dan makaranta) ganin duk ido na kanta yasa ta tashi bata tafi gun nashi ba tayi tafiyarta gida abinda duk da yace xai yi musu test hakan bai hanata tafiya gida ba. Shiru-shiru bata xo ba ya aiko wani dan ajinsu ya kirata yace mashi ta fito tun d`axu yace yah Allah! Mami kin cika matsala guy din da ya aika na tsaye yace rabu da ita kawaii malam cikin xafin rai da tsawa abdool yace get out!!! Cikin sauri ko ya fita. Tana fita daga makarantar ba ta wahala ba gun neman abin hawa ba sai gida koda ta shiga uguwarsu napep na ajiyeta ta hango motar halimcy a kofar gidansu halimcyn nan tasa mai napep ya ajiyeta dan gidansu abdool xata shiga saboda tasa in tashiga gidansu mama korota xatayi. Har takai kofar shiga gidansu abdool taji an fisgota harta kusa faduwa juyowar da xatayi sai taga halimcy tsaye tana ta huci wani tsoro ya dirar mata amman duk da haka sai da tayi ta maxa ta sake wanka mata mari har biyu tana sauke hannunta motar abdool nayi parking a gun cikin bacin raii ya fito daga motar tare da cewa da kyau pherty ta shige cikin gida abinta.
.
Cikin bacin rai halimcy ta dubi abdool tana kana gani Karo na biyu wannan marar kunyar yarinyar ta mare ni ina raga matane saboda kaii d`axu bakayi magana ba yanxu kuma kace da kyau saboda ni ba yar uwarka bace ba ko wani irin kallon raini yayi mata tare da cewa Ta fiki hankali me shiyasa ta hukunta ki ta hanyar marin tunda ke baki da xuciya kinkai kasuwa kare ya lashe akan namiji kiyita fada kan layi saboda rashin kamun kai kamar dabba yarinyar nan ko damuwa dake bata yi ba magana bata taba hadaki da ita ba sai yanxu xakiyita nemanta da fada kema kinsan kab xuri'ar karad`uwa bata dauki raini ga kowa ba bare ke kayan banxa nace ban sown ki dole ne ?. Wani murmushi tayi mai kama da dariya tare da cewa haka kuma gidan mu bamu tab`a neman abu muka rasa ba dan haka yarda kace kana sow nah da farko ka koyamin sownka dole ka aureni baka da mata wacce ta wucce ni kaii wallahi in kaga ban aureka ba mutuwa nayi kona mutu kaida aure sai a lahira. Kallon banxa ya bita dashi tare da jan dogon tsoki mtsww gida ya shige ya barta gun tsaye.
.
Pherty na daga kwance kunya kamar ta kasheta dan bata tab`a jin kunya irin ta yau ba k`asa tayi da kanta. Momy tace d`ago kanki takwara aii tsakani na dake ba sarakunta xo ki rakani uguwar cikin sark`ewar murya tace momy yah yaseer nan fa kuma duka na xayyi murmushi momy tayi tace yo aikunyi abin dukan but muna tare baxai miki komai ba ko mutuwa na kunyar idon mahaifi bare shi taso muje sumi-sumi ta fito tana lab`e bayan momy har suka kai harabar gidan. Hankalinta bai tashi ba sai da taga momy ta bud`e bayan motar yaseer ta shiga tare da cewa shiga gaba dan-danan idanuwanta suka kawo ruwa bakin ta na rawa xatayi magana taji maganar abdool yana cewa momy nima ina xuwa.
.
Tace ina xan tafi dakai k`ato dakai in kaika ina ? Yace momy gashinan xaki tafi da sweet berrynah. Tace ohh ni yau na shigesu abdool kwata-kwata inda kunya ta biyo baka bi ba yanxu ina surukar ka amman kaita xuba min ruwan rashin kunya tun ba'ayi auren ba kenan inaga anyi to baxan je da kai ba kuma yaseer xai kaimu. Abdool yace momy to gaskiya kije ke d`aya indai baxaki je dani ba to precious ma baxata ba. Momy mamaki ya hanata magana nadan lokaci. Tace aiko baka isa ba ashe iya shegen naka har yakai bansaniba juyawa tayi tana kallon pherty tare da cewa shigo muje pherty tayi k`asa dakai can kuma ta d`ago tare da cewa Reality in bita yace no precious ta d`ago tace momy yah abdool yace kar na biki but sowrie mum karkice sai naje dole wllh baxan iya tafiya ba tare da yarda reality ba. Takaici ne da mamaki ya kusa kashe Momy dan mutuwar xaune tayi kallonsu kawaii takeyi ta rasa abin cewa har suka juya suka nufi motar abdool yana rike da gefen kafad`arta suna isa ya bude Mata tashi ga kafin ya xagaya ya bude momy tace Abdool Ku fara shirin aure nan da wata d`aya dan wannan iskancin da rashin kunyar ba'a gidan nan ba murmushi abdool yayi tare da takowa har inda momy take.
.
Yace momy dan Allah ya koma 3weeks kinga dai-dai dana gama service har nama fara aiki kinga salary na nafarko na precious ne tunda dai ku xakuyi mana auren nan Tace nagama magana 4weeks ko ka shirya ko baka shirya ba murmushi yayi yace thanks sweet mother in-law. Abun ya dena ba momy mamaki yanxu tsoro yake bata yarda tasan abdool da kunya amman yanxu ya xabure anya wannan soyayyar ta lafiya ce. Ita keta maganarta cikin xuciyar ta. Dady na dawowa ko momy tayi mai akan su abdool yace toke uwar amarya in kin shirya kika sani ko iyayen yaron sun shirya tace sun shirya yace bari dai in kira mustaphan. Koda ya kirashi yaxo yayi mai bayani yace ba komai Allah ya kaimu lokacin shirye muke ko yau ma akace xa'ayi mun shirya.

0 comments:

Post a Comment