Tuesday, 13 March 2018
Home »
'YAR KWALLIYA 1-END
» 'YAR KWALLIYA Page 36-40 (The end) ISMAIL SANI
'YAR KWALLIYA Page 36-40 (The end) ISMAIL SANI
'YAR KWALLIYAP Page 36-40 (The end)
,
Aqeel yace hakane mun Bude yaki buduwa shine zamu duba dakin nan ko tana ciki Hajiya tace me kuke boyewa ne kwata kwata maganar Ku ba gaskiya kundawo a gajiye kuje Ku kwanta Ku huta kuzo Ku wuce ina kallon Ku Arif yace mommy Karka ce komai kuje Ku kwanta anjima na nan
.
Haka suka tafi badan sun soba Abu da binta na jin duk abinda ya faru dariya sukayi Hajiya ta shiga daki Binta tace ko bamu muku komai ba Wannan ma ya isheku damuwa damu zuwa inda muke yanzu kuka fara Suka Sa dariya suka tafa Koda suka shiga kasa bacci sukayi suka dawo falo suna kallo bawai dan suna gane waba Amal ta shiga dakinsu Abu da Binta hannunta daukeda kaya "aikinku ze fara daga yau suna falo kuje Binta tace to muna zuwa Abu tace Wannan fa Tace sawa zakuyi Ta ajiye musu ta fita Riga da wandone sunyi kyau sosai Abu da Binta kowa ya dauki nashi yasa kayan ya hau da jikin su dan kayan sun yi kokarin nuna dirin jikin su gashinsu parking dinshi sukayi da ribom kalar wandon jikin su Abu ta musu simple make up suka fito suna ta fiya kamar bazasu taka kasaba wayo yinsu rike a hannu suka zauna a kujera me kallon su Arif da Aqeel Cak suka Tsaya suna binsu da kallo Aqeel ya kalli Arif Arif yayi gyaran murya "dama muna son magana daku sai Gashi kun fito munji dadin hakan dakyar ya iya karasa maganar tare da kauda idonsa a kan Binta da ya rasa wana irin kallo yake mata Aqeel tuni ya rasa inda zesa kanshi dayayi niyar yin magana sai yarasa abinda zece nunfashin shi na dauke wa Arif harya fishi karfin hali Binta ta wa tsawa Arif wani kallo "muba dan Ku muka fitoba munfinto yin kallo kubari sai wani lokaci Aqeel yace ya...
..
Cak maganar ta tsaya Yakasa kara sawa ya shiga buka kafa Abu tace dan Allah kayi a hankali karka fasa gurin kaga harya fara rawa Ya dauka da gaske take yadauke kafar shi yana kallon gurin Arif yace kumanta da komai mun yarda munyi kuskure saidai yanzu zamu gyara daman cewa mukayi Binta tace dan Allah kayi shiru maganar ka nasamin ciwan kai kuma ma kai kadaine zakai ta magana shi nunar rana baya magane kokuma sabon rainin wayone hakan Aqeel yace ba... haka bane ni in... Abu ta tashi ta rike hannun Binta " kabari randa ka iya magana saika fadi abinda zaka fada Suka barfalon cikin tafiyar daya gigita kowan nan su hatta Arif dayake daurewa yake magana yanzu kam yakasa dan shikadai yaga abinda ya gani Aqeel kwanciya yayi kan kujera kamar mara lafiya ,
,
Suna shiga suka ga Amal suka tafa sukai dariya Amal tace ina zuwa tayi waje gurin su Arif Ta zauna taga ba wanda ya kulata "yaya sannun Ku da hutawa Ido suka Bude suka kalle ta suka dauke kai Tace Yaya a kwai wani temako dazan iya yi muku Aqeel yabu de ido baki na rawa " temako mezaki iya yi mukan mu mun kasa saike kice musu me fadi ina jinki Yaya kenan karka raina kwakwalwata zanyi abinda baka zataba nice nake tare dasu zan iya Aqeel ya daga mata hannu "jeki Amal dan Allah kinbi kin cikamu da surutu da Wannan surutu daba gurin su kika je kika gyara muba Arif yace zaki iya Amal nasani sosai kece kadai kika rage mana kice musu su saura remu koda baza suce komai ba Kinji To shi kenan nayarda zan musu magana amma saboda kai yaya Arif inda saboda yaya Aqeel ne ba abinda zance musu Arif yace yauwa qanwata tashi kije Tace Ehhto zantafi bazan tafi ba yaya Arif Usman ya dameni akan ya turo iya yansa maganar aure gannin ba kwa nan yasa bance komai ba amma Ku ya kuka gani Arif yayi dariya " Usman mutum ne nagari kuma duk macen da ta aure shi tayi Sa a kekanki kin sani Amal indai kina sanshi ba matsala kina gama makaran ta sai ayi bikin Ku kinga kina she karrar karshe Arif yace ke kina sanshi Amal ta sunkuyar dakai Aqeel yace dan Allah Arif kalli ita da kanta ta taso da zance daga tam bayanta tayi shiru Arif yace jeki Amal na gane Allah ya sanya alkyairi Aqeel yace ya zakace ta tafi batace komai ba fa Arif yace duk da bata ce komai ba yana yinta ya nuna tana sanshi ka kula da haka Bankula da komai ba sai matata Ni tamayi aure ta tafi mu huta kila idan ta tafi su saura remu nida kaina zance Usman ya turo kuma bazan bari a sa lokaci me tsawo ba Bari daddy ya dawo nizan fara mishi magana Kiran sallar maga riba sukaji suka tashi sukayi Alwala suka je masallaci a masallaci suka zauna har a kayi isha'i tukun na suka dawo gida Abincin dare ma kasa ci sukayi zuciyar su cikeda tina nin Binta da Abu Washe gari da Sa fe Abu Binta da Amal suka shirya ma yan gida abin karyawa basu jira fito war suba suka ci nasu suka tafi dakin Amal suna kallon ankon su da bata karada dinka waba Amal taci gaba da dinka musu ankon bikin kawarsu da zasu je a yau tin kafin ta gama din Kawa suka da meta da tayi sauri suna zaune a dakin harta gama kowa ya dauki nashi yana kalla Abu tace duk nawa yafi naku kyau dame musawa Amal tace babu me musawa idan yaya Aqeel yace yayi kyau magana ta kare Binta tace fada mata Amal tace harda kema ai yaya Arif na nan zegani jiya sukace na Baku hakuri Ku Tsaya kuji a binda zasu fada muku nimadai gaskiya Ku Tsaya kuji wata kila maganar Nada mahimmanci Sukayi shiru Abu tace kin san me harna kagu naga munsa Kayan nan zamu bada kala Sosai ma kuwa yan gurin hankalinsu ze dawo kanmu mu kuma zamu dinga daga kai da yau ki cewar Binta Amal tayi dariya tace "au Allah abinda za kuyi kenan idan munje karku manta dai Ku matan aure ne Abu da binta sukayi dariya a tare sukace "mun fiki sani tinda igiyoyin na kanmu bari muje dakin mu muna zuwa Amal tace to Suka fita tabi su da kallo Karfe 4 nayi suka shirya tsaf cikin material Ja sunyi kyau sosai suka fito falo suna kanshi tirare Arif Aqeel da Hajiya na zaune a falo tinda suka fito Suka dauke hankalin Aqeel da Arif duk wani motsin da Abu da Binta zasuyi akan idon su Abu da Binta suka gaida hajiya ta amma Har kun fito ina ita Amal din Abu tace tana ciki yanzu zata fito ta gama shir yawa Hajiya tace bari naje gurin ta Hajiya ta tafi ta barsu a falo Aqeel yace ina zaku baku sanar da muba yanzufa ba kamar da bane kuna karkashin mu duk inda zaku sai da sanin mu idan mun amince kuje shikenan idan bamu aminceba kuma Ku hakura Arif yace fada musu nasaki baki ina kallon ikon Allah Baku tam baye muba zaku fita da izinin wa zaku fita Abu da Binta suka kalle su basu ce komai ba Arif yace kuyi magana da izinin wa Binta tace dan Allah bana son haya niya surutunka ze samin ciwon kai mun fadawa mommy shi kenan Aqeel yace mommy ce take auren Ku da zaku tam bayeta ina zaku jema tukun na Abu tace bikin kawar mu sannan kuma ba a gidan Ku muke ba balle kuce dole sai mun gaya muku a gidan mu muke Arif yace tanan kuka fito to shikenan zamusa a gobe kutare sai muga idan kun tare kai tsaye zaku dinga fita Binta tace tab babu inda zamu je muna nan Anan zamu zauna dakuke cewa mu tare qazamai kucakai damu zaku tare a gidan Ku a'a ajinmu bekai nan ba Aqeel yace injiwa kunkai har kunyi yawa zamu yiwa mommy maganar tarewar dan Allah kuma Ku goyi bayan haka kunji Abu tace waaa mu ba abinda zamuce kuda kuka baro zancen kusan yanda zakuyi yama za ayi kucakai masu warin mushe Susa baki a maganar Ku Arif yace dan Allah Ku mance da Wannan maganar tsautsayine da subutar harshe yanzu kun wuce haka sai dai a jera Ku da manyan mata masu ji da Kansu Binta tace kinajin dadin baki irin nasu ko maganar da kake fada bekai zuciyar kaba kafada ne kawai dan ka ganmu kuma maganar ka bazeyi aiki a kan muba Aqeel yace ba maganar dadin baki Anan kufus kan cemu kuskure mun Riga munyi kumance da baya yanzu a kar ka shinmu kuke be dace muna fada kuna fada ba kunsan da haka tinda har sauka kunyi Abu tace ko to shikenan kunga tafiyar mu idan ta fito kuce mata ta samemu a can dan kun bata mana rai bazamu jirata ba Aqeel yace karku sake Ku fita bada izinin muba Abu da Binta Suka kalle su Arif yace bamu Baku izinin fita ba da ga yau Anan zamu fara gwada muku ikon mu a kanku Ganin da gaske suke yasa Abu da Binta Suka kalle su suka koma ciki rai a bace dakin Amal suka je suka samu hajiya na dakin Suka zauna rai a hade Arif da Aqeel Suka biyo bayan su dakin Suka shi ga rai a hade hajiya ta bisu da kallo daya bayan daya Me kuka musu naga ransu a bace Aqeel yace mommy kiji wani kwado fita zasuyi bada izinin muba mukace da izinin wa zasu fita sukace da izinin ki Shine muka ce musu ke kike auren su mune nan maza jansu na aure ko sunki ko kunso ba a canzawa tuwo suna bazamu taba rabuwa da kuba mutu karaba ko dan Wannan bazaku sassauta mana ba dan Allah Ku duba halin da kuke shirin jefamu mana Amal kince mubar komai a hannun ki me kikayi a kai nayi zaton zanga sauyi Ashe wani sabon salon zasu fito dashi da ana tsaga zuciya damun tsaga kodan kuga gaskiya qaunar da muke muku Arif yace irin qaunar da muke muku bamu taba nunawa wata mace ba dan'uwana yayi gaskiya Ku duba fusko kinmu shikadai ya isa ya gamsar daku Hajiya shiru tayi tana jin ikon Allah a gaban ta suke furta Kalmar so da qauna Kalaman nasu na faran tawa Abu da Binta rai "ko banza qauyawa kucakai sun kai matsayinda sonmu yake wa halar da Ku a zuciya gaskiya mun ciri tuta Abu ta fada a zuciyar ta Abin kamar A film maza irinsu Arif ne suke qaunar mu mutanen da su kaje guri daban daban amma yanzu sun zabe mu sun kuma yi na am da zabin iya yansu gaskiya a jin-jina mana Binta ta fada a zuciyar ta Dakin yayi shiru kamar ba mutane Amal tayi matukar jin tau sayin yayyun nata cikin muryar kuka" Abu Binta lokaci na kurewa fa idan bamu jeba bazata ji dadi ba Abu da Binta ko mutsi basu yiba Hajiya rasa abin cewa tayi kallon su kawai takeyi Arif yace da Alama Baku yarda ba ko to shikenan kuje sekun dawo duk abinda ya Sa memu kune sila Jikin su Binta yayi sanyi
,
Hajiya taja dogon numfashi "Aqeel Arif kum manta cewa ina gurin ne Mommy Kiyi ha kuri gaskiyar zuciyar mu muke fada musu kila suyarda idan sunji cewar Hajiya tace kuyi hakuri yanzu kubar su suje gurin bikin babbar qawar suce ita baza taji dadi ba idan basu jeba ina rokan alfarma a barsu To mommy suje amma karsu dade saboda maza nasan baza su rasa maza a gurin ba koda yake suzo mu kaisu cewar Arif Hajiya taci gaba da cewa Aqeel Arif zan yiwa su Abu magana zasu gyara insha Allah Arif yayi wani irin murmushi "To bakomai Ku taho mu tafi Abu Binta Amal Arif da Aqeel suka fito jiki a sanya ye suka shiga mota Arif ne yake tuka mota Binta a kusa dashi baya kuma Aqeel da Abu sai kuma Amal da take gefen su suna tafiya suna satar kallon juna har suka karasa ba wanda yake cewa komai suka fito harda su Aqeel suka je gurin Amarya taji dadin ganin su ta musu sauka ta mu samman Sukayi hotuna Abu tace mata zasu tafi suka dauki kautar da Suka zo mata dashi suka bata Amarya taji dadin kyautar ta musu godiya suka shiga mota suka dawo gida suna dawo wa hajiya tayi kiran Abu da Binta tayi musu nasiha hakan ya kara kashemusu musu jiki haka suka lallaba Suka shiga daki nasihar da hajiya ta musu na dawo musu Suna shiga ana kiran sallah sukayi sallah Suka kwanta wayo yinsu ya shiga kara ko da suka ga number ne ba suna suka ki dagawa saida number ta damesu da kira tukunna suka daga sallama akayi cikin nutsuwa tareda kiran sunan kowan nen su hakan yasa suka kara gyara zama Binta cikin mamaki tace dawa nake magana Shiru yayi bece komai ba jin shirun yasa zata katse kiran yasa yace Ni ne mosoyinki Wa kenan dan sunada yawa Sarai ta gane me magana Mijinki Arif nakira ne na Kafin ya karasa "ya wuce karka damu mune zamu baku hakuri A'a Fatima mune muka jawo duk abinda ya faru da bamu furta irin kalaman da muka furta a kan kuba nasan daba za Ku mana haka ba kuyi hakuri hakan baze sake mai-maita kan shiba insha Allah Dan Allah karka sake bamu hakuri mune ya dace mu baku hakuri baza mu sake fada kuna fadaba a matsayin mu na matan koba komai ya wuce zaku Sa memu yanda kuke so Naji dadin jin haka yanzu yaushe kuke ganin ya dace Ku tare Abu na gani a gefe daya tana waya harda dariya Aqeel sarkin zuciya yana ta tsara Abu Aqeel yace zainab yaushe kuke ganin ya dace Ku tare Abu da binta suka kalli juna Kamar sunsan abinda aka fada mata shi aka fadawa Binta Abu tace zamu fara waec da neko sai dai inmun gama tu kunna Aqeel yace a'a zainab baza a yi haka ba kutare ba komai idan kuna gidan namu zamu barku Ku je Ku zana jara bawar Ku ba komai Abu tayi dariya "na sani shiyasa nace Ku bari mu gama zanawa a gidan mu .mukanmu zamufi jin dadin haka
,
Aqeel yayi shiru "to badan munso ba dan dai kawai hakan ze faran ta muku shiyasa Abu tace godiya Muke haka suka shafe a wanni suna hirar masoya kafin suka yi sallama da juna Suka kashe wayo yinsu suka kwanta bacci Washe gari Usman ya sake kiran su Arif akan maganar Amal aqeel yace mishi karya damu Alhaji na kan hanyar dawowa idan ya dawo zasu sanar dashi Usman yaji dadin jin haka sosai gurin hajiya suka je suka sanar da ita tayi farin ciki da jin hakan bayan Alhaji ya dawo ya huta Aqeel da Arif Suka sanar dashi Alhaji Nasir ya yaba da hankalin Usman ya kuma san mahaifin Usman shiyasa yayi saurin amincewa da su turo ayi maganar aure suna sanar da Usman Yaji dadin jin haka dan haka ya turo iya yan Sa aka saka ranar aure wata1 Alhaji nasir yace baya son lokaci me tsawo Hajiya na zaune a falo tareda su Abu Binta da Amal suna hira Aqeel da Arif suka zo suka zauna Aqeel yace mommy me kuka fara yine akan maganar auren Amal dawani abinda zamu taya Ku Hajiya dariya tayi tace munyi komai ranar kawai muke jira Da kuma fatan Allah ya kaimu da rai da lpy Atare suka ce Ameen Arif yace dama mun yanke shawarar kaisu su zabo abinda sukeso ne mommy shine mukazo muji ko kina da sako A'a ni banida sako idan matan kune gasu nan Ku dauke su Ku tafi yanda kuke Sosa keyar nan nasan abinda ya rage ku tam baya kenan Arif yace A'a mommy da bamuyi niyar tafiya da suba tinda kince suje shi kenan Ku taso ba komai Hajiya tayi dariya "to shi kenan kuje Ku kadai su kuma Ku bar su Anan tinda badasu kukayi niyar tafiya ba Aqeel ya za bura " mommy kinriga kin Sa musu rai ki barsu muje kawai idan kika hanasu baza suji dadi bafa Amal Abu da Binta dariya sukeyi jin ga abinda suke so sai suce hajiya ce tace haka Arif yace Ku taso mu tafi Abu da Binta kamar jira suke suka mike Aqeel da Arif na ganin su suka mance da hajiya da Amal suka koma wa matan su suna tafe suna musu magana cikin rada suka yi hanyar fita ganin basu da niyar juyowa suyi wa Amal magana Hajiya tace Amal din ta fita kenan Aqeel a kun yace "kinga yarin yar nan ko mommy kina kallo ita na fara yiwa magana da magana nata da wan nan zaman da tayi yaci ace ta kai waje amma dube ta ki gani Arif yace gaya mata wan nan san jikin naki ba inda ze kaiki gwanda ma ki dena gidan wani zaki yanzu idan kinje gidan Usman abinda zakiyi kenan Amal baki ta saki tana kallon ikon Allah yanda suke shirin Dora mata laifi tana ji tana gani Amal tace yaya dan Allah kun manta dani abinda zakuce kenan hasa Lima bada ni kuka yi niyar fitaba shiyasa suna tashi kuka tafi Aqeel ya dawo kusa da ita ya zauna "Amal taso mu tafi zaki iya tafiya kona Goya ki abinda kike so mu muki kenan kadai ba karamar yarin ya bace da zamu dinga yi miki magana cikin rarrashi idan zaki ki taho idan baza kiba gaba ta kaimu Arif yace baza taba tace taho mu tafi tana bata mana lokaci Injiwa yanda ba kwaso naje kamar naje na gama kome za ayi ko a siya nima a siya min Arif yace kinga Usman Anan ne da zakice haka ba abinda zamu siyar miki idan kin bimu yarin ya kinje a banza Bakomai nayi gaba Ku biyoni a baya Amal ta bisu badan sun so ba haka Aqeel da Arif sukaita hade mata rai ko a kanta ita da Kansu suka gaji suka koma yanda suke Kaya suka siya musu bana wasa ba daga Abu Binta har Amal suka biya ta gidan cin abinci sukaci Aqeel da Arif sun zagaya dasu guri da ban daban dasu hakan ya kara saka sha kuwa tsaka ninsu da matan su suka fahimci junan su sosai hakan yasa Amal ta dena jin kewar rabuwa dasu sai dare suka koma gida har dakin su Aqeel da Arif suka rakasu suma suka wuce nasu dakin bayan sunyi sallah suka Ciro littattafan su suna karan tawa saura kwana 5 su fara waec Bayan sun karan ta suka kwanta bacci saida safe suka Ciro kayan da maza jensu suka siya musu suna dubawa Kayan nan sunyi kyau ko Binta Sosai ma wai yau lpy kuwa Amal bata shigo ba ko duk baccin ne Zo muje suna zuwa suka samu kofar dakin a Bude suka shiga kan gadon suka dira Amal a tsorace ta Bude ido Abu da Binta suka Sa dariya suna ce mata matsora ciya Cikin muryar bacci tace ba batun tsoro Anan koku nayiwa haka saikun tsorata ina nan lokacinda kuka zo dokan Ku su yaya sukayi a kafa kuka ce barayi barayi Amal Allah ya Baku hakiri gidan Ku muka zo Au abin yar Tina baya ne to ai shi kenan kije gaban yayyunki ki fadi haka Abu na gama fada tasa dariya daga ita har Binta Binta tace dafa munyi hauka wauta iya san ranmu kunyi hakuri damu Amal tace ni kanhin tiraren nan nafi so dama kunga biki ya maso yakamata kufara tanadin tirare na musam man danni da mutane tirare da ze fasa taro yasa a to she hanci Suka kara fashewa da dariya Abu tace wai na gode Allah na da na dena Wannan haukan koyan zu ya zanyi idan kanhin na Jikina Amal tana dariya "gaskiya zan g aya miki inda kina shiga suna to she hanci yanzu kam daki zasu miki su kulle ki saida mu Tsaya daga waje mu gaisa harda ke Binta Bakomai tinda za kuzo mu gyai Sa meye a ciki kanhi rahamane ga Almiski a bakin mu Tana gama fada suka Sa dariya Amal tace dan Allah Ku barni haka kar cikina yayi ciyo kuzo muje muci abincin nasan kuma Baku Ciba Yasin kuwa kamar kinsani ke muke jira mutafi Amal tace Yasin din nan baze fita daga bakin Ku bako Binta tace bama fada sai in munason Tina baya To shikenan mu tafi Suna tafe suna hira har suka karasa dining Suka ci abinci saiga Asibi da kande Asibi tace Amal zamu fita bazamu dade ba zamu dawo ko zaku temaka kukula da girkin dana Dora Abu da Binta kai a kasa Amal tace Eh zamuyi sai kun dawo Mun gode Amal tace bakomai Suna tafiya Binta tace ni gaba dayama kunyar su nake ji wlh Abu tace ke koni manya damu saboda qazantar mu su suka fara mana Wanka daga nan muka fara sabawa Amal dariya takeyi "to meye a ciki kila masu sun manta da zancen kune dai Baku mantaba Binta ta girgiza kai "ya zakice sun manta bayan muna tare saidai matan nan akwai karfi wlh wani riko da suka mana haryau mun kasa mantawa Aqeel ne yakatse musu hirar su da cewa mommy gaskiya abinda ake mana a gidan nan be da ceba Hajiya mariya fito warta kenan taji abinda yace saida ta samu guri ta zauna "da aka yi me fa Suma zama sukayi Arif yace mommy ya dace da auren mu da komai amma haryanzu muna tare daku kamata yayi ace muma muna gidan mu ko Hajiya cikin jin kunyar maganar "Arif ban gane inda ka dosa ba fa ka fahim tar dani Aqeel yayi gyaran murya "mommy kamata yayi wan nan abincin da muke ci Anan a gidan mu ake dafawa gaskiya ana hukun tamu da yawa Sarai hajiya ta gane abinda suke nufi saita shashantar da maganar da cewa Amal Abu Binta horan yunwa kuke musu shiyasa naga suna rama amma a sanina ana dafa abinci kowa na samu garin yaya haka tafaru Mommy bafa haka muke nufi ba fa muna nufin yakamata matan mu su tare a gidan mu horon ya isa haka Ko to gaku gasu Mommy ba haka ba fa munaso ki amince su tare yau Hajiya tace yaushe kuka zama marasa kunya ne Aqeel Arif yanzu dan bakuda kunya ni kuke fadawa haka to kunjawa kanku bazasu tareba duk abinku Aqeel a mairaice "mommy karkice haka mana ba dadi fa shikenan zamu zama masu biyayya a gareki duk sanda kuka ce keda daddy su tare dai dai ne Arif yace amma gaskiya zamu horu da yawa kafin su tare wai ace ka gama da wata matsalar sai wata ta kunno kai Aqeel yace taho mu tafi suka bar gurin rai a hade Abu da Binta kunyar ce ta rufesu Suka kasa cewa komai ahankali suka tashi Suka tafi Hajiya na kallon su ita dariya ma suka bata Akwana a tashi yau ya kama Abu da Binta zasu zana jara bawa waec da sassafe suka shirya a dining suka samu hajiya suka gaidata ta amsa sukaci abinci Aqeel da Arif suka kaisu makaranta haka sukai tayi har suka gama zanawa wa gaba daya suna jiran saka mako *An daura Auren* Amal da Usman ansha biki bana wasa ba Amal taga gata sosai Amal gidan da zata zauna na Abuja tayi nisa da gida Abu Binta Aqeel da Arif saida suka kaita har Abuja sannan suka dawo Washe gari kafin Amal ta fafi tayiwa Abu da Binta nasiha sosai wanda ya kashe musu jiki Aqeel da Arif baki har geya dan sunsan matan su zasu tare koda suka dawo yan biki basu gama watse waba hajiya tayiwa Abu da Binta nasiha itama yamma nayi tasa wasu daga cikin yan bikin su kaisu gidan maza jansu tin kafin su dawo daga Abuja hajiya mariya tasa aka gyara musu gida jen su da zasu tare babban gidane me part 2 gidan yaci Ado da kayan Alatu kowan nansu aka kaishi ban garen sa sannan suka koma
.
gida yayiwa hajiya girma sosai ban garen Ango Aqeel da ango Arif kuma baki yaki rufuwa suna ganin akai musu matan su suka baro gidan Hajiya rantsatsen gurin gasa kaza suka je kowan nen su ya siyowa matar sa suna dawo wa gida kowa ya wuci gurin matar sa Aqeel da Arif sun kasa boye inrin farin cikin da suke yi sallama sukayi sannan suka shiga dakin Abu ta amsa cikin miryar kuka Aqeel ya zauna a gefen Gado "zainab meye na kuka kuma keda zaki godewa Allah daya nuna mana Wannan ranar da ranmu da lafiyar mu Ba kuka nake yiba kukan farin cikine gaskiya zamuyi kewar Amal sosai Aqeel ya matso kusa da ita ya janyota jikin shi "idan kinyi kewar ta baga niba ni zan debe miki kewa Abu ta dago jajayan ida nunta da suka cikuka suka gaji Aqeel ya kashe mata ido da sauri ta sun kuyar da Kai Murmushi yayi " da alma cewa kunyata kike ji bakomai dai je Kiyi alwala kizo muyi sallah jiki a salube Abu ta shiga bandaki Bangaren Binta da Arif ma haka Binta ta fito bayan tayi Alwala Sukayi sallah raka'a2 sukayi Addu'oi Arif ya dauko kazar daya siyo mata da lemu ka ya ajiye a gaban ta binta kura jiki ba kwari ta kalla ta dauke kai Arif yace Amarya bakya laifi nakine na siyo miki Eh kici iya cinki Nakoshi hasalima bazan iya cin komai ba Saboda me Saboda na koshi Ba a gidana ba ki daure kici Kinji Ganin bazata Ciba yasa shida kanshi yake bata abaki saida ya tabbatar ta koshi sannan Yabar ta Da suka gama sukayi shirin wanciya ina ganin lbr ya fara sauya wa dagudu na fito har tintibe sanda nayi 樂 wai yau Kazamai ne a jikin Aqeel da Arif harda蘿 Amare da Angwaye ASIBA TA GARI Garin Allah na waye Aqeel da Arif kamar su hadiye mata nasu suko sai shagwaba suke zuba musu Hajiya tayi kokari wajan gyara yaran nata sunsha gyara da jiki shiya Aqeel da Arif Suka Hauka ce akan matan nasu Haka suka cigaba da rayuwa cikin soda qaunar juna Harsu Abu suka samu ciki suka haihu Abu yan2 dika maza Binta yan2 mace da namiji An yi suna an kuma nunawa yaran gata sosai Inda yaran Abu suka ci suna kamar haka Samir Salim Inda na Binta suke amsa Maheer Macan kuma taci sunan hajiya Mariya Abu da Binta sunyi karatu me zirfi da suka gama suka nemi aiki DARAUDAU suka je suka Bude makaranta da Asibiti da masallatai suka Bude kun giyar tallafawa yara mata DARAUDAU na Alfahari dasu mahaifiyar Binta tayi aure bayan bikin Binta Koda suka dawo gida kano Abu ta Bude gurin da za a dinga yiwa Amare KWALLIYA da kawayan su ta zuba ma aikata Binta ta Bude gidan abinci kamar yanda ta fada Amal ta hafi danta na miji wanda yaci sunan Alhaji Nasir Yaya Nura yayi aure ya zama babban ma ai kaci matarsa ta Haifa masa yan2 mata ya maida sunan qannen nasa 2 Zainab Fatima
.
*Alhamdulillah* GODIYA GA DUK WANI MASOYIN NOVEL din *'YAR KWALLIYA* bansan wana irin godiya zan muku ba kunmin komai na gode kucigaba da bani goyan baya ta yanda zan ci gaba da suburbudo muku novel din da ze dinga saku ni shadi Allah YABAR QAUNA - ISMAIL SANI
0 comments:
Post a Comment