.
Khadi kulum tana cikin k’unci, Gwaggo ta sata a gaba, baran in taga, Malam ya fita kasuwa. Gashi Dr Umar ya kwana biyu bai zoba, d’inki ma, tabar zuwa sabida bala’in Gwaggo, wai sai Malam ya saka su duka, don su Beeba su samu suma mai saya musu kaya. Malam ko yace”bata isa ba, tayi k’ad’an ta gindaya mishi sharad’i yabi. Tunda tun farko, Khadi ne tafara cewa tana so, dan haka ba zaisasu ba. Zaban tayar musu da hankali yasa Khadi ta samu Malam tace” Baba bana jin dad’i zan d’an huta da zuwa aiki, kafin wata sati, Tukun ya hak’ura. Dr Umar ko, bai da tunani da yawuce na Khadijat, so ya kemata, wanda shi kanshi, bazai iya auna shi, a mizani ba. Masu karatu zamu so musan, WAYE DR UMAR? Umar Adam Naira, shine cikaken sunansa, d’a, d’aya tilo girin Adam Naira. Adam naira haifafen d’an Kano ne, nan yayi karatunsa, har ya girma, ya Auri maransa Maryama, sun dade da aure, Allah bai basu haihuwa ba, sai daga baya Allah ya azurta su da haihuwan Umar, wanda yaci sunan Baban Mum d’insa, bayan shekaru da yawa, ta haifi Ilham, wacce itace auta, a yamzu haka.
.
Alhaji Adam Naira yarike muk’amai, na gwamnati da dama. Wanda yanzu haka shine gwamnan Kano State mai ci. Ya kasance mutum ne mai kwatanta gaskiya da adalci, hakan yasa al’uman garin Kano ta Dabo suke sonsa. Tunda Umar ya taso, shi bamai son yawan, hayaniya bane, sannan bai kula yan’mata,sai wata yarinya, Sakina da ta makalemasa, sam bata cikin tsarinsa, don bata da kamun kai, yar’gidan, matai makin governor ne, gata da rashin kunya, shiyasa basa shiri. Yanzuma saukin da yasamu, ya dawo yasamu sun fita waje, ita da Mum d’inta. Iyayensa burinsu shine, yayi aure amma baya kula yan’mata. Tun randa ya had’u da Khadi, tunda yasanar da Mum d’insa, da murna ta, tasanar da His Excellency. Yayi farinciki ba kad’an ba. Yace” yana dawowa zasu samu iyayen yarinyan, ayi magana a sanya rana.wanna shine labarin Umar a takaice. Dr Umar zaune yau, sai tunanin Khadijat, da ya damesa.
.
Key mutarsa ya d’auka, yana fitowa securitys, suka fara gaidasa, da gudu suka bud’e masa, k’ofar motan yashiga, gida ya nufa yayi wanka, dun zuwa gun Khadi. Yayi kyau sosai, ya shiga mota shi kad’ai batare da security’s ba, ya nufi gidan. Khadi ko tunda ta tashi, tashi tana son yin wanka, kayan da Dr Umar ya kawo mata. ta d’auko wani less, mai kyau purple da duwatsu farare a jiki. Tayi kwaliya sosai, ta kuma yi kyau. Kasancewan yanayi gari, da sanyi, gun sai yayi, bada yanayi mai kayatarwa. Gwaggo ta shiga makwabta, sai zuba take musu. Yaro ne yashigo”wai ana salama, da Khadijat inji Umar. Tace”kace ina zuwa. Yana fita ta d’auko hijab d’inta fari tasa, bakaramin kyau tayi ba. Cikin nutsuwa ta fito, tunda Umar ya hangota, zuciyar sa sai harbawa, ido ya k’ura mata. Gwaggo da tafito daga, gidan su abula, ganin Umar acikin k’atuwar mota, nan zuciyarta ya fara tafarfasa. Yau mai zanyi ma Khadi na huce?. Wata zuciya tace”kawai ki d’auko wuka ki burma mata. Mtss a’a za’a kamani, can shaidan ya tuna mata, kawai ki shek’a mata ruwan sanyi, tunda bata so. Da sauri ta koma gidan Abula, tace”dan Allah samin ruwan a fridge d’inki.
.
Sam Abula bata kawo komai ba, ta iba mata, a karami roban plastic. Da sauri tayi gida, ta k’ara dana randa, kamar wata mahauk’aciya ta fito. Dr Umar ya shagala, da kalon Khadi, itako tana wasa, da yan’yatsun hannuta. Sai jin shaaa… sukayi, take idon Khadi ya kafe, numfashinta ya d’auke, ta tafi luuuuu zata fad’i kasa. Da sauri Dr Umar ya fito, yana kiran sunanta, tareta yayi ta fad’i a hannusa yana jijigata, amma sam bata ko motsi. Malam sun isa Asibiti, direct office d’in Dr Abdul sukaje, Don tambayansa, ko nan aka kawo Khadija, don shi har yanzu, bai san a ina, Dr Umar yake aiki ba. Duk da yasan dai, shi likita ne, suna zuwa suka tarar da Dr Abdul a office, cikin yanayi damuwa Malam”ya gaidashi, ya tambayes ya aiki?. Alhamdulilah!, Malam yace”Dr dan Allah, ko nan asibitin, aka kawo Khadi?.
,
Dr Abdul ya amsa masa da eh!. Barin rakaku d’akin da take. Sai da sukayi tafiya mai d’an nisa kad’an, kafin suka shiga, wani Ward mai kyau, kana shiga, falo zakagani babba, sai gurin da likitoci ke zama, gefe kum d’akin hutun likitoci ne. Sai d’akuna da suke jere, gwanin birgewa, gurin tsab da shi, kamar ba’a cikin asibiti ba. Kowani d’aki gado d’ayane a ciki, sai yar loka da ke gefe, Malam suka tura, qofar d’akin da sallamansu. Dr Umar ne zaune ya zabga tagumin gaban Khadi, sam bai masan sun shigoba, suka sake mai-maita sallama, amma shiru, Dr Abdul ne ya isa gunsa da sauri ya dafasa, yace”my friend, cikin razana ya d’ago, sai a lokacin yaga Malam, duk kunya ta rufesa. Mik’ewa yayi da sauri, yana musu, sannu da zuwa. Kalo d’aya Malam yayi ma Khadi, yaji wani mugun tausayinta, ya kamasa, tambayan kamsa yayi anya bayi da laifi, shima acikin cutar da Khadi, da Gwaggo takeyi?
.
. Idonsa ne ya ciko da kwala, bakin gadon yaje, ya rike hannuta, cikin muryan damuwa, Yace”Khadijatu kiyafr min, duk nine silan saki, cikin wannan damuwar. Tabbas Hauwa watarana sai tayi nadama, mai d’umbin yawa, Allah ya miki Albarka, ya Allah kajikan Adamu. Duk wanda suke gurin saida jikinsu yayi sanyi, Beeba kam kuka takeyi sosai. Malam ya juya ya kali, Dr Umar yace”Umaru na rasa, da wani irin, kalma zan gode maka. Tabbas ka taimaki Khadijatu iya taimako, Allah ya bamu, abunda zamu saka maka dashi.Allah ya maku Albarka Cikin zuciyan Dr Umar yace”abida zaumin kad’ai kubani Khadijat, don zuciyata, takamu da azaban sonta. Gwaggo da ke gida, sai fatan take, “Allah yasa adawo, da gawan Khadi. Na tsani ganinta, kamar mayya, komai zakamata bata zuciya. Mtsss ina da daga nan, tashiga uwa duniya, in huta da fitinaniyan, yarinyannan. Ko da taji Beebah tabi Malam, sun tafi asibiti, bakaramin haushi tajiba. Tunanin kalan, rashin mutuncin da zan masu.
.
Kwanan su Khadi, biyu a Asibiti, Dr Umar shi ke d’awainiya da su. Kulum yana hanyan Asibiti, yana tashi daga aiki bayan ya duba Khadi, shagon waya ya zarce, yasaya mata, iPhone 7, wayar ta had’u. Gida yanufa, yana zuwa, yayi wanka, ya fito dining, Iham ce tazo tazauna a gefensa, tana masa surutu, can idonta ya kyalo waya maroon, tace”bros wannan fa?. Tare da kai hannuta ta d’auka, “bros wayan tayi kyau, bai kaleta ba Yace”na Khadiyat ne, ihu tasa tare da cewa”wooow wayan tayi kyau. Barin samata number, nan harda WhatsApp, ta bud’e mata. Sai da yagama tukun ya amshi wayan yafita. - ISMAIL SANI
0 comments:
Post a Comment