Monday, 5 March 2018

TANA RAINA Page 11-15

WASUNKU SUNA TAMBAYA KO NICE MAMAN SHUREIM DATA RASU WATO (ZARA'U BABA YAKASAI ALLAH YA JIK'ANTA DA RAHAMA AMEEN) TO GASKYA DAI NI BANKAI MATSAYINTABA DANNI BA BARUBUCIYA BACE KAWAI DAI ABIN YANA BAN SHA'AWA NE SHINE NACE BARI DAI IN GWADA, CIKIN IKON ALLAH WANNAN SHINE LITTAFINA NA UKU, NAGODE DA SOYAYYARKU.
   Love you all
33-34 Sabreen ta shiga gun kaka yana ta karatun Qur'ani mai girma, bayan ya idar ne ya juyo yana kallon sabreen data shafa addu'an a fiskanta tace ameeen kakana, kaka yace naji mai gadi yana cewa sannu da dawowa kardai har SHULE d'in ya dawowo, dariya sosai sabreen tayi sannan tace kaka ba shule ake cewaba SUHAIL sunansa, kaka yayi dariya yace to ai sunan nasane da wahala gara dai shi kamal d'in nasan sunan, amma shi shule kam bamma tab'a jiba se agunsu. kai kaka kaban dariya wlh EH yadawo, kaka yace dakike dariyannan se kikayi kama da mahaifinki sosai, hawayene atake ya cikowa sabreen a idanunta ta fara magana Allah sarki ABBA NAH Allah ya jikanku da rahama ameeen, kaka naso ace ina tare da iyayena inga soyayyar da ABBA zai nunamin amma kai da mammi ne kawai na samu naku itama yau babu ita a duniya har abada bazan tab'a mantawa dakuba "KUNA RAINA" kaka ma kwallaya yake sharewa a fiskarsa, ganin hakanne yasa sabreen ta tashi ta fita tana ta kuka harta shigo palon ko sallama babu ta wuce d'akinta yayinda su mum suke binta da kallo. Kamal yace hafsat jeki kiji meya sami sabreen take kuka, hafsat ta mik'e ta wuce lokacin sabreen ta kifu a gado tanata kuka babu irin tambayan da hafsat batayiwa sabreen ba, amma ko kallon hafsat batayiba bare tace mata wani abu. Hafsat ta dawo palo tace batacemin komaiba tanata kukanta, suhail yace hafsat jeki kirata, bayan hafsat ta gaya mata ne seta fito, sabreen ta dena kukan amma hawayene cike a fiskarta taja gyalen kayanta ya rufe mata ido taje ta zauna a kan kapet. Mum tace sabreen meya faru kike kuka, cikin wani irin murya mai cike da tausayi tace bakoma hajiya, wani iri kamal yakeji a ransa kamar yaje ya rungumeta. Sallamar kakane ya katsesu, bayan sun amsane kamal da suhail suka mik'e suka karsa gunsa dama basu gaisaba, wata yarinyace kakkyawa biye da kaka, bayan sun gaisane itama yarinyar ta gaishesu se kamal yace kaka meya samu sabreen ne? Kaka yace ta tuna da iyayentane shiyasata kuka. Suhail yace Allah sarki nayi tunanin hakan kuwa, kamal ya kalli yarinyar da take sanye da doguwar riga jah da gyalensa yace wannan fa kaka? Kaka ya kalleta yace dasu kawar sabreen ce tazo guntane, kamal yace ok shiga tana ciki, a nitse ta wucesu kamal yace sabreen kinyi bak'uwa, sabreen ta d'ago da kanta don ganin bak'uwan nata樂 wazata gani wannan MACENNE ta karaso tare dayin sallama taje ta zauna kusa da sabreen sannan ta gaida mum cikin girmamawa ta gaida hafsat sannan ta juyo tana kallon sabreen da mamaki ya cikata tare da d'an tsoro kad'an. MACEN tana murmushi tare da tab'a hannun sabreen tace kaka yacemin kinata kuka tare da d'aga mata girama'ana su shiga d'aki, sabreen tad'anyi murmushin karfin hali tare da wayancewa tace muje ciki toh, mik'ewa sukayi a tare suka wuce d'akin sabreen, shidai kamal idonsa nakan sabreen har suka shige ciki yayinda kaka yake lura da irin kallon da kamal yake yiwa sabreen...
                 Sad-Nas
[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
35-36 Bayan su sabreen sun shiga d'akine MACEEN tasa key ta rufe, da sauri sabreen ta juyo tace meyasa kika rufe kofan? MACEN tace karki damu sabreen bazan cutar dakeba nazone dan inyi magana dake. Bayan sun zaunane macen ta rik'e hannayen sabreen dukka biyu ta fara magana suna kallon junansu.
  Sunana SALMA kuma ni kad'ai ne agun iyayena, tun kafin a haifeki mahaifinki ya rasu ata dalilin cetona.
Wata rana nida iyayena muna zaune a cikin jeji suna koyamin harbi da kwari da baka, ina zaune daga nesa su kuwa iyayena suna tsaye agu d'aya mahaifina ya saita kwari da baka a daidai inda nake zaune akan zai gwada kona iya kwaucewa kamar yadda yake koyar dani, nima jira nake ya harbo in nuna masa kwarewata na kaucewa. Kawai sega wani bafulatani yana wucewa se idonsa yakai gun iyayena kuma yaga suna da niyan harbinane, bafulataninnan ya kalli lokacin ina zaune bazan wuce shekaru 7 ba, dai dai lokacin da mahaifina ya harba kwarinne se wannan bafulatani yayi sauri tare dayin tsalle danya tareni, amma se wannan kwarin ya sameshi a daidai setin zuciyarsa, nan take ya fad'i. Iyayena dani dukkanmu mukazo kansa lokacin jini nata zuba sosai daga jikinsa, hannuna ya kamo yana magana da kyar yana cewa haba bayin Allah wannan yarinyar kuma metamuku da zaku kasheta dan Allah ku kyaleta sannan ya juya yana kallona yace yarinya tashi ki gudu kinji ki gudu zasu kasheki, mahaifina ya share kwallan fiskarsa yace bawan Allah ba kasheta zamuyiba, hasalima 'yarmuce wannan na cikinmu gwaji kawai muke mata akan koyar da ita danayi, gashi abisa rashin sani na cutar dakai gurin kokarinka na ceton 'yata, dan Allah ka yafemin bawan Allah ba'a son rainabane. Bafulatanin yayi murmushi yace bakomai na fahimta, haka Allah ya tsaramin nikuma, ta wannan hanyar zan koma ga mahaliccina, nayafe maka har cikin zuciyata, sedai ina neman taimakonku, mahaifina yace taimakon me kenan? Bafulatanin yace matata tana gida d'auke da tsohon ciki ita da surukina suna can gida a wannan kauyen da yake gaba danan, inaso ku taimaka ku k'arasa dani gidana dan baajin zan iya karasawa da kaina dan yadda nakeji ayanzu. Dukda cewa mahaifina ya cire kifiyar daya soki bafulatanin, amma sam jini bai dena zubaba gashi daga gani yana shan azaba, haka mahaifina ya d'aukeshi mukaje har kauyenku, nan mutane suka taru a kanshi agun mai unguwa. Matarsa da surukinsa aka kira sukazo tana ganinsa ta fara kuka sosai, mai anguwa yace meya sameshi haka? Har mahaifina ya bud'e baki zaiyi gaya musu abinda ya faru, kawai se bafulatanin ya fara magana da k'yar yana cewa ina cikin tfy ne se nayi tuntub'e da wani abu, kafin in ankara se naji na fad'i akan wani abu mai kaifi kuma mai tsini, ban iya tashiba se naji mutane na zuwa, shine nace su taimakamin su kawoni kauyenmu, bafulatanin ya nuna mahaifina yace wannan shine wanda ya ciremin kifiyar data sokeni kuma ya kawoni gida. Hawayene sosai a fiskar iyayena dajin lbrn da bafulataninnan ya fad'awa yan kaiyensu. Matarsa da surukinsa suka fara kuka gashi asibiti se cikin garin, mahaifina ya d'aukesa yace muje asibiti, nan aka tashi da wuri domin zuwa asibiti, se mata mai cikinnan ta rike hannunsa tanata kuka tana cewa maigida karka tafi ka barni tun bakaga abinda zan haifa manaba, banaso abin cikina ya zama maraya dan Allah karka barmu. Bafulatanin ya rik'e hannun matarsa yana kokarin magana amma se mukaji yana salati tare da cikawa. Kuka sosai matarsa takeyi da kuma jama'an dake gurin musamman iyayena dani, matarsa kuka takeyi tare da rungume gawan mijinta kowa ya tausaya mata, da kyar mahaifinta ya janyeta ya kaita gidan makota inda nida mahaifiyata mukabi bayanta, bayan mahaifinta yakaitane seya koma gunsu mahaifina akayi mishi wanka tare da suturceshi akai masa sallah se gidansa na gaskya. Salma ta tsaya da lbrnta anan tana kallon sabreen da idanunta yayi jah dan kuka datakeyi SALMA ta dad'a matse hannayenta acikin na sabreen tana kwalla itama tace sabreen bakowa bane wannan bafulatanin illa MAHAIFINKI dan Allah ki gafarcemu nida iyayena.  idanu sabreen ta bud'e tare da tsananta kukanta sosai ta hankad'e Salma tare da mikewa tabud'e kofa ta fita a guje segun kakanta yana baiwa flawer ruwa, tunkafin ta karasa gunsa ya juyo ya tareta dan yasan komai. Sabreen tana kuka tana cewa kaka itacefa sanadiyan rasuwan mahaifina wannan ita da iyayenta sune sila kaka. Salma ta k'araso gunsu tana cewa sabreen kakanki yasan komai ke kad'aice baki saniba dama, sabreen da take kallon salma seta juya tana kallon kaka tace kaka wai kasan komai??
         Sad-Nas
[10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
      By Mmn Shureim
             (Sad-Nas)
37-38 Kaka yace eh nasan komai sabreen, mamminkine tace karna gaya miki ita zata gaya miki da kanta shiyasa nayi shuru. Sabreen tace to kaka amma dukda kasan hakan shine kabarta tazo guna akan me zatazo guna bayan ita da iyayentane nasadiyar kasancewata marainiya, juyawa tayi afusa ta sake hankad'a salma tana cewa kibar gidannan banason ganinki kuma bana buk'atan jin sauran bayaninki kawai ki fita a gidannan karki sake zuwa inda muke adalilinki mahaifina ya sadaukar da ransa, salma ma kuka takeyi tace kiyi hakuri sabreen ki saurareni, sabreen tace bana buk'atan jin komai kawai ki fita nace, salma tace haba sabreen nasan dama hakan zai faru amma dan Allah kiyi hakuri ki yafe mana hakan shiyasa nad'au alk'awarin taimakonki kota wani hanyane dan ki yafe mana, sabreen shiyasa na saudaukar da budurcina dan in taimakeki a hannun wannan MUTANE UKUN a tunanina hakan zaisa ki yafemin sabreen dan Allah. Murmushin takaici sabreen tayi tace kina nufin zan yafe mikine, to ai shi mahaifina RANSA ya baki saboda da haka ban yafeba kuma kibar gidannan salma. Shi kaka dayake yasan wacece salma da sauri yaje ya janyo sabreen yana cewa haba sabreen kefa musulmace bai kamata ki dinga fad'an hakanba mahaifinki kwanansane ya kare koda hakan bai faruba to a wannan ranan zai mutu. Da sauri sabreen ta cewa kaka da bazai mutuba kaka ka dena bin bayanta nidai ban yafeba salma kibar gidannan, kaka yace salma yi hakuri kije karki damu zata yafe muku dama bakuyi komaiba jeki kinji mun gode sosai banaso 'yan gidan su dawo suji me muke ciki. Kuka sosai salma takeyi sannan ta tafi tana fita daga wajen gate d'insu seta b'ace.
   Kuka sosai sabreen takeyi kaka yana ta rarrashinta tana cewa wayyo Abbana wayyo mammaina Allah ya jik'anku da rahama. Kuka tayi mai isarta sannan tayi shuru ta wuce d'akinta tanata tunanin abin a ranta, toilet ta shiga ta wanke fiskanta sannan ta fito zataje kichin ta d'aura abinci dare, wayartace ta fara kara ta duba taga yah kamal ne, ta dauka tare da cewa hello, kamal yace hello sabreen ina fata dai kin dena kukan yanzu? Murmushin karfin hali tayi tace EH nadena, yace to shikenan mun fitane dukkanmu hardasu mum amma zuwa anju kafin magrib zamu dawo kinji, to yah kamal sekun dawo nagode, yace sabreen kawar naki ta tafine? Eh tafi, ko to shikenan semun dawo, toh sannan ta katse wayar.
  Itadai bats ganewa yah kamal ba alamu dai ya Nuna sonta yakeyi, kuma gaskya yah kamal mutum ne nagari Wanda ko wace mace zatayi fatan samu a rayuwarta. Yana da kyawawan halaiya ga nutsuwa da Sanin darajan mutane, bugu da k'ari kyakkyawane shi sosai Dan yafi SUHAIL kyau gaskya, kawai dai shi SUHAIL farine tas kamar balarabe, shi kuwa kamal bak'ine sannan yana da saje mai kyau Wanda shi suhail Sam bayi da saje se gashin kai mai laushi. Kunsan kuma farin mutum da d'auke ido da kuma d'aukan hankalin 'yan mata gashi sun iya dressing sosai da iya d'aukan kamshi kuma suhail yafi kamal tsayi sannan suhail baida yawan dariya kamar kamal, wannan shine bambancinsu. Sabreen tanata tunani a zuciyarta tana had'a abinci har ta gama tuwo miyan kuka yaji DRY FISH. 6:20pm su mum suka dawo gida lokacin sabreen tana kwance a d'akinta, mikewa tayi dan taji dawowarsu ta karasa Palo tace HAJIYA sannuku da dawowa, mum tace yawwa sabreen sannunki da gida ya fama da aiki, sabreetayi tace alhamdulillah sannan tace ya kamal yah suhail sannunku da dawowa, sukai mata sukace yawwa sannu da aiki, ta kalli HAFSAT sukaiwa juna murmushi tace sannu da dawowa, HAFSAT tace yawwa sannu sanna itama ta shige d'aki. Suhail yace muyi alwala ko semu wuce masallaci, kamal yace to Kaje ina zuwa sannan suhail ya wuce ya barsu a tsaya, sabreen ta juya zata koma d'aki se kamal yace sabreen inasonyin magana dake, sabreen ta juyo tana kallonsa tace toh yah kamal ina sauraronka, daga Inda yake tsaye yace baridai muyi sallan magrib tukunna kinji, tace to badamuwa, murmushi yayi mata sannan ya wuce d'akin suhail ita kuwa tanata binshi da kallo harya shige sannan tayi ajiyar zuciya ta wuce d'akinta.
   Bayan sun dawo daga masallacine suhail yace toni bari in ciga ciki seka shigo, OK kamal yace dashi sannan ya kira sabreen a waya yace mata yana tsakar gida acikin mota, tace to ina zuwa shi kuwa ya shige mota ya zauna yana jiran fitowarta. Saida ta sake fesa turare sannan ta fito bakowa a Palo ta wuce gun Motansa ta bud'e gaba tare da sallama bayan ya amsa sallamarne seta shiga ta zauna tare da rufe kofan tace gani yah kamal kanta na kallon gate d'in gidansu shi kuwa yana kallonta yayinda take ganinsa da gefen idonta.
                                   Sad-Nas



TANARAINA
    By Mmn Shureim
           (Sad-Nas)
41-42 Kamal yana komawa gida ya watsa ruwa a jikinsa sannan yayi shirin bacci, wayarsa ya d'auka ya kira mummynsa ya gaya mata komai akan sabreen. Farin ciki sosai tayi mishi tare da addu'oi tace kaga se'a had'a aurenku dana suhail, kamal yace insha Allah mummy sannan sukayi sallama seya kira sabreen.
Ringing d'aya ta d'auka hello,  murmushi yayi yace hello sabreen kardai har kinyi bacci, a'a idona biyu ka tafine? Eh natafi kodai kinaso in dawone, a'a kawai dai na tambayane, yace bakinki fitowa muyi sallama ba, bahaka bane yah kamal kawai dai... se kuma tayi shuru, yace kawai dai me, tace bakomai ka isa gida lfy, lfya lau mummyna tace ingaisheki sosai, murmushi tayi tace nagode ka gaisheta, zataji me kikeyi yanzu? Bakomai ina kwamcene, har zakiyi bacci kenan, eh tace dashi, yace ok to shikenan bari in barki ki huta kinji, to nagode seda safe, ehen "I luv you so much sabreen" kunya taji sosai bata ce komaiba, yace sabreen, tace na'am a hankali, ya sake cewa "i luv u" itama tace "i luv u too" cikin wata irin murya wanda yaji dad'insa, murmushi yayi yace "ok good night" tace ok sannan tayi saurin katse wayar tare da sauke ajiyar zuciya tana murmushi. Mikewa tayi ta fito palo da niyan d'iban abinci dama bata ciba, anan taga su mum sunata hira inda yah suhail yake cewa hafsat yakamata ki dinga zuwa kichine kina ganin yadda sabreen take girki dan kinsan bazata dauwama agidannanba dole wataran zatayi aure, mum tace ai nima yanzu na samu sauki dan haka zan dingayi. Sabreen tace dasu sannunku hajiya, mum tace yawwa sabreen se yanzu zakici abincin? eh hajiya, sannan ta wuce inda ya suhail ya mike yayi gun daining d'in dan d'auko wayansa. Bayan ta gama d'iban abincinne ta juya zata koma se kafanta ya zame a tiles din saura kadan ta fad'i suhail ya tallafota da hannunsa biyu inda ta rike plate d'in da kyau suna kallon idon junansu, sabreen taga kamar suhail yaso ya gane idanunta, da sauri ta mike tate da janye jikinta ta sunkuyar da kai tace nagode sannan ta wuce d'aki yanata binta da kallo樂. Sabreen tana shigewa d'aki ta sauke wani ajiyar zuciya tare dayin murmushi tana jin dad'i a ranata ta d'ayan b'angaren kuma kallon da suhail yake mata alokacin daya tallafota kamar kallon sani yake mata, tace to yanzu idan yah suhail ya gane idanuna fa, gaskya nayi kuskure bazan sake yarda mu had'a idoba. Shi kuwa suhail bayan ya d'auki wayansa ne seya fita waje zuciyarsa cike da waswasi akan sabreen, dan gaskya idanunta sunyi mishi kama dana wannan yarinyar樂, kaka ya hango a tsakar gida suna hira da maigadi, ya karasa gunsu yace kaka nazo gurinkane. Kaka ya mik'e tare da cewa to muje daga can koh, gefe suka koma tagun ajiye motoci suka zauna a fararen kujeran roba, suhail yace kaka inaso in maka tambaya akan sabreen ne, kaka yace ina jinka. Suhail yace wato kaka gaskya bazan b'oye maka aduk lokacin dana kalli sabreen se inga kamar itace wannan yarinyar da neke nema mai nik'af d'innan dan gaskya bazan tab'a mancewa da idanuntaba, kakaji yaji k'irjinsa ya buga dan SALMA ta gaya masa komai kuma ta tabbatar mishi da cewa suhail shine wannan saurayin, kaka ya dawo daga duniyar tunani yace gaskya d'annan nidai jikata bata taba sa nik'af ba kuma ba'a mata fyad'eba sannan kasan babu yadda za'ayi ace an mata fyad'e kuma tab'oye mana kai kanka kasan bazai tab'a b'oyuwaba tunda kace MAZA ne harsu UKU kuma manya. Shi kansa suhail yabinda yake basa mamaki kenan yacewa kaka kwarai kuwa hakane to k'ila kamannine kawai idanunsun yayi, kaka yace eh zaiyu amma kai meyasa ka damu hakane d'annan? Suhail yace kaka bazan b'oye makaba wlh tun a wannan lokacin yarinyar "TANA RAINA" Allah ya d'auramin SONTA kaka fatana shine in sake had'uwa da ita dan in gaya mata sak'on zuciyata. Kaka yace kana nufin zaka aureta a hakan? Kwarai kuwa kaka don haka zuciyata take gayamin, kaka yaji dad'in hakan a ransa yace lallai sabreen tayi sa'an samun suhail a rayuwa gashi zai rik'eta tsakaninsa da Allah kuma jikarsa zata huta dan haka gobe zai sanar da sabreen komai sannan kuma zaice ta gayawa suhail d'in cewa itace wannan yarinyar kuma ba'a mata fyad'eba. Suhail ne ya katseshi da cewa shikenan kaka nizan shiga ciki seda safe, tare suka mik'e sannan kaka yace toh Allah ya tashemu lfy, suhail yace ameen sannan yayiwa maigadi sallama seya shiga cikin gida. Koda ya shiga su mum sun shiga bacci, sabreen ne ta fito da plate d'in abinci kanta ko d'ankwali babu dan tasan babu kowa a palo ta nufi kichine bata lura da suhail ya shigo palon ba, shi kuwa suhail gashin kanta kawai yakebi da kallo mai tsayi sosai dan batasa ribom ba yana baje a bayanta. Kichine d'in ya bita lokacin tana wanke hanunta akan sink yaje dab da bayanta ya tsaya, bayan ta gama wanke hannuntane seta juyo dan komawa d'akinta aiseta tsorata ganin mutum a bayanta har hannayenta sun tab'a kirjinsa inda ruwan hannunta ya jik'a mishi rigansa tana kallonsa cikintsoro suhail yace wlh kece kece wanan yarinyar daga razanarki na gane kece dan bazan tab'a mantawaba
                                   Sad-Nas
TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
43-44 Murmushi sosai suhail yakeyi yana kallon idanun sabreen, da sauri ta matsa baya tana cewa me kake cewane yah suhail wata yarinya kenan kake magana akai, cicefa sabreen ba wata yarinyaba. Suhail ya dawo haiyacinsa tare da sosa k'eyarsa yace kiyi hakuri sabreen idanunkune sukayi kama sosai da nata kiyi hakuri kinji, kai zanba hakuri yah suhail dana jik'a maka riga, karki damu ba komai seya juya zai fita se sukaga hafsat tsaye a kofar kichine d'in. Suhail ya tsaya yana kallon hafsat yace hafsat me kikazo d'auka, ta d'an wayance tace nazo d'aukan ruwane se naji murya a kichine shine na shigo ashe kune, tana kaiwa nan ta juya da sauri ta koma d'akinta, suhail yasan hafsat tasa wani abu a ranta, ita kuwa sabreen jikinta a mave yake dan hafsat ta gansu da suhail a kichine gashi da daddare, da sauri tazo gun kofan inda suhail yake tsaye tace dashi barin wuce, juyowa yayi yana kallonta ita kuwa kanta a sunkuye ya matsa mata yana kare mata kallo harta wuce sannan shima ya wuce d'akinsa da damuwa sosai a ransa. Hafsat ranta se tafasa yakeyi ita dai batan me sukaceba amma to me yah suhail yakeyi a kichine gurin sabreen bayan sam shi bayama shiga kichine lallai zan koyawa sabreen hankali idan dai har tayi kok'arin shigewa suhail d'ina, kai ina bazai yuba gobe zanyiwa mum magana akan aurenmu da suhail. Ita kuwa sabreen mamaki takeyi akan ganeta da suhail yaso yayi, lallai akwai aiki gobe zan sanar da kaka lbrn soyayyata da yah kamal gara kawai ayi aurenmu kar azo a samu matsala, sannan ita kanta taga yadda ran hafsat ya b'aci tace toko son yah suhail d'in takeyi oho, kishine ya tokarin sabreen a k'irjinta tace Allah sarki yah suhail shikenan zan rasaka, kuma na tabbatar daka fara sonane yanzu nima kuma ina sonka wlh.
  Washe gari da safe sabreen bata fitoba dan basa karyawa da wuri kuma bata sallah. Harse 8:00am tayi wanka tasa riga da siket cikin kayan da kamal ya saya mata material ne blue ya mata kyau sosai ta fesa turare sannan ta yafa gyale a kafad'arta ta fito ta wuce kichin toasted bread tayi musu wanda tasa saidin a ciki se kamshine yake tashi ta sake soya egg sannan ta tafasa ruwan tea da kayan yaji taje ta shirya komai a daining sega hasat tayi wanka tasha english wears riga da siket tayi ado tazo har daining tana k'arewa kayan jikin sabreen kallo ita kanta tasan mai t'sadane dukda tasan cewa itama kyakkyawace amma kuma tasan bazata had'a kanta da sabreenba ko kusa. Ta k'arasa tace ke sabreen me kukeyi da yah suhail jiya a kichine? Sabreen ta juyo tace ina kwana hafsat, hafsat tace ba wannan na tambayekiba ai, sabreen tace bakomai hannuna naje wankewa shi kuma bansan meyaje yiba, daidai lokacin suhail ya shigo palon lokacin hafsat tana cewa to wlh ki kame kanki ina gayamiki suhail shine mijin da zan aura dan haka ki dena wannan rawan kan nakisannan ta juya suka had'a ido da suhail ta wuce d'aki ko gaishesa bata yiba yanata binta da kallo. Jikin sabreen yayi sanyi dan maganan ya b'ata mata rai ta kalli suhail tace ina kwana yah suhail sannan ta wuce batare data jira amsarsaba ta d'auko abincincin su kaka dana mai gadi takai musu. Shi kuwa suhail yana tsaye agun yana binta da kallo harta fita sannan yayi sallama a kofar d'akin hafsat tazo ta bud'e yana tsaye fiskarta a had'e yace yau bazaki gaisheni bane hafsat, shuru tayi nad'an lokaci sannan tace ina kwana, yace lfy fushi kikeyi dani kenan ko? Ta marairaice murya tace gaskya yah suhail inaga lokaci yayi daya kamata muyi aure indai har kana sona, suhail yace to shikenan ki denayin fushi zanyiwa mum magana kinji, murmushi tayi tace to nagode muje muci abinci to, shima murmushin yayi mata yace to muje sannan suka nufi daining inda mum take zaune agun tana karyawa, dad'in ganinsu tare taji sosai suka zauna suna gaisawa. Sabreen kuwa bayan ta kai musu ta zauna agun kaka tana gaya masa yadda sukayi da kamal kuma ta amince. Kaka ayi ajiyar zuciya sannan yace sabreen shikenan tunda dai kina sonshi kema, amma shi suhail ya riga fara sonki tun lokacin da kuka fara had'uwa, sabreen SALMA ta gayamin komai kuma jiya da darema suhail yazo min da zancen yarinyar akan yanaga kamar kece ni kuma Sam ban gaya masa cewa kece d'inba, dukda dai shi atunaninsa an miki fyad'ene ahakan kuma yake sonki sosai sabreen. Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tace kaka wlh Nima ina sonshi amma kuma yah kamal fa, kuma kaka hafsat tana son suhail sosai nan taba kaka lbrn abinda ya faru tas. Kaka ya tausayawa jikarsa sosai yace to shikenan sabreen shima kamal d'in ai mutumin kirkine Allah ya zab'a miki mafi alkhairi, tace ameen kaka maganan me kukayi da salman? Kaka yace mun dad'e Muna jiran zuwan salma da iyayenta tun bayan rasuwan mahaifinki da kwana  7 suka dawo suka gayamana gaskyar yadda mahaifinki ya rasu kuma suka bamu hak'uri sannan suka tabbatar mana da cewa duk lokacin da Muke buk'atar taimako zasuzo garemu nan kaka ya gaya mata cewa wannan macijin daya sari mamminkima salman CE ta kasheshi ba jama'an gariba babu Wanda yasan hakan saboda suba mutane bane ALJANUNE
                                 Sad-Nas
TANARAINA
      By Mmn Shureim
             (Sad-Nas)
45-46 ALJANU, Aljanufa kace kaka, kana nufin salma aljanace shine nayita hankad'ata jiya? Kaka yace kwarai kuwa shiyasa naketa dakatar dake, danma kinyi sa'a salma tana sonki a ranta ne tace ranan tazo gunki a d'akinki ganin,yadda kika tsoratane yasa ta canja salon zuwa ta yadda kowa zai ganta dan karki tsorata, amma wannan maganan ya zama tsakaninmu mu uku kinji? Sabreen ta sauke tsorataccen ajiyar zuciya tace to kaka shikenan nizanje in karya, yace toh sannan ta fito har zata shiga palo se taji hon, bayan maigadi ya bud'ene se taga motar kamal ne yake shigowa, hon yayi mata tare da kunnan wutan motan yana hankata, murmushi tayi sannan ta k'arasa gun motan ta tsaya ta gefensa, fitowa yayi cikin farin shets da blue jeens yayi kyau sosai ga kamshi da yake tashi, "good morning my luv" yace da ita yana murmushi, kunya taji sosai ta kauda kanta gefe tace morng ya kake, lfyta lau kin fito gurin kakane? Eh nakai mishi abincine, ok to muje ciki kafin ya gama cin abincin se indawo gunsa. Ayate suke tfy yana kallonta tare da cewa gaskya wannan wankan yayi kuma na yaba, dariya tayi dai dai lokacin sun shiga palo tare da sallama, wani irin abu ne ya tokari suhail a k'irkinsa ayayinda ya hangosu suna tahowa, sabteen ta karasa ta gaida hajiya sannan ta wuce ciki sunaya binta da kallo dukkansu. Bayan kamal ya zauna ne suka gaisa sannan hafsat ma ta gaishesa tare da had'a mashi tea, suna sha suna hira. Anan ne kamal yake sanar da mum k'udirinsa akan sabreen, mum taji dad'i sosai kuma tayi farin ciki tace to ai gara dai kam kuyi aure zaifi, kaima suhail yanzu kam lokaci yayi da za'ayi aurenku da hafsat kamar yadda iyayenku sukeso. Wani irin dad'i hafsat taji a ranta tace kamar kina raina mum, suhail ya kalli hafsat yace mum tunda tana karatu a dai bari seta gama tundama saura 1year ne ta gama. Mum tace to shikenan Allah ya nuna mana, yace ameen, kamal yace to gaskya nidai zan rigaka dan banaso in wuce nan da 6 month, suhail yayi murmushi yace to Allah ya sanya alkhairi, sukace ameen.
  Ita kuwa sabreen tunda ta shiga d'aki taketa tunanin maganan da sukayi da kaka, nan ta kira munira ta gaya mata komai a waya. Munira tayi mamaki sosai tace yanzu bakya tsoro sabreen gaskya ina son ganinta, kuma inaso ta zama kawata wlh, sabreen tace lallai kam to idan ta sake dawowa zan had'aku. Munira tace to yanzu shikenan kin hakura da suhail d'in? Sabreen tace eh nahakura munna kawai zan auri yah kamal tunda ma kinga ga abinda hafsat tace min, munnira tace to shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agareki k'awata, sabreen tace ameen ina abbakar sadiq d'inki? Munna tace yanan shimafa ya dage wai miyi aire se inci gaba da karatuna, sabreen tace eh tundai zai barki ai shikenan nima hakan zanyi, munna tace eyye ashe fa kina son kamal d'innan, sabreen tayi dariya tace bakida kyau fa munna nikam se anjuma ki gaida su mama, munna tace to nagode zasuji ki gaidamin "ango to bee" hmm zaiji sannan ta katse wayar tana dariya.
   Bayan su mum sun gama cin abincine kamal da suhail sukaje gun kaka kamal ya gaya masa buk'atarsa akan sabreen, kaka yaji dad'i sosai kuma ya tabbatarwa kamal cewa yabashi tunda dai sabreen d'in ta amince, murna sosai kamal yayi sannan sukayiwa kaka godiya suka tafi. Suhail da kamal ne suke tfya a cikin motansu suna hira, suhail yace abokina ka kusa ka zama angon sabreen, kamal yace bawannanba tukunna, kasanfa matsalata suhail yanzu in gayawa sabreen ne ko dai inyi shuru? Suhail yace ina kace nanda 6month kake son auren, kaga daidai kenan kafin lokacin auren komai zai daidaita kamar yadda doctors sukace insha Allah. Daganan kuma shikenan seka jah kaya abokina gaskya zaka morefa da wannan sabreen d'in naka, duka kamal yakai masa yana dariya tare da cewa kaima ai k'i kayi damunyi tare. Suhail yace abokina kafi kowa sanin cewa ban tab'a "SON" hafsat a matsayin matar aurenaba sedai "SO" amatsayin 'yar'uwata na jini, nidai wannan yarinyar "TANA RAINA" itace nake "SO" a matsayin matar aurena dan haka sedai in auri mata biyu a rana d'aya wannan shine burina, da zab'in mahaifina da kuma zab'i nah. Kamal yace "ar u serious?" Suhail yace wlh abokina shiyasa nake so ka tayani da addu'a Allah ya sake had'ani da "TANA RAINA" kamal yace tofa harka lak'ana mata suna kenan toh ai semu sake komawa k'auyen gobe ko Allah zaisa mu dace, suhail yace hakan za'ayi kuwa, kamal yana kallon abokinsa kallon mamaki da irin son da yakewa wanda akaiwa fyad'e, yace sekayi angon "TANA RAINA" dariya suhail yayi yace eyyy angon sabreen sannan suka tafa✋suna dariya nima "SAD-NAS" na tayasu
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
    By Mmn Shureim
           (Sad-Nas)
47-48 Washe gari bayan su suhail sunyi breakfast ne sukayiwa mum sallama akan zasu fita, mum ta musu fatan alkhairi sannan suka wuce tsakar gida gun kaka inda yakeba flawer ruwa, kamal ya kira sabrenn a waya dan yau tunda yazo baigantaba, sunata hira da kaka sega sabreen ta fito da himar har k'asa tana tafiya a hankali, juyowa sukayi suna binta da kallo, tunda kaka ya hangota yasan cewa tayi kuka. Ta k'araso tare da gaishesu kanta na gefe, daga kamal har suhail sunsan akwai wani abu a k'asa dan sam babu ko fara'a a fiskarta. Kaka yace sabreen lfy kuwa yana ganki haka? Hawaye suka zubo a fiskanta ta share da hannunta tace bakomai kaka, kaka yace bakomai kike kuka kuma gashi sam babu fara'a a fiskarki meya samekine? Kakana karka damu bakomai kawai dai mun d'an samu matsala ne da hafsat kaka kasan cewa ina da hakui akan komai, amma kalamanta sunmin zafi sosai wanda idan na tuna tuna suna min zafi sosai, ta goge hawayenta ta juyo tana kallon kamal tare da cewa yah kamal dan Allah ka janye soyayyata kaje ka nemo daidai da kai, ni talakace 'yar kauye sannan jahila k'azama wanda take bin duk wata hanya koda ya sab'awa Allah ne taya yinshi dan ta janyo hankali yayyuna biyu da suke cikin gidan, akan suhail dai asirinki baiyi aikiba, shima bro kamal d'in ahankali asirin zai karye daga nan kuma ta k'are miki 'yar gidan matsiyata wanda bata da gatan uwa bare na uba.
  Kallon kamal da suhail takeyi har cikin ido tana kuka tare da cewa wannan sune kalmomin da hafsat ta gayaminsu saboda nazo yin aiki a gidansu, kaka yau da asuba danazo gaisheka ban gaya maka bane saboda nasan hakuri zaka bani, amma su yayyuntane na gaya musune saboda su zama shaida dan gaskya hafsat bazata sake gayamin hakan ban mayar mata da martani, gudun faruwan hakanne yasa nakeso mubar gidan kawai nida kakana masu girki suna nan dewa a gari na gwammace inci gama da zamana a k'auyenmu. Tana kaiwa nan ta juya da saurinta ta koma ciki tanata kuka. Gaba d'ayansu abin ya musu zafi, kaka yace karku damu da zaran ta huce shikenan. Ran kamal inyayi dubu ya b'aci, yace dama haka hafsat take樂, suhail kuwa cikin gidan ya koma yana kwalawa hafsat kira, da sauri ta fito don jin muryarsa da karfi. Ta k'araso tare da cewa na'am bro suhail gani, ransa a b'ace yace meya had'aku da sabreen? Atake ta b'ata rai tace bakomai, suhail yace kamar ya bakomai, kimin bayani meya had'aku da ita? Hafsat ta b'ata rai tace bro yanzu saboda sabreen d'inne kake min ihu haka har kana b'ata rai, nifa kanwarkace kuma wanda zaka aura, hafsat ba wannan na tambayekiba dan ke k'anwatace seki aikata laifi? Tace laifin me kuma na aikata bro wato takai k'arata gunka kenan harta samu fiskan kai kara agunka tabd'i to shisshigemin takeyi ni kuma bana son hakan shine nace mata ta fita harkata danni ba sa'arta bace. Suhail yace hafsat yaushe kika zama haka, wlh kinban kunya ban tab'a tunanin haka daga garekiba a irin tarbiyan da kika taso. Yah suhail waime ta gaya makane dahar ka yadda dashi haka kaketa min fad'a? Suhail yace abunda kika mata shita gayamana dan haka wannan ya zama na farko kuma na karshe kar in sakejin kin mata haka kina jina? Rai a b'ace tace naji sannan ta wuce d'aki kamar zata fashe. Mum ce ta fito tana cewa suhail meke faruwane kaida hafsat naji kamar fad'a kake mata? Suhail yace bakomai mum ki barni da ita kawai laifi tayi, laifi kuma, hafsat d'in laifin me tayi toh? Suhail yace sund'an sami rashi jituwane ita da sabreen kuma ita  hafsat d'ince da laifi. Toh yau kuma hafsat da fad'a bari inje inji toh, se mum tabi hafsat d'aki shi kuwa suhail ya shiga d'akin sabreen tare dayin sallama. Tana zaune akan gadonta tana share hawaye da hannunta, mik'ewa tayi tare da amsa sallamar cikin muryan kuka kanta a sunkuye, hanki ya ciro a aljihunsa ya mik'a mata, wani iri taji sannan tasa hannunta ta karb'a tace nagode. Yana tsaye daga kofa yace sabreen dan Allah kiyi hakuri kinji, na mata magana hakan bazai sake faruwa kinji? Wani sanyi taji a ranta ta d'aga kai alamun toh, murmushi yayi yace toki dena kukan pls, kawai setaji tana son kallon fiskarsa seta d'ago da kanta tana kallonshi tace "thankyou"☺. Muryar nata yayi mishi kama dana wannan yarinyar wlh suna kallon juna har cikin ido setayi saurin sunkuyar da kanta k'asa saboda wani irin kaunarsa da yake ratsa jikinta, shidai baisan me zaiceba seya bud'e kofan ta d'ago da kanta sunata kallon juna harya fita. Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tanaji dad'i acikin ranta wani gefen kuwa cewa takeyi kawai zancewa yah kamal yafito muyi aure dan gaskya bazan iya jurewa soyayyar suhail ba matukar ina sashi a idanuna gaskya. Afili kuma tace suhail kai nakeso tun ranar daka zubar da jininka akaina nice fa sabreen nice yarinyar da kake nema "I LOVE YOU SO MUCH SUHAIL". Suhail da yake tsaye a bakin kofa kuma dai yasan ba karya kunnensa yayi mishiba tabbas yaji abinda sabreen tace樂...
                                  Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
49-50 farin cikine ko bak'in ciki suhail yakamata yayi oho, shikansa ya kasa ganewa, yana cikin jimamin abunne yaji tfyar mum zata fito daga d'akin hafsat, da sauri ya fita ya wuce gunsu kamal da kaka inda suke tsaye suna magana. Suhail ya k'araso yace kaka dan Allah kayi hakuri da abinda hafsat tayiwa sabreen yani mata magana hakan bazai sake faruwaba insha Allah, kaka yace haba suhail aida ka rabu dasu, nasan sabreen zata huce sarai. Daganan sukayi mishi sallama sannan suka tafi k'auyen su sabreen, tunda suke tfy suhail hankalinsa sam yana gun sabreen barema dayaji tace shi takeso. Kamal yace abokina yanaji kayi shurune? Suhail ya dawo daga duniyar tunani yace fad'an danayiwa hafsat ne yad'an dameni kasancewar ban tab'a mata fad'anba. Kamal yace barina kirata to, take ya kira hafsat kamar bazata d'aukaba se kuma ta d'auka tace hello, kamal yasa a hands free yace k'anwata kiyi hakuri da abinda yafaru dan Allah gashi tun d'azu suhail se tunanin fad'an daya miki yaketayi abin ya damesa. Wani sanyi hafsat taji a ranta kancewa suhail ya damu da fushin datayi tace ina yah suhail d'in, kamal ya kalli suhail sannan suhail yace hello, dad'i taji tace hello yah suhail, yace na'am kiyi hakuri da abinda ya faru kawai banyi tsanmanin haka daga garekibane sannan kuma dan sabreen tana aiki a gidanmu bai dace mu tozartaba ina fata zaki fahimce, eh naji yah suhail nasan nayi kuskure amma kayi hakuri kuma zanje inbawa sabreen hakuri yanzu, dad'i yaji har cikin ransa sannan yace mata yawwa "my wife to be shiyasa nake k'ara sonki", karon farko kenan da hafsat daji kalma mai dad'i daga bakin suhail masoyinta, tace shikenan sekun dawo, yace yawwa byee sannan ya katse wayan. Kamal yace tofa soyayyarce ta tashi kenan? Suhail yayi murmushi yace eh d'ansa ido.
Shi kansa kamal yasan kawai suhail ya furta hakanne dan hankalin hafsat ya kwanta amma bawai dan yana sontaba. Haka sukaita hira, amma shi suhail tunanin sabreen ne a ranshi yayinda wani sonta yake k'aruwa a ransa. Sun isa kauyen sun dad'e sosai sunata nema amma shuru, musamman ma kamal duk wanda yagani zaiyita masa kwatance amma se ace musu ba'a santaba, shi kuwa suhail yacewa kamal kawai kazomu tafi tunda bamu sametaba na hakura zan auri hafsat d'in kawai. Haka suka kama hanya suka dawo lokacin 2:40pm, sabreen ta fito kaiwa su kaka abinci kenan segasu kamal sun shigo. Kallonta sukeyi dukkansu biyu harta shige ta ajiye sannan ta fito daidai lokacin sun fito daga motan tace dasu sannunku da dawowa, suhail yace yawwa sabreen sannu sannan ya wuce gaba ita kuma suna biye dashi ita da kamal. My luv yakike ya gajiyan aiki, bawani gajiya aina saba, kin tabbata? Eh sannan tace yah idan kaci abinci inason yin magana dakai, yace ok hope dai lfy koh? Tayi murmushi tace lfy lau, yace to idan na gama zan kiraki a waya kinji, tace toh sannan ta wuce d'akinta. Bayan ta kwantane munira ta kirata tana gaya mata cewa aisu suhail sunje k'auyensu yanzuma dagacan suka dawo sunje neman yarinya mai nik'af, sabreen tace toke waya gaya miki? Munna tace mutanen da suketa tambayane suka gayamin waiko nice, shine na tambayesu ina mutanen, se suka nunaminsu kawai senaga kamal ne da suhail ammasu basu ganniba. Sabreen tace nagode munna zansan yadda zanyi zan kiraki anjuma Sannan sukayi sallama sabreen tana ta mamakin abin aranta.
  Bayan su suhail sun gama cin abincine se suka wuce d'akin suhail suna hutawa, shi kuwa suhail kwanciya yayi tare da rufe ido kamar maiyin bacci. Kamal ya kira sabreen kuma yasa a handfree suhail yanajin komai, sabreen tace hello yah kamal, yace banace miki banason sunan nanbako, tayi murmushi tace to kayi hakuri ina kaje haka bakamin sallamaba? Am sorry luv naso inyi miki sallamanne se kuma kika tafi cikin fushi,  to ina kaje inadai bagun wata kajeba ko? Kina kishinane luv, sosaima dan gaskya ina da kishi, dariya kamal yayi yace to shikenan karki damu ke kad'ai kin isheni my luv na raka suhail, ananne suhail ya bud'e kunnensa da kyau donjin me sabreen zatace, ina ka rakashi, hira na rakashi luv kuma bamu sametaba, shuru sabreen tayi se kuma tace ok mummy ta kirani d'azu gaskya naji kunya sosai wlh, kamal yayi dariya yace kunyanme kuma keda zan kaiki gunta, hahah to shikenan Allah ya nunamana ameen luv gaskya inaso ayi bikin da wuri wlh, sabreen tace nima haka, dad'i kamal yaji yace da gaske kikeyi luv? Tace wlh kuwa, yace ok dama nace nanda 6month ne amma zanje in samu kaka ince mishi nanda 3month nakeso hakan ya miki? Eh yamin, ok zanyiwa mijin mummyna magana danshine zai karb'a min auren, ok badamuwa ina yah suhail? Gashinan a gefena inaga kamarma yayi bacci, ok shikenan zanje in d'aura abinci bye, "ok my luv bye i love u", murmushi sabreen tayi tace "me too" sannan ta katse wayar.
  Kamal ya daki suhail yace tashi abokina angon "TANA RAINA" nanda 3month zan zama angon sabreen, suhail daya gama jin duk hiransu ya tashi yana cewa baka da kirkifa shine zaka tasheni ina cikin bacci, sorry angon "TANA RAINA" farincikine yamin yawa wlh.
  Bayan sunci abincin darene sund'an tab'a hira kad'an se kamal yasamu kaka da maganar aurensu da sabreen, kaka yace bakomai zaije kauye danya sanar da aminan mahaifinta, kamal yaji dad'i sosai sannan ya tafi da farin ciki a ransa. Suhail kuwa bayan mum ta shiga baccine ta barsu a palo shida hafsat suna hira sannan yayi mata seda safe ya tafi d'akinsa itama tayi nata d'akin tanata farin ciki
  9:30pm suhail ya fito da jallabiya ajikinsa yaje kofan d'akin sabreen yana nocking, sabreen ta d'auka hafsat ce dan haka batasa ko himarba daga ita se kayan bacci, dogon wandone har k'asa se rigansa iya cinyanta mai guntu hannu kanta ba komai tayi parking seta zo ta bud'e kofan yah suhail ne a tsaye yana kallonta tun daga k'asa har sama gashi batasa bra ba "BUBS" d'inta suna tsats tsaye
            

0 comments:

Post a Comment