Monday, 27 November 2017

'Ya'Ya Da Kudi Page 26-30 LATEST HAUSA NOVEL- ISMAIL SANI


'YA'YA DA KUDI Page 26-30
.
Tana fita suka nufi gida, da gudu ta shige d’akinta, kuka ta rinka rusa sosai, Hajiyarta ne ta shigo, tace”Zuly mai ya sami k’awarki ne?. Zuly tafara bama labarin komai. Hajiya tanisa tace”Zulaihat ba ki ba ma kawarki, shawara mai kyau, tunda Umar baya sonta, sai ta hak’ura, ko ana son dolene, kusani a ko da yaushe mace, ita ke jan kimarta, nikam bazan goyi bayan k’arya ba. Kunutsu kusan mekukeyi kun fa girma fa, ae ko irin shigan da kukeyi, wazai so ku?. Inayi fad’a Abban su Sakeenah, yace nacika takura masu, ga irinta nan, nima ina goyon bayan Umar, matsawan ba canzawa kukayi ba. Kukan Sakeenat ya karu, sai buga k’afa takeyi, tana cewa”Hajiya ni baki sona, tunda bakison abunda nake so, “tsawa ta daka mata, ke bana son aakarcin banza da wofi fa, sai da tamusu ba dad’i, tukun ta bar d’akin. Dr Umar kuwa lallashin Khadi yayitayi, Gwaggo ne ta shigo da sallamarta, tun daga waje an fata rahoto, shiyasa take fara’a, tana ganin Umar, tace” eehehe duniya yau taimin dad’i, in dai a kanka ne, da Khadi naso da dukan tsiya suka mata, ka wani shigo mana gida d’an iska, wato karuwanka ne suka kasa hak’uri suka biyo ka nan?.
.
Ran Umar in yayi dubu ya baci, don ba abuda yatsana kaman a danganta shi da mazinaci. Gwaggo ta zagesu tass shida Khadi, tayi d’aki, Beebah ko sai basu hak’uri takeyi, Khadi kam kuka takeyi, kafansa yaja jiki ba kwari ya bar gidan. Malam ya na dawowa ya samu labari, yajima yana tunani daga k’arshe, yace anya kuwa bazan dakatar, da Umar da zuwa gidan nan ba?. Haka ya ta sake- sake, har ya tsayar da amsa ma kansa. Bayan kwana biyu Umar yazo, tun a waje suka gaisa da Malam, nan ya fara ba ma Malam hak’uri, Malam yace”ba komai ya wuce, amma inaga ka hak’ura da zuwa kawai, tunda daman ba wata alaka bace a tsakanin ka da Khadeejat, cikin firgici ya d’ago, yanaso yayi magana ya kasa, Malam yajima yana zargin Umar na son Khadi, amma bai furta ba, shiyasa yayi hakan don ya tabbatar. Don zan bada dama ga mai sonta ya turo magabatan sa, ayi magar Aurenta kawai. Inaga hakan shine zai zame mata hutu, Umar duk ya rud’e, yakasa magana jiki ba kwari, yabar unguwan, gudu yakeyi Allah ne ya kaisa gida lafiya, yana zuwa ya tarar da Mum a falo, gunta ya nufa, ya kwantar da kansa, a kan cinyanta, sai ga hawaye. Cikin sanyin murya yace”Mum zan rasata, Mum ki taimaka min, pls dan Allah!. Cikin rashin fahimta Mum tace”wacece zaka rasata?. Ajiyar zuciya ya sauke, Yace”Mun Khadeejat ce, Mum tace”kamar yaya zaka rasata?. Nan ya kwashe labari, ya fad’a ma Mum komai. Tab lallae Sakeenat bata kyauta ba, amma ko da Dad d’inaka bai dawo ba zamuyi waya dole asan abinyi. A yan kwanakin nan duk Dr Umar ya rame, hakan yasa Mum, ta sanar da Dad d’insu, ko da sukayi magana dashi, yace”bazai samu daman dawuwa, a satin ba don haka zai sa mataimakinsa, yaje da kansa, Mum tace” ni a’a ban yarda ba, kasan Alhaji Bashir baya da sauki, akan yara , kawai inaga zamu nimi wani yaje, kuma kaga yanda yakeson Sakeenat, komai zai iya yi. Dad yace”shikenan duk yanda kukayi, Mum ta sanar da Umar komai yayi murna, sanna yace”shi yanaga a tura Baba Liman, don yana da halin dattaku. Haka ko akayi, Baba Liman yaje neman auren Khadi ma Umar, basu wani samu Matsala Baban Khadi ba ya amince. Nan suka zuba kayan mun gani anaso, da kud’in gaisuwa dubu 2k, Malam yaki karba yace sunyi yawa, amma Baba Liman ya dage sai da ya karba. Da murna yashiga gida, a zuciyar shi, yana mai cewa tabbas Khadijansa zata huta, don da alama Umar d’an manyan mutanene, kuma zai riketa da AMANA. da murna ya shiga gun Gwaggo, cikin zak’uwa takaleshi “Malam lafiya naga sai farin ciki kakeyi?. Hmm kedai bari kawai, ina cikin farin ciki, mik’omata su gidan goro da catoons d’in minti yayi, tare da d’aura mata damin kud’i akai, ido ta zaro su waje, “Malam wayan nan kud’in fa da kayan fa?. Cikin murmushi yace”na Khadijat ne, kud’in aurenta. Jakar uba! Ina bazai yuba, ina na Beeba ko Rabee’atu?. To ba a gidan nan za’ayi wannan abun ba, sai dai ko inda Beeba ne. Malam yayi dariya yace”Hauwa kenan wai meysa ba kya boye hassadanki a fili, ae ni na d’auka Khadi da Beeba da, Rabee’at, duk d’aya suke a gunki?. Allah ya sauwake, nawa-nawa ne. Kuma wannan auren bazai yuwuba, sai dai ko in zaka kawo na Beeba sai a had’a. Shikam dariya ta basa, don suk tagama fita a hayyacinta, ya d’ibi kayan ya kai d’akinsa. Khadi najinsu amma duk ta damu da taji wa Malam zai had’ata aure da shi?. Malam ne ya shigo d’akinta, ya zauna a kujera, cikin nutsuwa ya kira sunanta, ta amsa, sai da yamata nasiha, kamar yanda ya saba, tukun ya saida mata, Umar ya kawo kayan ,yagani yana so, ina fatan kin amince kina sosa?. Shiru tayi, daga yanayinta ya gane ta amince, albarka ya samata ya fita. Washe gari Dr Umar yayi wanka sa, yayi kyau sosai, sai da yabiya Sahad ya mata shooping mai yawa, tukun ya nufo gidan, yaro yasamu ya aika ta fito.
.
. Cikin nutsuwa take takawa, tana sanye da hijab ash yamata kyau, hannu tasa a aljihu yana kare mata kalo. Da sallama ta karaso bayan sun gaisa, yace”gimbiya Khadeejatu, murmushi tayi yace kali nan, tana d’ago fuska ya kashe mata ido d’aya, tare da d’aga mata gira, duk sai taji kunya ya kamata. Haka sukayi hiransu a zaure, sai dab zai tafi ya d’ebo mata, kayan saya mata, godia ta masa har zata tafi yace”tsaya barin yi surprising d’inki, murmushi tayi. Yace” pls close ur eye, ba musu ta rufe, ” miko hannuki, bata komai ba ta mika masa tana murmushi, wani zobe ya ciro sai kyali yakeyi, ya sanya mata a hannu, nan take hannuta ya d’au kyalu yana haskawa. Kiss ya kaimta a hannu, sai sukaji, la ha ila ha illalahu, uhu jama’a da sauri Gwaggo ta damke su duka. Ta kwalala jama’a ku kawon d’auki na kama yan iska yau. Ihu take kamar mahaukaciya, Khadi ko duk jikinta sai bari yakeyi, nan take hawaye ya fara zuba, Umar ko don takaici kasa motsi yayi.   Cikin takaici ya fincike rigansa, kalon tsana yake mata, da sauri Gwaggo ta sha gabansa, yau fa sai na tona muku asiri. Wani mugun kalon da ya aika mata, yasa Gwaggo bashi hanya, Khadi da gudu tabar gun. Gwaggo ta ga kayan da Dr Umar ya kawo da rawar jiki ta d’iba tayi cikin gida. Beeba na ganin haka tace”Gwaggo mai yasa keke ma Addah Khadi haka?. Gwaggo cikin zumud’i tace”kee bari kawai ae ido da ido na kamasu suna iskanci, cil da cil ganin annabin tsohuwa. Beeba tace”kai Gwaggo gaskiya Adda Khadi bazatayi haka ba, zata taba zubar da mutuncinta ba, kuma na yarda da tarbiyan da Malam ya bamu. Cikin b’acin rai Gwaggo tace”oh to! to! Wato Malam shi ya kula da tarbiyan ku bani ba?.
.

Beeba shiru tayi ganin Gwaggo ta d’au da zafi. Malam na dawowa Gwaggo da munafurci tazo ta fara labartawa Malam, Malam ya kaleta sama da kasa yace”tashi ki ban guri bana son gulma, a yanzu a kwai wani abunda zaki fad’an na yarda, bacin nasan irin tsanar da kikayi ma Khadija, yarinyan mai hankali, bataji ba bata gani ba, kna gallaza mata, jiki ba kwari Gwaggo ta bar d’akin. Dr Umar ko hankalisa kwance ke gudanar da aiki, yanzu Dad d’insa kad’ai ake jira a kawo sadaki, sai asaka ranar biki. Sakeenat kuwa sam Mum d’inta, taki goya mata baya. Hankalinta duk ya tashi, can ta tuno wata shawara, Zuly ta k’ira a waya. Tace” kqwara kina ina ne yanzu?. Zuly tace”gani a hanyan zuwa gidan ku. “Ok sai kin iso. Ta ajiye wayar tana zaman jiran zuwan Zuly. Ko da Zuly tazo bayan ta gaisa da Hajiyar Sakeenat, tashiga gun Sakeenat, bayan sun zauna Sakeena tace”kawa nifa bazan share mari da Umar ya minba gaskiya. Zuly tace”wani mataki zaki d’auka?. Sakeenat tace”na bayar a sayo min dorina hud’u masu kyau, zamuje unguwansu ba tare da securitys ba, in munga yarinyan ko mu aika tazo sai mu cazata.Zuly tace”good idea, haka zamuyi. Key motarta ta d’auka suka fita,nan idi security ya kawo mata sak’onta, ta karba suka ja mota sai Dakata. Sun dad’e a unguwan Khadi bata fito ba, can da suka gaji yaro suka tura yaro ya kirata, Khadi ko kamar bazata fito ba, amma can da yaron yasake dawowa, ta d’au hijab d’inta tace”Beeba ana kira na a waje barin duba ga wayata nan. Khadi na fitowa yaron yace”gasu can a wancan motar. Khadi tana ta raba ido, don Umar bai tab’a zuwa mata da irin motar ba. Sakeenat ko suka rike bulala kowa ne bibiyi a hannusu, sai da Khadi tazo kusa suka bud’e motar atare, suka nufota da gudu dukanta suke tak’o’ina. Khadi ihu take amma basu kyaleta ba, Beeba taji kamar muryan Khadi da gudu ta lek’o ganin ana dukanta, koma gida “Gwaggo dan Allah kizo, yaran ranan suna dukan Adda Khadi, Gwaggo tace”ha da gaske Beeba tace”eh!.
.
Duka suka fito da gudu. Dukanta ko suke Gwaggo ta fara kukara mata, kunyi min dai-dai. Rab Beeba ya b’aci sosai, ganin ba mai ceton Khadi, gashi ba maza a gun, yasa ta tuna da Dr Umar. Da sauri ta duba call history, ta kira number, bugu biyi yad’aga, “hello hello Ya Umar kazo ga wasu na ta dukan Adda Khadi, wanda suka zo ranana. Cikin figici yace”what suwaye?. Kashe yawar yayi ya shiga mota gudu yake kamar zai tashi sama. Sakeenat ko ganin sun mata lilis, ga mutane sun soma taruwa da gudu suka shiga mota, suka bar unguwan. Dai-dai zasufita a layi motar Dr Umar yadanno kai ganin motar Sakeenat yasa yasha gabanta, ganin zai tsaresu yasa taja motar da k’arfi sai da ta buge masa glass d’in mota ta gudu. Da har zai bita sai ya tuna kowani hali Khadi take kuma?. Sai ya fasa ya kara gudu. Beeba ko ganin sun tafi dakyar wata makwabciyar su, ta taimaka mata suka shiga da Khadi gida. Karkuga fiskan Gwaggo fal farin ciki. Dr Umar na zuwa yaga mutane, da gudu yayi salama ya shiga gidan, Beeba ya fara karo da ita cikin damuwa ke tambayrta ina Khadija?.
.
Hawaye ya k’ara zubowa “tana d’aki a kwance. Yana shiga yaga halin da take ransa ya b’aci sosai. Ya kira beeba yace” ki had’a ruwan zafi don tayi wanka, waya ya kira ba afi minti goma ba sai ga wasu ma’aikatan asibiti da kaya, da kanta yamata treatment, ya mata allura nan take bacci ya d’auketa. Yana fitowa yace”sistet Beebah barinje gida na dawo. Na mata allura ta samu bacci, in ta tashi ki kaimata ruwa ta watsa zataji dadi. Yana zuwa gida yasanar da Mum d’insa komai, cikin bacin rai takira His Excellency yana d’auka, tace” ranka shidad’e! Ya aiki?. Cikin jin dad’i His Excellency ya amsa. Nan ta sanar masa da komai, sai da ya jin-jina al’amarin yace”tun da Baba liman nanan zan sa a tura 1million sai akai sadaki, 2millions kuma a had’a kaya akai. Ina dawowa sai aure kawai.
.
Mumcikin farin ciki tace”Allah ya ja kwanan mai girma governor, godiya muke Allah ya tsare mana kai, Ya amsa da ameen. Malam ko da ya dawo ransa ya baci, amma yace”duk hakan baza’a fasa auren nan ba sai anyi, duk mai hassada sai dai yayi ya gama. Dr Umar ko kulum sai yayi sawu 3 a gidan kula ta musamman ke ba Khadi. Yau da yazo bayan sun gaisa da malam ya saida masa “iyayensa zasu zo, za’a kawo sadaki. Malam yace”Alhamdulilah! Allah ya kawosu lafiya mungode. Washe gari Baba liman yazo ya kawo sadaki, Malam sai da ya razana, kin karban kud’in yayi yace”gaskiya Malam sunyi yawa a rage. Baba liman yace”sam bazan koma da ko si-si ba, mudai fatan mu Allah ya sanya alkairi. Baban Khadi ganin Malam ya girmesa, kuma bazai iya masa musu ba ya sa hannu ya karb’a. Yana shiga gida don ya ba ma Gwaggo haushi yace”Hauwa kawo min taburma nan kizo kiga ikon Allah. Da sauri Gwaggo ta fito har tana tun-tub’e, ta shin fid’a masa tabarma bayan ya zauna sai taga ya zaro da min kud’i har bunch biyar, ido Gwaggo ta zaro, “Malam ina kasamu wanna kud’i?. Murmushi yayi yace”Hauwa wato zakaran da Allah yanufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi. “Kuma d’an hakin da karaina wataran sai ya baka mamaki. Gwaggo tace”ni dik ban gane hausanka ba Malam?. Malam yace”hmm Sadakin Khadi aka kawo har naira na gugan naira million d’aya. Wayyo nashiga uku sadaki ina Malam d’an yankan kai ne ba fa zaiyuba. Nima sai ka samo ma Bedba miji, Gwaggo ta sha kwalan Malam, ihu take tana kuka, tana fad’in ya cuceta. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment