Monday, 27 November 2017

'Ya'Ya Da Kudi Page 31-35 LATEST HAUSA NOVEL- ISMAIL SANI



'YA'YA DA KUDI Page 31-35
.
Gwaggo ta sha kwalan malam sai ihu takeyi, ya sa hannu ya ban-bare rigansa, yazo zai wuce ta sake shan gabansa, “yaufa bazaka fita agidan nan ba, yau saika kawo ma Beeba miji. Ya matsa tabisa yazo zai shiga d’aki ta tare qofar, sai ya tureta yazo fita ya iso zaure, tazo da gudu ta kama rigansa saida ta yaga. Ran Malam in yayi dubu ya b’aci bai san lokacin da ya kikifa mata mari ba, ya hankad’ata ta fad’i akasa. Yace”Hauwa hassadakin bazaikai ki ko ina ba, wannan aure matsawan in ima raye ba fashi, sai dai ki mutu da bakin ciki. Ya juya ya nufi d’aki ya canza kaya, yazo ya wuceta, har ya fita ya dawo yace”kuma wallahi in kika kuskura kika tab’a Khadija, a bakin aurenki saki zan miki ba dawowa, kina dukanta kin san sauran, Yasa kai ya fita. Gwaggo abun duniya ya isheta, tabbas Malam tun da ya rantse sai ya aikata, jiki ba kwari ta koma d’aki tafara kuka, cikin zuciyarta ko cewa take”wanna mari ba zai sha banza ba tunda yace karna daketa, to ae dole tayi aikin gida, dan haka ba duka akwai zagi da wahala yankuma. Khadi tana d’aki kwace, tana group chatt da kwayenta, wanda suka had’u a WhatsApp ta lura suna da hankali, shiyasa nasu yazi d’aya. A group d’in Khaleesat Haiydar suka had’u na Facebook dake Khadi mayar karatun novel ne. 
.
Hiran Novel d’in KAINE SIRRI NA littafin Aisha Muh’od, Queen Neenah tace” Khadeejat kin karanta KAINE SIRRI NA? khadi tace”eh ina karantawa kai, gaskiya novel d’in ya had’u. Farhat B Haske tace” Queen Neenah n Khadeejat kun karanta MARTABA TA da MATAR MUTUM na Mrs Umar Soja kuwa?. Sukace “a’a bamu karanta ba. “Lalle an barku a baya ni harna gama karantawa, yanzu ina karanta YAR WAYE NE?.na Khairat S Panisau, da KUDAN ZUMA na Zee Hrt. Suka had’a baki tare da cewa”Farhat littafin ya had’u ne?. “Eh kai ana rikici kam, ku tamabi. Hajiya Jamila Aliyu Haiydar tana dashi sai ta tura muku. Queen tace”Khady bari na nemomana zan tura miki ina samu. Khady tace”ok amma fa nagode. Farhat B Haske tace”gaskiya ya kamata yanda muka saba musan juna, gashi mun shaku sosai, ae zumuncin bai kamata ya tsaya a chatt ba. Queen Neena tace” ae fa gaskiya kam, yanzu musa rana sai mu fara zuwa gidansu Khady. “Ko ya kuka gani yan’uwa?. 
.
Duka suka turo da haka za’ayi. Khadi taji dad’i amma tana tunanin yanda zasu zo Gwaggo zata iya cin musu mutunci. Salama sukayi akan ran Friday za’a had’u, a gidan Hajiya Jamila Aliyu Haiydar sai su taho. Gwaggo tana gama sake-sakenata tafito ta kwala ma Khady kira, “fito dan ubanki, mai fiska kaman na biri, kin lashe wa mijina zuciya kin rabani da yata, gashi kin samu d’an mutane, kinsa yayi sata sun kawo kud’in aure ko?. “To ni kam dai ahir d’inki. “Kurwata kur bazaki iya ci ba. “Ko uwarki ma haka tagaji ta barni don nafi k’arfinku. Nan take idon Khadi yaciko da kwalla. 
.
Gwaggo ta tattaro wanke-wanke ta tara mata, tashiga d’aki ta d’ebo kaya harda wankaku, duk ta had’a mata. “Maza-maza kiyi ki gama su yanzu, ki kuma tabbatar an girkan abicin kar yayi dare. “Kin san halina basai an fad’a maki ba aha. “Ni ce Gwaggo Munguwa No1, in kika kuskure min a aiki sai na miki ba dad’i, tsohuwar mayya kawai. “Mai son raba aure, amma kuma bazaki iya ba sai dai a fasa naki. “Kuma ina kan bincike duk randa na gano gidan saurayinki, sai naje na had’a duk wata manakisa ta, an fasa auren. Niko Rash”nace Gwaggo rashin sani yafi dare duhu, da kimsan Umar d’an waye da baki fara masa rashin mutunci ba, don yafi k’arfin raini. Khadi ta dunkufa aiki baji ba gani, duk da ta gaji amma bata son ta nuna bare Gwaggo ta zagi iyayenta, don yafi komai cin mata rai.   Aiki sosai tayi, Gwaggo tana fita makwabta, Beeba ta fito tafara tayata aiki, Khadi tace”Beeba da kin bari nayi, yanzu in Gwaggo tazo ta samemu, ni zata zaga uwa ta uba. 
.
Beeba tace”karki damu Adda yanzu zamu gama aikin, Rabee’a ta fito sai mika takeyi, alamar daga bacci ta tashi, kitchen ta wuce ta duna tukunya, taga an kusa gama abinci, kwano ta d’auko ta d’iba. Beeba tace”Rabee wani irin iskanci kikeyi ne, kina kalo muna aiki amma kizo ki d’ibi abinci?. Baki ta murgud’amusu, Khadi tace”kyaketa Beeba, kinsan Gwaggo na dawowa saita huce a kaina. Aiki sukayi cikin ikon Allah dake, duna da zafin nama basu dad’e ba suka gama. Khadi ta raba musu abin ci suka ci, Gwaggi na dawoa tayi mamakin yanda Khadi ta gama aiki da wuri, d’aki tashiga kwano ta fito da shi, ta turo ma Khadi ga wannan masaran kina gama cin abimci ki surfa min shi, don yau surfen hannu nake so bana inji ba. Cikin girmamawa tace”to Gwaggo”. A gajiye tayi surfe ta gama ta wanke ta shanya shi. Yau takama jumma’a yau ne su Hajiya jamila da Queen Neenah zasu zo, yan kud’in da ke Hannuta ta had’a ta siyo kaya ita da Beeba sukayi girki. Ware dubu biyu zata basu kud’in Napep, ta gyara ko ina sukayi wanka ita da Beebah, sunyi kyau sosai. Gwaggo na ganin Khadi ta fito tace”mayya inda kinga fiskanki da bazaki na yawo cikin mutane ba.
.
Rabee ta mata kalon sama da kasa, sa’a d’aya Gwaggo bata sasu aiki ba. Sai kusan karfe biyar, su Farhat suka kira waya, Khadi ta d’auka da “sallamanta kun isone?. Farhat tace”eh! Gamu a dai-dai gun fire servise”. “Ok gani zuwa”. Ita da Beeba suka fita, suna zuwa kuwata gansu, da murna suka tari juna, farhat tace”ikon Allah yau Allah yayi zamu gana. “Eh wallahi sannu ku da zuwa. Su hajiya Jamila tace”wanna itace Beeba ko?. Khadi ta amsa da”eh! Itace, har kin ganeta. Suna hira suka shigo da sallama. Gwaggo ta musu kalon sama da kasa, Khadi ko sai addu’a takeyi, d’akin suka kai su. “Gwaggo ta kwala ma Khadi kira” ta amsa da “na’am gani zuwa”. “Kee dan uwarki ina kika samu wayan nan?. Ko maitan ki ya dawo har gida kike lashe mutane?. “Kiyi hak’uri Gwaggo kawaye nane fa”. “Eyeh har wani daman kawaye kika samu”.  “To yau zaku ci ubanku daga ke har kawaye”. “Dan Allah Gwaggo kiyi hak’uri ki bari in sun tafi kimin duk abunda kikeso”. 
.
“Kee ko uwarki bazata ban doka nabiba, bare kee yar karamar kwaro”. “Assalamu’alaikum Malam yayi sallama”. “Khadi ta amsa” Yana daga qofar d’akinsa yace”Khadejatu! ” Ta amsa da “na’am Baba”. “Maza kizo nan” Gwaggo cikin takaici ta ja tsuka. Sam bata so haka ba, taso saita wulakanta Khadi Malam ya dawo. Da sauri Khadi ta nufi gun Malam, da sallama tashiga d’akin, tsugunawa tayi tace”sannu da dawowa Baba” Cikin fara’a ya amsa da”yauwa d’iyata, naji dad’in ganin ki, a cikin wannan yanayi” “Ya jinin yau fatan lafiya ko?. “Eh! Lafiya lau, ga kwayena ma sun zi gaida mu yau”. “Ah madalla mun gode, in zasu tafi ki fad’amin”. “To baba” Da Murna tayi d’akin ta nan tayi sannu nasu Hajiya Jamila, Beeba ko har tayi serving d’insu. “Tace muje ku gaida Baba na” dukansu suka mike har qofar d’akin Malam sukaje suka gaida shi, ya sanya musu Albarka. Gwaggo ma tafito daga d’aki duka k’ara gaidata. A dakile ta amsa, suka koma d’akin Khadi, hira sosai sikayi, kafin suka mike zasu tafi don magriba yayi. Ta d’ibi kayan kwaliya, da sabulai, acikin wanda Dr Umar ya kawo mata, da turaruka tasamusu a laida. Sun fito Malam ya kirata yace”ga wanna kibasu su hau adai-daita. Ta karba ta “sukuma sukayi godiya”. Har bakin titi suka rako su ta mika musu tare da musu alkawarin zata zo ita da Beeba. Bayan kwana biyu Khadi na zaman hak’uri, kulum da kalan horon, da Gwaggo ke mata. Ana haka kwanwar Gwaggo da yaranta suka zo mata kwana biyu, kulum cikin kunci da matsi take, itaji sanyi to tana tare da Malam ko Beeba ko Dr Umar.     
.
.
Gwaggo ta buga k’irji tace”nashiga uku, anya kuwa ba Khadi mu bane. Matar tace”nan gidan mana”. Innna Yalwa tace”sannuku da zuwa ga gurin zama”. Cike da fara’a suka k’ara shigowa. Nan fa aka shigo da akwatuna, ko da aka shin fud’a taburma, hmm akwatuna bazai yiwu a bazasu, a tsakar gidan ba. Inna Yalwa tace”yan’uwa yana da kyau, kafin mu fara bud’e kaya, muyi addu’a Allah ya sanya alkairi, ya kad’e fitin-tinun dake ciki, ya kuma kawar da idon mahassada da makiya, dazasu kawo farmaki ma auren nan. Gwaggo tace”kee Yalwa wa zaiyi hassda ko makiyi nasan dani kikeyi, nan Gwaggo ta fara kwala, ko ta kanta basu bi ba, sukayi addu’a aka fara bud’e kaya. Yasalam masu karatu karkuso kuga kayan yawanci ready made ne, ga tsada, ko da ka zo kan takalma duk gulma na, na kasa k’irga yawansu, jakukuna da poss ba’a magana. Ko da aka bud’e na d’ankunaye hmm gwala-gwalai da fashion masu tsada, ga manyan balguls ba a cewa komai, can idona ya kyalo wani karamar a kwati acikin kayan, da sauri Inna yalwa ta d’auko, tayi-tayi ta bud’e amma ta kasa, wannan matar ne tace”kawo ki gani, tana tab’a qofar akwatin yafara k’ara sauti mai dad’i gashi da k’arfi.
.
Tana bud’ewa yace Hello My Master, cikin wata tausasashiyar murya na mata, kai ka d’auka a fili mutum yayi wannan maganan ba.  Wata mata da ke gefe, tace” a kula da wannan a kwatin, don White Gold ne a ciki, yana da matukar tsada sosai, kud’insa ya kai miliyan uku a kud’in 9ja. Inna Yalwa baki har kuni godia suka fara musu, sai suka d’auko d’an kayan da suka had’a musu suka mik’a. Inna Yalwa da dubu biyar a jikinta, ta k’ara musu yadawo 15k. San suki karb’a sai da su Inna Yalwa sukace”ko kun rainane?. Da fara’a sukace”a’a Allah ya sanya alkairi, wane mu da raina kyautan da zata fito, daga gidan surkan Gwamna, matar d’ansa d’aya tilo. Inna Yalwa cikin rashin fahimta tace” umm Hajiya bam gane kince Surkar Gwamna ba?. Matar tace” eh ko bakusan cewa Umar shine d’an Gwamna d’a d’aya tilo na miji. Inna Yalwa tace”sam bamu sani ba ya ma b’oye mana ko shi waye”. Take matar ta war-ware musu, aikafin ta rufe baki. Gwaggo tasaka ihu ta hau tsakiyar kayan tana watsi da su, tana cewa” wanna fa k’arya ne d’an yankan kai ne, Hajiya Suwaiba k’anwar Adam Naira cike da mamaki, tace”lalle tabbas yau naga halinki da’ake fad’a. “Bari kiji ga kayan Lhadijat nan abu d’aya ya bata sai mun miki rashin mutunci, kisani duk wanda zakana masa hassada da bak’in ciki, Allah kan masa sakayya, mugunta da kike mata ne Allah ta bata. Gwaggo tayi kanta zata cakumeta wani security ya kaimata naushi ta fad’i a kasa. Hajiya Siwaiba tace”ae da ka barta da yau na koya mata hankali, ni ba irin matan da suke d’aukan wargi bane. “Mtsss bamza sakarya marar imani. “Khadijat takusa hutawa da muguntanki. Gwaggo na ihu kamar mahaukaciya, tana cewa”sai kun kawo na Beeba da Rabee’ in ba haka ba zamana lafiya. Gwaggo hauka tuburan Inna Yalwa ta kali K’anwar Gwaggo tace”da fa kin kama yar’uwanki kartayi tsirara, tsabam bak’in ciki. Da kyar aka shigar da Gwaggo d’aki aka kule ta. Malam da yadawo, ko da yaji labari, Hamdalah yayi, ya k’ara gode ma Allah, tabbas Khadijat ta samu miji, don yana jin labarin halin d’an Gwamna. Kayan yasa ka aka d’eba a gidan aka kai gidan Inna Yalwa da daddare, ba wanda yasani, motar kuwa ya kai gun wasu masu ajiye mota aka ajiye masa. Yan’unguwa ko ina ka leka sai zance akeyi, wasu ko so suke su ga Khadi matar d’an Gwamna. Gwaggo tana d’aki sai zage-zage take, Beeba ko murna ba’a magana.  
.
A gidan su Dr Umar kuwa, sun gama had’a lefe nagani na fad’a, lefen nun ma sa’a. Cikin kayan harda key d’in mota, k’irar Honda CRV, Mum d’insa ta saka masa, Dr Umar shima ya karo wasu kaya aka saka, masu karatu kar kuso kuga kayan akwatina ma Set hud’u akasa, zannuwa kuwa ba kananu. Hmmm kayan d’an Gwamna d’aya tilo aidole ya zama abun kalo, Mum tace”Umar ka sanar da Khadijat jibi za’a kai kaya. Cikin murna ya shirya sai da ya je Store ya mata sayya, ya nufi gidan, bai wani b’ata likaciba ta fito. Sai da sukayi hiransu yace mata”My Khady!”. Cikin sanyin murya ta amsa da “na’am”. “Khadijat! Duk wani farin ciki na kene, ina matuk’ar qaunanki. “Alhamdulilah! Allah ya amsa min addu’a ta, na bani ke amatsayin mata. “Ki sanar da mutanen gida, In Allah ya kaimu jibi za’a kawo kayan lefe. Cikin jin kunya ta saki murmushi, tare da rufe fuskanta da tafin hannun ta. Hira sukayi mai cike da so da qauna, sai dab magriba, ya mata sallama ya tafi. Khady na shiga gida ko da Malam ya dawo, bayan ta masa sannu da dawowa, ta sanar masa da sak’on Dr Umar. Cikin farinciki ya yi musu addu’a. Washegari Malam ya aika ma dangin Mahaifiyar Khady, dangin Uba ya sanar ma wayanda yakama ta su zo karban kaya.  Malam ya sayo kayan karban bak’i, harda yan kajin sa, guda biyar ya tura kasuwan kauye, aka sayo masa.
.
Ya sayo multina da lakacera, kaya iya na talaka, Baba Yalwa k’anwan Maman Khadi su suka soya kaji, pepper meet sukayi, yayi kyau ko ina sai kamshi yakeyi. Gwaggo in banda harare-harare ba abinda takeyi, ko hannu bata samusu a aiki ba, karfe uku sun gama komai sun gyara ko ina sai kamshi yakeyi. Malam yaje ya d’an had’a kud’in da zai had’a na kasan akwati, ganin karamci irin na Umar ya samo dubu goma yaba ma Inna Yalwa yace a basu. Khady ko tayi wanka cikin kayan ta masu kyau, suka zauna a d’aki ita da Beebah don basa son yawo. Rabee’atu kuwa tana kusa da Gwaggo, sai lashe baki takeyi, don tunda taga ana soya kaji, yawunta ya kai. Su Inna Yalwa wanka sukayi, suka saka kayan su, mai kyau, suna zaman jiran baki. A gidan su Dr Umar kuwa, Mum kwanta ta kira da matan Baba Liman, sai Kwanwar Baban su Umar, bata tara mutane ba, sabida tasan yanayin gidan su Khady, kar suje su musu ba dai-dai ba. Milasalin karfe hud’u da rabi, suka d’au hanyan. Misalin karge biyar, cikin unguwansu Khady, ya d’au jiniya, motoci ne sukayi jerin Gwano ga securitys a motoci sun sanya sauran motan a tsakiya, suna shigowa take suka fir-fito dan gani mai zai faru. Motocin qofar gidan su Khady suka tsaya. Gwaggo dake d’aki taji jiniya mota, tace”ko lafiya naji karan motar yan sanda?. Rabee tace”ai inaga wanda suka daki Adda Khady ne suka dawo dukanta hala. “Don ranan da irin wannan suka zo. Gwaggi tace”Allah yasa sune, su dakata inga ta inda za’ayi auren. “Zo mu fita muga ya zasu kare. Suna fitowa dai-dai lokacin yan sanda suka shigo gidan da bindigansu, Gwaggo sai zare ido take. ana haka suka ga wasu Mata cikin shiga ta alfarma sun shigo. Gwaggo tace”lafiya dai naga kuna shigo mana gida?. Wata mata mai yar kiba tace”nan ne gidansu Khadijat?. Gwaggo tace”eh! Nan ne. “Lafiya dai?. “Lafiya klau, kafin tayi wani magana ansoma shigo da akwatuna. Gwaggi tace”wanna fa?. Matar tace”kayan Khadijat muka kawi”. Gwaggo ta buga k’irji tare da zaro ido. Nima Rash sai da wayata ta subuce don na tsirata da ganin yanayin Gwaggo. 
.
  Hajiya Suwaiba suna komawa, suka sanar da Mum d’in Umar yanda sukayi, tayi mamaki sosai ashe da gaske haka halin Gwaggo yake. Nan tace” hmm ni gwanda His Excellency ma ya dawo ayi bikin, yarinya ta huta. Hajiya Suwaiba tace”yaushe zai dawo? Mum tace” nan da 5days zai dawo. Hira sukayi tayi da yanda biki zai kasance. Gwaggi ko ta hana su Malam bacci sai ihu take, ko sallah anki bud’eta tayi. Khadi tayi murna tayi godia ma Allah da zab’in da ya mata, take ta kira su Farhat B Haske ta fad’a mata, Farhat ma take bata labarin tayi sabon saurayi, Sunansa Abdul-wasilu Humble, Khadi ta mata fatan Allah ya dai-daita su. Tana kashe wayar ta kira Queen Neenah ita ta fad’a mata, daga nan takira Hajiya Jamila Abubukar ta sanar mata, tayi murna sosai da sosai, takuma bata shawarwari da yanda zata kula da Umar kasancewa Hajiya Jamila ta girmesu, tana kwance dasune don taga suna da hankali shiyasa. Malam ganin iskanci Gwaggo zai wuce gona da iri, da safe yaje ta windoq duk ta wargaza d’akinta, yace”Hauwa ki nutsu, wallahi kinji na rantse, matsawan baki bar haukan da kike ba to yau zan rubuta miki saki, don ba za’azo biki ina matsayina na Surkin Gwamna a ga mahaukaciya a gidana ba, kuma haukanta akan bakincin take ma Surkan Gwamna. Ni Rash nace”hmmm Malam da biyu yayi maganan nan, don ya kuna Gwaggo ne. Gwaggo tace” eh dole kace haka ae dama baka sona don yanzu kaga Khadi zata auri d’an Gwamna dole kamin haka. Malam yace” kene bazaki gane ba ina sonki sosai, halinki ne bana so, ya fita abunsa. Gwaggo jin saki ta nutsu ko da tafito, jummai k’anwarta tayi mata nasiha tace”Yaya matsawan baki kwantar da kai ba, ina fad’a miki zaki wahala don yarinyan nan tayi gaba. Kiyi hak’uri kawao. Gwaggo tundafa wannan rana ta dawo kamar bata gidan yanzu bata dai magana da Khadi, amma ta bar hantaranta ko sabganta tabar shiga. Khadi ko kulum suna mak’ale da waya ita da Umar, suna waya ne yace”gobe Dad zai dawo ki shirya, in ya dawo ke da Beebah zakuzo ku gaidashi. Cike da murna tace”sai mun tambayi Baba in ya barmu. “Kedai nasan Baba bazai hana kizo ki gaida Surkinki ba. Haka sukayita hiransu mai cike da ni shad’i. Washe gari da safe inna ta d’aura ruwa a hita, dai-dai kusa da d’akinta a kwai soket, ya tafasa ruwan ta kashe, taje d’auko boket kenan ta sukuya tana d’aurayewa, sai tebur d’in ya karye yana shirin zubowa akan Gwaggo. Khadi tafito da ga d’aki karaf idonta ya sauka akan tebur, “kira ta kwala ma Gwaggo, ganin bata gane mai take nufi ba, da sauri tayi gun don ceton Gwaggo. Tana zuwa ta ture Gwaggo ta hantsula gefe kagin ta kauce ruwan ya juye mata ajiki, wani razanane k’ara tasaki, ta fad’i agun tana shure-shure. 
.
Gwaggo duk ta rikice, Beeba da Rabee sai Jimmai kanwar Gwaggo suma ihu suka saki, ana haka sai ga Mal da gudu yayi kan Khadi, wanda azaba yasa ta suma, d’aukarta yayi waje yafita da gudu yashiga Napep, Gwaggo ma da gudu duka bisa, Beeba kam sai kuka take, tana fad’i”wayyo Adda na!. Gwaggo sai hawaye takeyi, tabbas yau Khadi ta gwada mata yar halak ce ita, gashi taje ceton rayuwana itakuma zata rasa nata. Tabbas yau na yarda da kalman nan ta ‘YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU, bakan wanda zai tai makeka ba. Suna isa asibiti Dr Abdul suka samu gani halin da take ciki, akayi Emergency da ita, wayan Dr Umar yakira. Dr Umar suna Airport shida Mum da Ilham sunje d’auko Dad d’insu, don har jirginsu ya sauka, Dad ya sauko kenan, sun rungume juna, wayar Dr Umar tayi k’ara gani Dr Abdul yasa yad’aga da sauri “hello yace”. Daga d’aya ban garen Dr Abdul yace”kana ina, kazo ba lafiya Khadijat ta kone bansam ko garin yaya bane, amma ina zati ko Gwaggo nane ta konata sabida halinta. “What ina bazai yuba sai na d’au mataki. Mum tace”Kai da wa?. Cikin muryan kuka ya fara basu bayani, His Excellency yace” what muwuce Asubiti yau matan na zata gane ita bakomai bane. Suna zuwa Asibiti ta ko ina ya amsa da jiniya. Dr Umar da Gwamna da gudu suka fita duka shiga Emergency, Umar na ganin halin da Khadi ke ciki, kara ya saki ya fad’i sume. Mum da Ilham sai kuka suke, Gwamna ya fita kiran Doctors suka d’au Umar shima. Yana fitowa yaga su Malam yace”ina Gwaggo da take?. Malam ya nunata da yatsa, His Excellency da gudu yayi kanta wani damka ya mata, ya fara kwara mata kyawawan mari, yace”wallahi in har na rasa d’ana d’aya tilo, da abar qaunar sa, to kema sai kinyi mutuwar wula kanci. Kisani ‘DA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU.
.
amma ke munguwa nai bakin hali zaki gane kurenki. Ball yakeyi da ita, yana fad’an magan ganu, da kyar aka rik’e shi, sijoji yace atafi da ita CID agana mata azaba. Basu tsaya jiran komai ba Women police suka d’au Gwaggi sama aka sata a mota, aka nufi CID da ita. Ni ko Rash tsaban gulma ina leka motar naga bakin Gwaggo har ya kun bura, fiskan taji marin manya, tamkar ba Gwaggo mai bala’i ba.   Umar kuka yake ana haka har suka iso New Delhi, motane tazo ta d’aukesu har asibitin da za’a mata aiki, kasancewa a sanar musu, sun sanda suwansu, ana shiga da ita likitoci, suka hau bata taimak’on gagawa. Sun d’au awani suna mata surgery, Umar ya kasa zaune ya kasa tsaye, duka sun dun kufa sai addu’a sukeyi. cikin ikon Allah likitan ya fito cike da fara’a, hannu ya mika ma Gwamna, yace’ In Allah ya yarda musa tsamani komai normal” Hamdalah suka rayi, suna gun akazo aka wuce da ita zuwa d’akin da zasu ajeyeta. Khadi bata far-fad’o ba sai kusan 3:00am na dare, doctors aka kira duka dubata, Umat ko sai addu’a ke mata. Haka suka kasance cikin jinyan Khadi yau kusan watandu d’aya kuma yau ne za’a ware mata, bandage, doctor yace”suyi fatan Allah yasa aikin yayi nan aka shiga da ita, wani room don since mata, su Umar sai addu’a yakeyi. Awa d’aya ya d’aukesu, likita ya fito nan ya saida musu komai normal, zasu iya shiga su ganta, Umar da gudu yayi d’akin yana zuwa ya ganta kwance, suna had’a ido murmushi ya sakarmata, zuwa yayi ya rungumeta, ana haka su Malam suka shigo, sai da Dad yayi gyaran murya, tukun ya san sun shigo, cikin jin kunya ya koma gefe, sannu suka ringa mata. Tun daga wanna ranan Umar shike mata dressing d’in ciwonta, ya bata abinci abaki, ya mata alwala, da daddare kuwa kafin ta kwanta zai d’auko story book yana karanta mata, da joke masu dad’i tana dariya, har tayi baci, inyaga tayi nisa da bacci yazo ya ru gume matarsa haka rayuwansu, ya kasance gwanin dad’i.
.
Ganin Khadi ta warke suka fara ahirin dawo 9ja don ayi biki kowa ma ya huta. Gwaggo kam taci a zaba, in har kasanta ada kaganta yanzu bazaka ganeta ba, tayi baki sosai, gashi har hak’urinta sun zube, tsaban duka da wahala, sai daga baya ne, Beeba ta sanar ma Dr Abdul gaskiya, shima ya fad’a ma Baban Umar, sai da sukayi bincike suka tabbatar da gaskiyan al’amarin kafin aka saketa, randa tashiga unguwansu, matasa suka tashi zasu mata duka da kyar aka kwaceta, Gwaggo tayi nadama ba kad’an ba. Kulum cikin saloli take, tana addu’an Allah ya tashi kafad’un Khadi. Yau jirgin su Khadi ya sauka 9ja, Umar ko sai wani rawan kai yakeyi, ko kunyasu Dad baiji, sai yawani rok’o hannuta, sai da Mum ta zo ta rik’e hannu yarta, Mum tace”Malam za’aban aron yata, zan tafi da ita kafin biki. Yace”bakomai ae Khadi takune. Suna isa gida ta kira Hajiya Suwaiba da Ameena tace”ga yata nan kuje a gyara min ita, banson Umar ma ya ganta sai biki. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment