Sunday, 10 December 2017

'Yar Boko Part 6 (THE END) Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YAR BOKO part 6 (THE END)
.
 A bangaren nasmal hankalinshi kwance,kullum jin so d kaunar matarshi yakeji yana shiga jini d tsokarshi,  Anan gida nyja abin dunia y ishi neenerh duk d tanasan mijinta amma dole y auri nanah Dan samun kwanciyar hnklinta d nutsuwa,  Akwana atashi b wuya neenerh an gama PhD,t samu aiki ,dawowar nasmal yayi daidai d 3yrs  anniversay n kamfanin shi mai suna *nasneer*  Awannan lokaci y baiwa neenerh matsayin director t kamfanin,sanadin haka yasa tai resigning daga wancan aikin,da kyar neenerh t lallabashi y amince d batun auren nanah badan ransa yasoba,sai d suka kai ruwa rana  Momy dadi tamkar y karta,shirye shirye suka shigayi haikan ,Adan kankanin lokaci suka hattama komai,tare d tsaida ranar biki  Abangaren neenerh d nasmal.kuwa sun yanke shawarar zuwa a cire mata inplant da aka sanya mata Dan hana daukan ciki.  Iko sai rabbana,aikuwa a watan d t cire,t samu ciki,murna gun ma'auratan har sujjada sukai Dan nuna gdyarsu g Allahu subhanahu wata ala.
.
 Cikin y xo mata d matsanancin laulayi ,ko abinci saita daure take iyaci,kullum nasmal n kusa d ita,danganin tasami saukin halin datake ciki,tare d bata magungunan d doctor yai prescribing akan lokaci,  Akwana atashi b wuya,duk abinda akasa mai rana sai yazo,yaune zaafara shagalin bikin nanah d nasmal  Abarin amarya dad'i tamkar t yanke kunnuwanta,Ango kuwa b yabo b fallasa,y sanar d ita cewa bazai samu damar halartar taron bikin,  Duk yanda mom taso t tankwarashi Abu y gagara,haka suka hakura,sukasha bidiri b ango  A t kama asabar , Murna gun amarya tamkar t kai kanta gidan angonta,karfe hudu t gama shiri tsaf tare d feshe jikiinta d da d'ad'an turaruka masu daukan hankali  Dakin auntynta t nufa,tare d cewa aunty n gama shiri,yaushe zamu tafine kar yamma tayi,(iko sai rabbana koni ayusha dake zaune agefe nace ko yan boko basuyi rashin kunyar d karamin Sani k'uk'umi sukeyiba)  Tare d friends dinta d auntynta suka nufi gidan ango danyi mata rakiya,  batare d jiran y'an zuwa daukan amaryaba,  Part din nanah suka zarce ,suna habaice habaice tare d wake wake,speakers din palon suka ware suka dinga tikar rawa harda amarya tamkar a gidan rawa b gidan aureba,mai karatu kuwa sai yace ikon Allah sai kallo,amaryar bahaushe d aka sanya d kumshe kai,harsai an sai baki kanta bude fuska,ko *yar boko*batai wannan fetsarancin ba.  Itakuwa neenerh n part dinta tana murk'ususun ciwo,wayanta t dauka t kira nasmal tare d sanar dashi halin d take ciki,  A sukwane yataho tamkar Wanda zai tashi sama,ganin halin d take ciki y sukunceta sai asibitin get well dake unguwar red bricks  Ankarbesu cikin gaggawa ganin halin d neenerh keciki,tare d umartarsa y sa hannu Dan ayimata C.S, alamu sun nuna bazata iya haihuwa d kantaba,  Within some minutes aka shiga da ita dakin tiyata,cikin ikon Allah akasamu nasarar futo mata d jarirai guda biyu duka maza.  Shidai nasmal n zaune a reception,b abinda yake sai adduar,Allah yasa ayi mata cikin Sa'a.  Nurse Ce t futo cikin faraa tace Kaine mijin patient din d aka shiga d ita operation ?yace e, Tace ana bukatar kayayyakin t ,sai a lokacin y tuna Ashe basu taho d komaiba  Hakuri y baiwa nurse din,ya tanbayeta angama ne? Murmushi tayi tare d cewa e ,ansamu tagwaye samari  B karamin farinciki nasmal y tsinci Kansa a cikiba ,murmushi ne y subuce masa, tare d daga hannu yayiwa ubangiji gdya  Gida y nufa,b tare d yabi takan nanah ba,straight bangaren neenerh y shige yadauko jakar kayayyaki yafuto y Kulle bangaren,Dan adazu y manta d wani batu wai rufe gida  Lokacin d y isa asibitin anrigada an gama gyara neenerh d jariranta,kallonsu kawai takeyi,take rayawa a ranata,in ba Allah b waye zaima kyautar ya'y'a har su biyu lokaci daya,  Abinda y bata mmki ,ganin baby d'aya yayi kama d ita,haka zalika d'ayan kuma mai kama d nasmal,lallai Allah shine mai halitta,buwayi gagara misali,Haiti kaga kamarka.
.
 Nurse Ce t kwashi jariran Dan kaima nasmal ,y daukesu tare d yi musu adduo'in d annabin Rahma yaimana horo d yiwa yaran mu d zarar sun iso duniya.  Dubu biyar y baiwa nurse amatsayin tukwici ,aikuwa saboda murna batasan lokacin datai gud'a tare d rawa ba,t kara d cewa wanga jarirai Allah y muku albarka y sa ku zamto shu gabanninmu,Allah yasa ku yi riko d adalci d addini d kuma dabiar kyauta iron t babanku,lol.
.
  Duk wannan Abu d ke wakana ,hanklinshi n kan halin d wifey dinshi ke ciki,addu'arshi d'aya Allah y kara mata lfy y tashe t cikin koshin lfy.  Nurse dince t Sanar d shi cewa zai iya shiga y ganta,rungume d jariran a kafad'arshi y shiga,bacci mai nauyine y dauketa,fuskar nan tayi fiyau,  Shimfid'e jariran yayi a gadan dake gefenta,y karaso kusa d ita,gashinta y shiga shafawa,tare d yi mata kiss a goshi d kuncinta,ahankali y furta love u alwaix my lyf.  Sai a wannan lokacin ya dau waya y sanar d mutan gidansu d Nasu neenerh,kan wani lokaci asibitin y cika d yan uwa d abokan arziki kowa n tayasu murnar samun twince. 
.
A bangaren Nanah kuwa t cika tayi bam,abin duniya y isheta,kukane y subuce mata,n takaici,yitayi tayi tamkar jiniya,  Duk burin dataci a wannan dare amma b ango b dalilinsa har misalin karfe 4 na dare,yanda taga rana haka taga dare,  Misalin karfe 12 aka sallamosu,gidan nasmal suka nufo,jin karar dirar motoci yasa nanah lekowa t window danganin abindake faruwa,hango neenerh d wasu wadanda batasansuba,rike d Abu kamar jarirai a hannu,  Azuciyarta tace Allah Dai yasa b jariran neenerh bane,sabida taci alwashin salwantar d cikin ko hakan zai yi sanadin mutuwar neenerh(wa iyya zubillah ,Allah k shiryemu d shiryawarka)  Bangaren neenerh sai bidiri ake,baki t ko ina barkowa sukeyi Dan taya murna,jarirai gwanin ban shaawa lafiyayyu  Sai awannan lokacin nasmal y tuna d wata aba wai  nanah,d sallama y shiga bangarenta,tana kwance akan 3seater tana kallon tashar *Arewa 24*ganin shi y shigo kamar daga sama yasata ta mike t nufeshi Dan yi mishi oyoyo  Zamewa yayi y koma gefe,saboda wani Abu d yaji y ziyarci hancinsa mai kama d hamami daurewa yayi suka gaisa,Allah Allah yakeyi y bar dakin  Y tanbayeta akwai wani Abu datake bukata ? Tace a'a akwai komai,nan y Sanar d ita haihuwar neenerh tare d umartarta taje tayi mata barka,sanin halin nasmal yasata amsa d to badan ranta yasoba,  Mayafi t dauka t nufi bangaren neenerh uwargida t tadda wajen acike d jama'a,b sallama tasa kai tashiga,duk suka bita d ido,mamakine y cika musu xuciyarsu  Ai d'an musulmi dai zai Shiga guri ai y kamata ya Shiga d sallama,neenerh kadai tayiwa mgana tace Ashe ansamu karuwa?neenerh tace e sistr,t kara d cewa Allah y raya? neenerh tace amin.sim sim sim t fuce daga sashen. 
.
Futarta keda wuya wad'anda ke d'akin suka bikaci Sanin wacece nan? neenerh t Sanar dasu,cewa abokiyar zamantace,Allah wadai sukai d irin tarbiyyarta,(Ni ayusha dake gefe nace ana gudun *yan boko* ana cewa basu d tarbiyyar Ashe rashin tarbiyya naga wadanda basuyi bokon ba)   Kullum gidan nasmal acike,ranar suna anyi taro n gani n fada ,anyi publishing a magazines saboda haduwar taron,mai jego tasha gayu tare d jariranta ,anci ansha,an bada gifts kalakala,k'arshe taro y kare San barka cikin farinciki,jarirai sunci sunan dadyn nasmal d dadyn neenerh,neenerh t samu kaya tama rasa yanda zatai dasu,daki guda t ware n danfare kayan tamkar bada kudi ake saya ba,kowana bangaren so yake ace y burge,wato Barin mahaifin neenerh Dana nasmal,saboda takwara d akaiwa y'an uwan su.  A bangaren nanah,batasamu yanda takesoba sai bayan suna d kwana biyu,wani dare ta dau wanka,t sanya rigar bacci wadda d ita d babu duk daya,t shafe jikinta d mayuka d turaruka iri-iri,karshe t d'auko turaren d auntynta t bata t shafa,duk namijin da ya shaki k'amshin turaren xaiji hankalinshi y tashi ,dole y bukaci mace a wannan lokaci,sannan t k'arayin matsi d wani daban d aunty dinnata t bata .  Isarta bangaren nasmal tayi knocking door din dakin,abinka d gwauro yana kwance agado y bararraje y zurfafa cikin dogon nazari tare d tunanin rayuwa,jin shiri ba'ai mgnaba t Tura kofar dakinta Shiga batare d  sallamaba, tamkar b diyar musulmiba,  Baisan t shigo dakin ba balle yayi yunk'urin motsawa,sannu a hnkli t isa kan gadan,k'amshin turaren tane y doki hancinsa,Wanda y hargitsamai tunani,take idanuwanshi suka kad'a,tare d bukatar san kasancewa d diya mace,( tarkon data d'ana mishi y kamashi)  A hankali  ta kwanta akan faffadaan kirjinsa,tare d shasshafamai gashin kirji ,Wanda y taimaka wajen kara daga mai hankali.
.
 Hankalin maza y tashi,take y jawota kirjinsa y Shiga sarrafata yanda yakeso,batare d wani tinaniba,dadi agun nanah baya misaltuwa,dankuwa t Dade tana d burin samun wannan dama,karshe y biya bukatarshi,jinsa y shige sululuf,ya Shiga duniyar dadi ya Lula sama y dawo Kasan dadi, bayan d bukatarshi t biya,take y dawo taitayinsa amma ina nanah t k'ank'ameshi ta k'i sakinsa saboda jin dadin data tsinci kanta ciki  A hankali y bude idanuwanshi,nan yayi toxali d nanah bararraje akan gadanshi ,shikuma yana kanta,a firgice y d'agata,yana Mirza idanu,sai a lokacin y gane abinda y wakana,bakinciki d takaicine y lullubeshi tare d dana sanin Barin kofar dakinsa abude,wata tsanarta yakaraji a zuciyanshi,cikin karaji yace get out,sai ta maida kai ta kwanta batare d niyyar tashi ba,cikin k'araji y kuma cewa bazaki b'acemin d ganiba,nayi danasanin aurenki nanah Ashe dama abinda nake zargi akanki haka yake,kin gama zubda mutuncinki a titi,to ki tafi gida Ni nasmal n sakeki saki daya in kin samu miji kiyi aure,kuka t fashe da ,tana rok'arshi Allah annabi yayi hakuri y maida ita,amma inna fuxgota yayi tare d cillota wajen d'akinsa,y maida kofa y rufe cikin bakincikin abinda y wakana tamkar a mafarki  Ayau ya San bak'aramar ni'ima ubangiji yayi masa n mallaka mai neenerh amatsayin matarshi uwar y'ay'ansa,duk d zurfaffan ilimi datai hakan baisa t sarayar da mutuncinta a titi ba,addua y shigayi Allah y barsu tare cikin so d kauna,Allah kuma yasa mutuwace zata rabasu,(Ni ayusha dake gefe na amsa d amin). 
.
Na tsara wannan littafi mai suna *yar boko* Dan nusar d alumma cewa, in ance *yar boko* b wai hakanna nufin yarinya Mara kamun kaiba ko Mara kunya, *yar boko* macece data Tara duk wani Abu d akeso mace t mallaka Dan a aureta, *yar boko* ko *yan boko* d yawa sunfi wad'anda basuyi bokon ilimi d hakuri d Sanin ya kamata  Idan muka duba rayuwarmu baki daya zamuga cewa kallon d akeyiwa *yar boko* ada yanxu y canja , *yar boko* bawai yana nufin mai girmankai ba,ko wulakanta mutane.  *yar bokon*wannan zamanin d addinin musulunci y yadu a duniya,tasha banban d *yar boko* azamanin jahiliyya period. - ISMAIL SANI
.
.
Dan samun chi gaba dama wasu to shiga nan
http://www.hausanovels.tk/
http://www.ismailsani.ga/

0 comments:

Post a Comment