Saturday, 30 December 2017

'Yar Jami'a Part 6 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YAR JAMI'A 006 .

Ina so kisan wani abu baba mak'asudin zuwan mu gidan nan ba don komai bane illah mu nema wa tsoho lafiya,babu yadda za'ai muna ji muna gani mu kai shi inda zai wahala,tunda mu musulmai ne,bisani ma wannan jikarsa ce,maganar asibiti kuma da kika baba shekara nawa kuna zaune gida ana yin na hausa,wane sassak'e da mad'acin ne ba'a bashi yasha ba?ina ce duk an gwada amma jikin jiya i yau,kinga kuwa bazamu zuba ido ace haka za'a barshi cikin wahala ba dole a samu abin yi!kuma ina ganin son da zaki nuna wa tsoho shine ki barshi muje mu jarraba na baturen ko Allah yasa a dace! . . Jimm baba yagana ta d'an yi uwa mai nazarin wani abu kowa ita yake jiran jin abinda zai fito daga bakinta,kwatsam suka fara jin k'uhul...k'uhul...k'uhul....alamun k'arar tari na tasowa daga d'akin dake gefensu,cikin sauri baba yagana ta mik'e suka rufa mata baya sukai cikin d'akin! Kwance suka iske shi yana yunk'urin mik'ewa amma ba hali don wani matsanancin rawa da jikinsa ya soma va shiri sameer ya k'ara suka dashi bai jira cewar suba yadda yaga jikin tsoho na gyargyarwa ya sungume shi yayi yayi waje dashi,haka suka k'ara d'ungumowa gaba d'ayansu suka yo waje banda kuka da kururuwa babua binda baba yagana ke sumbud'awa" . . . Abakin k'ofar zaure ne suka ci karo da malam sale mai shago wanda kukan baba da ya jiyo yasashi shigowa ba shiri,ganin yadda aka fito da tsoho ranga-ranga yasa shi shima kwarma uban salati ya ja gefe ya tsaya,ba wanda ya iya bi ta kansa suka haura sukai waje,cikin aljihu sameer ya fiddo key ya mik'a wa beauty nan ta bud'e motar ,gidan baya sameer ya zauna shi da tsoho d'an ladi na k'ok'arin turo kai ciki ya dakatar dashi yace a'a ka zauna gida ka kula da baba yanzu zamu dawo,badan yaso ba haka d'an ladi ya ja gefe yayi turus! Juyawar da sameer zai yi ne kicib'is suka had'a ido da beauty dake gefen baba tsaye hannu rike da mukullin mota"cikin tsawa ya furta mata" ke dalla malama ki shiga ki drivern namu kikai tsaye akan mu kamar sanda,ba ta bi ta maganar saba duba da yadda jikin tsoho ta tsananta ta nufi driver seat da sauri ta shiga ta kunna motar,ta nufi asibitin dake k'auyen! Da idarsu asibitin waje beauty ta samu ta aje motar wanda har lokacin numfashin tsoho ya kasa dai-daito cikin sauri sameer a bud'e k'ofar ya d'akko tsoho suka fito beauty na take musu baya,cuncurundon jama'a kad'ai kake hangowa ta ko'ina acikin asibitin ga hayaniya na mutane duk inda ka juya mara lafiya ne zaune,abinka da ba'ai saba shiga waje haka ba kafin kace me duk sameer ya rikice ya rasa ina ma zai yi dashi,waje ya gano gefe da wata mata dake goye da yaro ba kowa cikin sauri ya isa wajen ya zaunar dashi juyowa yayi ya kalli beauty rai b'ace yace ki kula dashi ina zuwa kuma banda nuna hali!yana kai wa nan sameer ya sakai yayi gaba" sakayau beauty ta bishi da kallo fuska yamutse uwa mai shirin kuka ta shiga zancen zuci"toh wai shi wannan me ya d'auke ni akuya ko kuwa tunkiya da duk inda naje sai na bi maza?ba takai ga baiwa kanta ansa ba ta jiyo tarin tsoho ba shiri ta katse guntun tunaninta ta nufi wajensa ta na mai sannu! Bai wani jima da tafiya ba sameer sai gashi ya dawo gefensa wani matashi da alama likitane sai wasu samari suma dai cikin fararen kaya dake nuna jami'an lafiya ne,ko da suka k'araso samarin nan cikin sauri da nuna gogewar aiki haka suka janyo gado a wani d'aki dake gefe damu suka d'aura tsoho suka nufi can wani sashen na asibitin,biye muke binsu har suka isa wani b'angare da hayaniya ta tsagaita a wajen,office dake ciki suka nufa muna k'ok'arin biyo su ciki likitan dake biye damu ya d'ago musu hannu badan sunso ba dole yasa suka dakata anan! Waige sameer ya shiga yi ko ya samu wajen zama can ya hango wasu kujeru da basu wuce 4 a jere a k'arshe wajen ba take ya nufi wajen yazauna itako beauty ta shiga sintiri tana kai kawo a wajen! . . Har kimanin minti 30 babu alamar motsi ko fitowa daga ciki! gajiya beauty tayi da zagayen dole ta nemi gefen wata window dake nan ta jingina tana kallace-kallacen jama'ar waje! Can suka fara jiyo taku na tahowar mutum ido duk suka k'ura wa k'ofar sai gashi d'aya daga ciki samarin nan ya fito hannunsa d'auke da takarda!mik'ewa sameer yayi da sauri ya nufoshi inda itama beauty ta yo kansa tana fad'in dan Allah malama ya jikin nasa?bai iya tanka mata sai ma kallo da yakai ga sameer yace yallab'ai dr.ya rubuto allurai da ruwa da za'a siyo,karb'ar takardar sameer yayi k'ok'arin yi sai yaji yace dashi,a'a yallab'ai ai wannan aikin ba naka bane kadai bayar a siyo,lummm sameer ya d'anyi sai kuma can ya wuce gaba yace muje toh wajen! tafiya suka shiga yi har sun kai k'ofar barin wajen sameer kamar wanda yayi mantuwa ya juyo ya kallo beauty wacce itama dai su take kallo yace toh sai ki samu waje gashi can ki zauna a bar lek'en taga don babu abin gani kuma dai a kama kai don nan gidan HIV ne,yana kaiwa nan yasa kai ya fice abinsa!beauty dake tsaye hannu sak'ale da k'aramar jakarta bata ankara ba taji wasu zafafan hawaye sun fara kwaranyo mata a fuska wanda sam batasan dalilin hakan ba! . . Kusan minti biyar kenan da fitar su sai gasu sun shigo rik'e sa ledoji biyu,office d'in saurayin ya shige shi ko sameer ya dawo nan ya nemi waje ya zauna! Kawo lokacin beauty na zaune saman kujerar ta duk'e kai k'asa tana nazarin halin da tsoho ke ciki, Sallama har sau biyu sameer yayi amma ina beauty tayi nisa a tunani"wasu dai anyi asarar kud'in tara wallahi ace sallamar ma basu iya amsawa ba"furucin da beauty kenan ta tsinta daga sameer hakan ya tabbatar mata da sun dawo don haka ta d'ago kai tana kallonsa"kafin daga bisani ta saki doguwar tsuka had'e da tab'e baki ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya ta juya masa gyeya! Dariyar k'arfin hali sameer ya saki mai cike da tuhuma sannan ya furzar da wani zazzafan iska waje yace"Wato in aka ce dai akuya wallahi an gama da kai,don kuwa ita ko ina sai ta nuna halinta sai dai in bata samu waje ba! Bai kai ga sauke lumfashinsa ba kamar wacce aka mintsina beauty ta juyo a kufule ta shiga gyad'a masa hannu taba magana"kai malam shiru-shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne,ko dan kaga tun d'azu ina raga maka shiyasa kake ganin kai ka isa,toh wallahi ina yi maka kashedi na k'arshe ka fita a harkata tun kafin na nuna maka kaina a zahiri" A razane sameer ya mik'e tsaye ya dafe k'irje had'e da fad'in wa iyazu billahi yanzu banda wannan munanan ayyukan da kika shahara dau kina so kice min har akwai wasu na xahiri?ehh toh lallai ke tashin shuri ce don daga gani bade rainon mutim basai dai aljani! . Ganin yadda sameer ya samu damar ci gaba da gaya mata magana son ransa yasa itama ta mik'e tsaye ta shiga jijjiga jiki uwa mai shirin dambe kana tace na lura kana wasa dani ko?da sigar ko in kula sameer ya bata amsa da,ni kuwa yaushe zanyi wasa da wacce tayi ikrarin kiran kanta da sunan 'Yar jami'a ai ban isa ba tunda ban tab'a bin wani malami tsoho mai nauyin shekaru ya prof KAS na buk'aci b'ata masa mutunci ba,ban kuma tab'a nuna tsiraici na afili don samun distinction ba kin ga kuwa baxan tab'a had'a kanki da ni ba! Hucin da beauty ke fitarwa kad'ai zai zayyanar dakai irin halin da take ciki na k'unar rai na lura da duk wata gab'a da tabi don taga ta d'au fansa sameer ya kasa bata wannan damar! Awulak'anceta watsa masa wani mugun kallo had'e da sakin wani mugun zagi ta koma ta nemi waje ta zauna jiki ba kwari"abubuwa kala-kala ta shiga sak'awa a zuci ganin yadda ko da sau d'aya zatai nasara akan sameer amma nazarinta ya kasa bata,dole haka ta hak'ura na lokacin ba don ta janye k'udurinta arai ba dai don ta gama da jinyar tsoho tukunna! shi ko sameer lura da yadda ta yi lagwas yayi don haka ya shiga murmushin mugunta ala dole ya iya furta hmm kad'an kika gani yarinya in dai kin ce ke 'yar jami'a ce toh mu masu gyara jami'a ne kuma dole ki ladabtu ko kin k'i ko ki so!daga haka shima ya nemi can nesa da ita ya zauna tare da janyo waya a aljihunsa ya shiga yin game na zima revenge ko ya samu sauk'in rai! Haka sukai zaune har wajen azahar kafin nan dr ya fito hannunsa rik'e da wani abin kwajin numfashi ya nufosu,ko da sameer ya hangoshi tashi yayi fuska a sake ya nufi wajensa yana fad'in dr. Ya jikin nasa?murmushin k'arfin hali ya saki kafin nan yace c'mon down prince ba wani abu ne na tada hankali ba jimawa da yayi a gida ba tare da an kawo shi asibiti ba shiya haddasa masa hawan jini amma yanzu cikin ikon Allah mun samu munyi controlling nasa sai dai tarin da yake ne wannan sai a hankali kuma ana shan magunguna,yanzu haka yana ciki ya samu sauk'i sosai don nayi masa allurar bacci zaku iya shiga ku ganshi in har jikin naga ba matsala zuwa yamma kafin na tashi a aiki na sallame ku! Amsa masa sameer yayi da toh sannan ya k'ara gode masa da namijin k'ok'arin da yayi yabar duk wani aiki nasa yayi nasu!musabaha suka yi kafin ya basu izinin shiga ciki shiko ya wuce waje,jami'an lafiyar da suke tare suka mara masa baya! . Duk bayanin dr. a kunnen beauty ake yi duk da tana can zaune amma hankalinta na kansu haka bata jira cewar sameer ba duk da tasan ba wani abu zai ce mata ba yana shiga d'akin ta biyo bayansa ta shiga!kwance suka iske tsoho yana bacci hannunsa d'auke da ledar k'arin ruwa da aka saka masa,cikin sauri beauty har tana bige kafad'ar sameer ta k'ara gefen gadon ta rik'o hannunsa cike da tausayin halin da yake ciki ts shiga rero kuka!. Cike da b'acin rai sameer ke binta da wani wulak'antaccen kallo shi ala dole ta buge masa jiki gashi yak'i jinij yaga mace tana kuka balle wannan daya lura kamar ita jin dad'in kukan ma take,tsawa ya daka mata a tsawace yace dalla malama ki wa mutane shiru uban me akai miki da zaki cika mana waje da k'ara?wannan shegen kukan naki ai se ya tashe shi" Bata iya tanka masa ba beauty illah tsagaitawa da kawai ta iya yi da kukan!ta nemi waje gefe dashi ta zauna ta k'urawa tsoho ido, a sukwane shima sameer ya koma can baya ya jingina da bango tare da hard'e hannayensa biyu a k'irjinsa cike da damuwa ya ke kallon yarda robar ruwa ke d'iga cikin kwaroron robar hannunsa! . . . Har wajen k'arfe d'aya na rana tsoho na kwance bai tashi ba,jin kiran sallah na tashi daga cikin masallacin ya baiwa sameer damar fita ya barsu anan,yana sa kai ya fita beauty ta waigo ta k'are ma wajen daya tsaya kallo nan ta saki wata doguwar tsuka tare da fad'in"aikin banza ai na zaci bara kaje sallar ba gafin mu zaka zauna yi ka wani kafe mutane da ido uwa soja gona,tsukar dai ta kara saki don yadda duk take jin ta atakure ita bata saba wannan zaman ba musamman ma na asibiti ga yunwa data fara addabarta,k'are ma wajen kallo tayi tas taga dai babu wani abun ci a wajen balle tai tunanin ci,ga babu bayi da xatai alwala ballantana daddumar sallah cike da b'acin rai beauty ta shiga gunguni wanda ita kanta baza ta tantance abinda take fad'i ba do takaici! Tana haka taji an turo k'ofa an shigo, sanin wanda zai shigo yasa ko takan k'ofar bata bi ba da mamakinta sai ta ji muryar mace,hakan ya bata damar d'ago kai ta kalle ta" Sannu dai" jami'ar asibitin ta fad'a, yawwa sannunmu,bata k'ara tankawa ba matar ta shiga jere mata kayan dake d'auke a hannunta,ledojine guda hud'u bak'ak'e sai sallaya da hijabi data mik'a mata sannan ta iya cewa dama yallab'ai ne yace a kawo miki kuma in kina son wani abu ga d'aki nan na kusa da wannan kina fita daga hannunki na dama sai ki min magana"murmushin karfin hali da jin dad'i beauty ta sakar mata don ko ba komai tasan dai abinci ke cikin ledojin nan don haka ta ce toh nagode amma ina bayi yake?hannu jami'ar takai ga wani labule da ke manne a saitin gadon tace gashi nan madam"madam kuma? Abinda beauty ta furta kenan a ranta,toh me yace musu game da ni?kar dai fa ya gaya musu wani abu na b'atance don k'aramin aikinsa ne?ciskune fuska tayi na dole ba don taso sunan ba tace ok zaki iya tafiya yanzu,da haka jami'ar ta fice tare da janyo mata k'ofar! . . Bayin ta nufa ta d'oro alwala ta fito,inda ta aje hijab d'in je ta janyo ta ta saka dogone har yana d'an ja mata k'asa,haka ta janyo sallayar da shirin sallah sai kuma tayi turus tana bin d'akin da kallo ?can kuma ta nisa tace wayyo ni ina ne yanzu kuma gabas d'in?ganin ba fahimtar hakan zatai ba yasa ta yanke shawarar zuwa ta tambayo matar,aje sallayar tayi ta doshi k'ofa don fita,tana murd'a k'ofar taji an murd'o ta daga waje an turo,saurin matsawa da baya tayi don kar ta bige,har ya shigo kallo,sameer kallo ya bita dashi cikin hijab kwanan sha'awa kamar tayi ta zama kullum haka sai kuma can ya basar ya juya kai gefe cikin izzah ya jefota da tambaya,ina kuma zaki?ita madai kauda kai gefe tayi uwa bazata amsashi ba sai kuma can ciki-ciki tace gabas zan tambayo,kamar be jita ya tab'e baki yayi mata nuni da hannu,kalli nan! Kallo ta kai wajen,bai k'ara tanka mata ba ya nemi guri ya zauna! Bango ta kai wa harara beauty kamar yana kallonta ta juya ta zare sallayar cikin fushi ta shinfid'a ta fara sallar! . . Tana idarwa kenan ta fara azkhar ta ji k'arar wayarta cikin jaka,kallo ya bita dashi sameer ya na jiran yaga cikin biyu wanne zatai azkhar ko waya,da mamakinsa sai yaga ta share wayar taci gaba da addu'ointa,k'arar da cikinta ya bayar da k'aramin sauti yasa ta dole badan taso ba tsagaita adduarta ta shafa,wani abu ta ji ya tsaya mata a rai kuma gashi dai tana son janyo ledojin abincin amma kunya ta hanata don yadda k'afafunsa suka tokare ledar" jim ta d'anyi tana nazarin abin amma lura da yadda yunwa ke nuk'urk'usarta yasa ta dole ta maze had'e da tsuke fuska uwa wata 'yar dambe ta saka hannu ta shiga janyo ledojin,karaf ledar k'arshe ta buge masa k'afa, ai kamar jira yake sai ji kai d'asss.. ya kai ma hannunta duka da k'arfi,ledar beauty ta saki a razane ta d'ago kai ta kalle shi,me kuma nai maka?cike da mamaki take tambayar,mugun kallon nan dai nashi ya k'ara jefo mara ya galla mata wata harara yace"ehh lallai kam tunda kin maida tab'a jikin namiji abincin ki ai baza ki san me kikai min ba,toh wallahi na bar kyaleki kina tab'ani kina cin na jaki banza akuya,zunbur beauty ta shiga yi har tana hard'ewa da hijabin jikinta ta mik'e tsaye ta kama k'ugu ta rik'e tana wani karkad'e-karkad'e tace kasan Allah wannan abin naka ya ishe ni ehe,don ba jaka aka kawo maka ba,mutum sai bala'in naci da shishshigi idan baka son alak'ata dakai tun farko wane karanbanin yasa ka neman tahowa dani? Me yasa baka jefar dani a hanya na san inda dare yayi min ba?ko an gaya maka bani da wajen zuwa?meya hanaka zaman wajen da ka dawo yanxu tunda ban kama hannunka nace zo zauna kusa dani ba?toh dan haka malam kasaurara min ko na ci uban.....ba ta k'arasa k'arshe zagin nata se ji kake fau..fau..fau wasu zafafan mari har biyar da sameer ya sauke mata a fuska,bai jira wani abu ba yayi wulli da ita gefe har tana karo da bango ya zari sallayar dake shinfide a k'asa ya shiga jibgarta da ita,kiciniya suka shiga yi sosai dukkan ninsu a wahalarce musamman beauty dake kwance k'asan tiles jiki duk shatin duka,shiko haki ya shiga furzarwa na wanda bai saba shan wahala irin hakaba! Ganin yadda ta galabaitu yasa sameer dakatawa da dukan yayi cilli da sallayar gefe ya nunota da yatsa yana maida haki yace"wallhi duk randa kika kuskura kika k'ara magana irin wannan sai kin raina wa aya zak'inta mutuniyar banza kawai,har ni zaki kalli mahaifina ki zaga wanda ya bani cikakkiyar kulawa da tarbiyya?toh baki isa ba wanda duk kike tunanin ya tsaya miki shima bai isa ba,da kuma kike cewa na takura miki,eh naji na takura miki don bazan zauna ina kallo karuwa ta lalatamin rayuwa ba,don haka ki kama kanki! Yanda take kwance k'asa tana maida numfashi haka ta shiga nuna kanta da yatsa tace,ni ka kira da karuwa?karuwa fa?k'ok'arin mik'ewa zaune tayi amma ina jikin yayi tsami dole ta komar da kai ta kwanta k'asa wasu mugayen hawaye suka shiga anbaliya a kuncinta! . . . Yarda take maida hak'i na kuka haka sameer ke maida hakin wahala suna haka sai rurin waya ya k'ara tasowa daga jakar beauty,sai alokacin ta tuna da d'azu an kirata tana addua haka da janjiki ta isa gaban jakar ta sa hannu ta fito da wayar,lambar zee-zee ta gani rass gabanta ya fad'i ba tare da wani dalili ba,d'aukan kiran tayi ta kara akunne tana fad'in hello"murya k'asa-kasa beauty ke amsa ta can kuma kome zee-zee ta gaya mata sai cewa tayi what??kina so kice min yau akayi test d'in?toh ba cewa akai se last week ba?har nawa akayi?biyu?wanne da wanne?sir p... maganarta yayi dai dai da kallon sameer wanda ke zaune gefen tsoho ya dafe kai da alamar damuwa tare dashi,a sanyaye ta k'arashe wayar sukai sallama da beauty duk jiki ba kwari,tana kashe wayar ta k'ara sulalewa k'asa ta kwanta,tunani kala-kala tun tana iya danne zuciyarta har ta gaza a fili ta shiga dukan tiles din dake shinfid'e k'asa tana fad'in mugu,mugu,azalimi wallah Allah sai ya sakamin! . Tana cikin wannan hali taji daga sama rurin wayar sameer dole ta tsagaita da kukan ta maida kanta ta had'e da gwiwoyinta, zaro wayarsa sameer yayi daga aljihu ya amsa kiran bai wani jima ba ya gama wayar,wata lambar ya shiga laluba beauty na kwance taji cikin wayar yana fad'in kamal yanzu za'a zo a kawo maka test d'ina pls ka adana min kafin na dawo! Da haka suka ci gaba da hira har ya gama,aje wayarsa ke da wuya yaji alamun motsi daga bayansa,da sauri ya juya idonsa ya ci karo da tsoho dake kwance yana k'ok'arin tashi,k'arasawa sameer yayi ya tallabo shi yana tai masa sannu,wanda hakan ne ya tabbatar ma da beauty cewa tsoho ya tashi ,a hankali ta d'ago ta zauna,dishi-dishi haka ya shiga bud'e idonsa har Allah ya saka ya bud'e su gaba d'aya,alama ya fara nuna masa da yana buk'atar ruwa don haka cikin sauri sameer yayi waje don kiran dr. Sameer na fita tamkar ya baiwa beauty damar k'arasowa wajen tsoho ne cikin jan jiki haka ta k'araso suna had'a ido suka sakar ma juna dariya haka ta rungume shi da haka ta hau masa sannu!suna haka sai ga sameer ua shigo tare da dr.dole ta basu guri dr yayi 'yan bincike-bincikensa ya gama da yake ruwan hannunsa ya kai k'arshe zare masa yayi kafin nan ya rubuta masa magunguna yace su zauna nan ya k'ara samun k'arfin jikinsa zuwa anjima sai a sallame su!dad'i sosai ya lullub'e jn yadda cikin k'ank'anin lokaci tsoho ya samj sauk'i,takardar maganin dr. Ya mik'a wa sameer sannan ya basu waje,ledae dake aje sameer ya hau bud'ewa har ya gano wacce ke dauke da ayaba,hannu yakai ya d'ebk yadawo gefen tsoho a hankali ya shiga bashi yana ci har ya gama dai tsoho ba emm ba em em duk tunani ya gama cika game da dabuwar fuskar daya gani tare da jikarsa amma lura da yadda beauty ta kasa sakin jiki suyi hira sosai kamar yadda suka saba sai yayi zaton ko kunyar had'uwarsu da sirikinsa yasa ta shiru(loh tsoho bai sai su beauty duka aka sha ba)da haka ya kauda tunanin a rai"! . _4:30 na yamma:_ . Tsaye suke bakin asibitin rike da takardar sallama inda sameer ya rik'o hannun tsoho duk da jikin da kwarinsa sai dan bashi kulawa kawai,ita ko beauty tafe take nik'i nik'i da ledoji ,baya ta bud'e ta shiga inda sameer ya sanya tsoho gaba ya zagaya ya shiga motar suka fita a asibitin! . Tun saka kan motar sameer a layin tururuwar jama'a kad'ai kake gani ta ko ina ana biye dasu ana ihu na farin cikin tsoho ya dawo,yara ko se d'ane motar suke da yake yamma tayi duk wasu magidanta sun dawo k'ofar gidan tsoho mak'il yake haka suka tsaida motar,inda da kyar Sameer ya iya bud'e wa tsoho k'ofa ya fito dan jama'a,k'ok'arin bud'e marfin motar beauty ta hau yi don ta fito taji an buge hannun daga waje,sanin waye yasa bata ma bi takai ba da sauri ta bud'e k'ofar ai ko yayi saurin maida marfin motar ya kulle kafin ya fidda tsoho yasa mata lock,tururuwar taron jama'ar data gani shi ya hanata magana dole ta koma ciki tai zaune ta bi su da ido har suka shige cikin gida!don tasan sarai sameer na iya dizgata gaban bainar jama'a! . . Juyi da murna babu irin wanda baba yagana batai ba,sam zama ya gagareta,d'akko wancen aje wannan shine kad'ai aikin kai kawo da take wa sameer sai da ta tabbatar ta cika masa gabansa taf da kayan abinci da fura sannan ta iya samun waje ta zauna,baba yagana sameer ya kalla yace baba wai ina d'an ladi kuwa?nisawa tayi kafin nan tace ai d'an ladi ya tafi gona tun bayan tafiyarku watakil ma yanxu duk inda yake yana hanya,wani abu zai yi?a'a dama maganin tsoho zai rakani na siyo cikin gari"sameer ya fad'a" K'aramin murmushi baba ta saki sannan tace ai ban baka labari ba d'azu bayan tafiyarku drammer aka sha ni da shi,wai ala dole anyi masa haramiyar jin rab'ar mota,da gunguni haka ya fita ko ta kansa ni kam ban bi ba ina tunanin yadda tsoho zai samu lafiya duk na gama tada hankali,tunani ya kasa yarda cewa zai dawo da rai sai gashi ya shigo da k'afafunsa kai amma fa mungode da wannan taimako naka! Ba komai baba ai yiwa aki ne yanxu dai ki sama wa tsoho wani abu yaci kafin ya dawo mu siyo maganin"haka baba ta amsa da toh ta mik'e ta nufi cikin uwar d'aka! . . Hankali kwance sameer ya gama cin tuwon alkama miyar gyad'a da baba yagana tai masa ya bishi da fura wacce tasha kindirmo,ya jingina kenan da bango yana son abincin ya ratsa masa yaji maganar d'an ladi yana shigowa" Maimakon ya shigo da sallama sai 'yan wake-wake da yake sakin kamar d'an makid'i har ya zauna dariya kawia sameer yayi masa sannan yace,har ka dawo daga gonar?banza yayi dashi kamar be ji shiba da haka sameer ya ci gaba,dama kai nake jira ka dawo muje mu siyo wa tsoho magani a mota,da jin haka cikin sauri dan ladi ya waigo yana kallon sameer yace wai da gaske kake zaka shigar dani mota?gyad'a kai sameer yayi da zummar eh,ai lokaci d'aya d'an ladi ya saki fuska hira ta b'arke tsakaninsu ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,har da alk'awarta wa sameer yau zai had'a masa taro mai kyau a dandali suje kallo,da haka dai sukai ta hira,sai can da hira ta nisa d'an ladi ya waiga ya kalli sameer yace wai kuwa ina hajjo?sakin baki sameer yayi cike da kid'ima bai jira basa amsaba ya mik'e ya zuri takalmi da sauri yayi hanyar zaure". Koda ya isa gaban motar kwance ya Taradda beauty sai had'a zufa take kana ganinta kasan ta galabaita,cikin sauri ya bud'e k'ofar ya shiga lek'enta!.. . . Lura da alamun bacci da ta shiga yi na wahala yasa sameer bubbuga gefen kujerar yana fad'in ke!ke!firgigit beauty tayi ta mik'e zaune kana ganinta kasan ta wahala,fuska cuskune ta kallo shi babu ko kwakwkwaran nauyi a jikinta ga tsamin duka da jikinta ya riga yayi,koma wa da baya yayi sameer wanda hakan ya bata damar fitowa a motar a daddafe ta maida k'ofar ta rufe,cikin sanyin jiki haka ta shiga tafiya sai yaji duk babu dad'i abin bai masa ba,amma dole ya dake ya kallota ta wutsiyar ido yace ke!kike wani cilla k'afa uwa summy cillare(Loh) in zaki saki jiki gara ki saka in ko ba haka ba na fasa kwai yau kowa na k'auyen nan ya san halinki,da sauri beauty ta d'ago raunannun idanunta ta kallosa cike da takaici,murmushin mugunta ya sakar mata had'e da kashe mata ido d'aya yace kinsan dai xan iya don haka sai ki zab'a yana kaiwa nan yayi gaba abinsa ya shige ciki ya barta nan tana jan jiki uwa wacce kwai ya fashe wa a jiki! . . A cikin zaure beauty ta tsaya nan ta k'ara gyara jikinta sosai,cikin k'arfin hali kuma ta saki fuska ba yabo ba fallasa ta nufi cikin gida,Da sallamarta ta shigo tsakar gidan babu kowa sai k'arar muryar d'an ladi dake tashi duk ya karad'e gidan da surutu shi ala dole labari yake ba sameer,muryar beauty da yaji yasa shi tsagaitawa da hirar ya juyo baki a washe yana kallon k'ofa,har ta k'araso wajen sameer bai d'ago kanshi daga duk'en da yayi ba tun jin sallamarta,cikin k'arfin hali beauty ta kalli d'an ladi tace ina tsoho yake,yana d'akinsa"d'an ladi ya bata amsa,bata k'ara cewa komai ba ta sa kai ta wuce su zuwa d'akin,yadda ta gifta ta gaban sameer haka ya d'ago kai ya bi bayanta da kallo,k'arewa tafiyar kallo yayi sam babu wani alamar sauyi ko canji daga tafiyarta,murmushin gefen kunci sameer ya saki a kasalance ya raya a zuciyarsa"lallai yarinyar nan a iskanci ita yarinya ce har da take tsoron k'aramin k'auye kamar wannan susan sirrinta,toh ko dai tsoho ne bata so ya sani? Bai kai aya a tunanin nasaba yaji an tab'o shi a kafad'a,a d'an tsorace ya juyo,lafiya dai ko bak'on birni?tambayar da d'an ladi ya jefo masa kenan,gudun kar d'an ladi ya fahimto abinda yake kallo yasa shi kauda kai gefe ya d'an ja numfashi yace ai da kaga na kau da kai ba wani abu nake mazari ba illah b'aci da rai na yayi ace yadda kake suburbud'amin wannan labari ka kasa bani labarin budurwarka?(kwana ba sai a mota ba)bud'e idonsa sameer yayi da sigar son jin wani abu ya k'ara langwab'ar da kai gefe sannan yace toh ko dai baka da ita ne? . . K'afa d'an ladi ya d'aga sama ya dire a kan tabarma sai kuma ya kwashe da wata irin muguwar dariya mai cike da mamaki,sai da yayi ma'ishiyarsa sannan ya d'ago kai a gadarance yana wani faffad'a kafad'a yace Wato d'an birni ni d'in nan da kake gani na duk ranar da naje dandali sai 'yan mata sunyi fad'a akai na,shiyasa kaga samarin garin nan duk kishi suke da ni don mero 'yar gidan mai gari wancan satin da naje dandali baka ga yadda take nuna kauna k'arara akai na ba,har wani kod'a ni take wai tana son tsagun fuskata,amma ni duk basa gabana ,jin maganar d'an ladi na k'arshe yasa sameer k'are wa bak'a k'irin d'in fuskar d'an ladi mai cike da tsagu kallo,jinjina kai yayi cike da mamaki,ganin yadda d'an ladi ke ta faman kod'a kanshi ba ji ba gani,surutan 'yan mata barka tai yasa shi d'aga masa hannu yace toh suda sarkin magana yanzu dai gaya min wace zab'inka acikin nasu?cikin sauri d'an ladi yayi hanzarin kai hannunsa ya rufe fuskarsa shi ala dole yaji kunyar tambayar" Murmushi sameer ya saki ganin yau ya had'u da wani garan yace sai kuma can yace haba d'an ladi meye na rufe fuska kuma kai dai gaya min ko wace zan baka shawarar yadda zata so ka fiye da tunaninka, jin haka tuni d'an ladi ya zare hannunshi yace wai da gaske?eh mana kai de gaya min,turo baki gaba d'an ladi yayi uwa mai shirin surb'ar koko yace bawata bace illa haj...hajj...sai kuma yayi shiru! haba kai kuwa meye haka ka fad'i sunan sosai mana ni ban gane wannan yaren ba, jin hak a kunyace d'an ladi ya nok'e kai ciki-ciki yace ni fa hajjo nake so tun dana ganta d'azu" . Hahahahahahahahaha!wata irin muguwar dariya sameer ya saki wacce shi kansa bai ma san lokacin data kwace masa ba don kid'ima da abinda yaji,ido waje ya zaro yana fad'in wace hajjon?ba dai hajjo ta birni ba?washe baki d'an ladi yayi don jin dad'in yadda sameer yayi saurin gano shi yace alqur'an ka gano ni sarkin wayo!k'ara kecewa sameer yayi da wata muguwar dariya ta k'eta ganin bazai iya dai-daita kansa da dariyar ba yasa shi mik'ewa da sauri ya kamo hannunsa yana fad'in kaga taho muje a siyo maganin,a can ma tattauna komai,ba shiri d'an ladi ya mik'e ya bishi sukai waje! . . Tun bayan shigar beautu d'aki hira kawia suke da baba yagana don abincin ma kasa cinsa tayi don yunwar taci ta har ta cinye,duk da kuwa ta jin zugin jikinta,a tsammaninta su sameer suna zaune a tsakar gida,shiko tsoho na kwance yana bacci tun bayan abincin da baba yagana ta bashi,jin kiran sallah da baba yagana tayi ya sata mik'ewa da sauri tana fad'in yau naga yarinyar kawai duk na biye miki da hira gashi ko abinci ban aje miki balle na baki ruwan wanka,dariya beauty ta saki sannan tace ai dama ba sona kike ba yanzu dai bara nai sallah sai ki bani jagolgolon da kike yiwa tsoho na ci,dariya duka suka saki kafin nan baba ta fita ta barta anan! . Gyalen data yale kanta dashi shi ta cire ta k'ara gyara tukkuwar gashin kanta sosai sannan ta janyo wani k'aramin d'ankwali data gani nan gefen shinfid'ar tsoho ta d'aure kanta dashi ta nufi tsakar gida!wayam taga wajen babu alamar mutum wanda hakan ya tabbatar mata cewa su sameer sun tafi sallah ne!k'aramar tsuka ta saki cike da b'acin rai ta furta d'an masifa kawai mutum kamar maye se shiga harkar mutum gaskiya ya kamata ko ba komai na gaya wa daddy abinda duk yake faruwa tunda nan ummah bata nan balle ta tsawatar min in ma dawowa zai yi gara yayi amma duk mutanen nan biyi sun takura wa rayuwata kamar ni kad'ai ce mutum a duniya?wata tsukar ta k'ara saki cike da cin haushi haka ta nufi bakkin tijiya da zummar kafin tai bacci daren yau zata sanarwa dady duk kan abinda ke wakana bayan tafiyarsa,butar dake gefe sanye da ruwa ta d'auka ta nufi bayi! . _8:00p.m na daren ranar!_ . Ruwa ta watsa beauty ta shigo d'akin baba yagana wanda ke jere da na tsoho,zaune ta isketa saman gado tana k'idayar kud'i, eyyeemba su baba an yi arzik'i irin wannan kud'i ince dai kayan d'aki zaki saya mini dasu?tayi maganar tana yarfe ruwan hannunta,dariya baba yagana ta saki nan ta d'ago kai tace mata toh sarkin son banza wannan ba kud'in tsoho bane balle a jere miki d'aki da kumbo wannan kud'in dashi ne da muke yi jiya aka kawo min d'ibata ko k'idayasu banyi ba don dama na maganin gargajiyar tsoho nake tari sai gashi yaron kirki yazo ya share mana hawayenmu,abinda shekara da shekaru ake magani yau lafiya gobe babu amma kiga jikinsa yau har da cin abinci da shigowa gida da k'afafunsa aiko lafiya ta samu,jinjina kai beauty tayi had'e da tab'e baki ta kauda kanta gefe,tana rayawa azuciyarta"lallai baba baki san wanene shi ba da har kike yabonsa mutum mugu azalumi wanda babu tausayin 'ya mace a zuciyarsa,da har zai mun dukan ajali kusa! . Gafaranku dai masu gida,maganar d'an ladi kenan wacce ta dawo da beauty cikin hayyacinta ta k'arasa shigowa da sauri ta nemi gefen gadon kusa da baba yagana ta zauna! Waige ta shigayi ko ta samu abu ta rufe jikinta don zanin atanfar baba yagana ne d'aure a k'irjinta,sai alokacin ta tuna da akwatin kayanta na motar sameer da suka zo basu fito da kayan su ba haka suka tafi asibiti,bata an kara ba taji an yaye labule sama, cikin rawar jiki,ido na kyarma ta d'ago ido sama me zata gani?d'an ladi rik'e da hannun sameer tsaye a bakin k'ofa!yarda ta matsar da kwayar idonta akan d'an ladi sai gashi ta kasa sauke idonta daga kallon da suke mayarwa da juna ita da sameer!ko wannen su da abinda zuciyarsa ke raya masa,cikin k'arfin hali da mazantaka sameer yayi saurin sunkuyar da kansa gefe tare da jan hannun d'an ladi cikin zafin nama yace fito nan waje musha iska mubarsu ciki!bai jirayi amsar d'an ladi ba sai ganinsa d'an ladi yayi an finciko shi da k'arfin tsiya tsakar gida,inda farin wata ya haske su! . . Duk kan abin nan daya faru akan idon baba yagana dake rik'e da kud'i a hannu ta tsaya da k'idaya tun shigowarsu!juyowa tai sosai ta fuskanci beauty wacce ke zaune kanta a duk'e ta zuba wa zanen ledar tsakar d'akin ido,wanda ita kanta bata san dalilin yin hakan ba taji baba ta dafo kafad'arta! Da yake hankalinta ya d'an gushe zuwa tunani sai ya zamana a tsorace ya d'ago kai ta kalli baba!murmushi mai cike da fassara baba ta saki sannan ta saukw ajiyar zuciya ta kira sunanta!hajara! Beauty ta amsa kanta na k'asa! Allah yasa ayi damu! Me za'ayi daku baba?ido waje ta d'ago kai tana tambayar,jin baba tayi shiru tana dai 'yan murmushin nan nasu na manya da suka san me duniya ke ciki!nan ta ci gaba da magana Allah kuwa baba ki yara da n... bata iya sauke lumfashin ta ba baba ta tsayar da ita ta hanyar nuna ta da yatsa tace kul hajara naji kince wani abu!ki tashi ki shirya ki sallah kawai shi ya fi miki ga kuma tuwonki can rufe a tasa!daga haka baba yagana ta mik'e ta maida kud'inta ma'ajiyarsu tayi waje abinta! - ISMAI SANI

0 comments:

Post a Comment