Saturday, 30 December 2017

'Yar Jami'a Part 5 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YAR JAMI'A 005 . 

Misalin k'arfe 9:00p.m kenan a agogon bangon dake mak'ale saman d'akin ummah kallo ta kai gareshi sannan ta nisa,juyowa tai gefe ta ga hankali kwance beauty na rik'e da waya sai latse-latse take yi?me kike yi da wayar??ummah ta tambayeta,cak beauty ta tsaya da charting d'in da take ta d'ago kai a hankali tace ummah gaisawa muke da daddy!daddy kuma?me kike ce masa?shiru beauty tai ba emm ba em em,toh ki ce masa ya kirani zami magana,toh ummah sannan beauty ta samu damar ci gaba da latsa yawar ta sanar masa,daga haka ta kashe datan nata ta sauka akai gaba d'aya,gefen kujera ta maida wayan ta aje don tasan halin ummah yanzu k'iris take jira ta kwace ta,ba'a d'auki wani tsawon lokaci ba sai ga kiran daddy ya shigo wayar beauty,hannu ta kai ta d'akko wayar ta ga sunan daddy a jikin wayar,juyawa tai ta kalli ummah tace daddy ne ya kira!wani dumm ummah taji kanta yayi mata yanzu kenan bazai kirata a wayar ta ba sai dai ta 'yar ta!haka ta danne damuwarta ta sa hannu ta karb'i wayar!gaisawa sukai kafin nan suka shiga hira ainun suna k'ara nuna wa juna tsantsar kulawa da rashin juna da sukai!acikin hirar ne beauty dake can gefe zaune taji ummah na sanar da dady zancen tafiya har tana ce masa beauty ta rok'i bak'on gidan nan ya kaita ta dubo jikinsa,da mamaki beauty tabi ummah da kallo har ta kammala wayar,ba abin tai magana ba sai kallo da ido,ke lafiya kika kafe ni da ido haka?cewar momy"nasan dai kin ji me nake cewa sarai toh dan haka ki shirya gobe da sassafe zaku tafi minjibir!minjibir kuma ummah?eh minjibir kuma wallahi naji kin kira dady kin gaya masa wani abu ni dake ne,don haka sai kije ki fara shiri tun yanzu don bansan kwana nawa zai ce kuyi ba!ba shiri beauty ta mik'e tsaye ta amso wayarta a hannun ummah ta fice a d'akin! Da gudu beauty ta fad'a d'akinta kuka sosai ta shiga yi ba ji ba gani sai wani shure-shure take da hannu ita ala dole an b'ata mata"teddyn ta dake ajiye tsakiyar gado ta d'auka tai cilli dashi saman mirrow duk wasu kayan kwalba suka zube k'asa,tun tana kukan da sauti har ta gaji ta fara tsagaitawa dan kanta"kalaman ummah ke ta faman mata yawo akai toh yanzu haka kawai zata bi wani bak'o k'auye bata ma san waye bane,don kawai an ga daddy baya nan,har kusan sha d'aya na dare beauty na kwance sai faman mirgine-mirgine take saman gado" Can wata dabara ta fad'o mata"tabbas zan had'a kayana da zarar mun fara tafiya sai na nemi na bashi kud'i kawai ya sauke ni a wani hotel d'in in yaje ya dawo sai ya biyo ya d'auke ni mu tafi!!yes yes beauty ta mik'e tsaye tana murna ta nufi drawer d'inta,duk wani abunda zata buk'ata sai da ta kammala su a jerin akwati biyu don ko ta batun karatunta bata yi sanin dama can baya gabanta! . Kiran sallar asuba na farko beauty ta tashi"ita da sallah sai gari ya waye take yi,wanka ta d'auro kafin nan ta fito ta shirya tsaf ta nemi hijab tai sallah"tana zaune kan dadduma kamar daga sama ta ji ta fara tariyo abinda ya faru jiya a stop and chop,yanda matan nan su kai mata tayin shiga k'ungiyarsu,tunani sosai tayi har dai daga k'arshe ta yanke shawarar in har ta samu zuwa hotel an jima zata kirasu ta shaida musu amincewar ta akan buk'atarsu! Duk yadda tayi saurin lokaci yayi ummah ta kirata sai gani take lokacin baya ja,sauka k'asa tayi ta nemi breakfast tayi amma har yi war haka 7:00a.m batai ba, tsuka ta saki ta k'ara haye wa sama"tana zaune saman stool tana k'ara gyara kwalliyar fuskarta taji turowar k'ofa,ummah ce ta shigo dan haka cikin ladabi ta gaisheta!shigar jikinta ummah ta k'are ma kallo"doguwar riga ce light pink sai yalolan gyalan rigar data nad'e kanta dashi"jinjina kai ummah tayi sannan tace tun d'azu fa ya fito yana mota ke yake jira"jin haka yasa beauty cikin sauri ta aje lip stick d'in dake hannunta kamar ba ita jiya ke b'ata rai ba,ta shiga jan akwatinta,don yanzu ummah ta hana kowa yi mata aiki a gidan in banda wanki da guga,ummah ce ta taya ta da d'ayan akwatin har bakin mota inda ya ajiyeta saitin fitowa daga falo,bud'e taga booth d'in don haka suka zura akwatunan ciki,jiyowa tai su kai sallama da ummah sannan ta nufi k'ofar gaba na motar ta bud'e,da yake motar dimm take da duhu ko ina bak'i ne in banda side mirrow na waje baya ganin na ciki,shiko sameer rik'e yake da waya yana fama zuma revenge game da yake mayan game ne kawai yaji wani k'amshin turare ya doki hancinsa daga bud'e k'ofar!!! . A hankali sameer ya d'ago dara-daran idanunsa ya sauke su akan k'ofar motar har lokacin beauty na tsaye tana k'ok'arin gyara doguwar rigarta don ta zauna,zanen rigar ya k'ura ma ido yadda yake ta shek'i na tamabarin tauraro(star) sosai ya shagala da kallon zanen kamar daga sama yaji k'arar demmmmm...Alamun an masa game over kenan, saurin sauke kansa yayi a phone d'in inda hakan yayi dai-dai da shigowar beauty had'e da tsayuwar ummah a bakin k'ofar tana fad'in toh sameer Allah ya tsare hanya,da saurinsa ya d'ago kai sama don baiwa ummah amsa!dass yaga idon mace kafe saman nasa wanda tun kiran sunansa da ummah tayi hakan yasa ta waigowa taga wannan waye abokin tafiyar tata,what??abinda sameer ya iya fad'a kenan yana nuna ta da yatsa, beauty da tai saroro kamar wata dutse tana kallonsa,can kuma cikin razani lokaci guda ta turo k'ofar motar har tana bige ummah da marfin motar haka tayo waje sai faman haki take kamar wacce tai tseren gudu!ido waje take kallon ummah da take tsaye tana luliye inda ta bug'e tace ke lafiya haka?bata iya cewa komai ba beauty sai nuni da ta ma shiga yi da motar!ganin ta kasa cewa ko uffan yasa ummah sunkuyar da kai cikin motar don ganin ko wani abu ya faru ciki!zaune ummah taga sameer ya dafe kai da hannu!cikin rashin fahimta ummah ta k'ara nanata maganar ga sameer shima dai yayi shiru!k'ok'arin komawa ciki beauty tayi,ai kuwa cikin sauri ummah ta rik'o hannunta!ina zaki?tambayar da ummah ta jefo ta dashi kenan?cikin dak'ilewar murya beauty ta amsa ta da ciki zan koma ummah wallahi na fasa tafiyar nan ya fito min da kaya na kawai!ciki kuma?akan wane dalili?kafin beauty ta iya bata amsa suka ji bud'e k'ofar sameer daga d'aya b'angaren yana fad'in emmm ummah dama ba komai kawai tayi mamaki ne jiya na d'an daki motar ta ban sani ba har ta kasa hak'uri ta fito tanai min fad'a,sai kuma gashi yau Allah ya had'amu amma babu komai,cikin k'ik'ina da sark'ewar murya sameer ke maganar!kana ganinshi kaga wanda ke b'oye da wani abu a rai,k'ara yunk'urowa beauty tai zatai magana nan ma ya k'ara tare ta da cewa,ina ga ummah in ta shirya kawai mu wuce don kar muyi latti ko?jin an ambaci latti yasa ummah saurin kallon beauty tace kin de ji kunya wallahi ko ina se kin nuna halinkina rashin hak'uri yanzu gashi dara ta ci gida,sai ki wuce yanzu ku tafi ai,kasa ko da kwakwkwaran motsi beauty tayi,duk wasu jijiyoyin kanta sun gama tsayawa cak da aiki,tunani fal sun gama cika kwanyar kanta,toh yanzu dama wannan shine bak'on dady?wanda ya gama tozartani a bainar jama'a?anya kuwa burin dana cimma yau zai iya bari na cika shi?toh yanzu ya ma za'ai na iya binshi mu tafi daga ni sai shi?bata dawo daga duniyar tunanin data shiga ba kamar daga sama taji wuf an finciki hannunta da k'arfin tsiya an wullata cikin mota,an maida k'ofa an kulle da key,a razane beauty ta hau jijjiga k'ofar da k'arfi ita ala dole sai ta bud'e,tana kallo haka cikin sauri sukai sallama da ummah ya shigo motar,bai bi ta kanta ba ya hau kunna motar,batai wata-wata ba ta jiyo kamar wata zararra ta rik'o hannunsa da yake kan key tace wallahi ka bud'e min motar nan,kar ka kuskura ka fita a gidan nan ba tare da ka sauke ni ba na dai gaya maka,sauke idanunsa sameer yayi a karo na farko a hannunsa yaga hannun beauty saman nasa,wani irin kukan kura yayi kamar wani mayunwacin zaki yayi wurgi da hannunta gefe,yanda taga jikinsa na wani kyarma tamkar mayak'in soja yasa ta shiga taitayinta ta fara rok'onsa Allah,da annabinsa ya sauketa,da yake motar duhu gareta sai ya zamana ummah duk wannan dramar tasu ba wadda ta gani haka ya tada mota hankali kwance ya fice daga gidan yana gyad'a kai! . Wallahi ka sauke ni, zan maka ihu, Allah zan juyar da kan motar nan kowa ya mutu,wai ba da kai nake magana ba ka mai dani wofi,kana jina fa? Nace ka tsaya na fita,surutai sosai beauty keyi,tun tana gunguni har takai ga samun sararin d'aga murya,ganin har lokacin sameer tafiya yake bashi kuma da niyyar tsayawa yasa ta kwarma wani uban ihu da bashi ba ita kanta sai data firgita,lura da lokacin ya fita daga wajen mutane ya fara yankar daji yasa shi jan birki ya maida motar gefen titi ya tsaya,kana ganin sameer kaga wanda yake cike da b'acin rai basai an gaya maka ba,wani wawan kallo ya jefe ta da shi mai cike da tsana,kusan minti 2 yana mata shi ganin hakan bazai gama isar da sak'onsa ba yasa shi magana"tur da wayewar gari irin wannan a wajena,ina ma ace mafarki nake,wallahi da tuni na farka na shiga gari na hau sadaka,don wannan munin mafarkin yakai matuk'a!kaicona sai gashi wai a zahiri ne,ni ne yau kusa da mace fasik'a,fajira,wacce bata san k'ima da mutuncin kanta ba,balle kai tunanin samun tsarki tattare da ita,nikam Allah wadai da mace 'yar Allah bani musha kunin kanwa,wai ya ma akai kika zama 'yar ummah?how??duka yakai a sityarin motar rai b'ace cike da nadamar hakan! . Tun tana danne zafafan kalaman dake fitowa daga bakin sameer har abin ya fara kai ta mak'ura gashi yak'i ci gaba da tuk'in kuma yak'i yarda ya sauketa,wasu zafafan hawaye ne suke k'ok'arin gangarowa kumatun beauty cikin sauri ta sharesu dan kar sameer ya ga lagonta ko kasawarta,juyowa tai cike da tsiwa tace ya isa!ya isa haka malam,ka ishe ni da surutai nace ka sauke ni ko dole ne sai ka tafi da ni? Cikin huci sameer ya amsa ta"dole sai na tafi dake,ke kanki kinsan hanyarmu ta sha ban ban in banda k'addara!hayaniya sosai suka shigayi ya fad'a ta fad'a kamar wasu karnuka,har takai ga ta big'e masa hannu don masifa,kan uban can!ni kika bige ma hannu?ai sameer be jira ta bashi amsa ba ji kake fau fau ta ko ina dukanta yake kamar an aiko shi,duk da wuyar dukan da take sha amma hakan baisa bakin beauty ya rufu ba,sai da yaga yayi mata lilis sannan ya kyaleta,nan ne kuma tai lamo saman kujerar mota tana maida ajiyar zuciya! Sai a lokacin ya janyo goran ruwa dake sak'ale a marfin motar ya sha,sannan ya bud'e motar,hannunsa ya wanke kafin nan ya maida k'ofar ya rufe yata nanata astaqfirulla,shi ala dole ya tab'a mace(kun ji sameer fa)wata doguwar tsuka ya saki yana fad'in ni dai duk iskancin mace da makircin ta na fi k'arfinta don ni ba ta shin shaid'anu bane,in ma sune ke bibiyarki gara ki gaya musu su barki dan nan baza ku sami waje ba,sai a bari sai an koma *'jami'a* sai a ci gaba,yana kaiwa nan yayi saurin kai hannunsa ga cd rom d'in motar, kaset d'in qira'a ya kunna, a hankali kake jin muryar sudais na tashi aciki,cikin sanyayyar muryarsa mara sauti haka ya shiga raira qira'an yana wani kwantar da kai saman kujera,sannan ya tada motar yaci gaba da tafiya! . Duk da ba wani bacci beauty take ba amma haka tai shiru itama dai tana sauraron qira'ar da haka har bacci ya d'auketa!lura da yadda ta makure kanta waje d'aya sameer yayi,nan da nan ya k'ara k'arfin ac d'in motar inda ta ko ina kake iya jin sanyi,shi kansa sanyin yayi masa yawa amma don mugunta haka ya hak'urar ma kansa,can cikin bacci beauty ke jin sanyin a jikinta, juyowa tai ta kai hannu ido a rufe tana laluben makunnin ac,d'all...taji an kai mata duka a hannu,wani irin zugi taji hannunta ya d'auka ba shiri ta bud'e ido,kansa na a titi amma yasan tabbas shi take kallo yace,kar ki kuskura ki bari najasa ta tab'a tsaftataccen abu in ko ba haka ba,yanzu ki sake shan wani dukan! K'ara gyara zamanta sosai beauty tayi har tana wani bank'aro k'irji waje ta murgud'o mai baki tace bismillah d'an halak ka fasa, Kallo d'aya sameer yayi mata ya k'ara sakin wani tsakin yace kaga balama,wato na dake ki d'azu kin ji dad'i hankali ya kwanta,har da lumshe ido shine yanzu kike so jikina ya k'ara tab'a naki ko?toh na gano ki!gaskiya ke akuya ce ko wacce harawa ci kike!God forbid! Wannan irin rayuwa taki yarinya kamar tashin getto! Marairaice murya tayi beauty uwa mai shirin kuka take nuna kanta da yatsa tace,ni nake son ka tab'a ni?kai kuwa kasan ni wacece?cikin tsiwa shi ko sameer ya dawo mata da amsa"ahaf ni ko nasan ko ke wacece,ko ba kece wannan karuwar malaman jami'ar ba? wacce sunanta yayi k'auri a wajen d'alibai kai har da malamai ko ina ka zagaya *'yar jami'a* duk mutumin banza ya sanki!bayan wannan sanin akwai wani sani da zan miki ne?don haka ina gargad'inki in kina son tafiyarmu ta k'are lafiya toh ki iya bakinki kuma ki nisanci zama a inda nake,bata jira taji k'ashen maganar tasa ba ta juya masa baya har da cire gyalen data yale kanta dashi ta rufe fuskarta! Murmushin gefen kunci sameer ya saki me cike da mugunta yace dad'in ta dai kin ji a jikinki don haka in kunne ya ji,toh gangar jiki ta tsira,yana kaiwa nan ya basar da ita ya shiga bin qira'arsa yana tuk'i! . Har suka isa garin minjibir beauty kwance take fuska rufe,gashi yana son tambayar ta inda zai shiga amma zuciya tak'i barinshi,can dai da yaga ba haza dole ya k'ara d'aka mata wani dukan,beauty dake kwance tunani duk ya gama cikata ta sak'a wancan ta kunce wance,tai firgigit ta d'ago fuska tana cire gyalen fuskarta,dilla malam ni kar ka sake duka na ai ba jaka bace,shiru yayi mata don yanzu bashi da lokacin biye mata haka,ina zamuyi?ya tambayeta kansa na kalon gaba,karkato hannunta tayi tana nuna masa kwanar data yanki gefensa cikin saurin yayi baya da jikinsa sameer can kuma ya kallota yace ke dilla ba sai kin kara kanki da ni ba da baki zaki min magana!wani abu taji ya kawo mata wuya beauty wai shin me ya dauke ta haka yake ta wulak'antata?kwanar yasha ya shiga tafiya a hankali don sun shigo gari baya so ya wuce wajen!tafiya suke tayi ba tare data k'arayi masa magana ba sai ma chewinggum data fito a jakarta ta jefa baki,ta shiga tauna, har sameer ya kai k'arshen titi beauty bata tanka masa ba,a k'ufule ya juyo don yaga babu wani sauran gida gma inda suke sai gonaki na mutane, yace ke wai ina zami yi ne kuma?kwai beauty ta sakar masa ji kake k'as-k'as sannan ta saki wani kasalallen murmushi tace inda waccen akuyar take nan zaka bi!waige sameer ya shiga yi amma sam wajen baiga wata alamar ko kaza a wajen ba balle akuya,lokaci d'aya ya fahimci beauty bak'ar magana ta yi masa,juyowa yayi a b'ace yaga ta k'ara sakar masa wani kwan k'ato,ai bai san sameer lokacin daya cafko hannunta ya murd'a shi da k'arfin tsiya ba,ihu sosai beauty ta saki har da d'aga k'afa d'aya sama bayan ido data zaro waje,ji kake tana cewa wallahi baya ne,kwanar da muka baro ne,waccan kwanar ce fa ta baya,amma ina sameer k'af yak'i kulata sai da yaga ta ji jiki sannan yayi wurgi da hannun ya juya kan motar suka dawo baya,rik'e take da hannun tana juya shi da haka tayi ta masa kwatance a nutse har suka isa k'ofar gidan nan tace toh ka tsaya haka mun zo! . Yi yayi sameer kamar ba ze amsata ba, sai kuma can ciki-ciki uwa mai gunguni yace toh!k'ok'arin bud'e k'ofa beauty ta shiga yi ta fita don taga alamar sameer bashi da niyyar fita, taji yace toh sai a kama kai nan dai gidan tsoho ne ba gala ba,wani miyau mai mugun zafi beauty ta had'e ta gyad'a kai ta fice abinta,kamar jira yake ta fito shima ya fito ya biyo bayanta, zauren gidan suka shiga tana gaba yana biye har suka cimma tsakar gidan sallama beauty tayi shiru ba motsin kowa sai data k'ara d'aga sautin nata fiye da wancan sannan ta ji daga can d'akin dake kallin kusruwar gidan wata dattijuwa ta amsa! Wana ke ji kamar muryar jikalle? Eh tsohuwa me ran k'arfe mune! Toh! yagana ta fad'a tana yaye tsukakken labulen dake sak'ale a k'ofar tana fad'in lalle marhabun k'araso ciki!ta kai ayar maganar kenan kanta ya kai ga sameer wanda ke mak'ake bayan beauty!. Auf ashe da bak'o kuke tare!hannu baba yagana takai saman katifar da ke shinfid'e tsakar d'akin ta janyo gyalenta ta yale akanta dashi sannan ta k'araso waje,cikin nutsuwa sameer ya tsugunna ya gaisheta ta amsa hannunta d'auke da tabarma! Ashe ana ganin ku mutanen birni?cikin farin cikin ganinsu baba yagana ke jefo mata tambayar! Hmm kaji baba ai yanzun ma wajen tsoho na zo ba ke ba!tana maganar yayin da take tallafamata wajen shinfid'ar tabarmar! Yunk'urawa beauty tayi zata zauna baba yagana ta jefota da wani irin mugun kallo tace na bige ki anan guraren,ke zan wa shinfid'a ko siriki na?gafara can ki ba bak'ona waje ya zauna yau ta shi nake bake ba!" Ba beauty ba hatta sameer se da maganar tayi masa mugun nauyi a kai!siriki kuma?nanata kalmar yayi cike da rashin fahimta,haka nan dai ya iya dai-daita nutsuwarsa ya nemi waje ya zaune,k'ara gaisawa sukayi nan kuma hira ta b'arke inda sameer ya ji komai game da raahin lafiyar tsoro dake can cikin k'uryar d'aki ya samu bacci! "Gafara dai masu gida!e Muryar wani matashi kenan wanda a tsawo bai wuce na sameer ba ya shigo tsakar gidan rik'e da kekensa mai cike da damin harawa! Baba yagana ce ta amsashi da gafara dai!tana kallon shi cike da nuna sanayya! K'eeee.. suka ji ya saki keken k'asa ya shiga nuno su da yatsa yana fad'in kan uban can wazan gani zaune kamar hajjo? Sororo hajjo tai tana kallonsa kamar zata iya tuno shi amma ina rashin zuwanta yasa ta kasa tuna shi!! . Ganin tayi shiru ya sashi k'arasowa ya nemi waje gefen sameer ya zauna nan ya mik'a mai hannu sukai musabaha sama-sama amma duk hankalinsa naga beauty,baba yagana ce ta katseshi da hannu tace kai wannan kallo haka d'an ladi kamar baka san taba?washe baki ya shiga yi yana kai hannu k'eya yana susawa yace"ai baba hajjon ce duk ta canja tayi fari tai gyau wallhi hala tana shan lemon birni(apple) ne? dariya duk suka sa har da beauty!jim suka d'anyi da sigar shiru hakan ya baiwa sameer damar kai kallonsa ga bak'ar agogon dake sak'ale a hannunshi ya duba lokaci inda ya nuna 9:30a.m da sanyin jiki ya d'ago kai ya kalli baba dake jn gene da garu yace ina ganin baba yagana ya kamata a tashi tsoho haka yayi kumallo mu je asibiti ko? Don kar lokaci ya k'ure mana"baki sororo baba yagana ta bud'e baki hangam tabi sameer da kallo can kuma ta nisa tace kai d'an nan rufa min asiri ina yabon ka sallah kar ka kasa alwala mana,mu yanzu ina mu ina zuwa wani wajen asibiti kayan yahudu da nasara bakaji jami'an su ana kiransu likita bokan turai ba?wannan ai sai ka saka mu zama abin fae'e a yankin nan,toh bada niba wai shiga d'akin mayya!fad'a-fad'a,tsiwa-tsiwa haka baba yagana ke maganar kafin ta kai ga cigaba d'an lami yayi caraf ya karb'e maganar! Ai dama wallahi baba ni nasan da walakin goro a miya tunda na yanko kwanar layin nan naga an kicciye mota gaban shagon sale me rake nasan cewa wa'adin tsoho yazo don na tabbatarda wannan d'an farin(nan ya nuna sameer da yatsa)uwa aljani ba haka nan yazo ba,toh wallahi ahir d'inka tsoho sai ya ga aure na don baza kai min haramiyar damun hatsin daya tanadar min ba yazama na magada!jin yarda d'an ladi ke ta zuro bayani ba ko tsagaitawa yasa beauty rai b'ace ta daka masa tsawa! Kai dalla can kai wa mutane shiru,ashe kai har yanzu sokancin nan dai baka bar shiba?har kana wani d'aga wa mutane murya?toh bara kuji zuwa kamar anyi an gama" . Kin yi kad'an wallahi kin yi tsararo baki isa kizo cikin sanyin safiyar nan ki d'aga mana hankali ba,ko uwarki ina magana bata ja balle ke! yau naga waze raba ni da d'an uwana"tana kaiwa nan a magana sai ta b'arke da wani irin kuka mai cike da k'ara baba yagana kenan, kai kace wani mugun abun akai mata! Ganin yadda hayaniya ke tashi sosai ga kuka da baba ta saka yasa sameer matsowa kusa ita ya saisaita muryarshi k'asa-k'asa uwa mai rad'a ya shiga aikin lallashi! Da kyar baba yagana ta hak'ura ta tsagaita da kukan wanda lura da hakan ya baiwa sameer damar fara yi mata bayani! - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment