Saturday, 27 January 2018

BANA KAUNAR KA page 1&2

==BANA KAUNAR KA 1 ==
.
WAHIDA! WAHIDA!! na"am gani nan d sauri na isa "salamu alaikum,yaya gani zauna magana zamuyi da ke na zauna ina kallonsa wahida tsakaninmu babu boye-boye babu munafintar juna saboda Allah me yasa ba kya son yayanki dan uwanki shahid (bom boy)? na sunkuyar da kai yaya zan iya fitowa in fada wa ya al'ami shahid na shaye-shaye?no ba zan iya ba na dago ganin yana kallona duk saina dabarbarce nace haka nan bai kwanta min ba ba kya sonsa kenan? na daga kai...magana zaki yi ni gaskiya bana sonsa...aka banko kofar yaya faruk ne cikin karaji yace ai kuwa dole kiso shahid ko kin ki ko kin so sai....ni dai gaskiya BANA KAUNARSA haka kurum sai a tura min ni wallahi...a fusace yayo kaina da gudu (bedroom) din yaya al,amin ina fadin yaya kai masa magana wayyo yaya al,amin yace kar ka duke ta faruq kar ka taba ta amma ina ya finciko ni yayi bool dani na wuntsila ya kuma kai min kafa al,amin ya rike shi da gudu na fita ina rusar kuka dakin abbanmu na nufa suna zaune suna kallon nigerian film ,mahida tai saurin mikewa ta rike ni sister waya taba ki?
.
jikin mom na fada ina kuka tuni sister mahida ma ta kama kuka da kyar abba ya shawo kaina please i,m sorry baby waya taba ki? ba ya faruq bane mahida maza kira min faruq ta mike da sauri ta tafi ya kazo inji abba wata tsawa ya daka mata ke fita min daga daki ba zan zo ba wato keme yar uwa dan an dole tashi ne za ki shigowa mutane daki bako sallama to koma kiyi sallama ko in ci ubanki mahida ta juya tana gunguni koda tazo sai ta cewa abba ya ce yana zuwa ai kuwa ba ayi cikakken minti goma ba sai gashi yana zuwa yayi sallama abba ya kalle shi faruq me wahida tayi maka? nan take yaya ya fadi duk abin da ya hada mu abba ya kalleni wahida baki da gaskiya dan me zaki masa rashin kunya alhalin shine sama dake?
.
nai shiru maza ki bashi hakuri ko in bata miki rai na durkusa don Allah ya faruq kayi hakuri yai murmushi dana fassara shi murmushin mugunta mahida ta kamo hannuna muka bar dakin suna fita alhaji sulainman ya kalli faruq yace abin da kake yi baka kyautawa ummaru yarinyar nan ka maida ita kamar jaka koda wanne lokaci kana dukanta me yasa? abba wallahi wahida bata da kunya tayi mugun raina ni to ai kai kaja ta rana ka tunda kai kuke wasa dasu me yasa basu raina al,amin ba? kaga ko kadan alamin baya dukansu." KAYI hakuri abba insha Allahu ba zan kuma ba shi kenan Allah yai muku albarka mon tace "wai ya amin ya fasa tafiyar? ai kin san jirgin sha biyu zai hau ko da naji WAYE NE ALH SULAINMAN WATO MAHAIFIN WAHIDA DA MAHIDA??
.
**** *** ***** ****
Alh, sulainman haifaffan katsina ne kasuwanci ya kawo shi garin kano kasancewar Allah ya sawa abin albarka cikin kankanin lokaci alh sulainman yayi gidan kansa sannan ya gina wani gida daban kasancewar mahaifinsa ya rasu sai mahaifiyarsa nana Aishatu da kanwarsa nana khadija sai yayansa mohd rabiu da kyar ya shawo kan mahaifiyarsa ta yadda ta dawo garin kano shi kuwa dan uwansa wato yayansa dama tuni ya saida shanunsa da gonakinsu shima yaja jari, alh sulainman ya hadu da matarsa haj, maryam can garin kano sun kulla soyayya wadda ta kaisu ga yin aure haihuwarta ta farko ta haifi yaya biyu hassan da hussaini,hassan shine (al,amin) inda usaini yaci (faruq) shekara goma sha shida ta kara haifar biyu hassana (mahida) inda usaina kuma suke kiranta (wahida) sai yayan alh sulainman mai ha daya jal wadda aka sa mata sunan kanwar alhaji sulainman wato khafiya suna kiranta mamy sai kanwarsa khadiya ma wadda take auran wani babban ma,aikacin gwamnati mai suna alh aliyu haidar, haifuwarsu daya jal inda ta haifi yaya biyu hassan shine (shahid) usaini kuma suna kiransa haidar amma sunan ubansa gare shi tsakaninsu Al'amin da su shahid tsiran kwana goma ne dukkanin yaran sun taso cikin tsantsar kulawa sannan sun samu ingantaccen ilimi inda al'amin yake matsayin dan kasuwa domin sana'ar mahaifinsu ya fada sa faruq ma'aikacin kwastam (costom) a turanche shahid soja yake son zama,haidar doctor,
.
sai matan mamy wadda take bautar kasa,mahida da wahida kuma karatun likita suke sai dai yanzu sun dakata ko meye dalili kwaji nan gaba. mahida ta kalleni kema duk abin da akai miki keki kaja,wai me yasa ba kya son shahid din? kinga mahida kai ki dameni bana sonso ko ana dole a so..? ya Al'amin ne ya shigo yayi shirinsa tsaf ya zauna kusa dani sister zan tafi na kalle shi cikin kulawa yaya sai yaushe kuma zaka dawo? sati biyu zanyi ku taso ku raka ni air port na mike muka daura after drees akan kayan jikinmu muka rufe dan kwalin rigar ya faruq shi yai mana direba domin shi da mahida suna gaba nida ya amin muna baya ya kalleni ni me zan siyo miki?
.
yaya irin man wanke kan nan da ka siyo min wancan zuwan sai kuma sabulai masu kyau koda zai tafi kuka na dinga yi ya rungumeni yana lallashina da kyar muka rabu a motar ma ban yi shiru ba ya faruq ya daka min tsawa.
.

==BANA KAUNAR KA 2  ==
.
KE malama rufe mana baki ina kuma binsa zaki yi mu samu labari na tabbata da nine zan tafi ko kishi ba zaki yi ba mahida tace ya faruq muje gidan su small boy tana nufin gidan su shahid nai tsaki ni gaskiya ba zani ba ai kuwa jin nace ba zani ba yace ai kuwa sai munje koda muka isa gidan kin fitowa nayi nace kaina ke min ciwo sukai ficewarsu shahid da haidar da mamansu wadda suke kira anty suna zaune a falo suna (break fast) anty tace a,a mahida faruq sannunku da zuwa shahid yace ni ban muku magana ba tunda baku zo da wahida ba tare muke tana mota wai kanta ke ciwo da sauri ya mike bari in shigo da ita tasha magani ina zaune na kifa kaina kan sitiyarin ya bude motar ya shigo da sallama tuni kamshi turaransa ya cika ni banda gobe shiru na minti goma na san in na biye ta miskilin mutumin nan sai muyi minti hamsin na dago abin mamaki idonsa fea a kaina cikin sakan biyar na masa kallo sanye yake da farar t-shirt da wando (3 coter) kin tashi lafiya?
.
nace lafiya na maida kaina na kwanta ya kalleni ba zaki shigo ku gaisa da anti ba? banyi magana ba wahida? mahida tace eh kanta ne yake ciwo oh sannu kinji na zauna kan (carpet) ina gaida anti,anty ta ce wai ina Al'amin ne? yanxu muka raka shi airport ya tafi china bom boy yace oho shi yasa wahida take kuka anty tace bom boy kawo mata paracitamol,ya kawo min magani tuni na soma hawaye domin bana son shan magani kasancewar duk sun san halina sai ya ajiye maganin ya kama min kan koda muka koma gida abba baya nan kuma mon ta tafi unguwa muna zaune muna hira mahida tace gaskiya sister ina son small boy..
.
nai saurin katse ta ai ki ta sonsa ni dai nace bana son bom boy amma kin san aure tsakaninku bbu fashi.........to Abba sai ka aura masa ni kamar kin sani ko ban aura masa ke ba zan sanar da abba irin matsannancin son da bom boy.........kan ta karasa na finciko ta na tsinka mata mari maganar ya faruq naji la! la!! la!!! kika mare ta me tai miki? dan me zata dinga raina min hankali cool down wahida da kyau wai ke wacce irin yarinyace mara kunya iye! mahida ba yayarki bace? ke wallahi ko sunanta naji kin kara fada sai na babbala ki"...to ai saika fada min shekara nawa ta bani ko wata nawa ko kai ba ka fadar sunan ya amin....
.
da sauri ya finciko wayar soket abin haushi ko gezau ba tai ba ya finciko ta ya cilla kujera ya shiga dukanta tana ihu tana kiran mominta mahida kankame ta tai suka shiga kukan tare, by muhd abba gana, na mike ina fadin wallahi ba gaji gidan zan bari don an ga ya amin baya nan dole aci zalina ina kuka na hada kayana na datse na shiga jan akwati mahida naja gidan kakarmu na nufa wadda ta haifi babanmu ina shiga na tadda mamy' yar baba rabi,u tazo hutu da gudu muka kankame juna,atu kakarmu ta shiga murje ido wa zan gani kamar wahida? atu kenan ni sunana mahida!!!
.
KODA mum ta dawo tace ina auta? mahida ta kwashe labarin duk yadda akayi ta fada mata ran mom ya baci tace shikenan shida abba koda abba ya dawo mahida taje yi masa sannu da zuwa yace ina wahidar? mahida ta fede masa biri har wutsiya ya girgiza kai shikenan maza kije gidan sister khadija ki gano ko tana nan mahida ta shirya tsaf sai gidan anty bata same ni ba daga nan tai gidan baba rabi'u nan ma bana nan a gidan atu muna zaune da mamy muna hira ta fado tayi wujiga wujiga domin bata kawo zata same ni gidan atun ba,duk a tunaninta ko na gudu katsina,ta fado jikina dalla can ni kin ban wahala, wallahi ban zaci kina nan ba nice har gidan su mamy........
.
to ni na aike ki ta kalli mamy tace anti mamy yarinyar nan bata da kunya kin ganta ko yaya faruq bata ragawa ba mamy tace in an bi ta barawo to fa abi ta mabi sahu, in wahida nada laifi ya faruq na da laifi.....ki daure mata gindi nan kenan to ai shikenan abba ne ya turo ni ki tashi mu tafi na mike wallahi babu inda zani in kin ganni a gidannan to dan uwana ya dawo....haka kika ce? yes bbu inda zani shikenan mamy na tafi oho ki gaishe su umma ta gaida aisha zasu ji amma ki sani abba na nan zuwa tai ficewar ta ina jin tashin motarta da yamma muna zaune nida mamy muna hira sai ga su bom boy shi da small boy muna gaisawa na tashi na shige dakin atu ai kuwa banyi cikakken minti goma ba ya shigo ya ya tsunguna gabana yayi kusan minti goma na dago lafiya nace cikin sanyin murya,hannuna ya kama ya murza "my sweet heart, na lumshe ido tare da zare hannuna tunaninme kikeyi?
,
tunanin big brother okey ni ba kya tunanina haba dai gaka me zai sa inyi tunanin ka shima don baya nan,anya sister har yanzu ba kya sona? haba kana dan uwana in ki sonka ina sonka ainun,zaki aure ni kenan? tambayar tayi min tsauri nace haba dai kana yayan nawa? oh my god me yasa kike wahalar dani kina wahalar min da......"
.
kai dai kaso ka wahalar da kanka domin ban mumafice ka ba na fada maka gaskiya ya dafe kansa wahida gaskiya na ji dadin yadda ya furta sunan kamar a bakinsa aka rada min sunan.
.
Zamu cigaba da safe, inshaallahu

0 comments:

Post a Comment