Saturday, 27 January 2018

BANA KAUNAR KA Page 3,4,5

== BANA KAUNAR KA 3 ==
.
please help me wahida,help me,billahillazi ina tsananin sonki son ki zai iya zama sanadi ajalina.......bana fata kayi hakuri bom boy bani da niyyar yaudarar ka domin sam a yanzu bani da lokacin soyayya asalima ni karatu nasa a gaba ban jira ya kara magana ba na barshi a nan.kwance nake ina tunanin irin son da bom boy ke min tun ina mitsisiya ta har kawo yanzu ba zan taba mantawa ba lokacin muna makaranta primary 5 lokacin ina da shekara tara min fito breakfast a wannan lokacin shekara shida ya shahid baya nan yana kasar Rasha,ina zaune ni da wata yar class dinmu sahura mannir sai ga mahida da gudunta wahida ga yaya shahid wallahi ya dawo gashi can yazo ganinmu na kalle ta shine kike wannan uban gudun kamar wadda akaiwa bushara da kujerar makka??"
.
-------------------------------------------------------------------
.
SAHURA ta cabe ai ina ganin ko kujerar makka ba zata yiwa rawar kai kamar....kar ku takura min ba dole inyi murna mutumin daya tafi tun ina yar mitsitsiyata yace kixo na mike muka jera nai sallama yana zaune a mota na bude na shiga yaya sannu da zuwa ya zuba min ido ko meye abin kallo a jikina,oho nace ya shahid gani kaina rame ko? ai zazzabi nai. WACECE WAHIDA?? wahida yarinyace kyakkyawa ajin farko domin mahaifinsu bafulatani ne mahaifiyarsu ma bafulatanar kamaruce a wajen ta kuma suka samo tsantsar kyau tana da manyan idanuwa masu tsananin haske kamar takadda tana da hanci sannan tana da wadataccen gaashin gira baki sidik zara zaran gashin idanu,karamin baki mai dauke da jajayan lips hakoranta masu daukar hankali tana da gashi sosai sannan tana da kyandiri son bata ki ba amma akwai abubuwan jan hankalin namiji kai a takaice de zan iya cewa irin sune qurun ini na duniya inka samu ka huta,(amma fa idan mai hankakice),hannunta ya kamo taushin hannun kar flourn dangote wanda yakan gamsar da mutum,
.
a hankali yace waya yi miki kunshinnan mom ce tai mana nida mahida duk abin dana lissafa muku wahida nada shi to mahida ma haka domin kamarsu daya ko malamansu basa gane su sai dai banbancin su nutsuwa,mahida tafi wahida rawan kai wahida akwai langwai da jan aji sannan tsiwa ita kuma mahida tsokana.wahida kina jina wahida ta daga kyawawan idanunta ta kalleshi ya shahid ka fasa zama sojan? yayi murmushi wahida kenan kina so in zama? ta girgiza kai ina tsoran soja la! daga yau ki bar tsoron soja domin yayanki ma soja ne yaya amma dai baka harbin mutane ko?
.
ina harbin masu laifi mana.....karararrawar da aka kada ne yasa mahida fita da gudu tana fadin nina tafi wahida sai kin taho wata leda ya dauka yace gashi ku raba na amsa nai masa godiya naceya shahid ka gaisar min da anti zata ji ina tsaye har motarsa ta kule ina shiga class na tadda malami yace zo nan daga ina kike? kan in yi magana mahida ta taso taja hannuna muka wuce malamin ya girgiza kai haka nan yaran suna birge shi.ana tashi direba yazo daukar mu na nemi mahida na rasa koda na tambayi kawarta a ina sai ta ce min suna ofis fada sukayi ita da wata haushi ya kamani ina fita na nufi ofis din ina shiga na gansu tsungune gaban malamai na finciko ta na wanke ta da mari nace wallahi kamar a kunnen abba abba fada ko zaki sani nina tafi in kun gama fadan kya taho kuma wallahi zan cewa direba kar ya sake ya dawo daukarki na juya ina jin guntun kukanta malam ne ya kirani zo wahida ki tsaya ta fada mana gaskiya mallam ba zan iya tsayawa ba zan fadawa ya faruq yazo ya dauke ta to shikenan ku tafi gobe kwa dawo. a mota tace wahida don Allah karki fadawa abba kin ga fa ita ce fa ta fara jana,dallacan rufe min baki da dai ace ban san halinki bane ni dai karki fadawa abba ai kuwa sai na fada masa muna zuwa bangaranmu muka wuce mukai wanka mukayi sallah sannan muka nufi dakin mom da gudu muka karasa muka fada jikinta,
.
==BANA KAUNAR KA 4  ==
.
TA rungume mu tana shafar tattausan gashin kanmu ta kalli mahida waya taba min ke? ba wahida bace ta mareni ke wahida ba antinki bace kike dukanta mon fada sukai duk da haka in kun kuma sai na fadawa abbanku nai raurau,Allah mom na daina tace yauwa autata ya amin gaba daya muka fada masa ya rungume mu yana fadin I miss u la! mahida me akayi miki kila yi kuka? ba wahida vace ta duke ni wahida ashe baki da kunya lalle zan miki bulala yaya tsaya kaji fada fa sukai a makaranta mom ce ta kwala mana kira da gudu muka fito ku zo kuci abinci bana so yunwa ta kama min ku nace mahida jekiki dauko mana abincinmu lalle ma wallahi sai dai in kar aci wacece babba? mom ai dai nice babba ko?
.
mom ta girgiza kai tace kinga mahida aka fara haifa ita a gida ke kuma sai da muka je asibiti mahida ta shiga tsalle na mike ina zumbura baki dakin ya alamin na koma yana zaune yana cin abinci na zauna kusa dashi ya kalleni me kuma aka yi miki? ba mom bace tace a hospital aka haifeni shine kuma abin jin haushi yi hakuri zomuci abinci na dau dan spoon ya janyo flet gassassun kajine ya dinga yagowa yana daura mana kan abinci sai dana ji nai hani an ya zuba min madara me sanyi nasha tuni sanyin AC ya kwashe ninna kwanta bacci me nauyi yayi awon gaba dani Al'amin ya kalleni yayi murmushi yace wahida sarkin rigima kenan.
.
BAYAN SHEKARA TAKWAS lokacin da mukayi candy gaskiya mun fito da sakamako me kyau don haka mun samu kyaututtuka gun yayanmu da iyayanmu a bangaran arabic kuwa munyi sauka yanzu hadda mukeyi. wayar mahida ce ke ta ruru ina dubawa naga yaya Al'amin salamu alaikum wa alaikas salam,yaya al'amin kaki dawowa ko oh sister bako gaisuwa? la! na manta kina so in dawo ko? eh mana to kizo airport da gaske? eh mana to kizo gobe airport da gaske? mahida ta warcewa yar ya amin da gaske in sanar da mom eh ki sanar mata insha Allahu gobe zan dawo shahid ma yayo min waya wai iya suka zauka amma yana legas sukayi sallama ta kalleni ke shahid ya dawo to ina ruwana,ta kai min duka kar kiyi ruwan,da guduna ina fadin wallahi sai na rama dakin ya faruq taje ta kankame shi tana fadin yaya ka mata magana ya buga min haraea tare da fadin ki kazo nan sai nayi boll dake,wallahi sai na rama wayace a dokeni duk kurarinsa sai da naje na kai mata duka ya dauko belt ya shiga lafta min ina kuka mahida ta rike belt din haba yaya me yasa zaka dinga dukata wallahi kai mugune what nine mugu??
.
mahida ta tsunguna kalli yadda kaji mata ciwo sai kawai tasa kuka muka dinga kuka yai mana banza ganin kukan namu bbu sauki sai ya daga niyi shiru kinji wahida ta mom ta shigo wai faruq me kai wa yarannan mom wai danna duki daya shine dayar ma ta kama kuka to me dayar tai maka?? mom fada suke yi shine na mike mom ya faruq ya tsane ni baya kaunata baya son bude ido ya ganni ni wallahi gidan zan bar masa mahida tace wallahi nima bin ki zan yi mom ita tai ta lallashinmu da kyar ta shawo kanmu ya faruq ne ya shigo da gudu mom na shiga uku kunama a dakina oho kai ka jiyo alhakin yaranan ma ai ya ishe ka wahida mahida kuyi hakuri abu kamar wasa har abba ya dawo kunaman nan suna nan yai tai wa abba magiya yazo ya cire masa amma abba yace bbu ruwansa,kuma kar ka sake ka kashe su tun daga wannan lokacin muka samu saukin cin zalin da yake mana washe gari ina zaune dakin ya amin shahid ya shigo ya tsunguna gabana ya zuba min ido na kalli kaina ni ban ga abin kallo ba shi dai haka Allah ya yo shi da kallo yaya me yasa kake kallona?
.
gani nai kin girma kinyi kyau nai murmushi na mike na tafi dakinmu a falo na same ta ita da small boy suna hira abinsu kamar su cinye juna dan sona gaishe shi na wuce daki na kwanta ya amin ya shigo sister me ke damunki? me kaga ni gani nai kin kwanta bbu abin da yake damuna to tashi kije inji bom boy na narke ina faman lumshe ido ni wallahi bacci zanyi ki daure kijr kinji kanwata na mike zan fita ya janyo hannuna dawo kisa hijabi ya fice na kallo kaina riga da wando ne ruwan madara rigar ta dan kama jikina gashi masha Allah kirjina ya tumbatsa na yafa mayafi na fita nai sallama ya zuba min manyan idanunsa na sunkuyar da kai sai daya gama jan ajinsa ganin bani da niyyar magana yace min kin wuni lafiya? lafiya ina antinmu?.tana gaishe ki ina amsawa na mike ina kuma zaki ba lumshe ido ya shahid bacci nake ji ya miko min wata karamar akwati na amsa nace an gode Allah kara mana dankon zumunchi yace amin,nima na gode da addu'arki gare mu Allah ya amsa,ina shiga daki na bude kayan make up masu tsananin kyau da tsada sai dogayan riguna da takalmi da jaka gaskiya na yaba na kuma gode wa yayana bom boy.ina kwance mahida ta shigo ta zauna kusa dani sister ara min kaset din ki nace gata can dauki ta dauka ta dawo ta zauna hello,ta fada cikin kwantar da murya haba my love kai fa kace min gaka nan kuma naji shiru kiyi hakuri my dear kin san akwai cinkosan ababan hawa amma yanzu na iso ina nan shigowa okey Allay ya kawo ka ta sumbaci wayar tare da fadin i love you,i love you na kalle ta waye kuma my love?
.
==BANA KAUNAR KA 5 ==
.
Abba mamy ce yar baba rabi,u da kyau inji Abba mahida ina jinki nima abba na samu wanda nake so haidar din anty da kyau wahida ina jinki tuni nai raurau hawaye ya soma shatata,abba yace ban da kuka cikin rawar murya nace Abba ni karatu zanyi ya faruq yai farat yace ba wani karatunda shahid za,a hada ku ai kuwa na saki kuka ni wallahi bana sosa karatuna zanyi abba yace yi shiru bbu me yi miki dole yadda kowa ya ce ga wacce yake so ke ma sai kin furta sannan zan hada ki da wanda kike so abba kana ji ya faruq yace da ya shahid za,a hada mu rabu dashi bbu me yi miki auran dole ni a ra,ayina bani da niyyar tauye muku hakkinku duk da ina da right din da zan zaba muka maxan da suka dace daku amma nafi son ku kawo da kanku tunda kin zabi karatu Allah ya bada sa,a Allah kuma yai muku albarka amin ya faruq bai so haka ba domin so yai ko ina so ko bana so a aura min bom boy,koda abba ya tara yan uwansa ya fada musu ra,ayin ya,yansu sunyi farin ciki ainun sai dak sun so ace wahida ta zabi shahid ko da abba ya fada musu ra,ayin wahida na son karatu sun yi na,amm sannan sunyi mata fatan alkairi shi kanshi yaji dadin yadda yan uwan nasa sukayi na,am da ra ayin wahidar dama su yake ji domin in sun tubure sai wahidar ta amince da shahid din dole na ta amince ko bata so domin yayansa alh.rabi,u zai iya cewa ba a isa ba dole abi son ransa.
.
bayan kwana biyu da yin maganar ina zaune dainmu ina karatun wani littafin addu'o'i ya shahid yai sallama na amsa ciki-ciki'domin yanzu haushi yake bani ya zauna kusa dani bai magana ba sai da ya shafe kusan minti goma sannan ya kalle ni 'ba ki iya gaisuwa ba ne ?na dago " sorry na manta ka tafi lafiya? gani nan lafiya ba lafiya ba lafiya nan da sauki wahida ina son muyi wata muhimmiyar magana okey ina jinka wahida kin san ina sonki ko? what nikake so? wahida me yasa kike son wahalar da dan uwanki...?
.
ban gane nufin ka ba kin san mahida ta zabi dan uwana a matsayin abokin rayuwarta ina so kema ki sauke ra,ayin son karatu ki amince min billahillazi nayi alkawarin barin ki ki ci gaba da karatunki nai murmushi shahid kenan na fada maka bani da lokacin soyayya kwata-kwata ba zan iya hada karatu da soyayya ba shikenan zan iya jiranki ko nan da shekara goma ne no ka nemi wata kawai wahida kin san kuwa irin azabar da nake ji? oho kai kaso ka don haka bbu abinda ya demeni domin na fada maka gaskiya wahida nifa dan uwankine wahida me yasa ba kya sona in wani hali nake dashi wanda ba kya so dan girman Allah ki fito ki fada min kaga na farko bbu abin dana tsana irin shan taba kai kuma kana shan taba,maganar gaskiya ina zarginka da abubuwa da dama shahid ko ba haka ba dama ance sojoji suna shaye shaye kuma suna neman mata wa'iyazu billahi yace tare da mikewa ya cillo min kati gashi nan na baki cikakken sati kiyi bincike a kaina bayan taba me take sha tabar ma koki ka sank sha amma insha Allahu daga yau na barta har abada yana gama maganar ya fice jiki babu kwari.tunda wannan lokacin na shiga bincike kan bom boy har har sati biyu amma ban ga wani aibunsa ba in ban da da yake samu gun jama,a da dama sai dai wani abu ko kadan bana jin sonsa sai ma hausinsa da nake kara jiba kamar in na tuna shi soja ne kuma mugu ne na karshe domin bana mantawa ina karama mugun tsoransa nake innai abu aka ce za a fada wa shahid na kanyi kuku domin ban bashi da wasa gashi da girman kai rashin son magana yanzu ne fa da yake sona yake sakar min iska ni na san yana aurata zai daina sakar min fuska koda dama ance matar soja sai hakuri.kamar kullum ina zaune ya shigo da sallama tun kan ya karaso kamshin turaransa ya cika dakin kai gaskiya ina son turaransa haka nan kamshin kan sani farin ciki ko da kuwa ina cikin bacin rai gashin ban san sunan turaran ba bare in siyo gashi ina ganin kamar zubda ajine in tambaye shi sunan turaransa,
.
kamar kar in amsa sallamar sai kuma na tuna girman sallama da darajarta sai na amsa ciki ciki na janyo remote na kunna T.V domin ta taya shi hira na mike domin in bar masa dakin suyi hirar da T.V caraf ya kamo hannuna sai naji hannunsa dumi ga wani irin taushin ji nai kamar in kwace hannun don wani irin sanyi dadi naji yana ratsa zuciyata na daddage na tofa masa yau a hannu ya daga hannun a tunanina mariina zai ko ya goge min yawun a jikina amma sai naga akasin haka domin ganina yasa harshe ya lashe yau din yace baki san yawunki yafi ice cream ba a gurina na yamutsa fuska ashe kai kazami ne??

0 comments:

Post a Comment