Friday, 19 January 2018

'Yar Mafiya Part 4 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI


'YAR MAFIYA Part 4
.
Yasirah cikin zuciyarta cewa take“tabbas Yasar ya had'u irin had'uwar da kowacce mace ke fatan malakan miji kamar sa, had'uwa bana wasa ba ni sai yau naga yafi min ko yaushe kyau da kwarjini gashi wasu na farauta rayuwanka d'an uwana kai nake so ada gashi yanzu ina jin abubuwa game da kai da dama alokacin da wasu ke neman yi mana sha maki da juna".
Yasar shima a gunsa abun haka yake baran shida tun haihuwar Yasira ya ke tsananin sonta matsalar d'aya ce abunda ta aikatawa". Bai san lokacin da ya saki ajiyar zuciya ba kafin ya sake duba Yasirah ta b'ace ba labarinta shi yanzu abun ma tsoro ya fara bashi sai da ya 'yan waige-waige bai ga kowa ba da gudu ya tayar da mota ya bar gun ko da ya isa gida yamma tayi sosai abincin ma kasa ci yayi tunanine kala-kala a zuciyarshi sai da aka kira sallah ya fita sai bayan isha'i ya nufo gida zuciyarsa cike da tsoro da ikon yau yashigo lafiya ba abunda ya gani har kusan tara na dare hakan yasa yayi shirin kwanciya ya kwanta.
Cikin wani surkukin daji, babu gida gaba babu gida baya Yasar ya tsinci kansa.Take garin ya juya masa, sama tai jajjur a kasa kuwa wasu irin macizaine nannade da kafaffunsa ya kasa katabus wani nannauyan naushi aka kaiwa kuncinsa a sukwane ya kauce dukan yafi iska. Wata muguwar bahaguwar murya ta ziyarci dodon kunnuwansa, cikin rashin zato. 
"Yasar ka fita hanyar Yasiraht, domin ita din mallakin shugabanmu ce kuma dokar kungiyarmu babu aure".
"Bazan fita ba domin Yasiraht rayuwata ce".
Ya fada da kakkausar murya mai amo, take wata irin dariya ta soma karade kunnuwansu.Cikin tashin hankali ya sa hannu ya toshe kunnuwansa, bai auneba aka soma jansa wani wawwakekken rami ya na ji yana gani ya kasa kubuta.Cikin bazata ta bayyana a wajan cikin sakan guda ta warceshi suna hadda ido ta watsa masa harara cikin fushi tace.
"Mudin kana sakaci da addu'a kana tare da gaggarin rayuwa".
Firgiggit ya tashi, zufa, zazzabi tashin hankali sukai masa rufdugu lokaci guda.Ya daga kai ya kali agogo, karfe biyun dare cike da tsoro ya dire ya dauro alwala ya soma gabatar da nafilfili.
Sai goshin asuba ya dakata ya dora da karatun alkur'ani mai girma, ana kiran asuba yai raka'atul fijir yai sallah ya dan kwanta.
Washegari ya tashi da karfin zuciya yana jin nishadi a ransa sossai, karfe takwas ya fito cikin shirin fita.A daining sukai clash da Yasiraht suna hada ido wani abu nannauya ya daki zukatansu Yasiraht ta lumshe ido batare da ta sani ba.Cikin zuciyarta tace "Allah ya yi hallita" tai saurin dauke idonta daga kansa tace"morning broth" bai tanka ba ya wuce abinsa.Tai murmushi tana jinjina yadda ya shareta.
Yana fita yaje ya gaida su Abba nan Abba yake
tambayansa “ya shirye-shiryen biki?". Cike da jin
kunya Yasar ya amsa da “Alhamdulilah! Abba mu
kai". Abba ya ce“madallah! Allah yayi albarka a
kara kula katashi ka tafi aiki kar ka makara".
Cikin ladabi ya mik'e ya fita motarsa ya shiga ya
nufi office cike da jin ni shad'i.
aiki yayi sosai sai da lokacin sallah yayi ya fita
yaje masallaci bayan ya idar da sallah ya nufi
office kenan suka had'u da Nawas cikin zolaya
Nawas ya ce“Ango! Ango!! Kai tun ba'ayi bikin
bama naga kasha mai sai wani shek'i kake yi
dan Allah miye sirri?". Cikin sigar zolaya da raha
yayi maganan.
Yasar ya ce“ sirrin da ka gani Amarya na kusa
dani ya bazanyi mai k'o ba". Shima cikin sigar
wasa ya mayar masa da amsa.
Nawas ya ce“maganar gaskiya ya kamata mu
tsaya mu tsara biki yau saura sati uku biki amma
banga kana wani shiri ba?".
Yasar ya ce“shiri ai nakune kune manyan abokai
nawa akai min ne kawai".
Nawas ya ce“ai baka isa ba dole mumaka 'yan
jike-jike sabida ka dawo tuzuru kaga kar kaje
ka....“.
Yasar ya ce“kai ka sani ni lafiyata lau aha zam-
zam nake".
Haka suka yita raha daga k'arshe Yasar ya ce“ka
bar magan bikin nan inaga sai a weekend sai mu
tsara komai in Allah ya kai mu".
Nauwas ya ce“ba matsala Angon Yasirah kuma
'Ya'yan Abba". Da haka kowa ya nufi office
d'insa basu fita ba sai yamma da'aka tashi daga
aiki kowa ya nufi gida.
Yasar ya na zuwa gidan Abba ya wuce don haka
kurum yaji yana son ganin Amaryansan yana
zuwa ya ajiye mota ya shiga gida da salalmansa
ba kowa a falo hakan yasa ya wuce d'akinta.
K'ofan ya tura ya ganta tana bacci sai murmushi
take yi a hankali ya tako har zuwa bakin gadon
ya zauna a d'an k'aramin kujeran da ke bakin
gadon kalon ta yakeyi cikin so da k'auna bai san
lokacin da bakinsa ya fara furta “Yasirah ina
tsananin k'aunarki gan-gan jikina mallakin kine a
duk lokacin dana kalli kyakyawan fuskanki nakan
tsinci kaina cikin nishad'i wansa bazai misaltu
ba".
A hankali ya sauk'e numfashi tare da lumshe
idonsa ya bud'e ya cigaba da cewa“ban san mai
yasa baki sona ba kuma kika fad'a wani irin hali
wanda nagasa a hak'uri akanki ina matuk'ar
kaunanki Yasirah". Hannuta ya kama ya mata
kiss ya fita abunsa.
Rash
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji biki ya
rage saura sati daya,duk kauce kaucan Yasiraht
saida ta tsaya ta saurari Yasar suka shirya
lamarin bikin.Duk ta rame ta fita hayyacinta, ga
yawan barazanar Samar da kungiya da take
samu.Ga rama Najwa ta lafaffa mata ganin zata
auri wani ta barmata Samar.Sai dai a wani fannin
tana taya Samar kishi domin samun shiga
wajansa, tare suke yakin.Rana bata karya sai dai
uwar diya taji kunya, cikin hukuncin ubangiji aka
soma shirye-shiryan biki gadan-gadan babu kama
hannun yaro.
Ranar Alhamis sukai kamu, a babban dakin taro
na Hajiya Rash dake Bauchi.An shirya wajan ya
kawatu sossai, yara matasa aka samu sukai
shigar yoruba kowace tasha murjani ta tamke
kugu tamkar ahlin emeka su goma shabiyu ne
suka saka amarya a tsakiya suna tafe suna
watsa mata wani hadin turare mai hade da furani
sunai mata kirari.Har zuwa tsakiyar dakin taron
wanda ya kawatu da shimfidu kilisai da tum-tum
tamkar diyar sarauta.Yasiraht sanye take cikin
wani rantsatsan swice kalar blue light, an mata
head pink kafarta flate shoe shima pink sai
mayafi da aka lulluba mata kalar azurfa mai
ratsin golden.Fuskarta ta kawatu matuka,sai
sheki take tana zama ta dago kai dam! Gabanta
ya fadi saboda hango Najwa da Samar cikin
tawagar biki tai saurin dauke kanta tana
mamaki.Batai auneba yara matasa kimanin
mutum sha biyu suma suka sako ango gaba,
tamkar yadda akai mata. Dukkansu suma suna
sanye da kayan yoruba da izga da murjani nan fa
waje ya dauki tafi ni kaina sun burgemu har Rash
ta dubeni tace.
"Cwt Sanah nima haka zan yi da bikina amma
shigar Larabawa".
Na saki murmushi nace "ni kau shigar Fulfulde ko
Kanuri zan yi".
Mukasa dariya muka maida hankali kansu, a
hankali Malama Husnah Muhammad Inuwa ta
bud'e taro da addu'a ta soma lacture kan
biyayyar aure.
_"Bisimillahir-rahmanir rahim yake kawata yata
yayyata kakkata, da duk wata mace dake wannan
waje. Inaso ki bude kunnuwanki ki ssurarreni,shin
kina cikin sahun mata nagari? Idan ma bakya ciki
saurarreni domin zama abar alfaharin mijinki in
kuma kina ciki kikara kaimi. WACECE MACE
TAGARI?.Mace tagari itace takan yi kokaarin
tazamar wa mijinta aljannarsa ce, batason taga
gazawarta a idanunsa,don haka takan yi farin ciki
idan taga murmushinsa takan damu matuka in
taga fushinsa koda badaita yake ba.Bata jinkiri a
wajen abinci, kuma ta iya dafawa batare da
almubazzaranci ba, itace amintacciyar abokin
shawararsa, mai iya rike masa sirri, bata yarda
wani yasani ko waye kuwa, sannan ga taimako._
_Mace a kullum mai sanyaya raice ba mai jiran a
sanyaya mata ba, farin cikin maigidanta shi ne
nata, komai yabata takan gode, ga fadin yi haquri
kamar nunfashinta.Tana fama da baqin ciki
amma tayi dariya,tanajin zafin abin da mijin yayi
mata amma tayi tunanin yadda zata faranta
masa rai._
_Aure sunna ce da Annabawan Allah duk
sukayi,ya kamata mugaya matansu suka zauna
dasu ???Bai dace ba kowane mutum ya riqa jin
matsolinki da mijinki, sai in abin yafi
qarfinki.Mace tagari mijinta shine komai, koda bai
iya soyayya ba.Bata zama a gabansa ko gefensa
saida yardarsa,takan cika da ladabi aduk inda
yake, takan nuna masa qauna sosai ta gaskiya
ce ko qirqira ce kawai.Idan zai fita qafarsa
qafarta, idan taji ya shigo ta tarbo shi cikin fara'a
da annushuwa, nan da nan tafesa turare ta
shafawa lallenta mai yafito sosai ta danyi
kwaskwarima, ta canja murya tareda yawan
murmushi da fari.Idan zai fita addu'a, in yadawo
godiya da murna dafarin ciki._
_Asma'u bnt Kharijatul Furaziy take cewa 'yarta
ranar budar kanta cewa:ke cewa 'yarta ranar
budar kanta cewa:"Yanzu fa kinfita daga sheqar
da aka kyankkyashe zuwa shimfidar da baki
santa ba, da abokin tare da baki san shiba, ki
zamar masa qasa sai ya zamar miki sama,
kizamar masa shimfida zai zama miki turaku, ki
zamar masa baiwa, zai zama miki bawa, kar ki
nace wajen neman abubuwa domin karya gujeki,
kar kiyi nisa dashi domin karya manta dake, idan
ya matso, ki kusance shi, idan yaja jiki, kema ki
dan ja da baya, amma ki kiyaye hancinsa da
kunnensa da idonsa, karya shinshini komai a
wurinki sai qamshi, kar yaji komai sai
kyakkyawan abu, kar yaga komai sai wanda zai
burge shi.Girki, mahalin kwanciyya girmama
danginsa mahaifiyarsa haka abokansa.Tattalin
kayansa tare da kilace masa su, kula da
damuwarsa insha Allahu zai yi farin ciki
dake".Dan uwana maigidanta shawara zan baka,
ga amana zamu baka a cikin hannunka.Ci da
shanta da tufafi suna hannunku,kyautattamata ka
rike amana insha Allah ka zamo mai kauna zatai
zaman lafiya_
Bayan an gama aka soma rabon abubuwan
kayatarwa, lalle turare littafan addu'o.Mazan
suka watse aka soma rawar gada.Yasiraht ta
saki ajiyar zuciya ganin an kare lafiya su Najwa
basu tada rigimar komai ba.
Washegari aka daura aure da safe da yamma
akai dinner zuwa dare aka soma haramar sadata
da dakinta.
Sanah
Rash.
Tunda aka soma shirye shiryan kai amarya
Yasiraht ta rasa nutsuwarta ga wata faduwar
gaba da take mai tsananni. Da magarba aka
soma yimata mitar taki shiryawa tilas ta soma
niyyar shiga wanka lokacin data fito babu kowa
dakinta ta lumshe ido tana tuna kalaman Yasmin.
"Aunty Yasiraht nima inaso ayi biki a gidanmu,ayi
taro musha shagali".
Hawaye mai zafi ya zubo mata, tai murmushi
tana furta.
"Yasmin saina dauki fansa jininki yantacene'.
Shigowar kanwar mahaifiyarta yasa tai saurin
gogge hawayan ta hau shafa mai. Kafin mintuna
goma ta shirya aka wuce sashin mahaifinta da
ita.
Nasiha sossai mai ratsa jiki yai mata haka ma
mahaifiyarta, daga nan aka nufi wajen mota da
ita wani gunjin kuka Yasiraht take musamman
dataga dagaske nisa zatai da gida. Haka aka
sakata a mota zuwa gidanta dake unguwar
nassaraea law cost.
Yan kai amarya kowa ya watse sai ita da
kadai,kamar almara bangon dakinta ya soma
darewa suka dunga biyo layi a shirye a shirye
harsu ashirin da hudu cif.
Kowannansu sanye cikin jajjayan kaya da bakin
dankwali, hannunsu rike da kokkouna cike jini
suna kallonta.Najwace kan gaba tana murmushin
mugunta.Samar na gefe a tsakiyarsu yaci kunu
yana dubanta,ya tsuke girar sama da kasa yana
muzurai ya dubeta da kakkausar murya.
"Yasiraht kin bata mana tsari kin cutar da
zukatan yan kungiya, yau bandan inasonki ba
saina hallakaki amma zamu dauki fansa kan
mijinki kwatankwacin kuntatta mana"
Bat suka bacce saboda shigowar Yasar da
abokansa, nan akaita barkwanci Nawas yai musu
nasiha sukai salama ya ta
Yasar ya je musu rakiya yana cike da farin ciki yake hawar matakalan har da d'an gudunsa. Yana isa falo ya tarar tashiga d'akinta kasancewar lokacin k'arfe goma da kusan rabi a hankali ya taka har zuwa d'akin ya saka hannu zai bud'e k'ofa  sai yaji kamar ana kwan kwasa gareji ya share zai bud'e d'aki sai yaji yanda ake buga garejin kaman za'a cire a jiyeshi a gefe.
Cikin b'acin rai da fushi ya nufi fita ya waye haka mai buga k'ofan don shi ya gama tanadin bazai fita ba ya shigo kenan ya sanya k'afarsa a step na farko a kattt! Wutan gidan gaba d'aya ya d'auke tare da wani irin k'ara mai shiga kunne a hankali uuuuuwu! Irin karannan wanda zakana jinsa cikin yana yin abun tsoro. Duhu sosai yake gani baya iya ganin hannuda bare fararen kayan da ke jikinsa duk sun zama baki.
Cikin dauriya ya sauk'a zuwa gate yana fitow haraban gidan yaji bugun k'ofan ya tsananta, sauri ya k'ara abun mamaki yana zuwa aka daina kuma ba mai gadi a gun k'aramin k'ofar ya bud'e ya leka waje amma ba kowa a ciki da sauri ya dawo ya mayar da gate d'in ya rufe.
Har lokacin da ya dawo gun d'akin mai gadi baya nan a hankali yasoma tafiya yazo dai-dai zai shiga cikin falo sai hango wani yayi da fararen kaya yana tafiya zai nufi garden kuma wannan yana yin jikin bana mai gadi bane don yayi tsayi da yawa ga shi ko fiskansa baya gani fararen kaya sun b'oye shi.
Da sauri ya ce“Baba Mai Gadi yaji bai amsa ba kuma ya ci gaba da tafiya ganin haka ya soma binsa da sauri kafin ya cimmasa har ya b'ace sai da ya duba gurin bai ga kowa ya juyo sai ya sake ganinsa ya nufi cikin gida mai fararen kayan da sauri ya sake binsa.
Har yanzu wannan k'aran yana jinsa da sauri ya fara haurawa mata kalan yana bin mai farin kayan ha hau matakala sai yaji an rike masa k'afa cikin sauri yasaka hannu agun sai jin hannu yayi amma ba alamar mutum da sauri ya feta k'afarsa sai yaji an sake sa da gudu ya haura sama ya shiga falo.
Yana zuwa hakki yasoma yi ya d'an jin gina da k'ofar gashi da duhu gun ga wayarsa ya manta a motarsa ba kuma toci bare ya haska, sai yaji ihun mai gadi da k'arfi yana kiransa yazo ya tai maka masa.
Cikin tsoro ya soma bud'e tagan don ya lek'a ya ga miye  amma yaki bud'uwa gashi ihun sai k'ara yawa yake yi, da sauri ya soma sauk'owa don ya tai maka masa bakin Yasar ya kasa furta ko da kalma d'ayabna addu'a.
Yana isa bakin gate yaji ba kukan kuma ba mai gad'i a gun yana 'yan dube-dube sai yasake jin ihunsa a cikin gida da sauri ya haura saman ya zo dai-dai k'ofar shiga falonsu ya yi k'aro da wani abu kamar katako amma dogo ne da tsayi sun kuyawa yayi ya fara lalub'e cikin zuciyarshi ya ce“wannan kaman ```Makara``` ne cikin ```Makaran``` ya taba yadi ko da ya d'ago yadine fari kal kaman likkafani ko ince likkafanin ma.
Tsoro ne ya fara kamasa ya soma ja dabaya gani yayi ```Makaran``` yana binsa ga yadin likafanin sai k'ara haskawa yake yi a hannusa.
Cikin wata irin murya mai firgitarwa ya ji ana cewa“ ```Yasar``` kayi gan-ganci shiga hurumin da bana ka ba kasani yau kwananka ya k'are nine nan zani ```ALAJALINKA".``` ido ya zaro sai
Cikin rawan murya Yasar ya ce“ waye kai dan Allah?". Sai da akayi wani dariya mai amo sanan ya ce“nine nan ```ALJALINKA! AJALAINKA!! ALAJALINKA NE!!.``` hahaha!!!!". A ka ci gaba da dariya Yasar na ganin haka bai san lokacin da yayi wani tsalle ya tsallake makaran ya nufi cikin falo da gudu.
'Dakin da ke farkon shiga falon ya shiga yana shiga sai yaga an kawo wuta nan yaga abu a lulub'e da farin kyalle wanda zamu iya kiranshi ```likkafani``` an rufe abu dashi ga jini ya b'ata shi da sauri cikin tsoro ya je ya bud'e wa zai gani Baba mai gadi ne wance matatce a cikin jini da baya yasoma ja jikin tsoro dun ya gama razana.
Samar ya kalli Najwa ya ce“ki je gun Yasirah kiyi ta janta ban yarda ki cutar da ita ba kin san ina matuk'ar sonta ni zanje na gama da Yasar". Yana gama fad'in haka ya b'ace bat kamar ba shi a gun.
Samar ne ya bayyana a gabansa yana dariya ya ce“kad'an da ga aiki na". Ya nuna kansa da d'an yatsa ya ce“kai ma yanzu zamu gama da kai".
Yasar ya soma bashi a hak'uri batare da b'ata lokaci ba Samar ya ce“da ka bar b'ata bakinka ko ka manta irin jan kunne da mukayi ta maka da tsoratarwa kala-kalq amma ka share don haka yau ba sassauci.
Wani sanda ya soma nuna Yasar dashi take wata irin iska mai k'arfj tayi sama dashi tasoma jujuya shi a saman d'akin tana buga kanshi da bango take jini ya fara zubowa tamkar an kunna famfo.
*33*
Samar na b'acewa Najwa ta kece da dariyan mugunta ta ce“daman wannan ranan nake jira tazo ranan d'aukar fansa ta d'aure fiska ta ce“ni Najwa ```Bana yafiya bana manta ranan d'aukar fansa".``` tabbas Samar kayi gan-ganci barina da Yasira a ranan ta yau". Tana gama fad'in haka ta b'ace bata bayyana ko ina ba sai d'akin Yasirah.
Amarya Yasirah ganin ango ya fita rakiya nan ta soma rage kayan kyale-kyalen dake jikinta zoben gwal ta cire sannan tashiga bayi ta watsa ruwa tana fitowa ta shafa mai tasaka kayan bacci riga da wando masu d'an kauri bayida shara-shara sosai sabida yanayin huturu da ake ciki.
Najwa ne ta bayyana gaban Yasira nan ta kalleta ta ce“kee Yasirah ina mai farin cikin sanar da ke ranan dana ke jira tazo ki sani ina tare da Mijinki Yasar Yanzu haka kuma yana gab da mutuwa". Tana fad'in haka ta b'ace.
Yasirah na jin haka itama tayi siddabaru ta b'ace nan ta hango Najwa ta nufi wani jeji cikin hanzari ta bita da kyar ta isota tana zuwa taha bata gun sai can ta hango wani k'aton maciji yana kawo mata hari nan ta gane Najwa ne itama ta rikid'a ta dawo wani k'aton kububuwan maciji nan suka fara fafatawa cikin salon tsafi dankwarewa. Sun d'au kusan awa d'aya da kyar Najwa tayi nasaran cire wannan babban Zoben sihirin da ke hannu Yasirah wanda dashi ne yake sarrafa mayan siddabaru da tsafin da takeyi.
Najwa tana saka zoben a hannuta ta kece da dariya ta ce“tababs yau buri na ya cika yau zan b'atar dake a doron k'asa sannan kuma Yasar yana gun Samar ya gama dashi". Nan ta bayyana mata hotonsu Yasirah na ganin haka ta saki k'ara ranta ya b'aci gashi ba halin yin wani yink'uri.
Najwa ta nuna Yasirah da wannan zobe tasoma wasu surkulle. Kuma in har wannan surkulen ya kama Yasirah to narkewa zatayi ta k'one q gun ta zama tarihi.
Shin masu karatu
Samar yana nasaran kashe Yase kuwa?.
Shin Najwa na cimma burinta akan Yasirah kuwa?.
Don jin wannan amsoshin sai ku biyo mu.
Take Najwa ta soma wani irin surkule tana karanta wasu dalamusan tsafi batai aune ba ta nemi Yasiraht ta rasa.Nan ta soma yunkurin nemanta amma babu alamunta hankalinta yai mugun tashi ta bace saboda yadda tsafin ya soma cin jikinta.
Yasiraht bata bayyana ko inaba sai gidanta, nan ta riski Yasar kwance shabe-shabe cikin jini.Hankalinta yai mugun tashi nan ta dauki waya tana kuka ta kira mahaifansu a rikice suka karaso gidan.Sai dai tun kafin karasowarsu hankalinta yai mummunan tashi kan ya zatai da gawa maigadi.Ana haka Samar ya bayyana ya dauke gawar ya tafi da ita,tana kallonsa ya fice taji dadi sabida batasan mizata cewa police ba kuma dole ta zamo abar tuhuma. 
Cikin tashin hankali aka dauki Yasar zuwa asubiti,babuma lokacin tambayarta ya hakan ta faru.Dr yaita fada sabida yaga yamusu matsalarsa, to harzuwa wayewar gari baima farfadoba hankalinta ya tashi sossai duk tayi zuru-zuru.
Can Dr ya fito duk ya hada gumi, da sauri Yasiraht ta tare shi"Dr lafiya jikin nasa ya farfado?".Tausayinta ya kamashi yai murmushi, "i'am sorry to say Yasiraht bai farfadoba kawai da bugawar kirjinsa muke gane yana da rai kansa ya bugu sossai". Abu daya ta ayyana Yasar ya rasa tunaninsa wanu giggitacan ihu ta saki ta zube sumammiyya a rikice iyayan sukai kanta bata ko motsi Najwa na gefe tana dariya bata an karaba Samar ya bayyyana ya shaki wuyanta yai sama da ita.
Bai dire ko'inaba sai cikin wasu mugayan tsaunuka, take yai nuni da hannunsa wani dutse ya fashe wasu sarkoki suka bayyana ya daureta  a jiki tamau tamkar daurin goro.Yai nuni kujera ta bayyana ya hau kai ya dora daya kan daya yana murmushin mugunta.
"Baki da mutunci Najwa, zanyi maganinki".
"Kayi kuskuren bani amanar Yasiraht walahi saina illatata".
Bai tanka ba ya wuce, ya bari ana azabtar da ita.Kwanan Yasiraht uku a gadon asibiti bata magana sai kuka Yasar kuma kwanansa hudu bai farfadoba hankalin kowa ya tashi musamman da likitoci suka bada tabbacin in ya kai kwana biyar komai zai iya faruwa..
...
Take Najwa ta soma wani irin surkule tana karanta wasu dalamusan tsafi batai aune ba ta nemi Yasiraht ta rasa. Nan ta soma yunkurin nemanta amma babu alamunta hankalinta yai mugun tashi ta bace saboda yadda tsafin ya soma cin jikinta.
Yasirah na hango a hannu wata Tsohuwa mai shiga ta kamala ko da na kalli k'afar matan kwafato ne orin na doki gashin kanta fari k'al kamar auduga. Cikin ke keb'antacan daji mai cike da ni'ima, take tafiya da yafira a kafad'arta sai da tayi tafiya mai nisa naga ta tsaya a wani gili wanda namun daji irin su Kura, Damisa, Zaki, B'auna su suke mata gadin gidanta.  Katangan gida na alfarma da gani kasan ginin aljanu ne saboda bene ne hawa uku komai akwai a ciki. Tsohuwan ne ta kai Yasirah wani d'aki ta kwantar da ita gashi ko motsi bata yi da alamar kamar ba numfashi a tare da ita.
Washegari da safe aka aiko a kawo musu abinci, dan 'yar aika tana shigowa ta haura sama shuru taji kamar alaman bakowa haka kurum taji gabanta na fad'uwa, da sallamanta nan tayi karo da Yasar kwance cikin jini ko motsi ba yayi.
Cikin tashin hankali ta fita da gudu ta sanar ma driver tare suka shigo ganin halin da Yasar ke ciki ya d'aga waya ya kira Abba ya sanar masa cikin tashin hankali ba tare da b'ata lokaci ba sula iso.  Aka dauki Yasar zuwa asubiti, babuma lokacin tambayar ya hakan ta faru.Dr yai ta fada sabida yaga yamusu matsalarsa, to harzuwa wayewar gari baima farfadoba hankalin Hajiya Nafisa ya tashi sossai duk tayi zuru-zuru.Sai lokacin suka soma bincikar ina Yasiraht asibitin suka baro Yasar  kwance suka nufi gidan.
Samar ne ya bayyana gaban Najwa yana huci bai saurareta ba ya sureta. Bai dire ko'inaba sai cikin wasu mugayan tsaunuka, take yai nuni da hannunsa wani dutse ya fashe wasu sarkoki suka bayyana ya daureta  a jiki tamau tamkar daurin goro.Yai nuni kujera ta bayyana ya hau kai ya dora daya kan daya yana murmushin mugunta.
"Baki da mutunci Najwa, zanyi maganinki".
"Kayi kuskuren bani amanar Yasiraht walahi saina illatata".
Bai tanka ba ya wuce, ya bari ana azabtar da ita. Kwanan Yasar hud'ua gadon asibiti bai san inda kansa ba kuma kwanansa hudu bai farfadoba hankalin kowa ya tashi musamman da likitoci suka bada tabbacin in ya kai kwana biyar komai zai iya faruwa.. 
Take Najwa ta soma wani irin surkule tana karanta wasu dalamusan tsafi batai aune ba ta nemi Yasiraht ta rasa. Nan ta soma yunkurin nemanta amma babu alamunta hankalinta yai mugun tashi ta bace saboda yadda tsafin ya soma cin jikinta.
Yasirah na hango a hannu wata Tsohuwa mai shiga ta kamala ko da na kalli k'afar matan kwafato ne orin na doki gashin kanta fari k'al kamar auduga. Cikin ke keb'antacan daji mai cike da ni'ima, take tafiya da yafira a kafad'arta sai da tayi tafiya mai nisa naga ta tsaya a wani gili wanda namun daji irin su Kura, Damisa, Zaki, B'auna su suke mata gadin gidanta.  Katangan gida na alfarma da gani kasan ginin aljanu ne saboda bene ne hawa uku komai akwai a ciki. Tsohuwan ne ta kai Yasirah wani d'aki ta kwantar da ita gashi ko motsi bata yi da alamar kamar ba numfashi a tare da ita.
Washegari da safe aka aiko a kawo musu abinci, dan 'yar aika tana shigowa ta haura sama shuru taji kamar alaman bakowa haka kurum taji gabanta na fad'uwa, da sallamanta nan tayi karo da Yasar kwance cikin jini ko motsi ba yayi.
Cikin tashin hankali ta fita da gudu ta sanar ma driver tare suka shigo ganin halin da Yasar ke ciki ya d'aga waya ya kira Abba ya sanar masa cikin tashin hankali ba tare da b'ata lokaci ba sula iso.  Aka dauki Yasar zuwa asubiti, babuma lokacin tambayar ya hakan ta faru.Dr yai ta fada sabida yaga yamusu matsalarsa, to harzuwa wayewar gari baima farfadoba hankalin Hajiya Nafisa ya tashi sossai duk tayi zuru-zuru.Sai lokacin suka soma bincikar ina Yasiraht asibitin suka baro Yasar  kwance suka nufi gidan.
Samar ne ya bayyana gaban Najwa yana huci bai saurareta ba ya sureta. Bai dire ko'inaba sai cikin wasu mugayan tsaunuka, take yai nuni da hannunsa wani dutse ya fashe wasu sarkoki suka bayyana ya daureta  a jiki tamau tamkar daurin goro.Yai nuni kujera ta bayyana ya hau kai ya dora daya kan daya yana murmushin mugunta.
"Baki da mutunci Najwa, zanyi maganinki".
"Kayi kuskuren bani amanar Yasiraht walahi saina illatata".
Bai tanka ba ya wuce, ya bari ana azabtar da ita. Kwanan Yasar hud'ua gadon asibiti bai san inda kansa ba kuma kwanansa hudu bai farfadoba hankalin kowa ya tashi musamman da likitoci suka bada tabbacin in ya kai kwana biyar komai zai iya faruwa.. 

Sai can dare Hajiya ta soma tambayar ina Yasiraht lamarin daya haifar da kace nace ita ta zauna mahaifinta ya nufi gidan.Tunda suka shiga shi da Nawas gabansu ke faduwa harzuwa cikin falon nan suka tsaya turus sakammakon ganin gawar Baba maigadi cikin kaduwa sukai kansa harya soma bugawa da sauri Nawas ya kai hannu zai buda Daddy ya rike shi karka taba kira police.Kafin mintuna uku yaiwa abokinsu waya nan da nan aka shigo tare da magunguna akai amfani dasu aka dauke gawar harta soma bugawa.Nan suka hau neman Yasiraht babu ita babu dalilinta sai kayanta wanda aka kawota dasu jiki a sanyaye suka fito daganan aka nufi policestation akai refort babu amarya babu dalilinta.
Hankula ya tashi sossai neman Yasiraht ake amma amsar d'ayace ba'a ganta ba lamarin daya dugunzuma hankalin danginta sossai ga Yasar rai a  hannun Allah kwata-kwata bai san wanda yake kansa ba.Tsayin kwana biyar ana nemanta, nan iyayanta suka fida tsamanin ko an sace ta ne nan da nan suka buga bayanai a jaridu da mujalu tare da makudan kudi kyauta ga wanda ya samota.
Najwa ta shiga matsanancin tashin hankali, daboda tunda Samar ya daureta ya tafi bai waiwaye ta ba hakan yai matukar tada mata hankali duk wani yunkurinta na tsinka sarkokin tsafin da suka daureta abun yaci cura duk ta rame ta kwantsame ta fita hayyacinta yunwa da kishirwa sun soma galabaitar da ita kwatsam Sabir daya daga cikin yan kungiyarsu wanda ya kasance daga Samar sai shi ya bayyana ya kwance ta suka bar wajan. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment