Friday, 19 January 2018

'Yar Mafiya Part 3 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI


Haka Yasiraht ta cigaba da rayuwa tsakanin mafarki da zahiri, a haka suka gama jarrabawar gwajin shiga aji shida sukai hutu suka koma gida.Komawarta gida babu abinda ya ragu tsak'aninta dasu Samar kullum iyayanta na ganinta amma da zarar dare yayi Samar kan zaagayo ya d'auketa.
Tsakanita da Yasar kuwa babu jituwa ko kad'an,shi yana mata kallon azalluma ita kuma kallon ya takura mata.Hakan ya jawo sab'anin ra'ayi sossai tsakaninsu ko gun cin abinci sun dingi fad'a kenan tamkar mage da kare a haka taci hutunta saura sati biyu ta koma wani mummunan lamari ya auku gareta wanda ya tsaya mata arai.
Kwance suke kan makeken gadon da yake mallakinta.Tun dawowarta tare suke kwana da Yasmin, misalin k'arfe biyu na dare Samar ya bayyana a gefan gadon yana murmushi.Gabanta ya tsananta fad'uwa ta aro juriya ta yafa ta kalleshi.Murmushu sukai wa juna cike da tsantsar kulawa.Bai wani d'auki lokaci ba ya dubeta"Yasiraht zuwa nai in gaya miki muna buk'atar jinin Yasmin nan da gobe kiyi tunani".A fusace ta mik'e "ban yadda ba Samar" "ba damuwata bace yardarki ko akasinta".Fu! Ya bar wajan yana huci.
Washegari haka ta yini sukuku da'ita babu abinda take asassawa kanta, Hajiya Nafisa ta lura da yanayinta tai ta janta a jiki amma bata gaya mata damuwarta ba.Yasar ne ya daukesu zuwa shooping bayan magarba suka nufi hanyar zoo road.Cikin nutsuwa yake tuk'in har suka k'arasa, kwata-kwata hankalinsu nakan siyayyar da suke yi sai jin k'arar Yasmin sukai ta fad'i ta kakkafe jini na bin kofiffin hancinta. Karaf ta hangi wulgawar Najwa ta bacewa ganinta, wata giggitafiyar kara ta saki tai kan Yasmin bata ko numfashi take Yasiraht ta zube sumammiya.
Ku biyo mu
[8/8, 8:44 PM] Sanah S Isma'il Matazu:
Yasar yayo kansu cikin rud'ewa ya d'aga Yasmin ganin yanda jini ke zuba wasu mutane ne suka taimaka masa suka d'aukesu sukai mota cikin rudu ya shiga ya ja motar suka nufi T.H ko da sukaje emergency aka shiga da su likitoci sun dad'e akansu kafin babban su ya fito fiskansa ba alamar murmushi, Yasar ya taso da sauri yazo gun Likitan ya ce"Likita ya jikin su jinin da ke zuban ya tsaya?". Cikin sanyin jiki Likita ya dafa Yasar ya ce"Babban ta farfad'o yanzu haka". Yasar ya ce"Alhamdulilah!". Likita ya sake duban Yasar ya ce"kai musulmi ne kuma ko da yaushe ana so musulmi ya kasance mai hakuri da juriya da amsan kaddaransa, sannan Ubangiji yana mana kyauta wanda zamu saba mu shaku da kyautarsa rana d'aya shi da yafi muson abunsa sai ya d'auke".
Likita ya nisa ya cigaba da ce wa"inason kayi hakuri Allah yayi rasuwa ma k'araman...". Take bakin Yasar yasoma b'ari ji yayi duk wani hanyan tafiyan jininsa ya tsaya da aiki kujeran da ke gefen sa ya zauna tare da furta"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un ya Allah ka jik'an Yasmin". Sai da ya d'au mintuna likita na kwantar masa da hankali kafin ya ciro waya ya sanar da su Abba suna Asibiti yazo yanzu.
Jikin Yasar a sanyaye ya ce"Doctor zan iya shiga na gansu?". Doctor ya ce"eh ba matsala zaka iya shiga". Da kyar Yasar ya iya d'aga k'afarsa ya shiga d'akin gun Yasmin ya nufa ya sanya kunnesa a k'irjinta yaji ba alamar numfashi ya d'aga hannuta ma haka ya saki jikinsa a sanyaye yana furta"Innalilahi wa inna ilaihi raji'un". Ya juya gadon da Yasiraht ke kwance nan ya ga idonta  a rufe amma tana wasu surutu a hankali wanda sai ka kai kunneka kusa da bakinta ka iya jin mai take fad'a.
Da sauri ya isa gadon ya sunkuya dai-dai bakinta ya ji tana fad'i " bazan tab'a yarda ba ku bada jinin Yasmin d'ina, Najwa kece jagoran d'auko ta har ki yanka ta da hannu ki to tabbas sai na d'au fansa da ga yau ba mutunci a cikin k'ungiya yanda kuka bada jinin Yasmin ma dodon tsafi duk wanda yake da hannu a cikin abun sai yayi na dama sai na fitini kowa a k'ungiyan nan wannan alkawari na d'auka ma.
Abba ne suka shigo Hajiya Nafisatu sai kuka takeyi a asai likita ya musu bayani a waje suna shigowa Yasar ya d'ago da sauri ganin su Abba ne ya niyyan fad'a musu Yasiraht ce tayi sanadin mutuwar Yasmin take bakinsa ya rik'e ya kasa furta komai sai b'arin da bakin ke yi.
Bakinsa ya cigaba da rawa tamkar mazari, tilas ya hakura zuciyarsa na kuna tamkar garwashi a haka aka dauki Yasmin zuwa gida akai mata sallah zuwa makwancinta. Yasiraht kwananta uku a asibiti duk ta kade ta rame tamkar mai cutar wata da watanni.A haka suka koma makaranta zuciyarta cike da kudurin daukar ransa.
Tun komawarsu take neman hanyar fanshewa,kwatsam ranan tana zaune ta nufi kafteriya cin abinci ta tsinkayi muryar Najwa tana bawa Shany labarin daya faranta zuciyarta. 
"Walahi shany inason kakus,dole in je jos yau cikin dare in ga lafiyarta, ita kad'ai ta ragemun bani da kowa"."Gaskiya ya dace ki dubota Najwa ko zan rakaki? " "a'a ta fada cikin ci da zuci. Cikin sauri Yasiraht ta yi baya tana murmushin mugunta zuciyarta wasai. Tun daga lokacin take bibbiyar motsin Najwa har dare ya tsala misalin daya taga fitowar wata katuwar tsuntsuwa daga hostel dinsu take tai girgiza ta rikida zuwa suffar tsuntsuwar sama ta lula tabi Najwa.
Cikin tsananin gudu suke keta gajimare,tsafi gaskiyar maishi cikin awa daya zuka isa garin tafiyar awa hudu a awa guda lallai sai tsafin.Yasiraht ta samu waje ta labe a tsakar gidan tana hangen Najwa ta koma ainihin suffarta ta shiga wani kayatacan fallo ta ratsa zuwa bedroom gidan ya kawatu komai akwai can ta hangi Najwa na neman kurewa ganinta saita rikida zuwa suffar wata mage data hanga a harabar gidan tai wuf ta fada dakin baccin ta window ta riga Najwa shiga tai kwance jikin tsohuwar tai linkim.
Da hanzari Najwa ta shiga jin motsi sai dai bata ga komai ba idanunta sukai wani haske walai tauuuu!  Tai jim tana karewa magen kallo ta saki ajiyar zuciya ta shafi kafaffun tsohuawar.
Mikewa Dattijuwar tayi, tana mutsittsika ido tai murmushi"yar Momah kece yanzu a daran nan,ban hanaki tafiyar dare ba? ""Momah so nake in ganki shiyasa nazo amma da safe zan wuce gida koma ki kwanta nima ruwa zan watsa".Komawa tai ta kwanta tace"Pussy na nan da halin ta nanike jikinki?" bata tanka ba ta kwanta Najwa tai waje tana fita harabar fallon gabanta ya fadi, ta dake kawai karaf idonta yakai kan Pussy kwance tana baccinta da yayanta uku.Cikin tashin hankali gabanta ya doka das!  Tai sashin Momah da gudu, turus ta tsaya sakammakon ganin Yasiraht da wuka tana digar da jini ta kyalkkyale da dariya tace "fansa Najwa jinin Yasmin 'yantace ne".
Sama da kasa ta nemi Yasiraht ta rasa,durkushewa tayi tana gunjin kuka kamar mahaukaciya ta mike tai girgiza tana wasu surutai.A firgice ta bayyana tsakiyar dakinsu tana rangaji Shany ta mike tana jijjigata Emeka na gefe tana dariya a ranta tace"ai dama na fada Najwa sai ta fitineku" lallabawa tai ta fice daga dakin ta nufi mahadarsu riskar Najwa tayi tana numfashi ta dafa kafadarta.Bata juyoba itama bata damu ba"sannunki jaruma, ga wannan soban ki saka ko Samar hai isa ja dake ba balle Najwa asalin zoban na kakana ne".Cikin sauri ta warci zoban tasaka wata kara Emeka ta saki Yasiraht na juyawa taga Shany ta dabamata wukar tsafi ta fadi mataciyya "karshan maci amana kenan" Shany ta furta.
Cikin salon tsafi da sihiri Yasiraht tayi gir-giza ta dawo wani irin hallita kamar kada ta tayi kan Shany gadan-gadan, Shany ta ciro sanda tsafinta ta nuna kadar amma ina sai sandan da ya narke ya koma ruwan wuta ya zube a k'asa Yasiraht ta fashe da wani matsanacin dariya bakin ta yana fitar da aman wuta sai hayaki yakeyi ta ce“kee Shany ai kun makara don yanzu sai kun raina kanku sai kunyi nadaman jawoni cikin ku do  zan zame muku k'adangare bakin tulu hahahaha…".
Ta kece da dariya sai da tayi mai isarta ta tun k'aro Shany tana fesa wuta a bakinta Shany ta soma ja da baya Yasirah ta yi wasu surkule ta ke wajan yasoma juyawa Shany tasoma ihu, Yasiraht ta na isowa ta fara fesa mata wuta Shany na ihu sai da ta bata wahala tukun ta kece da dariya ta ce“Shany ba zan kashe ki yanzu ba sai na baki d'an lokaci ki kuma kai ma Najwa labari in har ta kuskura tashiga gonana to sai wata ba ita ba".
Yasiraht na gama fad'an haka ta b'ace bat Shany jiki ba kwari ga shi duk taji ciwo zobenta ta murza take itama ta b'ace sai a gidansu Najwa ta bayyana.
Najwa duk tayi kuka har ta gode ma Allah masu aikin gidan ta kira ta shaida musu mutuwar kakanta a dare aka gyarata aka mata wanka washe gari da safe aka mata sallaha aka kai ta makwancinta Najwa duk ta dawo wani iri ta na tunanin kalan fansan da zata d'auka Shany ta bayyana a hankali ta taka har zuwa kusa da Najwa ta dafata nan ta soma bata hak'uri ta kuma shai da mata abunda ya faru wani gwauro numfashi ta sauk'e a fili Najwa ta furta “tabbas Yasirah ta mana nisa amma ko ta halin k'ak'a sai na rama sai na d'au fansa. A haka akayi kwana bakwai tukun Najwa suka soma shirin komawa makaranta.
Yasirah tana b'acewa bata bayya na ko ina ba sai cikin dajin makarantansu tana dariya nasara wai ita ke da wannan zobe da matsafa da dama duke nimansa sai da ta sai ta kanta tukun ta koma cikin hostel.
Najwa ko da ta dawo tana bibiyan Yasirah amma a b'oye don yanzu Yasirah tsoro take bata ko a gun mitin Samar yanzu yana d'an shakkar Yasirah don yanda take da zoben hannuta.
A haka su Yasirah da Najwa suka fara jarabawansu ta gama makarantar gaba da primary yanzu Yasirah ta samu 'yanci gashi duk ranan mitin sai ta kawo musu tun d'aya ko biyu an shayar da jininsa.
Kwanci tashi suka gama zana jarrabarwarsu masha Allahu komai lafiya aka sallamesu suka koma gidajansu zaman jiran sakammako. 
Tsakanin Najwa da Yasiraht kuwa abun yakai intaha domin ta zame musu karfan kafa, tun dawowarta gida samari kemata tururuwar zuwa amma babu wanda take saurara sai Samar shi kadai kawai ta bawa gurbi a zuciyarta.Kwatsam tai karo da soyayyar Muhseen dan aminiyar mahaifiyarta, lokaci daya ya kwanta mata a zuciyarta nan da nan suka amincewa juna ta tattara Samar ta watsar hakan yai bala'in kona ran Samar ya rasa hanyar da zaibi dan kauda Yasiraht ganin babu dama sai ya soma bibbiyar Muhseen.....
Muhseen da daya ne tilo tsoka guda a miya ga Alhaji Lawali mai akwai, asalin mahaifinsa bafulatanin garin Kurfi ne mamansa balarabiyar Egypt hakan yasa Muhseen ya dauko kyau gaba da baya kyakkyane na gaban kwatance.Tun tasowarsa baisan kwaba ba balle harara sangartacan yarone kaf karatunsa a waje yayi hakan yasa ya budi ido da harka da Mata over.Ko kadan mahaifansa basa son laifinsa, yasha yiwa yaran jama a cikkuna da fyade.Tunda Samar ya gama gano waye Muhseen ya cika da farin ciki domin ya samu hanyar gumawa Yasiraht a sadaka.Hanya ta farko daya soma bi neman shiri da Najwa nan da nan suka koma kamar da sannan ya bijiro da bukatarsa dake tayi shirin fansa babu jinkirtawa ta amsa bukatarsa nan da nan ta soma shirin fuskantar matsalar.
Ranar Asabar da yammaci Muhseen ya fito daga Shanawa club, harya gota tarin wasu gun-gun matasan yan Mata ya hangi Najwa a gefe tana taunar cingum daga ganinta babu musu ya tabbatar yan good evening ne in kiya yai mata sarai ta gani sun hada ido ta kanne ta cigaba da hidimar gabanta.Bai yi kasa a guiwa ba ya karasa da fari ta kalleshi ta watsar, daga bisani tabi yarima akasha kida basu wani jimaba ya ribaceta yajata cikin club din ya kama mata daki.
Tsayin kwanaki uku suna tare, Najwa na hillatasa ko kiran Yasiraht bata bashi damar yi ranar kwana na uku ne ta samu suka fita yawo tare, cikin ikon Allah sukaiwa Sahad tsinke anan sukai kici6us da Yasiraht,Najwa ta kalleta ta watsar Muhseen kuwa ko kallonta baiba a haka suka gama siyayyarsu suka fita suna tayar da mota da gudu taiwa motarta key wadda ta aro wajan Yasar ta rufa musu baya.
Tunda Najwa ta hangi tahowar Yasiraht taiwa Muhseen wayau ta amshi tukin, tuki suke na fitar hankali ko gabansu basu duba a haka sukaiwa cikin gari nisa.Najwa ta saki murmushi ganin tarkonta ya kama kurciya.Cikin rashin zato tai ribos motarta tayo baya take motar Yasiraht ta wuntsula ta kife ta kama hayaki bata hakura ba tasake turata tai gaba ta fada rami ta kama da wuta.Tai juyi taja motar  tana kallon Muhseen tana murmushi wanda yakasa hanata kudurinta.Sunyi tafiya mai nisa sun shigo gari ta shammaci Muhseen ta nufi wata katuwar mota cikin hanzari ta danna zobanta ta bace take motar ta murkushe Ammar sai gawa.Tana daga gefe tana kallon mutane kowa na budurunsa, nan da nan tabar wajan.Batai nisaba taji jikinta na shock, tsoro ya shigeta tuni ta bayyana wajan motar Yasiraht.
Gabanta ya tsananta faduwa lokacin da tai arba da Samar,idonsa jajjur yana huci kamun tai wani yunkuri ya kaimata cafka ya dinga azabtar da ita tana ihu, ihuntane ya farkar da Yasiraht daga dogon suman da tayi.
Murmushi ta saki lokacin da tai arba da Najwa nacin azaba wajan Samar kafin su farga ta bace bat, wani hadiminsu tasa ya dauko mata motarta zuwa kofar gida da dingishi ta shiga gidan, nan ta riski tashin hankali labarin mutuwar Muhsun.Kara ta saki ta zube a sume. 
Sanah
Rash
Kara ta saki ta zube a gun sumamiya da sauri Yasar sukayi kanta suka zuba mata ruwa ta farfad'o ajiyan zuciya ta saki, sai jin abun take kamar mafarki sai da ta mutsuke idonta taga su Yasar nan ta gaskata abun da ta tarar wani irin kuka mai ban tausayi ta saki tare da tsuma zuciya.
Bayan kwana bakwai duk Yasirah ta dawo shiru-shiru bata son yawan hayaniya mitin ma taki fita haka Samar zai zo yayi ta damunta a satin ne ta fara fita Najwa ko duk a tsorace take don tasan karonsu da Yasirah bazaiyi kyau ba. A haka jarabansu ya fito tare da Admission d'in jami'a batare da b'ata lokaci ba aka mata komai ta fara zuwa makaranta.
'Dabi'u Yasirah sun k'ara canzawa wanda hakan ya k'ara bama S Marafa tsoro sam yanzu Yasirah bata shakkan kowa komai zatayi gabanta gad'i zata yi shi ba tare da tsoro ko shakka ba ga taurin kunne kamar k'ashi.
Kwanaki sun tafi watanni sun wuce shekaru sun shud'e game da halayan Yasirah ko ba abun da ya ragu haka gun tsafi ma tayi nisa sosai don tafi kowa a tsabibanci kuma in taso kawo mutum sai ta kawo ka wanda hakan ya kara mata matsayi a gun matsafa.
S Marafa ganin halim Yasirah ba abunda ya ragu gashi bata kula samaruka hakan yasaka ya yanke shawaran had'ata aure da Yasar d'an uwanta tunda daman sun shaku da ita sosai.
Yasar ya samu aiki cikin ikon Allah yana gudanar da komai a haka ya koma gidan mahaifinsa da zama sabida barazana da tsorata da yake yawan yi.  B'angare guda aka bashi a gidan baya tare dasu don gun kam zamu iya kiransa da gida don basa had'e da Dad d'insa k'ofar su da ban nashi daban sai ya ga dama ya shiga gurinsu.
Yasar yanzu ya gama gane duk abinda Yasirah ke aikatawa amma ba halin fad'a don ko ya zo da niyayar fad'a bakinsa sai ya rik'e gashi hasali Yasar mai wasa a addu'a ne wannan yasa Yasirah ke nasara akansa.
S Marafa ne ya d'aga waya ya kira Yasar ya ce"kazo ka sameni a gida". Ba tare da b'ata lokaci ba Yasar yazo sai da ya gaida Hajiya kafin yaje gun Abbansu ya gaida shi bayan ya zauna Abba ya kira Yasirah nasiha sosai ya fara musu daga k'arshe ya ce“na yanke shawaran had'a ka aure da Yasirah 'yar uwanka kusani ba shawara nake baku ba wannan umarni nane". Yasirah ta d'ago ta fara bama Abba hak'uri tsawan da yadaka mata ne yasata yin shiru take ranta yasoma a zazzala yanayinta yasoma canzawa cikin sauri tafita daga d'akin harda gudunta ta nufi d'akinta. Ko da muka bita nan take d'akin yasoma gir-giza wani wuta ke fita daga bakinta kanta ma naci da wutan kwayar idonta shima wutar yake ci wanna abu ba k'aramin tsoro ya bamu ba na bud'e baki da niyar ihu Sanah tasa hannu ta toshe min baki na.
CI GABAN LABARI....
Yasar an sallame shi a Asibiti tare da garg'ad'in ya kiyaye shan magani da kuma abunda zai janyo makansa mumunan buguwa don zai shafi kwanyansa. Ko da suka dawo gida Ammar shi ya ci gaba da kula dashi har ya warke sosai.
Samar ne ya shigo da motar sa haraban gidan su Yasirah mai gadi ya gaidashi Samar ya amsa cikin sakin fuska mai gadi ya ce“barin kiraka Hajiyar". Mai gadi ya shiga gida ya tarar da Yasira tana shirin fitowa haraban gidan daman ta san da zuwan Samar, mai gadi shi ya sanar mata da sak'on Samar ta ce" gata nan zuwa k'irjinta sai bugawa yake yi don ta san Samar ba zaiyi sassauci akan maganan ba.
Tunda ta fito Samar ya kafeta da ido sai jin zuciyarsa na harba masa da sauri-da-sauri kasa d'auke idonsa yayi daga gareta, tana isowa ta ce"King barka da yamma". Cikin sanyin jiki ya amsa“lafiya ya kk?". Yasirah ta rausaya ta ce“lafiyalau". Shiru gurin yayi sai Samar da yayi dauriya da d'ago ya kalleta cikin so da k'auana. Yasirah ta ce“Samar nayi duk yanda zanyi Abba yaki afasa aure ya ce aure dole ba fashi".
"Yasira gaskiya da sake"cewar Samar dake zaune kan mota fuskarsa babu alamun walwala. Tayi ajiyar zuciya tana dubansa ranta duk a cakud'e hawaye ya ciko ido taf tasa hannu ta share. "Samar bansan ya zamui ba, Abba ya dage kan lamarin sossai.Gashi shugaba kullum cikin gargad'ina take bisa kaucewa dokar k'ungiya".Ta k'arasa maganar cikin raunin murya.
Cikin kaushin murya yace"zanyi hukunci"cikin sauri ta tari hanzarinsa "nasan hukincinka bahagone Samar karkayi pls na rokeka."Bai jira cewarta ba ya kwashi mota da tsananin gudu yabar harabar gidan. Durkushewa tayi  take yanayin halitarta ya soma sauyawa daga yadda take zuwa wata suffar da gudu ta tashi ta shiga cikin gida d'akinta tashiga tasaka ma makulli ta kulle kanta..........
Yasar jiki ya warke kwance ya ke yana tunanin irin had'in da Abba ke shirin yi masa da wannan azzaluman don shi ba wai sonta bane ba yayi a'a sai abunda take aikatawa gashi yakasa sanar da kowa ko yayi yun k'urin hakan bakinsa nauyi keyi ya kasa fad'a. Da wanna tunani aka kira sallah ya fita ya tafi masallaci bai dawo ba sai da yayi sallah isha'i yana zuwa ya samu an kawo masa abinci dining ya je ya zauna ya bud'e kular sai ya manta bai d'auko ruwa ba mik'ewa ya sake yi ya je friza ya d'auko hollandia mai sanyi yazo dining.
Ido ya zaro alamar tsoro don wasu manyan tsutsotsi ya gani suna yawo a rabin abinci da baya yasoma ja sai ganin koyayen d'akin sun d'auke hoton Yasirah dake mak'ale a d'akin ya haska ya tsatstsage wani irin mumunan fuska ya gani a cikin hoton sai ji yayi ana kiran sunansa Ya....sa...r! Ya.....sa...r!! Ya....sa...r!!! Cikin wata irin murya mai ban tsoro ga haske da ke haskashi wal-wal sai ya d'auke gurin yayi duhu tsoro ne ya soma kama shi
nkali yai baya, kansa ya soma juyawa wani abu ya daki kirjinsa.Ya zube kan gado Allah ya bashi sa'a ya soma jan addu'o'i duk wada tazo bakinsa.
Take dakin ya daina girgiza, komai ya koma mazauninsa har abincin tamkar komai bai faruba.Ya yi jim yana tunanin lamarin ture abincin yai ya mike ya dauki mukulin motarsa kai tsaye ya wuce wajan park ya dauki motarsa kirar corrola.Gidansu Nawas abokinsa ya nufa saidai bisa akasi baya nan haka ya dawo gida jiki a sanyayye.
Kwanci tashi maganar biki kara kusantowa take, babu wani jituwa tsakaninsu sai kallon banza da bakakken maganganu in kuwa suka hadu a gaban iyayyansu nunawa suke tamkar babu komai tsakaninsu a haka aketa cudawa.
Yasiraht da Samar hankalinsu yayi mummunan tashi, musamman yadda duk yadda Samar da Najwa sukai kokarin runkarar mahaifan Yasiraht basa nasara saboda karfin addu'a.Har lamarin ya soma taba tsafinsu wanda yake kawo musu koma baya,hankulansu yai matukar tashi sossai.
Yasar ne zaune a office haka kawai yaga office din na girgiza, take kasa ta dare wasu irin hallitu masu kahunhuna suka bayyana suna kawo masa cafka.Ya rintse ido yana ta'awizi wani mashi kakkaifa ya ratso tsakani ya nufoshi gadan-gadan.Take ya runtse yana jiran me aukuwa ta auku jin shiru na lokaci yasa ya bude ido abin mamaki mashin ya gani tsaye dai-dai kirjinsa yana daga ido yaga Yasiraht ce tsaye tana masifa ta tsayar da mashin da karfin tsafinta.
"Shima kasheshi zaki yi Najwa?"
"Tabbas Yasiraht walahi saina illata rayuwarki,ninai sanadin zuwanki kungiya yau gashi kin fini komai".
"Kinyi kuskure Najwa n shirya ja dakowa cikinku, ciki hada daukar rayukan masu neman bibbiyar lamurana".
Take suka soma gumurzun tashin hankali, wanda hakan yaja farfashewar wasu cikin kayan.Can Najwa ta saki kara sakammakon nasarar sokarta da tai da mashin hannunta a gefan kafad'a b'acewa tai tana kuka.
Yasar ya saki ajiyar zuciya, Yasiraht ta gyara office din tas ta dago tana dubansa tai masa murmushi tace.
"Kana musulmi kana sakaci da addu'a ko Yah Yasar?".
Bata tanka ba ta wuce ta rufemasa office din, ya cigaba da jujjuya maganarta a ransa.Shigowar Nawas ya katsemasa tunani, yace "ango! Ango!! ango!!! Dariya kawai yai  suka soma hira.
Sun jima suna hira yai masa sallama ya wuce, haka Yasar ya yini sukuku dashi.
Bata tanka ba ta wuce ta rufemasa office din, ya cigaba da jujjuya maganarta a ransa.Shigowar Nawas ya katsemasa tunani, yace "Ango! Ango!! Ango!!! Dariya kawai yai  suka soma hira.
Sun jima suna hira yai masa sallama ya wuce, haka Yasar ya yini sukuku da shi.
Ana tashi daga aiki ya d'au jakarsa da wayoyinsa ya fita motarsa ya bud'e ya shiga ya tayar ya d'au hanyar gida zuciyarsa cike da tunani kala-kala yana cikin tuk'i sai yaga wata ya rinya cikin fararen kaya ta baza gashinta ba'a ko ganin fuskanta ga ganin haka ya yi shirin taka burki cikin sauri ta juyo garesa tare da ihu ga hak'oranta sun fito, bai san lokacin da ya saki ihu ba ya sake sitiyarin motar ya rutse ido don ya sadak'ar mutuwa zai yi.
Cikin sauri Yasirah ta bayyana gaban motar ta rik'e sitiyarin cikin salon tsafi ta mayar dashi gefen hanya duk abunda yake faruwa idonsa na rufe jin motar ya tsaya ya bud'e idons a hankali dai-dai lokacin Yasirah ta juyo garesa karaf fiskansu ya had'u dana juna hancinsu har na gogan na juna take numfashinsu yasoma fita da sauri-da-sauri kasa d'auke idonsu suka yi daga kallon juna kalon ido-cikin-ido. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment