Sunday, 21 January 2018

RARUWAR NIHILA 3

==RAYUWAR NIHILA 3== .
Daddy shi ya dawo da maghrib yaje ya sameshi har parlour uban ya rungumi dansa sukayi musabaha ya gaisheshi sunata labari saiga mum dinsa tazo tace ooh yanzu alhaji da yaron nan ne ka zauna sai hira kake kaman wani sa'an ka yace haba ke kuwa altine in banyi dashi ba dawa zanyi shi kadai fa nakeda ai dole in soshi.
.
WANE NE HISHAM? Dane daya tilo ga alhaji jameel pindiga tunda sukayi auren zumunci da altine yar wajen ummansa ce shekaran su 5 Allah be basu rabo ba ana shida ta samu ciki ta haifa da namiji aka sa mishi hisham daganan kuma shiru ba aihuwa ba labarinshi. son dau son duniya Sun daura mishi primary kawai yayi a nigeria Amma secondary da university duk a cyprus yayi. Hisham fari ne ba kuma fari har can ba yanada kiran maza wanda suka amsa sunan su dan daga nesa zaka hango abs din da Allah ya masa Ga faffadan jirgi da tsayi he's just the perfect guy da mata ke so saidai duka wannan kyan Dan maciji ne dan kuwa zuwansa Cyprus ya lalace da neman mata da zuwa clubs sa'a daya dai baya shaye Shaye.Hankalin sa tashi yayi da yaji fadan da daddyn yake tayi akan wani cousin dinshi yaje neman aure har sokoto yace shi bazai lamunta in bazai nema auren a gombe ba ko wani wuri kusa bazaije masa ba sabida nisa da kuma rashin sanin tushe.wani gumi yaji ya tsatssafo masa ya ji jikin shi ya mutu ya tuno da nihilan sa Wanda bazai iya rayuwa babu ita ba gashi yanaso yaje ya ganta Amma babu hali Dan kuwa daddyn shi ya sashi a gaba da ayyukan company dinsa atm dinsa gaba daya suna hanun hisham minti daya biyu zai neme shi yace it's high time ya zama responsible man. nihila kuwa tana can ta rasa meke mata dadi idan taga pictures din hisham da emmata a wayanta saitaji duk ya fara bata haushi tace yau kam ko mutuwa za'ayi sai sunyi ta ta kare.
.
Ta shiga watsapp dinta saita tura picx din Wa hisham yana zaune yana tunanin yanda zaiyi da daddyn shi batun nihila kawai yaga watsapp dinshi ta turo picx baisan sanda ya tashi tsaye yana zaro ido ba hankalin sa ya balain tashi tambaya kala kala a ransa ina nihila ta samu pics dinnan kardai tasan halayen shi wanda yaketa boye mata? Ta ina zai fara mata bayani gaba daya ya Burkice aiko ana haka sai ga text dinta hisham ka bani mamaki u disappointed me I trusted u my whole life Amma da abunda zaka sakamun kenan? Forget u ever know me in your life. Gud bye. Tashin hankaliiii!! Ba'a sa maka rana shin kuna ganin hisham zai hakura kuwa muje zuwa.
.
Hankalin sa a tashe ya kira ta a waya taki dauka missed call kusan goma sannan ta dauka ana sha dayan tana dauka ya fara magiya nihila plsss let me explain to you tace ba abunda zaka gayamun hisham na riga na gani da idona ko zakace ba kai bane yace nine nihila Amma Dan Allah kiyi hakuri na miki explaining tace bana bukatan wani explanation kaban mamaki hisham ashe dama abunda kakeyi kenan Allah daya halicce ka bakaji tsoron saba mishi ba baka kuma ji kunyan yana kallon ka saini mutum wanda ba komai ba baiwar sa ya halicce ni nine zakajin kunyan idona kar na sani. yace nihila nasan nayi abubuwa da dama a rayuwa na but wallahi shigowanki rayuwana is a blessing to me kinsa na daina 70% din abunda nake I have changed much more than before for u tace ooh sabida nine ma kayi changing not because kana tsoron abunda zakaje ka tarar wurin ubangijin ka yayi shuru yana jinta kawai sai hawaye yaji a idonshi nihila pls dnt leave me without u my life will be miserable plss nihila tace hisham its too late to cry when the head has been cut off just leave me alone i adore and cherish every moment we had together but this has to end ta fashe da kuka tace goodbye hisham ta kashe wayanta ma gaba daya tasa favourite waqanta wanda take sawa in tana bakin ciki wato bhula dena (forget me) na ashiqui ta kuka har taji ba dadi.Taci kukanta son ranta saiga bahijja ta tsaya tana tausaya mata duk tasan be wuce kan hisham ba ta girgiza kai sis meya sameki kawai ta qara fashewa da kuka ta rungumi beejay he betrayed my trust and life beejay he lied to me ya zanyi da raina gashi mummy tace na fita harkanshi bata yarda da soyayyan mu ba i just dont know what to do beejay ta rarrasheta tace mata tayi hakuri ta manta da hisham sabida koda ya canja halin sa iyayen su da kyar ne su yarda sabida nisan garuruwan da suke kuma basa son auren nesa. idonta duk sun kumbura sunyi ja ta dawo kaman ba lively nihilan da take da ba ta canja completely.
.
Hisham kuwa yana kuka ya je ya samu mum dinshi tace hisham lafiya me haka kake kuka kaman yaro wa nine ya mutu yace momi aa ba mutuwa bane wata yarinya ce ya bata labarin nihila amma bai gaya mata dalilin fadan ba kasancewar suma iyayen basusan tsiyar da yake tafkawa ba Dan inya dawo nutsuwa yake tace hisham da ka hakura da yarinyar kasan daddyn ka ba yarda zaiyi ba da kunnen ka kaji yana fada akan neman auren da cousin dinka yaje yi a sokoto bazai bari ba yace mommy wlh bazan iyaba kiyi hakuri ki mishi magana she's my life tace shikenan zan gwada amma abunda kamar wuya.
Zan cigaba anjima. Kuna tare dani?

0 comments:

Post a Comment