Sunday, 21 January 2018

RAYUWAR NIHILA 2

== RAYUWAR NIHILA 2 ==
.
Na tsaya kawai ina sake da baki nace beejay yanzu kin kyauta ma kanki kenan kiji tsoron Allah fa inni na rufa miki wani ya ganki yaje ya fada fa a gida tace kin fara ko naji shikenan a haka dai ta gama rawe rawen ta suka koma gida nihila na jimamun alamari irin na bahijja.Sun koma gida beejay ta Kara tunatar da ita batun alkwarin rufe sirri tace da ita tayi shuru tace toh.. wannan kenan! Suna waya ne da hisham yake kara tunatar da ita irin sonta da yake nihila kin sauya mun rayuwa kin canja ni gaba daya wasu abubuwan da nake da yanzu kusan duk na bari tace wasu irin abubuwa yace hmm bazaki gane ba sai a hankali nidai pls keep my love I promise I will be the best u ever had n I will make u my wife! Ummm hisham kenan...
.
Yana can yana tsula tsiyar shi son ranshi a kasar cyprus wanda shi a ganin shi wayewa ne ya kawo hakan Ga neman mata ga zuwa clubs kowace rana saiya yi attending ba'a barin shi a baya shima wai bazai bawa shedan kunya ba... nihila tace yau kam bari ta shiga account din hisham na insta tayi bincike tana shiga taga pictures kusan 30 ta shiga ta fara duba comments duk wani abokin shi da taga yayi comment shima sai ta shiga account dinsa ta duba hmmm me zata gani saiga pictures din hisham baja Baja da emmata a clubs ya kamo wannan ya kamo wancan ta ji kaman an caka mata wani abu a zuciyanta..
.
Nima daganan saida naji rasssss.. batasan sanda hawaye ya zubo mata a idonta ba tayi munching picx din duk ta ajiye.. comments din mata kam kala kala kan pics dinshi daga wnda yake cema sweetheart sai me my wife da dai sauransu ta ajiye wayanta ta rasa meke mata dadi tasaka waqar bhula dena(forget me) na ashiqui ta risgi kuka son ranta saida idonta sukayi luhu luhu har bacci ya dauketa anan sausan tazo ta sameta ta dau wayanta ta bude kawai saitaga picx aiko ta tura taje ta nuna ma momin su waiga samarin da nihila take so en iska marasa tarbiyya... Ran momin su da yayi dubu saida ya baci ta sameta a daki ta mata tas tace tunda taki jin maganan ta bazata bada wayan ba sai taga canji a tattare da ita..
.
Tayi kuka sosai da taje skul take gaya ma habibaty tayi ta bata hakuri sannan tace mata itama ta hakura da hisham din mana tace mata inaa bazata iya ba tasan hisham yana sonta ita kuma ta dau alkawarin she will change him for good koda bazata aure shi ba amma bazata barshi a munanan halayen da yake ba na sabon Ubangiji habibaty tace shikenan Allah ya baki sa'a... watan ta kusan daya ba waya har sun gama exams dinsu sannan da kyar da rokon beejay momi ta bata wayanta hisham kuwa hankalin shi dayayi dubu saida ya tashi da bai saba jin wayanta a kashe ba kullun suna waya ko chatting sai yayi tunanin kodai taji labarin halayen sa shiyasa ta guje shi tanata jimamin abun a zuciyar shi.. kawai saiga call dinta ya shigo ya dauka yace haba sweet ina kika shiga for weeks inata nemanki saita mishi karya tace ai wayanta ne ya fadi saida ta siya sabo yace kaii har kinsa naji sanyi a raina plss kina sanar dani irin haka tace to shikenan insha Allah bazata kara ba..
.
Yace yauwa my nihila dats y i love u more n more each day tace I love you most.. A zuciyanta tana mamaki halin hisham kaman bashi ta gani da emmata ba abun ma har ta kasa yarda duk da ta gani da idonta... tace a ranta akwai ranan tonan asirinka!.Sun gama exams dinsu lafiya aka fara shirye shiryen candy dinsu murna a wurinsu ba'a magana dan a kansu ne za'a fara graduation ceremony... ranan candy sunsha kyau ita da bestyn ta habibaty sunyi shigen white and black Ga gown dinsu royal blue da white ya karbesu sosai aka fara gabatarwa inda aka kira Nihila Muhammad Tahir tazo ta bada opening speech ta fito da takunta na kasaita kaman gimbiya taje ta bada kaman wata baturiya nan aka dau tafi raf raf raf sai shewa ake an bada prizes da dama wanda kusan rabi ita ta dauka tayi kukan farin ciki bayan taro sun dau pictures sosai da jawad ganin karshen zaman su yazo yanzu sun bude wani chapter a life dinsu sunyi kukan rabuwa da jona sabida shi zai tafi university of herriot watt a dubai ne karatunshi..
.
it was a day of happiness and wonderful memories a life dinsu wasu Sun karba numban juna saboda keeping in touch... Hisham nacan nata shirye shiryen project dinshi na kammala university yanata Allah Allah ya dawo Nigeria Dan yazo yaga sahibar sa Allah cikin ikonsa ya gama komai ya fito da result mai kyau ba laifi.. ya yi visa Nigeria tayi masa kira mum dinshi tasa an dauko shi a airport yanata kalle kalle gombe ya canja mishi sosai dan ya kusan shekara koma fi be zo gida ba.. yana isa dakin maman shi ya wuce tayi masa oyoyoo ya gaisheta ya zauna suna labarin yaushe rabon duniya da ayyaraye yace ina daddy tace bayanan yaje office saiya dawo zasu hadu..
.
Ya ce a siyo mishi layin mtn yana sawa ya kira nihila taji mamaki sosai da taji yana Nigeria yace mata dama surprise yake son mata tayi mishi sannu da hanya..
.
Zamu ci gaba da safe, inshaallahu. Allah yatashemu lafiya

0 comments:

Post a Comment