Wednesday, 17 January 2018

SANADIN SELFIE Part 3 and 4

===== SANADIN SULFIE 003 =====
Ni dai gaskiya Hajiya bazan iya zama a haka ba nai yi girki kuma ban wanka ba tab, ae bazan iya ma bacci ba
Hajiya in ya kawo ki karba ki ajiye min zan shiga ciki kya Ji da shi,
Nai shige wata daki,aunty najma na kira yawwa aunty ya karaso ne a'a to ki hado masa da system dina,
Wai baza ki dawo bane zan dawo akwai abinda zan yi da ita ne Kwana nawa zaki zan ma iya dawo jibi tom shikke nan agaida min da sweet Fatima,
Na shiga wanka haka kawai naji ina wani nishadi ko na mene oho.
Salamu alaikum ko Hajiyan tayi bacci ne wane irin bacci da magariban farin nan Ashe zaka dawo eh mana hajiya an huni lapiya,
lapiya lau nifa yunwa nake Ji kai jama'a sai kace me yawo da yunwa nifa bana jurewa yunwa kuma kin san fa kullum a restaurant nake cin abinci wllh Hajiya yanda kika ga na jawo karshen satin na su mome   su dawo,
Ko na wajen ma daurewa kawai nake, to bari hanne tazo sai ta zubo ma
Hajiya ni fa bana cin girkin en aiki barshi kawai naje restaurant naci kawai,
Yar uwar ka ce tai girkin wa fa Salmah, Kai gaskiya na dade ban ga yaran nan ba yanxu duk sun girma nasan,
oh tana nan ne eh to Hajiya bari na zuba ah'ah bari hanne tazo ki bari na xuba ni fa kyenkyamin su nake Hajiya suna da rangwamen tsafta,
.
To Allah yasa dai  matar da zaka auro ta iya girki irin kune sai dai ku buge da zuwa wajen sai da abinci
Ae Hajiya indai na lura bata iya girki ba to gidan su zan turata ta koyi girki na wata uku sannan ta dawo ni bana ma Fatan haka to shikken nan Allah ya kaimu lokacin Ameen Hajiya.
To sai ka je kitchen ka debo,
bayan ya debo ya dawo Hajiya kin san wannan girki yana daya daga cikin abincin Danake so kace kayi sa'a sosai ma haka ya dinga kwasar abinci yana ci yana santi,
Telle ne ya shigo da karamar trolley Hajiya ga kayan wai tana gaishe ku tom sannun ka,
Wanna kayan fa na mene na Salmah ne,wai Hajiya sabida me baza ki ce mata Naureen ba,
banga dama ba to Hajiya har nagama bata fito ba ki gaisheta amma na so haduwa da ita dan rabona da ita tun ranar birthday nata na 5years tab gaskiya zumunci nan naku ban san a wane waje kuka koyo shi ba,
Bari iyayen naku su dawo to Hajiya na tafi sauri nake akwai inda zani,
Amma zan dawo in Allah ya yarda to Allah ya kiyaye Ameen,
Fitowa nai ina goge kaina da towel,Hajiya wai Ke da wa kuke magana tun dazu inajin ku kasa kasa,
da kina so kiga da  wanda ake magana me yasa baki fito ba sallah nai sannan nai wanka yayan ki ne Sameer Allah sarki Ashe ze dawo din  bece yana gaishe ni ba,
Yaran nan wai daman har yazu kuna nanda sa maganr ku shi ya gama Kema zaki fara taki to mutun da lapiyar sa yaka sa magana ni ga kayan ki nan ki duka ina so zan huta...........????
.
Ina zaune ina aiki a system dina gaba daya hankali na yana kan abinda nake yi sallamar su dadi ne yasa na dago,
Daddy sannu da zuwa au daman kina nan eh daddy na ma Kwana biyu Ke daga Kije kiyi kwana biyu shine har yanxu uhmnn dady ae gidan ba kowa su Rauda da Huda ma Basa nan to ae suma yau zasu dawo saboda gobe su Hajiya hadiza zasu dawo wooow kai kace gobe akwai sha'ani,
Hajiya yanxu yarinyar nan haka za'a zuba mata ido ana kallon ta,
Me tayi au Hajiya baki ga abinda tayi ba tana zaune ita ba aiki ba taki ta yi kuma taki ta koma makaranta ta karo karatu gashi ko maganar auren ma bata yi au wannan kuma ran nan zan mata maganr ta shashantar da zancen,
Ni daddy ba wani aiki da zanyi bana son fita ga karatun 9ja sai a hankali,
to mene amfanin karatun naki in baki aiki ki tallafawa nakasa dake ba ki zama lawyer me kare haqqin yan uwan ki mata,
in ma baki son karatun anan to sai ki koma inda kika yo ki karasa ko wata kasar to dady zan duba,
Haba ta hannun daman karfa azo anajin mu dake in kin ki kuma a cikin yan uwan ki a baki wani to daddy a bari su Abee su dawo sai ayi maganar to ae ni duk abinda nace shi kan sa Naseer din be musan to daddy
credentials dina ae suna cen in zasu tawo ae xasu tawo miki dashi,
Ina son ma zuwa can din,Me ake yi bakomai akwai abubuwan da zanyi ne uhmmm Kaga yar nan wai ita me wayo duk hanyar da aka bi sai tayi kokarin toshe ta,
Zamu dai ga iya gudun ruwan kitashi nai na shigowa na daki,ina jin su suna ta maganganun su ni duk haushi ya ishe anbi an matsa ma mutane duka duka shekara na 23 kuma ni ba wanda zasu ban na aura da kaina zan zabi wanda nake so sai dai sucen banda kunya,
Har dady ya gama maganganun sa ban fito ba, tashi nai na shiga wanka ina fitowa ana sallar azzahar da kyar na bari hudu tayi na fito janye da trolley,
Hajiya na tafi nai kicin kicin dani oh dan an fada miki gaskiya shine zaki tafi to ki fi ruwa gudu
Haba Hajiya wai duka duka shekara na nawa ne ni ba girman jiki ba bare ace wani abu ina fada ina kuka,
Kuma ae ni naga daman zama a gidan dan na taya ki za shine Toni wajen Abee na zan koma shi kadai ne yake son na,
Muma muna sonki muryar ya Asif naji daga bakin kofa kuka na na shigaba na ja trolley na fice wata kuma bazan kuma zuwa ba,
Da sauri Hajiya ta taso salma ki tsaya mana indai akan wannan zance kike kuka to andaina kiyi haquri ficewa ta nai ban saurare su ba,
Da sauri ya Asif ya biyo ni ina Ji yana kira na nai masa banza na tsayar da adaidaitan zan shiga naji an rike min jaka haba Naureen kiyi haquri ki fito na kai ki,
Gaka malam ja mu tafi in kuma baza ka ba na sauka zai ja Asif ya rike karfen jiki ki saukko mana Kaga ka kyale ni ba inda zan saukko ba yanda be ba naki haka ya haqura yana gani har muka tafi sannan ya juya ya shiga gidan................????
.
Hajiya wai me akai mata ne har sai amma wannan shagwababbiyar wani abu ah'ah Hajiya me ya faru tunda kika ga tai fushi dake to ba karamin abu bane duk yanda kuke da ita,
Ita da alhajin ka ne too babbar magana ta hannun daman nasa tab me yayi mata zance karatu ko kuma aure ga dukkan Alama ba wanda yake gaban ta daga karatun har aure ko me yasa oho,
To Hajiya a kyale ta mana aga iya gudun ruwan ta ita kanta baza ta so ta zauna haka ba aure ba kuma Kila tana da wani kudirin a ranta tom shikke nan,
Yanxu dai nasan ta isa gida bari na kirata,am koda yake naje ko zuwa anjima ko kuma gobe tom shikke nan ina sauran 'yan uwan naka kowa yana wajen sabgar sa kin san yau Sunday,
Hajiha duk kinyi collops ko dai tunanin yar jikallen taki kike yi kai rabu dani bana son magana ya fita yana dariya,
Ita kuwa tana sauka da bawa me adaidaita 500 tai gaba Hajiya canjinki ka rike tai gaba me adaidaita yace gaba ta kaini dama kullum da irin ku nake haduwa,
Me gadi yana ganin ta ya tashi da sauri ya bude mata gate yana mata kirari amma kamar wanda yake ma dutse too yau an bata ma mata rai ko wane ya jamin asarar 'yar fara ta abuja ya rufe gate yana maganganun sa,
Ya suhal ne da wani daka gani abokin sa ne ya rako shi sun fito daga sitting room, tunda ta shigo abokin nasa yake kallon ta,
Ina wunin ku ta fada bata jira amsar su ba ta kara gaba,Kaga malam wannan kallon fa wallahi aboki wannan fa kanwar ka ce eh to ya za ae,
Kamar ya daga ganin mace kai daman har yanxu kana da son matan naka,
Shamsudden yace wallahi in zaka bani zan aure ta dan irin macen dana Ke so ce to ina zaka kai madam ah'ah inada right din da zan kara uku nan gaba,
To amma banda wannan dan ankusa bikin ta tana da miji, kai dai kawai kace baza ka ban ba,
Abokina kenan ya dakatar da zancen to sai munyi waya ya mika masa hannu sukai musabiha ya shiga mota shi kuma ya shige gidA parlo na tarar da aunty fadawa jikin ta nai ina kuka lapiya wake mene haka duk sanda zaki shigo da kuka sai kace wata karamar yarinya to ba Sune ba su wa,
Tana sharbar kuka tace dadyn Rauda da Hajiya kaka tab wazai shiga wannan fadan kazo kaji kunya dan duk wanda ya shiga zaku bashi kunya, ba dani ba daga ni ni ina da abun yi,ya suhal ne ya shigo wai me akaiwa 'yar kanwar tamu ne,
Ita da dady ne da Hajiya kaka aunty najma ta bashi amsa to abin babba ne   me ya faru nan na kwashe komai na fada musu kai to mene abin tada hankali a wannan zance in karatun ne baki so shikken nan ae kinyi kokari tunda kina da degree sai ki fiddo da miji ae miki aure,
Kinga ma abokina da kika gan mi tare yace ae miki magana ki masa tab wllh Allah ya sawwake me zan wannan,aunty in tsoron maza ma nake too ??
Me sukai miki bakomai ni bana kulasu bare suyi min wani,kawai ni ina tsoron na fara soyayya, abu to mene dalilin ki na kin soyayya ya suhal ya fada ina tsoron kar abunda ya faru da *mufeeda*  ta cikin *LABARI NA* ya faru dani wacce mufeeda ya tambaya  kawarta ce,matar *muhseen* yanda zaka gane oho wani abune ya faru da ita ae ko jiya na hadu dashi kuma naga ba wani matsala a tare da shi ae ba wani abun bane nan na kwashe labarin na fada masu Kema dai ae kowa da irin jarabtar sa ki cire wannan daga ranki,tom amma ni gaskiya bazan aure zumunci ba to menene illar sa kina ga dai yanda muke.zaune da najma  Kema me bawa wadan su labari ne, daki na tafi na kwanta...................????
.
Ina sakawa da kwancewa to ni ya zanyi tun yanxu gwara na sami mafita tun kan azo ana ban wanda bana so,
Juyi nake a gado ina neman mafita duk cikin samarin da suke sona ban ga wanda yayi min komai da komai ba,
Halin su basu min ba amma zan cigaba da addu'a Allah yai min zabi nagari,
A haka har bacci ya kwashe ni sai ana sallah magriba sannan na tashi,
Wanka nai na shirya cikin wasu kana nan kaya riga da wando rigar iya gwuiwa ce  na daukko karamin mayafi kalan kayan na daure kaina dashi ina zaune na idar da sallah wayata ce ta fara ringin ya Asif ne tsaki nai na ajiye wayar wani kiran ne ya kuma shigowa nan ma ban picking ba,
Aunty ce ta shigo me kike yi ne haka ana kiran ki baki dauka ba sallah nake nace mata to ki fito parlo ya Asif yazo,
To ni mai zan masa oho miki ki dai fito yana jiran ki in kuma baza ki fito ba to ki fadan,
Ba yadda zanyi haka na bi bayan aunty najma yana zaune shida ya suhal yana ma Fatima wasa, ya suhal ne ya fita sannan aunty najma ta dau Fatima ta fita aunty ya zaku fita,
Naga za'ae ganawar sirri ae sai mu baku waje tabe baki nai lallai kam
Sis ya kike lapiya nabashi amsa a takaice nazo ban baki ne game da me fa abinda akai miki dazu to ae ni ban dauki wannan a matsayin laifi ba nasiha ce akai min yawwa tunda kin gane hakan yayi dai dai to amma dan Allah ya kamata ki dau daya daga cikin abinda aka fada in so samu ne ma ki hada duka,
A cikin masoyan ki ki duba ki zabo wanda yai miki kar azo ana baki wanda be miki ba,
Tom shikke nan zan duba Naureen ya fada dago wa nai na kalle shin dan jin yanda ya fadi sunan pls Naureen kiyi haquri akan abinda nai miki abaya dan Allah ina so kiyi haquri ki manta komai ya wuce mu cigaba da zumunci ki dauke ni kamar ciki daya plz kokarin durkusawa yake da sauri na dakatar da shi bakomai ya Asif komai ya huce,
Haka yai ta Jana da hira har sai da yaga ba sauran bacin rai a tare da ni sannan yace najo na raka shi wata unguwa,
Daki na shiga na daukko mayafi sannan na fada ma aunty muka fita,
A wani store muka tsaya ya fito ya buden kofa ya Asif irin wannan abu haka sai kace wata yar mulki to ae dole na lallaba ta hannun daman dariya nai au kaima haka zaka ce eh mana,
.
Shiga mukai yace na zabi duk abinda nake so wajen cosmetic naje wata kit na dauka,sannan na dibi chocolates nace wannan ya isa,
Ah sweet sis gaskiya ki kara ya isa haka wajen taddies yaje ya fara diba ni dai ina biye dashi
Har muka gama yaje ya biya kudi sannan muka tafi gidan aunty najma ya kai ni to ni dai daga nan Kice masu na huce gobe su mamee zasu dawo zaki ne eh ina jin zan je tom shikke nan sai da safe na bude kofa na fita shi kuma yasa me gadi ya shigo min da kayan kai daman ya Asif ni ya Siyama wannan kaya haka tab,
ya Asif Ke nan waya na dauka nakira shi ya Asif ae kayan sunyi yawa fa, duk ni kadai ae naga har yanxu kina son taddy shiyasa na siya miki,murmushi kawai nayi daman yana hattare dani ne na tambayi kai na,kin yi shiru ina jin ka, in kuma baki so sai ki ajiye ma Fatima tab ya Asif ina so tom shikke nan
Ae bawani abu bane dan na siya miki wannan wanda ya fisa ma zan siya miki to nagode sai da safe naka she cikin jin dadi kamar ba mu taba samun sabani da ya Asif ba,
Su mamee sun dawo ana zaune a dinning suna hira cikin jin dadi dady ya kalli Sameer son wai yana gan ka haka ba wani kuzari dady bakomai kawai gajiya ce,
Sannu sai kaje ka kwanta zuwa wani lokaci,
shi kuwa duk tunanin heart disire din sane ya dame shi gashi tun wannan lokacin be kuma ganin ta a instagram ba gashi be san sunan ta bare ya searching nata a Facebook Allah ka bayyana min ita hk yai ta tunani
Masu zuwa yi Musa barka da zuwa suka fara zuwa ana farin cikin ganin su,su Rauda da Huda ne suka shigo tare da Momeen su da gudu mas'uda ta tashi ta rungume su I miss you so much sisters ina sis Naureen ne,
Tana gidan aunty najma au daman ba da ita kuka je abujan ba eh,
yayi kyau sis Huda kira mana ita tazo tom kira tai bata dauka ba siririn tsaki tai bata dauka ba Ayya ko tana aiki ne Kila amma gaskiya anan zaku Kwana ko,Rauda ce tace wai ina ya Sameer ne da saleem yana dakin sa ae shi ya riga mu dawo wa,amma gaskiya kun canja da yawa kun kara girma ae Kema haka Yasmin da Saleem ne suka shigo da gudu nan suka sake karewa da ihu ana murnar ganin juna.................????
.
Shi kuwa Sameer yana dakin sa hayaniyar suce ta ishe shi,kai wannan yaran zasu samin ciwon kai ya fito ya shigo bangare rai bace,
Wai ku har yanxu bakuyi hankali bane kun dami mutane da ihu kamar wasu yara ya juya yai ficewar sa,
Rauda da Huda ne suka tashi cikin mamaki kai wannan fa me yakawo shi gidan nan mas'uda ce ta ce kai ya Sameer ne baku gane shi ba ne,kun san shi baya son hayaniya in yana nan ba'a magana me karfi tab ae kuwa mun taba haduwa da shi kwanaki a ina yasmeen ta tambaya munje shopping ne tab amma baku gane shi ba,uhmm gaskiya ya Sameer ya girma da yawa,
Rauda ce ta dau waya da sauri ta fara kiran layin Naureen cikin bacci ta dauka rai bace dan tun dazu take jin ana kiran ta ya akai ta fada Naureen kina ina ne me ya faru ta tambaya ki zo gidan su Mas'uda yanxu da labri  bacci nake ta bata amsa cikin ko in kula ta kashe wayar ta,Abun ba karamin haushi ya ba Rauda ba sunyi shiru suna kallon ta sunje abinda tace sabida a hands free tasa tab har yanxu tana nan da muskilan cin ta saleem ya fada,
To basai tai tayi ba Rauda ta fada kuma wllh bazan kuma kiran ta ba,
Mas'uda tace ae ma sis dina uxiri Kila tana wani abun shiyasa ni bata min haka wllh saleem ya fada yasmen tace nima dai haka oho ma dai
Huda ta na mamakin irin muskilan cin ya Sameer ko tsayawa bayi sun gaisa ba haka suka cigaba da hira kamar ba gobe,
Naureen wai baza ki gidan mamee bane aunty bana jin dadi ne amma inaji daidai zani tom shikke nan yar mulki wai Ke dawa sai wani hade rai kike Hala en muskilan cin sun zo uhmmm aunty Ke nan ni kawai ammee da Abee nake son gani wllh too ki bari ma sun kusa dawowa fa nadai gaskiya a'a to sai kiyi abinda kika ga dama,
Ya suhal ne ya shigo in kun shirya ku fito mu tafi ita baza ta je ba kanta na mata ciwo aunty Najma ta bashi amsa to Allah ya sawwake,
Aunty ki barmin Fatima a'a da ita zan tafi,Suka fita suka barni Abee nakira yana dauka na fara kukan shagwaba lapiya uwata ta kaina Abee ni dai gaskiya ina son zuwa to kibari mana mun kusa dawowa fa ni dai gaskiya Abee ina son zuwa to me zaki na fada dade ban ganku ba ina missing naku,
To keda najma zaki tawo a'a ni kadai ki bari nan da three month fa zamu dawo fashe wa nai da kuka gaskiya nidai Abee sai nazo Ammee ce ta karbi wayar daughter ya akai ni ina son zuwa ammee dan Allah kisa baki tom shikke nan kiyi shiru zamu yi maganr duk yanda mukai zan miki magan to ammee shiyasa nake son ki kiss na watsa mata ta wayar ta kashe tana dariya yar rigima Ke nan Abee sai kaima suhal magana a shirya mata ta tawo ita kadai to ae Kaga ita kadai son zuwa ammar ne yai magana Abee in fa akace duk abinda take so za'ae mata to fa gaskiya sangarta ta za ae,
Ba wani sangarta shekaranta daya bata zo ba nima nan kaina ina son ganin ta Ammee ta fada tom shikke nan Allah ya sawwake ya tashi ya fita,
Ni kuwa tuni na fara nemo passport dina farin ciki ya ishe ni ina ta Allah Allah aunty ta dawo,Suna dawowa da gudu na rungume ta mene haka har kan ya daina ciwo uhmmm albishirin ki aunty me ya faru  Abee yace zan je gida sai mu taho tare, uhmmm Naureen Ke nan dan canja zance ban yarda ba
Nasan halin ki Kila ma kiran sa kikayi kika takura masa to aunty ni na dade fa bangan su  ba,to in kikai haquri Saura wata uku su dawo nidai tafiya zanyi tom inkinje Karki dawo dariya nai nashige daki cikin farin ciki..................????
===== SANADIN SULFIA 004 =====
Irin wannan kwalliya haka sai ina kuma,
Nasan dai baki da wasu kawaye sosai a garin bari Kice can zaki,
Tab aunty an barki a duhu ae idan kika ga kawaye na sai kinyi mamaki
Manyan yara ne masu Ji da gayu kuma wllh duk su suka ce suna so na da kawance ah lallai kam sabida kin iya wanka ba haka bane aunty kawai farin jini daga Allah,
Sukai dariya gaba daya  Siyo turaren dana ce miki zani shine nake so naje dan nawa duk sun fara kasa sai ki kira driver ya kai ki aa aunty zan nemi abin hawa yanxu zan dawo ina baby Fatima tana can yanxu nagama shiryata tare zaku eh nace ina kokarin fita.
Fatima yar aunty yar kimanin shekara daya da Rabi tana da kyau ga wayo shiyasa jama'a Ke son ta.
My baby zo mu tafi na dauke muka fita bamu zame ko ina ba sai alpen store dake kabuga kanti sai da Arabian performs ina zaba Fatima tana ta gwarancin ta cika hannu na tai tayi ta tafi da saurin ta tana fadin Abba Abba tana ja masa riga,
Juyo wa yai da saurin ganin cute baby yasa hannu ya dauke ta yana mata wasa, Gaba daya hankali na yana kan turaren da nake zaba  sai da naga naga ba Fatima ya salam na fada hankalina ya tashi ina ta shiga kar dai ace wani ya dauke ta,
Neman ta nake ina Fatima Fatima na biyo ta daya side din sai gano ta nai a hannun wani suna ta dariya kamar ta san shi da sauri na karasa  wajen su Ke tawu mu tafi,
juyowa yai ganin wadda take magana yasa ya furta Alhamdulillah a fili, Fatima Kije ku tafi ta make ka fada ah'ah Ke tawo mu tafi kememe taki zuwa waje na kinga yarinya kamar kin san shi,
Maganar da yai ne yasa nai saurin kallon sa take annurin fuskata ya tsaya wannan dan wulakancin ne  wanda yai min hulakan ci Jan hannun ta nai amma sai ta sa kara haka na barta nai gaba wajen biyan kudi
Me karbar kudin yace anbiya  miki tsawa nai masa nace rokan sa nai in zaka karba k karba in kuma baza ka karba ba na ajiye muku kayan ku na fita ba shiri ya karba ya zuban a leda,
Sam ban gano su ba daga fatiman har shi ,na kuma shiga sabon tashin hankali yau na shiga uku?? da sauri na fita har ina tuntube
Ganin sa dai nai a cikin mota na saki ajiyar zuciya da na karasa wajen cike da masifa Kwance take a jikin sa da alamar bacci tayi bani ita zamu tafi tunda baka da alaka da ita murmushi yai wanda ya bayyana tsantsar kyawun sa ni nake da alaka da ita tunda ta kira ni da Abban ta dan hk tun daga yau ta zama 'yata wani kallon wane kai na watsa masa
Kaga ina da abunyi ka ban ita kamin nai maka ihu ko na kira security,Cikin sanyin murya yace haba kiyi haquri in akayi mutsi da ita sai ta tashi eh bani ita mu tafi Alama yai min da hannu nai shiru sakin baki nai na tsaya ina kallon sa lallai Kaga mutun ya wani rungume 'ya kamar yar sa,
Fito wa yai a hankali ya bude kofar baya ya kwantar da ita a hankali,Tsayawa nai ina kallon sa cike da mamaki sannan ya karaso inda nake plz kiyi haquri ki daure ki shigo na kai ku bana bukata ban zan shigo ba Wai ma mene alakan mu da kai kaban 'yata na tafi,
Kiyi haquri ki shigo kinga tayi bacci kuma ga kaya a hannun ki Bazan shiga ba ae sai ka rufe ni da duka na kawo kaina har cikin motar ka pls dan Allah ki shigo mu tafi,
Wata matace ta karaso inda muke haba 'yar nan be kamata dan kun sami sabani da mijin ki kuma ki tsaya kuna hayani ya akan hanya kowa yana kallon ku,
Kuyi haquri in kunje gida kwa sasanta to hajiya an gode yace mata, Mata ta cigaba da yimin nasiha Hajiya ni fa ba mi jina bane nace mata haba yarinya wane zai yadda da maganar ki,dan kun sami sabani kuyi haquri ga shi harda rabo a tsakanin ku ta nuna Fatima dake mota tana sharar baccin ta,
Lallai ma dan kar na kuma magana taga nai mata kafiya nace nagode,
sannan ya bude murfin motar na shiga.....
.
Tafiya suke a hankali ba wanda yai magana ina zamu inda kai niya, na fada ba tare da na kalle sa ba kai amma naji dadi bari na kai ku wajen mamee kinga gobe sai a daura aure daman a gida ance na kawo mata kinga na fito a sa'a kallon rainin hankali nai masa kanne min ido yai??
Dauke kai na nayi dan kallon da yake min ya fara isata nan na fada masa inda zai kai mu ban kuma magana ba har sai da muka zo waje layin da zamu shiga sannan na fada masa,
Dai dai bakin gate din ya tsaya da sauri na fito na bude baya da niyaar daukan Fatima amma a kulle kallon sa nai nace ka bude sannan ya unlock na bude na nauke ta wanda har yanxu baccin ta take wai ake wannan kece sheman wannan bacci haka har a sace ki baki tashi ba na fada a rai na,
Na shiga gida da sauri,sai sauri take sai kace wadda za'a siyar ya fada yana shiga mota  fuskar sa dauke da murmushi kamar wanda ake ma albishir da aljanna??
Ganin ta manta ledan yasa ya kuma sakin wani murmushi  sai da yai kunsan 5munites sannan ta dawoyana zaune a mota Kaga baka Ji ba yai mata shiru lallai ma wannan dan rainin hankalin malam ta kuma kiran sa nan ma shiru kwankwasa glass din tai sannan ya dago ya kalleta da narkakkun idon sa da sauri ta dauke idon ta dan baza ta juri wannan kallon nasa ba wanda ya yasa taji duk wata tsiwarta ta kau
Da magana ne yace mata na manta kaya na ne sai a san nan ya bude ya fito  da biki manta kayan ki ba da haka zaki tafi ba sallama shiru nai ban amsa masa ba Nasan abinda nai miki nai yasa kike min haka amma dan Allah ina neman afuwa a yafe min,
Me kai min na fada tare da dauke kai ina kallon wani wajen plz baiwar Allah nasan baki manta ba kawai  irin halin nan naku na mata ne plz kiyi haquri daga ganin ki baki kalan wadan da Basa yafiya ba kiyi haquri for sake of our daughter Fatima pls  our daughter na sake maimaitawa eh ko banda ni za'ae min kabilan ci plz dan girman Allah kiyi haquri yana kokarin durkusawa nai saurin dakatar  dashi na haqura miko min na tafi,
Kawai dai kin fada ne amma har yanxu alamu sun nuna baki haqura ba dan Allah kiyi haquri sarauniyar kyawawa haka ya dinga yimin daddadan kalaman sa wanda yasa ha na saki raina.
Queen baki fadan sunan ki ba kai rufan asiri kafadi wannan sunan a gaban wasu ae su daken kai akwai wanda ya isa yai miki ko kallon banza bare takai ga duka
Murmushi nai nace akwai mana da sauri yace wane kai na nuna shu da hannu ya Allah akwai ki da dawo da bara bana  Ni dai ki fadan kar ki wayen ce kiki fada wani murmushi na kuma saki wanda ya tona asirin kyau na
Sunana Salmah sai da ya kalle ni sannan yace ni baki tambaye ni sunana ba ko baki son Ji murmushi na kuma saki sai dai in kai ne Bakai niyar fadan ba
Sunana Sameer ya fada nice name, Amma ina neman alfarma tame sai dai tai jim sannan yace your phone number ban da waya to ga wanan yana kokarin ciro wa daga aljihun sa, Da wasa nake  na fada,
lallai ma da ma ku tsofaffin nan kun fiye zolaya kamar ya na bata fuska
ae sunan kaka ta kike da shi kinga ae Ke granny dita ce ki daure ki bani ma dinga gaisawa da Ke in baki so sai mu dinga gaisawa da sweet Fatima dariya nai sannan na karbi wayar sa da sauri na kalle shi................????
.
Da sauri na kalle sa ganin picture din mu akan screen din wayar shima kallo yake sama sa nai sannan na bashi,
Bani wata Leda yai ga wannan na baby Fatima ne ah'ah ka barshi me zatai da shi hka ta fada miki ae kk bata fada ba haka ne to ki kai mata in tace bata so sai ki bayar kya ari bakin ta ki ci mata albasa
Murmushi nai san nan na karba ya miko min tawa na karba na shiga gida A Palo na zauna sai naga kin dade dg bari ki daukko kayan ki wallahi tsadani yai aunty da magana  ga wannan wai a bawa fatima,
Aunty Fatima dai ah'ah ita yace to Ke ma dai har yanxu da sauran ki baki da wayo ae yasan in yace Ke ba karba zaki ba shine yace haka
Lallai zazzage ledan mukayi turaruka ne kala kala hadaddun Arabian da kuma Zuma,dabino da su bagaruwa da sauran su wannan ne na Fatima aunty ta fada to ba sai ki dinga fesa mata ah yai mata karfi 
Sai dai a bata dabino da Zuma shine zai mata amfani amma wannan dai naki ne to aunty Kema ki duba ni na siyo nawa
Uhmmm kawai ki tattara kayan ki ae turare Basa kadan haka na tashi aunty bare naje daki nai Ajiye ledan ne ina tunani amma fa guy din nan yayi ina tsaka da tunani aunty ta shigo ga  wannan shima a ciki yake wata karamar akwati ne me dan Karen kyau karba nai da Alama mamaki a tare da ni
Kuma tawa ce tambayi kan ki ni aunty wanan mutun me yake nufi oho  Ni nadauki turare daya ga sauran nan tom  Wannan fitar dai ba'a yita a banza ba ammana kamu aunty Ke nan Allah yasa ba tsoho bane ta fada da tsokana dariya mu kai sannan na ce mata nifa ba saurayi na bane aunty Kuma ba son sa nake ba uhmmm to menene sarkin iya hada zance wanan karatun naki ya dace dake.
Na fa sanshi tun tuni nan na kwashe yadda mukai dashi na fada mata  Ayya sis ki masa uxiri mana Kila a lokacin akwai abunda Ke damun sa shiyasa yai miki haka ba wani nan aunty kawai dan yana da kyaua to ae Kema haka
Kuma kinga da halin sa ne hulakanci da yanxu ko kallon ki bazai ba hka ne kuma fa, Kuma ko number da na bashi ban fiye amfani da ita ba kinga bari ma na kashe wayar kar ya ishe ni
To me yasa kika bashi akwai dalili shiyasa zaki gani nan gaba a'a ki fadan inda shawarar da zan baki sai na fada miki  Aunty ae ko zan karbe shi sai na na ja masa aji,
Ke yanxu fa an daina wannan yayi sabida wasu Basa daukan wannan sai su kyaleka su sami wasu mata yanxu sunyi yawa, Ae kuma idan nai accepting nasa da wuri zai ga daman son sa nake
Ke dai kiyi a hankali duk dabarar ki wasu mazan sun fi ki amma bance kar ko ja aji ba hakan na da kyau dan su ma mazan sun fi son mace me kamewa tom aunty zan yi dabarun mu na mata
Ki dai yi a hankali kin manta abunda na karanta ne eh ko ina son sa bazan nuna masa ta farat daya ba Kamar kukan Fatima da sauri suka tashi suna rige rige kuka take sosai ta fado daga kan kujera daukan ta nai ina jijjaga ta har tai shiru sannan na baje mata kayan wasan ta
Inai mata wasa kamar wata mara abun yi aunty tsayawa tai tana kallon mu au ko daukan ta baza a bari nayi ba balle naji dumin ta Kai aunty najma wasa fa take kar a katse mata
Kar dai a katse muku wasa dan Ke ma har yanxu kina nan da halin ki na wasa kamar wata yarinya  Ni  nagaji ma bari naje na huta baki ci abincin ki ba anjima na ci uhmmm Ke dai baki son cin abinci shiyasa kike kamar kara dariya nai daki abuna..................????
   
.
Shi kuwa Sameer wani farin ciki ne ya baibaye shi ganin ya sami wadda ya Ke mafarkin samu  yanxu kuma Saura me? Gidan su Mahmud abokin sa ya tafi da farin cikin sa,
Mahmud na kokarin fitowa shi kuma yana sa kai ah ya abokina kai ne yau a gidan namu uhmm wallhi wani albishir nazo na ma
Me ya faru albishir aka ma za'a baka governor bank ko kuwa minister kai duk ba wannan wato aboki na hadu da wannan yarinyar da nake fada kai Masha Allah ah dole kai murna
To wane party za'a hada mana party kuma sai kace wanda na aure ta tab ae sai dai kaje kai ka sami alaranmomi kuyi min sauka da niyyar Allah ya mallaka min ita
tab lallai ma aboki ka tafi da yawa daman irin ku baku iya so ba,to yaushe zani na ganta mu gaisa ba yanxu ba to ace muna gaisuwa tom zan fada mata
Bari naje gida au baza ka zauna ba banga ta zama ba yanxu ma mamee zan je na fadawa too babbar magana,daman abinda nazo na fada ma kenan to Allah ya tabbatar da alkhaeri Mahmud ya mika masa hannun suka tafa ya fita,Yanaa isa gida ya tarar da mame a parlo tare da su mas'uda da Yasmin ah son yau yana gan ka cikin farin ciki wllh mamee abinda nake nema na samu yau to Masha Allah
Saleem ne ya tsugul yace  yaya menene sai daga baya  zaku Ji To yaya kamata yai ace ka kai mi shopping na taya murna sannan muga gari mas'uda ta fada tana kallon sa,
Yanxu ina da abunda zan yi amma in Allah ya yarda zan kai ku in na sami lokaci to Allah yasa To ku bamu waje zamuyi sirri mana au yaya akwai abinda zaka boye mana aa amma wannan sai mamee taji sannan zaku Ji tom
,
Haka suka tashi sunan mamakin wannan canji na yayan nasu,Yasmin gaskiya wannan abu da yasa yaya farin ciki ba karamin abu bane mas'uda ta fada uhmm nima wllh abun mamaki yake bani,
kika sani ko a gidan su budurwa sa akace ya turo tab lallai ma mas'uda yayan ne yake da budurwa,To haka zai zauna baya soyayya amma wanann budurwa zata sha muskilanci,
yi mata zai yi Ke irin su yammata sun fi garasu zan so na ganta mas'uda  ta fada muce ya kai mu mu gaishe ta Ke yaushe kika ga fuskar dan ma yau yana farin ciki da bazai ce zai kai mu ba da sai dai kawai ya watso mana a kudin,
Bari naje na jiyo mana hirar ba ruwa na wllh Ke dai Yasmin kin fiye jan maganaLabulan taga suka daga suna kallon su amma Basa jin me suke cewa,Mamee  tace ni to wannan murna ae na dauka cewa sukai ka turo ah'ah mamee to Allah yasa albarka ice ko dai 'yar gidan mutunci ka samo me tarbiyya  wallahi yarinyar tana da hankali ga nutsuwa kuma Kaga ta da kyau sai dai kinga ta mamee  tom shikken in Alhaji ya shigo nai masa zance
Yawwa mamee nagode Allah ya kara lapiya bari na shiga ciki tom Lallai wannan wace me sa'a ce haka ina ma a cikin yan uwan sa take da naji dadi
Sameer na shiga dakin sa cikin azarbabi ya kira wayar ta amma akashe ya kira yafi  kirga kai kodai wrong ta bani anyya kuwa zata min haka kuwa to ko aiki take shiyasa ta kashe bari anjima na kuma kira haka yai ta tunani har bacci ya kwashe shi
Naureen ce ta kira mas'uda nayi fushi sister har yanxu baki zo ba ayi haquri sisi na wallahi ina nan zuwa ya kike lapiya lau ran nan me yasa kikai wa Rauda haka Ke kyale ta wanan yar rai nin hankali ce uhmmm
Wai ba wani labari ne Naureen ta tambaya akwai mana amma sai kin shigo to zan shigo in Allah ya yarda dan nima na kusa tafiya ina zaki Turkish tom shikke nan
Ina Yasmin gata nan Yasmin ta karba gaskiya aunty na nayi fushi haryanxu baki zo
Aiki ne yamin yawa amma zan zo a week din nan tom aunty in kinzo Kwana zaki a'a mas'uda ce ta kwace wayar ta kashe kar ku cinyen kudina ki kira kuyi hirar ku...............????
.
Naureen ce ta kira Yasmin suka cigaba da hirar su Gaba daya hankalin Sameer baya jikin sa dan kullum sai ya kira wayar ta a kashe ga aiki yai masa yawa a office be dawo da wuri bare ya je messages kuwa aiki mata su yake kamar me
Me yake faruwa ne me yasa zaki min haka Salmah plz haka yake ta surutai kamar wani tababbe Badan ya so ba ya dauki su mas'uda,Yasmin ameera sai Ameer  suka tafi shopping suna masa hira amma.shi sam baya fuskantar su hk suka ja bakin su suka tsoke
Na shirya tsab na dau mota nai gidan mamee dake sharada phase ||| (3) zan musu zuwan bazata dan ko fada musu Banyi ba ina tafe cikin jin dadi har na isa gidan ina shiga harbar gidan saleem na fitowa ah'ah sai yau gaskiya munyi fushi ki koma au hka zaka ce plz amin afuwa tom shikke nan yar uwa amma kin daki gurbi,
Basa nan Ayya ina  suka tafi mamee taje gidan hajiya kaka ta gaishe ta su kuma sun fita shopping da ya Sameer kash to kai kuma yanxu ina zaka gidan su wani friend dina OK in sun dawo ka cema mamee nazo
Su kuma zamuyi waya to Kije gidan hajiya kaka mana can zasu zarce  a'a da inda zani yanxu tom shikke nan zaki dawo eh in Allah ya yarda agaida aunty zata Ji na fada mota na shiga na zoge glasses wanda suka sha tintac(bakin galas) wakar Nancy ajram ce Ke tashi a cikin motar cikin kwanciyar hankali nake tafe a nutse ina fita daga layin yana sake kai bakin glass fin dake motar ne ya hana ganin ta
Zaune suke suna hira da aunty najma mas'uda ta kira kai sis shine zaki zo amma baki fada mana ba uhmm naso nai surprising naku ne shiyasa,
Au ni na manta ba nayi fushi me ya faru shine zaku shopping kukai tafiyar ku sorry?? sisi na zan ajiye miki kayan uhmm tom sai anjima OK bye
Ina kwance a daki ina buga game din cookin fever a IPad dina waya na Samsung na daukko tsintar kai na nai da kallon pictures din mu wanda Rauda tai mana tare handsome guy gaskiya ka hadu, ko zan so ka ba yanxu ba sorryn ka uhmm lallai yarinya baki san so na sanda zaki jiki a ciki male-male baza ki sani ba nace mata wani kallon ta wurgo min ficewa nai daga dakin ina mata dariya??
Waya na na daukko sai yau na kunna tun haduwar mu messages ne suke rige rugen shiguwa tab lallai ma sai fa suka gama sanan na fara karanta wa
Yana zaune ya buga uban tagumi wayar sa ya dauka yana addu'ar Allah yasa ta shiga ringin yaji tana yi sai da ya Ciro wayar ya sake kalla number ce alhamdulillah ya fada sannan ya sa a kunne har ta katse ban dauka ba sai da yai wajen 5missid call sanan  na dauka ko ban tambaya ba nasan wane amma irin hali na mata yasa nace wanwane cikin sanyi murya wanda yaso ya ban tausayi yace Sameer ne ya akai na tambaye shi irin wannan turo sako haka sai kace wadda take aiki a  gida tura wasiku,
Kiyi haquri salma nasan baki gama hucewa ba shiyasa ki kai min haka ya kamata ki sassautan wallahi kin hora ni kin jefa zuciyata cikin rudani please Salmah ki yafe min ko naji sanyi a raina kin san yanda son ki yake azabtar da zuciyata kuwa kaji yanda yake zubo kalaman love kamar ba Sameer ba tab *SO* Ke nan...............????

0 comments:

Post a Comment