Wednesday, 17 January 2018

SHAUKIN SO Page 1 to10

SHAUKIN SO Page 1-10
.
Saurayine dan kimanin shekara 30yrs yake Jan mota kirar Accord 2016, cikin kwanciyan hankali yake tuki cikin motan kuma wani kidine mai sanyi yake tashi wakar Jennifer Lopez _what is love_ shi yake tashi, shikuma sai faman kada Kai yake alamar yana jin dadin wakar".
  "Parking yaja a daidai harabar _Sahad_ dake garin kano, sanye yake cikin  fariin yadi Wanda yasha aiki kana ganin kayan zaka San mai tsadane, kafarsa kuma wata takalmi mai kyaun gaske shima fari, hannun sa daure yake da agogon axurfa kirar campanyn Rolex,yasha kyau iya kyau fuskansa dauke da murmushi ya shige super market din."
" yana shiga ya fara binciken abinda zai saya, yana cikin duba kaya ya ga wata Yarinya kyakkyawa ya kalleta sama da kasa amma bai ce mata komai ba, ya ci gaba da sayayyarsa har ya kammala ya zo aka yi masa total din kayan ya biya ya fita, yana zuwa wurin motarsa ya bude bayan boot ya saka kayan da ya siyo, sannan ya dawo gaban motarsa yayi tsaye yana jiran wannan yarinya ta fito."
"Bai fi minti bakwai ba, sai ga yarinyar ta fito tare da sayayyarta ta tsaya bakin titi tana jiran mai taxi domin ya dauketa, yayi sauri ya shiga motarsa ya je ya faka kusa ga yarinyar ba tare da ya fito ba, ya sauke glass din motarsa tare da cewa “Assalamu alaiki ‘yan mata” sai ta amsa masa “Wa’alaikas salam” ya ci gaba da cewa “’yan mata ina zaki, kuma naga kamar kina jiran taxi ko?” tace “eh taxi nake jira” sai yace “to gani nima direbane kuma biyana ake sai ki shigo muje ko?” sai tace “a’a nagode” sai yayi dariya yace “aini ba godiya nake so ba, dan biyana zakiyi, in kai ki inda kike so sai ki biyani, ke ga ko ai baidace kiyimin godiya ba, ki shigo muje” tace “ni ba irin wannan mota nake son  shiga ba, taxi nake bukata dan haka kaje kawai wallahi nagode” sai yace “karki yimin haka dan Allah! Ai ci gaba ne nasamu shiyasa kika ganni ina yin taxi da wannan mota, amma can asali ‘yar taxi ce gareni, ki shigo kawai muje dan Allah karki yimin walakanci, ai duk dayane dani da dan Taxi, bai dace ace kamarki kina tsaye a titi ba rana tana dukanki” da kyar ya samu ya shawo kanta, sai ya fito ya kwashi kayanta ya saka Mota, sannan ya dawo ya bude mata kofar mota ta shiga ya rufe ya dawo ya shiga suka tafi."
" Suna cikin tafiya kowa bai cewa wani uffan ba, sai tafiya suke can sai ya dubeta yana murmushi yace “au nayi mantuwa ban tambayeki inda muka dosa ba, sai faman tafiya nake”.
"Murmushi tayi kan  tace “Borno avenue zaka kaini” yace “ok” daga nan bai sake cemata komai ba har suka kai kofar gidan ya fito ya dauko mata kayanta, ta dauko kudi zata bashi sai yayi dariya yace “ai bada wannan zaki biyani ba” sai tace “to dame zan biyaka?.”
" sai yayi murmushi yace “bazan gayamiki ba yanzu, amma kibani lambar wayarki dan idan natashi karba sai nakira ki, sannan kifadamin sunanki dan nayi saving dashi”.
" sai tayi murmushi mai alamar mamaki tace “hmm lamba kuma me zakayi da ita?”.
" sai yace “ai nariga na gayamiki abinda zanyi da ita, zata yimin amfani duk ranar da natashi karbar bashina agurinki zan kira ki na sanarda ke, kuma inason nasan sunanki dan nayi saving”.
"Tana murmushi a ranta kuma tana mamakinsa irin yadda yamaidata yarinya kawai sai tabashi lambar wayarta sannan tace “Suna kuma ka saka wacce kake biya bashi”.
"Da sauri yace “a’a gwara dai ki gayamin sunanki dan baki sani ba  ko wadan da nake biya bashin suna da yawa”.
  "sai tace “hmm idan suna da yawa sai ka sakamin sunan da zaka iya gane ni” sai yace “duk da haka zan so naji sunanki domin saka sunan yafi muhimmanci”.
"Cikin sanyin muryanta  tace “nima sunana na sayarwa ne” yayi murmushi yace “tow, amma duk da haka bai kai tsadar driving din da nayi miki ba, dan haka sai ki cire daga ciki, in yaso sauran na biyoki” tace “ai sunana ya zarce kudin driving din da kayimin ba” sai yace “ke dai tsadar naki kika sani, dan haka ki gayamin idan nakira ki zamu warware” ta dan ja aji, sannan tace “sunana Maryama amma ana kirana da Mama”.
"Dan guntun murmushi yayi tare da cewa “sweet name, ni kuma sunana Abdallah amma ana kirana da Abdul.’’
"Murmushi tayi tace kaima sunanka mai dadi ”.
" sai tayi masa bankwana tace zata shige cikin gida."
" shi ma bankwana hade  kuma da shige wa motarsa cikin farin ciki ya ja motan sa zuwa gida.....
Abdul na driving yana murmushi shi kad’ai Kai da Ka gansa zakaga tsatsan farinciki tattare dashi har ya karasa gidan su dake sharada phase 2, da Isar sa gida yakunsa kansa cikin falon bakinsa d'auke da sallama Mummy ce (matar kawunsa) ta amsa masa, zama yayi kusa da ita yace Mummy wlh yau am lucky fitan da nayi da sa'a na fita ya kare maganan fuskansa fal murmushi."
    "Lalle sirkina (haka take cemasa Dan yana d'auke ne da sunan kakansa, itakuma sunan baban mijinta) wacce sa'ace haka? Kodai kayi gamone da da surkuwata takare maganan tana kallonsa."
   "Keyaa yasoma tsotsawa alamar yaji kunya yace ehh Mummy wlh sai kin ganta yarinya mai hankali da tarbiya, amma fa har yanxu ni bancemata ina sonta ba kawai number'n ta na karba."
  "Ah hakanma yayi sirkina amma kayi saurin gabatarmata abinda ke ranka tun kan katsaya kallo kwad'o yama kafa."
  "Insha Allah Mummy zanyi yadda kika ce d'an baxan so na rasataba ina sonta sosai in narasata tamkar rayuwata narasa."
   "Ja'irin yaro ta wurgamasa tro &donnot pillow dake kujeran falon maras kunya."
  "Da gudu yayi hanyan d'akinsa yana dariya yace Mummy wai kunya hooo ai banajin kunya indai akan mama ne."
   "Yana karasawa daki yafad'a gado yana mai jin kansa cikin farinciki a hankali ya shafi fuskansa yafurta I love you Mama."
  "Kwanciya yayi nan bacci yayi awon gaba dashi....
Mama ma haka ya kasance da ita tana barin wajen Abdul tana murmushi har ta shige gida, a cikin gida ta tarar da ummanta tana hura wuta a kitchen tace yarnan lapiya kike murmushi ke kadai?.
   "Babu ummina kawai dai wani abune yasani murmushi tabata amsa a taikace tana shiga cikin d'aki."
   "Allah ya shiryeki inji umma da fad'i."
   "Amen tafad'a tana mai  kwanciya kan katifar dakinta murmushi tacigaba da tana Abdul kawai take ganin Funny guy ta furta a hankali.
  
         *** ***
Da daddare ya kira wayar Mama, bayan ta dauki wayar sun gaisa sai ya fara yi mata bayanin ko wanene, tace ta gane shi, sai suka fara fira harma take ce masa “halan katashi amsar bashinka ne” sai yace “a’a ba yanzu ba, dalilin kiranki yanzu shi ne dan naji lafiyarki kuma na rinka waya dake dan karki gudanmin da bashi” tayi dariya suka cigaba da waya har suka gama. "
  "Suna tsinke wayan yaringa dariya shi kadai Yakuma jin farinciki na shigarsa dawata zazzafan *SHAUKIN SO* na mama a haka har bacci ya daukesa....
"itama Mama haka kawai ta tsinki kanta cikin farinciki Wanda bata San dalili Ba, a zuciyarta kuma tace maybe it just d way funny he's shiyasa yasani farinciki da bark’wancinsa,, da ire iren wad'anan tunanin b’arawon bacci ya k’washeta......
  _*2 days later*_
Haka Abdul ya rinka kiran Mama suna gaisawa amma bai gayamata abinda zata biya shi dashi ba, saida suka yi sati biyu suna waya ya fara samun kanta, sannan ya fada mata abinda zata biya shi dashi, bakomai bane face zuciyarta kuma Mama ta amince da soyayyarsa. Sun fara soyayya da Mama cikin jin dadi ba tareda sun samu matsala ba."
  "Soyayyarsu sai habaka datake kullum suna manne cikin waya kamar Abdul ya had’iye Mama yake ji itama haka tana cikin *SHAUKIN SO* tanaji idan bata mallaki Abdul tarasa wani babban bangaren na rayuwanta. SO! SO!!..
  _Abdul azizu na kalla nace allah ya mallakawa kowannesu juna_
_Ameen yafad'a sannan yace ke neeratlurv yi sauri kidauko mana rohoto kibar surutu haka, okay nace dashi nan muka ci gaba da aiki_
"Wayan mama ne dake gefenta yasoma ringing _Sweery_ ne yafito kan screen d'in nan tadauka tasa a kunne hade da cewa."
"Assalamu Ala'ikum ."
"Daga dayan bangaren kuma akace wa'alaiki salam yake ma'abociyar kyau da wannan zazzakan muryan."
  "Cikin zazzakan muryanta tace Kai sweery kanafa fasa min Kai ".
  "Uhm toh bbyna Ba gaskiya nafad'ava by d way hope kinyini lpy."
  "Lpy lau sweery and u?."
   "Cikin muryan so da kauna yace Baby Ba lpy va."
   "Sweery what happen, Ba d'azu mukayi wayaba, zazzabine koh meye? Tayi maganan cikin voice na tausayi da so."
  "Huuhh babyna not something bad fa kawai dai am baldy missing ur pretty face and that smile of yours."
  'Cikin shagwa6a tace wlh sweery har Ka tsoratani I think wani abinne ya sameka, uhmm nima am missing you so badly fa."
  "Okay gobe zanzo toh koya kikace."
  "Yeah kazo kawai sweery na in ganka."
  "Tohm Allah ya kaimu."
  "Amen tace."
"Daga nan kuma suka sha kiransu ta soyayya sai wajajen karfe 11:00 dare suka yi sallama hade da So da Kaunar juna kowanensu yayi bacci.".......
baki da matsala, kafin ganinki naga ‘yan mata da dama amma banga wacce takai ki ba, ban kuma samu wacce ta mallaki zuciyata a ganin farko irinki ba, sannan bana jin SHAUKIN SON kowacce mace in bake ba, ni fa kasancewa ta tare dake a yanzu sai nake jina tamkar wani basarake wanda yake sarautar duniya”.
Mama ta fuskancesa tare da kallon so zuwa garesa tace “.
  "ni tunda nake a rayuwata ban taba sanin dadin kalamai ba, sai da na hadu da kai, tunda nake ban taba jin abu mafi saurin magance damuwar zuciyata ba irin kalamanka ba, a rayuwata bana banbance kamshi da wari, amma zuwanka a kusa dani sai nake jin daddadan kamshi yana shiga hanci na tare gamsar da zuciyata, tabbas ina da yakinin zaka zamo jagora a rayuwata wanda zai zamo mafi kawo taimakon gaggawa acikin zuciyata, wanda zai zamo mai kore dukkanin dattin da yake zuciyata”.
   "Abdul cike da SHAUKIN SO yace “ai ni da ke mun yi bankwana da dukkanin wani bakin ciki, na zamo fitilar zuciyarki mafi kawo haske a koda yaushe acikinta, sannan ke kuma kin zamo farin ciki acikin zuciyata wacce ta mamayeta tare da rufe dukkanin kofofinta babu yadda bakin ciki zai samu hanyar shiga, dan haka nake rokon Allah da yabarmu acikin aminci da son junan mu tare da yimasa godiya koda yaushe na babbar kyautar da ya bani wato ke!.”
   "sai Mama tace “ni kuwa ina fargaba acikin zuciyata, saboda wannan farin ciki da nake ji a zuciyata mafin dadi kar wata rana ya zamo min bakin ciki mafi kuna a rayuwata”.
   " cikin yanayin razana Abdul yace “haba Tauraruwa me yasa kike wannan tunani?”.
    sai tace “saboda ina tunani ne akan Abbana, bana tunanin zai iya baka aurena”.
    " da hanzari yace “saboda me?”.
   " tace “saboda kai ba yaren mu daya da kai ba, dangin mu basu aurar damu ga wani yare wanda ba namu ba, haka zalika dan dangin mu baya auren wata wacce ba yaren mu ba”.
   " jikinsa a sanyaye yace “in dai wannan ne ki kwantar da hankalin ki, insha Allahu ni da ke ba zamu taba rabuwa ba”.
   " sai tace “Allah yasa haka”.
" ya amsa da “Amin” sannan suka cigaba da hirarsu cikin farin ciki da jin dadi.
  "Sai da aka Kira sallah 'n magriba tuku Abdul ya Mata sallama ya tafi zuciyarsa fal cike take Da *shaukin sonta* haka itama Nata zuciyar."
        ***   ***
Bayan wasu kwanaki soyayya mai karfi takara kulluwa tsakanin Abdul da Mama, duk tsananin tsoron da Mama take yiwa mahaifinta sakamakon ya dauki alwashin bazai aurar da ita ba, sai ga dan danginsu wanda suke yare daya wato FAKANCI kamar yadda suka saba, amma tsananin soyayyar da ta shiga tsakaninta da Abdul yasa ta debe dukkanin wani tsoro ko fargabar mahaifinta, hakan yasa ta baiwa Abdul damar ya turo iyayensa dan a tsayar da Magana wato ayi musu baiko. Wannan Magana tayi matukar saka Abdul cikin farin ciki sosai. "
  "Amma yacemata da zarar yaje gida can wajen mahaipainsa zai sanar dasu inyaso ko bayan ya koma gidane sai ya turo."
  '"Mama tayi na'am da zancen masoyinta."
"Rayuwa tana tafiyar musu cikin kwanciyan hankali suna zuba soyayyarsu yadda ya kamata, soyayyane tsabtatatce Ba irin na zamaniba."
  "Abdul ya sanar da kawunsa sun yanke shawaran da zarar Abdul ya koma gida zai sanar da abbansa inyaso suji daga garesa akan wannan shawaran suka zauna."
"Haka itama Mama duk fargaba da tsoron mahaipinta datake hakan batajin zai iya hanata tunkarar sa da maganar Abdul duk da tasan abune mai wuyan yuwa amma zata gwada fasaharta ko Allah zai sa a dace."
  "Dan ita a gaskiya idan aka rabata da Abdul toh tamkar anrabata ne da numfashinta dan son sa shine bugun zuciyarta, fatan ta da addu'arta Allah yasa mahaipinta ya janye zancensa na aurar da ita wa FAKANCI yan uwan su, kuma ya mallaka Mata Abdul matsayin mijinta."

0 comments:

Post a Comment