Sunday, 28 January 2018

ZUMA SAI DA WUTA Page 1-10

ZUMA SAI DA WUTA Page 1-10
.
Na xahra Bukar
.
Su hud'u ne zaune cikin had'add'an office dinsa. Ko wanne sanye da kayan yan sanda, saishi na biyar dinsu dake sanye cikin Charcoal Gray and navy blue suit, kakkyawa ne mai cikar zati, kalan fatar sa wankan tarwad'a, ak'alla zai kai kimanin shekaru talatin da bakwai a shekaru. Tattauna issues suke game da ta'addanci da satan mutane dake addaban kasar gabadaya.
   Sun jima suna tattaunawa, daga bisani mik'ewa sukai had'e damai sallama suka bar office din. Guntun Tsaki yaja hade da kallon wayarsa dake ruri kusan awanni da suka shud'e, hannu yakai kan desk din yadau wayar hade da dubawa, miss call biyar yagani na Aunty B da na Hajiyar su. Dafe kai yayi cike da tsananin takaicin sanin dalilin kiran. Tsaki ya saki had'e da janyo side drawer na desk din ya fiddo file mai rubuce da sunan Ummi ajiki da stamp din missing daga sama, bud'e file din yayi yanai dubawa yaji an turo kofar office d'in, bai dago ba yacigaba da zabgarsa.
   Kyakyawan saurayine mai kimanin shekaru talatin da uku ya shigo, bai karasa ciki ba ya tsaye bakin k'ofar, fuskar sa ba walwala.
"Morning sir"
Ya furta atakaice.
Ba tare daya dago ba.
"Salim Abbas right ?
"Yes sir"
Salim ya amsa cike da haushin yadda ya ambaci sunanshi cikin salon rainin wayo.
Saida ya jima sannan ya Dago ya kallesa, wani mugun kallo ya aikawa mai.
"hope you're clean, kasan i dislike working with drunkard"
Kasa magana Salim yayi zuciyar sa na tafasa, ya mugun tsanan Ogan shi ba kad'an ba, banda 3 weeks suspension daya bashi ya dawo kuma yana neman wulakantashi.
Bai hankalta ba yaji ya cigaba da magana.  "kana iya komawa position dinka, amma kasani next time it won't be 3 weeks but a whole life time".
Juyawa Salim yayi ya fice daga office d'in batare dayace kanzil ba banda tafarfasa da zuciyar sa yake.
Shi kam gogan cigaba yayi da duba file din, hotunan Ummi dake ciki yad'au yanai dubawa, kallon k'urilla yakema hoton da tunanin ina zai nemota, asalima she is 10 years a hoton. Acewar hajiya kuma zatakai 19 by now. Saidai babban takaicin sa bai wuce ta ina xan fara binciko taba, a iya sanin sa a Gombe ta b'ata ba Abuja inda yake aiki ba. Rufe file din yayi hade da maida ta cikin drawan sannan ya mike ya fice daga office din. Inda maajiyar motarsa kirar formatic 350 ya nufa ya shiga sannan yama Aunty B text msg na gayanan zuwa. Jan motar yayi bai zarce ko ina ba sai gidan su dake Asokoro na cikin garin Abuja.
***
Shingid'e dattijuwa Hajiya Laurat take bisa lausassiyar doguwar kujeran palon, hannuta rike da waya tana sauraran kiran d'anta da tun daxu take danna mai kira baya picking. Babbar diyarta Aunty Bilkisu ta fito daga kitchen hannunta rike da mug tanai kurban shayin dake ciki, karasa shiga palon tayi tanai kara duban agogon hannuta hade da takaicin rashin karasowa Mujahid, gashi kuma tana da patience dake jiranta a asibiti.
Zama tayi kusa da Hajiya hade da kwantar da murya tace,
"Hajiya a hakura kawai, wanan wahala ce kawai zaki d'aurawa Mujahid, yarinyar nan fah dakanta tabar gidan Ubanta, babu wanda ya koreta, gaskia nidai banga amfanin nemo taba.."
Mugun kallo da Hajiya ta watsa mata yasa tayi azaman tsuke kalamanta.
"Bilkisu ki kiyayeni, na dauka kece babban mai hankali ashe baki da hankali, shiyasa duk cikin ku Jafar yafi yemin, shine kadai ke fahimta ta"
Shuru Aunty B tayi ba tare da tace kanzil ba, saima tsumu tsumu da tayi kamar wace aka tsamo cikin ruwa. tasan halin tsohuwar su yanzu saita dau zancen da zafi ta inda take shiga ba tanan zata fita ba.
Daidai bakin k'ofar palon ya tsaya chak sakamakon kalaman Hajiya na karshe daya tsinkawo a kunnuwansa, sallamar daya ke kokarin yi kasawa yayi jin tanai magana cikin daga murya da fusata.
"Muddin bai nemo Ummi ba saina mugun b'ata masa rai, tun yaushe mukai zancen dashi amma har yau babu feedback kuma lokaci na tafiya burina kawai ta bayyana na hadashi aure da ita"
Tashin hankali da firgici ne suka bayyana a fuskarsa, ji yayi gabadaya jikin ya sank'ame kamar jini bai zagayawa cikin jijiyoyin jikinsa. Dakyar samu karfin motsawa,
ahankali ya fara taku baya sannan ya juya da azama ya koma inda yayi parking motarsa ya tsaya hade da dafe kanshi.
Ruwane ya cinye Aunty B da mamakin kalaman Hajiya, Ummi data baiwa iskanci baya shine Hajiya take kokarin kakkab'awa kaninta, duban hajiya tayi, ganin lailai ba wasa take ba yasata fara kirkiro murmushin dole.
,
Dafe yake da kanshi kaman xaiyi kuka, gabad'aya Hajiya ta daura mai zafi, bai taba yadda Hajiya batason shi ba sai yau dayaji abunda take shirin aikatawa. Sai dai yayi alwashin hakan bazai faru dashi ba, harga Allah yana da niyya nemo Ummi saidai kudirin Hajiya yasanya bazai nemo taba saidai ma yayi fatan duk inda take a dosar kasar kar ta bayyana. Hannayan sa biyu ya hada had'e dakaiwa glass din motar noushi cikin fusata yanai huci. Horn din mota dayaji yasanya shi waigawa kallon motar data danno kai cikin gidan.
"Ya salam, from one Problem to another" ya fadi aranshi hade da saurin kawar dakai gefe tamkar bai ganta ba, cikin ranshi addu'a yake Allah yasa karta iso garesa.
.
Murmushin jin dad'i ta saki sakamakon ganin shi da tayi, taso su hadu da safe kafin ta tafi skull saidai tuni ya rigata sammako.
Gefen motarsa tayi parking motar ta kirar corolla xL sanna ta fito, jikin ta sanye da uniform din Premiere acedemy, short gray skirt da white long sleeve mai hade da maroon necktie.
Da murmushi ta doso shi, ganin ba fuska ya sanya ta shan jinin jikinta, gabanta na dukan uku uku.
"Ina kwana ya Mjay
Mugun kallo ya aikamata tare da kara shan magani.
"Da ban kwana ba zaki ganni anan"
Tsura mata idanu yayi jiran amsarta.
Kai ta girgiza.
"Naga kaman ranka abace.." Tayi shuru idonta ya ciko da kwallah
Gyara tsayuwar sa yayi hade da kokarin bude kofar motar yana fadin.
"bana hanaki shiga hurumi naba, waiku matan nan miye matsalan kune".
Guntun saki yaja cike da takaici yadda mata ke bada kansu, balle yar karamar yarinyar dake tsaye gaban sa, shiyasa har ilah baiga perfect woman data dace dashi ba.
Marairace murya tayi tace "yaya kayi hakuri, am not happy da yadda na ganka ne.
Tsaki yaja, tsayawa mata magana bata lokaci ne, shigewa yayi motar hade da janta yabar ta nan tsaye jiran tsammani.
Sakin baki tayi tanai kallon motar harta fice daga gidan, Kaman zatayi kuka ta wuce Jiki sanyaye ta fara takawa cikin gida. Duk a gaban ido Jafar, daga windon saman dakinsa ya hango draman su, tabe baki yayi, aranshi yanai fadin duk shishigi da takemai bashi zai hana ya gwasaleta taba, cusa kai ba kwarjini. Daukar wayar sa yayi ya fito daga dakin hannusa rike da briefcase da suit jacket, cikin sauri ya sauko daga stair din, inda Hajiya take ya nufa hade da mata sallama daman tuni tasan da tafiyar sa kaduna akan wani case dinsu can na kare hakkin mutane,  addu'ar saukar lafiya da fatan alkhairi tahau zuba mai, Aunty B kuwa shuru tayi gudu kartace wani abun tasha fada.
"Aunty kina nan ashe baki wuce ba" Jafar ya fadi.
"Yayanka ya shanyamu, nima tashi xan na wuce" Mikewai tayi tana ci gaba da fadin "hajiya nikam na wuce aiki, sai wani zuwan"
"A sauka kalau, ina gaida yaran" acewar hajiya cikin kota kula da yanayinta.
Daidai Bakin kofar sukayi kicibis da ita zata shigo, ganin aunty B yasata sakin fara'a hade da gaidata.
Cike da faraa ta amsa mata hade  dacewa "Junaina harkun tashi so early"
"Aunty yau bamu da exam, chilling da friends ya kaini skull, gajiya nayi na dawo, mun kusa ma gama Waec din"
Aunty B tace "Allah ya baku saa.." Cikin saurin tayi maganar sakamakon wayarta data shiga ruri, hannu ta daga mata hade da ficewa tanai kokar daukan call din, Sai sannan ta lura da Jafar dake tsaye yanai kallonta, da alamun bashi da shirin yi mata magana.
"ya Jafs sai ina haka rike da briefcase" ta fadi hade da karasawa ciki, zama tayi kusa da hajiya cikin salon yauki da shagwabe fuska..
Yace "idan kinason sani ki kirani awaya" ficewa yayi batare daya jira cewar taba.
Kaman xatayi kuka ta kalli Hajiya tace "Hajiyata waini miyasa su yaya keson kwasaleni, ya jaf da mukafi shiri saikiga wataran ya canxa min".
Dariya hajiya tayi.
"banda ke Auta idan sun kwasaleki, saiki fita batun sun kema ki sharesu"
Kai ta girgiza.
"Gaskia bazan iya share Ya mjay ba koda ma ace zaiina dukana kullum"
K'ura mata ido Hajiya tayi cike da mamakin abunda Junaina ta fad'a.
Aranta tace "Auta mujahid ya miki nisa, wannan yarinta gwara ki ajiyeshi gefe".
Afili tace "bansan shirme tashi maza kije ki cire uniform" shagwabe fuska tayi hade da turo baki. "Kai hajiyata daga magana sai korata awayance"
Harara hajiya takai mata ba shiri ta mike ta wuce dakinta dake nan kasa.
****
     Reckless driving da take bisa titin ya sanya mutane da dama da suka san ciwon kansu matsawa gefe sunai bata guri. Gudu take shantakawa iya san ranta hade da kyalkyale dariya ganin yadda kowa ya bata sarari, daidai data karaso traffic light ya nuna red, dogon tsaki taja tayi gaba ba tare data tsayar da motar ba.  Bata ankara ba kiris ya rage ta bugi motar data danno, cikin kota kula da abunda ya faru ta fizgi motar at 360. Gudu take sosai can ta lura da motar data kusan bigewa na biye da ita, tsoro ne ya kamata kasancewar last week kadai Daddy ya gargadeta da reckless driving,  bata daddara ba kuma takeyi, fatan ta Allah yasa ba yan road safety bane, dan dakyar daddy ya amso mata motar ta da sukayi seizing kwanakin baya.
.
Yadda take sharara gudu haka yake binta a baya, baisan waye acikin motar ba amma yayi alwashi koyawa koma waye lesson, dama ranshi a bace yake yasamu scape goat dazai huce haushi akanshi. Ringing din wayarsa ce ta katse mai hanzari, murmushi ya saki ganin wacce take kira, dauka yayi hade da sakawa a speaker.
"Fa'iza am driving, zan kira ki later.
Tace "Mjay karka manta by 2pm zaka zo dauka na".
Bata rai yayi yace "you know am not your driving, kuma am not a jobless man, bazan iya zuwa ba ki shiga cab" katse call din yayi but deep down yasan dole yaje yayi picking dinta bayason tana shiga motar haya. Kaman kiftawar ido yaga wayam  babu motar dayake bi, dukan sitiring yayi hade dayin U turn ya kama hanyar komawa office.
 
Ajiyar zuciya ta sauk'e ganin motar dake binta tayi gaba, ahankali tayi reverse ta fito daga supermarket inda ta shiga tayi parking, da gudu ta kuma fizgar motar, Karar shigowan msg wayarta tayi, da azama ta duba.
"Salma kiyi sauri, Malama Fa'iza ta karaso, da alamun zata dau Attendance"
Dogon Tsaki taja hade da duba tym, 12 to 2 suke da lecture dinta, amma dan maita stupid malamar harta shiga hall just 12.05, koda yake daidai take da ita. Wani mugun wuta ta baiwa motar, bata zarce ko ina sai gwagwalada Abuja.
.
Parking tayi daidai multi purpose hall inda suke da lecture. jakar ta dake ajiye gefe ta dau ta fiddo kayan kwalliya ta kara gyare fusk'ar ta dashi sannan ta bud'e kofar ta fito, cikin tsadaf ta fada ajin gudun kar Malama Fa'iza taji shigowarta kasancewar gabad'aya hankalin ta na bisa allon datake rubutu,  kallon banza yan matan ajin suka bita dashi, bata damu ba ta karasa inda maza sukafi yawa ta zauna a sit dinta da tuni sun kama mata.
Murya kasa kasa, abokinta na gefen ta yace
"Salma yau mutumiyar ki rashin kirki take ji, ta hana kowa rubutawa wani attendance"
Ajiyar zuciya ta sauke, zatayi magana kenan, Fa'iza ta juya tanai fadin sunan topic dinsu na yau, hada ido sukai tayi saurin mazewa kaman ta jima da shigowa ajin.
   Cikin rashin damuwa da ganinta Fa'iza ta cigaba da lectures dinta, tana gamawa tahau kiran attendance d'aya bayan d'aya bayan ta gargardi kar wata shegia ko shege ya bita office k'orofi, tana gamawa ta fice daga ajin.
Dariyan takaici Salma tayi, sam bataji haushi ba saidai shegia data ambata yay mugun b'ata mata rai tasan kuma babu tantama da ita take, tunda kowa was present banda ita.
Ko hira bata tsaya yi da abokanta ba, ta koma motarta taja ta at 360, department dinsu ta zarce ta fito tashiga ta tsaya bakin kofar office dinta. Hannu takai bisa kofar taji ta a bude, tsulem ta fada tanai karewa ko ina kallo sannan ta zauna tanai kallon hoton wani guy dage jikin frame akan table din. Hannu takai zata dauka taji motsi mukuli a kofar, adan tsorace ta duka kasa hade da boyewa under table.
Tsaki fa'iza tayi
"garin sauri ashe ban rufe kofar ba" ta fadi.
Turo kofar tayi ta shigo ta ajiye jakarta sannan ta shiga toilet dauro alwala.
Mik'ewa tsaye salma tayi cikin sauri tadau biro dake gurin ta rubuta "ba wani shege kowa da uban" ajikin wata takarda dake gurin sannan ta sure frame din hoton tayi waje ahankali, da gudu ta karasa cikin motar ta hade da sauke numfashi tanai kallon hoton, guy din bai wuce 36 ba, saidai kuma yayi wa Fa'iza yaro idan ma ya girme ta kadan ne
"Shi kuma wanan ya rasa waxai aura sai tsohuwar nan, lailai malama dole kanki yayi hayaki"
Surutai tahau yi ita daya.
Bangaran fa'iza kuwa, tana fitowa sallaya ta shimfud'a tahau sallahn azahar bayan ta idarne ta koma kujera ta zauna saidai wayam babu hoton data saba kalla  akullum idan ta zauna, baza ido tayi tana nema taci karaf da abunda ke rebuce, mamaki sosai ya kamata tahau cigaba da duban hoton, zuciyarta na zargi wani abu rashin tabbatar wa yasa ta kawar da tunanin.
Karfe 2 da minti goma ya karasa makarantar, parking yayi a gaban department dinta sannan yadau waya kokarin kiranta.
.
Jakarta ta zuge ta cilla frame din ciki, sannan ta juya yin reverse, Motar dazu dake binta tagani ya rufe mata baya, guntun tsaki taja hagonsa zaune cikin suit batare da jacket dinsa ba, kansa sunkuye yanai duban wayarsa.
"kut ashe ma ba officer bane, naketa kokarin boye kaina, am sure sona yake datx y yaketa bina, aikuwa xan koyamai  hankali"
Dogin tsaki taja had"e da bud'e kofar afusace.
Yana zanune yaji ana buga mai glass, bai dagoba sai wining glass kasa da yayi dan gabadaya hankalinsa nakan nambar Faiza dayake kokarin turama sakon ya iso.
"Uban wayace ga dinga bina duk inda na ratsa, ko an gayama so dolene, ko kuma ma dai ince Saceni kekeson yi dan kasamu kudi"
Ta fada cikin karaji da zare idanu,
Chak yayi da wayan ahannu, bai iya dagowa ba saboda kalamanta dayaji bambara kwai wai So, shi idan akwai abunda ya tsana bai wuce kalmar so va balle soyayya, who d hell is she dazai ma sota balle ya bibayeta, bai gaba zancen zuci ba yaji tana fadin.
"Kodayake nasan maganin ka, am calling the police saina ga ubanwa ya tsaya ma" wayarta dake aljihun wandon ta tadauka tafara dailing namba.
.
Shikam gabadaya ya gaba fusata, ba namijin daya taba mai cin zarafi irin haka balle mace, mata daya daukesu kanana k'wari wanda daga kuka banza sai shagwaba suka iya, murmushin dayasan munafarsa ya saki, sannan ya turawa faiza sakon ta fito nan da 30 min, dan kuwa zaman jiran dan sanda da zaizo arresting dinsa xaiyi.
Matsawa gefe Salma tayi tana wayan.
"Ya salim dan Allah karka jima, kayi sauri ka karaso kafin ya gudu.
Yace "Pretty  karki damu, yanxu zaki ganni, make sure kiyi keeping dinshi bizi kafin naxo".
"I'll' tafadi.
ta katse wayan.
Maida dubanta  tayi garesa, saidai har yanxu ta kasa tantance fuskasa dake duk'e, kuma window ma yayi wining dinta sama.
"Laila ma mutumin nan, mugun nan rainin wayo ne, tayama xanyi keeping dinsa busy alhalin baima kallo ni" tsaki taja tahau safa da marwa a gurin.
"Bari ma dai na kalli useless girl dinnan"
ya fadi aransa, juyawa yayi ya kalle ta, yarinya ce da iyakacinta 18 to 19, kyakyawa black beauty, jikinta sanye da white pencil jean da red top, da rad hulan yemi alade daure bisa kanta, kai komo take tanai duban agogon hannuta.
Mugun tsaki yaja hade da dauke kansan, he cnt believe abunda ke faruwa, amma yarinyar ta gaba dashi da irin insult data mai.
Tana ganin Motar Salim ya iso ta sauke numfashi, fitowa yayi tayi sauri karasawa gareshi, hade da kaimai hug
"Thank God yaya ka iso on tym" ta fade cike da murna.
Janyeta yayi yace "keda waye, miya faru ?
Hannu tasa natai nuna mai motar tana tab'e baki.
Duban motan yayi, atake yasha jinin jikinsan ganin motan Ogan sane.
"La'ilah mai salma ta tsokano mai yanxu" ya fadi aranshi.
.
Shikam Mujahid ganinsu ta side mirrow yasa shi kara daure fuska hade da fitowa yana masu mugun kalloi, hararar sa Salma tahauyi sai sannan tagano Guy din cikin frame din ne, mijin tsohuwa Fa'iza atunanin ta, saidai dalilin dayasa yake binta shine bata sani ba, kallon Salim tayi da tuni yayi tsuru tsuru tace
  "what are you waiting for, kayi arresting dinshi mana"
Karasa wa gurinsa Salim yayi, hade da risinawa yace
"Sir kayi hakuri, kanwa tace ay mata uxuri"
Girgiza kai Mujahid yayi yace,
"atunanin you are d useless person a family dinku ashe dai kana da kanwa data fita zama useless and shameless"
Shuru Salim yayi yasan hakan zata kasance.
Salma kam tagama fusata da abunda yace, tace "i tink you're d shamless person here, jibeka sanye da suit kaman mutum arziki,
Sauri rufe mata baki salim yayi
"Plz salma kiyi shuru
Cire hannusa tayi cikin masifa tace "haba yaya kanaji yana xagin mu, who the hell is he, dan kawai shida matarsa suna aiki saisu nemin raina mutane, or do they tink d world revolve around them"
Janye ta salim yayi sauri yi, yanai bawa mujahid hakuri, saidai kasan zuciyan shi yaji dadi yadda Salma ta mayar mai magana, suna cikin haka Fa'iza ta karaso
"Mjay make faruwane"
Nuni yay mata da hannu ta shiga motar sannan shima ya shiga, ran shi ya gaba bacci.
"Ban taba sani apart from student akwai dabbobi anan ba"
Kallon Salma tayi dake tsaye gefe Salim na bata baki,
tace "miya faru"
Yace "stupid gal din ta dauka sonta nake, dan kawai munyi crossing path daxu da yanxu"
Tsaki faiza taja tace "Salma Abbas maccido, ai sam yarinyar bata da kunya ga bin maza, ina zargin ma barauniya ce
Tayar da motar yayi yace "mita sace maki"
Shuru Fa'iza tayi dan kuwa bata da evidence tunda bata ganta ba, amma tana zargin itace.
Tace "haka naji wasu student na fadi.
Tsaki yaja ya figi motar hade da buda masu kura ya wuci, rikota Salim yayi yace "salma cool down mana, so kike yasaki a prison, babban police nefa".
Kaman xatayi kuka tace "and so, wana law ne yace yamin rashin Mutunci".
Masifa sosai salma tahau dakyar Salim ya lallbata ta shiga motar ta taja yanai biye da ita a tasa motar har suka isa gida hadaddan gidansu dake Asokoro.
   Suna isa momy ta iske zaune a palo, da gudu ta karasa gurinta fuska ba walwala.
"Yau kuma wace tsokana kika iyo"
Gunguni tahau yi
Salim yay mata bayani.
Haushi ne ya kama Mom tahau ta da fada, "nikam nagaji da fitinar ku, yau salim kaine gobe kuma itace, bari dai Daddy yadawo".
Hankalin Salma ne ya tashi tana mugun tsoro fadan Daddy, shiyasa akodayaushe take kaffa kaffa, hakuri tahau ba Momy kamn xatayi kuka, dakyar mom tA hakuri tanai tsokanan ta maganinta Daddy.
Banda Zagin salma ba abunda Fa'iza take a motar har suka isa  gidansu dake Garki 2,
  ya ajiyeta
Yace ki  tabbata motar ki an gyara nagaji da zama driver dinki".
Murmushi tayi tace "ba damuwa sai munyi waya"
Bye tamai sannan yaja ya koma office shidai Gida nedai bazai jeba.,( ni xarah nace xaka hadu da Hajiya)
Tana shiga Gida, Umma ta fake ta da Ido alamun tuhuma, sanna tace
"Faiza idan yaron nan sonki yake ya turo ayi magana, nagaji da wannan dangantakar taku, kusan shekaru ashiri kuna tare kinyi aure harkin fito kuma still kuna tare idan sonki yake ya turo.
Shuru Fa"iza tayi, ita kanta tarasa meke cikin zuciyar Mujahid, tun suna secondary skul suke tare as friends har yau kuma banda wanan bataga alamu love ba, tace
"Umma bafa saurayina bane abokina ne, kuma ma shifa babu so aranshi"
Kwafa umma tayi
"Karyan banza, duba fah yadda yake ji dake, ko gidansu ansanku tare, wa zaku rainawa hankali"
Faiza kam bata iya cewa komai ba ta wuce ciki, Allah yaga zuciyanta tun kafin auranta na farko takeso mujahid ganin bashi da niyya yasa tayi auranta gashi ta fito ba abunda ya canxa.
***
Cikin kayan yan sanda yayi shirin sa tsaf sannan ya sauk'o k'asa, jin shuru a palon yasanya shi ficewa waje da azama gudun kar hajiya tasan da fitar sa dan kuwa wasan b'uya yake da ita, adaran jiya ma cikin tsadaf ya shigo gidan yaci sa'an Hajiya ta jima da bacci.
Duk akan Idon Junaina dake tsaye ta window kitchen tana kurban tea, jikin ta tsaye da uniform na makaranta. Ajiye mug din tayi tama mai aikin su Lami sallama sannan ta fito waje haraban gidan inda motar ta ke ajiye, shi kuma alokacin yake kokarin tayar da tasa.
Murmushi yayi ya dubeta.
"idan bazaki damu ba kizo nayi dropping dinki"
Kallon gefen ta tayi dan kuwa batai tunanin da ita yake ba, ganin ita dayace yasa ta gano da ita yake.
Farin cikine ya cikata.
"Da gaske yaya.."
Kai ya d'aga mata, da sauri ta zagaya ta shiga ta zauna fuskar ta dauke da murmushi.
"Yaya ina kwana"
Ta fad'i.
Bai amsa ba yace,
"Hajiya bata ce maki komai jiya ba"
Kallon rashin fahimta tamai.
"wana abu kenan"
Daure fuska yayi yace ba komai sannan yaja motar.
Tace,
"ya Mjay zaka dawo daukana kenan
"A'a"
Ya fad'i atakaice.
Kallon shi tayi kaman zatayi kuka, aranta tanai takaicin gwanintarsa na kaita skull alhalin ba dawowa daukar ta zaiyi ba, kodayake ta riga ta gano shi, bata da wani amfani agurin sa sai yana neman information gurinta yake bata fuska.
Basu kara magana ba har suka isa premier Academy babu wanda yace uffan.
Sauka tayi motan, kafin takai ga mai magana yaja motar yayi gaba.
Guntun tsaki taja.
"Baima damu da yadda zan koma gida ba" aranta tayi maganar.
Murya k'awayanta taji abaya sunai kiranta, sauri sakin fuska tayi hade da sakin murmushi ta juya kallon su, kawarta Hameeda tace
"wow badai shine sweetheart dinki ba, gaskia ya hadu acikin uniform".
Dariya Junanai tayi aranta tana tunanin yadda zaici ubanta idan yasan da sunan sweetheart dinta kawayanta ke mai nuni.
Share zancen tayi taja hannusu suka shiga ciki.
Yana isa NPF (Nigeria police force Q), parking yayi ya fito k'arasawa dept dinsu ya hadu da abokin sa kuma abokin aikinsa Mubarak. Gaisawa sukayi har zai wuce ya tsaya yace.
"Mubarak nasan kasan manyan mutane agarin nan".
Dariya Mubarak yayi yace "ka shirya aure kenan, diyar wace ce yanzu nama hanya"..
Tsaki Mujahid yayi.
"Kaima kasan babu wanan a lissafina, kasan wani babban mutum Alhaji Abbas Maccido a agarin nan ? Ya fada, dukda baisan waye Alhajin ba yasan mai kudi ne ganin motar da shameless daughter dinsa ke driving.
K'ad'a kai Mubarak yayi yace
"nasan shi, babban dan canji ne (Burea de change) mai kudin gaske wanda anjima ana damawa dashi"
Numfashi Mujahid ya sauke.
"Good, inason details din komai game da family members dinsa, And plz make it Quick".
Cigaba yayi da tafiyan sa batare daya jira cewar Mubarak ba.
Dariya Mubarak yayi ya wuce, aranshi yana adduan ko abokinshi ya fara sanya So aranshi.
***
Yau lecture free day, ko wanka batayi ba ta fita palo yin breakfast, wanda k'idar gidan ne dole by 8am a hadu dining yin breakfast kafin nan kowa ya wuce zabgogin sa.
Kayan bacci ne jikinta riga da wando cotten,  gashin kanta baje babu kallabi, Su biyu ta tarar zaune kan dinning taja kujera ta zauna hade da yin mik'a da salati sannan ta kalli iyayan hade da k'ok'arin fara had'a tea.
"Dad n mom good morning"
Kunnan ta Mom ta rik'o tace,
"Salma bana hanaki fitowa da Nyt wear ba, idan Salim ko wani ya ganki haka fah".
"Kai mom bacci fah xan koma idan na gama"
Katse su Daddy yayi da cewa, "yau baki da lectures ne ko wani bak'in halin kikayi aka koroki " fuska daure yayi maganan.
Shagwabe Fuska Salma tayi, aranta tanai fadi "Daddy dai zancen shi kullum makaranta, kuma ma babu wanda ya isa ya koreni, i can defend myself".
Afili tace "Daddy bamu da lec yau, sai gobe muke da Math 105"
Yace "Good, make sure kiyi revising kafin kiyi bacci".
"Yes, Daddy" ta fada tanai dariya kasa kasa.
Mik'ewa Daddy yayi sannan ya kalle ta yace "ki zauna a gida, banso na dawo daga office naji labarinki in some kind of trouble"
"Okay Dad, Allah ya dawo dakai lafiya"
Ta amsa.
Murmushi yayi sannan ya wuce, mik'ewa Mom tayi hade da kai mata duka tace "kin daiji abunda yace wlh Salma ki kiyaye ni"
Dariya tayi.
"Momy mi nayi kuma".
Harara mom takai mata sannan ta juya da azama tabi bayan Daddy rakashi  bakin mota.
Kad'an ta iya cin abinci ta tashi ta koma Daki, jakarta ta jiya ta fiddo daukan handout dinta taga frame din hoton sa, Dogon tsaki taja, harga Allah ta manta da hotonsa a jarkarta, wani mugun haushin sa taji tunawa da yadda ya zage su jiya. Daukan Frame din tayi ta ajiye shi kan Console daidai inda hotonta dana Momy ke ajiye, harara hoton tahau yi taji an turo kofar dakin an shigo, da sauri ta kife frame din sannan ta juyo adan tsorace, ganin wanda ya shigo yasa ta daure fuska.
"Ya Salim miye haka, jifa yadda ka tsorata ni ko sallama babu ka fadomin daki"
Karasawa yayi ya tsaya gabanta hade da kai hannu bisa gashin kanta yanai shafawa.
Yace "ai nanma dakina na, yaushe kuma kika tsiro da sai nayi sallama zan shigo"
Hannu yakai kan habarta hade da dago fuskan ta sunai fuskanta juna, yacigaba "Miye kike boyewa bakya so nagani, kinsan dai no Secret tsakanin mu"
Janyota yayi jikinsa yanai kokarin hade bakinsa da nata, tayi sauri matsawa gefe hade da kara tamke fuska
"Oh yaya plz stop it, you're getting too close"
Hannu ta ya riko yace
"Just a kiss saina tafi, kinga babu wanda ya ganmu".
Takaici ne ya kamata
"Why cnt you understand, i don't have any feelings for you, tayama zan yadda kayi kissing dina cikin gidan iyayena adakina for dat matter"
Idon shine ya fara sauya launi, yace "karya kike salma, duk yadda kike hugging dina muke holding hands sannan kice baki da feelings, i know you love me kawai bakya son nuna wane".
Dafe kai tayi cike da takaicin abunda yace.
"I swear i dont love you kaman yadda kake tunani, d only people i love sune Daddy, mom n you, plz ka bini ahankali kar love din yan'uwantaka da nake ma ta koma Hatred"
Kaman zaiyi kuka yake kallan ta, yace "Salma ina sonki"
Dauke kai tayi gefe, yayi gaba zai wuce tayi saurin   rikon hannu shi ya juyo suna fuskanta juna.
Tace "yaya am sorry, babu so araina dan Allah karka ji haushi na"
Murmushi dabai kai zuciya ba ya kirkiro yace "ba komai, i hope randa kikasa so aranki ni zaki so".
Dariya tayi, dan abune ne mai wuya, tace "yaya by 9pm idan ka dawo aiki, zamuje Officers club chiiling, zaman gida ba dadi"
Ware ido yayi, yace "ba ruwana, kinsan dai Daddy ya hanaki fitan dare"
Shagwabe fuska tayi tace "don't worry satar fita zanyi yadda bazai gane ba, ko kuma nazo part dinka na boye idan yayi bacci sai muje"
Dariya yayi yace "nice idea, nizan wuce office, am getting late"
Hannu shi ta saki tace okay bye"
Sannan ya fita sukayi kicibis da momy a palo, kallon tuhuma tamai dan tuni ya riga kowa breakfast yace ya tafi ashe yana nan.
"Mom agogona dana bata ajiye naje karb'a" ya fadi cikin muryan marasa gaskia.
K"wafa Mom tayi batace komai ma ya fice cikin sauri.
****
Bayan Magrib Mubarak yasamu daman harharda Details din, zaune yake a office din yana dannan laptop din gabansa saidai rabin hankalinsa yayi gida, sarai yasan yama Hajiya laifi amma taurin kai bazai barshi yaje ya fuskan ceta ba.
Knocking Mubarak yayi ya shigo bayan anmai izini, zama yayi kujeran bak'i yana murmushi ayayinda Mujahid ya daure fuska yanai mai kallon dami kazo.
"Kwantar da hankalin ka nasamo ma komai akan Family din Alhaji Abbas Maccido"
Gyara zama Mujahid yayi yanai duban sa.
Mubarak yace "Alhaji Abbas matar sa daya Hajiya Zaituna da kuma diyar su tilo Salma, da wani saurayi da suke rike dashi a gidan tun yana yaro Salim ne sunan shi"
Anzo gurin, k'ad'a kai Mujahid yayi, sai yanxu yagane ashe Salma da Salim ba siblings bane, saidai akwai wani abun dake tsakanin su ganin yadda sukai ta mannewa juna jiya.
Duban Mubarak yayi yace "baka da komai akan Salma".
Kashe mai ido Mubarak yayi yace "kodai kana ciki ne, kaga yar kyakyawa ka susuce"
Tsaki yaja, aranshi yanai mai zaiyi da Bak'ar karuwa.
Afili yace,
"baka amsamin tambaya taba"
Nisawa Mubarak yayi  "Ba wani abu akanta, tayi secondary skull dinta a London, uban nata yaso tayi jamiar acan taki zama fir ta gudo Nigeria, uban nata sam baya wasa da karatun ta, yanxu dai nan gwagwalada take 100 level"
Jinjina kai Mujahid, yayi yanai zancan zuci.
"Tabbas biri yayi kama da mutum, sam yarinyar batta da tarbiyya amma yayi alkawari koya mata hankali da samun tarbiyyan da ubanta bai bata ba"
Sun jima suna magana daga bisani Mubarak ya fice daga office din.
Mikewa Mujahid yayi ya tattare komai gefe sannan ya fito, parking lot ya nufa ya hadu da Salim shima zai shiga motarsa, wani kallon suka aikawa juna dani kaina ban tantance kallon miye ba sannan kowanne su ya shiga motar sa yaja.
Tuk'i Mujahid yayi yana tunanin yadda xai rama wulakanci da Salma tamai, danya lura ma kallon banxa Salim yamai daxu duk akan rainin da salma tamai agabansa.
Sallah ishai da yaji ake kira yasa yayi parking a gefe hanya ya shiga masallacin dake gurin, bayan ya fito ne ya tuna da Junaina, wayarsa ya fiddo ya kirata, alokacin kuwa tanai zaune tare da Hajiya a Palo suna hira taji kirar sa.
Dauka tayi ta mike hade da matsawa can gefe da ita
"Yaya kana ina, daxu naji Hajiya da Aunty Bilkisu suna waya, kuma kaman zancen kane, hajiya nata fada.
Dafe kai yayi, yace "kin dawo gida ne "
Haushi ne yakamata, sai yanxu ya tuna da ita, tace "eh nadawo".
Katse call din yayi ba tare dayace komai ba, kallon wayar tayi kaman tayi ihu, jiki sabule ta koma ta zauna.
Tsaki yaja hade da kallon agogon sa, takwas da rabi na dare, muddin yaje gida yanxu xai hadu da Hajiyarsa, shawara ya yanke na zuwa Officers Club kafin sha daya ya koma gida, yasan by dat tym tuni Hajiya tayi Bacci.
.
Tafi mintuna ashiri da shiryawa cikin fitinannan matsatsan english wears riga da wando da sukayi mutukar fiddo da azahirin shape din jikinta, kai komo take a tsakar dakin tanai saka da warwaran neman hanya fecewa. Lek'awa tayi ta k'ofa ta hange Daddy da mom zaune parlour suna hira, susucewa tayi ta koma ta zauna hade da latsar nambar Salim.
Yana tsaye bakin mota yanai jiranta ganin call dinta yasashi azaman dauka.
"Kayan da kika shanya sun bushe" Ya fad'a cike da takaici zaman jiranta da yake.
"Ya salim am sorry kaban tym kadan, narasa yadd zan fito, su Daddy sun babbake apalo"
"Minti biyar nabaki idan baki fitowa zan koma daki na kwanta"
Tsaki tayi ta kashe wayan.
"harshi zai bata minti biyar waye shi" Aranta ta fad'i.
Wardrope ta bude tadau dogon hijab dinta mai hannu ta sanya sannan tadau wipes to goge red lipstick dake shafe bisa sexy lips dinta. Math textbook dinta ta dauka da biro sannan ta fita zuwa palon, kusa da Mom ta zauna tana dubu textbook din sannan ta kalli Daddy fuska shagwabe tace "Daddy nayi misplacing calculator dina gashi kuma ina da assignment dazanyi"
Murmushi Daddy yayi jin diyar shi taci serious da karatu, yace
"ki duba dakina cikin drawer bazaa rasa ba"
Mikewa tayi da azama, cikin sauri tace "yauwa Daddy, nagode, Mom gud nyt" ta karasa maganar hade da sauri fad'awa dakin Daddy.
Dariya Mom tayi suka cigaba da hirar su.
Kaman munafuka tadau calculator din ta fito, sad'af ta wuce hanyar kitchen ba tare da iyayan sun lura ba, cabinet ta bude ta ajiye textbook da cal din da hijab din jikinta sannan ta bude k'ofar ahankali ta fice waje bayan ta rufe da mukulli.
Salim dake tsaye yana kallon tahowar ta susucewa yayi, gabadaya ta rikitamai tunani wani abu yaji yana tsikaran shi da azalzalan zuciyan shi.
Bai ankara ba yaji ta gabansa yana shakar kamshi dake tashi jikinta.
Harara takai mai tace "wannan kallon fah, kasan dai i hate it, ka kama kanka"
Sose keya yayi baice komai ba ya bude mata motar ta shiga sannan shima yaja.
Officers Club...
.
Sun iso yayi parking, tura kofar Salma tayi ta jita gam...
Bata rai tayi ta dubeshi
"Miye haka".
Kallon ta yayi, gabadaya idanunsa sun sauya launi, hannu yasa ya fizgo ta jikinsa sannan yace "ki bani chance Salma, ina mutuwar sonki"
Kallonsa tayi cikin ido ba tare da tayi yunkurin dagowa daga jikinsa ba saima murmushi ta sakar mai hade da kai fuskan ta daidai fuskar shi suna jin numfashin junan su, kallon ta yake yanai tunanin kota amsa mar soyayyar ganin yadda ta sakar mai jiki, da kuma bakin junan su dake daf da hadewa, kallon lips din yayi, yana gaf da daura nasa yaji ta bugu uban tsaki hade dakai hannuta bisa lock tayi unlocking motar, janye jikinta tayi ta bude kofar ta fito ta zagaya bangaran sa ta window tace "kasan dai halin Daddy, karma ka fara" wuce wa tayi ba tare data jira cewar saba.
Numfashi ya sauke mai dauke da tari wahala da shaawa data motsomai, kallon joystick dinsa yayi ya ganta tsaye k'ekam, saidai ba yadda ya iya mafitar sa daya yasa hannu karkashin sit yadau kwalba mai dauke da barasa (giya) ya fara tuttulawa bakinsa.
Cikin takun isa da takama ta shiga gurin mai dauke da disco light, hadaddan gurine na watayawa, kowa da abinda ya shafe shi, ba ruwan wani da wani, wasu mazan na gefe suna rawa da yammata wasu kuma zaune suke gurin wine bar, wasu kuma makale da yammata su suna shan minti, wasu kuwa chess game sukeyi.
   Fara taku tayi gurin Wine bar taji wani a bayanta,
"Yammata..
Juyawa tayi
Yace "kin hadu fah, da irinku yadace aje Dubai hutawa.
Yak'e tayi hade da fari da Ido, aranta tace da uwarka zakaje Dubai hutawa badai dani ba, shege mai kan kwakwa.
Afili tace
"Dagaske" cikin nuna farin ciki, wayarsa ce tayi ringing yadauka hade da jan hannuta suka karasa gurin hade da zama kan long backless chairs dake gurin...
Daga can Gefe yake zaune, yana kallon abunda ke gudana agurin, agogon hannusa ya duba yaga goma ta cika, guntun tsaki yaja hade da gyara zama, ya dubi bartender dake guri..
"Bani sigari guda daya".
"Yes sir" bar tender ya fadi hade da mai lightening sannan ya mika mar.
"Sir do you need wine or beer ?
Kallon banxa da Mujahid ya wulla mai yasashi tsuke baki.
Cikin kwarewa ya fara zugarta juyawan da zaiyi ya hangota tanai kokari saka hannu cikin aljihun wanda suke zaune tare, ware ido yayi yana tuna abunda fa'iza tace mai akan yarinyar barauniya ce.
Shikam ya shagala da waya, Salma ta ciro wallet dinsa dake ajiye, budewa tayi taciro dari biyar biu dake wallet din.
Mugun tsananta Mujahid yaji hade da saurin dauke kai gareta.
Tsaki taja tana fadin "matsiyaci ko kudin kirki baya shi" maida kudin tayi cikin wallet din sanan ta maida mai abarsa ta mike tsaye, saurin riko hannuta yayi yanai mata nuni da karta tafi, harara takaima sannan ta fizge hannun tayi gaba.
.
Cike tsananin bacin rai Mujahid ya gama yiwa sigarin zukan Allah tsine uwar hegu, sannan ya mika hannu gurin bartender yana fadin karomin daya"
Mikomai bartender yayi, hannusa yasa zai amsa yaji hannu wata bisa nashi tanai shirin amsan sigarin saidai kafin yakai ga amsa ta rigashi amshewa.
Saurin Duban ta yayi dan ganin wace yar iskan ce da karfin halin shiga tsabgarsa.
"Kallamu ka gama kallo..." Ta fada cikin salo rainin wayo, kallon ta yayi saidai mamakin ganin tasa sigarin abakinta yasa shi sank'amewa gurin...
Dariya tayi ta cire sigari daga bakin ta
tace  "i never knew the decent and useful policemen smoke, much less a indoors inda babu wanda zai gansu"
Shikam ya gama kulewa da ita, tashi yayi ya canza guri dan bazai iya tanka taba yadda yake mugun jin tsananta da haushinta.
Matsawa tayi inda ya canxa tanai kuma darawa, tace "karka damu your secret is save with me, am sure irinku ke claming goods guys a gida"
Tsaki yaja aranshi yace "shameless bitch"
Karaf a kunnan ta baisan ma ya fada fili ba.
Ranta yadan sosu, sai yanxu ta gane kallon dayake mata, murmushin dole tayi tabar gurin. Fita  tayi ta wurgar da sigarin sannan tahau goge bakinta, abunda bata tama yiba asalima taimakon shi tajeyi, saidai inya san wata bai san wata ba, hannuta dake dunkele ta bude kallon agogonsa data zare ba tare da sanin saba, murmushi tayi ta cusa a bra dinta sannan tahau nema Salim su koma gida. Can lungu daga baya taganshi da azama ta karasa gareshi ganin baya cikin hayyacin shi banda barasa dayake ta kokarin sha, idon ji jajir.
"Na shiga uku, yaya miye haka" ta fada cikin tsoro, rikoshi tayi da niyya dagoshi suka fadi kasa tare ayayinda yake ta suburbuda surututai game da yadda yake sonta.
Tsaki taja, duk ya shafa mata giya ajiki, barin gurin tayi neman temako.
Mikewa tsaye yayi ya kai ido kan hannusa dan duba tym saidai wayam yagani ba agogo, k'asan gurin yahau dubawa saidai wayan, mamaki yayi dan daxu ma ya duba agogon,
"Kodai.. Ya fadi aransa, ba tantama itace amma how cms, can ya tuna daxu hannusa da nata sun hade.
"Yarinyan nan wasa take dani" ya fada, fitowa yayi  waje, kicibis sukayi xata shiga yayi saurin finciko ta hade da manne ta jikin bango, hannusa daya shake bisa wuyanta.
Zare ido tayi tanai kallon yadda ya koma mata kamar zagi, murya sheke tace "sake min wuya...
Kara shaketa yayi, ya matse ta tsam har suna shakan numfashin juna, cikin zare ido "dan ubanki, idan kina karuwancin ki, sata da rashin kunyar ki, ki tsayar can gurin k'ananan k'wari da kika saba yi suna kyale ki,  dont you dare ki kusanto gareni, am not one of those useless men da kike toying around dasu, Understand?
Harara takai mai ta kuma cewa "kasakeni ?
Sakinta yayi, yana kara kallon shegen kayan jikinta, sannan yace "ina agogona ?
"Ka bani ajiye ne"
Kara daure fuska yayi
"Tunda kinyi shaye shayan da kika saba ai dole kice haka" kara matseta
Yayi, jikinsu na gogan juna ya kuma tambayanta.
Wani irin yanayi taji da tunda taxo duniya bata taba jinsa ba, d'an matsar da jikinta daga nashi tayi ya kara matseta, daurewa tayi ta kallesa cikin dakewa gudin karya gano komai tace "bansani ba" hade da daure fuska, jikinta yahau dubawa baiga komai ba, can idanuwasa sukayi caraf akan boobs dinta, kallon su yahau yi, xaikai hannu tayi sauri sa hannunta ta tokare shi, bige hannu yayi yanai mata mugun kallo yace "Worthless prostitute kin dauka dason raina jikina ke goguwa da naki, banxa marar tabiyya" bai jira cewarta ba ya tumbula hannu cikin yar top din jikinta yafara laluban agogon shi, sai gashi ya dauko.
"Banxa barauniya" ya fada hade da tureta gefe.
Ranta ya gama bacci, saidai bazata bari yaci galaba akan taba, dariya tayi tace "ai ban cika barauniya ba tunda baka da guts din arresting dina, dan iska kawai"
Murmushin da shika d'ai yasan manufarshi yayi yace,
"We will see about that, useless girl, bani da lokacin ki" tafiyarsa yayi yabarta nan tsaye.
.
"Salma karki ma banxan nan kuka, you're strong" ta fada aranta, jiki sabule ta juya ciki takira maza biyu sukasa Salim a mota taja su sukayi gida zuciyar ta dauke da tunani iri irin. Tana isa gida dakyar tasamu ta rike Salim zuwa part dinsa danta lura sam baya cikin hankalinshi sannan tabi ta kitchen ta shiga part dinsu cikin sand'a ta gudun cikin dakinta.
Hankali kwace yasa mukulli ya bude palon gidan ya shiga, jin shuru yasa shi sauke ajiyar zuciya tare da kokarin haurawa sama.
"Mujahid.... "
Yaji kiran sunan sa tamkar saukar aradu, gabansa ne ya fadi ya juyo, Hajiya yagani sanye fuska babu annuri.
"Daga ina kake, wato ni mahaifiyar kake wasan buya da ita, ko kuwa dai ni saar kace ??
Cikin fusata ta jeromai tambayan tare da karasa wa gabansa suna facing juna.
D'aure fuska yayi yace "aiyuka sukamin yawa"
"Aiyukan banxa da haryau ka kasayin simple aiki dana saka"..
Kallan mamaki yay mata, "wai simple aiki, nemo mutum daya bata for 7 years ne simple, kuma ma just 3 month back aka san she is missing"
Afili yace "hajiya sorry to say, ya kamata ki manta da so called yarinyan nan, cox nayi iya kokarina ban ganta ba.."
Wani mugun mari Hajiya ta watsa mai kafin ya ida magana, cikin huci tace "diyar kanwar tawace so called, Mujahid ni kake gayawa maganan nan, yarinya da uwarta taci kashinka da fitsari kake kira da so called, atleast idan baka nemo ta dan niba ko adan yadda uwarta ta raineka ai ka nemo ta"
Idon shi sosai ya canxa launi, yace "shikenan Hajiya zan ajiye aikin, sai anemi wanda xai nemota amma bani ba, tunda duk kokarin da nake baa gani, narasa miyasa bakya kaunata acikin gidan nan, kowa zaiyi abunda yake so amma banda ni kuma tunba yauba kike treating dina haka" kaman xaiyi kuka yayi maganar, wuce warsa yayi ba tare daya jira cewar taba.
Jikin hajiya sosai yayi sanyi, tasan Majahid da taurin kai, tunda ya furta bazai nemo taba toh kuwa bazai ba, tsoro ne ya kamata kar ya ajiye aikin.
Zancen Abban su Mujahid ta tuna.
"Salamatu ki rage daukan zafi akan Mujahid, shi yaro idan yayi laifi baa mai duka ko zagi dan kuwa zai iya zama tsegararre, hakan da kikeyi yasa yazama mai mugun taurin kai acikin yan'uwan sa" abunda mijinta ke yawan fada mata kenan aduk randa Mujahid yayi mata laifi, Ajiyar zuciya ta sauke tana kara tuno wasu abubuwan da Abban yaranta ya fadi mata kafin rasuwar sa.
   
Cikin kunci ya karasa dakinsa, ya jima yana saka da warwaran neman mafita dan kuwa bazai yadda kudurin Hajiya ya tabbata akan shi na auramai ummi ba, ga kuma wata can Salma tanai daura mai zafi, tunowa yayi sanda ya matseta jikin sa dawani yanayi daya shiga, saidai abun daya lura ita ko ajikinta da alamun shi kadai ya shiga yanayin, tsaki yaja yace "ta saba da maza no wonder she wont feel anything...
  Dogon Ajiyar Zuciya ya sauke, aranshi sunan Ummi Salma ke yawo a kwakwalwan kanshi.
***
Bayan kwana biu...
Mujahid bai kuma fita office ba, kullum yana makale a daki, ko kiran shi akai a office saidai ya dauka yace baya da lapia, hankali Hajiya yayi matuka tashi sosai, saida taje dakanta ta lallabashi bayan tace mai ta hakura da neman Ummi harsai randa Allah ya bayyanata sannan ya saki ranshi.
    Ta bangaran Salim ma kusan hakane, mugun Haushi salma yakeji saidai sonta na nan daram aranshi.
.
  Kasancewar yau suke da lectures masu yawa, tun 10 Salma ta shiga skull. Karfe hudu bayan an fito sallah, sukaje faculty ita da abokanta Shehu da Habib submitting wani assignment da aka basu kwanaki baya kowa yayi submitting banda ita.
Zama sukayi kan dakali suna hira da musun Ball, dan kuwa Salma akwai son Ball, Suna cikin yi Malama Faiza taxo da motar ta kirar Civic tayi parking gurin ta fito rike da takardu hannuta, dawowar ta kenan daga lecture data dauki yan level 2.
Dariya Salma tayi ta kalli Habibu tace ka kalli wani film the sugar Mummy.
Shikam Habib ya dauka da gaske take, yace "miya faru, halan film din ya hadu...
"Ina fa ya hadu, wata tsohuwar matace ta auri Yaro koma ince sa'an ta, kaga couple din, ko dacewa basuyi ba, i dunno y old hags dinnan basa respecting kansu su nemi daidai dasu".
Dariya Habib da shehu suka kwashe dashi, tsaf Faiza ta gane da ita Salma take, dakewa tayi ta tsaya duban takardun hannunta duk dan taji karshe cin fuska da Salma ke mata.
Habib yace "indai akwai love ai shikenan"
Tsaki salma taja, "love my foot, kaga kamin submitting din nizan shiga Auditorium nasha Ac, kasan ban saba da zafi ba"
Shehu yace "Salma akwai fa Math 101 yanxu, kodayake Mutumin bai shigowa da wuri"
Yatsine fuska tayi tace "nikam sai 5.30 xan shigo hall, nasan Shirgegen gardin nan ba zuwa xai ba" juyawa tayi ta kara gaba.
Sai sannan su habib suka lura da Faiza dake kallon su, cikin rawar jiki suka gaidata hade barin gurin.
Ran Faiza ya gama baci, tana shiga office dinta tahau tunanin yadda zataci uban Salma.
Salam dai akwai kwakwala balle tabata F a course dinta, tunanin take can dabara ta fado mata, timetable tadau ta duban sunan wanda ke masu Math 102, Malam Dauda ne kuma suna gaisawa, mikewa tayi ta iske shi office zaune baya da shirin fita lectures, rokosan tayi akan ya bata aran space din, ba masu yabata dan kuwa bashi da niyya zuwa.
Office ta koma da azama tadau Test Question papers daya kamata ta masu test next week ta fita dashi.
Securities shida ta kira suka rakata Hall din, dalibai kam tsorata sukai ganin test zaai tuni wasu suka tsure, shehu kam kokarin kiran Salma yahau bata dauka ba, gashi kuma itace mai kokarin, nata suke kwashe idan zaai test.
.
Da sauri Faiza tahau raba papers sannan kowa ya fara, hankalinta kwance Salma bata hall din.
Sai 5.30 Salma ta fito daga Auditorium, miss call din shehu tagani, bata damu ba ta karasa gaban hall, jin shuru gabanta ya fadi, tana shiga taga kowa yayi wiri wiri da ido, kafin ta ankara taji Faiza tace "Hey Get out"
Tsaye Salma tayi, tsoro yakamata ana test, Daddy kadai take tunawa zaici ubanta idan yaji labarin batai test ba.
"Kumin waje da ita" Faiza ta fadi ma securities din.
Dakewa Salma tayi hade da watsa mata harara sanan ta fita bakin Hall ta tsaya kaman xatayi kuka.
   "Zakisan dawa kike" Faiza ta fadi a aranta hade da dailling numban Mjay, yana gida zaune gaban laptop yana dannawa saidai mintuna kadan yakan tuna haduwarsa da Salma.
   Daukan wayan yayi, ta fito waje gaban Salma cikoin yauki da kwarkwasa tace
"Mjay ya jikin ka
"Am alright, ya skull ko kin dawo gida ?
"Ina skull dai, hope dai kasha magani... Ta fadi murya a shagwabe
Salma kam kallonta take aranta tana fadi "zaki gane kuran kine"
"Faiza miya faru .. Mujahid ya tambayeta cikin rashin fahimtar yadda cikin sakon daya ta canza salon maganarta a shagwab'e.
"Ba komai" tace
Katse wayan yayi, kunya ta kamata,
Mugun kallo tama salma sannan tace "okay, i love you tooo, bye" cike rangwada ta koma ajin.
   Salma kaman ta hadiyi yawu ta mutu, tunowa tayi da worthless prostitute da Mujahid ya kirata dashi, shine ba kunya yake cewa tsohuwar nan i love you.
Haushi ne ya kuma kamata, afusace tabar gurin ta shiga motar ta taja.. Gurin wasu kawayanta area boys ta nufa, sun jima suna magana daga bisani tabar wajan zuxiyar ta fari tas.

0 comments:

Post a Comment