Saturday, 27 January 2018

BANA KAUNAR KA Page 19-23 (The end)

==BANA KAUNAR KA 19==
.
Nima zura kaina akayi cikin inji sai ma fafur inji yaki tashi sai dai wata kara ya dinga yi ka ka ka ka mutumin ya fusata ganin ina bata masa lokaci sai ya dinga dukana amma a banza mikewa yai ya fita bai jima ba ya shigo shi da wata mata suka nuna ni suna magana da turanci ni dai ban san abin da suke cewa ba na dai ga taja hannuna matanan ina jin ihunsu wasu na addua ni kuma zama nai nayi ta kuka ina zaune tace in yanka mata albasa ita kuma tana yankan alayahu sai kunama ta harbe ta tai ihu da sauri na kulle mata kafar da dankwalina sannan na kashe kunamar.
.
mahida ta dinga dariya tace mom ci gaba muji ko sun yanka ki nace bbu yanka fa bada sun yankata ma ganta wai ba zaku yiwa mutane shiru ba munyi shiru mom ci gaba mahida don Allah kiyi shiru ki barta zata laftu inta ji saukar socket.maryam zo mu tafi gida nayi shiru yace wai ma me ya fito dake? bbu abin da na boye masa zo mu tafi yace,ni fa bbu inda zani da kyar ya shawo kaina na bishi mahaifiyarsu taiwa yayansu fada sosai sai dai bbu wata sakewa da nake a gidan domin ya kasa ya tsare kullum cikin zagina yake sam ban damu ba tare amai bikinmu da kanwarsa khadiya,Allah yayi mata rahama ameen.
.
  ba zan taba mantawa da karamcin da wadannan bayin Allah sukai min ba shekara biyu khadiya ta haihu tsiranmu kwana goma na haife ku shekara takwas tsakaninku dasu wahida wannan shine labarina.Al'amin yace mom yaushe zaki koma? mom ta girgiza kai tace agaskiya nayi missing din iyayena amma ina tunanin yanzu bbu su,na mike nace gaskiya mom ni sai naje garinku koda kuwa su baffa sun mutu mahida tace tabbas nima sai naje ya amin ma yace shima za shi ya faruq yace nima zani kai nima sai na bisu amma sai na kulle baffa dariya sukai, sallamar abbanmu muka ji a falo da gudu muka fita,abba sannu da zuwa yauwa ya miko min wata leda gashi nan ke da antinki,yabawa ya faruq shi da ya amin ya wuce dakinsa.
.
washe gari misalin karfe 5:10pm ina zaune ina kwalliya ya amin ya shigo wahida gama kira kani unguwa nace to na shirya cikin wani arnan materials mai tsananin kyau daman ranar sallah bom boy ya dinka mana mu uku ni da mahida da mamy,material ne me kyau da tsada yasha aiki kamar ba a san ciwon zare ba,hatta fashion din da nai amfani dasu bom boy ne ya sai min kasancewar baya siyan abin banza akwai tsada akwai kyau ina fesa turare mahida ta shigo tace ke wahida ki dinga jin tausayin turaran mana,na harare ta ya amin ya shigo shima yayi kyau ya kalle ni kin yi kyau nai murmushi ya kalli mahida ba zaki ba ta tabe baki ta ce ba inda zani yace duk wannan kwalliyar? tace ya haidar nace Allah ya kyauta haka dai ku ka iya har mun fita sai gata da gudu wai zata.wahida zo kiji don Allah ki ban farin mayafinki ban ga nawa ba nace yana cikin kayana fararan mayafi takalmi da jakarmu duk farare mu kai amfani dasu mom ta kalle mu tace har kun shirya?
.
muka ce eh,tace Allah ya kiyaye.yaya wai ina zamu? ina wannan aminin nawa wanda suka zo kwanakin baya shida amir? eh to bikinsa akeyi karku so kuga irin naci da yai min in zo da ku wani kayataccen hotel akai fatin muna yin fakin muka fito sam bana son kallo tuni na dabarbarce ganin yadda akayo kanmu da ido da kyar na saita kwakwalwata muka soma tafiya a nutse ango da amarya muka ga sun fito mu gaskiya an karrama mu kasancewar bana son hayaniya saina mike na canza guri ina zaune ni kadai kan kujera naji dadin zama a gun domin tsalle_tsalle ake ganin mutane ai kuwa samari suka yo min ca sai dai koh kallo basu isheniba,
.
kamar yadda nake yi a makaranta sam bana kula samari kai hadda dattawan na kance ammin mji,amma an kusa bikina in naga zaka takura min in ma fata-fata.salamu alaikum,sai dana dan firgita domin ban san zuwan sa ba amin wa'alaikas salam,ya tsungunno sannu bebi ni sunana umran s sulainman tunda kuka shigo gurinnnan na kasa samun sukuni ina son inyi miki wata magana sai dai ki min kwarjini maganar gaskiya naji na kamu da sonki nai murmushi nace ah maganar gaskiya sai dai kayi hakuri domin tuntuni am mana miji ya wani zabura kin san koni waye? nai masa kallon sama da kasa ba shi da wani kyau na tabe baki yace waye shi wanda aka zaba mikin kin san Allah zan iya gogawa dashi nai murmushi na rasa wa zan ce masa sai dabara ta fado min nace ka san shahid yaro dan kwalisa,wai bomboy kike nufi nace ashe ma kasan shi gani nai ya sara min yace na barki lafiya nai murmushi,ina nan zaune sai ga wani guy yace sannu hajiya nace yauwa alhaji to ni sai sunana small ismail na jima ina ganinki sannan na dade ina fama da sonki domin na fuskanci ke yarinya ce nitsattsiya nayi bincike akan gidanku mahaifinku mutumin kirkine,da fatan zaki amsa tayina to mallam small na gode ainun batun so kuwa nima ina sonka da wannan damar kuma nake baka hakuri domin maganar gaskiya am min miji na gode da kika fada min gaskiya don Allah ya sunanki "wahida sulainman muhd,to wahida na gode.
.
BANA KAUNAR KA 20
.
wani guy yazo yana zuwa bbu wata sallama ya tsunguna gabana sannu bebi ban kalle shi ba nace bomboy ya kamata mu tafi gida what me kika ce? nace sorry na dauka shahid ne what ina kika san bomboy? nace ban gane ba ai yau saura wata biyu bikinmu kina nufin ke bomboy zai aura,ko ba mu dace da juna bane? no ba haka bane ina mamaki to ko za kai takara dashi ne? no ni da bomboy bama haka na hakura.wani guy ne ya nufo ni hadda masu take masa baya tun kan ya karaso kamshin turaransa ya cika gurin yana zuwa ya tsunguna ya kamo hannuna wata wawuyar sumba ya kai min na kuwa tofa masa yawu tare da fizge hannuna a fusace,nace kai wanne irin dabba ne a fusace shima ya mike yana shirin sharara min mari aka rike shi ta baya,yana kar ka taba musu bebi ka barni in duke ta in yaso inga uban da ya tsaya mata,
.
ita kuwa take da mai tsaya mata kasan ko waccece kar ka yadda ka tafka abin kunya,domin wannan yarinyar kanwa ce ga abokinku bomboy,sannan ta wani bangaran mata domin an kusa bikinsu.....ido ya zuba min da alamu kunya ce ta kama shi na mike da sauri na bar gun,gun motar mu na koma abin haushi har gun motar aka dinga bina raina ya baci na kudirce a zuciyata ni da zuwa fati sai de a aljanna.yaya ni dai gaskiya zan tafi amir yace haba anti wahida ko dan kinga bomboy baya gurin nai murmushi nace ai yanzu muka gama magana ta waya da shi sai sa ma ban damu ba,na fadi haka ne don in tura masa haushin ni dai yaya ka bani key din motar in tafi kwa taho,anty mahida zo mu tafi,no ni sai ya amin zai tafi shikenan ni ku bani in tafi in yaso ku direba yazo ya dauke ku ya amin ya mike mukai sallama musu sallama har kuzo kuga zugar yan rakiya sai kace shugaban kasa zasu raka an raka mu bakin mota amir yai saurin bude min mota na shiga to anti mahida sai naxo mahida ta kalle su da fatan zaku zo bikinmu?
.
ina gayyatar kowa da kowa insha Allahu zamu zo goode bye,suna daga mana hannu ya amin yaja mota.tun kan yayi fakin na hango abba zaune yana kallonmu toh abba ya dawo muka fito gunsa muka nufa abba sannu da zuwa kuya kamata inyi wa sannu ku da kuka iso yanzu daga ina kuke mahida tace abba daga gidan baba rabi'u muke na ce la! wallahi abba karya take abokin yaya muka je muka taya murnar bikinsu kaga abba inba ma zuwa muma bbu me zuwa namu yauwa wahida gwanda da kika fada min gaskiya,ya amin yace abba kayi hakuri abba murmushi yayi yace kunci arzikin auta amma da duk sai na muku bulala, mahida tace abba tsaya kaji....
.
Ni ba ruwana dame karya wai tace tawa mahida tace ni kuma ta mom da ya faruq yace ai shikenan ku wuce muka shige mahida tace me yasa kika fadawa abba gaskiya? ya amin yace gwanda data fadi gaskiya ai gaskiya dokin karfe ce in kin kula sam wahida bata iya karya ba. abba zaune yace abinda yasa na tara ku shine ina son hada aure tsakanin wahidda da shahid amma ba tare da sanin wahida ba har sai ranar da shahid din ya dawo dakin yayi tsit ba wanda yace kala abba yace alamin kayi shiru gaskiya abba ina gudun rikincin wahida shi yasa nake so a fara sanar in ta amince shi kenan ya faruq yace haba alamin wai me yasa kake nuna kana tsoron wahida ne mune sama da ita ko itace sama da mu?
.
ni shawarata anan itace in an tashi bikinsu mahida kawai a hada a daura musu aure in yaso a bar wahida a gida har sai bom boy ya dawo yanxu a sanar da smallboy shi zai yi komai,mahida tace haka shine daidai sannan ko bayan daurin auran abba kar ka hanata zuwa makaranta mun riga mun san halin wahida zata kare mutuncinta sauran dabara kuma ta mom ce sai a san yadda akai mata wayo aka boye mata. al'amin ya kastse ta wai me ku ka dauki wahidar? kuna nufin bata da hankali ko karamar yarinya ce? ni dai wallahi bbu ruwana, abba shawara ka samu wahida ka sanar nata inta amince na amince, in kuma bata amince ba ina bayan yar uwata yana kai aya ya bar dakin.zaune nake ina kallo ko da filim din ya kare sai na kashe na nufi dakin ya amin domin in samu wani kaset din nai sallama yana zaune ya hada kai da gwiwa ya dago nace ya amin lafiya yace lafiya amma ba lau ba na zauna kusa dashi meke damunka big brother yai murmushi yace ba komai bane illa ina tunanin big brother wafa bomboy tuni na tuna irin cin fuskar da bomboy yai min bbu wani namiji daya taba yi min makamancinyarta ban san sanda naja tsaki ba.nace bomboy n tsane shi na tsani halayansa ya amin ya kamo hannuna ya zaunar dani yace please my sister bani labari saboda Allah me ya hada ku ban fiya boyewa ya al'amin sirrina ba domin mun fi shakuwa fiye da kowa a gidan,don hakan bbu abin dana boye masa sai dai na lura na batawa yayan nawa rai mikewa yayi yana safa da marwa inalillahi wainna ilaihi rajiun kawai yake maimaitawa ya kalle ni ransa a bace,
.
wahida kowanne hali shahid ya shiga kece sila,domin wallahi tallahi ni shaida ne shahid bai taba shan wani kayan maye ba.
.
. BANA KAUNAR KA 21
.
.
shahid ba dan iska bane,shahid ba manemin mata bane,shahid mutum ne shahid mutumin kirki ne wanda samun irinsa sai antona kin ban kunya wahida,a da ina ganin kin fi mahida hankali amma wallahi mahida ta fiki sanin ya kamata ta fiki iya magana,ya faruq ya shigo shi da mahida saukar mari naji ya cire belt dinsa ya shiga dukana da kyar ya amin ya kwace ni ya faruq yace naji komai kuma kamar a kunennen abba ya amin ya dafa shi yace bai dace ba wannan sirri ne tsakin shahid da wahida,nima donna matsanta mata ne naji na mike nace wato shi shahid bakuga laifinsa ba baku yi kishin yar uwaarku ba sai shi ba kuji zafin abin da yayimin ba sai ni kuka ji zafin maganganun dana fada masa cool down na gode wa Allah daya tserar dani,ya kuma tsallakar dani daga mummunar manufar shahid ta son rabani da mutuncina ya goga min bakin fantin da har abada bbu mai iya goge min shi sanin kanku ns tun farko ban munafurci shahid ba na fito face to face na fada ba gaskiya bani da lokacin soyayya amma kun kafe kun goyi bayansa kuna shirin yi min auran dole toku tsaya kuji tunda nace bana sonsa bana sonsa soyayyar ba nayi toko zaku haka rami ku binne ni ba zan amince da shahid ba,domin ba sona yake ba sha'awata yake in kun kuskura kun bada goyon baya amin auran dole wallahi baku ba har wadda suka hada auran zan baku mamaki tai ficewarta .ina shiga dakinmu na hada kayana ina kuka ina fitowa na gansu a falo ina cikin jan akwatina ya amin ya fito lafiya ina kuma zaki? bar muku gidan zanyi tunda bakwa sona, din Allah madadin ku dawo da shahid tunda shi kuke so shi kun fi son farin cikinsa gwanda in bar gidan tun kan ku kashe ni,na shiga jan akwatina mom ta fito tace me ya hada ku? mom sun gaji dani ne basa sona farin cikina,burinsu su muzguna min,
.
burinsu su bakantamin gwanda in bar musu gidan .mahida ta rike akwatin ina ja tana ja koda naga sun dauki abin wasa sai na sakar mata akwatin basu ankara ba sai tashin mota suka ji da gudu suka fito suma suka shiga motarsu suka bita da gudu mahida kuka ta kama. matsala gosilo shi ya taka mata birki duk da kutsa motar take yi amma ina hanyar ta tushe kasancewar motar su al'amin tana bayan to wahida,al'amin ne yai hanzarinn fitowa ya sh iga motar wahida ta mudubi ta hango shi tace cikin fushi,tsiwa da masifa ni ka fita min daga mota ko yanzunnan in kurma maka ihu,ya kalld ni cikin kwantar da murya yanzu wahida niki kewa wannan tsawar kar fa k manta nine al'amin naki yi hakuri kinji wahida yanzzu ina za ki nace ni katsina zani shi kenan bari in raka ki kinga sai in taho da motar inna kai ki kona ce eh to dawo nan in yaso sai ka tuka mu ji mu kayi ana mana hon ashe tuni wannan cunkoson ya baje a guje ya amin yaja motar na dinga ihu kamar wanda ya sato ni muma zuwa ya tisani gaba har cikin gida,ai kuwa a falo na dinga birgima ina kuka bbu wanda ya kula ni har nai mai tsata na bar gun ina daki a kwance ina jin san da abba ya dawo yace ina nake? aka ce masa nayi bacci yace wanne irin bacci da magariba maza ataso ni inyi alwala inyi sallah. wahegari gaba daya gidan bbu wanda na gaida asali ma ko fita ban yiba ina zaune mahida ta shigo wahida good morning nai mata banza ta kare surutunta ta fita tana fita ya al'amin ya shigo wahida ya karaso tare da dafa kafadata,
.
wahida ina kwana nayi shiru oh wahida fushi kike dani im sorry my sister please na mike na bar masa falon haka ya faruq ya shigo yau sister tamu lafiya muka ji gidan shiru kai har mom hatta yan aikinmu sun rude autar mom ta zama kurma haduwa sukai suka dinga bani hakuri har na sauko na dawo normall. mamy muga littafinnan ta miko min "INSIYA" na kalle ta yana da dadi? gaskiya yayi min sai dai gaskiya tana shan wahala na tausaya wa yarinyar na daya dana biyu ne ko har na uku? na daya na siyo amma ina tunanin har na biyu zaiyi sai dai na dau alwashin duk matar data karkace ta shirya karya ya wuce 1-2 na daya dana biyu in tayi na uku ba zan ko kalli litrafin ba, me yasa kikace karya ne? kina nufin duk littafin da ake rubutawa karya ne? tabbas shida tatsuniya duk kusan daya na dauke su to me yasa kike bata lokacinki kina karantawa? ai a iya sanina tatsuniya bata da wani amfani ai kawai tunda kina ganin karya banza ce to kawai ki bar katantawa tunda bbu wani abu dayake amfana miki.baba rabi'u shi ya biyu musu sadaki kowannan su dubu hamsin hamsin (50,000) haidae kuma small boy shi ya hada musu lefe akwati shida shida manya masu tsanin kyau sai sabuwar mota kasaitacciya kirar zamani kai gaskiya koni na yaba haidar domin yayi bajinta sannan na jinjinawa ya al'amin domin shi ya zubawa kannansa kayatattun kayan kicin na azo a gani,ya faruq kuma yayo musu kayan daki ita kuma mai taji da gyaran jiki yaranta takanas ta tura sokoto aka samo me gyaran jiki sannan akwai wata makociyansu yar maiduguri ita tayi rawar gani wajen fito da yaran mom din ina zaune mom ta shigo na kalle ta fuskanta dauke da damuwa,.
nace nifa mom ban gane ba ni ba amarya ba amma komai sai a dinga yii min irin na amare,anya mom ba wani abu kuka boye min ba? mom ta gyara zamanta tace auta kenan,ai abin da yasa kika ga ana muku haka don anga ku yan biyu ne ya zama dole kome akai miki ayiwa yar uwarki domin tare aka haife ku na kalle ta au shi yasa naga komai ana mana iri daya nifa abin ya daure min kai shi yasa lokacin da yan katsina suka zo naji sunce min amarya,amaryar shahid ni fa ina jin haushin in aka hada ni da shahid to ai ko shima haka abokan wasanku zasu ce masa domin sunga ku yan biyu ne ni dai gwanda a hada ni da wani sam bana so ana hada ni da shahid.......na fafa miki abokan wasa sai hakuri in fa kika nuna musu ba kya so sun dinga ce miki kenan gwanda ma ki saki ranki ki dauki komai ba komaiba nai murmishi farin ciki nace ni kuwa har gabana ya soma faduwa,amma yanzu naji dadi sosai domin na fiso ku barni inyi karatuna mom ta rungume ni tace zakiyi alfahari damu auta..
.
yau saura kwana biyu daurin aure yaune kuma muka shirya zuwa gambu gurin su mom kasancewae mu rubuta komai mun amfani da direban gidanmu domin shima dan gyanmbun ne sai dai wani abu da baku sani ba,ko da wasa bamu sanar dasu mom ba bbu wanda ya san da tafiyar sai nida mahida,ya amin ya faruq sam bamu sha wahala ba wajen gani gidan kasancewar mahaifin mom fitace ne sannan gidansu bac wani boyayyan gida bane in kace gidan tsamiya koda titi ne to za akai ka gidan,munyi sallama dan ma dai dakin gidan mai yar katanga wadda duk rabin gidan ya rushe sai dai an gyara shi ta hanyar jera wasu karare,kallo daya zakai wa gidan kasan mutanen gidan suna cikin kunci talauci munyi sallama turus mukai fakin a zaure domin wata tsohuwa muka gani tanawa wani tsoho fifita zaune suke a soron suna shan iska sai dai da alama wannan tsoho bashi da lafiya domin gaba daya ya koma kalar tausayi,tsohuwa tace sannunku da zuwa yan samari ciki ta koma ta dauko mana taburmar kaba ta shimfida mana muka zauna ta kawo mana ruwa mai sanyi muka sha sannan muka gaishe ta muka gaida wannan tsohon ya amsa da kyar da alamu yana jin jiki mu kai masa sannu matar ta zuba min ido kafin daga bisani tace yan mata yan samari daga ina kuke don Allah ina kuke?.wallahi ina muku kallon sani sannan ina ji a jikina duk daga inda kuke ku jininmune amma meke tafe daku ya roki ya amin yace nanne gidan malam abdulkadir? tsohuwa tace nanne nanne gidan tsamiya? nanne ke kuma sunanki inna furera? ta amsa ya ce yayanku nawa ko baku taba haihuwa bane? tsohuwa tace a to mun taba haihuwa shekara talatin da biyar kenan tai shiru tana matsar hawaye,ya amin ya ce ina dan da kuka haifa koya mutu? ai ba namiji bane mace ce sunanta maryam amma kasancewar yar farice muna kiranta inna wuro,gaba dayanmu muka lalli juna tsohuwa ta bamu labari kamar yadda yadda mon ta shaida mana na sanadiyar barin gidan mahida tace inna ki bar kuka domin maryam tana nan da ranta tsohuwa ta rike kai da gaske kin san maryam kin san inna wuro? nan ya amin ya bata labarin ita da dan tsoho kuka suka dinga yi gaskiya mun ga gata gun wadannan bayin Allah washe garri tun safe muka tarkato tsofaffinnan zuwa kano ta dabo. a gida kuwa hankalinsu abba in yai dubu ya tashi har katsina anje bama nan wannan ya kara daga hankalin iyayenmu har gidan rediyo talabijin kafafan yada labarai ansa cigiyarmu misalin karfe biyar muka iso tun kan muyi fakin aka baibaye mu kowa ka gani fuskarsa akwai alamar tambaya,kai tsaye dakin mom muka nufa Allah sarki mominmu hankalinta a tashe ta mike ta nufo mu Allah mom har ta rame daga ina kuke na nuna mata tsohuwa mom ta zubawa matar ido sai kuma ta fada jikinta kukan farin ciki suka dinga yi ni kuma dakin abba na shiga duk da ya samu labarin dawowarmu nan na shaida masa gaskiya su abba sun taya mom farin ciki ganin iyayenta,mom farin ciki kamar ta goya mu tayi ta sa mana albarka.
.
.zaune nake anmin kunshi su ya amin anci uwar kwalliya shida abokansu sai faman shige da fice suke yi kasancewar yau ne daurin aure,ya shiga ya tsugunnna gabana yana kallona nai dariya yaya kamar kaine angon? yace wahida kamar kece amaryar na taba baki kawai na yi shiru yace wai me dame dame kuka shirya nace ai komai ma yaya mun shirya,yanzu so nake a gama samin rani inje in anso mana dinkinmu,munyi da telan zai aiko min amma shiru yace ki bari zan anso miki amma kiyi zamanki.dan kar wahida ta san me ake ciki yasa aka daura auran a babban masallacin juma'a sai dai ita ko a jikinta,fati sun sha shi kalala sun rakashe sun case duk inda zaka ga mahida tana manne da mijinta yayinda wahida ta manne wa yayanta gwauro al'amin mamy ma tana jikin angonta faruq a ranar aka kai amare wahida sunyi kukan rabuwa ita da mahida an kai amare dakunansu sai dai ban da wahida domin baba rabiu yace a barta sai bomboy ya dawo.yau watan mahida uku a gidan miji yaune kuma na kai mata ziyara muka rungume juna hadda kukan farin ciki tare muka shiga kicin muka shirya komai bayan mun gama cin abinci muna zaune muna hira muka ji takun takalmi kwas kwas alamar za,a shigo
Aka turo kofar wata budurwace tai sallama ta shigo muka amsa ya shigo daga yanayin shigarsa dressing dinsa ko ba a fada ba kasan ko waye sanye yake da kayan sojoji ya turo kofar muka zubawa juna ido wani annuri ke fita a fuskarsa yayi kyau ainun,inalillahi ji nai sam bazan iya daina kallon kyakkyawar fuskar ba.A daren ranar haka na kwana jiki babu qwarie, ko baccin kirki ban samu nayi ba, da zarar bacci ya daukeni sai in tuno da abnda idona ya gane min, dakuma abnda kunne na yajiye min. Tabbas na cuci rayuwata, na yaudari kaina, idan masoya sukaji labarina na tabbatar da zasu shekara dubu suna tsine mun. Washe garie tunda safe na shirya cikin riga da skirt na atamfa mai manyan flowers red, hijab na dauko shima red madaidaici na saka, na jawo flat shoes suma red ina qoqarin sakawa mom ta shigo dakin mu tace "Wahida wai me kike ne da har yanxu baki fito break fast ba?" Nace "mom am ok fa" "Kamarya kin qoshi? Me kika ci tunda safen nan", "Mom banci komai ba, kawai dai bana jin yunwa ne", Karki 6oye mn komai Wahida, nasan dole akwai abnda yasa kika qoshi", Neman wuri tayi ta zauna tukuna tace dani "Wahida! Ya kamata ki fada mn damuwarki, kinga dai ni mamanku ce, baki da wacce tafini idan kuma akwai sai inji", Kai kawai na gyda mata alamar "a'a", Batace komau ba ta fice daga dakin nabita a baya ina fadin "mom na tafi skul", A parlour na samesu da Dad yana braekfast yace "auta har anyi shirin skul din kenan?", "Ehh dad na fito ken...", ban gama maganar ba naji sallamah, na dago kaina ina shirin ansa sallamar, wa zan gani? Bom boy ne tafe bayanshi da wannan mummunar matar rashi mai zubin kilaki, da qyar na iya ansa sallamar, dad fuskarshi da annuri yace "aahhh mutane lagosi sannu sannu, yaushe a garin?", Bom boy yace "wlh dad yau kwanan mu uku kenan", Mom ta 6ata rai tace "au yau har kwananku uku amma sau yau zakazo mana? Munyi fushi a koma", "A'ah mim ayi mana afuwa, wlh mun dawi a gajiye ne, jiya kuma munje gidan Mahida ne daga can muka wuce gidan farouk, daman dan mu kankare laifin mu ne yasa nace mata muyi sammakin zuwa yau, sai dare mu tafi",
.
Dad yace "tou sannunku da hanya, amaryarmu an same mu lafiya?", Cikin kisisina tace "lafiya qalay dad" har qasa ta duwa tace "Gud morning ma'am", "Morning too dear, ya mutanen gida ya baqunta?", "Alhamdulillah mom", Sai a lokacin Bomboy ya kalle ni yace "sister Waheeda ina kwana?" Mom tace "yanzu ke wahida bakiji kunya ba? Ace yayanki shine zai gaishe ki?", Nace "mom banfa ganshi bane", fita nayI ko bankwana ban masu ba, zuciyata cike da qunci da nadama, a raina ina fadin "ashe sama su dad sun san Shahid zayyi aure shine suka qi su fada mun?" Dan guntun tsaki nayi nace "tou kuma ai bai zama dole su fada mn ba, tinda sun san BANA KAUNARSHI, da wanann tunanin naja mota ta na kama hanyar skul.A 'bangaren su Bomboy kuwa da fita na mom tace "Zainab ai sai kuzo ku karya, nasan dai bakuci komai ba", Bomboy yace "wlh mom mun gode Alhamdulillah saida muka karya tukuna muka fito", Mom tace "ai sai kabari "yata ta bani ansa, nasan dai bazata qi cin girkina ba", Murmushi Zee baby tayi tace "mom wlh karki damu a qoshe muke, ai anan zamu yini dole zamuci girkin ki insha Allahu", Mom tace "tou shikenan, kuma gashi Wahida da zata taya ki firar ma ta tafi makaranta ko bankwana babu, amma da yake yau friday lecture daya kawai takeyi (10-12)", Zee baby a ranta tace "aikuwa bazamu shirya da wannan yarinyar ba, dan da alama 'yar rainin hankali ce, jifa yanda take kallo na tun daga sama har qasa, ba wai dan ta fini da komai ba kuma". A zahiri kuma tace "tou mom allah ya dawo da ita lafiya".
.
Haka nayi lecture cikin rashin fahimtar abnda lecturer'n ke fad'I, har ya gama ban san ya gama ba saida Hafiza ta ta'boni tukuna na zabura nace "ya akayi ne?", "Au baki ma san menene ba kenan? Tun dazu fa aka gama lecture har kowa ya watse, na sa miki ido ne inga iyakar ki dama", Jaka ta kawai naja tana tambayata "me yake faruwa dake ne Wahida?" Ban bi ta kanta ba na qara gaba, direct inda aka yanada domin ajiye motoci (parking space) na dosa kamar mahaukaciya nake jan motar da qarfi. A hankali maganar Shahid ke dawo mn, ina tuna furucinda dad yayi, da qarfi na doki sitiyarin motar nace "ohh shetttt! Na cuci kaina ni Wahida, me yasa na za6i kin bin umurnin iyaye na? Me yasana za6o karatun boko akan sunnar manzon Allah (SAW)? Me yasa nayi ZURFIN CIKI? Daga d'ayan 6aren zuciyata kuma tace mn ai Wahida mace dole sai tana da class, mace babu aji ai bata cika mace ba, ni d'in da maza ke bi suna so ina wulaqanta su taya zan iya nunawa wani soyayya ta?. Zafafan hawaye keta ambaliya a fuskata nace "qarya kike, baki isa ki zuga niba domin kuwa girman kai rawanin tsiya ne, "A'UDHUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM, ALLAHUMMA AJIRNI FII MUSIIBATI, WAKHLIFNII KHAIRAN MINHA" Na fada tare da parka motata a bakin titi, saida na samu natsuwa sannan naja mota ta, har na kama hanyar gida kuma na tuna da Bomboy yace sai dare zasu tafi,
.
BANA KAUNAR KA 22
.
Na fada tare da parka motata a bakin titi, saida na samu natsuwa sannan naja mota ta, har na kama hanyar gida kuma na tuna da Bomboy yace sai dare zasu tafi, corner nayi na kama hanyar gidan Mahida. Na sameta kwance bata da lafiya duk tabi ta qare cikun kwana biyu, a hankalu nake taku har na isa inda take, a kidime nace "sister me yake damunki?", Murya qasa qasa tace "wlh ciwo ne jiya jiyan nan na kamu dashi, sai fama da zazza6i nake, ga amai baya ko qaqqautaw....."
,
  bata gama fadi ba saiga wani aman, dafe bakinta tayi tare da saurin zuwa toilet, acan na sameta tana ta nishi bayan aman data gama.
Bayan samun natsuwa sosai nace "amma fa sis psychologically kina dauke da juna biyu, duk da ba likita nake karanta ba kawai sai na karanto hakan, but ya kamata ki ziyarci dr. Yayi miki awon jini". Maheeda tace "sis ai ba sai naje asibiti ba, ko kin manta da miji na likita ne?" Ta qasara maganar fuskarta dauke da annuri. "Sis nidai sai inga kamar kina cikun damuwa, ya kamata ki fada mn damuwarki idan ina da mafita wlh zanyi bakin qoqari na dan ganin na fitar dake daga cikinta, d'azu mom ta kirani tace duk yanda zanyi ince kizo gidana in bincike ki saboda bata son ganinki cikin damuwa,
.
cikin ikon Allag kuma sai gaki kinzo", A hankali na fara share hawayen daya fara bin kumatuna, tabbas nasan idan ban fadawa mahida damuwa ta ba tou babu wanda zan iya tunkara da Ita ciki kuwa harda mom.Ganin banda niyyar fada mata ne yasa tace "Wahida talk mana", A hankali na share hawaye nace "Mahida tabbas idan nace bana son Bomboy nayi qarya, tun dama can da nake ce maku BANA KAUNARSHI wlh qarya nake, kawai dan ina tsantsar son yin karatu ne, ina ga kamar idan na yarda na auri Bomboy zai hana ni karatu na, sai yanxu nake ta faman da na sani,
.
ina zagin kaina, yanzu da nasan banda mafita, saboda ya riga da yayi aurenshi"... Sosai nake kuka dan ba qaramin tausaya mn Mahida tayi ba, ta rasa abnda zata fadi sai runguma ta da tayi tana share min hawaye.
A hankali muke jin qarar taku kamar ana tafiya, ban dai daga kai na kalli masu tafiyan ba, saboda qarar tafiyar tafi karfin ta mutun daya, muryar dad mukaji yace "Assalamu Alaikum", "Wa Alaikumus salam" Mahida ta fada. Tuni na gama kidimewa dan a tunani na dad ya gama jin zancen da mukeyi.
. Ban gama kidimewa ba sai dana dago kaina naga jerin mutane sun qura mn ido cikin tausayi suna kallo na. Cikin dattako dad ya qaraso ya zauna kusa dani ya rungume ni, tsam nima na rungume shi hawaye na na sauka a jikin shi, yace "Wahida ina so ki sani qaddara ta riga fata, duk abnda kika ga ya faru to daman can Allah ya gama tsara shi. Ni nasan kina son Shahid ko dama, kawai dai rudin zamani ne yake dibarki da kuma son karatu da kikeyi. Zainab da kike gani yarinya ce mai hankali da sanin ya kamata, ina so ki sani zata dauke ki tamkar kanwarki ta jini, bazata taba yin kishi dake ba domin kuwa ni nasan halinta sosai saboda ni na hada aurensu da Shahid".
Zumbur na miqe tsaye cikin rashin fahimtar furucin dad, naji yana maganar Zainab bazata iya kishi dani ba, tunda niba matar Bomboy bace ba dama ya za'ayi tayi kishi dani? Ya akayi dad ya aurawa Ya Shahid mata ba tare da na sani ba?", Ban gama tunani ba naji dad yace "zauna duka zan baki ansar tambayoyinki", Ashe maganar zucin da nakeyi ta fito waje, zama nayi cikin son jin labarin na fuskanci Dad.
"Labari ne mai tsawo Wahida, tun kafin Shahid ya tafi Lagos ranar da yake shirin tafiyar, Small yake fada mn wai Shahid yana shirin tafiya kuma wai bazai dawo ba sai da mata, nayi baqin ciki sosai a lokacin da naje gidan har ya tafi, numbern wayarshi a kashe, sau uku ina neman wayarshi bai kunna ba, ganin haka yasa na rubuta mashi text kamar haka:
Assalamu Alaikum Son, Naji labarin tafiyarka a bakin Small, amma lokacin danazo gida har ka tafi, ina ta kiran numbernka kuma shiru, kuma kace bazaka dawo nan ba sai kayi aure, to ni kuma gaskiya kusan duk ban yarda da matan Lagos ba musamman na bariki, akwai wani abokina dake zaune Lagos da iyalinshi, yana da 'ya'ya duka 'yan mata, zan mashi magana sai ka zabi guda daya a ciki saboda yaranshI suna da tarbiyya, amma bazan mashi magana ba sai ka kirani dan in tabbatar da kaga text dina. BISSALAM.
Bayan kamar sati biyu naga kira da wata sabuwar number, na dauka nayi sallamh najI muryar Shahid, munyi magana sosai kuma ya amince da za6i na, yaje gidan amini na wato baban Zainab, ya za6i zainab saboda tafi duk sauran yaran hankali, ba'a dauki lokaci ba aka daura aure"Cikin damuwa na miqe tsaye saboda wani irin ZAFIN SO (A novel by Amrah) da naji na Ya shahid, ya kishin shi da nake ji. Dad yace "koma ki zauna mana, ai ban gama ba"
.
Komawa nayi na zauna jiki babu qwarieh na fuskanci Dad, yaci gaba da "tunda aka daura auren Shahid kullun sai munyi waya dashi, ganin ya kasa daurewa da rashinki yasa na yanke hukuncin a hada aurenku dana mahida, ba tare da kin sani ba, yanxu haka maganar da nake miki ke matar Shahid ce"
.
BANA KAUNAR KA 23
== == == karshe == == ==
.
Ido bud'e nace "what? Dady me kake fada ne? Yaushe na auri Bomboy?", Dad yace "ki kwantae da hankalinki zaki fahimci komai", Kai kawai na daga sannan yace "har mahaifiyar ki ta san da maganar auren, kuma kema inda kin kula a lokacin da ake maganar auren kusan komai sai an ambace ki, duk dangi sun sani ke dai ce baki sani ba, sannan kuma tunda aka daura aurenku na hanaki fita mara muhimmanci, ko a skul na hana ki hulda da maza baki daya sai dai mata, matan ma wanda na yarda dasu kawao".
Sai a lokacin na tuna da duk maganganun Dad, na tabbatar da ni matar shahid ce, tou ni yanzu murna zanyi ko baqin ciki?
.
  Na ma rasa abnda ya kamata nayi, gashi fai ina son Bomboy amma bazan iya zama da kishiya ba.A hankali Shahid ke taku har ya iso Inda nake, hanky din hannun shi ya fara goge min hawaye dashi, sosai naji kunya amma sai na samu kaina da kasa hana shi. Sai daya ga babu sauran hawaye tukuna ya daina gogewa, yace "Wahida ina so kiyi haquri ki dauki kaddara, ki cire duk wata damuwa dake ranki, duk abnda kike gani ya faru tou dama can rubutacce ne.
.
Zainab da kike gani wlh bazata taba yin kishi dake ba, ki dauke ta tamkar kanwarki ta jini, Wahida ina sonki, son da bazan taba iya yiwa wata mace ba".
Zainab tayi saurin zuwa inda nake tace "qwarai kuwa Wahida, tunda nake a rayuwa ta ban taba ganin soyayyar gaskiya irin wadda shahid yake miki ba, so da yawa yana yi mn maganarki, sai dai naita mashi adduah akan Allah ya karkato da hankalinki ki so shi, sai gashi yau ke da kanki kin furta kina son Shahid, nafi kowa jin dadin hakan. Dan Allah ki riqe ni tamkar yar uwarki ba kishiya ba". Tsam ta rungume ni tana mayar da numfashi, hawaye na na sauka a kafad'arta.
.
Babu wanda baiji dadi ba musamman Mahida da harda sajdatul-shukr tayi, mom ma har da hawayen murna tayi tana shi mana albarka.
Bayan shekara hudu.
Wasu yara muka hango su uku kusan duk girman su daya, sai dai daya tafi biyun girma. Biyun siffar su daya baka ita banbance su, sanye suke da kaya pink iri daya. Tun daga nesa mukaji suna fadin "Momy! Momy where you dey?", "I dey here my bebes, ba dai kuna nufin har kun dawo ba?", wadda tafi girman ce tace "Momy Afrah ce ta fara kuka wai Ita sai an dawo gida, shine momy Mahida tasa driver ya dawo damu". Wadda aka kira da Afrah tace "Momy fa Farhat ce tace wai tunda gobe Monday muyi saurI mu dawo yunda bamuyi Home work na Friday ba", Farhat tace "Laa Momy fa babu ruwa na, dan Allah Aunty Meenat ba Afrah ce tace mu dawo ba?". Tun daga cikin gida mukaji muryar Zainab tana fad'in "kai yaran nan akwai ku da rigima, ku dai dole sai kowa yasan kun dawo".
.
Da gudu Farhat ta rungume Zainab tace "My dear wlh babu ruwa na Afrah ce", nan suka hau rigima kowa na fadin babu ruwanta.
Zainab itace ta fara haihuwa bayan tarewar Wahida, ta haifu kyakkyawar yarinya aka saka mata Aminatu (Meenat). Bayan shekara daya kuma Wahida ta haifi twins duka mata aka saka masu Afrah da Farhat. Yanzu haka Wahida na dauke da juna biyu haihuwa ko yau ko gobe. Zaune suke cikin farin ciki da qaunar juna, idan ba an fadawa mutun ba bazaka taba gane kishiyoyi bane. THEY LIVES HAPPILY.
.
TAMMAT BI HAMDULILLAH. ANAN WANNAN LITTAFIN MAI SUNA "BANA KAUNAR KA" YAZO QARSHE. KURAKUREN DAKE CIKIN SHI MUNA ROQON ALLAH YA GAFARTA MANA.
MUNA FATAN AN FADAKARTU KUMA AN NISHADANTU A CIKIN WANNAN LABARIN.
.
SHAWARA GA 'YAN MATA:
mu daina cewa lallai mu sai mun gama karatun boko tukuna muyi aure. Aure baya hana karatu, haka kuma karatu baya hana aure. Sannan kuma mu daina tsananta tsanar namiji, saboda wannan muguwar tsanar otace take zama soyayya, wadda daha qarshe mu koma dana sani. Allah yasa mu amfana da abnda muka karanta.
.
KALAMAN GODIYA: Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsira da aminci ka qara su ga shugaban mu annabi Muhammad (SAW) tare da alayensa. Muna godiya ga duk kan masoyan mu maza da mata aduk Inda kuke, Allah ya qara dankon zumunci Ameen.
.
SADAUKARWA: na sadaukar da wannan littafi ga kannena da yan uwana da iyayena da masoyana Allah ya bar zumunci.
.
JINJINA GA: Marubucin wannan littafi Muhammad A Gana Da Amrah
.
Nikuma Abdullahi yahaya saad nake cewa sai mun hadu a wani littafin...

0 comments:

Post a Comment