Wednesday, 31 January 2018

ZUMA SAI DA WUTA Page 41-50

ZUMA SAI DA WUTA Page 41-50
.
Yafi minti goma tsaye kanta yana taunting dinta da mugayan kalamansa marasa dad'i sannan ya zura mukullin cuffs din a aljihu ya fito daga dakin, fuska daure ya dubi yan sanda uku dake gurin sannan ya gargad'esu da karsu bar kowa shiga dakin idan ba Doctor ba.

Parking Jafar yayi a haraban asibitin bacin ya gano dakyar nan gurin ambulance din ya kawo Salma, duba girman asibitin yahau yi yana tunanin ta inda zai fara bi, juyawa yayi ya hangi Mujahid tafe daga can nesa dashi, da azama ya nufesa, Mujahid na ganinsa yakara shan kara shan mur.
Ajiyar zuciya Jafar ya sauke ya tsaya gabansa cike da tashin hankali yace "thanks Goodness you're here, kasan cewa Ummi ce yarinyar daka aika mutanan ka har gida dauko ta ?"
Cikin rashin nuna damuwa Mujahid yamai kallon banxmza yace "is dat y you're freaking out ?
Kallon rashin fahimta Jafar yamai yace "kana sane kenan ?
Tsaki Mujahid yaja, baice komai ba yayi gaba abunshi, mamaki ne ya kama jafar, ba tantama Mujahid yasan Ummi ce saidai bai san dalilin dayasa yake kokarin hunting dinta down ba, koma miye zaiso sani daga bakin Ummi, duk azuci yake magana  Hanyar daya hangi yan sadan tsaye ya tabbatar nan Ummi take.
Karasawa gurin yayi suka ki bari ya shiga, haka ya hakura komawa gida saboda dare yayi.

General clinic inda aka mik'a gawar Baba nayaro nan Mujahid yanufa, police dayabar incharge din dauko gawar ya iske tare da wasu mutane zaune suna Kuka.
Yace "suwaye wannan ?
Police din yace "family din deceased dinne nayi contacting, kai suke jira tun dazu"
Kafin yayi magana daya daga masu kuka yace "dan Allah ka taimaka ka bamu Babanmu, mu mikashi gidan gaskia, bamu damu dasai an dauki mataki ga wanda ya kashe shi ba, wlh mun yafe" kuka sosai saurayin yake, daga gani ba masu hannu da shuni bane.
Tausayin su Mujahid yayi, yace yana zuwa, so yake ya amshi evidence mai karfi dazaiyi preventing Salma zuwa prison. Idan har ya karba ya boye sai randa yaga dama zai fito dashi ya ceceta.
Gurin Doctor ya shiga suka gaisa sannan yace.
"Ka gama autopsy (dissection da akeyi dan gano possible cause of sum1s death)
Doctor yace " komai anyi, zuwa gobe result will be ready.
Kwantar da Murya Mujahid yayi yace "make sure karka nunawa kowa, zan zo dakaina na karba"
Doctor bai kawo komai aranshi ba ya amsa bai da toh, fitowa mujahid yayi ya fadima mutanan cewa zasu iya tafiya da gawan, sukam kuka kawai suke.
.
Hankali tashe Daddy ya dawo Gidan, nan Mom ta labarta mai abunda ke faru, kuka sosai take babu labarin Salma, ran Daddy sosai yabaci ya kira Salim awaya, kaman wani majinyaci ya fado palon, duk ya fita hayyanci tsabar gulity conscious dake damu shi.
Cikin tsawa Daddy yace
" dan uwarka ina ka kaimin Salma?
Tsuru Salim yayi ji yake kaman asirin shi zai tono, yace "wlh Daddy nima neman ta nake.
"Karya kake, duk wani rashin jin Salma tare kuke yi ka dauka ban sani ba, dan haka gayamin gaskia awana dalilin ake tuhumarta da kisan mutum ?
Shuru Salim yayi baice koma ba, Daddy ya cigaba "asararrar banza tashi ka bani waje, kuma ka binciko min duk inda Salma take".
Jiki ba kwari ya mike ya fice.
Mom tace "wayarta na ringing baa dauka"
Bara na gwada atawa, Daddy ya fada hade da dailling no dinta.

Jafar na Isa gidan yayi parking, fitowa zaiyi yaji ringing din waya, dubawa yayi ya hango Pink Jakar Salma, dauka yayi ya bude yaci karo da frame mai dauke da Hoton Mujahid, kallon hoton yayi cike da mamaki, nanya tabbatar sunsa Juna, "toh make faruwa ? Ya tambayi kansa, wayarsa ya duba yaga miss call Mom hamsin saina Dad guda biyar, ajiye jakar yayi cikin motar sannan ya karasa gidan rike da wayan, dakin Hajiya ya shiga ya iske ta zaune tayi tagumi, fada mata yayi yadda sukayi da Mujahid hade da nuna mata wayan ummi da iyayanta kerlta kira, ranta sosai  ya kara baci da kuma tsoro daya kamata da ganin Dad naciga da kiran Salma. Kallon namban jafar yayi kaman yaso yagane nambar, wayarsa ya danna yayi compare din nambar Dad dake kira, gabansa ne ya fadi, ya kalli Hajiya yace nasan Gidan da Ummi take, tace ai zuwa zamuyi bamuga ta zama ba, tashi tayi da sauri ta zuri hijab sukai waje.

Hankali tashe Daddy ya kira no din abokinsa head of police gabadaya, sun jima suna magana daga karshe ya yanke gobe zaiso office suyi magana.
Baa fi mintin uku ba maigadi ya kwankwaso wai sunyi baki, izini yamai dasu shigo, Su Hajiya na shiga Daddy yaga Jafar, Hajiya kam kallon Mom take wanda tasha kuka harta gaji.
Zama sukayi aka gaisa, Daddy yace "jaafar yanxu nake shirin kiran ka awaya"
Ajiya zuciya ya sauke ya mikawa Daddy wayan Salma, karba yayi, ya labarta masu haduwa su da Salma da kuma yanxu asibitin da take. Salati Mom tahau yi hade da fashewa da sabon kuka, Hajiya kam binta kawai tayi da ido, Daddy yace "amma officer in charge of this case sai yaci uwarsa, saiya fadamin yaushe yaga yata ta kashe wani dahar zaiyi babak'eran aresting one n  only daughter na"
Katse shi Mom tayi da cewa, "Alhaji tashi zakayi muje mu dibo yarta."..
Jaafar yace "baa bari, saidai gobe.."
Sai sannan Mom ta dubi Hajiya dakyau sun danyi yanayi da Salma, sharewa tayi tace "mungode sosai da temakon yarmu da kukayi, Allah ya saka da alheri"
Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tace "nice da gode maku, Allah kadai yasan dami xai saka maku"
Kallon rashin fahimta Mom tayi mata, hajiya taci gaba "basan ya akayi Salma ta dawo hannunku ba, saidai kun cancanci riketa yadda naga duk kun damu" k'walla hajiya ta share tacigaba "ni yayar mahaifiya salma ce, na jima ina neman ta banganta ba"
Ware ido Mom tayi, shikam Dad baiyi mamaki ba, koda ya hadu da Salma daman neman yan'uwanta taxoyi a garin Abuja, ganinta karama lokacin yasanya ya kawo ta gida yarike ta tamkar yar cikinsa, saidai yaji dadi ganin Jaafar amatsayin d'an Hajiya, hada aura salam da Jafar yazo asauki kenan.
Kuka Mom take sosai tana rokan Hajiya karta rabata da Salma, Hajiyan ma kuka take tace "karki damu Salma takuce halak malak bazan rabaku da ita ba"
Dddy yace "ikon Allah kenan, jaafar Allah yayi bazaku hadu da Salma ba tun shekarun baya dana ma zancen auran diyata, ashe kai dan'uwan ta nema, faduwa yazo daidai da zama".
Sosa keya jaafar yayi hade dayin murnushi..
Hajiya kam jikinta ne yayi sanyi jin Daddy zai ruguza mata plans, saidai ba yadda ta iya tunda shiya rike Salma, bata isa tace Mujahid ta kamawa Salma ba, balle yadda taga Daddy yadau zafi da officer dake kokarin aika salma gidan yari....
   Sun dan jima suna magana, daga bisani su Hajiya suka bar gidan bayan sunyi zasu hadu gobe a asibiti.

****
Washe gari bayan Mujahid yayi Sallar asubah asibitin ya nufa gurin Salma danso yake ta farka agaban idonsa.
   Salma kam Baccinta take, wata nurse ta shigo dakin tacire roban jini sannan ta sa mata na ruwa, fita nurse din tayi, baiyi awa daya ba Salma ta fara motsi, ahankali ta bude, ganinta cikin farin daki yasata mikewa azabure, wani kara tasaki jin ta karce hannuta, duban gurin tayi taga haunta da karfen gadon makale da handcuff, kokarin cixgewa tayi ta kasa, "na shigu uku" ta fada bayan ta tuna abunda ya faru"
kuka ta soma yi, jin motsin xaa shigo yasata tsayar da kukan hade da kafawa kofar ido.
Mujahid ne ya shigo, jikinsa sanye da dagon jallabiya, tana ganinshi ta hade hade rai, tuna neman kasheta da yasoyi tayi.
Murmushi yayi mai dauke da ma'ana iri iri sanna ya karasa daf da ita ya tsaya, murya ciki ciki yace "ya jikin ki ?
Banxa tayi dashi
Yace "hope you're ready to spend  30 years a gidan yari"
Dogon Tsaki taja, tace"am ready, then after 30 years kuma i'll come back to destroy you for good".
Dariyan rainin hankali yayi yace "kina da guts dayawa" gashin kanta ya damko, saida tayi kara, daure fuska yayi yace "dan uwarki ni kike yiwa tsaki.."
Dukda ciwon da jikinta yake mai hanata kokarin cizge hannusa daka kanta ba, kaman mai shirin yi kuka tace "idan banyi tsaki ba mai kakeso nayi, apologise or beg your pardon kake so nayi, toh kasani, that will never happen, badai so kake ka kaini prison ba, bismillah, kuma point of correction uwarka badai uwata ba..."
Iya k'ulewa Mujahid ya kai, wuyanta ya damko da karfin gaske, yace " uwata kike zagi.."
Tace "uwa batafi uwa ba, idan kana nonsense dinka dont ever include my Mom."
Sakinta yayi yana Huci, juyawa yayi zai fita tace "am hungry, get me sumtin to eat".
Bai iya tanka taba ya fice zuciyarsa na zafi, baiso reaction din Salma haka ba, yaso ace kuka zatayi ta rokoshi amma dan karfin hali irin nata ba ita tayi kisan ba but she is willing to serve 30 year a prison... Tsaki yaja yana tunanin yadda zaisa a azabtar da ita a prison. Motar sa ya shiga ya koma gida dan shiryawa zuwa office.
.
Sai da gari yayi haske Mom da Daddy suka shirya fita asibiti gurin Salma, har sun shiga mota yan'uwan Baba nayaro suka kira Daddy suka fadimai rasuwar, hankalinsa sosai ya tashi  fasa zuwa asibitin yayi ya nufi Gidan taaziya, Mom kam asibiti ta wuto nan ta iske Hajiya da Jafar na jiranta a haraban gurin, shiga sukayi wards din, sukayi saan police daya ke gurin wanda ya iso da safe baisan da order din Mujahid ba yabar Jaafar ya shiga, Mom da Hajiya sun tsaya suna magana awaje.

Bacci Salma take ya karasa ya zauna kusa da ita, kallonta yake cike da so da kauna, shafan pretty face dinta yayi har zuwa kan lips dinta yana admiring dinta, dan motsawa tayi yayi sauri cire hannusa, bude ido tayi ahankalin ta dubesa, atunaninta Mujahid ne, tace "ina abinci ? Can kasan makoshinta tayi maganar.
Murmushi yayi yace "yanxu xaa kawo, how are you feeling ?
Sai sannan tagane ba Mujahid bane, yunkurowa zaune tayi kokarin yi, yayi sauri temaka mata.
Kallan shi tayi ayayinda shima kallon ta yake, murya kasa kasa tace "thank you"
"For what" ya fada hade da rike hannuta mai sakale da handcuff, haushi ne sosai yakama shi yasan aikin Mujahid ne.
Murmushi tayi, jikin sanyi voice tace "kaman nasanka wani wuri kafin ranar da kayi saving dina?
Dariya yayi wanda ya kara fiddo kyau shi,
aranta tace "so cute dashi, ba kaman banzan nan ba kullum fuska daure"
Magana zaiyi Mom ta shigo dakin, Hajiya abayanta, da sauri Mom ta karasa gurin Jafar ya mike tsaye ya matsa gefe, kuka Salma ta fashe dashi ganin Mom, nan take ta susuce tahau rarrashi, dakyar Salma tayi shuru tace "Mom yunwa nakeji, kuma acire min wannan abun" turo baki tayi tanai mata nuni da cuffs din hannuta.
"Mun shige su" Mom ta fada cike da mamaki, kallon Hajiya tayi tace "amma babu azzalimi kaman Officer nan, ji mugunta dan Allah.."
Sai sannan Salma ta lura da Hajiya dake kallon su jiki sanyaye, shuru Hajiya tayi sanin cewa d'anta ne azzalimun da Mom ta ambata.
Maida dubanta Salma tayi ga Mom, murya kasa kasa tace "Mom matar nan kaman Hajiyar Ummata"
"Itace, tare da d'anta daya taimake ki" nuna jaafar Mom tayi,
Farin ciki ne ya mamaye Salma, duk sai taji Jafar ya kara kwanta mata,  ashe dai jinin tane shiyasa ya ceceta.
"Hajiya.." Salma ta fada tana kallon Hajiya, murmushi hajiya tayi ta mike ta karasa gareta tana fadin "aina dauka bazaki gane niba" rugume juna sukayi, Salma na kukan farin ciki.
.
Daddy na zuwa gidan Baba nayaro taaziya yayi masu, bai samu janaizar saba, abun tausayi dayaji sanadin Mutuwarsa, tashin hankali biyu ne suka hade mai, jiki babu kwari ya wuce NPF (HQ) gurin head of police, sir Ahmad.
Kara tattauna abunda ke faruwa sukayi, Sir Ahmad yace tabbas yasan da case din saidai baisan diyar shice major suspect ba, atake ya tura department dinsu Mujahid kiran sa, baa same shiba ya aika a kira mai Mubarak sanin cewa su biyu ne witness aranar da abun yafaru.
Mubarak na zuwa, Sir Ahmad yahau shi da tambayo yi, bai boye komai ba ya zayyane masu labarin salma da mujahid tun farkon haduwar su har zuwa ranar da abunda ya faru, ya kuma jajjada wa sir Ahmad lailai Mujahid baya cikin hankalin sa, So da kiyyaya sun rufe mai ido.
  Zufa Daddy yahau yi, gano cewa duk case dun revovle around Baba nayaro, "amma yaron nan ya cika dan iska, yan'uwan marigayi basu pressing charges ba saikai dan kawai wata manufarka daban zaka tsangwama d'iyata" azuci Daddy yayi maganan.
Sir Ahmad yace "zaancen banza kenan, wato personal feeling dinsa yake hadawa da aikinsa dan cimma burinsa, dan bashi da kunya kuma harda aika gawa asibiti ayi autopsy alhalin yasa ko kyankyaso yarinya bata iya kashewa"
"Kaga Mubarak, nemi wani ya amso mana autopsy din mugani"
Ba musu Mubarak ya mike ya fice, police din daya kai gawar asibiti ya tura ya amso, Doctor kam zuciya daya yabada atunaninsa Mujahid ne ya aiko.

Mujahid na Tuki ya dunga ganin call daga office, asibiti zaije amsan autopsy ya fasa ya wuce Office, yana isa aka sanar mai Sir Ahmad na kiran shi, hankali kwance ya shiga office din, wani mugun Harara Daddy yakai mai, shan jinin jikinsa yayi ya dake ya karasa gurin Sir Ahmad.
Sir Ahmad yace "yanxu M. Abdulsalam ka kyauta da abunda kayi, kaida kake daya daga cikin wanda suka san aikinsu, miyasa kakeso yin injustice ?
Kallon bangane ba Mujahid yamai, police ne ya shigo da autopsy result ya mikawa Sir Ahmad, Mujahid kaman yayi ihu.
Budewa Sir Ahmad yayi ya karanta sanna ya dubesa yace "the deceased was beating with severe blows before stab to death, yanxu gayamin ita buduwarta ka da kakejin haushi itace tamai dukan kafin ta kashe shi ko kuwa she is stupid dazata kashe shi kuma ta tsaya yimai kuka ba tare data gudu ba"
Shuru Mujahid yayi yana kallom Mubarak da wutsiyan ido, sarai yasan shiya tona komai..
Sir Ahmad yace "ka godewa Allah Mahaifin yarinya baiyi pressing charges akan attempting kashe diyar sa dakayi ba, daga yanxu nayi closing case dinnan, kai kuna you're suspended till further notice".
Mugun Kallon Mujahid yakaiwa Sir Ahmad, afusace ya ciro bage, Id da bingidar ya zubarsu kan table dinsa, hade da ficewa afusace yanai huci, mikewa Mubarak yayi yabi bayansa..
Daddy yace "hukuncin yayi tsauri da yawa.
Sir Ahmad yace "Barni dashi, so nake yagano bambancin sentimental feelings dinsa da aikinsa".

Mubarak na kwalla mai kira ko kallan sa baiyi ba,
Ya shige motarsa yaja afusace, gurin abinci ya nufa ya siya take away sannan yaja zuwa asibiti gurin Salma.. 
   Tundaga nesa ya hangi babu police gurin, haushi ne yakamasa, yana shiga dakin mutanan daya gani yasa shi daskarewa gurin, Hajiya da Mom zaune gefe suna hira, Jafar zaune kusa da Salma yana bata tea abakin tana zuba mai shagwaban ta koshi, sai wani lallabata yake.
   "Kai kuma fah, daga ina ? Mom tafada fuska ba annuri ganinsa sanyen da kayan yan sanda.
Afusace Hajiya ta mike ta kwashe shi da marin da saidai Salma ta saki ihu tsabar razana. 
Bai damu da marin ba banda jafar dayake watsawa mugun kallo.
  "Dan ubanka bani mukullin Handcuffs din.." Hajiya ta fada cikin karaji.
Karamin mukullin ya mikata ta amsa ta jefawa jafar ya cabe yayi sauri bude handcuffs din, mikewa yayi yabawa hajiya, "ungo tsiyar ka, kuma ka fice anan" hajiya ta fadi hade dajan haunnsa ta dunkule mai Handcuffs din ciki, Mujahid baice komai ba yayi kokarin ajiye abincin, tsawa Hajiya tamai tace ya wuce da abinci baa bukata, zuciyarsa na tafasa ya juya ya fice.

Mom tace "dan banxan yaro, waishi police, kinyi maganin shege"
Mugun Kallo Salma takai mata ba tare data lura ba, aranta adduaa take Allah yasa Mujahid ba d'an Hajiya bane, idan kuwa hakan ya tabbata she won't forgive him da boyemata shi dan uwan tane da yayi.

Mujahid na Fitowa ya Hadu da Daddy zai wuce ciki, kawar dakai yayi gefe ya wuce ranshi na kuna.
  Dariya Daddy yayi yace "kaji da rashin aikin ka, Salma kuwa tama nisa".




Daddy na shiga d'akin yayi farin cikin ganin Salma ta warware, nan ya basu albishiri din yadda komai ta kasance. Mom kam tafi farin cikin rashin aikin mujahid sai d'ura mai zagin Allah tsine take. Hajiya kuwa murmushin dole kawai take, tana mamakin karfin hali irin na Mom, kodayake Salma diyar tace duk abunda tace daidai ne. Salma kam tagama gano komai da Reaction din Hajiya sai fama yiwa Mom ido take akan tayi shuru bata sanma tana yiba. Aunty Bilki ma tazo dubata, sun dade asibiti kafin daga bisa suka koma gida.

Kwana su Salma biyu a asibiti Likita ya sallame su. Gidan Mom suka wuce wanda ba hakan Hajiya taso ba. Bayan kwana biyu kuwa Daddy dakan sa yacema Salma ta shirya Jafar ya kaita gurin Hajiya tayi mata kwana biu, dadi sosai taji dama ta jima dason tambayarsa zataje sai Allah yasa ya furta mata hakan.
Ranar da zasu Jafar na waje parking lot yana jiranta, ita kuma tana tare da Mom a palo suna Sallama, mik'e mata wayarta Mom tayi tace
"Saura idan kinje ki manta dani"
"Haba Mom taya zamanta dake, kece fah uwa ta" ashagwabe tayi magana.
Kunnan ta Mom tajA, cikin zolaya tace "banda rashin ji, kinga Allah ya kawo maki mijin mai kirki karna kuskura naji kinma Jafar rashin Mutuncin, nasan halin ki"
Dan k'ara Salma tayi hade da cizge ruk'on da Mom tayi mata, dariya tayi sannan tace "kai Mom ina laifin wanda ya taimake ka cikin tsaka mai wuya"
Dariya sukayi atare sannan sukayi sallama, har bakin Motar Mom tarakata tanai kara mata fada, motar zata shiga ta hangi Salim bakin window dakinsa yana kallonta, dauke kai tayi tana mamaki yadda yake acting crazy kwana biyun nan. Saida Mom taga sunja sannan ta koma ciki.

Shuru sukayi kowa da abunda yake sak'awa aransa, satan kallon ta Jaafar yayi yaga tana juya wayar dake hannunta, da alamun kuma tunanin take ganin  bata cikin hayyacin ta. Cikin cool voice yace "tunanin mi kenan, ko har yanzu jikin ne ?
Sai sannan ta dawo daga duniyar tunanin inda jakar ta da hoton Mujahid suke, tasan dai tare suke da wayarta cikin jakar amma Wayar kadai Mom ta bata ba jakar.
Murmushin ta saki hade da dubansa, tace "everytime i close my eye kai nake gani, kana da kirki sosai"
"Uhmm are you sure, ba wani can daban kike gani ba.." Cikin zolaya ya karashe zancen.
Dariya tayi bata ce komai ba, banda murmusawa da take.

Gabadaya duniyar tama Mujahid zafi, ba aikin fari balle na baki duk zaman kadai ce ya ishe ba, tun ranar dama bai kuma bi takan Salma ba, mugun haushi da tsanarta yake ji duk asanadin ta ya rasa komai, one thing dayafi damunsa shine yadda ya kasa yakaceta aransa, wani mugun Tsaki yaja hade da kaiwa hannusa daya haushi, gidan dayake zaune ma bakin kirin yake ganin sa tsbar takaici, mikewa tsaye yayi daga kan kujerar palon da yake zaune, kai komo yahau yi yanai nemawa kansa mafita, karshe dai ya yankewa kansa komawa Gida tunda dama ba koransa akayi ba shiya kori kasan, duban agogo yayi yaga biyar na yamma ta gota fasa tafiya yayi ya bari zuwa gobe.

Suna isowa Gidan, Salma ta jinjina kyan da girman gidan, fitowa tayi daga motan tanai karewa ko ina kallon, kallon Jafar tayi, tsaye yake bakin boot yana ciro trolleys dinta.
Tace "wow yaya this house is beautiful.."
Magana zaiyi sukaga an bude gate motar kirar avensis ta shigo, dauke kai Jafar yayi, salma kam kallon motar take har tayi parking idan suke tsaye, Junaina ce ta fito amotan hade dakaiwa Salma wani mugun kallo aranta tana fadin "i cnt believe this devil is my sister" wani mugun tsanan Salam takaraji tun ranar da Hajiya ta fadi mata ita kanwar tace, dan haushi ma ko asibiti kasa zuwa dubo ta tayi.
"Ya jafs ina wuni" tafada batare data kalle saba, tayi wucewarta

Bai amsa ba, sai kallon Salma dayayi yaga duk jikinta yayi sanyi, murya maraice tace "i dont think she will forgive me..
Yace "she is very angry but trust me she will hose down"
"I pray so" Salma ta fada hade da sauke ajiyar heart, ciki suka karasa, Hajiya na zaune palo tana kallon aljazeera, ladabce Salma ta gaidata, farin ciki mara misaltuwa ne lullube Hajiya,  kasa zaune tayi ta mike tahau nannan da Salma, babban dakin mai kyau anan kasa Hajiya ta nuna mata amatsayin nata, Salma kam kin zama tayi ta nace lailai ita a dakin Hajiya zata sauka, hajiya kam taji dadi hakan, ranar kam Salma taga gata gurin Hajiya da Jaafar, sai wani narke masu take suna biyeta, Junaina kam sai binta da harara da tsaki take, zama tayi dakin tahau trying namban Mujahid dan kai masa rahota, taji wayarsa kashe.

****

Washe gari Mujahid yayi shirin sa tsaf cikin kananun kaya dayayi matukar fiddo azahirin kansa, kulle gidan yayi ya fada motarsa yaja yabar Gidan.
   
Bayan sun kare breakfast, wajen gidan Salma da Jaafar suka fito yanai nuna mata ko ina da garden dun gidan. Kaman masoyan juna gwanin shaawa suke tafe suna darawa abunsu ba tare da matsala tattare dasu ba, zayawo sukayi suka tsaya bakin motar sa, da alamun fita zaiyi.
Marairace murya tayi tace "yaya yaushe zaka dawo ?
Folding hands dinsa yayi a kirji hade dakai mata wani killer smile, yace "tun baje gate ba harkin fara missing dina"
Dariya tayi, sai kuma ta tsayar da dariyan tace
"Yaya you're very special,
Shuru sukayi suna duban juna for some seconds sannan tace "plz karka dade.."
Agogon hanusa ya kalla yace "i promise..
Okay bye" ta fada..
Kashe mata ido yayi, sukai smiling atare sannan ya shiga motar yaja.

Palo ta komo hade da sauke dogon ajiyar zuciya, sai sannan ta tsaya karewa ko ina na palon kallo kasancewar babu kowa..
   Palon ya hadu, idanuwan ta suka sauka kan Katunan frames mai step guda biyar manne jikin bangon palan, wata farar kyakyawan Tsoyuwar mai glass ce a babban frame din, "ko wace ce wannan" ta fada.
Mai bi masa ta kalla Hajiya da late Abban su Jaafar wanda sanye yake da kayan Sojoji, sai saura kuma hoton jaafar, junaina da Mujahid, sun mata kyau sosai, kallon na Mujahid tayi ta buga uban tsaki aranta tace "to hell with you".
   Afusace ta juya zata bar gurin tagan shi Tsaye bakin kofar shigowa, kusan minti daya yayi tsaye ganin ta tsaye gaban Hotonsa, baisan wace ce ba, yadai tsaya jiran ta juyo.
   Harga Allah ta tsorata da ganinsa, ihu yarage batayi ba ta maze ta tsayaa mayar mai da mugun kallon dayake wurgo mata.
   Magana zai yi Hajiya ta fito daga daki tanai kiran Ummi, "naam Hajiya" Salma ta amsa aladabce, ganin Mujahid yasata daure fuska tace "kai kuma daga ina ?
Sosa keya yayi ya gaidata, tabe baki tayi
Da sauri Salma ta risina tace "yaya ina wuni, sannu da zuwa" fuskar ta daure da fara'a..
Kallon mamaki yabita dashi..
Hajiya tace "bada kai take ba, mugun banxa, Allah yasa dai zuciyarta a tsarkake take shiyasa bata nufeka da shairi ba upon all abun  dakai mata, idan baka sani ba toh yar'uwarka ce"
Ware ido yayi in shock.
Hajiya tacigaba "iskancin banxa au dama baka sani ba ?
"Bansanta ba, yama sunanta ? In serious tone yayi maganar
Kallon Banxa Hajiya tamai sannan ta kalli Salma tace "kiyi hakuri da abunda ya maki, Mujahid sunan sa, daga shi sai jaafar a haife.."
Shuru Salma tayi, ta mugun kuluwa da denying dinta da yayi, sai yanxu ta kara tabbata wa dagangan yaki nuna cewa yasanta tun farkon haduwan su..
Dakyar tace "ba komai hajiya ya wuce" wuce wa tayi daki, hajiya tabita abaya..
Tsaye Mujahid yayi gun hade da daura hannu akai, "yaushe tazo gidan nan ? Ya tambayi kansa..
   Tifowa Salma tayi rike da Plate a hannu, ko kallan shi batayi ba ta wuce ta gabansa, fizgo hannuta yayi da karfi, ihu tasoyi yayi sauri rufe mata baki da hannusa yaja ta suka shiga kitchen, can karshe bango ya turata hade da matse ta da jikinsa har suna juwo numfashin Juna, tsuro tayi da ido, fuska ba annuri yace "What are you doing here, evil tramp from hell..
Alamun tamai da bakinta is close, cire hannu yayi daga bakinta, harara takai mai tace "the evil tramp is you, you kept me away from knowing my family and the worst part of the story you try putting me behind bars, why, do you hate me that much ?"
Cikin rashin damuwa da abunda tace yace "datx your story not mine, i need to know uban miya kawo ki gidan nan ? Cikin zare ido yayi maganar.
Dariyar takaici tayi tace "the only reason y am here, its because of your brother, he is such an Angel, so sweet, i cnt wait to be in his arms..".
Murde hannuta yayi, yanai mata mugun kallo da idanuwa sa da suka sauya launi zuwa ja, ko ajikinta saima kokarin gyara gashin kanta daya bazu gefe, hannu ya nunata dashi, "badai karuwan ci ya kawoki cikin gidan nanba, we shall cee about that.."
Tsaki taja ta kalli hannuta dayake rike dashi tace "M.u ka saki hannu karuwa mana, ko ka fara shiga tarko ne.." Cikin salon rainin wayo tayi maganar.
  Haushi biyu ne ya kamashi, "wai M.u, amma yarinyar nan ta raina ni, kodan Yaya bamu" aransa yayi magana.
Rai bace yayi wurgi da Hannuta sannan ya juwa zai fita sukayi kicibis da Junaina zata shigo, "yaya yaushe ka dawo" ta fada da murnan ta, ko kallanta baiyi ba yayi gaba abunsa.
Tabe baki tayi, ganin Salma Mak'ale gurin kaman mai shirin kuka, karasawa gurinta tayi tanai kai mata kallon banxa sann tace "bawai kinzo gidan nan ba, better stay away from my boyfriend, Mujahid nawane nikadai, kodayake y am i wasting tym talking to you, very soon zaiyi kicking dinki out of this house cox he hate you so much Big sister" tsaki taja ta juya ta bude fridge tadau drink sannan ta fita tabar Salma daskare tanai kallon ta.
"Oh ma God, little sis you're too good ki falling wa M. U, na shiga uku" ta fada hade da zamewa kasa ta zauna.
Kanta ta daura kan kafafunta tahau yin kuka dani bansan dalili ba.

Ido jajir ta mike ta k'arasa bakin sink ta wanke fuskarta sannan ta fita zuwa palo, Junaina ta iske zaune tana kallon cartoon, kallon banza suka aikama juna sannan ta wuce dakin Hajiya. Kallon daya Hajiya tayi mata tagano kuka tayi batace mata komai ta mike ta fita a dakin. Jiki ba kwari ta fada gado ta kwanta, lumshe ido tayi hade da girgiza kanta tana fadin kanwata da Mujahid, no no it wont happen gaskia, mutumin nan mugune, i wont allow him hurt my little sis" maganganu tahau yi tamkar tababbiya daga bisani kuma shuru tayi tanai neman mafita.

Karfe takwas na dare Jafar ya dawo gidan, baiyi mamakin ganin Mujahid ba, ko takansa biya ba ya karasa kitchen inda yajiyo muryar Hajiya tanai bawa masu aikin ordern su tsaftace ko ina.
"Sweetheart da kanki, yau kece a kitchen" ya fada yanai karasa shiga kitchen din.
Dariya tayi ta rufe kofar fridge datake rike dashi tana duban yadda yake kyalli, "Son kansan dole saida sa ido, maid dinnan sumtymz basu sanin aikin su"
Sosa keya yayi yace "naga Mujahid ya dawo, why ?
Tabe baki tayi,
"Wayasan mai, ni tunda yaxo baice min komai ba"
Nisawa Jafar yayi.
"Ummi fah, tana ina ?
Kwatar da Murya Hajiya tayi, tace "tana daki, i dunno watx wrong with her amma dagani she is depressed"
"bari naje naganta" ya fada da azama hade da juyawa.

Zaune take bisa praying mat tayi tagumi bayan ta idar da sallar ishaai. Shigowa yayi hade da Sallama, amsawa tayi tare da saurin gyara zama tanai sakar mai murmushi, kusa da ita ya zauna yanai kare mata kallo, yace "meke damunki ?
"Maika gani, ba abunda ke damuna..
Hannuta ya riko, tadan razana, ya lura da hakan ya share yace "you're lieing, nasan akwai abunda ke damunki i can feel it"
Kallon shi tayi ido cike da tear, ahankali ta zame hannuta daka nasa, cikin sanyi murya tace "you're a good man, i dont tink you will be happy with me"
"Miyasa kikace haka, Don't you love me ?
Kuka ta fashe dashi hade da kawar da fuska tana shesheka, hannu yakai bisa fuskar ya juyo da ita sunai fuskan ta juna, murumshi ya sakar mata yace "bana son kuka tashi muje muyi Dinner"
Atare suka mike, ya goge mata hawaye yace ta shiga toilet ta wanke fuska, ba musu taje ta wanko ta fito, cikin zolaya yace "to miye kuma na b'ata rai, sai kinmin murmushi zamu fita".
Dariya tayi bata ce komai ba suka fita tare zuwa palo.

Dining area suka nufa, Mujahid na zaune shida Junaina tanai mai magana kasa kasa, shikuma yayi kicin kicin da Fuska, ganin Salma da Jafar yaka daure fuska. Hajiya kuwa tana palo zaune, bata fiya cin abincin dare ba.

Zama Salma tayi ba tare data kalle saba, gefenta Jafar ya zauna.
Hararar iska Junaina tayi sannan tace ya jafs kaifah muke jira tun dazu"
Dariya yayi
"Ai gani nazo you can served us.."
Cikin zumudi dajin dadi yay mata dariya unlike kwanaki dayake daure mata fuska, hannu takai kan serving spoon zata dauka Salma ta rigata dauka, tsaki taja ta janye hannuta. Murmushi Salma tayi ta bude warmers din, ganish macroni ne da pepper chiken, plate din gaban Jafar ta zuba abinci sannan ta ijiye serving spoon din.
Kallon ta Jaafar yayi yace "bazaki zubawa kanki ba"
Spoon tadauka tace "habibty tare zan ci dakai" ashagwabe tayi maganar.
Mugun kallo Mujahid yakai mata, so yake su hada ido amma taki kallon shi, saima faran cin  abincin sukayi tana zuba mai yauki da yanga.
Junaina kuwa tafi shi k'ulewa yadda Salma ta nuna halin kota kula da serving dinsu, kallon Mujahid tayi, tanaso tasama masu abinci tare tana tsoron ya dizga ta, mazewa tayi ta zuba mai da niyyan suci tare taga ya mike yadau plate din abinci ya koma kujerar dake fuskantar Salma ya zauna..
Kuka ne kadai ya rage Junaina batayi ba, akule ta dibi nata abinci tanai kaiwa su Salma Harara.

Ajiye Spoon din Salma tayi, murya kasa kasa tace
"Yaya feed me Hannu na ciwo"
Murmushi Jafar yayi, ya fara feeding dinta, fork ya dauka ya yanki kazar xai bata abaki, da sauri ta girgiza kai tare da turo mouth "no yaya hakorina ke ciwo, bazan iya ci ba ka faraci abakin ka idan yayi laushi saika ban"
Dariya sosai tabashi, ya   dake yasa naman abakinsa yafara ci, sai kallon shi take tana lumshe ido.

Dogon Tsaki Junaina  taja jin abunda Salma tace, aranta tace "so disgusting"mikewa tayi hade da daukan abincinta ta koma palo.

Duk yadda Mujahid yaso su hada ido da Salma ki tayi, iya kuluwa yakai da rainin hankali da suke agabansa, saidai bazai bari ta amshin Kazar bakin k'anin saba. kafarsa yakai daidai kan nata hade da murjesu da karfin gaske.
Dan karamin kara ta tsaki takai dubanta kan Mujahid,
"habibty miya faru ? Jafar ya fada, duk ta kidime zabar yadda Mujahid ke cigaba da take mata kafa.
Cikin inda inda tace "yaya hakorina xai cire.."
"This is serious" jafar ya fada hade da mikewa yace bari nakawo maki warm water" da sauri yabi hanyar kitchen.

Matso da Fuskan sa Mujahid yayi kusa da fuskanta, sannan ya kalli palo dan tabbar da babu wanda ke ganin su, Duban ta yayi fuskar daure, yace "what do you think you're doing ?" Ahankali yayi maganar.
Harara takai mai, ta matso da fuskan ta tsatin kunnansa tace "Datx non of your bizness, kuma kabar taka min kafa"
"You're trying to seduce hime right  ?
Bitting lower lips dinta tayi tare da kashe mai daradara eyes dinta yace "kwarai kuwa, are you jealous ?
Dariya yayi yakai mata cixo a kumatu sannan yace
"Dont even tink about it"
kallon banxa tamai, ta shafa inda ya cixa tace "dan iska kawai" mikewa tayi afusace zata koma palo yasa mata kafa tafadi tim akasa.
"Subhanallahi" Hajiya da Jafar suka fada tare, fitowan shi daga kitchen yaga duk abunda ya faru, sharewa yayi ya karasa gurinta, "sorry Habibty" ya fada yanai kokarin taimaka mata,
Mikewa tayi batare data bari ya tab'a taba, yaken dole tayi tace "yaya ba komai fah, faduwa kawai nayi"
Sannu yahau cemata suka zauna a kujera 3 sitter, Hajiya ma sannu tai mata, junai kuwa sai dariya take kyalkyalewa.. Oga Mujahid baima san suna yiba, banda abincisa da yakeci ko ajikinsa.

Warm water din Jafar yabata, kin sha tayi tace hakorin yadaina ciwo, shuru tayi bata kuma cewa uffan fa tsananin yadda Mujahid ya bata mata rai, tunanin yadda zata rama kawai take. Duk yadda Jafar yaso suyi hira kin kulashi tayi daga bisani ta koma
daki ta kwanta........

.
Barin palon sukayi yarage Hajiya da Mujahid. Mik'ewa yayi kamar marar gaskia zai haura sama tace "koma ka zauna" fuska ba wahala ta fad'i hakan.
Komawa yayi ya zauna ba tare dayace uffan ba.
Hajiya tace "miya dawo dakai gidan nan ?
Nisawa yayi.
"Ba komai, kawai naga banda aikin yi ne"
Mugun kallo ta aika mai.
"Mujahid ka fita ido na, ka dauna banga sanda kasa mata kafa ta fadi ba, kuma nasan sarai saboda ita ka dawo gidan nan".
Sose k'eya yayi, murya kasa kasa yace "nifa ba ruwana da ita bamma san da zaman taba, infact ko ak'afa aka d'auramim ita bazan jaba"
K'wafa Hajiya tayi, ta shak'e abunda yace ba kad'an ba.
"Tashi ka bani guri kafin na kwashe ka da mari"
Dariya yayi ahankali ya mike hade da mata asubah ta gari ya haura Sama.
Washe gari yakama weekend, kowa sai sanda yaga dama yake tashi bacci, around 10 Salma ta tashi tayi wanka ta shirya cikin dogowar riga atamfa, fitowa tayi daka d'akin ahankali gudun karta tashi Hajiya, kitchen ta shiga had'a tea ta hango shi ta window yana playing basket ball, Murmushi tayi tace "perfect timing, yanzu miya kamata nayi mai" tunani tahau yi, can dabara ta fado mata, fridge ta bude ta dibi atarugu da yawa tasa a bowl ta jika da ruwa zafi Sannan ta sane ruwan a bowl, daukan ruwan tayi ta haurawa Sama da sauri. Dakuna Hudu tagani mai dauke da parlour, shiga na farko tayi babu alumun da wani ciki, tana leka na biyu ta hangi Jafar zaune gaban laptop yana dannawa, saurin komawa baya tayi, next dakin data shiga ya tabbar mata da dakinsane, daddadan kamshi da sanyi ke tashi ta ko wana lungu da sakon d'akin.
Dariya tayi ta shige Toilet  tadau shower gel dinsa ta bude ta zuba ruwan taragun sannan tafito da sauri tafara saukowa, kafin ta ida sauka Junaina ta fito daki  wucewa kitchen, hada ido sukayi Junaina tayi saurin dauke kai bayan ta maka mata uwar harara. Salma kam bata damu ba, palo ta zauna hade da kunna Tv.

Kusan rabin awa Mujahid yayi yana playing b-b kanan ya koma cikin gidan, jikin sa sharkaf da zufa, so yake kadai yayi freshen up dan samun dadi jikinsa, Salma naji shigowarsa ta maida dubanta garesa, dogon tsaki taja ta hararesa hade da dauke kanta, bai ce mata uffan ba ya haye sama, aranshi yana fadin "bari nayi wanka na sauko zakici ubanki ne"
Toilet ya fad'a ya sakarwa kanshi ruwan shower mai dumi, shower gel din yadau ya matso hade da shafawa a fuska daidai kan idanunwa sa, runtse ido yayi sakamakan azaban daya ziyar ci idon, "wanna yajin daga ina kuma" yafa d'a aranshi, kara tasar gel din yayi yakuma shafawa dan wanke idon da kyau, raradi ya kuma ji yayi azama kashe warm water aganinsa yajin daga ruwan dumin ne, ruwan sanyi ya kunna ya kuma murza gel din a ido, azabar tafi ta daxu, wulli yayi da shower gel din yahau murza ido da ruwan sanyi saidai ina ko alamun sauki baiji ba banda radadi da idon suke, sosai suka sauya launi zuwa jajir. Ganin ba madafa yasa ya dau sabulun dake gurin yayi wanka adaddafa idanu a kulle.

Murumshi kawai Salma keyi ita daya, jira take taji ihun sa shuru bataji ba, jin taku ana saukowa yasata azama mik'ewa tsaye hade da kallon gurin. Jaafar tagani, laptop rike hannusa yanai sakar mata murmushi.
Yace "har kin tashi ?
Risina tayi
"Yaya ina kwana ?
Lapia" ya amsa, aranshi yana mamakin bata kirashi da Habibi ba.
"Yaya fita zakayi"
Kai ya girgiza, "garden zan futa na zauna, akwai aikin da nakeyi nagaji da zaman d'aka"
"Muje na tayaka zama" Ta fada hade da daukar wayarta dake ajiye kan kujera.
Murmushi yay yayi gaba ta mara mai baya.

Duk akan Idon Junaina dake makale bakin kofa kitchen, haushi ne yakamata.
"matar nan sai shishigin tsiya wlh, da farar safiya ko miye nabinsa waje" ta fadi, tsaki taja wata zuciya tace kema kije gurin masoyinki Mujahid mana, kai ta girgiza tace aikuwa dai kila ma bacci yake bara naje na tasoshi muje waje. Da sauri ta haura saman.

Dakyar Mujahid ya iya bude ido, sosai sukayi Jajir, ko lotion bai iya shafawa ba ya shirya cikin kananun kaya, black shade yasanya a fuska ya koma toilet yadau shower gel din yana kalla cike da mamakin sabon al'amari.

Ahankali Junaina ta turo kofar dakin ta shigo, babu kowa ciki tayi tunanin koya fita, wayarsa data gani kan gado yasa ta karasa ciki hade da daukar wayar, camera ta shiga zata dauki kanta Selfi ya fito daga toilet. A tsorace ta dire wayar, cikin inda inda tace "Good morning".
Mamaki ne yakama shi, yaushe Junaina ta renashi haka harda shigomai daki batare da izinin saba.
Fuska ya murtuke "ke!!! Miya shigo dake nan..
Kaman marar gaskiya ta ware idanu, "dama wai kiran ka zan..."
Katse ta yayi da cewa "wato bincike kika zo yimin ad'aki harda daukan wayata, gayamin waya aikoki ?
Yadda yake magana yasa ta tsorota, bata ga alamun wasa tattare dashi ba, kaman zatayi kuka tace "wallahi yaya ba bincike nazo yi ba ?..
Cikin tsawa yace "karya kike, ni nasan halin ki  am sure kuma rahoto kikazo samu dan kaiwa gaba".
Kasa magana Junaina tayi, gabanta na dukan uku uku, ga kuma haushi  kalamansa daya turnuk'e ta, koda take nemo rahoto aishi take kawo wa shine kuma yau zaiyi turning tables around.
"Get down on your kneels" ya fada cikin harsh voice.
Kuka ta fashe dashi "yaya dan Allah kayi hakuri"
Rab'awa yayi ta gefenta ya wuce yana cewa "bari na dauko belt, yau sai kin gayamin ubanwa ya aiko ki"
Da sauri tayi kneel down tana rokansa, belt ya dauko ya tsula mata daya abaya, ihu tayi tace "na shiga uku, yaya wlh da akwai zafi"
Jinjina kai yayi yana tunanin anya ba ita tasamai abu mai yaji a shower gel dinsa ba, dan kuwa kafin yafita playing b-b yayi wanka da gel din baiji yaji ba.
Fuska ba annuri yace "wato daxun kin shigomin daki ko ?.
Ware ido tayi cikin rashin fahimta, yace "badake nake ba" daka belt yayi zai tsula mata.
Tace "yaya wlh yanxu nashigo, daxu dai naga Adda Ummi ta sauko daga stairs bansani ba konan ta shigo" kuka sosai ta fashe dashi
Cize Lab'a Mujahid yayi aranshi yace "lailai yarinyar nan ta cika yar daba" kallon Junaina yayi yace "b4 d count of three tashi ki bace anan"
Mikewa tayi ta fita da gudu tana sosa baya.

Nisawa Mujahid yayi yakarasa bakin mirror, cire glass dun fuskar sa yayi yanai kallon idonsa dayai jajir ya duru da ruwa, wani irin raradi da azaba yake ji.
Sunan Salma kadai yake ambata aranshi, shi kadai yasan rashin mutumcin dazai mata.

A can Garden kuma.....

0 comments:

Post a Comment