Wednesday, 31 January 2018

ZUMA SAI DA WUTA Page 51-60

ZUMA SAI DA WUTA Page 51-60
.
Acan Garden kuwa zaune suke kan d'aya daga cikin kujerun, Jafar kam duk'ufa yayi da danna laptop dinsa kasancewar wani babban aiki dayasa agaba, Salma kuwa wayarta kadai take latsawa, so take ta kira Mujahid amma tafasa gudun karya dago abun data mai, ajiye wayar tayi a cinye hade da sauke ajiyar zuciya.
"Kin gaji ne ? Jafar ya fad'a yana cigaba da aikin sa ba tare daya dube taba.
Dubansa tayi.
"Bakai ka shareni ba" ashagwabe tayi maganar.
Dariya yayi
"Kinga wani case nake bincike akai, mayb zuwa next week zanje Kaduna"
Dadi Salma taji aranta, idan ya tafi zata samu sararin yiwa Mujahid rashin mutunci.
"Murna kike zan tafi ko ? Ya jeho mata tambaya.
Kunya ce takamata, ta dake tace "yazaka ce hakan bayan kai yayana abun alfahari nane, ni wlh banso ka tafi kaine kaidai good abu arayuwa ta"
Murumshi yayi, ciki ciki yace "naga alama kam".
Bataji abun da yace ba, zatayi magana suka ji ana rangad'a uban horn daga can bakin gate, maida dubansu sukayi b'angaran, wata mota jeep ce ta shigo ta karasa maajiyar motoci ta tsaya.
Salma tace "suwaye ne..
Mikewa tsaye yayi itama ta mike suka fara tawaka gurin....
Wata kyakyawar tsohuwar matar ce ta zuro kafa daga motan ta fito, da ganinta kasan ta hada alak'a da masu gidan, da azama driver ya zagawo gurin ta hade da risinawa ya mika mata wani sliver walking stick, amsa tayi tanai karewa gidan kallon hade da sauke sanyayyiyar ajiyar zuciya.
Gaban Salma ne yafadi, tagane matar data gani a hoto ce, murya jafar taj yace "Granny dinmu ce, mahaifiyar Daddyn mu"
Yaken dole Salma tayi, kwakwata bataga alamun annuri a fuskar taba, shuru tayi suka cigaba da takawa gurin da take tsaye tana shakar sanyayyar iskar gurin.
Daga inda suke tagowa Jafar yace "wa nake gani kaman Annah." Karashe maganar yayi cikin zolaya.
Dariya Annah tayi har hakoranta suka bayyana.
Ga mamakin Salma taga Annah ta juya wani bangaran tana lalube, cewa take "Jafar kaine ko kuwa kunne na ne ?
Karasawa yayi ya rikon ta, yana dariya gani tanan".
Tace mikomin gilashi na yana mota, dauko mata yayi ta amsa tasa sannan ta kallesa "wato kun gurma ko ganin ku baa yi, tunda baku iya zuwa gurina gani zo gurinku"..
Dariya yayi.
"Kai Annah daga zuwa sai neman sababi ?
"Kaga ni bani guri" ta fada, wucewa zatayi Salma tace "Annah ina wuni ?
Kallon Salma tayi, bata amsa ba sai tab'e baki datayi ta wuce.
Jiki sanyaye Salma ta dubi shi.
"Bata gani ne ?
Alamun tayi shuru yayi mata, saida Annah ta masu tazara yace "zaki sha duka idan taji kinci mata bata gani, tana gani amma sai da glasses,
Ware ido salma tayi.
"Miya sameta halan
"Bakomai, ciwon idon gada sukayi gurin babansu, sai dai nata yayi worst, sau biyu ana mata operation"
"Allah sarki, amma naga ku yaran Hajiya baku gada ba"
Dariya jafar yayi, yace "inji wa, koda yake niban da matsalan ido, Aunty Bilki da Mujahid suka gado ta"
Mamaki ne yakama Salma bata ga alamun ciwon ido ga mujahid ba, dama ma Aunty Bilki tanasa glass.
Shuru tayi suka cigaba da tafiya ciki.

Side drawer Mujahid ya bude yadauko wani magana a tube ya diga a idon, wani mugun azaba yaji, maida black shade  yayi ya fice daga d'akin.
 
Ta bangaran Junai kuwa kitchen ta shiga ta zauna matsar kwalla, koda Hajiya ta fito ta isketa a hakan ba tambayar da batai mata ba taki fad'a mata komai sai cewa tayi cikinta ke ciwo, Palo hajiya ta riko ta suka dawo tanai mata sannu.

Banko kofar Palo Annah tayi batare da Sallama ba ta kutsa kai ciki ta fadin "ba kowa agidan ne ?
Adan tsorace su Hajiya suka juya kallanta jin yadda aka banko kofar,  bata yi samma nin ganin taba ba dan kuwa sunyi waya jiya bata ce mata  tana tafe ba.
Dakyar Hajiya ta iya hadiyan yawu tace "Annah sannu da zuwa, aibansan kina tafe ba"
Tabe baki tayi ta kalli yadda palon ke haskawa da kayan alatu, tace "yanzu kin ganni ai
Shuru Hajiya tayi, Junaina ta gaidata, nunata tayi da walking stick din tace "kece haka kika girma ?
Magana Junai zatayi Salma da Jaafar suka shigo palon adaidai lokacin da Mujahid ya sauko daga stairs.
Zubamai ido sukayi, ko kallonsu bayi ba, fuska daure ya kama hanyar ficewa, dakatar dashi Hajiya tayi da cewa "bakaga Annah ba zaka wuce ?
Tsaye yayi chak yanai ma wani Annah mugun kallo ta Black shade din fuskar sa, aranshi yace "uhnm sai yadda ta yuyu kenan, nakuda ad'aki mayya"
Afili yace "mai makauniyar nan tazoyi agidan nan ?
B'ata rai Annah tayi ta k'arasa kusa dashi, bai ankara ba yaji ta fara kaimai Duka da Sandar hannu ta tana fadin "uwar ka nazo, dan tselan uwa kawai" ta ko ina tahau kaimai bugu, ihu kadai yarage baiyi ba tsabar yadda sandar keda zafi, Salma kam dariya tahau babbaka wa, ayayinda saura kuma suke kallon Annah cike da takaicin abunda take, Mujahid kam ganin ba bari zatayi ba yasa yayi hanyar waje da sauri, baima lura ba yaji ya buge kai da bango, da azama ya fice waje.

"Ni zai nunawa duniyan ci kamar wace ya samu sa'ar sa" Annah ta fada Masifa sosai tahau yi, Salma kam kasa daina dariya tayi, da sauri tabi bayan sa waje, Mugun kallo Annah takai masu, tace da Hajiya ke kuma muje ciki ina da magana dake, haushi biu ne yakama hajiya ba yadda ta iya ta marawa Annah baya suka shiga daki.

Ajiyar Zuciya Junaina ta sauke ta kalli Jafar dake tsaye yana jin haushin fitar Salma, tace "yaya Alhakina ya kaima ya Mujahid, dazu bakaga dukan da yayi min ba
Da mamaki ya kalle ta, "duka kuma, mi kikayi ?
"Daga daukar wayarsa, wai bincike zan mar, yahau ni da zagi da duka"
Dariya zancenta yabashi, yace "yayi maganin ki kenan ?
  Turo baki tayi "aini yanxu ba ruwana dashi, he is so mean".
Murmushi yayi, Baice komai ba ya wuce ya haura sama, turo baki tayi ta tahau gungunin baice mata sannu ba.

Haraban Gidan Salma ta fito waigen inda Mujahid yake, daga can nesa ta ganshi gurin parking motaci zaune kan boot din motarsa, kansa daure bisa cinyar sa.
Karasawa tayi gurin tana mamakin miyake yi gurin. Yana jin tsayuwar ta gurin yaki d'ago wa, hannu tasa ta d'ago da fuskar sa tana fadin "yaya badai dukan nan yasaka kuka ba" cike da zolaya tayi maganar, saidai ganin shatin dukan da yadda fuskarsa ta kumbura yasata ta shan jinin jikinta.
Hawaye taga ya fara gangarowa bisa kunci sa, yace "hankalin ki ya kwanta koh tunda kinga karshe na?
Cike da kidima da tsoro take kallan sa, gabanta sai faduwa yake..
Murmushin takaici yayi yace
"Am sorry nasan nayi hurting dinki, plz forgive me".
Tausayin sane ya kamata saidai bazata bari ya raina mata wayo ba, tace "miyasa sai yanzu zaka nemi afuwata ?
Ahankali ya zamo daga kan motar, suna fuskan tar juna, cikin sanyi murya yace "Salma i love you alot, dou nasan ba lailai ne ki yadda ba but tun ranar dana fara ganinki nakasa samin nutsuwa, kawai karfin hali da ego irin nawa yasa ban taba fahimtar hakan ba sai yau"
Kur Salma tayi mai da idanu, danson tantance gaskiar maganar sa ko kadan bata yadda dashi ba, saidai taji dadi i love you daya ce mata, kalamar data jima take son ji garesa, koda ace karya yake itadai taji dadi.

Dariyar rainin wayo ta saki sannan kuma ta daure fuska tace "do you tink am stupid, if i could recall, kwanakin baya haka kazo kace you liked me, ka bukaci friendship dina nikuma i was dumb nayi accepting, at last miya biyo baya, you wanted killing me, tnkx to Allah nayi surviving but still saida kaso ka kaini prison, gayamin wannan so ne ko kiyyaya or is it part of your egotistical behaviour ?
Hannuta ya riko, yace "nasan baza ki yadda ba, kin tsane ni, but plz find a place in your heart ki yafemin"
Dogon Tsaki Salma taja.
"You're not serious" ta fada hade da kawar da kanta gefen, sam ta kasa fahimtar inda ya dosa.
Gani tayi yayi kneeling down, da sauri ta kalle shi hade da ware idano.
Black shade din fuskar sa yacire yace " ciwon ido zai zama ajalina, i dont tink zan iya kaiwa jibi da irin azabar da nakeji, bazaki bani tym ko kadan ba ?
Tsoro da firgice ne suka kamata ganin yadda idonsa yayi jajir suna zubo ruwa, runtse ido yayi da sauri dan bazai iya barin su bude ba.
Tsugunna wa tayi gabansa,
Cikin rawar Murya tace "yaya miyasa me ka haka?
Kuka ya fashe dashi "i dont know, mayb kuma shower gel dina yayi expire nikuma nayi using yayi affecting dina, koma. dai miye ne ya illatani dayawa coz i cnt see clearly".
Na shiga uku na kasheshi, Salma ta fada aranta, sai yanxu tagane dalilin buguwarsa a bango daxu. Kaman zatayi kuka tace "plz yaya tashi muje asibiti, i cnt see you liked this"
Kai ya girgiza.
"karki damu nariga nayi using wani magani na, kuma banaso Hajiya tasan ina cikin matsala zata iya shiga tashin hankali"
Hannuta ya riko gabaya, "just tell me kin yafemin ko zanji dadi araina"
Sosai yabata Tausayi, wani irin haushin kanta take ji da muguntar da tamai, tace "yaya na yafe maka dukdai ban rikeka araina ba, but plz kadaina cewa xaka mutu, you cnt leave me"
Ajiyar zuciya ya sauke, ya zauna akasa had'e da zaunar da ita yace "kinga no secret between us, nafada mike zuciyata, do you have something to confess ?.
Shuru tayi, gabanta na faduwa, tanason gayamai itace silan komai tana tsoro.
Ji tayi yace taimaka min mu shiga ciki, kinsan yanxu na zama makaho.
Mikewa tayi jiki sanyaye suka fara takawa ciki, sun kusa shiga Palo Salma ta tsaya tace "yaya karsu Hajiya su ganmu tare, miza muce masu ?
Yace "hakane ga wayata ki kira Faiza tazo, tunda na makance bakya so aganmu tare, nasan ita komin rintsi she wil stand by me"
Cire wayar yayi aljihu ya mike mata, kin karba tayi tace "wasa nake fah"
Aranta kuwa tace "wana hauka ya kaini kirama wannan bazawarar"
Ciki suka shiga suka ci saa ba kowa a palon sai junai da hankalinta gabadaya yana kan Tv, ahankali ta taimaka mai suka haura sama.

Masifa Annah tahau yiwa Hajiya adaki, akan yara sun girma har zasu tsofe taki aurar dasu alhalin ga yammata har biyu a gida, Hakuri Hajiya tahau bata tace "Annah so nake Mujahid da ita Ummi su shirya kansu sai ayi auran, nafison su tare akan da Jafar, da dukkan alamu kuma suna son juna"
Tasaki Annah taja tace "zancen banxa kenan, ina ruwan wani da shirin su ko boyayyar soyayyar su, ni Ummi tafi kwanta min da Jafar, baki gansu dazun ba gwanin shaawa sun dace sosai, kuma da bakinki kika cemin Marikin Ummi yafi son ta auri Jafar".
"Annah gaskia hakan baiyi daidai ba"
Ware ido Anna tayi tace "toh uwata saiki dakeni ai, kinsan dai na fiki iko da yaran nan tunda ni uwar uban suce".
Hajiya tace "hakane, duk yadda kikayi daidai ne"
Washe baki Annah tayi tace "Dadina dake saurin fahimta, tunda yanzu nazo gidan yaushe zaki tafi Maiduguri yi masu albishir din bayyanar Ummi da kuma batun auran, bana so adau lokaci, gwara ayi buki tunda karfi na ".
Mamaki ne yakama Hajiya, sai kace tace mata zataje Maiduguri, kodayake dama tana da niyyan zuwa.
Tace "sai wani watan na shirya zuwa"
Ware ido Annah tayi, tace "nan da wata daya, lailai salamatu bakya so naga auran nan, tab aikuwa hakan bazai yuyuba gobe zaki tafi Maiduguri, dan kuwa ba zama nazoyi a garin nan ba, Buki ya kawoni, ki shirya gobe ki wuce kafin ki dawo kuma zan nemi Daddyn Ummi mu tsayar da rana"
Hajiya kam bata iya cewa komai ba tsabar takaici, tasan zaman Annah gidan husuma kawai zata hada ta tsangwamawa yaran gidan.
Allah ya kaimu gobe" hajiya ta fada, barin daki tayi ta koma dakinta tahau shirya kaya a akwati.

Daki Salma ta shigar da Mujahid, zama yayi gefe godon yace "i really need some sleep"
Jiki na rawa ta yaye comforter dake gado, kwaciya yayi ta rufa mai comfortee din sannan ta zauna gefe sa tana kallon kyakyawan fuskar sa, idonsa rufe, yana fidda numfashi ahankali.
Ta jima zaune harta lura bacci yayi gaba dashi, da sauri ta mike tsadaf ta shiga bandakin sa, showee gel din tadauka ta fito ahankali ta fice daga dakin, duk akan idonsa, abun da yakeson Tabbatar wa kenan wato itace tamai mugun tar nan, yunkurowa yayi zaune hade da wrugi da pilo, dafe kai yayi yace "what should i do na huce abunda kika min, most annoying part shine ko kuka batayi minba ayadda taga condition dina"
Dogon Tsaki yaja, jin motsi kofa yasashi komawa ya kwanta hade da runtse ido, Salma ce ta shigo ta karaso da sauri ta zauna gefen sa, pilo data gani akasa tadauka ta runguma tanai aika mai kallon mai cike da so da kauna, batasan sanda bakinta ya furta I love you..., shuru tayi saurin yi hade da kama bakinta, Allah yasa bai jita ba tafadi aranta. Tafin hannuta tasa ta rufe fuskan ta.

Bude ido yayi ya kalleta hade da sakin Wani irin shuumin Murmushi wanda dashi kadai yasan maanar sa, lumshe ido yayi cikin jin dadin kamshi jikinta dayake shaka.
.

Gidan shuru kowa lafe cikin turak'arsa, zuwan Annah sam bai d'ad'ara suba, ganin kowa ya batsar da ita yasa ta dunga saka da warwara rashin nasiha da zata shukawa yaran gidan.
Ta b'angaran Salam kuwa yuni ranar ita ta funte hajun Mujahid.

Washegari da safe yakama ranar da Hajiya zata tafi Maiduguri, zuge zip din akwatinta tayi sannan ta kalli Salma dake gyara gadon, kiran sunan ta tayi cikin wata murya bai abar tausayi, dubanta Salma tayi had'e da amsawa.
Hajiya tace.
"Mujahid ya tashi daga bacci ?
Kunya ce takama Salma, duk'ar dakai tayi k'asa sanna tace "bangan shi a palo ba, k'ila bai tashi ba"
Nisawa Hajiya tayi, ta karasa kusa gareta had'e da zaunar da ita kan gadon suna fuskan tar juna, tace,
"Salma burina bai wuce na had'aki aure da mujahid ba, dan Allah kiyi hakuri kuyi sorting difference dinku kafin nadawo, nasan kuna san junanku, i just dont know miyasa kuke nunawa juna k'iyayya"
Shuru Salma tayi tana wasa dayan yatsun hannayan ta.
Hajiya tacigaba.
"wani abu daya da mujahid ko yanasan abu hardly yake nunawa, saboda yadda ya d'auki kanshi yafi karfi ko wana abu, amma deep down he really carez, sometimes saiki kiga dan hakkin daya raina yana neman tsone mai ido"
Murmurshi kawai Salma tayi, ganin haka yasa Hajiya tadan ji sanyi aranta, fitowa sukayi Salma biye da akwatin suka shiga dakin Annah, sallama Hajiya tayi mata suka fita haraban gidan.  Jafar da Junai tsaye bakin motar suna jiran Hajiyan, da ganinta Junai tahau kukan zata bita, dakyar dai Hajiya ta lallab'ata tayi shuru sannan ta shiga motar, Driver dake zaune ciki yajata suka wuce.
Sabon kuka junai tahau yi  ayayinda Jafar sai bata baki yake tana k'ara tunzura da kuka shagwab'a, Salma kam murmushi tayi ta juya ciki ta barsu nan ganin abun nasu bana karewa bane.
.
Kitchen ta nufa tadau Breakfast din Mujahid tahaura sama dashi cikin sauri gudun kar Annah ta cafketa, ahankali ta tura kofar Palon ta hange shi can nesa kwance kan 3 sitter yana kallon nta news. Mamakine ya kamata, mai ciwon ido da kallan Tv, Sallama tayi ta tsaya nan inda take.
   Mikewa zaune yayi ya kalleta sannan ya amsa sallaman, takowa tayi ciki tana kallon idonsa, ba laifi idon ya koma normal said'an kumburi dabaza arasa ba.
Murmushi tace "yaya harka tashi ? Karashe maganar tayi tani kai mazauninta kan kujerar dayake zaune sannan ta ajiye abinci kan side table din gurin.
Murmushin kasaita ya sakar mata, irin murmushin nan dake fizgar zuciyan wanda akayi wa, kallon juna sukayi for some seconds zuciyoyin ko wanansu harbawa yake, kowa da abunda yakewa sak'awa cikinta, Dakyar Salma ta iya dawo wa duniyar ta, lumshe ido tayi tace "yaya ga abinci"
Jingine kansa yayi cikin kujerar yanai cigaba da kallonta, wani irin shaukin sonta ne ke ratsashi wanda shi karan kasan baigane hakan ba, abu daya ya fahimtar indai tana gurin baya tuna kowa bayan ita, cikin wata murya mai kashe garkuwan cikin bil'adama yace "feed me"
Wanni irin yir taji ajikinta da salon dayay maganar, hannuta na rawa tadau abinci dake plate din, kallonshi tayi taga yana kallon hannuta dabai bar rawa ba, "oh my God, kar mutumin nan ya gano weekness dina ko baa fada ba nasan nafi sonshi" ta fadi aranta.
Rike hannuta yayi, taji wani iri har cikin kwakwalwan kanta, da sauri ta mike kamar wace aka sikara, ajiye plate din tayi tace "na manta Annah ta sani aiki" ficewa tayi batare data jira cewar saba, Binta yayi kallo har ta fice. Aranshi mamaki yake anya shine kuwa, mike faruwa ne, daga pretending abu na neman zama gaskia, yasan yana son Salma kad'an saidai  baiso yafara having feelings sosai game da ita ba, asalima so yake ya mata rashin mutunci, inyaso daga baya saiya fara mata son gaskia.
Girgiza kai yayi yadau wayarsa dake gurin ya kira abokinsa Mubarak.
Bugu daya ya dauka, cikin zolaya yace "jobless man ka sauko daga fushin ?
Tsaki Mujahid yaja yace "kai banza ne, ana takai wayake ta kaya, ina cikin bigger problem"
Nutsuwa Mubarak yayi jin yadda yayi maganar in a serious tune, nan Mujahid ya kwashe komai yafa dimai sannan ya kara dacewa "inaga na fara sonta dagaske, jiya kwana nayi ina tunanin ta"
Nisawa mubarak yayi yace "yanzu toh ya zakayi, dont tell me kana kan bakanka na rama abun da tama"
Dariya Mujahid yayi
"bansan abunda zan mata ba, mayb hakura zanyi na rugumin sorry"
"dadai yafima, if not idan kace zaka kara mata wani mugun abu i dont tink zata cigaba da kula"
Shawara sosai Mubarak yayi tabashi, amma ayadda Fuskar Mujahid ya nuna banyi zaton zai bar Salma taci Bulus ba.

Tsaye Salma tayi bakin stairs, har yanzu jikinta baibar rawa ba, she need to be strong karya raina ta much less yanzu da take ganin ya riga ya gano sonshi a kwayar idanta, tanason Mujahid saidai wata zuciyar taki aminta dashi, tsoro take ya yaudari zuciyar ta datayi mugun kamu da kaunar sa. Muryar Annah taji a fito palo tana fadin "ba kowa agidan ne" leke tahau yi ganin babu kowa gurin, Tsoro ne ya kama Salma lafewa tayi gurin ba tare data iya k'wak'waran motsi ba. Jafar da Junai ne suka shigo, sai wani narkemai take shi kuma yanai biye mata. Tsawan Annah sukaji akansu, afusace tace "wanan sabon salon fah, miye haka ?
Harara Junaina takai mata, Jafar yace "Miya faru ?
Nuna Junaina tayi da sandar hannuta tace "dan baki da kunya Mijin Yayar taki kike narkewa haka"
Ware idanu Salma da Junaina sukayi atare jin abunda tace, Junai tace "ban gane miji yayata ba?
Tsaki Annah taja tace "uwar taku bata fad'a muku ba, toh bari kiji dakyau ita Yayar taki data fiki nutsuwa itace matar Jafar, ke kuma da Mujahid da kuka raina ni tare zaku dauwama"
B'ata rai Junaina tayi, tahau gunguni hakan bazai yuyu ba, sandar Annah ta daga da niyyan kai mata tayi sauri fecewa hanyar dakinta da gudu.
Salma kam daskarewa gurin tayi, kallon ta Jafar yayi tayi sauri kawar da kai gefe kaman mai shirin yin kuka.
Duban jafar Annah tayi tace "muje daki, akwai abunda zan gayama" afusace ta juya yabita abaya yana mai cigaba da kallon Salma, jiki sanyaye Salma ta sauko ta wuce daki.

Adakin Annah kuwa abubuwa da dama tayi ta kimtsa wa Jafar akan lailai yaja Salma ajiki, shikam jinta kawai yake baice komai ba, bayan ta gama batun ta fita yayi daga dakin ya nufi gurin Salma.

Zama Salma tayi kan center carpet din dakin, kanta daure bisa gwiwar kafafunta, shigowa Jafar yayi ahankali ya zauna gefen ta, d'agowa tayi jin kamshin turararsa, kallon sa tayi yaga idanuwata mak'ale da hawayen dake kokarin zubowa, hannu yasa aljihu ya fiddo hanky ya mika mata, amsa tayi zatayi magana ya katse ta da cewa "shiiii...basai kince komai ba, i understand everything"
Shuru tayi tahau goge idanta sannan ta dubesa tace "Thank you"
Yace "you're most welcome, if you need anything, ko shawara game da brother na kina iya min magana, i'll alwayz be around to support you"
Cikin sanyi murya tace "yaya kana da kirki sosai, am sure kanwata zata ji dadin zama dakai"
Murmushi yayi, baice komai ba ya mike ya fice daka dakin. Ajiyar zuciya ta sauke ta shingid'e a gurin, tunani tahau yi daga bisani kuma ta mike ta fice Palo.
.
Junaina da Annah ta iske ana fadan kallon Tv, Annah hausa takeson kalla ita kuma Junai ta nace sai Disney channel, dariya draman yabata, sai kace babu Tv a dakunan su.
Ganinta Annah tayi tace yauwa diyar albarka zoki zauna nan" nuni tama Salma da tazo kusa da ita ta zauna.
Fuska ba yabo Salma takarasa ta zauna.
"ina kika baro jafar, aina dauka kuna tare". Annah ta fada tana washe hakori tamkar wanda akama albishir da abun arziki, Salma kuwa yaken dole tahau yi
Dogon Tsaki Junai taja tace "sai kace wani danta da zasu kasance tare, shifa yana study room yana wasu aiyukansa.." bata rufe baki ba taji sandar Annah abayan, mikewa tayi azabure.
"dan ubanki dake nake dazaki saki baki kina magana uwa an b'arka zani, hegiyakai tamulmule mai nono daya"
Turo baki Junai tahau yi, Annah taci gaba "niyau banma ga Mujahid ba, maza jeki kira min shi, dan tselan uwa wato bazai sauko gaida niba"
Junai kam ta gama kulewa, bakin stairs taje ta tsaya tana tunanin yadda zata doshi Mujahid.

Kallon Salma Annah tayi tace "ke kuma dauko min ruwa insha" mikewa Salma tayi ta nufi kitchen, da sauri Junai tabi ta abaya. Daukar ruwan Salma tayi ta juyo sukayi kicibis da ita tsaye gabanta tanai makamata harara.
Salma tace "lafiya ?
Tsaki Junaina taja tace "i dunno why kike claming kaman wata saint,  kodayake ba wannan ya kawo niba, so nake kiyi using halinki nayan daba ko ma ince yar tasha, kisan yadda kikayi Annah ta sauya zancen ta na kokari lak'amin Mujahid da lak'amiki Jaafar"
Murmushi Salma tayi, sai kace ba rannan kadai Junai ke threatened dinta ta rabu da Mujahid ba, yau kuma table yayi turning kan Jafar.
Tace "abu mai sauki why not kicewa Annah bakya son ya Mujahid"
Ware ido junai tayi tace "so kike nasha duka kenan, muguwa kawai"
Salma tace "toh ya kikeso ayi, kinga ni am not complaining".
Mugun kallo Junai tai mata. "Ai dole kice haka, saboda jafar aka lak'amaki toh wlh baki isaba, yadda kike yar tasha da ya Mujahid kika dace, two devils"
Insult din yafara bawa Salma haushi, dakewa tayi tace "we have to work together idan kinaso musamu solution"
"Kaman ya kenan ?
Mika mata ruwan Salma tayi tace "ki kaiwa Annah ruwan, bara naje sama na kira Mujahid, ke idan kinje kice mata yana zuwa"
Amsan ruwan Junai tayi tace "idan ta tambayi ne kefa ?
"Datx your problem not mine"  juyawa Salma tayi ta wuce tabar Junai tsaye gurin baki sake, dakyar ta tsaitseta kanta ta wuce gurin Annah, mika mata ruwan tayi tace gashi, harara Annah takai mata tace "akarambana waya aike ki, ina mujahid ?
Kaman marar gaskia tace "yana Zuwa, Ummi kuma ruwa ta zubar akitchen shine take gogewa tace nakawo maki ruwan".
Amsa ruwan tayi tanace mata "ja'ira harda kwantar da murya kamar gaske".

Da sauri Salma ta haura sama, tana shiga palon yana fitowa, yar gware sukayi kowa yayi saurin matsawa baya, dafe gurin tayi tana kallon yadda yayi kyau sai zuba kamshi yake, kananun kaya jean da top ke sanye jikinsa. Gyara murya yayi yace "yau kuma kinzo fasamin kai ne ?
Bata gane inda zancensa ya dosa ba, murya shagwabe tace
"Kai yaya kodan sannu babu ?
Murmusawa yayi ya janyota wajan palon yana cewa "waya biyoki kike zabga uban gudu ?
Alamun yayi shuru tamai, murya kasa kasa tace "Annah na downstairs tana jiran ka"
Tabe baki yayi "muje ki rakani Shopping" hannuta ya riko suka karasa stair, da sauri ta zame hannuta tayi saurin rigashi sauka tana dariya kasa kasa.

Yana sauka ko kallan Annah bai yiba yace da ita sannu da zama, tagane da ita yake amman ta share. Duban Salma yayi da tuni ta zauna kan kujera yace "5min nabaki kisame ni waje bakin mota.."
Mikewa tayi kaman munafuka Annah tace "koma ki zauna, ke Junaina tashi ki sameshi awaje"
Galala Mujahid yabita da ido sannan yace "niba ita nace ba, ita wace na kira kasuwa zamuje da ita"..
"Aikuwa wace kakeso bazata bika ba.... Ke Ummi shiga ki kira Jafar yazo saiya kaiki kasuwan" nuna Junai tayi tace "dauko mayafi ki bisa" kaman bazata ba ganin Salma tai mata ido yasata dauko mayafin, takaici ne yakama Mujahid ya fice daga palon Junai ta bisa abaya kaman munafuka.
  
Fitowa Jafar yayi cike da taikaicin katse mai aiki da Annah tayi, jarabar ta yafara isanshi, so yake sati ya kama yabar masu gidan, fitowa waje sukayi su ukun, Annah sai washe baki take, saida taga ko wana couple sun shiga mota sunja sannan ta sauke ajiyar zuciya, tace "aifa dole kowanne taso hadin nan nawa, shegun yara kawai, Sannu-sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dad'e ba a je ba" wani mahaukacin dariya ta saki tana cewa "muje zuwa, mahaukaci yahau kura".

Fuskar Mujahid daure babu annuri, tuki kawai yake har suka karaso babban titin, tsayar da motan yayi sannan ya kalli Junaina da tayi kicin kicin da fuska yace "zaki sauka ko saina bakin wawan mari "
Bude motar tayi ta fito tace "aiko baka fad'aba bazan bika ba, mugu kawai" rufe murfin kofar tayi da karfin gaske ayayinda shi kuma yake dariya, ba karamin dariya taba shi ba.
  
Motar Jafar nabiye dashi abaya, ganin ya tsaya shima ya tsaya, kallon Salma yayi yace "i guess ke yake jira"
Murmushi tayi, tana shirin bude kofar Junaina tabude afusace tace "malama saiki sauko mai guri tazo, sannan kuma awa biyu nabaki kidawo muyi exchange, kinsan Annah ba wasa, ban yadda tamin duka abanza"
Salma batace komai ba ta sauka, shiga motar Junaina tayi tana jan tsaki, bata rai Jafar yayi yace "idan kika sake tsaki zan ajiyeki nan nakoma gida kuma learn to respect your sister"
Okay, am sorry" Junai tafadi amaraice.

Motar Mujahid Salma ta shiga ta zauna, gani tayi sai fama murmusa wa yake, itama murmushin tayi cikin sanyi voice tace "yaya whatx d good news?
Wani sexy look yakai mata, murya kasa kasa yace "muje miyu shopping daga nan sai muje mu gaishe da Aunty dinki, kwana biyu tana missing dina"
Kallon rashin fahimta tamai sannan tace "wace haka... ?
Bai kalleta ba yaja motar yace "Malamar ki mana, Faiza.."
Gabanta ne ya fada, murmushin da take dauke dashi ya koma bacin rai, "faiza" ta fadi aranta
"Faiza dai, ko kin manta ta ? Ya fada jin ta kira sunan afili batare data sani ba.
Shuru tayi bata iya cemai kala ba,  tunani tahau yi anya batayi kuskuren fadawa tarkon Mujahid ba, shida baya da lafiya ina ruwanshi da wata Faiza, kila ma shopping din ita zaai wa...surutai barkatai tahauyi azuciyanta.....
.

Murmushin dole Salma tahau k'irk'iri kar ya gano wani abun dake zuciyar ta. Haka suka isa Sahad stores, abubuwan amfani masu kyau da tsada ya loda cikin lodoji sannan suka fito, ita dai Salma bata cemai k'ala ba suka zo shiga mota ta mak'e abakin kofar batare da niyyan shiga ba, alama yayi mata data shigo su tafi ta make kafada had'e da shagwab'e fuska, dariya ta bashi, ya zago gurinta had'e da bud'e mata k'ofar, k'in shiga tayi tace "nifa gida zan koma, bazan rakaka gurin taba" murya raunane tayi maganar.
Hannu ta ya riko, muryar kasa kasa yace "haba habibty malamar kice fah, ina laifin wanda ya karantar ka"
Turo baki tayi.
"ni ba abunda ta koyamin, mostly korata take a class, dan haka bazan je gidansu ta wulakantani ba"
"Toh ya kike so ayi yanzu, already na kirata awaya ina tafe.
Dadi ne yakama Salma jin sai yadda tace, daure fuska tayi tamau tace "muje gidan amma a bakin gate zaku gaisa mu wuce"
Dariya yayi, ta shiga motar sannan ya zagaya ya shiga yaja zuwa gidan su Faiza. Awaya ya k'irata, ta fito ta iske shi waje, daganin Salma ta had'e rai, dukda ma Mujahid ya fad'imata Salma yar'uwa sa ce bai hanata jin haushin taba balle inta tuna yan daba dana aiko mata, ko kallon juna basu yiba ta k'arasa gefen da Mujahid ke zaune, sai wani yauki take mai tana mitar kwana biyu ya shareta, shikam lallaba ta yahau yi harta d'an hak'ura suka fara yar wasa da dariya, Iya k'uluwa Salma takai, wayarta sai ringing take takasa dauka tsabar takaici, sakon ne ya shigo nacewa "muna jiranku abakin gate" nanta gane Junaina ce, Gyaran Murya tayi had'e da kawar dakai gefe.
Kallon ta Mujahid yayi sannan ya maida dubansa ga Faiza yace "frndy ya samari, ko kuma dai nace ya bazawarai ?.
Annuri fuskar tace ta sauya, tahau wasa da yatsun hannuta, tace "tukun nadai"
Murmushi yayi ya d'auki ledar shopping din ya mika mata, yana fadin "gashi ama mai rabo kwalliya" cikin zolaya yayi maganar.
Harara tamai cikin wasa sannan ta amsa tace "niba wanda zanma kwalliya"
Magana zaiyi, Salma ta katse shi dacewa "yaya muje kunnena na ciwo"
Wani mugun kallo Faiza ta jefe ta dashi ganin yadda yayi saurin bata attention, ciki ciki tayi godiya ta wuce batare data jira abunda zaice ba. Idanuwan sa nakan Salma yanai mata sannu dukda ma dai yasan karya take, juyawan dazai yi yaga bata gurin, kallon tuhuma yama Salma sannan yaja motar sukayi gida.
Bakin gate suka had'e dasu Junaina nan sukayi canze, Jafar da Salma suka shige agidan atare, shi dariya ma abun ke bashi, Mujahid kam ko ajikinsa kota kan Junai bai biba suka shige gida, daganin su Annah tahau washe baki, aganinta sun daidaita kansu tunda taga sun jima da fita, albarka tahau shi masu tanai jinjina nutsuwa da hankalin Salma ganin yadda komai tace ayi Salma na mata biyyayya.

*****
Kwanaki sun ja, Soyyaya sosai Mujahid da Salma keyi babu wani ruwanshi da sa Idon Annah dukda ma dai Salma na kokarin kare kanta gurinta na nuna cewa ba ruwanta dashi, hakan kuwa ba karamin Dadi yama Annah ba aganinta dagaske Salma take, sau tarin yawa tafi bawa Junaina laifi akan bata kula Mujahid, ba kunya Junai kece mata ba sonshi take ba, dukda hakan Annah taki hakura ita adole zabinta kowa zaibi dan ta lura ma Jafar baya bi takan Salma, indai yana gida ta tare zata ganshi da Junaina, hakan na mugun b'ata mata rai.
Hajiya ma shuru bata dawo ba, akullum Annah saita kira tai mata albishirin yara sun daidaita kansu, da kuma yaushe zata dawo afara shirin buki, Hajiya dai jinta take tasan ba hakan bane, iya kaci tace mata ta kusa zuwa bada jimawa ba.

****
Gidan shuru kowa kwance dakinsa kasancewar ruwan da ake tafkawa tun bayan Magrib. Sanyi ne kadai ke ratsa ko ina, lamo Salma tayi cikin bargo tana lumshe idanu, hannu takai karkashin pilo tadauki wayarta ta duba lokaci, karfe goma da kwata na dare tagani . Murmushi tayi ta yunkuro  zaune hade da dialing nambar Mom, sau biyu tayi ringing Mom ta dauka, idanta biyu, alokaci tana shirin shiga dakin Daddy, tana ganin call din Salma tasan bai wuce zancen Mujahid ba wanda akullum sukayi waya saita mata zancen sa, ta rasa wana irin so Salma kema mugun yaron nan.
Gaisawa sukayi cike da fara'a, sannan Salma ta gangaro mata dacewa "Mom kin sanar da Daddy kuwa ?
Dariya Mom tayi.
"Yar gatan daddy kinsan duk abunda kikeso hakan zaai, amma are you sure he is the right man for you, nifah i dont like him"
Nisawa Salma tayi, kaman mai shirin kuka tace "haba Mom, wlh ya Mujahid nasona, bashi da matsala, trust me"
Mom tace "okay dear, dama Daddy yace na tambayeki tunda kinyi insisting sai shi, babu damuwa, your happiness is ours"
Farin ciki ne sosai yakamata Salma, sun jima suna hira daga bisani sukayi Sallama, sai sannan taga Miss call din Mujahid hudu ya kirata kusan mintin arba'in da suka wuce.
Da azama tayi dialing no dinsa ta jita akashe, mikewa tayi da sauri tana tunanin kilan wani abun yakeso takaimai ko kuma wani mugun abune yasame shi, cike da Fargaba ta fito daga dakin, jikinta sanye da sliky night wear riga da dogon wando ko dankwali babu kanta tayi saurin haurawa stairs, bata ma lura da Annah dake tsaye bakin kofar dakin Junaina ba. Mamakin ganin haurawan ta sama Annah tayi, kullum dare takan fito dan tabbatar da Yammatan kowanne  na dakinta sabod tsaro da kuma tarbiyan su, basu kadai ne agidan ba, shiyasa duk inda kake da yaran mata da baligi namiji a gida yazama dole kasanyan idanu saboda gudun shairin sheden dazai afko.
K'wafa Annah tayi ta juya dakinta dauko sandar ta.

Ahankali Salma ta tura k'ofar dakin ta shiga, can ta hango sa dunk'ule tsakiyar gadon kud'undine cikin bargo kansa kadai ke waje yana baccin sa hankalin kwance, ga wata sanyayyiyar kamshi dake tashi ta kowana lungu da tsakon d'akin. Karasawa tayi gefe gadon sannan ta kira Sunan sa ahankali, shuru bai amsa mata ba, tsoro ne yakamata kodai baya da lafia, rarrafawa tayi har tsakiyan gadon ta tsugunna daidai fuskar sa, hannu takai bisa goshinsa taji temperature dinsa is normal, ajiyar zuciya ta sauke ta zubawa kyakyawan fuskar sa idanu, murmushi tayi zata juya taji ya riko hannuta tafado jikinsa, cike da kid'ima ta kallesa,  gani tayi idanuwan sa bude yana mai mata wani irin kallo mai fizgar zuciyar wanda ake ma,  Saurin d'ago da jikinta tayi, suna kallon juna..
Ganin tayi ya mika hannunsa zai taba jikinta tayi saurin rintse idanu, murmushi marar sauti ya saki, yasa hannu ya gawar da gashin kanta gefe daya zubo ya rufe rabin fuskar ta.
"Kin dauka na mutu ne ?
Ya fada cikin salon da bata taba ji garesa ba.
Bude ido tayi ta dubesa, murya shagwabe tace "naga miss call dinka"
Marairace fuska yayi yace "sanyi nakeji, i need your body to warm me up" karashe maganar yayi ya kuma janyo ta jikinsa.
Mintsini takai mai, tace "are you crazy ? Cikin salon wasa ta fad'i.
Dariya yayi yace "am crazy about you"
Chakwulkuli yahau yi mata, tahau rokonsa ya bari, wani mugun dariya ke cinta, kasa jure wa tayi tadau karamin pilo tanai kaimai duka cikin salon kauna, tace "plz stop it..
Ganin ba bari xaiyi ba tahau kokarin sauka kan gadon da ya hargitse gaba daya, kowannan su dariya yake suka ji an bango kofar dakin da karfin gaske, atare sukayi surrender cike da tsoro.
Tsaye Annah tayi ranta na mugun tafasa da bacin rai, mugun kallon tama Salma tace "Miye hakan, nonuwa awaje, gashi a hargitse ?
Saurin karasa saukowa Salma tayi cike da kunya, adjusting hannun rigarta data zabulo kasa tahau yi.
Tsaki Mujahid yaja yace "waike Annah sa idon naki har dare ma kasuwa take ci"
Haushi ya kuma kamata, Salma kam tsuru tsuru tayi.
Annah tace "zakaci uwar kane, yarinyar mutane ka matse a daki, wayasan ma mikai mata, kaga yarinya shuru shuru".
Dariyar rainin wayo yayi yace  "ki tambayeta idan nina ce tazo"
Kallon ta Annah tayi tana jiran amsa, Salma kam ihu yarage bata yiba dan kunya, kuma abun haushi ma ita takawo kanta....bata ankara ba taji saukar Sandar Annah a ajikinta, kara marar sauri ta saki zabar azaba, da sauri Mujahid ya sauko kan gado ya amshe Sandar yaja Salma gefe, yace "Allah kuwa kika kara dukanta awaje zaki kwana".
Tafi Annah tayi tace "ubanka ma yayi kadan" nuna Salma tayi da hannu tace "keda nake yabonki Sallah ashe ko alwalar ma baki iya ba, nasan maganin ku, kafin ku b'arko abun kunya kwara na aurar daku cikin satin nan yan banza yaran kawai" warce Sandar tayi hannusa ta juya tafita.
Adan kidime ya kalli Salma yace "hope bata ji maki ciwo ba.?
Kai ta girgiza alamun a'a, sai kuma tace "yaya sandar akwai zafi ashe" kaman tayi kuka ta fadi hakan.
Sosai yaji tausayinta, dan kuwa yasan zafin sandar, zaunar da ita yayi kan gadon yace "am sorry, duk laifi na ne"
Murmushi tayi batace komai ba, sai kallan juna da suke, Annah ce ta kuma dawowa tana fadin "kina fitowa ko saina zo na kara maki ?
Da sauri ta mike, tace "Ya good nyt"
Kaman karta tafi yaji, lumshe ido yayi  yace "nyt dear, sleep tight"
Ficewa tayi da azama, yabi bayanta da kallo cike da tsatsan sonta, zuciyar sa sai kara tuna mai yake ya rama abunda tayimai kwanakin baya.
   Labb'an sa nakasa ya ciza, sannan yace "i love you so much but dole nayi hurting dinki kema ki dandani azabar danasha" kwanciya yayi kan gandon yana tunanin hope he isn't making any mistake.

Saida Annah ta raka Salma har daki sannan takoma Palo tazauna tana huci, wayarta tadauka ta kira Hajiya, Hajiya kam duk ta tsorata ganin kira alokacin, tana dauka Annah tahau ta da Masifar akan lailai saita dawo gidan Gobe, dan kuwa cikin wani sati take so ayi aure tun kafin yaran Gidan su kasheta da bakin ciki.
   Hajiya kam bata gane inda zance yado sa ba, saida Annah tayi mata bayanin abunda ya faru, Salati Hajiya tahau yi, tace bataga ta zama ba dawo wa gida yakamata.
.

Har wayewar garin Allah Annah bata bar jinini ba, ganin babu wanda ya tashi bacci a mutanan gidan yasa ta tusa Salma agaba akan lailai saita koma gidan su kafin ta janyo mata abun magana, ita kam dariya ma batun ya bata, had'a kayanta tayi cikin akwati ta fito, har waje bakin mota Annah ta tisa keyarta gaba tana kumfan baki, Salma kam ko ajikinta tafad'a mota Driver yaja maida ta gidansu. Ajiyar zuciya Annah ta sauke ta koma ciki tana magagganun ita d'aya kamar tab'abb'iya..

Salma na isa gida Momy taji dadin ganinta, dan kuwa ta jima da son dawowarta alkunya yasa kawai batai mata batun dawowa ba dan har Daddy taima zancen yace da ita karta manta Salma gidan yan'uwanta taje ba wani gurin ba.

Ta b'angaran Mujahid kuwa koda ya sauko kasa around 12 baiji duriyar Salma ba, sharewa yayi atunaninsa abunda ya faru jiya yahanata fitowa. Around 4 bayan ya dawo Masjid ne ya lura something is not right ganin yadda Annah kemai mugun kallon tana cika tanai batsewa, baibi takan taba ya leka dakin Hajiya, wayam yagani babu salma balle alamunta, ransa ne yabaci, atake ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Salma, dariya tayi dataga call din though she was expecting ya kira ta tun dazu, tana dauka yace kina ina ? Atakaice yayi maganar.
"Gidan mu" ta fada tanai cigaba da dariya, shikam haushi ma tabasa ya katse call din ya fito palo gurin Annah, fuska ba annuri yace "Annah miyasa Salma tabar gudan nan ba tare da izini nabaa ?
Harara ta watsa mai sannan ta d'auke kai tana fadin "Zancen kake so, wai ance da gwauro ya iyali"
Iya k'uluwa Mujahid yakai baima san mai kalamanta suke nufi ba, yace "bar ganin kin koreta kamar kinci galaba akanmu, ni yanzu gidan su zan nufa ganin ta, sai inga abunda kika isa yi" cike da karaji yayi maganar.
Dogon Tsaki Annah taja ta tab'e baki had'e da ware hannuwanta biyu, tace  "Abu mai sau'ki, shan koko da matsami, kuje can ku karata badai agidan nan ba, idan kaga kuma ta dawo toh an shafa fatiha ne, jarababbun yaran kawai"
K'wafa Mujahid yayi ya fice waje afusace.

Salma tare da Momy a d'aki suna hirar su cike da annushuwa, Salma tace "Momy nikam ina ya Salim tunda na tafi bai kira niba ??
Tab'e baki Mony tayi tace "these dayx bansan maike damun saba, he is always indoors, dukya rame ba yadda banyi muje yaga Doctor ba yaki acewar sa kalau yake"
Jikin Salma ne yayi sanyi, sosai taji tausayinsa, ada bata da wani aboki sai Salim tanson shi sosai, halinsa kadai yasa take maintaining distance.
Wayarta ce tayi karar shigowar text, dubawa tayi tare da murmusa, kallon Momy tayi tace "sweetheart dina ya iso"
Dundu Momy takai mata tana fadin "marar kunya kawai" dariyar sukayi atare ta mike da azama taje dakin ta tadau veil tayafa akan doguwar rigarta sannan ta fita haraban gidan inda yake tsaye bakin motar sa, fuska murtuke.
Da fara'a ta karasa garesa, gaidasa tayi ya kuma tamke fuska ya dauke kai.
Rud'ewa Salma tayi, sam batason ganin one love dinta ahaka, kaman zatayi kuka ta shagwab'e murya da cewa, "yaya am sorry, wlh Annah ta tisa ni gaba shiyasa banma Sallama ba"
Sai sannan yakalle ta, cike da haushi yace "atleast you could have holla me on phone before leaving, bakiga yadda hankalina ya tashi da rashin ganin kiba"
Hakuri Salma tahau bashi shikam sai wani cin magani yake, dakyar tasamu ta lallaba shi haryayi dariya, hirar su mai cike da so da kauna suka hauyi daga bisani yaduba agogon hannu sa ganin lokaci, duban agogon Salma tayi hade da dariya tace "ya agogon nan yan nan ?
Murmushi yayi ya kalle ta yace "babu inda zaije tunda baki sace shiba"
Dariya ta kumayi tuna haduwar su ta biyu a club data zaremai agogon yabiyo ta ya kwace.
"Wlh i was only looking for your trouble ranar, amma yaya do you still smoke ?
Gyara tsayuwar sa yayi yanai kaimata wani shumin kallo sannan yace "har yanxu kina zuwa Club ?
Harara takai mai cikin salon wasa, bata bashi amsa ba tace "yaya inason agogon nan, ban taba ganin irin saba"
Kallan sliver agogon yayi yace "ba normal agogo bane, but i cnt tell you kona miye"
Ashagwabe tace "yaya kabani plz, inason agogon"
Dariya tabashi da yadda tayi maganar, zai iya bata amma yana tsoron karta batar mai dashi. Cire ogogon yayi ya rike hannuta yace "promise baza kibari asace ba"
Kada kai tayi cike dajin dadi, yace "aro nabaki fa"
Kai ta kuma d'agawa cike dajin dadin, sakala mata yayi a hannu tana shakar kamshin sa dake fita daga agogon, sosai tajita cikin farin ciki sun kara jimawa agurin daga bisani sukayi sallama yabar gidan.

Bangaran Salim Salma ta nufa ta iske shi yashe kasan tsakiyar palo, da ganin baya cikin hayyacin sa, karewa ko ina kallo tayi komai kaca kaca, ga uban emty bottles na barasa, gabadaya ya gama muzanta. Ranta ne ya baci ta tsugunna gabansa inda yake kwance, afusace tahau kiran sunan sa, bude idanuwasan da suka sauya launi zuja yayi ya sauke su akanta, adan zabure ya mike zaune atunanin sa ko imagination dayasaba yine.
Fuska daure tace "Ya Salim miye haka, why are you trying to useless your life ?
Sauri riko hannuta yayi tabi gemai hannun da karfin gaske tana hararar sa, murya raunane yace "Salma yazanyi da sonki, duk yadda kika ganni da kuma duk abunda nake Sonki ne Sanadi (littafin Jiddah Aliyu)  na rasa ya zanyi da rayuwa ta" kuka ne ya kufce masa hade da sauri rungumarta, Haushi ne ya turnuketa ta turesa daga jikinta ta mike tsaye tanai mai mugun kallo tace "ya salim kabar bata lokacin ka akaina, cox i dont love you, tayama xaai na soka jibeka so useless and irresponsible, the only gentleman i love is your Boss, get that in your dummy brain" ahasale ta karasa maganar, shikam kuka yaci gaba, tsaki taja tahau gyara ko ina na gurin sannan ta fita ta barshi cike da tausayin so maso wani dayake mata.

*****
Washe gari ne Hajiya ta dawo gida da yan'uwa birjit na fara shirin buki. Annah kam baki har kunne zata aurar da jikoki, sunyi magana dasu Daddy an tsayar da rana one week kacal.
 
Su Junaina kam sai sabon iyayi daya karu an kusa shiga daga ciki, sosai take jin dadin yadda Jafar yake nuna mata so da kulawa, itama baa barta baya ba dama gashi ta iya shishigi da ladabi a soyayyan shiyasa sukafi dacewa da juna.
Su Oga Mujahid da Salma baa magana soyayyan sosai suke ba kama hannu yaro, wataran har Mamaki Hajiya take da irin son da Mujahid yakema Salma dan kuwa bata zata ba..

Daddy ne ya amshe zamewa Salma da Junai Uba game da komai na auren, kafin satin auran sukaje Dubai yin siyayyan abubuwan amfani masu shegu tsada sannan suka dawo.

Satin Buki.

Gidan su Momy ya cika sosai da jamaa, yan'uwanta ma sunyi kara sunzo saboda son datake ma Salma, wasu yan'uwan Salma na dangin uwa duk can suka sauka, masu gyaran jiki irin irin kusan goma Hajiya ta aiko suke gyara Salma anan gidan, Junai ma acan gidansu gyara sosai ake mata, saidai har yanxu ba wani shiri suke da Salma ba.. Event ma da suka hade kin Amincewa Junai tayi suyi tare cewa tayi kowa yayi nasa daban a inda yakeso, hakan Sosai yabawa Hajiya haushi sharewa kawai tayi ta barta ahanka, mazan ma baa barsu baya ba sai nasu shirin suke.

Three Dayx to Daurin aure, kuma gobe ne zaai event din Arabian night.
Su salma ansha murja dakayan Dilka da turaran kamshi, duk inda ta ratsa shining take da kamshi, tayi kyau sosai, kayan tsumuwa na mata (Aunty Guarantee) ba wanda baa bata tasha ba, na cushe cushe ne fir taki amincewa dasu dan bata yadda dasu ba majority ma ovary cancer suke sanyawa.

Around 8 na dare ta fito wanka sai kyalli skin dinta yake, zama tayi gaban mirror ta murje jikinta da turaruka masu dama  sannan ta sanya night wear riga da wando cotton ta kwanta, agogon mujahid dake kan side drawer tadau tana shakar kamshinsa sannan ta makala a hannuta. kaman jira take taji wayarta na ringing, da azama tadau ka ganin wanda ke kira.
Daga can bangaran yace "Angel am dieing" cikin wata irin salo mai rikitarwa yayi maganar.
Adan rude ta mike zaune "My love you're killing me, plz talk to me, miyasa meka ?
Lumshe ido yayi "am sick, cronic ciwon kai ke damuna"..
"OmG" ta fada adan kidime, ta mike tsaye.
Tace "yaya kana ina
Murya wahale Yace "ina gida, apart din Baki".
Ajiyar zuciya ta sauke tace "yaya plz stay calm, i cnt sleep idan banzo naga condition dinka ba, am coming right away" katse wayan tayi da sauri ta suri Hijab dinta tadau mukullin mota ta fita dakin, mutane sosai tagani palo anata hira, ta kitchen tabi ta fita waje batare da kowa yaganta ba. Mota ta shiga taja tabar gidan at 360.

Dariya sosai Mujahid yayi bayan sun gama wayan, zaune yake shida wasu cousin dinsa guda biyu a palon bak'i, duk wayar da yayi da Salma a speaker yasan ya suka ji komai.
Dayan mai suna Khaleel yace "Mjay kaci saa yarinyar nan na bala'in sonka, jifa yadda ta rud'e, dama nice nasamu Babe haka" dariya sosai yake yana maganar.
Murmushi Mujahid yayi yace "nima ina bala'in sonta, i cnt live without her, she is my everything but some scores have to be settle, Salma ta mugun wahalar dani ba kadan ba"
Harara Dayan mai Suna Abdul yamai yace "miye amfanin settling scores tunda nan da 3 dayx she is all yours, koma dai miye ka barta kawai"
Mujahid yace "aiko mi nayi mata bazata ji haushi na ba, she is madly inlove with me"
Dariya Khaleel yace "babaa wai wana irin wahala kake nufi tabaka?
Mikewa Mujahid yayi yace ina zuwa" fita yayi can bakin gate yayi magana da mai gadi sannan kuma ya dawo palon ya zauna. Labarin tun farkon haduwan su da Salma yafara basu, jifa jifa kuma yakan kalli wayarsa.

Salma na isowa Gidan wani mugun Horn tahau yi, da sauri mai gadi ya bude mata ta cilla motar ciki da sauri tayi parking ta fito... Sauri sauri, gudu gudu tayi tafara karasawa part din Baki dake can nesa da main house, takusa daf da gurin taji ana kyalkyalewa da dariya, tsoro ne yakamata tafara takawa da sauri, daidai bakin Kofar taji Muryar Mujahid na magana cikin dariya, gabanta ne ya fadi ta daskare gurin ba tare data iya kwakwaran motsi ba.

Cikin dariya Mujahid yace "kasan most funniest part of the story, bayan munyi plan da abokina nayi kissing dinta still bata bada kai ba, saida nayi fooling dinta na aika wasu Maza sukamin Duka atiti sannan fah ta waiwayeni"
Khaleel yace "gaskia kayi fooling dinta dayawa, ni yaushe zan yadda nasha duka abanza"
Mujahid yace "bayan ta fara kulani i had to pretend loving her duk dan na shuka mata rashin mutunci, kuma nasan itace same Ummi da Hajiya ta isheni saina nemo, niku kuwa na share naki nunawa Hajiya nasan wata Ummi. The next tin kawai naganta a gidan nan, kasan kuma miya faru ?
Haushi ne yakama Abdul, Khaleel kam dama player ne, kuma dadin labarin yake ji yace "what next ?
Mujahid yace "Could you imagine, yarinyar nan tasamin attarugu a shower gel dina, nikuma arashin sani nayi using, ranar ko i felt like strangling her to death"
Dariya sosai Khaleel yakeyi, abu sai kace a film, yace "Mjay gaskia ka wahalu, ya kayi kuma?
K'wafa Mujahid yayi yace "ya kuwa nayi, fooling dinta bashi da wuya, tricking dinta nayi into biliving ina sonta, ita kuma tayi saurin bada kai as usual .."
Khaleel yace "amma fa Salma ta hadu, koba laifi zaka huta da jikinta.."

Kaaa cigaba da Sauraro Salma tayi, hannu tasa kan kunnuwan ta tana fadin "innalillahi wa Inna'ilaihi rajun" hawayan Bakin Ciki data jima basu zubo mata ba suka hau ambaliya a fuskar ta, kuka sosai take tafara ja dabaya tayi tuntube tafadi kasa, ihu ta saki cike da tashin hankali.

Jin ihun Salma yasa Mujahid mikewa akidime ya fito waje, ganinta yayi zaune kasa tana rusa kukan daya jima yanason Ganin hawayanta. Da sauri ya karasa gareta yana fadin "Habibty yaushe kika zo ?
Wani sabon kuka tafashe dashi, jin sabon yaudarar dayake shirin yi mata, mikewa tayi tsaye tana kallon yadda duk ya gigice, rikota yayi cike da kulawa, wani irin feeling yaji ya ratsa jikinsa, ga kamshi jikinta sai ratsa mai gabobin jikinsa yake gabadaya.
Murya kasa kasa yace "sweetheart mi aka mike, plz stop crying, your tears are breaking my heart" janyota yayi zai rungumeta tasa hannu da karfi ta turesa baya.
Cikin kuka ta nuna shi da yatsa tace "dont you dare lay your filthy hands on my body, banza macuci, dan iskA, Allah ya isa tsakani na dakai, i hate you..", kuka sosai ya kufce mata, rike kanta tayi dake mugun sara mata lokaci gudu.
Hankalin Mujahid ne yatashi baiyi tunanin Salma zata dau komai da zafi ba ayadda takeson shi.
    Matsowa yayi kusa da ita tayi saurin ja baya, kaman zaiyi kuka yace "plz forgive me, i was only joking, nasan kinji komai wlh ina sonki Salma"
Wani mugun tsanan shine taji ya diru azuciyan ta, she has never been humiliated like this in her life, kuka sosai take cike da tausayin kanta, tarasa miyasa Mutane biyu nan Abbanta da Mujahid datafiso arayuwan ta suka fi kowa kuntata mata. Innalilahi kawai take ambata aranta.
Kallon shi tayi tace "ko kana sona ko baka sona i dont give a fucking damm about it, cox ko kaine autan maza na hakura dakai, na gwamma ce na kashe kaina akan na aureka balle na zauna dakai" sautin kukan tane ya karu ta juya da gudu ta koma gurin motar ta, binta yayi shima da gudu yana kiranta, bata saurare sa tashige motar taja ta wuce ta gabansa wanda kiris ya rage bata kwashe saba, bai damu ba yabi motar da gudu amma tuni ta fice daga gate din.
   Hannu Mujahid ya daura akai cike da tashin hankali yace "Am died...
Muryan Abdul yaji abayan shi yace "in life you rather learn leason the easy way or the hard way, da dukkan alamun i don't think she will ever accept you back".

Kuka Mujahid yahau yi cike da haushi abunda ya shirya dan rama abunda tamai, gashi komai ya fado kanshi.
.

Daran ranar Mujahid bai samu rintsawar arziki ba, ta b'angaran Salma kuwa bata san duniyar da take ciki ba, Salim kam yafi kowa farin ciki ranar, kodaya koma gida kwanciyar sa yayi yana hagon yadda rayuwarsa zata kasance tare da abun kaunar sa.

Washe gari babu wanda ya lura da Salma bata gidan, sai kuwan azahar da Kulchumi mai gyara mata jiki ta shiga dakinta yi mata wanka turare, wayam tagani babu alamun Salma tayi kwanan dakin, bandakin ta leka bata nan ta fice da azama ta fad'i ma Momy rashin ganinta. Ran Momy ne yabaci, shiga d'akin tayi dan tabbatar da zancen kulchumi, mamakine ya kamata gasgata zancen, da sauri tahau kiran nambar salma da wayar dake hannuta, ringing take bamu mai dauka.
Fitowa tayi waje ta hangi motar Salma a parke, mamakone ya kuma kamata toh ina salma ta shiga by this tym, karasawa tayi bakin motar hade da lekawa ciki ta hangi wayar Salma ajiye kan seat, bude motar tayi tadau wayar hade da duba dawa tayi waya last, sunan Mujahid tagani, ranta ne ya kuma b'acci, atunanin ta ko Salma na gidan su Mujahid, afusace ta koma cikin gida, batare da bata lokaci ba ta kira wasu yan'uwanta uku suka shiga mota zuwa gidan Hajiya.

Mujahid kam duk ya figi dare daya, tun yana jiran Salma tadau kiran wayarsa harya saduda ya zubawa wayarsa ido karshe yanke zuwa gidan su yayi Abdul ya hanashi da cewa ba lailai ne ta saurare shi balle yanzu da gidan ke cike ana hidimar buki, kumai ai Salma bata fasa auran saba tunda har yanzu basu ji bayanin komai daga bakin hajiya ba. Da wannan kalaman Mujahid yadan ji sanyi aranshi.
.
Annah baki har kunne, Jallabiyo yi ne matsu tsada gabanta tana zaban nasawa yau adaran Arabian nights, dakin makil yake da wasu yan jikokonta da yan'uwan ta, sai zolayar ta suke tana masu tsiya, Hajiya ce ta shigo dakin adan birkice taja Annah suka fito haraban gida kasancewar ciki makil yake da bak'i yan buki.
Cike da kidima Momy tace "Annah kinga Salma gidan nan ?
Tsaki Annah taja tace "dalilin katsamin jin dadi kenan.
Mom tace "yanzu momyta ta kirani ta tambaye ni, nace mata bata nan, da alamun kuma ba lafiya ba"
Gaban Annah na yafadi, aranta fadi take "sabon tuggu kuma yaran nan suka kulla dan karna rakashe abukin nan, toh wlh baku isa ba"
Magana zatayi sukaga an bude gate motar su Momy ya shiga da gudu, parking tayi duk suka sauko fuskar su dauke da kunci.
Babu ko gaisuwa Momy ta dubi Hajiya tace "kun mamaki wlh, a tunanin na Salma bata da wata uwa data wuce ni shine zaku rabani da ita sannan kuma kice min ke baki ganta ba, kuma ni nasan tana gidan nan"
Tashin hankali ne ya mamaye Hajiya, nanta hau kokarin fahimtar Momy da kwatakwata ta kasa gamsu wa da kalaman ta, Annah kam binsu tayi da ido tana tunanin indai dagaske Salma guduwa tayi ko sace ta akayi ba lailane ayi buki budiri ba, itakam bazan lamunci a bata  mata bojet ba ayadda ta shirya juya mazauni wanga bukin. Kamar an tsikareta ta fashe da kuka hade da daura Hannu akai, duban ta su Momy sukayi adan tsorace.
Cikin kuka Annah tace "Kuyi hakuri duk laifi na na, nice na tura Salma Kano amso min may an in ciwon idona, batayi niyyan zuwa ba saida nace idan bata jeba zan hanata auran Mujahid, ba shiri ta kama hanya batare da bata lokaci ba" kuka sosai Annah ta kara fashewa dashi.
Ran Momy ya gama bacci, kasa magana tayi ta juya tace da yan'uwanta su tafi, yaukam taga matsayin ta gurin Salma da danginta.
Kirata Hajiya tayi ko kallan ta batai ba suka shiga mota yaja. Takaici ne yakamata Hajiya ta dubi Annah da har yanzu kuka take, kasa ce mata uffan tayi ta koma cikin gidan. Dariya Annah tayi tare da debo rawan shoki  tana fadin "yo ina dalili kura da daukan kayan kare dashan bugu, ai baima yuyuwa ne dan ita baa ganta ba nasan halin hajiya sarai sai afasa bukin".

Da bacin rai su Momy suka komo Gida, gurin Daddy ta nufa ta tsara mai abunda ke faruwa, shikam baidau komai da zafi ba yace ba komai karta damu aci gabata kudanar da buki, inayaso ranar da Salman ta dawo shi yasan yadda zai nuna mata rashin kyautawar sanar dasu da batayi ba.
Jiki sabule Momy ta amince da hakan, ba yadda ta ita tunda shi daya kawo Salman ma baiji haushi ba.

****
Da daddare aka fara shirin Arabian night, su Mujahid kam suna zaune tare dasu Abdul harda Mubarak ba yazo, hirar su suke basu da damuwa banda Mujahid dayayi sukuku dashi, yasan ko karan hauka ne ya cize Salma bazata fito arabian nights ba, wayarta ya kuma latsawa kira tana ringing ba'a dauka ba, babban matsalan shi ma yarasa wa zai tunkara da maganar dan yasan duk wanda yaji maganar a iyayen saidai kuwa afasa auran..wata zuciyar tace miye zaka damu tunda kaji shuru kila ta hakura ayi auran, murmushi yayi zuciyar sa nagasgata masa hakan.
.
Arabian nyt kam yayi shagali da maana, su Junaina da Jafar ansha kyau, jamaa sai tambayan Salma suke ba kunya Annah ke dankaro karya, hajiya kam ba wata walwala tattare da ita, sam bataji dadin Abunda Annah tayi ba, ganin Mujahid bai tunkareta da zancen ba yasa bata cemai komai ba, shikam gogan baisan da wata tafiyar Salma Kano ba.

****
Bayan Kwana Biu.

Tun Ranar da Salim yakai Salma Gidan bai kara komawa ba gudun kar a zargeshi, saidai yadda yaga anata cigaba da hidimar buki yasa shi mamaki, dabara yayi ya kira momy yace zai karbi mukulli mota a hannun Salma, ita kam bata kawo komai aranta ba tacemai Salma na Kano.
Dadi yaji yafara kiciniyar hada mata passport dan guduwa da ita Ghana.

Tsoron Allah ne yakama Annah bayan an gama shagalgulan Buki, daurin aure ne kadai ya rage daza ai gobe, kullum tambayar ta ake ya labarin salma saidai tace mai magani bai gama hada magani ba, Hajiya kam taso tagano Annah karya take saidai rashin damuwan mujahid yasa tayi tunanin bakin su daya, da Yamma Annah ta fita zuwa bangaran dasu Mujahid suke, gabanta sa faduwa yake tana tsoron rashin Mutuncin zai mata, ta window ta hango su zaune da abokai suna ta hirar su tare dashi kaman babu abunda yafaru, tace "kai Mujahid fito muyi magana"
Dafe kai yayi cike da takaicin mai matan nan takeso, fitowa yayi yanai aika mata mugun kallo.
Kamar munafuka ta sinne kai tace "dama batun Salma ne, baa ganta ba nace nina aiketa kano dan kar acinye min shagali, yanzu kuma naga buduri ya k'are yasa na gayama"
Agigice yake kallon ta dan kuwa bai gane inda zancen ta ya dosa ba, "wana kano taje, bata gida ne? Ya jaho mata tambayoyin.
Tsurewa tayi tace "bansani ba, kaje ka nemo ta"
Zare ido yayi in shock yace "Annah ina take ?.
Kara tsurewa tayi tace bansani ba, bata jira cewar saba ta rugu gida da gudun dani kaina bansan yar tsohuwa ta iya ba.
Innalillahi Mujahid ke ambata, bai koma palon ba ya rugu gurin motar sa yabude ya shiga, mukullin na jiki ya kunna yaja yabar gidan.

Salma bata farka ba sai washegarin daya kaita da daddare, juyi tayi taji ta tim tafado kasan, arazane ta bude ido, wani mugun ciwon kai ke dawainiya da ita, dakyar ta mike tsaye tana karewa dakin kallo, kasa gane dakin tayi ta dafe hannu jikin bango ta fito palon, tsoro ne yakamata bata gane komai na gidan ba, wani mugun jiri taji ta fadi kasa sai bacci.
Saida tayi kusan 4 hours a gurin sannan ta kuma farkawa, so take ta tuna wasu abu amma takasa, data fara kokarin tunanin saita yanki jiki ta fadi sai bacci.
The next day ne ta kuma farkawa, da sauri ta mike koma toilet din dakin, ruwa ta kunna tasha sannan ta kirkiro wa kanta amai, saida tayi amai sosai sannan ta dawo hayyacin ta abubuwa suka dawo mata, ya Salim ta fara ayyanawa aranta, wana mugun magani ne haka yabata daga ciwon kai, ita bataji saukin ciwo ba sai hallaka da magani yasoyi, tasan kuma shi kawo ta gidan, ranta ne ta baci ta mike wani jiri ya kuma dibarta, saurin dafe bango tayi, ga wata uwar yunwa nacinta, adaddafe ta fito kofar palo taji kofar a rufe kasa jure tsayuwa tayi ta rarrafa zuwa kitchen, komai na abinci akwai, tea na ruwan sanyi kadai ta iya hadawa tasha ta kuma rararfa zuwa dakin.
Sai sannan tahau neman wayarta ta tuna a mota ta barta, kwaciya tayi akasa tana tuna Betrayal din Mujahid bata sanda kuka ya kufce mata ba, agogon shi dake hannuta ta duba taga karfe biyar na yamma. Mikewa tayi ta koma toilet, dakyar ta iya watsa ruwa tayo alwala tamai da night wear din jikinta da hijab dinta tahau rama sallolin dabata yiba. Bayan ta ida ne kuma wani mugun baccin ya kuma sace ta.

Parking Salim yayi a haraban gidan ya fito rike da ledan abinci daya kawo mata, ahankali yasa mukulli ya bude kofar sannan ya shiga, kasa ya ganta kwance a dakin ta kudundune cikin Hijab, Murmushi yayi aranshi yace wato tayi kokarin yaki da maganin.
Sunan ta ya kira ta bude ido ahankali ta kallesa, bakin magana kawai take dashi amma babu wani karfi  Tattare da ita.
"my love kin tashi" ya fada yana shafan fuskar ta, murya sanyaye tace "yaya why, miyasa zaka kawonin nan ?
Murmushi yayi ya dagota zaune suna fuskan tar juna, yace "Salma ina matuka sonki, bazan iya hakura ki auri mujahid ba, cox nafishi sonki"
Dakyar ta iya sakar mai harara, tace "miyasa kace ka fini sonshi
"Salma biliv me, akwai certain time danayi confronting mujahid akan ki nace mai kin zubar da cikina, inda yana sonki dagaske bazai nemi wulakanta ki ba harya yayi kokarin daura miki kisan daba ke kika aikata ba"
Kallon mamaki Salma tamai dajin shairin da yayi mata, amma toh yaushe akayi hakan Mujahid bai taba gayamata ba, wata zuciyar tace ba sonki yake ba tayaya zai gayamaki, Ajiyar zuciya ta sauke, tana son Mujahid bazata bari Salim ya nemi aibata saba.
Bata rai tayi tace "wanda kema son gaskia baya binka da shairi, no matter how bad Ya Mujahid yayi treating dina i still love him, kaga tashi ni kamaida ni gida"
Daura fuska Salim yayi yace "keda gida har abada, you're mine, Ghana zamu tafi gobe"
Mugun kallo tamai sannan ta mike tsaye da kyar tace "you're crazy, no wonder kayi drugging dina dan ka gudu dani, toh wlh baka isa ba" afusace tayi maganar, wucewa zatayi gefensa ya fizgo ta tafada cikinsa, matse ta yayi gam yana shakar kamshi jikinta, batasan sanda wani karfi yazo mata tasa hannu ta turesa hade da kai masa kyakyawan mari.

Kallon mamaki yayi mata sai kuma ya kwashe da dariya uwa tababbe, hannu yasa cikin aljihun sa yadauki wasu kwayoyi gudu biyar ya watsa a bakin sannan ta kalleta
"Ni kika mara ?
Harara takai mai.
"Dont you dare touch me, banza marar hankali"
Murmushi yayi hade da lasar labb'an bakin sa, ya karasa daf da ita ya  shako wuyanta tare da hijab dinta, zare idanuwa tayi da already sun canza launi, magana take sonyi takasa tsananin yadda taga ya koma mata uwa zaki, harshen sa yakai kan fuskar ta yana lasa, da sauri tasa k'afarta ta ture sa hade da matsawa, yawu ta hada abakin sannan ta tofa mai a fuska tace,
"wanna ba so bane, rashin hankali ne" akufule yace ni kika tofawa yawu ?" Ba tsoro tace "eh kai din, niba kare bace da zaka na lasar min fuska."

     .

Haushi da takaici ya cika sa, ya tako gabanta tare da bata k'akk'aywan mari guda biyu a fuska, ihu ta sakani dan azaba, bakinta ya fashe yana zubda jini, yace "zan nuna miki kare ya fiki daraja"
Daukar ta yayi tsam ya wurga ta kan gado.

Ihu take tana kiciniyar kwace kanta, shikam ko kallon baiyi ya yage wuyan hijab din ya cire, danne mata hannuwa yayi yahau kai mata kisses ta ko ina ajikinta, kuka tasoma tana rokansa, bai saurareta ba yahau kiciniyar cire mata riga, ringing din wayarsa a aljihu ne ya katse mai hanzari dubawa yayi yaga Mom ce, gabansa ne ya fadi yayi saurin dagawa daga jikinta, itakam Salma kuka take, kallon ta yayi duk ta firgice, yace "zanje na dawo inci gaba daga inda na tsaya"
Sauka yayi kan gadon tayi saurin rikosa "yaya kayi hakuri, na yadda zan auraka, dan Allah karka cuci rayuwata, ka kaini gida plz"
Yace "saboda kin raina ni ko, na maida ki gida dan ki auri wacen banza ko ?
Kai ta girgiza, tsaki yaja ya tureta da karfin gaske har tana bugewa da gadon, yayi gaba ya fice yabarta nan dafe da kanta.

Gidan su Salma Mujahid ya nufa, dakyar ya iya samun ganin Mom a haraban gidan saboda yawan mutanen dake cikin gidan, fuska daure tamai iso saboda haushin su Hajiya da Annah da takeji.
  Hankali tashe yahau tambayar ta ko Salma na gidan, ranta ne yakuma bacci da sabon rainin wayon da takeji, banza tayi dashi saida yace mata Annah tacemai batasan Inda Salma take ba sannan Mom ta saurare shi, mamaki ne yakamasu, Mom ta kwalla kiran maigadi ta tambayase ko yaga fitar Salma, yace tunda ta dawo baiga fitar taba. Hakalin sune ya kara tashi Mom ta kira Salim awaya, koda ya iso tsaye yaga Mujahid da Mom akidemi, cike da tashin sense Mom ta tambayashi koya ga Salma, ware ido yayi kamar gaske yace bai ganta. Salati Mom tahauyi. Mujahid kam kallon banxa ya aikawa Salim dan kuwa bai yadda dashi ba, karasawa kusa dashi yayi da niyyan mai magana yaji kamshi Salma ya ajikinsa, kaman jira yake ya damko wuyan sa, cikin huci da haushi yace "ina ka kaimin Salma ?
Bata rai salim yayi ya turesa, Mujahid yakai mai naushi, nan dambe ya chakwade, Hankalin Mom ne yatashi gudu kar yan ciki su fito, mai gadi ta kuma kwallawa kira, yazo ya shiga tsakanin su dakyar.
Saurin jan Salim tayi gefe ta kalli Mujahid, tace "yanzu ba lokacin fada bane, nemo inda ta shiga yakama ta kayi, tun kafin Daddy yasan cewa b'ata tayi, kuma kai kasan Hajiyar ku bazata so jin wannan mugun labari ba, duk inda aka shiga kaine main suspect saboda dakai tayi waya last kafin na nemeta na rasa" tana gama maganar taja Salim sukabar gurin tanai bashi hakuri.
Fuzgar da Iska Mujahid yayi ya juya ya fice daga gidan ya tsaya nan waje bakin motar sa, yasan cewa indai Salma is missing bashi da haufin cewa babu hannu Salim ciki, amma yazai yi bashi da evidence da zaa yadda dashi, duk Annah ta kara wuta cikin lamarin, inda tun asali batai karya ba da tuni ya binciko inda Salma take.
    Haushi ne yakamasa baima san ta ina zai fara ba, wayarsa ya ciro a aljihu ya kira Mubarak, sun jima suna waya sannan ya katse ya shiga motar sa yaja yabar gurin.

0 comments:

Post a Comment