Tuesday, 6 February 2018

ALJANA CE KO MUTUM Page 21-30

ALJANA CE KO MUTUM Page 21-30
.
wutan dakin ya dauke ko ina bak'ik'irin baka iya ganin komai" ameenatu bin saifullah tace mallam ya kamata kayi wani abu don suna dab da isowa inda muke, kuma ga nawwara cikin wani yanayi, wannan bakin abun dake fitowa daga bakinta alamun suna son fitowa ta jikinta ne, wanda hakan daidai yake data rasa rayuwarta, nawwar yana jin haka yace mallam kataimaka dan Allah.
bani son in rasa nawwara arayuwata" shikansa mallm al'amarin yasoma firgitashi' bayyi tsammanin abin yakai hakaba' karatu yasomayi cikin gaggawa, suma su nawwar suna karanto duk ayar datazo abakinsu"saida sukayi kusan minti 30, sannan hasken dakin yasoma dawowa , gdan kuma yadaina girgiza, nawwara ta bud'e ido, sai dai takasa magana, sai binsu take da kallo
kamar wata tab'abb'iya.
.
*DUNIYAR ALJANU*
lokacin da su ambar suka karaso basuga su ameenat bin saifullah ba' don sunriga sun bace musu, sunyi sunyi su bisu amma ina sun kasa" sarki yayi takaicin haka sosai, suna tunanin ta ina zasubi suje duniyar bil adama, saboda wani katanga dake tsakanin su, sunyi tsafin su amma ina sunkasa rusawa, shine suka yenke shawaran fitowa ta jikin nawwara, amma ina basu sami hanyar fitowa ba, saboda karfin addu'ar da mallam keyi don saida ta kona wayansu, dole suka koma ta katangan suka fara aikin rushewa.
*MAIDUGURI*
Tunda suka kama hanyar zuwa mai duguri,  mallam yafad'ama babban mallaminsa gasunan tafe,  sun isa lfy an tarbesu cikin karamci, inda akayi musu masauki da kayan abinci'  mallam ne zaune da babban mallaminsa isma'il maiduguri"" yana fayyace mishi matsalan dake tafe dasu akan nawwara"" sai daya numfasa sannan yace lallai rayuwar yarinyar nan yana cikin had'ari.
amma insha Allahu komai zai daidaita zata dawo yadda take da izinin Allah, nan mallam yasa aka kawo mishi nawwara sam takasa hada ido dashi""yayi mata magana  bata amsa shiba" d'aya daga cikin  almajiransa yakira yace yad'au kasko yasamo garwushin wuta acikin gida"
garin hantiti yad'ibo yazuba acikin kaskon, yamik'ama nawwar man jeedah y'ar saudiyya' yace yashafa mata a fuska"  dakyar nawwar yasamu yashafa mata" da taimakon awwal dayarik'e mata hannaye" mallam isma'il yasa aka kira mai sauran malaman dasuke karatun dasu".
  .
yatashi yahada magani misk  habbatus sauda da zaitun sai man ta farnuwa, da kuma gayen magarya duk yahada waje daya, sannan ya karanto addu'oi ya tofa aciki, ya umurci wasu  malaman  dasu sake riketa dakyau, ya matso yashafa mata a fuska da kafafuwanta" wani irin uban k'ara sake tana fizge fizge,
tace mallam kusakeni kada ku kasheni, ni ban zamto daga cikin jinsin bil adama ba, niba jin___bata karasa ba sai ta fadi sumammiya, zoben dake hannunta yana fitar da hayaki, nan take yakoma launin ja, sai alokacin ne mallam ya hango zoben, yasa hannunta acikin wani kokon magani don cire zoben" da kyar zoben yafita.
amma kuma me zai faru ana cire zoben sai sukaji kara acikin zoben kamar ana cewa kar Ku karasani tuni mallam yasaka shi cikin wani kwalbar magani ya narke , juyowar dazasuyi gareta kuma sai sukaga halittan nawwara yacanxa, bakaman da datake ruwa biyu ba, yanxu ta dawo asalin nawwararta.
awwal yace mallam yanxu duk asirikan dake jikinta sun karye  kenan, yace a'ah da sauran kadan dama babban matsalan itace wannan zoben, shine karfin asirin , yanxun kuma mun cire shi alhamdulillah, jira muke ta farfado sai ad'ora da ruqiya"" ameenatu Bini saifulla dake gefe, tace lallai babu abun bautawa da gsky sai ubangijin mu Allah, yanxu da ayoyin Allah akacire wannan zoben mai karfin tsafin, kuma anriga da angama halaka wannan zoben da me zoben wato gimbiya sameeratu.
yanxu saura sarki gulmiyanu da mukarrabansa' dan bazai ta6a yafewa ba"  gwara ma a halakasu duka, don muma musamu yancin kanmu da yadda zamu bautama ubangijinmu Allah , _Allahu sami'ul Aleem_.
.
duniyar aljanu kuwa afadan sarki gulmiyanu'  masarautar su tana girgixa yayin da wayanxu suka fadi suka mutu, saboda wannan zoben da aka kona , gininsu sai zubewa kasa sukeyi yayin da ruwa yacimma masarautan, suna neman ceto, sarki da kiyara da ambar suntsira da kyar, sarki yace ankona zoben nan shiyasa wannan abun ke faruwa, cikin huci ambar yace baza su yarda ba sai sun d'au fansa" kiyara tace mu koma jikin nawwara mudagargaza naman jikinta,munakasa ta tareda duk wanda keson ganin bayan mu, sarki yace haka za ayi.ta kalli ambar cikin 6acin rai" tace ai duk laifin kane' badan ka nuna kana sontaba aida tuni mun dad'e da mance shafinta"
can kuma kowa ya bude alqur'ani donyin karatu sai sukaji ihun nawwara tana cewa wayyo zasu kasheni, ameenatu tace mallam kuyi kutaimaketa zasu kasheta wlhy,tunda hartayi silar tarwatsewar komai nasu bazasu barta da rai ba"
nandanan suka fara karatu sosai, su sarki dasukaga za a kona su, sai suka fara cewa zamufita karku kona mu, itako ameenat cewa take mallam kuci gaba kada kubarsu azzalumai ne basa yafiya' zasu iyayin abinda yafi wannan idan aka barsu"
duk yadda su sarki da ambar sukaso fita sun kasa' sbd yadda d'akin gaba daya yake warin magunguna ga kuma ayoyin Allah dake fita abakin manyan malaman cikin sauti"  karatu suke har sai da suka tabbatar dasun konasu kurmus, sannan suka daina.
ita kuma ta fadi kasa kamar matatta ,mallam yace alhamdulillah komai ya daidai ta ankona su, yanxu kawai mujira  muga yanayin tashinta, ameenatu, tace mallam mun gode sosai yanxu ni zanyi tafiyata duniyar mu, tunda komai y daidai ta, idan nawwara ta farka agaisar min da ita, ta juya ta kalli nawwar da awwal tayi musu murmushi tace musu saduwar alkhairi, nawwar kari ke nawwara da amana, duk da dai nasan ayanxu idan ta farfado baza tasan waye kai ba, bazata tuna komai akan soyayyar da kukayi ba, amman nasan kai d'in jurumine, adalilin sonda kake mata ka tsamota daga aljanu zuwa asalinta (mutum) ka saida rayuwarka donka
ceto abar sonka "" jarumtarka ta burgeni,
sai dai kash ina mai tausaya maka saboda yanxu zaka sake shiga cikin wata jarabawar so' dan asalin nawwara bata soyayya' hasalima duk wanda yace yana sonta to daga ranar yazama makiyinta' don acewarta haryanxu bata had'u da namijinda yayi dai² da ra'ayinta ba" koda ta farfad'o yanxu batasan da soyayyar kaba, ba lalle bane ta amince maka, sai dai nasan kaid'in mijine wanda za'a kira dasunan namiji acikin jaruman maza" kayi hakuri da duk abinda zai biyo baya' inshaAllah komai zai dai²ta
       take anan nawwar yaji gabansa ya fadi'   idanu yazaro cikin wani sabon tashin hankali" gumi tako ina ajikinsa........
_kutara agaba donjin anya nawwar yana daga cikin tsarin mazan da nawwara take so kuwa._
.
gumi yake tako ina ajikinsa'  innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai yake nanatawa a zuciyarsa, ameenatu tace nabarku lafiya cikin amincin ubangiji, cikeda kewar nawwara da tausayin nawwar ta tafi, ganin yadda duk ya d'aga hankalinsa akan abunda tafad'a masa"
   nawwar dake zaune cikin matsanancin damuwa kasa amsawa ameenatu sallamar data keyi musu yayi'  sai tunanin zuccin dayake" anya zai iya jure rashin nawwara a kusa dashi kuwa? dan ba karamin illa soyayyarta yayi masa a zuciya ba;
awwal ne ya dafa shi, yace kar kadamu abokina, insha  Allahu kana cikin tsarin irin mazajen da nawwara zataso, kuma da yardar ubangiji sai kasamu soyayyar ta.
uhummmm to Allah yasa' amman awwal na tabbatar da kaddara ce tafado min, kowani dan adam da kalar tasa kaddarar, fatana ubangiji ya kawomin agaji acikin al'amarina, awwal yace hakane doctor Allah ya shige mana gaba Ameen.
nawwara dake kwance tasoma motsi alamun tashi kenan, awwal  ne ya lura da hakan , da sauri ya ta6a nawwar yace kalla kaga tana motsi'  barin kira mallam, su duka biyun suka shigo , mallam yace karku damu zata tashi da kanta, yana gama rufe baki, nawwara tayi mika tare dayin salati, bud'e idon dazatayi sai taga bak'in fuskoki akanta tsaye'   tayi saurin waro idanu, tace nashiga uku lafiya naganku adakina, nan tafara laluben Neman hijabinta don ta kulle  jikinta.
karaf sukayi ido hudu da nawwar wanda yaji gabanshi yafadi, ita kuma tace mallam lafiya katsura min ido sai kace kaga sabuwar halitta? cikin tsiwa take maganar, cikinsa ne ya murna alamun kamar zaiyi zawo, nan kuma ta saki kuka tana kiran hajiya  hajiya nashiga uku wasu mutane adakina' dan Allah kuyi hakuri kufitar min a d'aki"
mallam yayi murmushi yace alhmdllh lallai kam sauki yasamu, sai ta juya ta kalli mallam da alamun tambaya abakinta, sannan kuma takara duban dakin data ke"" taga ashe ba gidan su bane, sai ta fashe da kuka, tana cewa ina ne nan kuka kawoni, mallam yace yi hakuri sameeratu baki da lafiya ne shiyasa, yanzu dai kitashi kiyi wanka ki canza kaya sai in miki bayani," batare data musa ba tace to, mallam yace dasu nawwar  da su fito subata waje.
mallam yakira yar uwarsa da ta taimaka mawa sameeratu tayi wanka, tace to mallam, tashiga tasamu nawwara ta tashi amma jikinta yana mata kamar ciwo ciwo, da taimakon matar nan tayi wanka da ruwan magani sai taji jikin nata ya mata dadi, ta fito wanka matar ta kawo mata kaya tare da abinci,  bayan tagama ne , mallam yace tafito tasamesu a falo,
bayan ta zauna suka kara hada ido da nawwar taga ita yake kallo sai taji ta tsane wannan nawwar din don tak'in jinin kallo , shiko zuciyarshi sai har bawa takeyi, kamar zata fashe, don  ya hango tsagwaron kiyayyar sa a idanun nawwara, mallam yayi gyaran murya yace sameeratu, nasan baki San Ina ne nan ba , kuma baki san suwaye muba, wato kin dade baki da lfyane tsawon shekaru bakwai dasu ka wuce, tayi saurin zabura tace shekaru bakwai fa kace ? wannan wani irin ciwo ne dake damuna har natsawon shekara bakwai ban sani ba? mallam yace kar ki damu a sannu zaki san komai.
yaci gaba da cewa zaki iya tuna yaushe  rabonki da gida? tayi shiru tare dayin tunani, sai tatuna abunda yafaru lokacin daza taje sallah gdan baba rabi sai ga wani guguwar isaka  yatasu, tayi saurin cewa wallahi jiya ne danabar shagon dinkin mu zanje gdan baba rabi sallah sai ga wani  guguwan iska yataso.
abunda kawai zan iya tunawa kenan, mallam yace yauwa, toh ba jiyabane yanxu kusan shekaru bakwai kenan da faruwan wannan al'amarin, ta dafe kirjinta tace nashiga uku mallam, toh yanxu ina iyayena? badai tsawon shekaru bakwai bana tare dasu ba! , wayyo Allah abbana, wai meya sameni hakane?
Kai malam ya d'aga mata alamar bata tareda iyayenta"
toh yanxu  nan wani gari ne! yace maiduguri, idanu tazaro, sai kuma tasaki  kuka,  to waye yakawoni maiduguri!  mallam yace labarine mai tsawo kuma cike da al'ajabi da tausayi:
  yanxu dai kibari idan kin huta zakiji komai in Allah ya yarda"  kuka kawai take tana cewa dan Allah sukaita wajan iyayenta taga awani hali suke" mallam yace ya isa haka nawwara kiyi hakuri insha Allah zamu sada ki da iyayenki, tace to ngd'  nawwar da awwal tabasu tausayi sosai," mallam yace tashi kije ki kwanta abunki kar kisaka damuwa aranki kinji, kai tad'aga masa tana sharar kwalla.
bayan tashiga ciki mallam isma'il ya kalli mallam da su nawwar yace yakamata mukai  yarinyar nan wajan iyayenta, awwal yace haka ne kam sai muje gobe ko?  tunda kano ne wajan bazai yi mana wuyan ganewa ba, hakane Allah ya kai mana rai.
yaune ranar dasu mallam isma'il da su awwal zasu kano da nawwara, tafiya suke cikin mota kowa da abunda yake sakawa azuciyar sa har suka isa kano.
*KANO*
Alhaji idrisa ne kwance Afalonsa yana tunanin rayuwa"  hajiya maimuna takawo masa ruwan sha da abinci, zama tayi kusadashi,  tace mallam haryanxu bazaka daina yawan tunanin nan ba!  yace haba maimuna' ai tunani ya zamemin dole  yau ace shekara bakwai babu nawwara  babu alamar ta" yau koda gawarta nagani daya fiyemin kwanciyar hankali , bamu san awani hali take ciki ba , hakane Alhaji, haka Allah y kaddaro mana muciga ba dayin addu'a, insha allahu zamu sami mafita , suna cikin magana ne wani yaro yazo yace ana sallama da Alhaji wai baki Daga maiduguri, yace to kace su shigo.
.
yace to kace su shigo, dan Aiken ya koma yace wasu mallam isma'il ance su shiga, nawwara tana cikin mota zaune da badan su mallam sun dakatar da itaba da tuni ta falla da gudu ta shige gdan, sai tsaki take ta ja, shiko nawwar kallon ta kawai yakeyi, yadda ta hade giran sama data kasa" azuciyarsa yace wannan yarinya za ayi daru da ita.
muryan mallam ne ta katse masa tunanin sa, mllam yace sameeratu fito kimana jagora  cikin gdannaku, kamar ko jira take amata magana, cikin murna ta fito waje tana washe hakora" tace to mallam, yace to bismilla mujenku, itace agaba tana tafiya cikin nutsuwa.
.
suna karasowa tsakar gdan sukaci karo da zainab tana wanke wanke, karaf sukayi ido hudu da sameeratu, zainab ta saki kwanon hannun ta, ta arce cikin gidan da gudu tana ummu ummu ummu, gatanan gatanan, yayin data fada jikin Hjy maimuna, tace ke lafiyarki kuwa, alhajine yace zainab wakika gani kike gudu haka"" sai haki kike.
ji yayi ance abba nice kunnuwan shi ce ta jiyo mishi muryar da bazai taba mantawa dashi ba, muryarda a kullum yake mafarki da tunanin Allah yasake had'a fuskokinsu kafin mutuwarsa" atare suka d'ago idanu cikin sauri shida hjy maimuna, suka zubasu ga kofa, nawwara ce tsaye tana hawayen farin ciki.
Alhaji idrisa da hjy maimuna sukayi zumbur suka mike tsaye, kowanne bakinsa na rawa sun kasa furta kalma d'aya" dakyar kamar had'in baki sukace sameeratu kece kuwa,  karasowa tayi  falon da gudu ta rungume iyayen nata , tana kukan murna, abba umma nice nawwaran Ku, ban mutu ba inanan.
su nawwar dake gefe sun basu tausayi, har sai da kwalla  ya  fito musu, nawwara tace zainab nice fa sis dinki wacce kuke kwana daki daya, da gudu zainab ta rungume nawwara, sister nah ina kika je nayi kukan rashinki na tsawon shekaru, amma kin dawo kenan baza ki koma ba ko?, nawwara ta share mata hawaye.

tace karki damu sister zee na dawo kenan insha Allahu bazan sake tafiya na barki ba, Allah sarki dama yan magana sun ce sabo turkin wawa,sai alokacin Alhaji idrisa ya kalli bakin kofa inda su mallam isma'il ke tsaye cikin tausayi.
.
ya karasa wajan su tareda mik'a musu hannu sukayi musabaha, sannan ya nuna musu waje suka zauna, aka gaggaisa, mallam isma'il ne yafara magana, yace Alhaji mu baki ne daga maiduguri, munxo ne don mu sadaka da yarka sameeratun nawwara, sannan kuma mufayyace maka abubuwan da muka sani, Alhaji yace ikon Allah ashe duk shekarunnan da suka shude sameeratu tana maiduguri  bamu sani ba.
mallam yace a'a bata maiduguri tana duniyar aljanu har natsahon shekara bakwai nawwara tazaro ido waje tareda dafe kirji tace duniyar aljanu kuma? mallam yace eh, Alhaji ya jinjina kai, yace lallai kam nayarda, sbd na tafka babban kuskurenda  ko makiyina bazan masa fatar  shiga halin dana shiga ba, nan dai mallam ya kwashe labarin bacewar nawwara har  izuwa lokacin da aka ganta, babu abinda
Hjy maimuna alhaji idrisa da ita kanta nawwaran keyi sai  kuka, nawwara tana cewa yanxu nice nayi tarayya da aljanu, abbanta yace nawwara kiyafe min, duk ni naja miki na rashin d'aukar shawara da maganar malaman islamiyyarku.
a'a abba ni baka min komai ba kaddara ce kawai tafado mana, Allah ya yafemu baki d'aya" ta d'aga ido tayiwa su mallam godiya, mallam yace ba sai kin mana godiya ba, kiyawa Allah godiya sannan kuma ki gode masu awwal abisa sadaukar da ransu da sukayi sbd ceto taki rayuwar, sannan kuma  ameenatu bin saifulla duk da wannan tariga ta koma duniyar su.
nawwara takalli su nawwar  tace yaya awwal yaya nawwar , ina matukar godiya akan tsamoni da kukayi daga aljana zuwa mutum, Allah ubangiji yasaka muku da mafificin alkhari, yabaku abokanan rayuwa na har abada, yasa aljanna fiddausi ce makomar ku" kowa yace amin su nawwar sunji dadin addu'ar ta," mallam yakara yiwa Alhaji idrisa nasiha akan shiga hurumin aljanu, da yawaita addu'oin  kariya,, nan dai mallam yayi tanuna musu abubuwa masu muhimmanci dakuma hanyoyinda za'abi dan gujema shed'anun aljanu,
.
Daga bisani aka kaisu dakin bak'i tare da abinci da abunsha, ankarramasu sosai.
nawwara da kanwar ta suka fad'a daki ana hiran yaushe rabo, Alhaji idrisa ya hana afadama kowa dawowan nawwara, yace sai tayi kwana biyu lokacin ta huta,, kwanan su mallam biyu suka tafi' kowa ya kama hanyar garinsa  tareda abun arziki,dakyar suka amsa, nawwar ya tafi cike da begen abar sonshi.
kwanan nawwara biyu a gida cikeda jindadin ganin y'an uwa da abokan arxiki anzo tayasu murnan dawowarta"  harda mallaman islamiyarsu da aminiyarta khadija, wanda sai da sukayi kukan farin cikin sake ganin juna' sauda kuwa wato yayar nawwara,harda dan kwarya²n walima ta shirya ma nawwara ,
mami hafsa da autar ta mimi" sunyi murnan dawowan su nawwar, mimi tashirya ma yayan nata abinci kalala, bayan yayi wanka yaxo yaci abinci, sannan yabasu mami lbarin abunda ya faru"" mimi tace lallai hamma kai jarumine, da kowace mace zataso samunka amatsayin namijita, gasky aunty nah nawwara, tayi dacen gwarzon namiji dan kwalisan matasa, hamma zan so inga wannan auntyn nawa, harara yatsa mata' yace kajimin yarinya da iyayi' ke harkinsan wani jarumi! murmushi tayi tarufe idanunta tace laaa hamma aida gske nake koh mami!'
mami tace gsky nima zanso inga wannan nawwaran data kad'a kwakwalwar hamman nawa.
suka sa dariya, mami tace dafatan dai bakayi kauron baki wajan furta abunda ke xuciyarka ba, nawwar yace mami cikin raunanniyar murya,da wuya sameeratu ta soni, don yadda ameenatu tace mana kwata²ita bata da lokacin wani d'a namiji, sannan kuma da alamun ta tsaneni, mami tace meyasa kace haka, nan yabata labarin sbunda aminatu bin saifullah tafada masa daza ta tafi, da yadda kuma nawwaran ta nuna masa a maiduguri.
mami ta tausayama d'anta, lallai jarabawa ce ke binka nawwar" abunda zan ce maka kadage da addu'a insha Allah idan nawwara alkhairi ce agareka babu makawa saika aureta,  murmushin jindad'i yayi yace nagode mami nah, Allah ya barmin ke kiga jikokin ki.
bayan kwana biyu da dawowansa yana kwance akan gado yana tunani nawwara, da yadda zai tunkareta maganar soyayyarsu"  ya tuna yadda yaga farin cikinta a lokacin da sukaje gidansu taga iyayenta, yayi murmushi, tare da lumshe idanun shi, yace ana hubbiq tartin ya samra, ,hubbee ilaiki abadan ya samra,yakara sakin murmushi, jiyayi antab'ashi.

0 comments:

Post a Comment