Tuesday, 6 February 2018

ALJANA CE KO MUTUM Page 11-20

ALJANA CE KO MUTUM Page 11-20
.
Tun daga lokacin da ameenatu bintu saifullah tace nabazama duniyar bil adama don neman addinin islama"daga ranar na dau niyyar shiga duniyar bil adama, da haka rayuwata taci gaba da tafiya, ba abunda nasa agabana sai neman addinin musulunci, nayi yawo dayawa acikin duniyar bil adama, narasa wazan tunkara da wannan batu nawa" ana haka ne ranar sallar ku ta edi na hadu da kai, alokacin da kake k'ask'an da kanka wurin ubangijinka' kana addu'a, kana niman taimakon Allah.
          tun a lokacin naji ka burgeni' zuciyata ta aminta dakai, naji bawanda yadace na  tunkara sai kai, daga ranar nafara bibiyarka, atunani na kaine zaka taima kamin gurin gano wacece ni,  kuma ka koyar dani addinin islama""nawwar kataimaki rayuwata ina cikin tsaka mai wuya, ka taimakeni ka tsamoni daga duhun jahilci" ta karashe mgnr muryarta na rawa"
          Nawwar ya numfasa yace sameeratun nawwara naji bayaninki, amma wannan batu da kika zo dashi daidai yake darasa rayuwar mutum, ayanayin labarin da kika bada na fahimci duk wanda yayi  yunkurin taimaka miki gurin gano asalinki, to shima dai dai yake da rasa tashi rayuwar gun wad'ancan azzaluman!!" amma addu'a itace takubin mumini,  *innallaha laa' yamli lizholimin.* _lallai Allah baya kyale azzalumai_  da sannu zai nuna musu isar sa....
zan taimaka miki don Allah da kuma son dana ke miki, sannan da yar dan mahaifiyata" idan ta amince shikenan sai mu tsananta addu'a Allah ya mana jagora.
.
          Tace nagode nagode sosai kuma insha Allahu wani abu bazai taba samunka ba, namaka alkawarin haka" kuma mami hafsat baza ta hanaka taimako ba da yardar Allah"" dr awwal ne yayi gyaran murya yace wani hanxari ba gudu ba, kun manta abu guda daya, kar ku manta  sai da taimakon ameenatu bintu saifullahi   zaku samu cikan burinku, saboda ita ta turo nawwara duniyar bil adama don tasamu mutumin daya rike addu'a don suje su taimaketa tafito daga hannun su ambar,  ta bakin ameena ce za agano wacece nawwara!!! yanzu dai abunda zakuyi shine kutaima keta tafito, ko ba hakaba" sameeratun nawwara tace tabbas gskyan kane awwal dole sai yar fulani tafito, amma gurin da take akwai hatsari, nawwar yace karki damu da taimakon Allah zata fito.
          toh yanxu dayaushe ne zaka fara koya min addininna ku?, inshaAllah nan da sati daya ok nagode, bayan sunyi sallama sai ta bace.
        nawwar da awwal  sunshirya yadda zasuyi su samu mami hafsat da wannan zance, labari har yakai kunnan mami hafsat, sai da ta girkiza dajin labrin" amma dayake da awwal ne kuma shi yake mata bayani sai ta amince musu tare dayi musu addu'an samun nasara,nawwar yaji dadi sosai da maminsa ta amince daman mace ce mai hakuri da tawakkali!!! 
*wanene nawwar*
da'ne ga alhaji isma'il  da hafsat, alhaji isma'il haifaffan garin yola ne iyayenshi duk acan suke gaba da baya shi ba fulatani ne, yayi makarantansa tun daga primary zuwa universty abti yola, yayin daya gama ne, aminin mahaifinshi wato alhaji kasim shiyasa ma mishi aiki a jahar kaduna" isma'il tun yana karami alhaji kasim ke sonshi" anan gdan alhaji kasim  na kaduna isma'l ya zauna, yana da yaya mata uku, maza biyu babban dan alhaji kasim namiji ne me suna abdalla, sai ibrahim, sai hafsat da mariya sai  khadija autar su kenan,  mahaifin isma'il takanas yazo kaduna wajan amininshi alhaji kasim, don ne mama dansa auren hafsat, , kasan cewar dan nasa yaje masa da batun son auren hafsat , alhaji kasim yaji dadi sosai" kuma antambayi hafsat din itama ta amince, mafarin auren iyayen nawwar kenan!!" bayan auren su da shekara biyu Allah ya albarkace su da d'a namiji wato nawwar  sai kuma  sulaiman, daga sulaiman sai autar mami  wato, maryam wace ake ma  lakani  da mimi, macen ta daya tal maza biyu,, mami hafsat ta bama ya'yanta tarbiya dai dai gwargwado, ga kuma addini daya ratsa jikin su, dukkansu suna da haddan alqur'ani mai girma, don shi sulaiman ma baban malamine a islamiya, yayin da nawwar shi kuma doctor ne, sai autar su mimi itama karatun take afannin boko tana ss 1, afannin islamiya kuma tana *sanawiyya* .
wannan shine lbrin su nawwar.
*****************
*dunyar aljanu*
sarki  gulmiyanu ya tara dukkan aljanu yana shaida masu" nan da wata daya za ayi gaga rumin bikin dansa *ambar* da *sameeratun nawwara*, nan take taji gabanta yafadi, shi ko ambar da kiyara me zasuyi inba murna ba har gaban mahaifin nashi yazo yana godiya"  ambar ya dago ido yana sakar ma nawwara murmushin samun nasara, sarki gulmiyanu yaci gaba da cewa' nan da sati biyu ina son akashe ameenatu bintu saifullah' cikin tashin hankali samiratu taje gaban sarki ta tsugunna tana rokonshi da abar yar fulani da ranta!!" amma ina sarki yaki amince wa, ganin sarki yaki sauraronta"  tuni ta garzaya duniyar bil adama wajan nawwar don neman mafita, tafada mashi abunda ke faruwa shima hankalinshi atashe yana innalillahi wa inna ilaihi raji'un , la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin"" ai bashiri nawwar yashiga koyar da sameeratun nawwara addinin islama, addu'oi iri2 yasoma koya mata' kan kace kabo sameeratu tayi zurfi sosai, idan yana koya mata wani abun ma sai ta dinga tunanin kamar ta tabayin abun ada:!!.
           akwana atashi ba wuya a wajan Allah, a yaune su awwal da nawwar da sameeratun nawwara, suka shirya hanyar da za adauko *ameenatu bintu saifullah* 
.
sameeratun nawwara ta kammala shirinta  tsaf tare da daukan makaman ta, saboda tsaro , bayan tagama ne ta garzayo duniyar su nawwar , ayayin da ta iskesu suna  zaman jiranta shida awwal'  nawwar ke kara karfafama awwal gwiwa akan wannan tafiya daza suyi.ganin yadda duk yake a tsorace,
   yace haba abokina" kada kabada maza mana' kadafa kamanta *Allah yace yana nan aduk inda bayawansa yake tsammaninsa'*
    kasa aranka Allah yana taredamu kumashi zai taimakemu" inafatan dai kayi azkar d'in safiya, da addu'ar dana baaka jiya? murmushi awwal yayi cikeda kwarin gwiwa yace nayi Allah ya taimakemu'  Ameen...
         Sallamar sameeratu ne ya katsesu da karatun suratul yaseen dasuke bayan sungama karanta wasu ayoyi acikin suratul baqara"  takaraso  ciki, dukansu suka amsa mata sallamarta,fuskarta dauke da murmushi yayin da take kallon nawwar, shima ya mai da mata martani, tace masu *masa'un khair* suka ce mata  *masa'u *noor*.
         auwal ne yace ai nayi zaton baza kixo ba, tace tab mai zai hanani zuwa, yanxun ma duk nakosa muje, nawwar yace ' ki kwantar  da hankalinki insha Allahu zamu samu nasaran zuwa wajan ameenatu bin saifullah, tace toh Allah yasa nagode sosai" awwal yace ya naganki da makamai, tace ai saboda tsaro na dauko, yayi dariya,  yace haba ai ayar Allah kadai ta ishemu makami' sbd haka karki samu damuwa, to awwal, yanxu sai kutashi muje don lokaci na kurewa.
          nawwar yace to amma bari mugabatar da addu'a kafin mutafi, suka ce to, nan suka karanta *suratul iklas* *falaq* da  *nas* sai  *ayatul kursiyu* sannan suka shafa, sameeratu tace kurufe ida nuwanku, yadda ta umur ce su haka sukayi.
.
    *duniyar aljanu* awani kurmin k'ogo suka sauka' tace subude idanunsu" nawwar ne  yafara budewa tare dayin addu'ar neman tsari, shiko awwal yakasa bude idonshi saboda tsoro, don bai San me zai fara gani ba idan yabude idon.
       nawwar da nawwara suka dubi awwal  cikin mamaki, nawwar yace awwal lafiya bude idanunka mana mun isofa, cikin rawar murya awwal ya soma magana , yace nawwar wallahi tsoron budewa nakeyi" sameeratu tace kar ka damu ba abunda zaifaru da kai kabude , nawwar yace haba doctor be a man mana, Kasa aranka  kana tareda sojojin kariya daga Allah ,
ahankali  awwal ya bude ido shima tare dayin addu'a.
      haka sukabi wajan da kallo cikin kurmin dajine ,  sameeratu tace nayi mana Rabin zuwa, sauran tafiya kuma da kanmu zamu karasa, saboda bani da karfin da zanjamu a iska mukarasa wajan, suka ce to " nan da nan suka doshi hanya tafiya suke sosai kowannan  su da abunda yake tunani azuciyar shi,  tafiya suke babu kakkautawa,  har suka gaji suna samu gefe don su zauna suhuta.
      Duk abunda ke faruwa su sariki *gulmiyanu* ba su sani ba' sbd kafin sameertu sutafi sai da taje ta to she madubin da suke ganin hangar da zai sadasu da ameenatu bin saifullah , cikin ikon Allah kuma dukkansu babu wanda ya hankalta da hakan,  itako ameenatu tananan cikin dakin azaban da aka ijyeta, tanaji ajikinta sameeratun  nawwara natunkaro wajanta don taimako.
       awwal  yace sameeratu wai bamu iso bane! wlh nagaji nikam, sameeratu tace yi hakuri saura kadan mukarasa, Allah dai ya kaimu lafiya amin.
     *Ambar* ne zaune  da kiyara suna hira sai sukasa ajuyo musu madubin dazai sada su da ameenatu bin saifulllah , aiko anajiyo dashi sukaga abu bakin kirin, Akbar yayi saurin mikewa, yana cewa garin yaya wannan abun yafaru?tayaya ba aganin hoto? kiyara tace lallai akwai wani bakon al'amari ayi sauri aje abin cika, sannan kuma akira sameeratun nawwara , labari yaje kunnan sarki shima hankali tashe don ba'a taba mishi irin wannan abun ba.
           kiyara ta dawo cikin sauri tace babu sameeratu , nan take aka bude madubin da kyar , kafin subude su nawwar sun Isa ga ameenatu , duk sun kashe masu tsaronta da ayar Allah,  sameeratu ta rungume ameenatu bin sai fullah, daidai lokaci sarki dasu ambar, suka hango abunda ke faruwa, ambar yasaki wani irin gigitaccen kara nabakin ciki, saida su sameeratu sukaji , ameenatu tayi saurin cewa maza maza kuzo mu wuce dan  sun ganomu, su nawwar gabansu sai faduwa yake, yana ta karanto addu'a" haka awwal ma.
         sarki yace garin yaya haka tafaru bil adama har suka samu damar daza su shigo mana duniyar mu, cikin huci kiyara tace wannan duk aikin sameeratun nawwara ce, ambar yace mufar musu baza abar su da rai ba.
         nawwar suna ganin bak'in abu natasowa da sauri duk suka tsorata , sameeratu tace ameenatu kiyi sauri kifitar da mu gasu nan zuwa,  tace to ni yanxu ina zamuje, nawwar yayi saurin cewa musauka aduniyar mu kawai, aiko dafda wani guguwar iske ya kusa  dasu suka mace bat, cikin nasara, sai gasu  aduniyar bil adama, cikin office din doctor awwal , suka zube akasa awwal da nawwar kamar wasu matattu, can suka farfado bakinsu d'auke da addu'a'  nawwar yace anya baza su iya biyo mu nan ba? aminatu tace a'a, nayi wani abun da baza su iya gano inda  muke ba, nawwar yace akwai wani gdna dake kusa da asibitin nan, yakamata muje can.
            suka ce to kowannan su zaune awwal dai shiru yayi don sai yanxu yakejin gajiya,  bayan kwana daya da dawowan su duk kan su zaune afalo, idan kuka ga sameeratu da ameena bin saifullah sai ka rantse da Allah mutanene, sbd idan zasu hadu da bil Adam sukan fito asuffan mutane , yauma hakan takasance .
      nawwar yace naje nasamu malamina nayi mishi bayanin komai, kuma ya amince dashima yataimaka mana , gashinan zuwa nan da yan mintuna, don agabanshi za awarware wannan kullalliyar al'amarin, amenat tace tabbas kayi tunani nawwar , hakan nada kwau ,bata   gama rufe baki ba mallam yayi sallama , suka amsa nawwar yanuna mai waje ya zauna"  duk suka gaisar da malamin.
        saida  mallamin yayi doguwar addu'a sosai sannan ya bukaci ameenatu bin saifullah data bayyana wacece sameeratun nawwara" kowa ido yazuba mata donson jin abun da zata fada, tace Allah y gafarta mallam sameeratun nawwara takasan ce ajinsin_____?
.
         A hankali *Ameenatu bintu saifullah* tace Allah ya gafarta mallam hakika sameeratun nawwara ta kasance acikin jinsin bil adama gaba da baya,  awwal ya zaro ido, yayi saurin cewa kina nufin asalinta mutum ce ba aljana ba? tace tabbas mutum ce ba aljana ba, nawwar da nawwara sai kallon aminat suke cikin mamaki da d'aurewar kai.
              Nawwar  yace ameenatu  munaso kifad'a mana tayaya sameeratu tazama aljana" alhalin kuma kince asalinta mutum ce, daman mutum na rikid'ewa ya koma aljan? ta dago ido ta kalli mallam da baice dasu komai ba sai kallonta yake hana nazarin wasu abubuwan"  ta juya takalli su nawwar da suka zuba mata ido suna jiran amsarta,
sannan ta maida kallon ga sameeratu data matsu taji ko ita wacece'  dafata tayi ,tace karki damu yau zakiji asalinki" kuma zakiji ko suwaye iyayenki.

*shekaru bakwai*
*da suka wuce*

Akwai wani bawan Allah me suna Alhaji idrisa da matarsa hajiya maimuna, dukkan su haifaffun garin kano ne, Alhaji idrisa dan kasuwa ne kuma Allah ya hore mashi arziki, babban danshi na mijine me suna muktar, sai nabiyu mai suna isma'il sannan na uku macece mai suna sauda   sai abba,  sameeratun  nawwara sannan  zainab, yayanshi biyar kenan ukun sunyi aure , sai yarage daga sameeratun nawwara sai zainab.
      sameeratun nawwara yarinya ce me hazaka sannan tana da kyanta daidai gwargwado, tsakaninta da kanwarta zainab babu wani jaa, don ba ayaye sameeratu ba aka samu cikin zainab.
   
gidan Alhaji idrisa babba gida ne, daya gada ga iyayensa" gidan hade yake d gdan gona, ko ta ina acikin gdan akwai bishiyoyi, kama daga bishiyar mangwaro, kashu, Tsamiya, dalbejiya, zogale, kukan Fulani,  da dai sauran su"" lokacinda sameeratu na karama mamanta kan shimfida taburma da yamma sai ta ijye nawwara akai ita kuma tana aiki ga kuma tsohon ciki datake fama dashi, da haka sameeratu take gangarawa cikin wayannan bishiyoyin tayita  wasa da y'ay'an aljanu, duk mahaifiyarta bata sani ba,  dan duk sanda ta gama aiki tazo d'aukarta, zata isketa a inda ta barta"  da haka yarinyar tasaba dasu, yakasance duk lokacin dabata je wajanba ta dinga kuka kenan, tun mahaifiyarta na hanata har ta kyaleta.

akwai wani rana da ake meeting na aljanu, wacce shugaban aljanu itace *gimbiya sameeratu* ta garde akan kujeranta na sarauta kowa na girmamata, ga kayan marmari anjere mata agabanta, alokacin ne hajiya maimuna ta ijye nawwara agefenta don tayi sallar magriba afalo, tafara sallah bada dadewa ba nawwara ta rarrafa tafito waje har ta Isa wajan da aljanun suke taro ba su lura da itaba, sai  dataje daidai kusa da gimbiya sameeratu, sukayi ido hudu, abunka da yaro sai nawwara tasakar ma gimbiya sameeratu dariya, itama ta maida mata tare da daukan nawwara tabata kayan marmarin dake gefenta, tundaga lokacin  gimbiya sameeratu taji tana son nawwara, alakacin ne ambar yaji shi bawadda yake so aduniya irin nawwara.
       dahaka dai nawwara tashiga ran aljanu, amma tana karamanta ne take ganin su, data fara girma sai sukayi kamar sunbarta , alhalin basu barta ba, Alhaji idrisa yasa ansare duka bishiyoyin gdansa inda yatada Gini aciki, sare bishiyoyin nan bakaramin tashin hankali ya afku a duniyar aljanu ba" don alokacin daza asare bishiyoyin gimbiya samiratu tana kwance tana hutawa, abun ya afka da ita daidai tsakiyar cikinta aka sare, sai yatsar ta mai duke da wani shegen zobe mai kyau yafado kasa, daidai saitin dakin nawwara" .
       anan rai yayi halinsa, duniyar aljanu sungirgixa da mutuwan gimbiya sameeratu,  sarki gulmiyanu yayi takaicin rasa yar'uwar shi da sauran aljanun su," mutumin dayasare bishiyar ba ayi kwana biyu ba  yarasu , mutane suka fara jita jita akan cewa ai bishiyan daya sarene agdan Alhaji idrisa na aljanune, kuma ba shakka su suka kashe shi,  kuma daman sai da akace ma alhjy karyasa asare don dadewar bishiyoyin , yace shi sam bai san da wasu haittu aljanu ba,  kuma koda akwaisu badai a gidansa ba"
bayan mutuwan gimbiya sameeratu da sati daya, nawwara ta tsinta wannan zoben gimbiya akofar dakinta, taji yabata sha'awa tasaka a hannunta, ya mata kyau sosai.
        suko can duniyar  aljanu sun kudirta aniyan raba alhaji idrisa da farin cikin shi kasan cewa Allah ya daura mai son nawwara, gashi yarinyar akwaita da haddan alqur'ani akanta,tana zuwa  islamiya sosai.
         tun lokacin data sa zoben nan taji kamar bata da lafiya, kuma tayi rauni akaratunta, tun mahaifiyarta namata fada har tagaji takyaleta, ikon Allah kuma babu wanda ya ta6a lura da zoben hannun ta.

akwai wata rana taje islamiya taji sam takasa zaman ajin duk ranta abace yake kuma tarasa dalili' tashi tayi tafita waje tasamu wuri ta zauna' me zai faru kawai sai jitayi ance sameeratun nawwara kitaho gareni zan yaye maki damuwarki' zan baki duk wata kulawa data dace ke tamuce har abada, a tsorace take waige² bataga kowa ba"  mikewar dazatayi saiga___?
.
        Mikewar dazatayi  saiga maciji yayi saurin bi ta kafafunta, tasaki wani uban ihu tare da sumewa kasa , nan take yan makaranta suka rufa mata, aka kira mallamin su, yasa yan ajin sanawiya su dauke ta sukaita aji.

yasa aka kawo mai ruwa a kofi yayi addu'oi aciki ya watsa mata fuska, a firgice  ta farka tana cewa gasunan suna kirana, wayyo Allah zasu..... mallam yayi saurin cewa suwaye ke kiranki nawwara?
kasa magana tayi ta tafi suuu zata fadi aka tare ta, shugaban makarantar ne yazo, yace yana ganin alamar jinnu ne ajikin yarinyar nan"   ayimata  ruqiya  agani idan aljanun ne za'a gane" mallamin su yace hakane don nima nayi tunanin haka.
nan aka shiga yiwa sameeratun nawwara ruqiya , nanda nan aljanun suka bayyana   ajikinta, alokacin ambar ne ajikinta, abisa umurnin mahaifinsa dayace  yasoma bayyana gareta " don ya isar musu sakon dasuke dashi.
mallam yace kai waye' kuma me kuke nema awajen wannan baiwar Allah'n, me tamuku  kukeson cutar da ita?  shuru ambar yayi' mlm yace zakuyi mgn kosai na kona ku da ayar Allah, cikin wani irin murya da babu dad'inji ambar yafara magana "" yace mallam kar ka kona mu zamu fita dama sakone muke son isarwa ga  mahaifinta" kiransa zakayi mufad'a masa ko kai zamu barwa sakon ka isar gareshi!"
.
mallam yaga idan yace akira mahaifin nawwara ana iya d'aukar lokaci, ga yarinyar nabuk'atar taimakon gaggawa" tunda sunce zasu iya bada sakon aba mahaifinta ai shikenan'  yace wace irin sako ne! kafad'a zamu isar zuwa gareshi"
ambar yayi wata irin dariya tukum sannan yace ciki tsawa  mallam muna so afadama mahaifita zamu dauke sameeratun nawwara zuwa duniyarmu......
.
mallam yace wa'iyazu billah meyasa zaku aikata wannan mummunan abun, ambar yace sbd mahaifinta yaraba mu da farin cikinmu, saboda haka muma zamu rabashi da farin cikinsa ta hanyar d'auke  y'ar wacce yafi so aduniya"  daman  kuma tamuce.
mallam yace menene wannan abun daya rabaku dashi!, ambar yace yasa ansare bishiyoyin dake gdansa batare daya sanar  mana ba, balle mu kwashi muhimman ajiyarmu'  kuma alokacin gimbiyarmu me suna sameeratu, tana kwance akan gadon hutawarta  abun ya afka da ita'  da sauran yan uwan mu, saboda haka baza mu yarda ba, muna so a Isar masa da wannan sakon" mun sassauta hukuncinmu akansa ne sbd sonda muke ma nawwara" badan hakaba damun dad'e da d'aukar mummunar fansa akansa"
kafin mallam yace wani abu har yafita daga jikinta , ita kuma sai tari take aka bata ruwan addu'a tasha sai bacci ya dauketa.
Bayan kwana daya da faruwan haka shugaban makarantansu  da mallamin ajin na su suka je gdan Alhaji idrisa , bayan sun gaisa ne suke bayyana mishi abunda ke faruwa, yace sam shi bayyarda da wasu aljanu ba, yar shi kuma bazai wuce maleria bane ke damunta,  ai wannan ma tatsuniya ce, aljanun banxa aljanun hufi,  duk wannan ta tsuniyace, da karyan yara, mallam yace a'a Alhaji, kar kamanta fa Allah da kansa yana fad'a acinkin alqur'ani cewa ( *wama khalakatul jinna wal insa illa liya'a budun* _bamu halicci mutane da aljanu ba face dan su bauta mani_ )
.
Ashe kuwa kaga aljanu gskya ne,  su suna ganin mu amman mu bama ganin su,   kuma maganan gsky sare bishiyan nan da kayi batare da kasan matakan daya dace kayiba kafin hakan akwai matsala, sannan kasan  bishiyoyinnan sunyi sama da shekara  talatin da y'an doriya ba asare su ba sai yanxu? kaima kasan dole asamu matsala,
zaman lafiyarka da iyalinka shine kabasu hakuri, inba haka ba, watarana zakayi kuka da idanun ka, don bakasan kaidin aljanu bane shiyasa, muna kara baka shawara da kabasu hakuri kawai" dan tsira da iyalanka"
, Alhaji idrisa mutum ne mai taurin kai da kafiya akan ra'ayinsa, da kuma karyata aljanu, ya tashi cikin fushi yace mallam dan Allah kutashi kutafi sun dad'e basu dauke ta dinba makaryata kawai, cikin fushi suma suka bar gdan.
aljanun sunji duk abunda Alhaji idrisa yace, kuma sun dau alwashin sai sun dauke sameeratun nawwara, duk ranar da taje islamiya sai suntashi mata kuma sai sunkara fada zasu sace ta.

Ranar jumma'a sameeratun nawwara taci kwalliya  zataje gdan yayar babanta ta gaidata daganan ta wuce shagon dinkin su"" dayake tana koyan dinki, bayan taje gdan goggon nata ta wuce shagon su,   kawar tace  khadija tace kin makara nawwara yau nariga ki zuwa , nawwara tayi murmushi" tace  wlh nabiya gdan goggona ne, Ayya ke kadai ce ashagon ina aunty marry, khadija tace taje kasuwa ,ok, nan sukaci gaba da hirar su har la' asar tayi,  nawwara tace Khadija bara nashiga gdansu baba rabi nayi sallah tunda ke kina fashin sallah, tace to fad'awa duniya bana sallah yau takarashe fad'a tana dariya, nawwara tayi dariya.
.
ta kama hanyar zuwa gdan kenan sai ga wani guguwar iska yataso ya dumfaro nawwara, kiyara ce tazo ta dauke ta, tun daga lokacin nawwara bata sake sanin ita wacece ba, kawai ta ganta ne aduniyar aljanu , duk sun tsafeta da abubuwan su tazama irinsu, amma kuma kana ganin nawwara sai kace ruwa biyu ce, wato aljana da mutum, haka takoma"" wannan zoben dake hannunta  shi yakara bata duk wani karfin tsafi, shiyasa tazama kamar aljana, amma kuma akwai wajajen dabaza ta iya zuwa ba aduniyar aljanu, kasan cewarta ita ba asalin aljanar bace.
  
in baku manta ba ko wajan da aka daure ni bata karasa daku ba sai da kafa fuwanku kuka karasa, sbd batada   karfin isacan,   da sunyi niyyan kasheta ne sai ambar yace yana sonta , acan kuma duniyar bil adama, khadija tajiki shiru baki dawo ba.
nan aka bazama neman nawwara lbrin batanta yazagaye ko ina, har makarantar islamiyar su, mallaman su sunyi takaicin haka'  shiko mahaifinta kamar zaiyi hauka, yana cewa karya kuke kud'auke min yarinya ta, yayi ta sambatu yana tsine musu, abu wasa² har anfidda tsammanin ganinki, kowa ya dangana anmik'ama Allah lamuransa"
sai bayan batanki ne mahaifinki yafara daya sani sai alokacin mahaifinki yayarda da akwai aljanu, shi sam daya karyata aljanu, yana ganin duk karya ne, damuwa tamasa yawa' wanda hakan ya kwanta ciwo na tsawon shekaru biyu sannan y warke duk yan uwanki sun dangana.
ke kuma kina can kina rayuwa da aljanu, sun gusar miki da kwakwalwa, wannan shine abunda ya faru deke nawwara, awwal saida ya zubda hawaye , nawwar yace wai meyasa mutane ke son karyata aljanu, bayan kuma Allah yafada, da akwai, acikin aljanun ma akwai masu bauta mai, kamar yadda akwai amutane akwai musulmai a kwai kafurai, sameeratu dake zaune tazuba musu ido tarasa meke mata yawo a kwakwal warta.
nawwar yace to meza ayi mata ta dawo yadda take cikakkiyar mutum,ameenatu bin saifullah tace kunga wannan zoben dake hannunta za'ayi kokarin cireshi, sannan kuma sauran aikin malllam ne yasan yadda za'ayi.
mallam ne yayi magana yace nawwara ba ita kadai bace akwai gimbiya sameeratu ajikinta kuma  karya wayannan asiren dake jikinta bakaramin aiki bane, zamuje da ita Maiduguri, don nikadai bazan iyaba , bai gama rufe bakinshi ba sukaji  gdan y girgiza yayin da nawwara ta xube kasa wani bakin abu nafita Daga bakinta,duk kan su suka nufo kanta cikin tsoro wutan dakin ya dauke ko ina bakin kirin.

0 comments:

Post a Comment