Wednesday, 28 February 2018

AUTAR HAJIYA Page 41-50

AUTA HAJIYA Page 41-50
.
Da sallama Fadila ta shiga gidan, falo ta tarar da momynta tana zaune hannunta rike da (newspaper) jarida tana dubawa,
Cikin fara'a ta kalli Fadila ta amsa mata sallama, dai-dai lokacin Fadila ta tsinci kanta da tinanin yanzu idan momynta ta tambayeta meya kawota me zatace,
Muryar momynta ta katse mata tinanin datake,
      "Ina me gidan naki na ganki ke kad'ai? Fadila tayi saurin dawowa daga tinanin datake ta kalli momynta tayi murmushi, dan bataso ta gane tana tattare da wata damuwa, tace "shine ya saukeni yana sauri ne yanada meeting a office d'insu shine ya wuce, yace idan yadawo d'aukata ze shigo, Momy tace "owk"
Sukayi shiru na 'yan wasu mintittika, Fadila kuwa tunani tashiga yi, a zuciyarta tana cewa:
*_Yanzu wannan 'karyar danayi idan khaleed ya'ki biyoni ya zanyi, kokuma idan yazo yace bada izininshi na fito  ba , Allah dai yasa ya rufa min asiri_*
"Fadila lafiya naga kinyi shiru kamar kina tunanin wani abu, kodai akwai abinda ke damunki ne?
     Da sauri Fadila ta washe ta tashi tana murmushi tace "lah ba kome Momy, tanufi hanyar kitchen tana fad'in me kuka dafa wlh yunwa nakeji,
Bata jira amsar Momy ba tashige kitchen tazubo tuwon shinkafa da miyar d'anyar ku6ewa, sannan ta d'auko lemu a pridge ta dawo falo ta zauna tafara ci, Momy kuwa kallonta kawai take azuciyarta tace *Anya Fadila*
"Fadila yanaga kinatacin abinci haka kamar wacce ta kwana bataciba?
Fadila tayi saurin kai dubanta ga momynta tace " banci abinciba na fito saboda ina d'okin ganinki Momy, tafad'a tana murmushi,
Itama Momyn murmushin kawai tayimata tacigaba da duba jaridar dake hannunta.
Har misalin 'karfe shidda da rabi na yamma khaleed bezo d'aukar fadila ba, momy ta kalleta tace "khaleed shuru kodai ya manta dake ne,
Fadila taji gabanta yafad'i tace "a'a Momy yana zuwa, inaga har yanzu begama abinda yake bane.
Fadila tashiga damuwa hankalinta yafara tashi ganin har angama sallar magrib amma khaleed bezo d'aukar taba, gashi bataso dadynta ya tarar da ita  kuma tasan ana gama sallar isha'i ze dawon gidan.
Karar tsayuwar motarahi ce ta dawo da ita daga dogon tinanin datakeyi,
Da sallama ya shigo gidan, Momy ta amsa tare da yimashi sannu da zuwa, falo akayimashi masauki, bayan sun gaisa ya kalli fadila wacce dama on ready tagama shirin tafiya zuwanshi kawai take jira, yace "ki taso muje ko kinga dare yafara,
Wani sanyi fadila taji cikin zuciyarta, da khaleed be fad'i dalilin tahowarta ba.
Haka suka bar gidan, Fadila, nata godema Allah daya rufa mata asiri, dan yau da Momy tasan da yanda ta taho gida da ranta idan yayi dubu sai ya 6aci.
Haka suka shiga mota suka d'au hanya, tinda suka fara tafiya ba Wanda yacema d'an uwansa kome har suka isa gida.
Koda fadila tafito daga motar kasa shiga tayi gidan saida tajira khaleed sannan suka shiga tare,
Falo suka iske Auta zaune kan kujera, sanye take da wata riga me hannun bes da wani d'an 'karamin siket iya gwiwa, hannunta ri'ke da remote tana canja tasha zuwa *ZEE CINEMA*  dayake ita meson kallon Indian film ce, kanta babu ko d'an kwali gashin nan ya zubo 'kan kafad'unta, cike da murna ta taso ta rugume khaleed, "sannu da zuwa mijina, murmushi yayi tare da bata kiss a kumatu yace "yauwa matata.
Fadila kuwa tana tsaye tana kallon ikon Allah, sai lokacin Auta ta kalleta tace "Andawo lafiya,
Bata amsa mataba illah wata uwar harara data buga mata sannan taja dogon tsaki "mtswwwww ta wuce d'akinta.
Khaleed ma d'akinsa ya wuce,
Auta kuwa dariya tayi, dan ganin tagama 'kule fadila, ta koma ta zauna taci gaba da kallonta, canja tasha tayi zuwa *STmusic* aiko ta iske an sanyo wa'kar *justing viiver* cikin wa'karshi me taken _(Love me love, kiss me kiss me)_ dama tana masifar son wa'kar duk ta iya ta, saboda haka taciga da bi, tana 'yar rawa daga inda take zaune.
Lokacin Fadila tafito daga d'akinta tanufi kitchen, ta kai dubanta ga Auta wacce tayi kamar batasan da mutum a falon ba, wani 'kululun ba'kin ciki ya tsaya mata tayi tsaki Mtsww "Aykin banza tafad'a sannan tawuce kitchen din.
.
 Washe gari, Fadila tagama had'a musu break fast, kunun gyada ne ta she'ka musu, yayi gwanin kyau, dan ta masifar iya kunun gyad'a dan duk cikin abinda take girkawa a gidan shi kad'ai ne takeyi susha cikin kwanciyar hankali, kuma wani lokaci har khaleed ya yaba.
Yauma shine ta she'ka masu, tare da soya masu dankakali da kwai, bayan tagama ta jera kome kan dinning ta koma d'aki dan yin wanka.
Auta kuwa dayake ba itabace meyin girkin tuni ta dad'e da yin wankanta ta shirya cikin Riga da siket na material tayi kyau sosai.
Tana jin shigewar Fadila d'aki, sai tafito tana tafiya ahankali, sad'af-sad'af yanda ba Wanda ze iya jiyo 'karar takun ta, hannunta ri'ke da wani 'karamin cup, dining tanufa inda fadila tagama jera kayan break fast d'insu, ta bud'e, plask d'in dake d'auke da kunun gyad'a wanda yaji peak milk yayi fari 'kar, ta zuba abinda ke hannunta cikin cup, ta d'aga plask din tad'an jijjiga yanda ze gauraye kada a gane anzuba wani abu daga baya, tayi saurin komawa d'akinta.
Zazzaune suke kan dinning kowane da cup me d'auke da kunun gyad'a a gabansa, dankalin da kwai suka fara ci saboda kunun akwai zafi,
Khaleed ne yafara d'aukar cup din gabansa yakai baki, dan yana sauri yafita aiki dan yau yanada patient's dayawa a hospital,
Wani irin d'and'ano yaji na daban, cikin kunun Wanda ko a mafarkin baya tinanin jinsa cikin kunun,
.
Cike da 6acin rai ya kalli Fadila, ya daka mata harara tare da Jan wani irin dogon tsaki "Mtswww,
Fadila bata kai ga fara shan kununba saboda haka batasan yanda testing d'insa yakeba, cike da 6acin rai tatashi tafara magana tana d'aga murya "gaskiya khaleed nagaji da cin mutunci da cin zarafi dakakemin cikin gidannan, shikenan ni kullum nice abin wula'kantawa dan kana ganin wannan kod'dad'iyar yarinyar tare da kai.....
Kafin ta ida rufe baki, sai jin abu tayi ajikinta, wata irin 'kara ta saki dan kunun yanada sauran zafi, zuciya takai khaleed ya watsa mata shi, cike da masifa yatashi yana cewa "ke har kinada bakin dazakice anyi maki rashin adalci, kenan adalcinne yasa zaki zambad'a mamu uwar kanwa cikin kunu, wannan kanwar da kika zabga ko kunun kanwa aka zubamawa baze shawuba, barantana kunun gyad'a wanda beda had'i da kanwa.
Sai lokacin Auta tayi magana, tace kayi ha'kuri mijina, kayimata uzuri, wata 'kila da kunun kanwa zatayimana, kasan shima yanada dad'i sosai.
Bebi takansuba suduka, cike da 6acin rai ya d'auki makullin motarsa yafita,
Har yabar falon Fadila na tsaye gurin kamar an dasata, ba abinda take sai zubar da hawaye,
Auta ta tashi ta kalli fadila, datayi tsaye da kunu ajiki, har ga Allah tabata tausayi, amma kuma koma miye ita ta fara,
Dariya tayi, tace *"Kije ki wanke*, tashige daki tana cigaba da dariyarta, har Fadila na jiyo sautin dariyar.
Haka Fadila ta tattare rigar tanufi d'akinta, tacire, sannan tafad'a toilet ta sakarma kanta showar, bayan ta gama wankan ta dad'e toilet tana kuka.
Bayan tagama wanka ta sake shafa lotion me dad'in 'kamshi, ta saka wasu kaya.
Auta kuwa tana d'akinta ta kwanta ruf da ciki kan gado, tana danne-danne cikin wayarta, kawai jitayi kamar alamar mutum a kanta, da sauri ta d'ago takai dubanta kan Fadila wacce ke tsaye tana cika tana batsewa.
.
Take wani irin mugun tsoro yakama Auta,dan ganin Fadila yau har cikin bedroom d'inta, tasan idan za'a barta da Fadeela sai dai taci na jaki.
*_innalillahi'wa,inna'ilaijirraji'un_* tashiga furtawa duk illahirin jikinta kyarma yake, gashi ba kowa gidan daga ita sai Fadila.
```Su Auta anbani ga tsoro ga jan fad'a  nidai zee barin gidan nayi dan bazan raba wannan fad'an ba, tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan doka``` 
.
 Tafiya yake a mota amma zuciyarsa cunkushe da tinani kala-kala, saida yakusa kaiwa asibiti, ya tuna da ya manta wasu muhimman takardu wanda yau ne yakamata yaje dasu,
    Juya akalar motar yayi, ya koma gida, me gadi yatashi da Sauri ze bud'e mashi get, amma sai ya tsaidashi, yace" kabarsa kawai zan ajiye anan dama wata yar mantuwa nayi zanshiga na d'auko, me gadi ya russuna yace "to ranka ya dad'e.
Shiru ya iske falon alamar matan gidan kowace na 'dakinta, sallama yayi sannan yashiga, d'akinsa ya wuce kai tsaye,
Auta kuwa tana kan gado ido ya raina fata, ga fadila na tsaye bata dai tankamata ba, kuma batada niyyar barin d'akin,
Cikin sa'a Auta tajiyo sallamar khaleed a falo, wanda ko kad'an fadila bata jiba, kodan tana cikin 6acin raine, oho Saukowa tayi daga kan gado, tazo gaban fadila ta kama wuyan rigarta tacimata kwala, sannan ta kwanta kasa ta fasa ihu tana cewa "dan Allah kiyi hakuri, wayyo nashiga ukku zata kasheni, menayimaki zaki kama dukana, wayyo Hajiya kizo zata kasheni, iya karfinta take maganar cikin murayar kuka tana kuma buga 'kafarta jikin gado da bedside, sannan kuma takama wuyan rigar fadila ta ri'ke sosai, hakan yasa dole fadilar ta duko yanda idan kagani sai kace dukanta takeyi da gaske.
.
Fadila kuwa mamaki ne yagama rufeta, tanata kokarin 6am-6are wuyar rigarta daga hannun Auta amma ta kasa, saboda Auta ba 'karamin ri'ko tayi mataba.
Khaleed na d'akinsa yana tattara takardun dayazo nema, yajiyo ihun Auta tana Neman taimako, aiko da hanzari yanufi d'akinta dan ganin abinda ke faruwa.
Fadila yagani duke kan Auta, itakuma tana kwance 'kasa tana Neman taimako, da sauri ya Isa gurin ya jawo fadila da iya karfinsa, wadda ganinsa yasa Auta tasaketa daga sha'karar datayimata,
Wani lafiyayyen mari ya d'auketa dashi, Fadila tayi saurin dafe gurin daya mareta, zatayi magana ya'kara d'auketa da wani lafiyayyen mari, yana huci yace "bakida hankali fad'ila zaki kama 'yar muatne da duka haka, so kike ki kasheta.
Lokacin kuma Auta ta tashi daga Inda take kwance tayi wujiga-wujiga, fuskar nan sharkaf da hawaye, idan ka ganta saika rantse kace mugun duka akayi mata.
Fad'awa tayi jikin khaleed tana kuka, shikuma ya rungumeta yana rarrashinta kamar wata yarinyar goye, sannan ya maida dubansa ga Fadila wacce ta dafe kunci tana zubar da hawayen takaici,
Yafara bal-baleta da masifa, ta inda yake shiga batanan yake fitaba, iya tsawon rayuwar Fadila bata ta6a sanin khaleed nada fad'a haka ba sai yau.
Bayan yagama zazzagamata bala'i sannan ya nuna mata Kofa yace *(Get out)* ki fita nace daga d'akinnan tin kafin inyimaki mugun bugun dazaki kasa tashi, sha-sha-sha wacce batasan girmantaba, in banda sakarci me zaki daka jikin Zainab,
   Ki duba girmaki ki duba nata, kin kai biyunta,
   duk maganar nan dayake Auta na rungume jikinsa tana kukan shagwa6a.
Haka fadila tabar d'akin cike da takaici, tana mamakin yanda Auta ta Jamata sharri cikin 'kan'kanin lokaci.
.
Babban falo ta zauna tana sharar hawayen ba'kin ciki,
Kusan kimanin minti talatin Fadila na zaune falo tana kuka, sannan khaleed yafito shida Auta,yana mata magana wacce fadila batajin me suke cewa amma dai taga Auta na dariya hadda kyalkyatawa,
Saida sukazo gab da ita khaleed ya kalleta ya buga mata wata uwar harara, yace "gatanan zan tafi gurin ayki, idan kin isa' kin haihu ga iyayenki, kuma kin isa marar mutunci to in dawo in iske gawar Auta a gidannan, yabuga wani dogon tsaki "mtswwww sannan ya wuce, tare da ba Auta lafiyayyen kiss a kumatu yace saina dawo matata, *(Tak care of your self)* ki kulamin da kanki, wani lafiyayyen murmushi tayi mashi tace *(never mind my husband)* karka damu mijina.
Haka tarakashi har bakin get saida taji 'karar tashin motarshi Alamar yatafi, Sannan takama hanyar komawa cikin gidan.
Saida tazo 'kofar shiga falon tatsaya tana tinani,
"{```Yanzu idan nashiga Fadila takamani ba abinda ze hana ta rama marin da nasa akayimata, me sau'ki kenan idan batayimin d'an banzan duka ba}```
Tsayawa tayi tana shawarar yanda zata shiga d'akin, ga kuma fadila zaune.
Ta dade nan tsaye kafin ta yanke shawarar ta wuce d'akinta da gudu kada tabari Fadila ta kamata.
Haka kuwa akayi da gudu, tashigo falon da niyyar ta wuce d'akinta ta kulle kanta, bazata fitoba sai khaleed ya dawo, amma ina, tariga ta makara, dan ko kusa da 'kofar d'akin bata kaiba Fadila ta dam'kota.
.

 Auta tagama tsorata da yanda Fadila ta dam'kota, tanayimata wani mugun kallo,
Lokaci guda 'yan cikinta suka  motsa saboda tsoro, harta hangoma kanta irin dukan dazatci gurin Fadila.
Amma a fili saita nuna dakewa, ta kalli Fadila Alamar ba tsoro ko 'kadan a tartare da ita, tace "dallah malama sakeni, kin wani kamani kin ri'ke ko nayimaki satane, tafad'a tana wani hararta.
Wani guntun murmushi fadila tayi mai d'auke da takaici, ta kama hannun Auta ta kaita kan kujera ta zaunar da ita, sannan itama ta zauna kusa da ita, ta kalleta tace "Yanzu Auta abinda kakayimani kin kyauta, ki duba kiga yanda kika shiga tsakanina da mijina, menayimaki dazaki saka mani da wannan,
Wani sanyi Auta taji cikin zuciyarta, dataga Fadila bata nemeta da fad'aba, danko da dafarko tafara tinanin yanda zasu kwashe, amma sai taga Alamun Fadila na Neman sulhu ne.
Har cikin ranta taji tausayin Fadila, yakamata, dan ita dama tincan mutum ce mai matu'kar tausayi.
Cikin sanyin murya Auta tafara magana, "ni dama ba da niyyar wani Abu nayiba, naga kin shigone kamar zaki dakeni, nikuma kinga dole in nemarma kaina mafita.
Fadila tayi wata nannauyar ajiyar zuciya, cikin Zuciyarta tace
```{"Da kinsan abinda nazo dashi lokacin da baki sakamin da abinda kikayimaniba}```
  
"Koda kikaga na shigo ba da niyyar tashin hakali Nazo ba, nazo ne kawai muyi magana.
Auta tace "To ayni bansaniba, da saikiyimin sallama kafin ki shigo, tunda naga kin shigo ba sallama sai inyi tunanin ba arzi'ki yakawokiba,
"Amma kiyi hakuri, tafad'a tare da juyar da fuskarta gefe, tana wani turo baki.
Fadila ta 'kara zama tare da matsowa kusa da Auta, Auta tad'an matsa, dan ita har yanzu da d'an sauran tsoro tattare da ita, gani take fadila nada wata manufa cikin zuciyarta
Fadila tace "Amma miye yasa kike 6atamin duk wani abu dana dafa, a gidannan?
Auta ta turo baki tace "to ay ke kikafara, dan rannan da kaina na kamaki, kina zubamin gishiri a binci, kawai kyaleki nayi a lokacin, idan bazaki manta ranar danayi sakwara da miyar agushi.
Fadila tayi murmushin takaici, mai cike da nadamar abinda ta aikata tun farko,
*_(Dama ance farau batada zafi sai ramau)_*
"To yanzu dai nazo neman sulhu, yakamata mubar duk wannan abun damukeyi, kinga bekamata ace mun zauna muna yima kanmu abunda be daceba.
Auta tace  "ni dama ban d'auki abun da zafi ba, kawai dai kinsan hausawa sunce _*"Ramuwar gayya tafi gayya zafi*_
Amma kome ya wuce Allah shige mana gaba, Fadila ta Amsa da "Ameen.
*```To you my namesy Autar Hajiay```*
_ina mi'ka gaisuwa ga masoya a duk inda kuke_
~kibiyo *Zee Mmn khady* akwai sauran labari~
.
 koda Hajiya ta farfad'o daga dogon suman datayi, doctor ya'kara dubata ya tabbatar da lafiyarta, sannan yace za'a iya tafiya da ita, amma ari'ka kula da kiyaye abinda ze jefata cikin tashin hankali.
Daga asibitin gidan khaleed aka wuce da ita kai tsaye, dan an riga an wuce da gawar a can.
Cikin likaffaninsu ta iskesu, hankalinta yayi matu'kar tashi, ta fashe da wani sabon kuka,  tana cewa.
*shikenan zainab kin tafi kin barni bayan kinsan banida wani d'a ko d'iya sai ke, Allah kai ka bani zainab kuma kai ka kwace abinka badan baka sonta ba, ya Allah ka ji'kan zainab ka kai haske cikin kabarinta*
Haka tacigaba da kuka tanayima Auta addu'a nan mutane aka shiga rarrashinta ana kwantar mata da hankali.
A asibiti kuma momyn khaleed da momyn Fadila sunacan suna jiran abasu dama su shiga su duba me jego da babynta,
sai bayan magrib aka basu izinin Shiga,
Haka suka shiga jikinsu ba 'kwari ko kad'an,
Zaune take kan gado, ga baby gefenta, kuka take kamar zata fitar da ranta, idanunta sun kumbura fuskarta tayi ja, tayi face-face da hawaye, jin motsin shigowar mutane yasa ta d'ago da fuskarta wadda ruwan hawaye yagama wankewa, takai dubanta garesu.
Momyn fadila itace gaba, tana zumud'in ganin fadila da babynta,
```Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un```
Ta faurta lokacin da idanunta suka sauka kan Auta, Zaune kan gado ga babynta kusa da ita.
Momyn khaleed ce ta dafe, 'kirji Alamar mamaki tace
*"Auta dama ba ke bace aka cemana kin mutu ba*
.Auta ta fashe da wani sabon kuka, tana cewa, Momy fadila.....fadila.... ce tatafi ta barni, wani sabon kuka ya kwace mata.
.
Momyn fadila najin haka tanemi numfashinta ta rasa, nan tafa'di sumammiya, Momyn khaleed tarud'e da ganin yanda 'yar'uwarta ta suma,
Da sauri ta ebo ruwa ta yayafa mata, nan ta farfad'o,
Zaunar da ita Momyn khaleed tayi tana rarrashinta, tana gaya mata, irin Rahamar da Wanda yamutu gurin haihuwa yake samu, tace "kawai yanzu Addu'a Fadila take nema garemu ba kuka ba.
Wani sabon kuka Momyn Fadila ta fashe dashi, dan rarrashinma da akemata jitake kamar ana zuba mata garwashin wuta cikin zuciyarta, shiru suka d'anyi nawasu yan mintittika, bakajin kome sai sheshshekar kukan Auta, Momyn khaleed ta maida hankalinta kan Auta tana rarraahinta, sai jin fad'uwar Momyn Fadila tayi,
A hanzarce tajuyo gareta, tarin'ka jijjigata tana kiran sunanta, amma ina ba maganar lumfashi tattare da ita, cikin tsananin rud'ewa momyn khaleed tafita tana Neman taimako, wasu leburori ne mata suka taimaka mata, suka d'ora momyn Fadila kan gadon da ake tura marassa lafiya aka nufi Emergency da ita, nan fa lokitoci suka taru anata Abu d'aya amma numfashi ko Alamarsa babu jikin momym Fadila, amma kuma da an Auna sai aga zuciyarta na bugawa Alamar akwai rai tattare da ita.
Oxygen aka sanya mata *(Abin jawo numfashi)*
Sai lokacin Momyn khaleed ta buga waya ta sanar da daddyn fadila halin da ake ciki, aiko cikin tsananin rud'ewa ya iso asibitin, dan shima yayi tinanin Auta ce ta rasu amma yanzu ance Fadila ce
d'iyarshi wacce yakeso, wasu guntayen hawaye suka zubo daga idonshi, yasa hannu ya goge.
Sai 'karfe hud'u na asuba Momyn Fadila ta farafad'o, da misalin 'karfe takwas doctor yabata sallama dan ganin jikin nata da sau'ki sosai.
Lokacin kuma aka sallami Auta, bayan likitan ya tabbatar da lafiyarta data babynta.
'Karfe tara dai-dai suka isa gida, lokacin an fito da gawar Fadila data babynta,
Aiko da gudu Auta ta fito daga motar, tana goye da babynta, yayinda momyn khaleed ke goye da 'diyar da fadila ta bari.
.
Bata ko kalli yawan mutanen dake gurinba tabi tacikinsu ta isa gaban makarar ta ri'ke tana cewa ```Wayyo sister fadila kada ki tafi ki barni, fadila ki dawo mu zauna mucigaba da gina rayuwarmu yanda muka tsara.... Fadila kin manta munce zamu rike yaranmu mu had'a kawunansu su tashi tsin-tsiya mad'aurinki daya, wayyo sister fadila ki dawo garemu....```  haka tayita surutai tana kuka, nan aka kakkamata ana bata ha'kuri aka shige da ita cikin gida,
Hajiya tana cikin gida tanajin hayaniya daga waje, sai kunnuwanta suka ri'ka jiyo mata kamar muryar Autar ta, amma saita share tacigaba da istigifari tana nemar ma Auta rahamar ubangiji, dan tariga tasan Auta ta mutu kuma Wanda yamutu baya dawowa.
Da sauri ta taso dan ganin anshigo da Auta tana kuka, wasu mata sun rirrekata,
Cike da mamaki ta isa gareta tace Auta dama bake bace kika mutu, bata bata amsaba sai wasu zafafan hawaye dasuka 'kara ganagarowa daga idanunta.
Hajiya batasan lokacin data rugume Auta ba tana wani irin kuka me wuyar fassara, na farin cikine kona ba'kin ciki.
Da misalin 'karfe sha d'aya yan kai gawa suka dawo, Allahu Akbar ankai Fadila makwancinta.
Lokacin Kuma akayi addu'a aka shafa, gidan yayi tsit bakajin kome sai sheshshekar kukan mutane 'kasa-'kasa.

0 comments:

Post a Comment