Wednesday, 28 February 2018

AUTAR HAJIYA Page 31-40

AUTAR HAJIYA Page 31-40
.
A firgice Fadila ta farka daga baccin datakeyi da niyyar zuwa falo dan kada  khaleed ya dawo ya wuce d'akin Auta bata saniba.
Innalillahiwa'ainna,ilaihirraji'un tafad'a tare da saurin le'kewa ta windon d'akinta dan tabbatar ma idonta abinda ta gani gaskiya ne,
.
      Hasken ranar daya haske idonta shine ya tabbatar mata da cewa tabbas ba mafarki takeba, safiya tayi, da sauri ta fita zuwa d'akin khaleed dan taga nan ya kwana ko kuwa, tana zuwa ta tura 'kofar d'akin tashiga taga ba kowa aciki, kuma babu Alamar mutum ya kwana aciki.
Take wani irin kishi ya turni'keta, "shikenan abinda ta kwana ukku tahana idonta bacci sabodashi yariga ya afku, jitayi 'kafafunta sun kasa d'aukarta, batasan lokacin data sulale 'kasan d'akinba kan tiles tayi zaman dirshan tana zubar da wasu zafafan hawaye, a zuciyarta take cewa:
*_(Shikenan khaleed ka cuceni ka gama sanyawa yarinyar nan ta rainani, shikenan khaleed ka fito fili ka nuna kafi son Auta a kaina, )_*
Shiru tayi na kimanin minti goma tana tunani, tana sa'ke-sa'ke a zuciyarta, zuwa can sai tayi wani shu'umin murmushi, tace
.
*~Hmm Auta idan Kin san wata baki san wata ba "Hmm dani kike magana~*
: Tashi tayi daga zaman takaicin datake, tanufi d'akinta tafad'a toilet tayi wanka sannan ta d'auro Alwala ta kabbara sallah lokacin har karfe bakwai da minti sha shidda na safiya, bayan ta idar da sallar ta wuce gaban dressing mirror ta 6ata lokaci gurin gyara fuskarta, sannan ta sharce gashinta wanda koda yaushe yake a 'kone, ta d'aure shi tsakiyar kai, bayan tagama wannan wadrop tanufa wasu Riga da siket na atamfa ta d'auko d'inkin zamani ta sanya ajikinta, kayan sun matu'kar zama ajikinta, dan ba 'karamin kyau sukayimata ba, sannan ta d'auko manyan turarrukanta masu dad'in 'kamshi ta feshi jikinta dasu, bayan humra data rin'ka mungulawa ajikinta.
 
Lokaci guda kuwa 'kamshinta ya mamaye dakin,
   Tana cikin d'aura d'an kwali ne khaleed yashigo d'akin da sallama, sanye yake cikin farar shadda d'inkin zamani, bayan ta amsa sallamar ta juyo ta kalleshi, tayi mashi wani tattausan murmushi tace "Barka da fitowa my man, wani irin dad'i yaji ya ratsashi har cikin zuciyarsa, dan yayi tunanin Fadila zata tada hankalinta ne idan gari ya waye ta tabbatar da d'akin Auta ya kwana, shima wani murmushi ya sakar mata, har cikin ranshi yaji dad'in yanda ta tarbeshi, ga kwalliyarta ta masifar yimata kyau, lokaci guda yaji ta matu'kar burgeshi, take kuma yaji wani sabon sonta ya shiga zuciyarshi.
Ahankali ya 'karaso inda take yayi mata wata kya'ky'kyawar runguma, sannan yabata kiss a kumatu yace "Gud morning my special wife, har cikin ranta taji dad'in kalamansa, itama ta mayar masa da nata sakon kiss d'in a lips, tace "morning my man.
Auta kuwa koda ta tashi kitchen tafad'a dan had'a musu break fast,
    Cikin k'ank'anin lokaci tagama had'a kome na break ta jera kan dining table, sannan takoma d'akinta ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta tsaya gaban dressing mirror tayi simple make-up sannan ta nufi Wadrope ta d'auko wasu English wear riga da siket, siket d'in farine har 'kasa, amma ya kameta daga sama, sannan k'asan ya bada fad'i, jikinsa akwai kwaliyya flowers da copee zare, sai rigar copee colour, tasha ado da duwatsu daga gabanta, rigar batada hannu, sai wani siriri kamar na bes, bayan tasanya kayan sun matu'kar yimata kyau, wani 'karamin farin gyale ta d'auko tayi rolling din kanta, sai ta ida fitowa balarabiya sak.

.
 Zaune suke kan dining suna break, kowanensu ci yake yana jin dad'in abin, dan kuwa Auta ba daga baya ba gurin iya girki, ita kanta Fadila ta jinjina ma Auta a zuciyarta, dan ko a hotel abinci baze wuce wannan dad'i ba.
Bayan sun gama ne khaleed yafara magana "Amma gaskiya naji dad'in yanda kuka dawo yanzu, kungane wannan rigimar ba abinyi bace, saboda haka inaso inyi amfani da wannan dama inyimaku nasiha akan dan Allah ku had'e kawunanku ku zauna lafiya, ba cuta ba cutarwa, domin zamanku lafiya shine kwanciyar hankalina.
Sannan ya kalli Fadila, yace "kinga Fadila jiya na kwana d'akin Auta, to gobema zan kwana d'akinta kinga kwana biyu kenan, daga lokacin kuma zan dawo d'akinki inyi kwana biyu.
Suduka sunyi shiru suna saurarensa, kowace da abinda take kitsawa a ranta.
Auta tace "to wane lokaci kake ganin ya dace ari'ka kar6ar aykin? Khleed yace "Ku yakamata ku fidda, sai lokacin Fadila tayi magana tace kamar da 'karfe biyar da rabi na yamma, ta kallesu tace hakan yayi koh,? Khaleed yace "yayi.
Haka dai suka d'an ta6a fira, wacce yawancinta tsakanin khaleed ne da Fadila, dan Auta ita haushi ke hanata magana, dan ita kome Fadila zatayi bala'in haushi yake bata, wani irin mugun kishin khaleed ne ke kamata duk lokacin dataga yana kula Fadila.
A haka aka cikama Auta kwananta d'aya batare da wani tashin hankali ba, dan Fadila ta hakura,  kuma kullum girkin Autar takeci, dan kuwa tare suke cin abinci su duka,
••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Yau yakama ranar da Fadila ta kar6i kwana, saboda haka itace tayi masu abincin dare,
        Ta had'a kome ta jera kan dining, da misalin 'karfe takwas na dare suka zauna cin abinci, Fadilar da kanta ta zuba ma Auta bayan ta zuba ma khaleed ta tura mashi gabanshi.

Auta cike da jin haushi ta debi abincin takai bakinta, bata San lokacin da tasaki wani tattausan murmushi ba dan jin testing d'in abincin, a zuciyarta tace
" ~_Salmanu!...... kada inga salame idan haka take_~"
Dan jin abincin tayi ba wani testing ko kad'an, aiko take wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta, data tuno cikin kwana biyunan yanda khaleed ke buga santi idan yana cin abincinta, koda yaushe yana yaba mata kan iya girki.
Khaleed kuwa koda ya d'ebi cokali d'aya yakai bakinsa, yaji abin ba'a magana, daurewa yayi ya had'iye na bakinsa, haka dai ya daure yaci gaba da ci, itama Auta dataga haka saita ri'ka tutturawa tanaci tana jin dad'i aranta, ita kanta Fadilar daurewa kawai take tanaci dan tasan ba yanda za'ayi tayi girki kuma ta'ki ci' sai afara zargin kota tasarma rashin gaskiyane, amma ko ita kanta tasan abincin beyi dad'iba, saboda haka ta dage tayita d'ibar girki.
Bayan sun kammala sun d'an ta6a fira har kusan 'karfe sha d'aya da rabi Auta nata jan khaleed da surutu dan kada su tafi su kwanta, shikuwa ya biye mata dan bemasan lokaci yayi nisa haka ba.
Saida Fadila tagaji, ga bacci tanaji, tanata hamma sannan ta kalli khaleed tace "my man bacci nakeji kazo muje kaga dare yayi har sha d'aya, sai lokacin ya duba agogon wayarsa yaga k'arfe sha d'aya da minti arba'in da tara, saboda haka khaleed yatashi sukayima Auta sallama suka wuce d'aki.
Itama nata d'akin tanufa, ta cire kayan jikinta ta sanya wata doguwar riga ta bacci ta haye gado da niyyar yin bacci, amma ina kasawa tayi lokacin data tuno yanzufa khaleed yana d'akin wata ba itaba, kuma ze nuna mata soyayya irin yanda ya nuna mata.
Zunbur tayi ta tashi kamar wacce aka tsikara, takama zagayen d'akin zuciyarta nata tafarfasa, falo ta dawo ta zauna ta sa hunnu biyu ta buga uban tagumi, zuwa can taga zaman beyi ta tashi ta dinga safa da marwa tsakanin falo da d'akinta, daga 'karshe da takaicin ya ciyota batasan lokacin data fashe da wani irin kuka ba, tafad'a kan gado tacigba dayi, har misalin 'karfe ukku da rabi na dare Auta na aykin kuka, daga 'karshe dai bacci 6arawo yayi awon gaba da ita.

.
 Haka Auta tacika kwanakinta biyu kullum zata tsaya ta kwantar da hankalinta ta tsara girki tun kafin ta kai kan dining saita d'and'ana taji testing d'insa saita tabbatar da lafiya lao sannan take ajiyewa, amma abin mamaki sai sun zauna cin abincin suji gishiri za'ka'ka, Abin yana matukar damun Auta amma ba yanda zatayi, dan batada hujjar kare kanta akan cewa ba ita ta zuba gishiri haka ba,
ba abinda ya kara d'aure mata kai sai lokacin da tayi girki ranar ko gishiri bata zuba ba dan gudun kada yayi yawa, amma babban abin mamaki shine suna fara ci sukaji gishiri zau' abin ba dad'in ji.
****************************
Fadila ce cikin shigar 'kananan kaya riga da wando sun matseta sosai, wasu had'ad'un kuloli ne take d'aukowa daga kitchen tana jerawa kan dining, gefe kuma lemun ```5alive``` ne sai ruwan swan, abin gwanin ban sha'awa.
Da misalin 'karfe biyu da rabi khaleed ya dawo gida, Fadila ta tarbeshi cike da murna, Auta kuwa tana zaune gefe, cikin sanyin jiki tace "Sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ya wuce d'akinsa,
    Dan yanzu Auta tariga tagama sure mashi, kwata-kwata tagama 6ata ranshi, ace kullum mutum baze iya tsayawa yayi Abu cikin tsariba, sai ace yau ayi girki acika gishiri, kuma gobe ma haka za'ayishi,
babban abin takaici sai kaji gishiri cikin zo6o ko kunun aya, wnnan ay rainin wayo ne.
Wani 'karamin tsaki yaja "mtsw, sannan ya wuce d'akinsa, Fadila ta bishi tana wani karairaya, koda takai bakin 'kofar d'akin saita juyo ta kalli Auta dake zaune kan kujera abin duniya duk ya dameta, tayi wani shu'umin murmushi sannan tashige d'akin tare da canja salon tafiya tana wani juya mazaunai.
Fadilar ce ta taimaka mashi ya cire kayan jikinsa yayi wanka, da kanta taje cikin kayanshi ta dauko mashi kaya marassa nauyi ya Sanya, sannan suka fito falo,  dining suka sauna dan cin abinci Auta kuwa ba'kin ciki ya gama cika mata zuciya, bayan shigewarsu d'akinta tanufa tafad'a kan gado ta rushe da wani irin kuka, sai da tayi me isarta sannan tafad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta shafe jikinta da cream me dadin kamshi da gyara jiki sannan ta shafa powder ta dauko man le6e ta shafa,
  wadrope tanufa ta d'auko wata doguwar riga ba'ka me adon fararen  duwatsu daga gabanta ta Sanya, sannan tasa d'an 'karamin gyalen rigar ta rufe kanta dashi, lokaci guda ta fito balarabiya Sak, dan ba 'karamin kyau Auta tayiba.
Kan dining ta iske Fadila da khaleed suna jiran fitowarta, guri ta samu ta zauna duk da zuciyarta na cunkushe da ba'kin ciki da kuma jin haushin Fadila amma ko kad'an bata yadda khaleed da fadilar suka fahimci halin datake ciki ba.
        Bayan Fadila ta zuba abincin ta ajiyema Kowa nashi gabanshi, jalouf d'in taliyace wacce taji kifi, cike da fargaba Auta ta ebi taliyar takai bakinta, ```Ya salam```...... Auta ta fad'a tare dayin hanyar toilet da gudu ta rina'ka kwara amai, saida ta amayo duk abinda ke cikinta, khaleed kuwa binta yayi daga baya yana mata sannu, bayan ta gama ta wanke bakinta khaleed yakamo hannunta suka dawo falon, kan kujera ya zaunar da ita yanamata sannu, ita kuma sai wani langwa6ewa take, tana lumshe ido, Fadila ta kalleta cike da jin haushi, amma sai ta daure dan bataso a d'ago da ita, tace "sannu dama bakida lafiya ne? Auta tace lafiyata lau, kifin da akasa agirki ne 'karninsa yayi yawa shine ya tayarmin da zuciya,
Fadila ta ta6e baki ta samu gu ta zauna, a zuciyarta tana cewa
.
```lallaima yarinyar nan nizakima duniyanci kice wai bakison kifi sau nawa ke kikeyin girki da kifin akwai dai inda kika dosa```.
Auta kuwa 'kara narkewa take tana wani shagwa6ewa, 'karshe ta kwanta kan kujerar datake tayi filo da cinyar khaleed,
   Shikuwa sai wani rarrashinta yake yana tarairayarta, "sorry my dear ki daure kici abincin bekamata dan kinyi amai ki zauna da yunwa ba.
   Cikin shagwa6a Auta tace " nidai banison wannan ka siyomin wani, tunda yanzu ba time d'in da zan girka wani, yace "fad'i mi kikeso in sayo maki, cikin shgwa6a tace ka siyomin kome kaga ze Sani farin ciki, yace "kada ki damu my only ina zuwa, makullin motarshi ya d'auka yafita, be kobi takan Fadila ba wacce tacika tayi fam saboda takaici.

.
       *_BAYAN KWANA BIYU_*
 Auta ana kitchen anata faman girki, yau tasha Alwashin tsayawa tsayin daka tayima mijinta abinci wanda ze faranta ranshi, wanda zesa ya manta duk wani 6acin rai na baya, kuma ya dawo da tsananin so da 'kauna da kulawar dayake mata.
Sakwara tayi niyyar dafa mashi da miyar agushi, saboda haka doyarta me kyau ta fere ta d'ora kan wuta, sannan ta dora miya kan wani stove kusa da doyar, bayan ta kammala sakwarar ta maida hankalinta kaf gurin miyar, cikin 'kan'kanin lokaci ta kammala miyar ta juye kome cikin wasu kuloli masu Khan gaske, fridge tanufa da niyyar ta d'auko abarba domin yau *(pineapple juice)*lemun abaraba tayi niyyar had'a musu, tana bud'e pridge din kuwa cikin rashin sa'a saitaga ashe batada sauran abarba, sai lokacin ta tuna aahe fa ta kare tin bayan kwana biyu datayi lemun da ita.
'Dakinta tanufa ta dauko karamar hijab ta sanya sannan tanufi harabar gidan da niyyar taba  me gadi ya siyo mata Abarba,
     Zaune ta iskeshi kan benci yana ri'ke da yar rediyonshi yana sauraren labaran duniya, cike da ladabi ta gaidashi sannan ta bashi sa'kon ba musu ya kar6a yafita ya siyo mata, dayake kusa da su akwai wurin da ake saida kayan fruit.
Data tashi dawowa sai bata biyo ta babbar kofar falon ba, ta baya ta biyo hanyar da zata sadata da kitchen d'inta kai tsaye,
tazo dai-dai window kitchen dinta kamar ance tayi duba gurin,
    Wani irin mummunan fad'uwar gaba taji dan ganin abinda ke faruwa a kitchen d'inta.
    Fadila tagani da kullin gishiri cikin leda ta bud'e had'ad'd'iyar miyar agushinta wacce keta zuba 'kamshi ga nama zud'u-zud'u aciki tsoka zallah tayi amfani da ita gurin yin miyar.
Aiko da sauri Auta takoma baya ta la6e dan taga ikon Allah,
Gani tayi Fadila tasa cokali ta ebo gishiri ta zuba cikin miyar ta 'karo wani cike da cokali ta juye, saida ta zuba cokali biyar ciakakke sannan tasa cokali ta motse,
Ta kulle ledar gishirinta ta kakka6e hannunta tayi saurin barin kitchen d'in.
Cike da mamaki Auta ta shigo kitchen d'in, ta bud'e miyar tasa cokali ta motsa lokacin gishirin yagama narkewa cikin miyar, saboda haka zubar da miyar tayi ta ta d'ora wata cikin 'kan'kanin lokaci tagama had'a wata sabuwar miyar ta gama kome ta had'a lemun abarba, tasaka pridge sannan ta gyara ko'ina na kitchen d'in,
    'Daki ta wuce ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito simple kwalliya tayi sannan ta d'auko riga da siket na atamafa ta sanya ta dauko turare ta feshe jikinta dashi, tafito falo sai 'kamshi take bugawa, sannan ta d'auki makullin kitchen d'inta tafita zuwa kitchen d'in, dan tin lokacin dataga abinda Fadila tayimata data gama girkin ta kulle kitchen d'in ta tafi da makullin d'akinta.
Bayan tagama jera kome kan dining, lokacinne kuma khaleed yashigo gidan, cikin murna dajin dad'i Auta ta tarbeshi tayi Mashi sannu da zuwa, ciki-ciki ya amsa, sannan ta kar6i jakar hannunsa tayi gaba zuwa d'akinsa shikuma yabi bayanta, bayan ya rage kayan jikinsa suka fito zuwa falo
Sun zauna kan dining Auta ta zuba ma Kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda 'kamshin girkin ya mamaye falon,
.
Fadila tasa hannu ta d'ebi loma guda zata kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalli khaleed tace "my man , ya juyo ya kalleta, tace "nifa wallahi fargabar saka abincinnan nake a bakina, saboda kasan gishiri yana iya yima mutum lahani, kasan fa da mutum ya d'ibgama cikinsa gishiri 'kara yaci ba dad'i.
Auta tayi murmushi tace "Fadila kici mana kiji, idan kikaji gishirin yayi yawa ai baza'ayi maki dole akan sai kinci ba, sannan ta kalli khaleed tace "my dear kaci abincinnan hankalinka kwance, nayima Alkawarin daga yanzu kagama jin wani aybu cikin abincina, wancan lokacinma matsala ce aka samu amma yanzu kome yakoma normal inshaAllah.
Khaleed bece kome ba, sai dai ya ebi abincin ya kai bakinshi cike da fargabar irin testing d'in dazeji,
Cike da mamaki khakeed ya ida saka abincin bakinsa, dan wani irin dad'i yaji yartsa kwanyarsa.
Besan lokacin daya sakarma Auta wani tattausan murmushiba, yace *Weldon* my wife, amma nayi matu'kar farin ciki dajin wannan gyara naki, gaskiya yau kin matu'kar faranta raina Allah maki Albarka ya saka miki da Aljannah, cike da jin dad'in yabata da kuma addu'ar da mijinta yayimata, tayi dariya har dimple d'inta ya lo6a tace Ameen mijina, Allah kara dan'kon soyayya tsakaninmu, yace "Ameen my wife.
Cike da mamaki Fadila ta kai abincin bakinta, take dad'in abincin ya ratsa mata kwanya, batasan lokacin data cigaba da cin abincinba, dan dama su duka akwai tsohuwar yunwa tattare dasu dan tin lokacin da Fadila tafara 6ata ma Auta abinci da gishiri suka daina cin abinci su 'koshi,
Domin dai ita Fadila kotayi ba sosai suke iya Ciba, saboda ba dad'in yau bare na gobe
Ranar dai haka suka ci abinci cike da farin ciki da annushuwa,
Sa6anin Fadila wacce ba'kin ciki yagama cika zuciyarta.
```Auta dai tagano Fadila ce me 6ata mata abinci, amma kuma bata tanka mataba kuma bata nuna 6acin ranta ba```
*_Kome take nufi da hakan kubiyo zee mman khady dan jin yanda za'a kwashe tsakanin Auta da Fadila_*
.
 "Haba 'kawata aini wallahi bayi fushi dake, ace tunda aka kawoni gidannan sai yau kika tuna dani, 
Sadiya tace "Ayimin afuwa wallahi kinsan hidimomi idan sukayima mutum yawa sai ahankali, Auta ta harareta cikin wasa tace "kinjiki ko, ke har wata hidima ke gareki kamar wata me iyali, Sadiya tace "ay iyalin ake niyyar yi shiyasa hidimomin suka fara tun yanzu,
"Hakane fa yau saura 3 week's koh? Sadiya tace "au tambayata ma kike, duka yaushe mukayi waya dake na gaya maki.
Haka sukacigaba da firar yaushe gamo, nan Auta ke tamabyar ta "waini ina uwar gidanki? Tunda nazo ban gantaba, "Auta ta harereta tare da kaimata duka cikin wasa tace "Uwar gida fa kikace, kodai amarya' ay nice uwar gidan kamar yanda nad'au Alwashi, nan auta tabata labarin yanda sukayi ranar da aka kawosu da kuma kwanakin da suka kwashe suna kwanan zaune.
Sadiya tayi dariya sosai sannan ta kalli Auta tace "kai Auta bakida dama gsky rigimarki tafiki 'karfi, khaleed d'in kuka samu shiyasa kuke yanda kukaga dama, idan nice shi wallahi sai in za6i d'akin danikeso kawai inyi kwanciyata kuma dole wacce ban za6a ba ta hakura.
Auta tayi dariya tace" Ay koda hakan yayi nasan d'akina ze za6a dan na dad'e da fahimtar irin tsananin son da khaleed kemani, shiyasa bani yarda inyi abinda zai 6ata ransa,
   Sadiya tace Yauwa 'kawata haka yakamata kiri'kayimasa shine zesa ya'kara jin sonki da 'kaunarki, kuma kada ki yadda koda wasa kiyi fad'a da abiyar zamanki wanda ze d'aga hankalinsa randa duk haka ta kasance sai son dayake maki ya ragu a cikin zuciyarsa.
Auta tace "ina ay bazan yarda haka ta faru ba, dan nayi al'kawarin babu ranar daza'ayi kace-nace  dani a gidannan, amma kuma naga take-rakenta tana Neman ta ragemun son da mijina yakemin ta haryar 6atamin duk wani Abu dana girka dan na faranta ransa.
  Nan Auta ta kwashe labarin yanda Fadila tari'ka zabga mata gishiri cikin abinci, Wanda sanadin haka khaleed yafara juya mata baya,
   Sadiya tace "tab ammafa yarinyar nan makira ce, wato ita nata ba dad'i shine ta 6ata maki,
tsabar ba'kin ciki kawai, amma kin kyauta da kika kyaleta, kawai ki ri'ka kaffa-kaffa da duk wani Abu wanda kikasan zata iya 6ata maki.
"Tab wallahi bazan 'kyaletaba, Auta ta fad'a cikin d'aga murya, Sadiya tayi saurin sa hannunta ta rufema Auta baki, tare da cewa "ki rufamin asiri kada kiyi wani Abu ace nice nazo na sakaki, kuma kinsan fa yanzu haka tana jinmu,
Sai lokacin Auta tayi 'kasa da murya tace "wallahi bazan 'kayletaba dole sai na rama abinda tayimin, sadiya tashiga bata hakuri akan ta hakura ta 'kyaleta ai dai tasan tafita, Auta tace "Hmm Sadiya inaga kin fara manta ni, sadiya tayi murmushi tace "ina zan manta da rigimarki Auta, amma ai yanzu yakamta ki rage wasu abubuwan saboda yanzu gidan aure kike ba gidan iyayenki ba.
.
Auta tasan halin Sadiya idan ta biyemata tsaf zata sage mata gwuyawu taji bazata iya aiwatar da kome akan ramuwar abinda Fadila tayimata ba,
    Yawarta ta d'auka dake ajiye kan bedsite ta duba, sannan ta kalli Sadiya tace "kinga rana tayi har karfe sha d'aya da yan mitoci, bari nashiga kitchen na samo maki abinda zakici, nasan bazaki iya cin abincin waccan matar ba,
Sadiya tayi murmushi tace "wallahi da kin barshima dan tafiya zanyi yanzu, Auta tace wallahi bazaki tafiba sai kinci abinci, kinsan me zan dafa maki, bata jira abinda zata fad'a ba tace taliya da manja da yaji zan dafa, nasan ke mayyar tace, suduka suka sa dariya.
Tare suka shiga kitchen d'in, cikin minti talatin suka gama girka taliyar suka zuba a flate, sauka zabgo uban yaji, amma duk da haka saida Auta ta taho da wani Yajin cikin wani 'karamin vowel wai zata 'kara gabanta.
Sai gurin karfe sha biyu da rabi Sadiya tayi haramar tafiya gida, tare suka fito daga d'akin a babban falo suka had'e da Fadila ta fito daga d'akinta zata shiga kitchen, nan suka gaisa da Sadiya kowanensu ba yabo ba fallasa, sannan suka wuce, har kusan get Auta ta rakata sukayi bankwana, tare da mi'ka mata wata yar 'karamar leda wacce ta had'amata kayan make-up aciki.
Auta na komawa d'akinta, toilet ta fad'a ta she'ka wanka, bayan tafito ta zauna gaban mirror ta d'and'asa kwalliya, sannan ta d'auko wasu 'kananan kaya riga da wando ta sanya,
Rigar ta d'an sauko dan ta rufe mata rabin cinyarta, amma ta matseta sosai, sai wando pencil, sannan ta dauko wani karamin gyale tayi rolling, lokaci guda ta tashi daga jinsin Hausa zuwa na larabawa, dan idan ba magana tayiba sai kace bata ta6a jin yaren hausa ba.
Fadila kuwa itama lokacin tagama tsara kome na abinci kan dining, sannan takoma d'aki ta she'ka wanka shigar doguwar riga tayi ta atamfa, itama tayi kyau gwargwadon nata.
Da misalin 'karfe biyu da minti arba'in khaleed yadawo gidan, suduka falo ya iskesu, sukayi mashi sannu da zuwa, hankalinshi duka nakan Auta, kallonta kawai yake yanajin wani feeling tattare dashi,
Saida Fadila ta lura da irin kallon dayakema Auta sannan tayi dabarar zuwa kusa dashi tace, "muje ka watsa ruwa ko, ga kuma abinci yana jiranka.
Beyi mata musu ba suka wuce d'akinsa, amma cikin ransa jiyake inama Auta ce suke tare da ba abinda ze hana su kashe arna kafin su futo.
.
 Zaune suke kan dining sunyi shirin cin abinci, kamar yanda suka saba duk wacce ke girki ita ke zuba ma kowa ta ajiye masa gabansa, yauma Fadila ce ta zuba masu ta ajiye masu, lokaci guda Auta ta ebi abincin takai bakinta, 
Dadai lokacin shima khaleed ya ebo abincin yakai bakinsa,
Wani irin zafi yaji ya ziyarci 'kwalwarsa, ya mamaye duk illahirin Kansa, har cikin kunnuwansa yakejin bala'in yajin da aka zambad'a cikin abincin,
Wani mugun attaruhu aka zabga irin me yajin nan,
Kalmar innalillahi kawai yashiga furtawa, dan shi mutum ne wanda be shiri da yaji ko kad'an,
Robar ruwan dake gabanshi yayi saurin jawowa, ya tsiyaya ruwan cikin cup ya shanye, ya kara cika cup d'in ya shanye ko zeji sau'kin rad'ad'in yajin dayakeji amma abanza dan ko alamar zebar jin zafin beyiba.
Dai-dai lokacin kuma yaji Auta ta fashe da wani irin kuka, yanda kasan wata 'karamar yarinya ta tashi tsaye, duk ta wani gigice tanata yarfa hannu, ta bud'e baki tana sha'kar iska tana fad'in yaji, lokaci guda fuskarta tayi jawur, abinka ga farar mace, ga hawaye share-share.
```{Niko zee da nike tsaye ina kallon ikon Allah ri'ke baki nayi ina mamakin Auta dake kukan yaji, kamar ba ita bace tagama cin abinci da 'kawarta suka zabga yaji amma ita saida ta 'kara kan wanda suka zuba}```
Khaleed kuwa koda yaga yanda Auta ta fita hayyacinta, tanata kuka saboda yaji, besan sanda yayi saurin zuwa inda takeba ya rungumota jikinsa, ya nufi kujera three saater da ita ya zauna ya d'orata kan cinyarsa, yana rarrashinta kamar wata 'karamar yarinya, ruwa ya d'auko ya zuba cikin cup yabata ta shanye amma yana cire cup d'in daga bakinta saita fashe da wani sabon kuka,
Lokaci guda  khaleed ya rud'e yarsa yanda zeyima Auta taji sau'kin yajin.
Bakinsa ya d'ora kan nata tare da tura harshensa cikin bakinta yashiga tsotsar bakin nata kamar yasamu wani sweet , wai a dole ze tsotse mata yajin,
Dama abinda auta ke nema, itama tacigaba da kissing d'insa tana 'kara shigewa jikinsa, lokaci guda khaleed ya susuce ya manta da maganar wani yaji dayakeji, yacigaba da aika mata da sa'konni masu wuyar fassarawa, ita kuma sai wani 'kara shigewa take jikinsa tana shagwa6ewa,
Abu yayi nisa hannuwan khaleed kan 'kirjin Auta yanata wasa da dukiyar fulaninta, itako batayi 'ko'karin hanashiba saima 'kara mi'ka mashi kanta datayi.
Wani irin kukan ba'kin ciki Fadeela ta fashe dashi, dan duk abinda sukeyi gabanta sukeyi, kallonsu kawai take takasa magana saura kad'an zuciyarta ta buga, wannan kukan dayazo mata shine samun sau'kin takaici da ba'ki cikin da Auta ta 'kunzuga mata.
Da sauri ta tashi tanufi d'akinta, minti biyar batayiba da Shiga, sai gata ta fito, sanye da gyale, da takalmi a 'kafarta, sai yar poss a hannunta,
Sai lokacin ta iske khaleed ya sake Auta, amma suna zaune kusa da juna kowanensu yana cike da sha'awar d'an'uwasa saboda wasanni da sukayi, abin ba'a cewa kome .
Bata ko kallesuba tanufi 'kofar fita daga falon, fuuu kamar zata tashi sama, khaleed ne yayi saurin tashi yabi bayanta yana tambayarta "Fadila ina zaki?
Bata ko saurareshiba tayi gaba abinta.
Tana fita get d'in gidan takoyi sa'a wani me napep ya ajiye wata mata wani gida kusa dasu, nan tafad'a mashi inda ze kaita, tashiga.
Khaleed na fitowa napep d'in na barin 'kofar gidan, "ya salamm ya furta, can kuma sai yayi wani guntun tsaki yace
.
```"kinyi laifi kuma kifi wanda kikayiyamawa zuciya```
Gida ya koma ya iske Auta zaune inda yabarta, nan take tambayarsa, "Lafiya kuwa saboda me Fadila ta tafi, be bata amsa ba sai rungumota dayayi jikinsa yafara shafata ta ko'ina, Auta batayi 'ko'karin hanashiba saida taga yana neman wuce gona da iri, sannan tayi saurin tureshi, ta tashi zaune, nan khaleed ya marairaice mata yayi kalar ban tausayi yace (please Auta help me) ki taimakeni nariga na shiga wani yanayi, cike da tsoro Auta ta kalleshi taga yanda idanunshi suka kad'a sukayi ja,
Lokaci guda ta langa6e tana bashi ha'kuri "kayi ha'kuri my dear kaga ba aykina bane, yanzu idan nabaka kaina mun shiga ha'k'kin Fadila, kayi hakuri kada kasa kanka cikin maza masu  rashin Adalci tsakanin matayensu.
Haka Auta ta rarrasheshi har ya hakura, nan ya wuce dakinsa, ya shiga toilet yasake watsa ruwa sannan ya dawo yabi lafiyar gado.
Itako Auta yana shiga d'akinsa, itama nata d'akin tanufa tana ahiga ta she'ke da dariya tace
~_(Fadila dani kike magana)_~

0 comments:

Post a Comment