CIWON SO Page 1-5
.
Na Hafsat ( Hafsy baby)
.
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai.
.
Yan Mata guda biyu sunata shiri zasu school adauki wannan A shafa wannan cikin sauri Meenat tadauko kaya tasa Amma safeeya batada niyyar tashi A bakin mirror har Meenat tasa cikin fada Meenat tace Amma kinsan yau muda lecture din Dr Ahmed kuma shine first, kuma kinsan idan ya shiga class babu wadda zai Kara shiga Amma kintsaya sai wani lindar fuska kike. Safiyya tace sorry, sis yanzu Zan tashi kikara hakuri. Tana idarwa ta wuce ma' adanar kayansu(wadrope) tasawani red din material Masha Allah tayi kyau Abinka da farar Mace suka fito suka iske umma da Abba bisa dinning table domin break fast suka hada baki morning umma, morning. Abba, umma da Abba suka ce lafiya twins din Umma da dady. Sukaja kujera suka zauna sharp sharp sukayi break fast. Suka mike umma nd Abba muntafi school. Suka A dawo lfy. Suna. Fitowa safeeya tace pls, my sis kiyi driving zuwa school banason bata kwalliya na. Meenat tace chabb!! Sai dai muyi late sai inatukamu cikin fuskar rarrshin safeeya tace pls my sister nandai ta rarrsheta sukaje ( ummaru musa yar aduwa university).bayan sun isa suna shiga Suka nufi class suka zauna ko 5 minutes baayi ba saiga Dr Ahmed.ya shigo nanda kowa ya shiga hankalinsa yan Mata kuwa kowace jiki yace morning class. Sukace morning sir, yarubata test bisa Allo kowa ya firgita da hakan 30 mints yabada kowa yagama. Nan safeeya ta kalli Meenat masu niyya suka Fara masu maida hankali Akan Abinda Ake saffiya ta tambayi wani question tabata ganeba Dr Ahmed ya Lura da itah yace ke get out, tace pls. Sir Am sorry yace I say get out cikin sanyi jiki ta tashi tabar class din.
.
Safeeya na fita ta nufi wani wajen da babu mutane sosaitazauna tayi tagumi tafada tunani zuciyata meyasa kikayiman haka nafada cikin son Dr Ahmed mutumin daya tsane ni bayason ganina ba batasan sadda hawaye ke tsiyaya da fuskar ta ba saboda CIWON SO Dr Ahmed kedamunta kullum kara yawa yake tare da itah. Kamshi wani turare taji mai kamshi ya ziyarci A hanci tadago fuska ta ga waye sai sukayi Arba da Dr Ahmed ya wuce da barandar datake zaune. Can taji wasu yan Mata na gulmar suna cewa keh Aseeya wallahi Dr Ahmed ya hadu Amma ya cika miskilanci. Rannan naje office din Amma kinga fuskar yadda kikasan bataba dariya haka yadaure fuska nayi sallama nashiga nace sir inayini cikin daure fuska ya Amsa yaceman meke tafe Dani nacemasa Dama wutowa nazo yi nace bari nashigo bebari na ida ba ya kwasaman wata. Tsawa yace nabarmishi office dinshi cikin sanyi jiki. Nafito nagayamiki. Safeeya taja wani tsaki tana takaicin wasu matan dake bada Kansu ga wasu mazan domin ita ko ciwon so zai kasheta bazata taba tarar dr Ahmed tace tana sonshi ba. Can kuwa bayan Meenat sun fito tana ta neman safeeya. Tarasa can tagasu wadda. Suke gaisawa. Ta tambyesu sunga safeeya suka ce tana baya can tanufa ta iske ta zaune. Tace shine zaki bani wahala ko tace sorry sis Meenat ta nemi wuri ta zauna tace wai sis mekika yima Dr Ahmed yake miki haka ne safeeya tace wallahi sister bansan Abinda nayi masa yakeman haka. Tace yanzu yazakiyi da test din datawuceki tashi ne yau. Kizo muje office dinsa mubashi hakuri safeeya tace. Sister kinsan hali Dr Ahmed bazai yiba tace kedai tazo muje. Cikin sanyi jiki ta tashi suka nufi Amma sai sukayi rashin sa' a office din kulle yake.
.
Cikin damuwa Meenat tace kinga bayanan ko sis safeeya tace Eh mujuya gobe nashigo dakaina da munshigo school din nabashi hakuri suka juya suka koma cikin makaranta bayan sun idar da lecture din dasuke da itah suka hau mota suka nufi gida suna isa gida suka nufi dakinsu suka wasa ruwa Dama lokacin sallar Azahar yayi suka sallah Meenat ta Lura yau safeeya bata cikin walwala sosai bata surutun nan Nata data Saba tace wai sister meke damunki na Lura tun school bakya walwala meyafaru ne ko tun abinda Dr Ahmed yayi miki baki manta bane. Safeeya tace yazaayi na manta sis mutanan yatsaneni ban San Abinda nayimasa sister Abinka kadan ya zan masa ya disgani cikin mutane kina kallo yau fa bani kadai nayi magana Amma nikadai ya hango yafiddo ni. Bata Ankara sai hawaye shar shar. A fuskarta domin wani ciwon so Dr Ahmed ke tasomata A zuciya Meenat tace safeeya meyakai na kuka safeeya tace Abinda yakeman yasani kuka( batasan ciwon so Dr Ahmed bane yasa safeeya (Hawaye. Tace kiyi hakuri taso muje kinsan Umma batasan dawowar mu ba suka nufi daki umma su suka isketa zaune bisa darduma tana lazimi sukayi sallama suna shiga tagama laximin bayan ta idar tace yan biyun umma Andawo Eh, umma mundawo har munyi sallah ma tace toh madallah kuje ga Abicin kucan bisa dinning koh. Sukace to umma suka nufi dinning safeeya tura kawai take domin batasan Meenat tafahimci halin datake ciki. Bayan sun idar suka tashi suka nufi dakinsu.
Bayan sallar isha' I suna zaune falo da suna kallon labarai da Abba su duka dai. Har wajen karfe goma. Sannan sukayi ma iyayen nasu sai da safe suka nufi dakinsu. Meenat naxuwa tafada gado domin bacci takeji sosai. Safiyya tabi bayan ta Amma takasa Bacci tunani Dr Ahmed kawai take sai juye juye take.har dai bacci yadauketa. Asuba tagari
Washe gari
Abba yashiga kwankwasa kofar su safeeya domin sallar Asuba domin kullum dayatashi sai yaxo yatadasu shikuma ya nufi masallachi. Bayan sun tashi sunyi sallah sai kuma su shiga kitchen domin shirya break fast domin umma batada yar Aiki bata bukatar ta daga itah sai yayanta. Bayan sun kamallah. Sukaje sukayi wanka nanfa suka hau shirin school. Safeeya tajawo wata Arabia gown tayi rolling da blue din gylen Masha Allah gaskiya tayi kyau domin sai da Meenat tace Kai sister kinga kyan dakikayi KO sai kace balarabiya. Safeeya tace Kai sister banason zolayafa tace Allah kuwa kin wanku. Nan suka yan Mata biyu kyawawa dasu suka gaida iyeyensu sukayi break suka nufi school cikin motarsu. Suna parking suka fito suka nufi class. Sungama daukar lecture ta farko sai kuma karfe 2:00 pm bayan sunfito. Safeeya tace sis bara naje office din Dr Ahmed naji yazamuyi dashi game da test din jiya Meenat tace muje tare mana safeeya tace A, a bara dai naje naje ni daya kinsan halinshi fa nan Meenat tace shikenan kije ki iske ni inda nadaki jiya . Safiyya tace OK , tajuya ta nufi office din Dr Ahmed cikin sa' a ta iskeshi bude gabanta na faduwa tayi sallama ta shiga.
.
Safeeya nashiga ta iske Dr Ahmed bisa table yana rubutu tace sir Inayini bai dago fuskar yaga waye ba yace lafiya lau yacigaba da rubutun sa ta kusan 15 minutes tsaye sannnan yadago fuskar sa cikin daure fuska yace meke tafe dakene. Nan kwarjinin sa yayima safeeya yawa domin ya tsare ta da manya idanuwansa. Tace sir hakuri nazo baka Akan test din dakayi jiya kayi hakuri kasakeman wata. Yace sai dai kiyi hakuri kitari wata. Domin nawuce wannan Kuma. Kisake laifin haka nakara koranki. Ya sunkuyar dakanshi ya cigabada Abinda yake. Cikin sanyi jiki safeeya tafito ta nufi inda Meenat tace ta sameta can ta tanufa ta iske Meenat tana duba wani book. Tace yane sis kindace tace A, a yace saidai natari wata kuma nakara Abinda nayi nakara fita. Sister narasa abinda nayima Dr Ahmed yatsaneni haka. Nan tafashe da kuka domin zuciyar ta wani zafi take Mata Meenat nace kiyi hakuri ki kyaleshi sister kinji ko nan ta rarrsheta. Lokacin shiga lecture dinsu yayi suka tashi suka shiga. Bayan sunfito suka nufi gida Amma kowaya san yau safeeya bata cikin walwala daki tawuni yau.
Washe gari kamar yadda suka Saba sun isa school suka nufi class Amma me suna shiga suka tarar da Dr Ahmed ciki yafara lesson . Amma yabada baya cikin sanda suka shiga suka zauna Joyowar dai zaiyi saiyaga safeeya. Zaune yace keh!!!! Bakisan dokokina ne ba fita kibarman class har Meenat ta mike zata bita yace kan yajuyo kwanta yace badake nakeba ita kadai nake. Cikin fushi safeeya tatashi tafita cikin wani irin kuka mai ban tausayi tafita taji ma ta iya tsaya cikin school ba fitowa tayi ta tsaida nepep tanufi gida. Umma kawai ganni kawai tashigo tace lafiya safeeya kika dawo yanzu cikin dauriya tace umma bana lafiya ne tace subhanallah!!! Meyasameki tace zazzabi ne tace jeki daki bari nadauko miki magani safeeya tanufi dakinsu ta wurgar da mayafin da jakar tafada gado ta kwanta bata jimaba saiga umma da magani takawomata tace maza sha gabana nasan ki da kin magani. Nan tasha umma tace to Allah sawwaka tajuya tafita. Can kuma Meenat tafito daga lecture Dama yau daya garesu. Taduba duk inda take tsammani safeeya Amma bata Gantaba. Sai kawai takira wayanta. Safeeya tace tatafo gida. Meenat kawai tashiga mota tanufo gida. Ba. Inda tazame sai dakinsu ta iske safeeya kwance tace sis baki lafiya ne tace inafitowa wani zazzabi ya rufeni kawai sai na tafo. Meenat tace har kinsa hankalina ya tashi wallahi. Meenat tace gaskiya Abinda Dr Ahmed yakemiki yayi yawa. Kodai ki manta Akwai Abinda yahadaku ne. Safeeya tace Wallahi sis babu Abinda nayimasa.Tsane ce kawai. Amma gobe bazan duba kwarjini dayakeman Zan tunkareshi naji menayimasa ya tsaneni haka.
.
Meenat taja wani numfashi tace kinaga hakan zai yiyu kuwa sister safeeya tace hakan shine mafita sister domin nagaji dahakan dayakeman kamar ni kadai A fadi school. Meenat ta mike tace ke bari naje dakin umma batasan nadawo ba domin nan kawai nayo domin hankalina yatashi wallahi. Daban ganki cikin school ba tana shirin fita sai ga umma tashigo tace Ahh,Ahh, yaushe kikadawo ne ke tace yanzu nashigo umma da Ina niyyar shiga dakin ki sai gaki kinshigo umma tace nashigo ne dama naduba jikin safeeya naga yajikin karfe Safeeya tace umma da sauki sosaima yanzu zantashi nayi sallah ne. Umma tace to kitashi kiyi ga dan gidanki can nayi miki dan' wake kiyi sallah sai kici Nizan deka gidan Kawunku naji Alhaji nafadi dazu hajiya murja ta tazame da tayils ta goce da kafa Anjima kinkara jin sauki sai Ku leka kuganota. Safeeya tace sai kindawo umma. Umma tajuya tafita.
Bayan sallar Magariba safeeya da Meenat suka nufi gidan kawunsu domin ga gida ga gida suke suna shiga suka iske. Haidar zai fita( dan kawunsu ne) haidar yace yafara washe hakora kamar me tallar close up, safeeya takara daure fuska Meenat ce kawai tadan Saki fuska tace yaya haidar Ina yini yace bazan Amsa ba Ku baa ganinku sai da dalili ko yanzu ma don mamy tagoce dab aza gankuba ko Meenat tace wallahi karatu yadau zafi ne shi yasa . Haidr ya juya bangaren da safeeya take yace ke kurma ce dabazakiyi ma mutane magana ba safeeya inayini bata jira ya Amsa ba tashigewar wata ciki bata jira Meenat ba Haidar ya kada Kai domin CIWON SO Safeeya nadumshi tun lokacin da yafada Mata ta canza mishi. Bayan sun shiga ganin marar lafiya ne sun dan jima suka fito suka nufi gida bayan sallar Isha' ne suna zaune A falo bayan sun gama cin Abinci dare kamar yadda suka saba wajen karfe 10: 00 pm kowa ya nufi makwancin sa. Amma safeeya babu Abinda take sai juye juye bisa gado domin wani fitanenen ciwon so Dr ke tasomata kuma koda zai kasheta bazata iyah tunkarsa tace tana sonsa. Kuma gobe tayi Alkawarin tunkaranshi taji meta iyimishi ya tsaneta haka. Nan tana juye juye har bacci yasadodo ya saceta.Asuba ta gari yan biyun umma.
.
Washe. Gari kamar yadda suka saba tashi suka gama Abinda suke suka nufi school. Suna fitowa safeeya tace zataje gun Dr Ahmed. Meenat ta dakatar da itah tace tabari sufito daga lecture sai taje office dinshi . Meenat suna tafiya zuwa class take cewa nidama kin kyaleshi wallahi sister duka kingi one year mu ida school din fa, basai yakara ganniki ba sannan zai miki. Nan gaban safeeya yafadi ta tuna kingi shekara daya fa su ida school tadaina ganin muradin ranta(Allah sarki So duk irinda Abinda yakemata bata gani zuciyarta taki fushi dashi) Meenat tace sis yanaji kinyi shiru ne. Takakaro wani nurmushi tace Ahhh,, babu komai sis tunani nake wai kingi shekara daya mu ida school. Daganan firar su tazo karshe domin su iso class, Bayan sun fito daga lecture ne Meenat batasan zamewar safeeya tanufi office din Dr Ahmed. Tana isa ta iske yana kokarin rufe. Office din tayi sallama yajuyo yaga waye yanaga safeeya yace yakara daure fuska. Yacemata mekawoki wajena ba tunjiya mukayi magana dake ba nakuma baki Amsa. Ya bita ta gabanta zai wuce. Safeeya tayi saurin shan gabanshi. Tace sir bawannan yakawoni cikin fada take magana yayi mamakin haka daga bakin safeeya Amma benunamata ba yace mekawoki domin ina da Abinyi Ina sauri ne nabaki 5 minutes kifadi Abinda yakawoki. Tace bazan wuce hakan ba domin banga Abin tsayawa wajenka ( Karfin hali)
Sir naga duk cikin school babu wadda katsana kamanta. Mekake takama dashi, Kudi, mulki, kyau, komai daza kadinga wulakanta mutane yadda kakadama kasani babu Abinda yakai mutum daraja Amma Kaine Abin wulakacika, Kullum duk Abinda kake takama dashi fa Akwai wadda yafika. Ina sanar dakai kabi duniya A sannu ba matabbbata. Ba wurine dazamaba nar har Abadaba. Wulakanta mutane kuma kacigaba. Banyi maka wannan Maganar daka daina tsanata ba Ahhh, na tunatar dakaine. Nabarka lafiya. Safeeya tajuyo. Tatafi kawai tabar Dr Ahmed tsaye kamar butun butun butumi domin tunda tafara Maganar ya kuramata Ido nan yaji wani Abu yanayimasa yawo Akai ( tofa meye wannnan) A bangaren safeeya Kuma ba nufi wajen Meenat can baya takoma inda babu mutane tasha kukanta ta koshi har inda ta yacanza Allah sarki safeeya ciwon so Dr Ahmed na Amma tadaure tayimasa magana. Haka .
.
Safeeya nan wajen Tasha. Kuka tagaji taji kanta na ciwo. Tana niyyar mikewa taji wayanta na ringin taduba taga Meenat ce. Tace hello, Meenat cikin fada tace Ina kika shigane Ina nemakin tundazu tace sorry sis ganinan zuwa. Bayan sun idar da lecture din suka nufi gida. Kamar yadda bayan sun idar da Abinda suke sukayi ma iyayensu bakwana kowa yanufi makwancinsa safeeya tafara tunanin datasaba kullum dare. Takasa bacci ma baki daya tatashi tayo Alwalla tayi sallah ra' ka biyu. Ta roki Allah yayemata son Dr Ahmed inba Alkairi bane. Tare da itah. Bayan tagama tatashi tahau gado ta kwanta can sama sama bacci yafara daukar ta taji wani zafi A kirjinta tun tana daurewa har takai datafara numfashi sama sama. Can. Meenat taji kamar A mafarki taji numfashi firgice tatashi ta kunna lantarki taga safeeya ce cikin wannan halin A firgice tace sister! Sister!!! Amma taga numfashinta sama sama kawai yake A firgice ta Doro. Daga bisa Gado ta nufi Hanyar waje domin kiran Umma da Abba tazuwa tashiga knocking din kyauren Daki Abba. Da karfi A firgice umma da Abba suka farka sukaji buga kyaure ba kaukautawa Abba yazo ya bude kyauren yaga Meenat yace meyafaru Amina( domin haka yake kiranta) cikin kuka tafara magana Abba.. Safeeya bata lafiya gayanacan numfashi ta ....bebari ta ida yanufi dakinsu da sauri saidai umma tabi bayansa itada Meenat suna shiga suka iske safeeya tana ta numfashi sama- sama da sauri Abba yace mikar da ita kafinan na fiddo mota cikin sauri Abba yafito don fiddo mota domin tafita Asibiti yana fiddota su umma suka fiddo da safeeya tallabe baya Meenat suka shiga Alheri clinic suka nufa domin can suke da file suna isa suka fiddo da safeyya wadda takejin su sama sama. Suna shiga Akabata gado. Sunyi sa' a kuwa sun iske doctor dinsu wadda kedubasu. Nan danan yashiga duba Safeeya yaga Abinda kedamunta yayi mamakin dayaga ciwon zuciya kedamunta har yana nema yimata illah. Cikin zuciyarta. Yasan dai ba su rasa ci ba balle kayan sawa tomeke damunta ne nan yafito yacemusu suje gida sai dasafe sudawo domin yanzu zasu ajeta dakin Hutu bata bukatar hayaniya Abba yace doctor bazan barta ko yar uwata bace yace karku damu Alhaji daki dazamu ajeta bata bukatar kowa. Abba yace doctor jikin dai sauki yace da sauki mumata wasu Allurai yanzu. Tana bacci zuwa gobe insha Allah zata warware Abba yace toh Allah yasan haka. Doctor yace Ameen.
Abangaren Dr Ahmed kuwa tunda Safeeya tama gayamasa magana tajuya tatafi yakusan Minute 10 goma tsaye yana tunanin sannan yatuuka motar yabar makarantar babu inda ya nufa sai gida yanashiga ya iske mahaifiyarshi A falo tana kallo yayi sallama yace Hajiya tace naa' m Babana meyafaru naga yanayinka ya canza ne. Yace babu komai tace Anya babana babu komai inbaka fadaman waza kafadamawa ne yayi murmushi babu komai hajiya. Yatashi zai shiga ciki tacemasa Ga Abincika can kitchen naajemaka fa. Yace yanzu dai bari nashiga ciki nayi wanka. Nadan kwanta Ina fitowa zuwa Anjima naci hajiya taceshikenan sai kafito yajuya ya shiga ciki hajiya tabisa da ido har yashige ciki tace nasan Akwai Abinda kedamun yaron zurfin cikinsa da miskilanci bazai Bari yafadaman ba tagirgiza Allah sawakka karya jama kansa wani ciwo Dr Ahmed nashiga babu inda yazarce sai dakin sa yashiga toilet yawtsa ruwa yana fitowa jallabiya kawai ya zura yahau gado domin yasamu bacci Amma inah babu bacci magaganun Safeeya kemasa yawo. Nan yafara tunanin komai yacazama masa tsanar kowace mace cikin Ranshi
Bayataba mancewa shekara 2 datawuce yadawo daga Kano yanacikin tafiya.....
.
WAYE DR AHMED
.
DR Ahmed Dane ga Alhaji Ibarahim kwangila da hajiya Saudat. Shi daya Allah yabasu. Aràyuwa yayi karatu A kasar Engalnd primary dinsa kawai yayi Akasar Nigeria. Yakai matakin har PHD akasar Engaland sunso rikeshi A kasar Amma yace kasarshi zaidawo Dr baya cikin wañaann shashan ya masu kudi wadda idan Akatura karatu sutai sharholiya.
Abokinsa daya Hafiz. Shi kuma dan garin kano ne shima Hafiz babu ruwansa karatu suka sa gaba. Babu ruwansu da shaye shaye ko neman Mata.suka dawo gida Nigeria Dr Ahmed yasamu Aiki A ummaru musa yar aduwa university.
Dr Ahmed zayakai 32 years fari dogo ga hanci gashi sumar sa kamar kamar yanashafa Mata mai . Kai gaskiya Dr Ahmed ba karya ya hadu( dole saffeyya ta rude.
Maihifinsa yarasu shekara daya data wuce hanyar sa tadawo daga Abuja. Hajiya saudat taji mutuwar mijinta uba danta domin Allah ne gatanta mijinta gata ta domin yan garin Rimin local government ita dashi tatashi A hannun kishiyar maihafiyarta domin wajen haihuwarta mahaifiyarta tarasu su ukku ita da yayyenta yaya sule, yaya mustapa sai itah kishirya maifiyarsu masiffatace Muguwa domin fuska biyu gareta in maihaifinsu nan zata nunamsu Amma da yasa kafa yabar gidan zata Fara dukansu har tagaji.Abinci ma bata basu sai in maihaifinanan. Daga baya ma saita Asirce maihaifin nasu ko gaban idonsa dukansu take.Abinci saitagama dabasu nan ta tilas tawa sai yakai yakai mustapha da Sule karatun Allo tundai mahaifin nasu ya kaucewa domin yana son yayanshi sharrin Ade ne kawai (Allah yaravamu da mugunta)
Har dai taci galaba kanshi yakaisu garin katsina Karatun Allo. Daganan fa Hajiya saudt( mahaifiyar Dr Ahmed) tazama baiwa komai na gidan itakeyinsa Har takai Kimanin shekara17 samari sukayo Mata Ricah domin kyakyawa ce ga babu wadda tafidda ciki sai Iro. (Maihaifin dr Ahmed) nan dai Akayi bikin babu abinda Aka kaimata sai tabarma da fillo da cooler kwara daya taso ayi bikinta yayayenta nan nan Amma tun lokacin da babansu yakoma malamin yace tun wanilokacin dasuka fita bara bai kara ganinsuva. Maihaifin so yadawo hankalinshi tashe. Yana fadima Ade Amma data murza kambu Asiri sai yabar maganarsu.
Ayin bikin saudat babu dangi maihaifiya. Domin tun lokacin DA. Mahaifyar su saudat tarasu sukaso su tafi dash Amma maifinsu yahana sukayi fushi suka tafiyar su basu kar waiwayensuba. Haka Akayi bikinta Bayan wata daya bikin Iro yaje cikin katsina yagamu da Abokinsa wadda sukayi karatu yasamu Aiki daganan har yayimasa hanya yasamu Aiki.daganan yakoma Alhaji ibarhim kwangila. Anabashi kwangilar makaratu masallachi, rijiyoyi. Kumabaya ha inchi cikin Aikinsa shiyasa yayi Suna . daganan sukadawo cikin katsina suka gyara gidansu na rimi saidai insu dawo su sauka ciki dawowarsu da katsina shekara daya Aka haifi Dr Ahmed.
Abin yasamo Asali dalilin dayasa Dr Ahmed yatsani mace. Wata rana yadawo daga kano wajen Amininsa Dr Hafiz yakaimasa ziyara yazo daidai welcome to katsina saiyaga mace tsaye da hijabi tana daga hannu beyi niyyar tsayawaba Amma wata zuciyar tasa yayo baya cikin sauri tazo gabanshi ta tsaya yace cikin fuskar damuwa tace ya taimaka Mata mahaifiyar tace Asibiti bata lafiya. Yamikata gashi kuma bata da kudin zuwa . nan ya tausayamata domin ko yanayi shigarta zaka San tana cikin talauchi.
.
Dr Ahmed yace shigo tanashiga sunfara tafiya yace wane hospital ne , tacemasa General hospital, yace OK, sun isa General. Yakaita har can ciki tafito tace masa nagode. Yace babu damuwa yafito yace mushiga naga marar lafiya . domin nasamu Lada ko tayi murmushi tace nagode. Sunashiga cikin haske Dr Ahmed yaga wannan budurwa kyakyawace Amma talauchi yamaidata wata kalah.
Sun isa dakin da Aka kwantar da marar lafiya Dr duk yayi ma majinyyata sannu har suka isa gadon da wannan tanufa tanazuwa tazuwa ta tambayi wani. Yaro dabazai wuce 14 years ba Khalipa yajikin Inna ne khalipa wadda ta tambaya yace gayanan tunda kikabarta tana bacci haryanxu shi take yi kinsamo Kudin maganin domin tafiyarki Doctor yashigo sai fada yake Akan rashi sayen magani Kan lokacin.
Dr Ahmed yaji tausayi yaratsa masa zuciya yayi gyaran murya yace muga takardar magani kalipa yace Yaya Basma wannann waye. Tace shine naroki Alfaarma yarageman hanya Akan dawowata daga gidan Kawu Yusuf. Dr Ahmed ya Amshi takardar daga hannun basma wadda yaji sunanta bakin Kanneta yanufi pharmacy din cikin Asibiti yasiyo magagunan duk daaka rubuta yakawomusu yace su Kira likita sai ya gwadamusu yadda zasuyi Amfani dasu yace saidayaga komai ya kammalla. Yajuya zaitafi Basma tabishi daga baya.
Tace nagode Allah saka da Alkairi bawan Allah daban samu wannnan daga gareka Daban san yadda Zanyi yau ba. Dr Ahmed yace babu damuwa har sukaxo wajen motarshi zai shiga tace kabani number ka koma ringa gaisawa ko. Gashi zakatafi bansan sunankaba. Yace sunana Ahmed
Tace wow nyc name, nan yakaaranto masa number wayansa tasa. Yajuya yanufi hanyar gidan su dake Kwado.
Basma kuma tayi murmushi tace cikin ranta burina yakusa cika Zan Auri mai mota.Kuma kyakyawa (Tofaa daganin sarkin fawa)
One week later
Dr Ahmed ne zaune yana duba wasu papers, yaji wayansa naringi yana dubawa yaga new number ne Kamar bazai dauka Amma kawai yadauka yayi shiru can Akace hello yaji murya mace hello wake magana. Akacemasa Basma ce yace Basma wace vasma dominshi har ga Allah yamanta da bayaninta cikin ranshi tace Wadda kataimakawa rannnan nan tayimasa bayani yace Ayya!! Sorry nagane ykk yamaijiki tace dasauki har An sallememuma. Yau kwana Ukku Inna natayimaka godiya nancema tayi nakiraka kayiman kwantacen gidanku zatazoyi maka godiya. Dr Ahmed yace kicemata na hutar da ita basai tazoba saidai kibani Address naku inasamu time zanshgo ganinanta wani dadi yaratsa Basma (Tofah)
Nan tayimasa kwantacen gidansu Unguwar Yammawa.
Basma tana datse wayar ta waiwayen wajen wadda suke zaune tace burina yakusa. Cika munerrat wadda aka Kira da munerrat tace shakaman meyafaru Kawata Basma tace kinsa yau ko sati biyu baayi da kwanciyar umma Asibiti ba nan tafada yadda suka hadu Dr Ahmed. Kuma kinsa wani Abu Kawata wallahi yahadu daganinashi Akwai Kudi. Shiyasa Zan likemashi Har sai nasamu soyayar shi. Munerrat tace nadauka wannan burin yafita daga ranki nabaki Auren talaka sai mai Kudi Basma tace chabb!!! Inanh burina nanan na wayagayamiki Auren soyaya Zanyi Ai ingayimiki Ko yanzu nasamu wadda yafi Ahmed wallahi komin tsufanshi Zan Aureshi nataso cikin talaushi Kuma na Auri dan uwana talaka. Munerrat tace shegiya Kawata kina wuta, tace kedai bari. Dai muga zuwa Ahmed din.
****************************
****************************
Abangaren Dr Ahmed kuwa saida sukayi kwana biyu da waya da basma sannan yazo Gidansu Dayazo saiyakira wayanta wadda yayi saving da help, tafito tayimasa iso wajen innata tashiga dashi aga ibo masa ruwa. Cikin kwano duk lamba yanakaiwa yaji wani karni Amma hakanan yadaure yayi mashi kurba daya don karsu gane hakan.
Inna tayimasa Godiya kamar me nan yamike nan yana mikewa yazaro bandir yan 200 ya ajemata yace gashi nan. Inna kamar tayi Kuka taitayimasa godiya. Yafito waje Basma tabiyo bayansa Yaya Ahmed Angode Allah saka da Alkairi tana ta fari da idanuwa tasa wata Atamfa yellow da red. Wadda ta Aro wajen kawarta munerrat. Yace babu damuwa yashiga mota yabar unguwa.
Daganan tun lokacin Basma tashiga isar Dr Ahmed da waya tun bai kulata yana shareta har yana har yakai yana daga wayanta. Daganan fa soyayya tashiga tsakanin Dr Ahmed da basma. Domin basma tana da kyau ba laifi.
Daganan Dr Ahmed yaga halin dasuke cike yagyara musu gidan dasuke ciki, yashiga dinka Basma sutura Kala Kala masu tsada Daganan Basma tashiga wani girman Kai, tadinga jinta Kamar diyar shugaban Kasa, bata iyi ma yan unguwar su magana. Bata harka da sai da yayayen masu Kudi,
*********************************†**************†*******
Soyaya tayi Nisa tsakanin Dr Ahmed da Basma fa babu Kama Hannun yaro. Har yana niyyar fada ba. Daddy dinsa Akan Aiko Gidan su Basma domin ayi Maganar Maganar Manya kwatsam!!! Rannan Basma taje bikin wata kawarta diyar masu Hannu da shuni( domin Basma tacika shige shige inhar yayan masu shine)
.
Basma Anje bikin kawarta Anata yatsina saikace batasan wani Abu talauchi ba.
Anharde bisa Kujera Anata latsa wayar Tecno C8 wadda ko sati daya batayi ba Dr Ahmed yasiyamata itah. Saitaji sallama bisa Kanta tadago Kanta ta Amsa ciki ciki yace ko gimbiyar Mata zata bani damar zama. Tadago fuska tasake kalleshi taga bakalar talaka bane( kuji Basma da karfin hali)
Tace babu damuwa zauna yajawo Kujera Kusa da itah yazauna yacemata Barka da dare tace yauwa yace da farko sunana Mahmoud Kabir Nakowa. Basma tadago fuskarta A razane koshi yalura dahakan yace Kina mamaki ne Ko tace wadda nakeji A gari bama A gariba duka Nigeria Kowa yasan shi yace Shikam. Basma ta jinjina Cikin Ranta ( LaiLai)
Yace tunda kikashigo wurinan naketa hangeki Kuma naga kinyi mini Inasonki Kozan samu karbuwa wajenki Kuwa??? Basma tayi Murmurshi tace Hmmm.
Mahmud bai wurinba saida suka Kulla soyaya da Basma ya Amshi phone number ta tabashi Address din gidansu Ataikacedai shiyamaidata gida. Da akatashi daga party.
**********************************************************************************
Daganan fa Komai yacanza tsaninta da Dr Ahmed ta fara canza mishi inyakirata saitaga dama tayi picking yace Mata meyasa hakanan sai tace bata Kusa da wayar(kuma kunsan wani Abu duk tarrayar da Dr Ahmed betaba fadamaata wayeshi ba).
Rannan Dr Ahmed yazo Suna tsaye Basma wayanta sai ringin yake Amma taki dauka. Dr Ahmed yace Mata waye ke kiranki ne kinki dauka tundazu. Tace wata friend dina plashing danazo Dauka zata Katse ne. OK suka cigaba da zance Amma Abu takama waige waige dahaka sukayi dai bakwana yatafi yazo fitowa yaga wata mota itama tashigo Kuma bangaren Gidan su Basma tanufa Amma bekawo ma ranshi komai ba yatafi.
************************************************************************************
Kwatsam!!!!! Rannnnan Dr Ahmed bai Sanar da Basma zai zoba kawai yazo yanazuwa. Kofar gidansu yaga motar dayagani rannnan nan yakira wayar Basma saidayayi Mata Kira 3 Kawai yaga Basma tafito daga cikin wannan motar tana dariya. Naciki Kuma yaja yabar wurin jiyowar da Basma zatayi kawai taga Dr Ahmed ta firgita dagannishi Amma kawai tabasar tanufo wurinshi tace yallabai shine ko A sanardani zakazo ne. Yace kawai wurinki naji Ina shaawar zuwa ne.Basma Ina. Wayar ki nayi miki Kira Ukku bakiyi picking ba Kuma waye yazo wajenki yanzu questions 2 yajero mata duk tare sorry my dear wayana silance take banji Kirankabane. Wannnan Kuma wadda kaganni saurayin munerrat ne yakawo kararta Akan Abinda takemasa ne. Nan dai ta Dr Ahmed yadaina Zancen. Suka cigaba da firar har lokacin tafiyarshi yayi yatafi.
Lokaci natafiya kwanaki Suna Kara Yawa.Basma ce zaune. Ita da kawarta munerrat A dakin Basma wadda yasha yagyara. Munnert kecewa basma Yanzu ki kyauta Kina tarrayya da Ahmed Kuma Bikin da Mahmoud kingi 1 weeks. Bazaki Sanardashiba Gaskiya bazaki Aureshi ba??
Basma taya tsina Fuska tace dama Ai bamuyi yarjeniyaya dashi zau Aureshi ba ga ida Zan huta. Na hau motar danake so. Saina tsaya ma mai mota daya( 😊Rashin Sani) kyauttata da Ahmed bata wuce 10k zuwa 20k. Iyakarta takenan kiduba Mahmud Ko A sandiyar kyautar dayakkeman nabude Account yanzu Haka Ina 2 million ciki. Inbaki mantaba nafadamiki bazan taba Aure soyaya ba Aure Kudi Zanyi. Ahmed Kuma dama nafadamasa mun tafiya kauyen su Baba kawai sai dai yaji Sanarwa. Suka kwashe da dariya. Munerrat tace Amma baki kyautaba Kawata. Basma tace Kinga tashi mushiga Kasuwa Akwai Abinda nakeson siya.
*****************************************"************** Bayan Sati daya
Dr Ahmed zaune dakinsa yanajin labarai yanata trying din number Basma taki shiga domin yanason yasanar da itah cikin sati nan zai turo iyeyensa ( nufinshi inya fadamata gobe sai yasanar da daddy)
Anagama labarai kawai yaga Anhasko wani hall da Da mutane ciki anata cashewa can aka hasko fuskar Amarya DA Ango yaga kamar yasan fuskar Amarya Kamar sunsa Abinda ke ranshi Aka Kara dallaro fuskar zata ba Angonta Cake A baki. Kawai yaga fuskar Basma ya mike razane yace karya ne Ba Basma danasi bace Basma bazata yaudareniba. Kawai yaji Ana wakar Bikin Amarya Basma da Angonta Mahmud sunyi Aure. Dr Ahmed yazauna ragwab!!! Bisa Gado yace Basma nizatayi makahaka nixata yaudara Amma bata tabs nunaman ko Afuska ba .Amma babu komai Kanta ta cuta
Basai lokacin daya dauka yana tunanin ba shigowar text yaji awayashi shine yadauka yaduba yaga Basma ce. Tarutabamashi kamar haka
Aslm Ahmed dftn kana lafiya. Bawannan ba nasonka mutum ne mai Kallon labarai A kodayaushe. Kuma nasan zakaga wani Abu. Yabaka mamaki. Ba Abun mamakibane Domin ba muyi yarjejeniya dakai Zan Aureka. Inkuma Kana bukatar kudinka tundaga wadda kabiyama Inna Asibiti harzuwa yanzu zaka iya zuwa office din mijina Mahmud kabir Na kowa zaa biyaka bye bye.
Dr Ahmed yaja numfashi yagoge text din da number Basma baki daya
Daganan fa Dr Ahmed yatsani kowacce mace Aranshi Domin tunanishi duk haka suke( Anya kuwa)
Tofa shine Safeeya tafada ciwon so Dr Ahmed. Zata cimmma burinta kuwa. Kuwa .???
Wane hali take yanzu A Asibiti ???
KUBIYONI...........
0 comments:
Post a Comment