Monday, 12 February 2018

CIWON SO Page 6-10

CIWON SO Page 6-10
.
A bangaren  Safeeya can kuwa wajen 12 Am tafarka daga Allura bacci da akayimata.
Taga babu kowa A dakin sai ita daya cikin ranta tace nasan su umma suka kawoni Asibiti to Ina sukaje.
Tanacikin wannnan tunane taji  Antoro kofa ta waiwaiya taga waye.
Taga  Doctor  Sadeeq ne Family doctor dinsu ne.
Yazo har inda take yajawo kujerar yazauna yace Safeeya kinfarka ne,
Tace nafarka Doctor Sadeeq yace yanzu yakeke jin jikin naki ne  tace naji sauki.
Yace to Alhmdlh  safeeya. Yacemata safeeya meke damunki   ne Har ciwon zuciya yakamaki Haka irin wannan ciwon ne.
Dayayi yawa zuciya ke bugawa. Meke damunki haka gashi kinsa damuwa cikin ranki.
saffeya  tadukar dakanta kasa sai Hawaye cikin ranta tace Doctor Ciwon So mutumin dabasai  inayiba sai tsanata dayakema.
Amma bazan iya fadama kowan haka  tadago fuskarta tace Doctor kayi Hakuri bazaka iya jin komai bakina ba Amma Zan rage sa Abin cikin zuciyata insha Allah.
Dr Saddeq yace dayafiyi ko kima komai ga Allahh.kinji KO. Tace insha Allah. Yajuya zai fita Saffeyya tace Doctor Ina su umma ne???
Yace nace suje gidanane  domin baa bukatar kowa wajenki  sai gobe zasu dawo ne nima  inaga jikin yayi sauki  gobe Zan  baki sallama.
Haryajuya zai fita saffeya  tace    Amma... Doctor yace yane saffeya   yajuyo yadawo tace don Allah kada ka sanar da su Abba cewa ciwon zuciya ne.
Yace Mata meyasa tace masa don Allah kada kasanardasu Hakanan.
Kacemasu ulcer ne  ulcer ne.
Doctor yazare Ido  yace meyasa saffeya tace nidai Alfarma narokeka.tana niyyar Kuka☹☹
Yace tonaji Amma da sharadi?? Tace wane yace komai zaki cireshi cikin ranki . kidaina damun kanki. Inko baki dainanaba  zanfadama Abbanki Abinda kedamunki. 
Tace insha Allah Zan cireshi doctor. Yace yauwa safeeya. Yanzu saiki kwanta kicire komai.  Cikin ranki kinjiko. Ta gydamasa Kai ya juya yafita.
  Saffeya  ta rintse idanuwanta wasu zafafen hawaye suka zubomata.
Cikin ranta tace Ya Allah ka cireman Dr Ahmed cikin raina inba Alkairi ne ba. A tare Dani. Domin wani sonshi  yaji yana Kara shiga Ranta. (Allah sarki saffeyya)
WASHE GARI
Abba da umma harda Meenat domin tace bazata school saffeyya bata lafiya.  ( yar Uwa  Rabin jiki)
Suna shiga suka nufi office din Doctor suka iskeshi zaune A bisa kujera yana duba wasu file. Doctor saddeq yace Ahhh,,, Alhaji sannu dazuwa nan suka gaisa Abba yace doctor yajikin safeeya  ne yace  Alhmdlh zaku iya  zuwa  kuganta taji sauki yauma dasafe mun maidota dakin dakowa zai ganta.
Abba yace Alhmdlh to  Doctor yace muje nagwadamuku dakin suka rankaya suka nufi har dakin  suka iske safeeya kwance Meenat ta matsa wajenta sister yajikin safeeya tace mata dasauki saikawai taga Ashe tare suke dasu Umma tana kokarin mikewa ne Abba Aaaaa Safeeya kwanciyarki. Tace Abba da umma. Ina kwanku, suka ce mata lafiya lau Safeeya yajikin tace Alhmdlh. Sukace to Allah yakara sauki. Tace Ameen.Doctor yace Alhaji inkagama inason ganinka office. Abba yace to babu damuwa, Doctor yajuya yafita. Gaban saffeya yafadi.
Amma bata nunaba Abba yace bara naje umma tacemasa to.
Umma tace saffeyya kina iyawa Meenat takaraki toilet kiyi brush ko ruwan tea ne kisha, tace Eh Meenat takama ta suka shiga toilet.
Tadawo umma tahadamata tea mai kauri tana Kurba kadan kadan
Saiga Abba ya shigo cikin Fushi Gaban safeeya yafadi
Yace Safeeya mekika rasaAmmm....
.
Abba yashigo cikin fushi yace Safeeya meke damunki ne,haka, cikin inda zata Fara magana.
Umma tace Abba Yan  biyu me Doctor Din yafadamaka ne.
Yace man Ulcer ce takamata. Saboda rashin cin Abicin datake.  Mekikarasa rasa ne??  Ko meke damunki ne??
Safeeya tayi wata Ajiyar zuciya jin doctor befadi  Abba Abinda kedamunta.
Tadukar dakanta.
Batace dai komaiba. Abba yace Abinci kan yakare na aje wani.  A store.  Amma kifadi meye damuwarki.
Dahar yahanaki cin Abinchi ne?? Safeeya ta gigirza Kai Abba babu Abinda ke  damuna.
Yace Kuma Har ulcer takamaki haka. Ne. Banason haka kinji ko kidinga cin Abinci.
Tace Abba zandiga ci insha Allah  yace yauwa yanzu inki gama ci  farfesu Rago zakici Ko Faten   doya zakici ne. Ta shagwabe fuska.
Abba sai zuwa Anjima  Anjima naci yace A,a kidaure kici inki gama shan tea din
Safeeya tace Allah zanci Abba yanzu nacika cikina bakajiba.
Yace to shikennan Allah yakaimu Anjima to. Yanzu. Zan bar umma ki Zan tafi office sai nadawo. Allah sawwaka  tace. ameen  Abba.  Sai kadawo umma da Meenat sukace Allah yakiyaye yace Ameen  yajuya yafita.
Nan Safeeya tagama shan tea din suka dan tafa fira can  wajen  2 hour umma tace meza Samata takaradashi .
Tace Asamata  Fate doya yaji   wake da Alllayahu sai tashi Kamshi yake.
Can nahango  Aunty Saheeba itada Nana A Usman Suna   maida yawu Amma Safeeya taki yan  musu
Nandai Safeeya taci Harda tirsawawa umma taci da dan yawa. Ta Aje Tasha Magani da Doctor yakawomata dakanshi  yace shine zata sha insha Allah zataji sauki.
SCHOOL
Abangaren Dr Ahmed kuwa yau yashiga  school. Yanufi class dinsu Safeeya. Kawai sai nahango Dr Ahmed yana mika wuya yana waige waige ( Tofa meyake nema ne meya ke nema  kudai muje xuwa)
Yagama  Abinda yake yafita  babu Abinda  yanufa sai office dinshi yana zuwa ya zauna bisa kujera. Yadafe kanshi yace  meke damuna kardai Ace son wannan yarinya nake. Nan yafara tunanin domin  wata Rana   yashigo  school yaga Safeeya da Meenat    tundaga rannar Meenat tafara burgeshi saboda kamun kanta Amma yadinga karya ta zuciyar sa domin yace mace ba abin yarda bace. Daganan yafara  gwada Mata tsana domin  karyayi wasa sonta yashiga ranshi.
To Abin yakara rikicemasa tunda ga Ranar da  tazo har wurinshi.
Yau Kuma yashiga class dinsu begantaba ko tayi Fushi zata daina zuwa ne
Akan Abinda nakemata.
.
Asibiti.
Doctor ne ya shigo dakin da Safeeya take  yatadda ita daya su umma taje  gida  tadawo domin girkin Rana,
Meenat Kuma  tadan fita  tadawo, Doctor yace safeeya yakike jikin yanzu tace  Alhmdlh yace  to Zan baki wani magani sau 1 zaki dinga  shan shi   Kuma inkika cire damuwar ranki zakiji sauki sosai tace insha Allah,
Doctor zan kiyaye yace yauwa zuwa gobe insha  Allah Zan sallameki,
Tunda naga jikin naki yayi sauki.
Yajuya yafita. Bayan fitarshi saiga  Meenat tashigo tace sister Safeeya tace Naam sister  kindawo  Meenat Eh Aidama ba nisa na dan mika kafana ne. Nan suka cigaba da firar su  har Umma tadawo  tayo ma Safeeya Abinchi ta daban na marar lafiya. Nan tadaure taci domin umma tace inbataciba  zata fada ma Abba,
Washe gari
Da safe Doctor yashigo yaga jikin   Safeeya yaga  dasauki  yabata magani dasukayi Magana    yace taringa shan daya Arana Abba daban kan yatafi office  yabiyo   nan Doctor yake fadamasa yaga jikin  Alhmdlh zai bata sallama.
Abba yace babu damuwa.  Doctor yashiga ya rubutu takadar sallama  yabasu,
Abba yace suzo ya ajesu gida  sai yawuce office suka hada yan kayansu wadda sukazo dasu. Suka tafi
Abba yanashiga gidan ko yana Ajesu yanufi office
Safeeya ko Suna shiga tazauna bisa kujera domin tace tagaji da kwanciya  bari ta dan zauna ta huta.  Basu jimawa da dawo wa ba,
Saiga Haidar yashigo  yayi sallama ya iske umma da Meenat saffeyya, saffeyya naji sallamar shi tayi saurin rintse idanuwanta Kamar me bacci.,
Umma tace haidar Kaine shigomana   ya durkusa cikin ladabi yace umma Ina kwana, tace lafiya lau, haidar, ya wurin mamyn taka dajikin yace  Alhmdlh Ankwace daurin yanzuma taka kafar Amma ba sosai ba umma tace Ai sai A hankali Allah yakaro sauki. Yace Ameen umma,
Haidar yace  yajikin safeeya ne naso zuwa wallahi umma   Aikin office ne yayi yawa  dayau zance Sai naga shigowarku Abba ya. Ajeku.
Umma tace babu komai Haidar,
Dasauki sosai tunda An sallamemu  taji sauki. Umma tawaiwayen inda saffeya take Safeeya!! Safeeya!!!!
Cikin Alamun Kamar tana bacci naam umma  tace Haidar ne yazo ganinki. Cikin daure  fuska tace Ina kwana yaya Haidar cikin Fara' a yace lafiya Lau saffeyya  yajikin tace Alhmdlh, daganan bata karacemasa komai  sai da Meenat yake fira jefi jefi har yamike yatafi,
Dama umma tashiga ciki tadan gyare gyare kwana biyu  baiga gyaraba.
Meenat tadawo kujerar da Safeeya take sister wai meyahadaki da yaya haidar baki sakar masa fuska   ne, saffeyya tace babu komai keh tajawo wata first
School
Dr Ahmed ne zaune bisa kujera yana hada wasu file  yaduba Agogon Hannusa yaga lokacin shiga lecture yayi, Kuma class dinsu Safeeya zaya,  yanashiga yagama Abinda yake, Amma da kalleshi kasan yanacikin damuwa ( Abinka da miskili)
Yanufi office yazauna yace meke damun wannan yarinyar yau kwana3  batazo school ba ko yar uwata banganiba    gashi yau Friday.
Gaskiya rannan Monday inbatazoba Zan tambaya wadda naga  Suna zama  tare naga ko lafiya duk wannnan Maganar yanayinta cikin zuciya
Domin yanzu so  safeeya kawai yaji yana shigan zuciyarsa ( Tofa su Dr Ahmed Anshigo wajen)
Domin ko ga basma baijin wannnan beyi hakaba
,
Safeeya ce kwance bisa gado tana tunanin yadda zata fidda son Dr Ahmed cikin ranta,.
Amma  me datafara tuninshi zataji Kamar Anakaramata son shi naji take Kamar tajawo Ranar Monday.  Taje school don kawai taganshi, Amma tayi Mata kanta Alkwali zata ragema zuciyar ta tuninshin insha Allah,
 
Meenat tace shigo dakin datake sister  Kizo inji Umma ga girki can Angama, safeeya ta yatsina Fuska Kai sister Abinchin nan basai Anjima zanci ma Meenat tace A,a umma tace nataso ki har muntafi tare,
Badon safeeya nason cin Abinchi ba ta  mike suka nufi Dinning,  tadan tsakura ta mike.
Bayan Abba yadawo  ne   baya shigowa sai yayi sallar ishai to inyashigo Bayakara fita sai kuma gobe. Inba wani Abu mai muhimmaci ba ne zai fiddashi.
Abba ya shigo yatambayi safeeya yajikin tace Alhmdlh Abba,    yace yauwa dafatan dai kinacin Abinchi sosai.
Meenat tayi karaf tace Abba bataci sosai dan kadan kadan takeci. Safeeya ta wurga Mata harara tace karya take Abba inachi sosai. Anya kuwa tace Allah kuwa. Yace inma yadda Meenat tafada ne kidaure kidinga ci kinji ko. Tace shikenan Abba,
Abba yajuyo wurin umma yace ke babu Abinda zakicene Umma yan biyu tace Babu Abinda zance ni.,   Nan dai sukayi firarsu Kamar kullum har lokacin  tashi yayi kowa yatashi yanufi makwancin sa. Asuba tagari.
Monday.
Monday babbba Rana ko nasara na tsoranki.,
Kamar yadda suka Saba sukatashi suka Kimtsa suka gama Abinda suke sukayi wanka. Amma jikin safeeya suku suku.  Kamar  marar laka jiki Har dai Meenat ta Lura da hakan
Tace sister yane naga kin koma wani kalan kina komai A hankali ne
Safeeya tace babu komai  Meenat tace Anya ko Safeeya tace Haba babu komai, Meenat taja bakinta tayi shiru,.
Safeeya kuma tunanin take yadda yau yazasu kare Dr Ahmed ne  yau kuma dame zai zo Mata ne
Shine jikinta duk yayi sanyi. Haka har Meenat tayi Mata Magana.
Sun shirya saffeya tayi shigar Atamfa  yellow And red tadora hijab yellow domin red din yafi yawa cikin Atamfar shine saita Dora yellow hijab,
Masha karkuso kuga yadda Safeeya tayi kyau gashi dama rashin lafiya datayi fuskar tayi fayau. 
.
Ko Meenat sai datace   Masha Sister kinyi kyau Wallahi. Safeeya murmushi kawai tayi
Nan suka fito suka gaida umma da Abba sukayi Break fast,  sukayi masu Allah yakikaye  suka fito sukaja mota suka nufi school.
Daidai   su shigarsu school da  mota  shima Dr Ahmed ya shigo. Sukayi parking   suka fito  fitowar su  Idon Dr Ahmed yakai   Kansu  yakara waiga yaga itace dai ba idonsa ke masa gizo ba( su Dr Ahmed)
Yaga sun nufi class  wani dadi ya ziyartamasa zuciya kaganninta kawai dayayi .
Kagagere yake karfe 1: 30 pm
Domin sai sannan yake da Ajninsu. Don kawai yaganta .
Karfe 1: 30 student sunyi sallah sun dawo
Kamar jira yake kawai saigashi yashigo    cikin yanayi daya Saba shigowa ( miskili kafi mahaukaci)
Amma Abin kadan yawaiga wajen da Safeeya take  zaune can Dr Ahmed yagama Lesson. Yana tambaya kawai yatada Safeeya Gabanta yafadi ya jeho mata wani question,  Allah yaso ta iya wurin tabashi Amsa tiryan tiryan
Cikin Harshen turanchi,
Dr Ahmed yace what is your name?? Saffeyya my name is Safeeya  Suleiman, ok sit down class kowa ya mamakin tambayar  sunan Safeeya dayayi  Amma kowa dai yayi shiru.
Yana gamawa Abinda yake  yace Gobe zanyi test  yasa kafa kawai yafita.
Dr Ahmed daganan mota yaja yafita yanufi gida  yana shiga  ya iske  hajiyarsa bata falo dakinsa kawai yanufa yasakarma kanshi shower. Yafito  domin jin kanshi yake cikin nishadi.   Muryar Safeeya kawai dayaji.
Abangaren Safeeya kuma mamakin Dr Ahmed take yadda yayi Mata yau take . murna kawai take wannnan maganar dayayi Mata taji zazzzkar murysa.kowa ya fahimci tana cikin farin cikin
Washe gari.
Su Meenat sungama shiri kamar yadda suke  Amma sunata sauri domin Dr Ahmed First, Kuma test zai musu,Agurguje sukagama  komai suka nufi school Suna shiga  class ko minti biyar baayiba yashigo.
Kowa yasan dai test zaiyi dama yanashigowa yarubata test yace minti 20 yabada, minti 20 nacika kowa ya kammala. Domin question din masauki. Yayi
Yawaiga wajen saffeya yace  kitttaroman kikai man office. Baijira Amsataba yafita.. Gaban safeeya nafaduwa  ta tttara   ta nufin office din tana  tunanin kowani  wulakacin zai Mata
Nasaudakar da wannan page din gareki ( Mumcy husnah)
Allah yakara lafiya.
.
Safeeya Gabanta nafaduwa tanufi office din Dr Ahmed Tayi sallama yabata izinin shigowa jikinta nadar nadar.
Tace sir ga papers din  OK, yasa Hannu yakarba  Yacemata thank you,   tajuya. Tafita
Dr Ahmed yabita da kallo  Har tajuya tafita,
Muryata kawai dayaji yasa shi wani farin ciki. Da nishadi.
Safeeya nakomawa  Meenat tare ta sister wani wulankacin yayi miki ne. Safeeya tace girgirza Mata Kai tace A,a.
Lokacin tashinsu school yayi  sunnufo zasu dauki  Mota  suga Dr Ahmed tsaye wajen Motar shi yana latsa waya,  har suka shiga suka tafi.
Nan ko Ba latsa wayar yakeba kallon safeeya yake Afaikace.  Har sukaja motar suka tafi. Sannnan shima yashiga tashi.(Ciwon so fa yakama Dr Ahmed)
Abangaren Safeeya Kuma har suka isa gida datuno  Kalmar thank you,
Da Dr Ahmed yafadamata sai taji kawai cikin Nishadi, Har wani murmushi farin ciki take.
Suna zaune  Suna cin Abinchi Meenat kecema Safeeya  gaskiya sister nayi mamakin Dr Ahmed,
Safeeya tace wurin me  kenan, tace yadda yacanzamiki mana,
Rannnan fa har tambayar sunanki yayi, yau kuma harda cewa ki tatttara papers kikaimashi,
Bakiji yadda class Ake surutun hakaba Wallahi,
Safeeya saidai tace uhum sukacigabada da cin Abinchi, Bayan sun idar ne  lokacin   sallar La' asar ne suka tashi sukayi.
Bayan sungama sukadawo Falo. Suna Kallon AREWA 24
Suna shirin Muna  Kwarya
Umma dabaman batanan tafita zuwa  Gaisuwa matar Abonki Abba tarasu hadarin mota,
.
Bangare Dr Ahmed kuwa yana shiga gida ya iske hajiyarsa tayi tagumi  Har yayi  sallama  batasan yashigo ba,
Saida yazauna  yataba Hannunta Sannan ta firgita Ahh Ahmed yaushe kadawo ne, yace nashigo  ita sallama  bakiji Ba,   ne meke damunki Hajiya sai kawai yaga Hawaye sunbiyomata mata, Ahmed yace meke damunki ne Hajiya  harda  Hawaye don Allah  kifadaman kowani laifi na Aikata gareki bansani Ba,
Hajiya saudat tace babu Abinda kayiman Ahmed  Ina tunanin yan uwana Yaya sule, da yaya mustapha,
Tunkafin A haifeka rabon danasu idanuwana Basan suna da raiba ko sun mutu,   nan tabashi Labarin sanadiyar Batansu, Dr Ahmed yaja Numfashi yace  ki kwantar da Hankalinki Hajiya   insha Allah  inda rabon zaku hadu  zaki gansu. Nan ya kwantar. Mata da Hankali,
Yatashi yashiga ciki  yawatsa ruwa yayi sallar la'asar yahau gado. Yakwanta,
Yajawo wayarsa yakira Amininsa wato Hafiz, suka sha firar su irinta Abokai.
Bayan sungama wayar Dr Ahmed  yaruntse idanuwansakawaiyaga  saffeyya nayi mashi Murmushi, Dr Ahmed yayi saurin bude idonshi   yatashi zaune yace Meke damuna Kar dai ciwon so yazautani  ita batasan inayiba ( haka dai kace)
Amma tayaya Zan furtamata ne can kawai naga  yayi murmushi  nikaina Hafsat basan mumrmushi meye ba.
Amma mujezuwa
Saffeya da Meenat ce zaune   Safeeya  nayima Meenat calabar   umma Kuma tana zaune  suna fira jefi jefi  Saiga maigadi yashigo yayi sallama   ya agaidasu  yace  Hajiya wai Ana Neman Hajiya safeeya waje  wani mutum yace nakira  mashi ita, saffeya tace ni Akace kakira, yace Eh,
Safeeya tace jeka kace batanan, umma takatseta tace jeka    Audu gatanan, Safeeya tazumboro baki   umma tace tashi kije bakisan ko wayeba kikasan koda meyazo tunda  baa taba Aikowa kikasan komeya kawoshi,  tashi kije Kafin  Abba Ku yadawo kinji  Safeeya tashi ta zuri hijab tafita Meenat tanata tsokanarta  tacemata iyee su sister Anyi kasuwa. Safeeya kamar tayi Kuka  har didiren kafufuwa, umma kina jinta fa, saida umma ta tsawatar ma Meenat sannan ta kyaleta,
.
Saffeyya kuwa tana fitowa    tanufi wajen motar dataganni kuma mutumin ya juya baya   bata fuskarsaba   tayi sallama aka Amsa sai taji kamar tasan muryar Amma kawai tashare cikin ranta tace tunda nayi sallama   nafita hakkin kowaye  bazan Kara magana ba tafi minti biyar tanacewa wannan mutumin dan rainin wayo ne fa zsnshiga gida. Kawai taga Anjoyo fuska waza taganni...
.
Joyowar fuskar da Zaayi watazagani Dr Ahmed Safeeya tayi mutuwar tsaye tarasa bakin bakin Magana. Can dai tayi ta maza.
Sir... Inayini yace lafiya lau safeeya Kina  lafiya tace masa lafiya lau. Safeeya tace yallabai meke faruwa. Yayi murmushin dake karamasa. Kyau  Safeeya tayi mamakin  murmushi sa domin tunda take bata ba ganin murmushin sa ba.
Dr Ahmed  yace zakiyi mamakin ganina Safeeya  Amma ba Abin mamaki bane.
Safeeya cikin ranta tace kuma meke tafe dashi ne  yama Akayi yasan gidanmu.
Yakatsemata tuninin datake yace safeeya,  tace  Naam sir, yace kidaina kirana da wannnan suna kirani da masoyinki,  mai fatan zama Uban yayanki insha Allah,
Safeeya tawani firgita  tayi kasake kawai kamar marar rai, Dr Ahmed yace zakiyi mamakin haka  daga gareni. Domin kinga tsanar danayi miki cikin school,  
Safeeya bawani Abu yajaman tsanar kowace mace ba Nan yabata labarin soyayar sa da   Basma da irin yaudarsa datayimasa.
Yace daganan naji natsani  soyaya Kuma bana ra' ayi kowace mace,nadauka duk Haka suke,
Amma  Farkon ganin dake naji komai na nema yacanza daga gareni shine nadukkan yimaki Abu natsana konaji  ba sonki,
Amma zuciyata ta Karyata haka  gani  da kokon barata gareki. Duk wannan bayanin dayake safeeya hawaye kawai 
Tana girgiza Kai tana tafiyar baya baya hartashige gida da gudu. Tabar Dr Ahmed tsaye.
Tana shiga ta iske su umma basu falo  sun shiga ciki Domin lokacin sallar magariba yakusa. Tazauna Bisa kujerar Nan tafashe dawani kuka, tace cikin ranta Dr Ahmed yagano inasonsa shine Zan  biyo wata Hanyar salon wulakanta tani ko shine zai ce yanasona karya ne basona yakeba yaudararata zaiyayi ya wulakantani,  Nan takara fashewa da wani sabon Kuma,
Cantaga bafa ita kadaice kar umma ko Meenat tashigo ba kuma hujjar dazata bada, 
Tatashi tagoge  Hawayen ta tashiga cikin Domin taji Anfara tada sallahr magariba,
Tanufi  Dakinsu taddata Har Meenat  tadata sallah itama toilet kawai  tashiga tadaurayo Alwalla,  tadata sallah,
Bayan sun idar da sallah ne, sunyi Addu' a sun mike ne, Meenat tana linke Carpet, din sallah, tace sister wai waye yazo nemanki, mai Neman Kuka Anjefeshi da kashin Awaki.
Kawai saffeyya tafashe da Kuka tace wai Dr Ahmed yazo nemana, wai sona yake sister  kawai yazo ne yaciman mutunchi ya wlakantani,
Meenat tayi murmushin kawai tace sister meye ba Allah ne yakarbi rokonkibane, ya mallaka miki Abinda kikeso,
Safeeya ta figirt tajoyo wajen Meenat, tana manata Kallon mamaki, Meenat tace karkiyi mamakin jin maganar danayi miki sister,    
Tun wani lokacin da dadddre Kina sallah  naji kina rokon Allah, Akan Haka,  
Nayi mamakin dabaki furta mankahava, nima saina kyaleki, 
Saffeyya taja wani numfashi,
Meenat tace. Abinda zakiyi kawai kiba Allah zabi kawai.  Tashi muje falo. Suna fitowa suka iske umma zaune,
Suma suka zauna  Umma tace saffeyya wayene yazo wurin ki dazu ne,
Kunya tarufe saffeyya tarasa yadda  zata fadamata,
Umma tace takadara, to da kinata sunne sunne baki zuwa, Ashe kinsan kowaye,
Saffeyya tace Allah A,a 
Umma tace Ummm
Nan sukacugabada firar Har lokacin  sallar ishai  yayi sukayi,
Abba yadawo sukaci Abinchi. Lokacin bacci yayi kowa yanufi makawancinsa.
Bangeren Dr Ahmed kuwa  saffeya nashigewa gida tana Kuka  yafi minti biyar tsaye sannan yaja mota yafita, yana tunanin to me take ma Kuka, hakan meyafaru, 

0 comments:

Post a Comment