Tuesday, 6 February 2018

'Yar Talakawa Part 3 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI



'YAR TALAKAWA Part 3
.
Kasa tabuka komai tayi, wani kamshi kawai ke fita daga kirjin sa, yana bugun hancin ta, dara daran idanunta   ta dago ta dan kalli fuskar sa, mashaAllah, tun daga cute pink lips dinshi ta fara kallo, zuwa pointed hancin sa, tana kara gaba takai eyes din sa, medium ne a lumshe suke sai zara zara eye lashes dinsa, ohh God kawai ku sinfantashi da (shakti arora ko arjun kapoor).
Amir ne yayi motsi, tabi  a hankali tadan  zare jikin ta daga nasa, kara jin hannun sa tayi ya jawo taaa , ta tafi luu, fuskukin su suka hade, da juna,  lips dinsu suka gaisa da junaaa....a take ta lumshe idanunta.....
Gaba daya lumfashin neena sai daya tsaya cak na wasu sankwanni, jin kamar amir na niyyar mikewa yasa tayi kokarin zare hannun prince ta mike,  a hankali ta sauko daga gadon, ai kuwa tana dira amir na bude ido, yana ganinta ya amir da sauri zai kira sunanta, tayi saurin zuwa ta rufe masa baki, taja hannun sa suka fito daga dakin.
Suna shiga dakin amir din, ya rumgume ta yana murna, itama murnar take , tace little master , muje nayi maka wanka time ya kusa, amir yace ok, suka shige toilet. 
.
Da rana wuraren karfe 12 neena ta gama gyarawa amir dakinsa, ta wanke toilet, ta fito dan taya inna ladi aiki, dan haka take kullum, idan ta gama nata sai taje tadan taimaka mata.
Tana shiga kicin ta iske zuby a bakin fridge,  zuby ta juyo tace neena, ashe ba sauran milk shake din amir , sai sauri nake nazo na dauki dayan daya rage, inna ladi dake yanka cabbage tace, aikuwa dai dazun faruku ya shigo ya dauka, wai yana jin shan wani abu mai dadi..zuby ta tare lumfashin inna ladi, shine sai kika nuna masa milk shake din.
     Neena tayi dariya, anty zuby bari nayi miki wani now, zuby ta ajiye bottle water din hannunta, inaaa bazai yiyuba, tayi hanyar fita tana cewa, bari naje na amso, shi ya faruk dinnan ance masa shi kadai keson kayan dadin, amso zanyi tayi kofa tana masifa, neena ta bita tana cewa anty zuby ki bar masa nayi miki wani, inna ladi kuwa mai zatai inba dariya ba, abincin amir akewa wannan hadamai.
Direct side din abba sukayi, neena na baya. Suna shiga suka iske zarah kwance tana kallon keeping up with the kardashians, zuby na shiga tace, sisi ina ya faruk, kafin zarah ta amsa mami da abba suka fito da gani fita zasuyi, zuby tayi gum ta gaida dasu, neena ma ta gaishe su, suka amsa musu a sake suka fice.
Zarah ta mike tana cewa, kee sisi lafiya kuwa, ji yadda kika fito fa, kayan barci a jikin ki, gashi kinsan Sargents din ya prince na around,  zuby taja tsaki, for goodness sake ina ya faruk?, zarah tace yana gym a garden.
Zuby tace good,tayi waje fuuu..su neena na biye da ita suna mata dariya (dama zuby akwai masifa, ga saurin yin fushi)
.
Suna isa ta shiga rumfar gym din a masifance.
   Aikuwa ta iske shi yana motsa jiki yana sipping din milk shake din.
      Tace haba ya faruk,! Sai ka dauki kayan.....bata karasa ba ta hango prince a kwance yana press up,  da kyal ta iya karasa "kayaaan"
Prince ya mike, fuskar nan kamar zaki a tamke, ya kalle su, yace da muryar sa kamar mai jin barci, kee baki da kunya ko! Kin kwaso jiki kinzo ki masa fitsara, ji ji, ya nuna jikin ta, wit those slping clothes kika wuce ko'ina kika zo nan! Zuby tayi wiki wiki kamar mai shirin yin kuka, su kuwa su neena baya baya sukayi,  suka sulale abunsu.
    Ranar kuwa zuby sai da tasha punishments a wurin prince, yaya faruk kuwa yana gefe yana mata gwalo danshi akwai shi da zolaya.
,
Ranar friday, da sassafe mum ta shiga shirye shirye, mami ta shigo itama sai taya ta takeyi, zuby suna daki tare da neena da amir, wani movie suke kallo a laptop din zuby din.
        Zarah ta shigo dakin a gajiye, sisi kinji dadin ki wallahi, yau munci uban mu wurin, dr Ak saleem, kinga uban questions , zuby ta kwashe da dariya, kai dan Allah, kice yau su sumzzy anci uban cin biro, zarah tayi tsaki ba sumzzy kadai ba yau wallahi harda wannan, saleem din kin gane shi ai, zuby ta sake kwashe wa dariya dont tell me mai yawan zuwa cafeteria dinnan.
   Sai firan su sukeyi, su neena kuwa hankalin su gaba daya a kallon da suke yake.
Sun sauko, suka iske falon an gyara shi sosai, zuby ta zarah, wai wane irin bakine zasuzo yau dinnan, zarah tace nida na dawo dazun..mum ce ta fito daga kicin tana kiran neena, neena! Neena! ,  neena ta amsa, na'am mum, mum ta mika mata kudi, ga wannan kije driver ya kaiki ki siyo min fruits , neena ta amsa kudin ta riko hannun amir muje ka raka ni.
Suna kai wa bakin kofa, su mummy suma suna saka kafa, ikram tasha ado sosai, cikin fitted gown red n green, tayi kyau sosai, sai fuad .
   Da sauri neena taja baya, ta gaishe su, basu ko amsa mata ba sukayi kici, amir ya yace da fuskar shi a shagwabe, anty neena kinga fuad yazo, naje muyi wasa,? Neena tayi murmushi, kai dai bakason rakani, ta saki hannun sa taje yaje suyi wasan da fuad din.
Tana fitowa wurin balcony,  sukayi karoo da MOHA da sauri taja baya tace, kayi hakuri ban lura bane, moha ya kalli fuskar ta, a zuciyarsa yace, she's cute really.....ya wani kura mata ido....
.
Neena ta zagaye shi tayi gaba, moha yayi murmushin yan duniya, ya shige cikin gidan.
Neena ta samu idi driver a zaune bisan benci suna fira da mai gadi, ta fada masa mum tace ya kaita garki market tayi sayayya.
Suna isa , taje ta siyo duk abunda mum tayi mata list. 
      Suna yin parking, ta fito ta zagayo wurin but, ta kwashi ledojin kayayyakin da suka siyo, ledojin sun mata yawa sosai a hannunta, da kyal take tafiya ma.
Faruk ne ya shigo side din, yana hango ta tana cicciban ledojin, yayi murmushi, ya daga murja yace, nanny!  Neena tayi saurin juyowa, tana ganin shi tayi murmushi,  yaya faruk" faruk ya karaso wurin ta, yasa hannu ya amsa ledaoji guda biyu, let me help, neena tayi smiling daka barshi ya faruk, faruk yace kaji ta sai kace zaki iya dauka ke day.
.
Suna cikin conservation dinsu, motar ya prince ta shigo cikin gidan, motoci biyu ne? Sojoji suka fito daga dayar motar, sukayi saurin zuwa suka bude wa prince kofar mota, yana fitowa sukayi saurin sara masa, fuskar nan kamar garwashi.
Yazo fuu zai wuce su faruk, faruk yayi saurin cewa ya prince harka iso, dama dad ne yace na kira ka, prince ya kada kai kawai ya shige ciki.
    Neena kuwa da kallo ta bishi, a zuciyar ta tace, shi kullum fuska a daure.
   
   Ta kofar kicin suka kai kayan, mami da inna ladi ne a ciki, mami tace wa faruk, na'im din ya iso ne? Faruk dake daukar apple a leda yace ehh yanzu ya shigo, mami tace kaima sai ka shiga dan su abba na falon, faruk yace toh sannan ya fita.
Neena kuwa zama tayi, ta shiga taya su mami aiki, ita dai tana son ta koya girkin zamani.
     
Bayan sun kammala komai da inna ladi, ta dauki abincin ta taci, sannan tace wa inna ladi, inna bari naje nadan watsa ruwa, tayi saurin ficewa.
Tana zuwa dakin ta, ta cire kayan jikinta, ta dauki zanin ta ta daura, dama toilet dinta ya samu matsala, dan haka sai ta saka hijabi ta fito ta shiga dakin amir, ba kowa a ciki su amir na side din mami tare dasu zuby.
Cire hijabin tayi ta shige toilet.
Bango kofar dakin yayi ya shigo, ya fada kan gadon yana sauke lumfashi, ya naushi gadon yace ohhh darm it !!! Ya zakayi su dad su masa haka, a fili ya furta a hate Woman, dey r all d same!!!!!.
Neena na kammala wankan ta, ta dauro zani ta bude kofa, prince najin ana bude kofa yayi saurin kallo kofar, sukayi for eyes da neena, da sauri ta koma toilet din tana dafe da kirjin ta.
Prince yaja tsaki, mtswwww ita kuma wannan fa, me zan gani a jikin ta, yarinya karama da ita sai shegen fi'ili, harda su yawo da hijabi, ya sake jan tsakin, ya gyara kwanciyar shi, idan bazata iya fitowa ba sai dai ta kwana.
Motsin bude kofar dakin yaji, yayi saurin rufe ido, a tunanin sa mum ce.
.
Ikram na shigowa dakin, ta zauna kusa dashi, tana yanga, prince najin kamshin turaren bana mum bane ya bude idon shi, ikram ya gani zaune kusa dashi ta kura masa ido," ita dai tana son prince kamar ranta, shiyasa ta matsawa mummy tayi wa mum maganar , gashi har zata mallake shi" 
     Kee, prince ya fada, dan yadda ta wani kura masa ido kamar zata cinye, ikram tayi fari da ido, tayi murmushi, ya prince dama su mum ne sukace nazo mu fahimci juna, prince ya yamuste fuska, bai ce mata kala ba, wayarshi tayi ringing,  ya dauka , sai da ya dauki mintuna yana magana a wayar, ikram haushi ya ishe ta, taso suyi fira.
Neena dake toilet kuwa tana jin duk abunda suke cewa, tabe baki tayi, tace, aikowa wannan ikram din zata sha fama.
Mikewa prince yayi daya gama wayar, ya kalli ikram, sai muje mu fada musu ko? Wani kolulu ya tsaya mata a wuya, toh mai zasu fada, bayan basuce komai ba. Prince yayi gaba ta mike ta biyo shi.
Neena najin sun fita, tayi saurin bude kofa ta fito, tai saurin zuwa ta bude kofa zata fice itama.
Dai dai lokacin shima prince ya bude zai dauko wayar sa daya manta, sukayi karoo gumm
   Allah ya taimaka, bata da tsayi , kanta ya bugi korjinsa, jin santsin kafar ta zai fadar da ita , tayi saurin sa hannayen ta ta riko shirt din prince ta kankame shi tsammmm
.
Wani yarr yaji, da sauri yasa hannun sa a kafadar ta, ya ture ta, tadan buge da bango, yayi saurin karasawa ya dauki wayar sa ya fice, neena tayi dan guntun tsaki, ya zata ko wacce mace ce zata so shi, dan kawai yana da kyau, tayi wucewarta daki, dan saka kaya.
Prince na saukowa kasa, ya iske su abba, dad, mum, mami, mummy, faruk da ikram duka zaune, yana saukowa, abba yace, yauwa na'im zo muji ya kukayi, dan bama so bikin ya dade.
Ikram ta mike tazo inda prince ke tsaye, tace, mun riga mun fahimci junan mu, kuma mun yanke shawarar, ayi bikin nan da wata biyu.
.
Falon ya dauki, alhamdulillah, mum sai dadi takeji, tasan ikram wayayya ce, zata ja ra'ayin prince ya sake.
Dad yace toh yayi, Allah ya kaimu, sannan ya kalli faruk, kai kuma fa, dis week zaku kammala nysc din ai ko?, faruk yace eh dad, abba yace munyi maganar da mamin su, mun yanke shawarar hadashi da DEEJA (diyar yayar mami), faruk yayi saurin kallon abba, yace but abba, mami ta zungure da kafa dama kusa suke, abba yace but wat? Bamu isa mu zaba maka mata bane?, faruk yayi shiru.
       MOha ne ya shigo rike da hannun  su amir da fuad, sunyi kaca kaca da milo, suna shigowa mami ta mike, ohh God yaran nan bazaku kashe mu ba.
      Dad da abba sai dariya sukeyi, yadda fuskokin yaran yayi dame dame da milo, shi kuwa prince yanan tsaye fuskar nan a tamke, haushin ikram yakeji kamar ya shake ta.
Mum ma ta mike tana cewa, moha ina ka gansu wadan nan kuma?, moha dake shirin zama yace, mum a bisan dinning din gidan abba, suna ta faman wasan su da kwankwanin milo.
     Mummy tace, ina nanny din amir, sai tayi musu wanka, dan yanzu muke shirin tafiya.
      Mum ta kwalawa neena kira, sai gata cikin sauri, mum tace kinga mutuminki ko?, neena tayi murmushi tazo taja su sama, moha sai binta da kallo yakeyi. Faruk ya mike yayi waje abunsa.
.
Side dinsu ya dawo, yazo zai shiga daki, yaji su zarah nata kwasar dariya, dakin ya nufa yayi musu tsawa," Kai da Allah kuyi wa mutane shiru abeg!!!!! Gaba dayan su suka kalle shi baki bude, ya faruk lafiya??! Faruk ya karaso cikin dakin ya zauna kwajab a kujera, wai ni za'ai auren hadi, ai ko da anyi wa ya prince, ni bai kamata ba.
Zuby ta mike auren hadi??? Zarah tace wai meke faruwa ne a gidan, faruk yaja tsaki, sanna ya fada musu komai, zuby tace lallai sisi ya kamata muyi maza mu fito da mazaje, kafin ayi mana irin wannan hadin, zarah tace aikuwa dai, dan ni bazan iya zama da wanda bana kauna ba.
     Nan suka zauna suna ta firan su, da kuma kwantarwa yayan nasu da hankali.
.
Prince kuwa bayan anyiwa su mummy,  rakiya, dakinsa ya koma, ya zauna yana nushin hannun sa, gaba daya garin da gidan suka ishe sa, mikewa yayi ya shiga hada kayan sa, gobe zai koma lagos, dan bazai iya zama mum na hada da wannan mayyar ba.
      Yana cikin hada kayan, amir ya shigo da gudu, yana fadin, papa papa!  Ni bana son asa min riga now, kace wa aunt neena kada ta saka min, kafin prince yayi magana, neena ta shigo itama, gaba daya ta manta ma, da wane dakine, so kawai take ta sakawa amir rigarsa.
    Amir ya fara zagaye dakin, sai binsa takeyi, prince yayi tsaye yana kallon su, can carpet din da ke yashe a kasan floor din, ya kwashe ta, ta tafi suuuu ta fadi gwajam.
Wani irin dariya faduwar ta, ta bawa prince, ya shiga kyalkyata dariya, hahahaha
Neena ta juyo ta kalle sa, wani radadi duwawunta keyi, wani haushin prince taji kamar mai....shi kuwa harda su zama dan dariya, hahaha yana nuna ta....
.
Neena tayi dan tsaki a zuciyarta, ashe dama yana dariya, idan yaga abun mugunta, mtsw, tayi yunkurin mikewa, wani azaba taji a hannunta data dafa, washshshs....
       Tayi ihun wahala, amir yayi saurin dawowa wurin ta, yace aunt neena, kinji zafi ne? Neena ta kalle da kyal tace, eh little master,  amir ya mika mata hannun sa, yace let me help u, ta rike hannun, zata mike ta sake jin azaba a bayan ta, da sauri ta zauna, har sai da tayi dan guntun hawaye.

Amir na ganin haka, yayi saurin mikewa yayi gun papa dinsa.
Papa stop laughing,  aunt neena taji ciwo fa, prince ya kalle ta da gefen ido, yaga yadda take hawaye, yaji dan tausayin ta, dan yasan tiles din dole mutum yaji azaba.
Ya kalli amir, boy wat should I do, ai ita ta jawa kanta ko?amir yayi saurin girgiza kai, noo papa, nina ja mata, aunt neena dont knw hw to run, pls papa help ha, yayi folding hannunsa, prince ya wani dauke kai, amir ya sake shagwabe fuska, help ha like d way u helped me, lokacin dana fadi a steps.
Prince ya juyo ya kalli ya kalli neena, sannan ya sake kallon amir yace, should I?" Amir yayi saurin kada kai, yes papa.
Prince ya mike yazo kusa da neena, sai daya dan dauki lokaci sannan , ya mika mata hannu, neena tadan kalle shi, kamar kada ta amsa, sai kuma taga bazadai ta iya mikewar ba ita daya.
.
Ta mika masa hannunta, ba karamin mamaki prince yayi ba, a zaton sa tunda YAR TALAKAWA ce, hannunta will b hard, amma sai yaji laushi, itama neena mamaki taji, danjin hannun prince da tayi laushi kamar ba aikin soja yake ba.
Ya taimaka mata ta mike da kyal, tazo zatayi one step, taji kafarta ta rike, da sauri ta sake komawa ta zauna, ta share hawayenta, sannan tadan jawo kafar ta duba.
Tadan bugu da centre table,  amir yazo wurin ta, ya turo bakin sa, kamar yayi kuka shima yace, sorry aunt neena, bari naje na kira grany, a kaiki asibiti, neena ta riko sa, a'a basai naje asibiti ba, idan nasa magani zai daina, ina da magani a daki.
Amir ya sake komawa prince, papa ka goya aunt neena, kamar yadda kamin ranan, she need to go to room, pls papa, prince ya juyo adan fusace, leave me alone kaje ka kira inna ladi ta taimaka mata.
.
Amir ya zauna, ya hade fuska da gwaiwa ya fara kuka wiwi.
Prince ya girgiza kai, ya mike yazo wurin amir, zan kaita daki, oya bar kukan, amir ya goge hawayen shi yace thank you papa.
Prince ya dawo ya tsaya a kan neena, amir yace, papa muyi sauri, prince ya duka, yasa hannunsa, zai ciccibi neena, tayi saurin matsawa , prince yaja tsaki, ya sunkuto ta, ta ware idon ta, yau itace prince ya dauka???????
Tayi saurin kallon fuskar sa, ya tamke ta tsam, neena ta kura masa ido, wani abu taji ya tsirga mata a zuciyarta, 
Tayi saurin dauke kai.
Har daki prince ya kaita, yana kaiwa wurin gadon, ya jefar da ita ya juya ya fice, neena ta murguda baki, kadai kawo ni din, tayi gwalo.
Sai da tayi ta jinyar jikinta har safe.
Da sassafen prince ya fito da akwatinsa, ya shiga wurin dad yace shi zai koma lagos, dad yace toh shikenan amma biki nan da 2months ya tabbatar ya dawo kafin nan..
Bayan wata biyu
Ana ta faman shirye shiryen, daurin auren su faruk da prince.
Iyayen biyu, mum da mami, kullum suna busy.
Zuby da zarah kuwa, lokacin suna semester exams, suma basa da wani time sosai.
Yanzu kuwa neena ta kara wayewa, dan zama da zuby dole mutum ya goge.
Duk kayansu idan sun matse su, ko sun gama yayi, sai ku tarkata su bata, dama neena akwai body, dan jikin ta yafi shekarunta.
Yau ake sa ran zuwan prince, dan sai da dad da abba, suka masa fada sosai, dan cewa yayi, shifa bazai samu zuwa va, suna da aiki a bayalsa.
Amarya ikram, sai shiri akeyi, ta shirya events sunfi biyar.ita kuwa amaryar faruk, Deeja, dama yan maiduguri ne, acan zasuyi komai,sai dai a kawo amarya kawai.
.
Neena tare da amir a garden, suna wasan buya, yanzu amir a dauke a matsayin uwa, idan bata nan ba mai iya shawo kansa, shi yasa yanzu sai wata wata take samun zuwa wurin umma, kuma ta wayar zuby take samun gaisawa da yaya habu, dan har chat suke da zuby din (toh fa)
Amir yace, aunt neena, yau papa dina zai dawo, neena na shirin bude baki, zarah ta kwala mata kira ta kofar kicin.
Da sauri ta karaso wurinta, zarah dake zuba abinci a plate tace, kije inji mum.
Neena na zuwa, ta samu mun da mami a daki, sun baje kaya a tsakiyar dakin, dama yau kwanan su biyu da dawowa daga Egypt.
Neena ta gaishe su tace mum gani, mum ta mika mata wasu kayan a dinke suke, kala har biyar, tace ga kayan biki kema, neena tayi murmushi, sannan ta musu godiya.
  Tazo zata fita, mum tayi saurin cewa, yauwa neena, neena ta juyo, tace kidan shiga dakin Na'im ki gyara masa, suzy na min aiki a BQ, neena tadan ware ido, dakin papa!!!!! Mum tace eh jeki pls, ya kusan isowa....
.
Neena ta fito, kamar waddda kwai ya fashewa a ciki.
   Dakin ta, ta shiga ta ajiye kayan ta, sannan ta fito ta nufi dakin prince.
    Tana cikin tafiya suka hadu da zuby, dauke da kedar kayan data amso musu daga wurin tela.
    Neena takai hannunta zata taimaka mata, tace barshi neena na kai, kinsan anjima zamu, family dinner,  yanzu saloon zamuje, mami tace muje dake, dan haka idan kin gama aikin ki, ki hau taxi kizo, kinsan ai wurin?? Neena tayi murmushi tace ehh na gane wurin, a wuse 2 ko, zuby dake tafiya tace eh nan ne kiyi sauri pls.
Neena ta shiga dakin prince, ta zo wurin gadon sa, ta tsaya, take ta tuna lokacin daya jawo ta jikinsa, ta runtse idon ta, ta bude a hankali, sannan tazo ta fara gyara gadon, kamshin bed sheet din, tamkar shine a wurin , haka nan ta samu kanta da rungume zanin gadon, ta shaki kamshin, ta tuna lokacin daya dauketa, haka jikinsa keta kamshi, tayi saurin ajiye wa, taci gaba da aikin ta, da taga zata fara tunane tunane, sai tace a'uzubillahi minal shaidanil rajim, Allah ka raba ni da tunanin mijin wata, ni duka shekaruna nawa, ni inshaAllah karatuna zanyi nima, na zama kamar mum, tayi murmushin ta taji gaba da aikin gaban ta.
.
Ta gama kimtsa dakin, ta shiga toilet,  woow ta furta, katon toilet ne sosai, gashi shima sai kamshin freshener yake yi.
Ta shiga wanke wa, tana gama wanke na farko ta shiga wurin shower, din, dan daban daban ne, amma duka a cikin toilet dinne.
Ta shiga ta gama wanke wa, tahau kalle kallen wurin, duk glasses ne, ga kuma remote,  neena ta shafa'a da kalle kallen ta.
Sai jin bude kofar toilet din tayi, ware ido tayi, waye ya shigo kuma????
Tayi sauri tadan leko, Prince ta gama a tsale gaban mirror,  shaving din kasumbar sa yakeyi, daga shi sai, rigar towel fara.
.
Da sauri neena ta koma cikin shower din, ta dafe kirjin ta, yanzu ya zanyi, nasan ya prince ya gabe ina nan ciki, zan shiga 6 ne bama 3 ba.
Ta rasa ya zatayi, sai wiki wiki take yi da idanunta.
     
Shi kuwa prince, yana kammala shaving dinshi, ya wanke fuskar sa, ya juyo yana kallon shower din , da gani nan yake shirin shiga , ya watsa ruwa.
Neena tension dinta ya lunku, dan wanda ke ciki yana iya ganin na waje, shi dake waje bazai ganta ba.
        
  Take wata idea tazo mata, tayi saurin lalubar, aljihun pakistani wandonta, tana tabo wayar dake ciki, ta sauke lumfashin ta.
Wayar amir ce daya bata ajiya, lokacin suna wata a garden,  tayi saurin lalubar numbar papa, aikuwa ta gani, Allah ya sota ta iya karatun ta.
Da sauri hannun ta na kyarma ta danna kiran numbar...........
.
Prince ya mika hannun sa zai bude kofar ya shiga, yaji karar ringing din wayar sa daga daki.

Mtsww, yayi tsaki, zuwa fa wurin nan ba dole bane, ya bude kofar toilet din ya koma daki.
Neeena tayi saurin sauke ajiyar zuciya, wai Allah na gode.
Fitowa tayi da sauri, tazo ta lekasa ta kofar, ganin shi tayi zai dauki wayar, tayi saurin rakubewa, ta fito tana bin bango, tana sando, kamar wata munafuka.
.
Prince ya dauki wayar, hello dear, am busy nw, zan neme ka anjima kaji, prince bai jira jin komai ba ya kashe wayar, ita kuwa neena hankalinta na, wurin kawai taga ta fice daga dakin.
Sai lallabawa take yi tana bin bango, prince na ajiye wayar ya juyo zai koma toilet,  sai ganin neena yayi ta lallabawa zata fice, ya saki baki, ita wannan kuma fa?! Kaman ya make ta yake ji, ya daka mata tsawa, kee!! Mai ya kawo ki nan?!!
.
Neena ba karamin tsorata tayi ba, ta jingine da hango tana kallon shi a tsoracen.
Prince ya karaso wurin da take a tsaye, ya nuna ta da yatsa sa, mai ya kawo nan?, neena ta kasa motsa harshen ta, dan nauyin da yayi mata, prince ya sake cewa da tsawa, ba da ke nake ba??!! Neena tayi saurin runtse idon ta, dan tsawar da yayi mata kamar zai hadiye ta.
Tayi kokarin motsa lips dinta, tace , ni ni uhm ni dama ni uhm, mum ce , uhm tace wai, nazo na gyara maka dakin, prince ya wani wurga mata harara, ya juya yace, get out!!!! Da sauri neena tayi gaba harda su tuntube.
Sunje salon, an musu gyaran gashi, su zuby sai yaba tsayin gashin neena suke, zarah kuwa na nan zaune sai waya take da mates dinta, wai ance mata zasuyi paper da yamma, shine take ta kira dan taji koda gaske ne.
Sun dawo gida karfe hudu na yamma, neena tayi dakin amir, a kwance ta iske shi tare da faruk, suna game da ipad.
Neena na shigowa tayi sallama, amir yayi saurin saukowa daga saman gadon, ya rungume ta, neena tayi murmushi, my little master, muje nayi maka wanka, amir yayi tsalle zanje naga fuad yau inji uncle faruk, neena tayi murmushi,  sanna ta kalli uncle faruk, ina wuni ya faruk? Faruk ya juyo ya kalle ta, yayi murmushi,  lafiya neena, har kun dawo ne? Neena tace eh yanzun nan muka dawo, faruk ya mike, bari na shiga wurin ya prince, ya fice.
.
A zaune ya iske prince, yasha wankan shi, cikin wasu tsadaddun kaya, farare, faruk ya samu wuri ya zauna, yace ya prince , su dad sunce idan mun kammala mu same su a can family house,  prince ya tabe baki, faruk yayi dariya ya mike, haba yaya kadan saki fuska, kada ka bawa amaryar mu tsoro, prince yaja tsaki ya jefe shi da remote din da ke kusa dashi, faruk ya fita yana masa dariya.
.
Neena zaune ta gama shirya amir, yayi kyau shima sosai, ta shafa fuskar sa, little master kayi kyau abunka, amir ya shafa fuskar ta itama yace, u r pretty like a barbie aunt neena, neena tayi dariya, nagode, oya maza je wurin su antu zarah su tafi dakai, amir ya make kafada, ni sai dake zan je, neena zatai magana, mum ta shigo tare da zarah da zuby.
.
Mum ta kalli neena , ya baki shirya ba neena, oya tashi tashi, kije ki shirya, dan dole sai ke amir dinnan. Amir ya rike hannun mum yace, grany da aunt neena zamu ko? Mum tace eh da ita zamu, sannan ta kalli neena tashi kije ki shirya. 
Neena ta saka, riga da skirt dinta, dinki zamani, sun zauna mata sosai, kamar ba ita ba, sai juyi take tana kallon kanta, wai dama umma na na nan, ta ganni cikin kayan nan, tayi murmushi.
Zuby ce ta shigo dakin, neena kiyi sauri muje, tsayawa tayi tana kallon yarinyar, baki a bude, tace kin ganki neena, neena tayi murmushi tace kinyi kyau kema anty, zuby ta karaso ciki tace, sai dai bakiyi make up ba, kuma dankwalin ki, zuby ta sa hannu ta cire jakwalkwalon daurin da neena tayi, tace zauna na gyara miki.
Neena na murna ta zauna.
.
Zuby cikin mintuna kalilan, ta kammalawa neena simple but pretty makeup, woow zuby tace, kin ganki kuwa?, neena sai murmushi takeyi, dan tunda take ,daga powder sai mai , kawai take shafawa fuskarta, yau gashi harda su pink janbaki, tayi kyau mashaAllah, kamar ba ita ba.
.
Zarah ce ta shigo dakkn, cikin shiri itama, dinkin su kala daya da zuby, tace kuzo muje mana, su mum duk sun wuce fa.
Sakin baki tayi tana kallon neena, ta nuna ta da yatsa, who is dis sisi? , zuby tayi dariya, amir nanny,  zarah ta matso tace, dama kyaun neena yakai haka?, neena tayi murmushi tace anty kuma ai kunyi kyau, zarah tace toh matso muyi selfie kafin mu wuce, zuby ta matso hakama neena, zarah ta daga wayarta ta dauke su, sunyi kyau kamar wasu flowers (lols).
.
Sun isa wurin mutane a cike, duk family dinsu ne a wurin, amarya ikram tasha gayun ta, cikin wasu tsadaddun kaya, ga makeup an mata, tayi kyau sosai abunta, ango kuma ga kyaun amma ba fara'a, fuskar nan kamar kullum, a tsoke.
.
Neena ganin duk ba wanda ta sani, kuma duk inda tayi sai an kalle ta, wasu a zaton suma , irin ruwa biyun nan ce, dan a gaskiya neena farace soaai.
Neman su amir ta farayi dan ta tsare su, kada suje su tafka banna, mum ta hango ta, ta kwala mata kira, neena ta karaso wurin table dinsu mum, zaune suke su hudu, mami, mum, mummy,  sai wata mata, da ganin kaga su abba, dan kamannin su harya baci, neena ta gaishe su, mum ta mika mata car key, je ki dauko min, wasu kaya a mota, neena ta amsa tace toh.
Wannan matar mai kama dasu abba, tace asiya (mum) ina kika samu yarinya,? Mum tace nanny din amir ce, da sauri naga matar ta kalli mum, nanny? ? Shine taci gayu haka, bata da uniform ne ko me?, mami tace tana dasu, amma su abban faruk sunce kada ta ringa sakawa, matar nan dama da ganin ta yar masifa ce, dan fuskarta ba alamun wasa ko kadan, tace ban gane kada tasa ba, ita din yar Wacece??? Mummy dake jinsu tace yar wacece fa fashe _YAR TALAKAWA_ matar nan ta maimaita, yar talakawa, shine zasuce kada tasa uniform,  wannan yar yarinyar da ba'a gama rainon taba shine zaku bata rainon wani?, gata yar talakawa, ko karatun kirki batayi ba, tazo ta koya wa yaro tabi'a irin tasu?, toh wai ina professionals nannies,  dinda kuke masa hiring? .
Mum tace yaya B , wannan da kike gani duk tafi su wlh, yaya B taja tsaki, zamuyi dai maganar idan mun isa gidan.
.
Duk wannan maganar da yaya B keyi, neena taji, dan ta dawo daga daukar kayan taji ta tana aibata ta, a sanyaye ta kawo wa mum kayan, yaya B ta watsa mata kallon tsana, ta juya zata koma seat dinta, batasan lokacin da hawaye suka sauko daga idon taba, can baya ta samu ta zauna, ta buga uban tagumi, hawaye na fita daga idon ta, tunda tazo family duka suna sonta, amma da gani ranar tafiyarta ya kusa, wani kuka yazo mata, tayi saurin dukar da kanta, ita kam bazata iya rayuwa ba amir ba, haka takeji har zuciyarta.
Tana nan zaune gaji anyi kiran amarya da ango, ta dago kanta ta kallo su, sunyi mugun yin kyau , ta dauke kanta tace, ku kam kunji dadin ku.
Tana nan zaune har aka kammala family dinner din nan.
.
Su zuby suka fara neman ta dansu koma gida, sai suka hade da wasu cousins dinsu, meera da meena, nan suka fada firar yaushe gamo, ya faruk yazo yace musu suzo ya maidasu gida, nan suka bisa, suka ma manta da neena.
Amir kuwa yash neman neena bai ganta ba, su abba zasu koma suka tafi dashi.
Duk wurin an watse, neena ta mike ta shiga neman amir, amma duk wurin sai data duba bata kansa ba.
.
Tazo har bakin gate tayi tsaye, kowa ya tafi, ita tana can ta lula duniyar tunani, addu'ar ta daya Allah yasa amir ya bi wasu yana gida.
Can ta matso dan ta tari mai taxi, Allah ya taimake ta tana da sauran canjin dazu, data je saloon.
Wata bakar motace tayi parking a gaban ta, saurayin dake ciki ya fito, tana ganin sa, ta gane shi, Moha ne yayan ikram.
Ya fito ya nufo ta, sai wani layi yakeyi, da gani dai yayi dan shaye shayen sa.
.
A gaban neena ya tsaya kikam, tadan matsa kadan ta gaishe sa, ya amsa yana dariyar shakiyan ci, yace muje na kai ki gida, neena tace nagode amma kaje, zan hau taxi, moha ya sake matso ta zai kama hannunta, muje bana baby, neena tayi saurin ja baya tace da Allah malam nace kaje bazan bika ba!!
   
Moha ya kwashe da dariya, see dis village gal, ke harni zance kizo na baki lift kice bakyaso, who d hell r u, yar talakawa dake, bakauyiya.
Neena ta share hawayen ta, tayi gaba dan samun taxi, sai dai jin hannun moha tayi, ta cafko ta, yana neman rungume ta, ta fasa kara ta fara tura shi, dankwalin ta ya fadi, moha ya kurawa fuskar ta ido, ya yaye gyelen jikinta ya jefar , yasa hannunsa yana shafa gashin kanta, neena sai mutsu mustu take tana kuka, can taji kamar yana shirin zage mata zip, tayi kokari ta wanka masa mari, kai wane irin maye ne eyee, moha ya ciji leben sa yace yanzu zaki gane wane irin mayen ne ni, yayo kanta kadan kadan.....
.
Prince zaune a family house,  ajiye coffee cup din hannunsa yayi, ya mike, its over tunda naji shiru.
       Ya mike ya dauki, wayar sa ya fito, yasa key ya rufe gidan, sannan ya nufo gate dan a waje yayi parking din motar sa.
Tunda ya nufo gate din yake jin kukan mace, ya kara sauri, yana isa ya hango moha sai kokarin yage wa yarinya riga yakeyi, shi baima gane wacece ba.
Yana isowa moha na yage hannayen rigar neena, dan materials ne, ba wani wahalan yagewa gare shi ba.
Prince yayi saurin zuwa ya janye moha, ya wanka masa kyawawan mari kuda uku, sannan ya tsukomo rigar sa, ya nuna sa da yatsa, kada ka sake na kara maka ma moha, maza wuce jahili kawai, moha yayi saurin shigewa mota ya wuce fuu, dan yasan halin prince sosai, zai iya kai shi sell ne kawai ya rufe.
Juyowa yayi wurin yarinyar, yaga wayam sai gyelenta da  da dankwali, can ya hango ta tana tafiya kamar zata fadi.
Neena duk hankalin a tashe yake, gaba daya kwakwalwarta ta tsaya cak, ko prince dinma bata gane shi bane, tafiya kawai takeyi.
.
Harya shiga mota zai wuce abunsa, can ya fito ya dawo ya dauki, gyelenta da jaka da dankwali, ya koma motar, yaja yakai dai dai inda take, yayi horn, yaga bata tsaya ba, yajaa tsaki , shi kawai tausayi ta basa, ganin ta yar teenager,  ya fito yace kee!!! Neena taci gaba da tafiyar ta kamar zombie.
Prince yasha gaban ta, sai a sannan ta tsaya ta dago idanunta da suka rine zuwa jajaye, fuskar nan kamar tomatoe dan ja.
Prince ya kura mata ido, shikam kamar yasan wannan fuskar, take ya tuna dazun daya ganta a dakinsa, yace a fili nanny! !!! Toh mai ya kawo ta nan ? kuma ya akayi kowa ya tafi sai ita aka bari?? - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment