Friday, 9 March 2018

'YAR KWALLIYA Page 21-25



'YAR KALLIYA Page 21-25
.
Usman kuzauna bari na kira mommy  Usman yace To   Usman Sannu da zuwa ko nace ba maraba ba kawani kawo katon kanka shikuma harda shirya maka abinci hmm kaci mugani Abu ta fada ta wuce dakin ta  Aqeel yaje dakin hajiya yasanar da ita zuwan su Usman  Hajiya da saurinta ta fito   Manyan baki magana tatabbata Arif yace min ka zama kato  Usman yace mommy karki yarda bawani kato dana zama ina nan yanda nake shine kawai  Hajiya tace fada kake yi Usman duk wanda ya sanka da ya ganka yanzu yasan ka canza sosai ma kuwa  Hakane to mommy ina wuni ya gida yasu Amal  Lpy kalau ya karatu ya kowa da kowa  Lpy kalau ina Amal din ko tana maka ranta   A'a tana ciki zata zo yanzu   Kannen usman suka hada baki suka gaida hajiya  Ta amsa tace Aqeel ka kaisu dining bari na turo Abu da Amal su zo su jera komai  Aqeel yace to mommy ina zuwa ya zauna kusada Usman yace inda nine kai ba abinda zan dawo yi nan zamana kawai zanyi  Ko kai meyasa baka zauna ba ina ka rigani zuwa cewar Usman  Aini be karbeni yanda ya karbe kaba kuma ni gaskiya bazan iya zaman canba  Hmm shine ni kake so na zauna      Sukayi dariya   Kuzo muje dining  Aqeel wai ina Arif tinda nazo ban ganshiba   Fita yayi bajimawa ze dawo Ku zauna   Aqeel ya wuce kitchen  Hajiya dakin su Abu ta wuce ta Bude ta shiga  Bacci Abu lpy Binta kalau kuwa   Hajiya lpyan ta kalau wlh tsabar jindadi ne Gashi kuma taci ta koshi abinka da kura  Abu meye haka bintarce kura   Hajiya kenan tinda kikaji nace mata kura kiyarda kwai kurarce inkuma baki yardaba anatare zaki gani da idonki  Abu KWALLIYAR nan tayi yawa kirage ta kuje kitchen kudauko abinci Ku jera a dining Su Asibi sun fita  Tab harkinsa na tahi narage KWALLIYAR fuskata tab anrabani da tiraren jikina yanzu kuma KWALLIYAR ma hanani za ayi daga ragewa za kuma ace na dena yi   A'a Abu ni bazan hanaki KWALLIYA ba saidai yanda kike naki yana yawa hasalima yana canza kaman ninki shiyasa nace ki rage  Hajiya ina ganin girmanki gaskiya bazan rageba   To shikenan kuje Ku dauko abinci kina fita Za kiga Amal a waje     To hajiya natafi   Abu na fita ta ga Amal suka wuce gurin su Usman  Amal ta gaida Usman           Abu ma ta gaida su Kannen Usman satar kallon Abu sukeyi damagana abakin su amma sukayi shiru Usman ma haka azuciyarshi tanbaya yake wacece wannan    kai tsaye kitchen Abu da Amal  suka wuce Abu ta Tsaya daga gefe tana kallon Aqeel dake waya tana dariya  Amal tace bari nadauki Wannan yafi girma kekuma ki dauko Wannan      To Abu tace  Amal na dauka taji banauyi da sauri ta ajiye ta bude taga ba komai aciki  Yaya Ina abincin yake ko ankai dining     Bece mata komaiba yadaga mata hannu alamar yana zuwa  Ya kashe wayar           Yace me kikace   Yaya Bakomai a cikifa   Yace A cikin me   Amal ta nuna mishi da sauri yazo  yabude yaga bakomai yabude sauran ma yaga ba komai       Ya haka nida kaina naga sun girka abincin amma yanzu babu kuma kansu fitama sunfadamin sungama yanzu ya zanyi da Usman    Abu tace Amal waihi waye Usman din  Amal tace babban Abokin yayane tare sukayi karatu a America  Abu tace  hm kekika sanhi sunan garin da kika fada nida bansa ko inaba sai *DARAUDAU*  Ran Aqeel ya baci sosai dariya na niyar kwacewa Abu taita dannewa dan karya gano ta  Naji dadin ganin ranka a bace nunar rana tukun na ma Abu ta fada a cikin zuciyar ta  Amal tace yaya ya za ayi yanzu   Aqeel ya kasa cewa komai sai huci yake   Abu tace susha ruwa su tafi tinda abincin ba dole bane dama duk Wannan  aboki akayi wa girkegirke haka Nina dauka sarkine ze kawo muku ziyara ruwanma karku baso tinda gidan bana gyatimi bane  A fusace Aqeel ya juyo yana huci shi tinda yazo gun bekula da itaba se yanzu mur yarta Yaji sai lokacin yasan tana gurin ya zari shar bebiyar wuka tana kyalli yabi Abu dashi  Dagudu suka wuce su Usman Amal na binsu a baya sukayi dakin hajiya   Gudun da taji yasata saurin mikewa tace lpy Aqeel mezan gani haka  Yace hajiya matsa ki bani ita ina abincin da aka dafawa su Usman babu shi ita kadai tasan inda ta kai shi  Abu tace hajiya karki yarda da abinda zece wana tabbaci yake dashi na cewa nina boye abinci  Inni naboye abincin ina nakaihi  Yace mommy ita kadai ce zata aikata haka Nina sani   Abu ta fito daga bayan hajiya tana murguda baki zatayi magana Aqeel ya dauketa da mari  Abu ta gigice takurma ihu ta zube kasa tana birgima  Yaya meyasa meyasa ka mareta kome ta maka ka dinga hakuri mana cewar Amal   Yimin shiru yadaka wa amal tsawa kema yanzu nahada dake nakula tinda sukazo kike goyan bayansu bakyaso aimusu fada kuma kina ganin irin abin da sukeyi bedaceba  Hajiya tace Aqeel karka sake dukanta kome ta maka ka sanar dani ni nasan mezan mata
.
  Amma mommy  Tadaga mishi hannu tace ya isa bana son jinkomai            kanta karasa maganar ta tuno maganar da Abu tace mata Binta kurace taci ta koshi  Waiyoo Aqeel temako zoka temaka ka dauko Binta mukaita asibiti Abu karkicemin duk yawan abincin nan ita ta cinye  Hajiya Nifa ba tsoran nunar rana na keyiba maganar gaskiya hine Binta taci iya cinta sauran kuma na rabawa mabu kata   Mommy kina jiko kinajin abinda take cewa Wlh zan karkarya yarinyarnan  Nidai Aqeel yar mutane katemaka mu kaita asibiti  To naso ace ke kikaci ba ita ba saidai dani kike magana        Yafita daga dakin rai abace  Arif ya shigo hannun shi dauke da leda guda2      Aqeel dasauri ya karasa gurin shi yasanar dashi abinda Abu tayi seyai murmushi yace  Nasan wani Abu me kamar haka ze faro tinda na gane cewa indai ta fadi Abu saitayi yasa na ke fadada tina Nina karka damu ga Wannan nabi ya na siyo abincine masu dadin gaske   Kai naji dadi Amma hakan baya nufin na hakura dan yau raina ya baci sosai   Yace karka damu muma zamu hukunta su   Su kayi dariyar mugunta   Arif yaje suka gaisa da Usman  Aqeel ya jera abincin da Arif ya siyo Aqeel ya fita kunyar Abokin shi dan Abincinda Arif ya siyo kamar a gidansu akayi  Saida yamma Usman da kannan Sa suka tafi 
.
  Lokacin ne Aqeel ya maida hankalin Sa ga Abu hukuncin da ze mata kawai yake Tina ni  Aqeel Tina ninme kakeyi haka   Kabari kawai Arif zo muje   Arif yabi bayan shi suka tafi kitchen sukaje   Arif yace me za muyi Anan   Zuba ido ka gani   Aqeel ya Dora ruwa yana ta fasa yasa taliya yana laushi kadan ya sauke ya kwashe yasa miya   Aqeel yace nagama mu tafi  To amma ka hada mata da giyarta ta dazu  Haka ne jeka dauko ka sameni a kofar dakin su  Arif yace to yaje ya nauko lema yanufi dakinsu Binta     Atsaye a kofar dakin yaga Aqeel              Aqeel na ganin Arif yazo yabude dakin ya shiga bacci kawai Abu da Binta sukeyi han kali kwance     Arif da Aqeel sukayi dariyar mugunta   Arif ya tsaya a bangaren da binta take       Aqeel ya Tsaya a bangaren Abu     Atare suka daga hannu suka Kai musu duka me shiga jiki a gigice suka mike suna ihu   Aqeel ya daka musu tsawa      Suka yi shiru suna kallon su Arif  Arif yace kun kyauta a binta kukayi kunbirgeni sosai Ku zonan  Binta tace nan ina muyi me kuma banda Wannan cin zalin da kuka mana   Aqeel rai ahade yace cinzali ko to bari namuku dukan kawo wuka muga abin da zaku kira Wannan kuma   Abu tace nuna karmuyi haka mana bari muzo    
.
    Agabanshi so ka Tsaya   Aqeel yace ku zauna a gaban kwanan dana kawo      To sukace sukayi kamar yanda yace   Arif yace Ku Bude kuci  Binta tace dandai ci gidan kazo ta Bude kwanon tana ganin abinda ke ciki tasa kara  Aqeel ya zaro wuka yace kokiyi shiru kona caka miki ba ina nufin hakan zan farayiba saina fara gunduwa gunduwa daku tukun na  Binta ta rufe baki   Abu tace nunar rana bama cin sutsa fa kukawo mana wani abin banda Wannan yai dariyar mugunta  Arif yace Ko lokacin da kuka rabar da abincin kunyi shawara dani   Abu ta girgiza kai alamar a'a   Aqeel yace Yauwa dan haka Ku cinye sutsar nan gaba1 banaso naga komai a cikin kwanan nan  Baza mu iyaba harni har kwada yina ban taba cin sutsa ba yasin cewar Binta  Balle ni Abu bazan iyaba dan Allah kuyi hakuri  Aqeel yace Hakuri Sam bazamu hakuraba har sai kun cinye sutsar nan gaba1 ya daga wukarshi yana sha fawa  To za muci Abu ta juya kai tasa hannu ta debo taliya jitayi yana mata motsi a hannu ta zubar dashi   Aqeel ya hade rai yace 'YAR KWALLIYA kinjawa kanki bayan kuncinye taliya ga lemo kushanye shi tas shima  Giya dan Allah kayi hakuri malam Rabi'u yace ba kyau shan giya  fa  Tinda kika kirashi giya kekadai zaki shanye cewar Arif  Lokacinku ya fara daga yanzu inba Ku cinyeba ga Aqeel a kusa dani       
.
Aqeel ya daga wuka ya nuna musu  To shi kenan zamuci haka Abu da Binta suka rufe ido suna cin sutsa ta bakin nasu   Suna hawaye serige ciki suke kamar zasuyi amai               .
.
  Harsuka cinye Abu da Binta sai rike wuya sukeyi   Arif yace kun gama da Wannan saura lemo   Gaskiya Ku barmu haka   Aqeel ya wasa wuka   Binta tace Abu yi shiru bamu   Arif ya zuba ya basu       Suka ansa suna sha   Binta Kura kyaci da Gashi tana sha taji dadi ta kafa kai ta shanye ta mika mishi Kofi  Arif yace Me zanyi dashi   Tace Wani zaka zuba min       Arif ya zuba mata takuma shanyewa ta miko mishi Kofi shikuma yabata gaba daya ta ansa tashanye   Binta tace bawani Ku karo min Yasin giyar badai dadi ba wai kaf qauyen mu idan za a zagaye bana tinanin za a samu ya Wannan  Arif da Aqeel suka kalli juna   Aqeel yace ke harkin shanye   
.
Abu tace Eh na gama tafada tana hawaye  Aqeel yace Yauwa ita dai waccan wani hanyar zamu sake dan na kula Wannan kura ce yanuna Binta  Kiran salla sukaji suka mike zasu tafi masallaci  Aqeel yaga su Abu ba a daniyar tashi kwanciya ma suke shirin yi a gurin ya daka musu tsawa yace meye haka bakuji kiran sallabane kuke shirin kwanciya  Abu tace munyi tin a *DARAUDAU* ba a binmu bahin salla   zaro ido sukayi atare suka hada baki sukace mekukace sukace mun shiga UKU Akwai bamban aiki   Arif cikin mamaki ya dawo ya zauna yana fukan tarta yace ban ganeba  Binta tace sallar sati1 muke hadawa muyi a rana1 kaga sauran ranakun mun huta Ku kuna salla mukuma muna hutu ta fada tana dariya  Aqeel yace hauka zalla bana tinanin kan yaran nan a kwai kwakwalwa wlh kai kaji wani Abu ko yaro bazeyi shir mannan ba  Arif yace kuna zuwa islamiya a qauye  Abu tace muna zuwa malam rabi'un ne dan rainin han Kali Abu kadan duka hine muka dena zuwa ban fada makaba   har bokoko a wuta munyi sau1 mukaje shima ya raina mana hankali muka hukuntashi bamu sake komawaba sai gamu a barni tafada tana dariya harda tafawa   Aqeel kaji magana gangariya nakula jahilcine kawai yake dawai niya dasu amma komai yazo karshe   Aqeel yace shi malam rabi'un ne ya ce Ku dinga hada sallah   A'a mune mukaga hakan yafi dacewa saboda bamuda lokaci zama muyi akan lokaci saboda dasafe mu debo ruwa darana naraka Binta tallar gurjiya da yamma muje dandali tafada tana rawa  Aqeel ya kalli Arif yace a kwai matsala ke dena mana rawa ko kinji kidane nibana tinanin kawunan yaran nan zasu dau karatu  Arif yace koma meye sunan Ku ban damu na saniba kutashi kuyi Alwala kuyi sallah yanzu sannan Ku sani ba a hada sallah kowacce ana yinta akan lokacinta kunaji  Allahu'akubar kaji malamai munji kuma mun gane zamu gyara wai bazaku kaimu dandali bane natara rawa masu yawa Ku kaini na juye yanbirni su gani su sani mu yan qauye hmm tatashi tana rawa   Aqeel yace yarin yarnan a bace take bata gane komai zomuje masallaci kaga har an tada sallah  Suka tafi sukabar Abu na rawa binta na zaune tana shafa ciki  Binta tace Abu zoki rakani gona nayi kahi sunan basuda shadda Gashi a matse nake waiyoo  Abu ta dena rawar da take cikin mamaki tace binta kefa ki kace yan birni basa kahi ya haka kuma keza kice na rakaki gona  Kinga su wayanda aka Haifa a birni nake nufi banda mu kinga aimu zuwa mukayi ko   eh hakane kinga yanzu yamma tayi kihiga inda aka yi mana wanka ina randar nan ta ruwa Wannan farin  Binta tace Eh na ganeta   Kije Kiyi a ciki   Abu ba komai   bakomai jeki na Tsaya miki  Binta ta shiga tayi ta fito tana rike ciki tana yamitse fuska  Abu hanci a toshe tace Binta duk warin kahin kine haka kamar mushe  Bana son wula kanci lafiyace da bani dashi bazan yiba
.
Amal ta Bude ta shugo tana shigowa warin ya daki hancin ta tace meye haka warin meye Wannan  Binta tace ji wani Abu da takeyi kamar bata taba yin kashi ba wayasanima ko naki yafi nawa wari   Amal tace a ina kikeyi  Binta tace shiga nan ta nuna ban daki zakiga randar ruwan nan a ciki nayi karki damu sanda na Debi ruwan tsarki a randar tukunna nayi   Randa Amal ta mai maita cikin ban dakin tashi ga tasamu binta batayi shirmeba korawane kawai bata yiba ta kirata ta nuna mata yanda  akeyi  Abu tace Tab saura kiris mu fita waje Neman Gona da zatayi a can Ashe Gwanda da bamu fitaba da munsha wa halar  Banza  Shiyasa nace kome kuke so Ku tam bayeni  To ai mun gane yanzu kuma  Bari naje gurin mommy ina zuwa     Tabude ta fita su Aqeel ta samu a dakin  Aqeel yace mommy gaskiya a nemawa yaran nan malamin da ze dinga koya musu karatu a gida idan suka fara hankali a kai su makaranta  Arif yace mommy yaran nan naki da girman su hada sallah sukeyi   Hajiya tace Eh hada sallah bangane ba  Aqeel yace hmm dazu suka fada mana waisu sallar sati1 sukeyi a tare rana kunda zezo kuma sun huta   
.
Hajiya tace tab Allah ya rufa asiri yakamata musamo musu malami yanzudai malamin da ze dinga koya musu Qur'ani da sauran littattafai na addini shine malam kabiru dama shiya ke koyawa Amal  Arif yace hakan ma yayi idan suka ga amal kila su zauna mommy boko fa  Eh to Wannan dinma kabiru ze iya koya musu tinda tsohun malin makaranta ne   Arif yace to mommy zan Kirashi na sanar dashi daga gobe zasu fara inba hakaba abin nasu lalacewa ze karayi   Hajiya tace yauwa Aqeel idan malamin yazo kuja musu kunne karsu yiwa malamin halin nan nasu dan naga suna   tsoron ku sosai  Niko yakayi da Usman duk kunya ta hanani fitowa koda muke Salama Akunyace nake wlh   Aqeel yayi dariya yace mommy Arif ya findake kunya shiya siyo abinci ya kawo bazama kice a waje aka yiba kannen Usman sunce suna godiya da yautar da kika musu  Alhamdulillah amma naji dadi Allah ya muku Albarka  Ameen mommy tafiyar mu zuwa America na kara matsowa fa   Hakane fa harna fara kewar Ku   Mommy karki damu ga *'YAR KWALLIYA* da *KURA* za su debe miki kewa suka fada suna dariya  Hajiya tace yaran nawane kuraye lallai inajiye muku wlh ranar jinkunya musammanma Aqeel kafi kushe su   Tab indai wayan nan ne ranar bazata zoba nida zan dauko miki sirika a America me zanyi da wata yar qauye  Allah yaya to shi kenan zamu gani cewar Amal  Mommy saida safe mu zamu tafi  Allah yatashe mu lpy       Washe gari da safe Abu ko karyawa basu yiba suka fice daga gidan   Abu na tafiya tana mita  Kai dan Allah ki Tsaya Abu mitar me kikeyi  Binta tinda mukazo basu kaimu sun nuna mana gariba sun barmu a guri1 sannan gasu nunar rana gidan ma ba dadi ko dandali basu kai muba  Binta tace shine abin damuwa to ba Gashi mun fitoba muga gari iya san ranmu daga nan muje muga dan dali  Hakane kuma saida sukayi tafiya me tsawo sukayi nisa da gidan sosai    Duk wanda ya gansu mamaki yakeyi ganin KWALLIYAR dake fusko kinsu duk wanda ya kallesu baya karawa  Abu ta jabe a kasa tace daga nan babu inda zani     Meyasa   Saboda yunwa nakeji indan banciba bazan iya tafi yaba  To bari naga ko zamuga abin siyar wa  Wata yarinya ta wuce ta ga bansu tace zaku sai waina  Binta tace waina Abu kinji waina tab shegu yan birni nasani ai duk abinku saikun hada da qauye sauke mu gani  Yarin yar ta sauke sukace na nawa ne a ciki    Tace dubu1  Abu tace Yarinya kingama ciniki yidari    Yarinya tayi dariya    Abuda binta suka Sa hannu a robar waina suna ci  Can gida kuwa ne mansu kaiwai a keyi  suzo suci a binci gashi kuma malamin da ze koyar dasu yazo   Amal tace yaya Aqeel bangan subafa   Baki gansuba kamarya ina zasuto cewar Arif  Amal tace nima ban saniba  Hajiya ta daga hannu sama tana cewa Allah kasa muga yaran nan Allah kakaresu a duk inda suke  Aqeel yace mommy dan Allah karki damu zamu nemo su duk inda suke bari mu tam bayi me gadi koyaga fitar su  Dukan su suka je gurin megadi  Arif yace kaga fitar kannen mu guda2nan da sukazo  Eh nagani sunce min suntafi bude ido  Alhaji yace Bude ido kai Arif Aqeel kuzo muje Neman su  Aqeel rai a bace yacewa megadi tin yaushe kake aiki a gidan nan dasuka ce maka haka saika zo ka tam baye mu kafin ka barsu su fita  Ayi min Afuwa insha Allahu hakan baze sake faruwaba  Arif yace daddy karka damu kukoma ciki zamu nemosu da kanmu mu kawo su  Amal tace yaya zan biku  Arif yace taho mu tafi   Hajiya tace saikun dawo Ku kula da kanku idan kun gansu Ku kira Ku fada mana     To mommy  Me gadi ya bude musu suka fita Neman su abu    Saida su kaci suka koshi sukace taje ta siyo musu ruwa da kudinta tajeta siyo ta kawo musu suka sha   Alhamdulillah Allah na gode maka yanzu naji dai_dai dauki wai narki ki tafi Allah ya kawo ka zuwa  Yarin yar tace kubani kudina saina tafi  Binta ta kaiwa yarin yar duka tace rashin kunya zaki mana bazamu biya ba Kiyi abinda zakiyi                New writer's  Hakan Take *husba'ahfama* 
.
Yarin yar tace hakama zakice wlh Baku isaba duk abinda kuke takama dashi Nina fiku bala'i yanzu zan dakeku na daki kudina na kaiku gurin yan sanda  Binta tace Ko to bisimillah mafashi keda kinsan komu suwaye tsayawa ma baza Kiyi a nan ba  Yarin yar ta kai wa Abu duka   Abu rai a bace takai mata wani mugun naushi saigata a kasa Abu da binta suka rufar wa yarin yar sukai mata duka  
.
Abu tace Banza a banza kemu zaki nunawa taurin kai hmm Allah ya temakeki mu kara haduwa saina zubar da hakwaran bakin ki  Yarin yar kuka kawai takeyi danta daku bakadan ba   Allah ya isa kuma saina turo muku yayana ainaga gidan da kuke   Shegiya wato binmuma kikeyi ko kufa yan birni kunada matsala Yasin sa ido ya muku yawa Wannan KWALLIYAR ne Baku taba ganiba   Niba KWALLIYAR Ku nake ganiba a bayan layin Ku gidan mu yake zakuga gatana cewar yarin yar  Binta tace kafin muga gatanki bari mubaki ladan gida sukai mata dukan tsiya ko tashi ma ta kasa  Abu tace barta haka mu koma gida sai anjima kuma zamu kara fitowa  To mutafi    Arif yana tuki yana waige ko ze gansu duk sun baza ido suna duba hanya ko zasu gansu   Abu da binta sukazo zasu tsallaka titi Abu kaitsaye ta tafi ko hanya bata duba ba motar su Arif ya taho da gudu ganin  Abu da yayi yasa shi taka birki cikin sauri ya Tsaya   Aqeel ya Bude ya fiyo ya kaimata mari Abu ta gigice ta rasa inda zatasa kanta   Binta kura batama san anayiba me karas tagani yazo wucewa hanka linta ya koma gare shi  Arif Azuciye ya fusgota ya kaimata mari Gigi cewa tayi    Tana cewa gatan naki kenan badai kince abayan layi kikeba har gidanku zamu Yasin mudake ki  Jin haushin Abinda take fada yasa Arif ya kara marinta sai lokacin tagane wanda ya daketa   Ta fashe da kuka Abu ma kukan takeyi dan itama saida ta sake shan mari Amal takasa cewa komai kallon su kawai ta keyi tana kuka  Arif rai a bace yace Bakida hankali waya gaya miki haka ake tsallaka titi da kuka fito me kuka fito yi wakuka fadawa da zaku fito ke kuma kura daga   ganin A binci hankalinki yatafi dayanzu bamu bane wani dabanne  yabita kanta ya wuce kiceme baki ganiba ko bakya gurin   Aqeel yadaka musu tsawa yace su shiga mota  Da sauri suka shiga suka zauna har lokacin basuce komaiba kuka kawai sukeyi   Arif ya kira hajiya ya sanar mata sunga Abu da Binta          hajiya taji dadin jin hakan   Arif fada kawai yake musu har suka isa gida  Amal da gudu ta tafi ta fada jikin hajiya tana kuka  Hajiya tace me kuka mata take kuka   Aqeel yace meze sata kuka inban da taba yaran nan da mukayi saboda ita kenan kar a musu fada idan sun yi laifi  Mommy dana sani ban bisu ba suna sane suka tafi dani dan su dakesu a ga bana nima tsoran su sukeso naji kuma naji tsoran naku Amal ta fada tana kuka 
.
  Hajiya tace Amal dolene Amusu fada idan sunyi laifi basuba harda ke kema yaiyan naki suna so su Abu su dena abinda sukeyi shiya Sa  Amal ta goge hawa yan fuskarta tace hakane to shikenan nina dauki nauyin gyara su Binta zasu dena duk abinda sukeyi insha Allah      Tana gama fada ta wuce dakin ta  Arif yace Lallai indan baki gyara suba su Sa koya miki hada sallah da rashin wanka wayan nan yaran kuma hmm  Hajiya taiwa su Abu fada sosai fadan yashige su sukai mata Alkawarin cewa bazasu sake ba   樂 bari muga ko Abu da binta zasu iya cika Alkawarin da suka dauka  Hajiya tace kuje kuci Abinci kuyi wanka malamin Ku yazo  Atare sukace to        Suna tafiya suna hararar nunar rana   Kwafa Aqeel yayi yace mommy duk sanda me KWALLIYAR Aljanu ta fado hannu na hmm ina tausaya mata   Hajiya tace yara ne sai hakuri   Amal na dakin Abu da Binta rai a hade sai Kada kafa takeyi   Sukazo zasu wuceta  Amal tace Ku Tsaya a koda yaushe ina zuwar muku da sauki saboda Ku ba kine amma kun kasa ganewa ko to   shikenan daga yau Anan tafiya ta daku ta canza salo muguwace ni banida kyau idan raina ya baci   Binta tace tomu ina ruwan mu canta matse miki  Amal ta daka musu tsawa tace haka kuka ce ko naji dadi kushiga kuyi wanka ko kuma ta zira hannun ta karkashin Gado ta Ciro wani shar beben kara tace idan na fara zaneku dashi saiya karye zan barku  Abu ta matsa kusa da binta take rada mata tace gaba daya yan gidan nan hawai niya ne kinga itama ta canza   Binta tace ya za muyi yanzu   Abu tace muyi abinda tace dankuwa bada wasa take ba  Amal tace kun gama shawara     Suka daga mata kai           tace dakyau waze fara shiga  Abu tace binta        
.
  Binta tace Abu   Amal tace ya isa nida kaina zan zaba Abu shiga ki fara yi kuma ki tabbatar kin goge baki Tsaya nafasa bari nakira Asibi ta Tsaya a kanku   Abu tace A'a karki kirata zamuyi tin rikon da tamin rannan haryau gurin zafi yake min   To shiga ki fito   Abu ta shiga tayi wanka ta goge baki tafito Binta ta shiga tayi ta fito dariya na kokarin kwacewa Amal ganin yanda suke tsoran ta saidai Ta dake taki dariya  Tabasu mai su shafa suka shafa suka dauki kayan da suka cire zasu maida  Amal tace mezan gani haka kayan zaku mayar sunyi datti gawasu kusa wayan can kuma za a kaisu wanki  Tab gaskiya a'a jiyafa muka sasu mudai kar a wanke mana muna sansu a haka to ko kayan mu se sunyi wata kafin mu wanke balle sabin Kaya hikuma saiya hekara  Ya isa Wannan a qauye kenan nan kuma birni ne dan haka kuyi abinda nace kafin raina ya baci    Haka suka dauki wanda ta basu suka Sa badan ransu yaso ba  Tace muje kuci abinci   Munkoshi baridai muyi KWALLIYA  Eh banyarda ba haka nake son ganin ku  kuwuce muje malam kabiru na jirani mu  Abu zatai magana amal ta kafeta da idanu ganin haka yasa tai shiru har suka karasa gurin malam a waje suka ajiye mishi kujera sukuma suka zauna a tabar ma  Malam kabiru ya Bude Qur'ani yafara karan tawa Amal ce kawai take jinshi Abu da Binta hankalin su na wani gurin ji sukai garin ba dadi   Arif da Aqeel suka fito suka zauna gaba dasu kadan suna ganin su  Abu da Binta ganin su Aqeel yasa suka maida han kalin su gurin malam   Haya niyar me gadi da wasu mutane da basu san kosu wayeba Arif da Aqeel suka jiyo  Arif yace malam karka damu zamuji da komai kucigaba da karatu   Lokacin mutanen suka tunkude me gadi suka shigo  
.
Arif yace lpy kuka shigo mana gida   Tan gadi yakeyi hannun shi rike da taba  Yan ra konsa na mai busa da kirari   Kanshi sai fasuwa ya keyi   Yana tangadi yace ina suke  Aqeel yace qaura meya kawoka gidan mu  qaura yace daliline ya kawo ni kubanisu na fidesu harni qaura za a samu wayanda zasu budewa qanwata idon da raina da lpy ta yakarashe maganar yana layi  Dan koranshi yamishi kirari   qaura ya zaro wuka yana gogawa a jikin shi  Aqeel yace qaura ban gane abinda kake nufi ba fa  qaura yace qanwata ce ta tafi talla wasu daga gidan nan suka mata A kuya kotashi bata yi  Haya niyarda hajiya da Alhaji sukaji yasa su fitowa  Hajiya tace ba a gidan nan ba kasake tam bayan ta  qaura yace Na tam bayeta saboda me bayan qanwata bata karya  Alhaji yace idan a nanne to waye   qaura yace yeeeehu harni za a kawowa rainin hankali aiya maza jada baya ga rago ba tsoro bane yanzu zanyi fata fata da mutum na kwana lpy  Abu da Binta suka taho gurin Suna kallon qaura yana yiwa kanshi kirari  Abu tace qaryar banza kaje an disashe kaifin wukar kazo kana mana burga dashi mune nan muka daketa me zakayi  qaura yabude ido yana kallon Abu da Binta yace gaskiya bintu ta badani wayan nan dabefi ta murde musu kaiba amma ba komai  Ya sun kuya yana saita wukar ya saito gurin su Abu da Binta   Arif ya Tsaya a gabanshi yace qaura a'a karmuyi haka dakai wayan nan bakine fa  Ina ruwa na kabarni na fedesu Susan wadda suka taba   Alhaji yace qaura kayi hakuri muje naga yarin yar na kaita Asibiti  Abu tace Kawu tsimina na tahi dan'uwar makocin kishiyar kakan su binta qaurane ya jika ya bamu mu bama rike wuka ko gora namu salon na da banne matsa ka gani  Nanfa Alhaji hajiya Aqeel Arif da Amal suka shiga ba qaura hakuri qaura yaki hakura  Arif yace shi kenan gasu nan na bar ka dasu  Binta ta Ja da baya tace kawu matsa karma ya hakura abinda nake jira kenan  Suka sun kuya Suka debo kana nan duwatsunda aka baza a filin gidan suka fara jifan qaura da muta nansa tako ina  daga me fashashan baki saime goshi a fashe    Koda qaura da mutanan Sa suka ga Abu da Binta na ji musu jiwo nan fa suka Sa gudu kofar ma ta musu kadan qaura da yake a bige nanfa ya watsa ke yana gudu      har waje Abu da binta Suka rakasu da jifa       

0 comments:

Post a Comment