BAYAN WUYA SAI……
NA
RAMLERT y salis
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI YA ALLAH KABANI IKON RUBUTA DAI DAI KASA ABINDA ZAN RUBUTA YAXANMA HUJJA AGARENI BA HUJJA AKAINA BA.
WANNAN SHINE TYPING DINNA NA FARKO NASAN DOLENE ACIKARO DA KUSKURE DA YAWA KARAMAR YAR KOYOCE SAI DAI AMIN AFUWA 🏻
Wannan page na mallakawa masoya kuma masu karfafamana gwuiwa wato members na SIRRIN YAMACE BY FIRRAM ……munanan tare daku acigaba da gashi suya sai ranar ……
Page 12
Kuka take sosai ba abinda yafi tayar da hankalinta irin ganin yadda jini keta zuba ahancin mahaifiyar tata, jijjigata ta farayi ganin kamar ta dena motsi yasata saki wani ihu da yayi sanadiyya tsayawarsa cak... ya ja birkin motar tasa a dai dai kofar gidan da taji wannan ihun.……
Karewa unguwar kallo yayi gannin ko ina tsit bako alamar dan adama ,agogon dake manne jikin motar ya kalla 12:35pm ,ahankali yafito daga motar ya nufi kofar gidan gidan ya karewa kallo aransa yana cewa
"Yanxu mutane ne ke zaune cikin wannan gidan Allah nagode ma da kabani ni imarka"
taba kofar yayi ammah arufe duk da in yayiwa kofar kwakwkwaran bugu zata iya ballewa domin bawata koface mai kwariba.
kwankwasawa zanyi ? ko kawaii na tafine tunda nadebajin ihun ammah tabbas daga gidannan naji ihun Muryan mace ne kuma tabbas wani abune yake faruwa da ita domin alamun tashin hankali sun,bayyana cikin ihun ,kuma natsatstsiyar murya ce kowace me muryan tana da sanyin murya but...me yake faruwa ne naji tadena ihun ?
yakai mintuna uku yana saka da warwara a zuciyarsa daga bisani yadara kwankwasa gidan ,ya jima tana buga gidan ammah bako alamar motsin za a bude.
juyawa yayi yakoma motarsa domin har 1:00pm tayi ,key yasawa motar taja har ya ja kuma sai yayi reverse yayi parking ,haka kawai yaji baxai iya barin wajen batare da sanin dalilin kukan da yajiba tabbas me kukan tauki take nema.
Kafa yasa yafara dukan kofar gidan ,duka biyu yayi kofar ta bude kansa tsaye yashiga gidan dakuna biyu yagani suna kallo sa ammah ba kukan yarinyar.
tana kwance kan mahaifiyar tata tana kuka mara sauti,domin ita atunanita tariga ta mutu ,da sallama yashigo dakin tare da kunna haske a wayarsa domin dakin bawani wadataccen haske,aiko take haske ya gauraye dakin tamkar rana afirgice ta daga kanta domin dataji sallama ta sauka ko kunnentane yajiye mata karya ammah ganin haske yasatagane mutumne
Auzubillahi!tafara fada tana ja da baya ,shima tsoro tabashi gani yayi kamar aljana ce ba mutumba.
budurwa ce yar matsakaiciya bata da kiba kuma ba siririyabace,tana da san tsayi kadan bagajerabace,farace tas manyan idanuwanta dasukayi jajir suka kunbura sai suka kara fito da kyanta alamun taci,kuka har hawayen sun kafe ,dogon hancinta da matsakaicin bakinta sun dace da fuskarta ,gashin kanta yayi buxu buxu ya sauko har kafadanta yarufe wani sashena fuskarta, kirjinta cikeyake dadukiyar Fulani ,sa shape din kugunta daya bayyana acikin suturar dake jikinta,lokaci daya tamata wannan kallon da sauri ya sauke idonsa daga kallon kurillar da yayi mata dan cigaba da kallon ta ……
kanta sunkuye tana cigaba sa kuka tana karanto duk adduar datazo bakinta l,karfin hali yayi yakarasa gunta daya fahimta tsorone ya kamata,kiyi shuru dena kuka yacemata.haska fuskarsa yayi da fitilar wayan yace kingani i am woman being like you so stop crying bar tsorona,baze juri kallonta ahakaba sai yace Ina hijab naki sa sai muyi mgn ,kallon shi dai takeyi tana kokonto ko dai aljanine ,kisa hijab naki jeki dauko yana ina ?wannan karonma kallo kawaii tabishi dashi ammah da alamun tarage tsoronsa.yana ina indauko miki? ya tambayeta domin kayan jikin ta sun bayyana halittunta bai kamara suciga da mgn a hakaba rabin kirjinta duk awaje yake,yana ina ?yakuma tambaya akaro na 2nuni tayimasa da bayansa yana juyawa yaganshi rataye jikin kofa jawowa yayi yakarasa inda take yamikamata ,kallon sa tayi sa Kuma ta kalli hannun ta ,shima hannun nata yakalla a kunbure yake kara haskawa yayi kunace sabuwa,hartaja ruwa a duka tapikan hannun,oh!sannu yacemata daf da ita ya karaso ,hijabin hannun sa ya ajiye akasa yafara kokarin yayemata gashin da ya san rupe mata fuska jir jir tsikar jikin sa tafara tashi yanajin wani irin yanayi ajikinsa,itama jikin ta kyarma yakeyi domin jitakeyi kamar cutar da ita zaiyi, sannu ahankali ya dauremata gashin abayanta hijabin,ya dauka yasamata,sannan ya san ja da baya
Nazo wucewa naji kukanki harda ihu meyasameki?kuma ya akayi,aka barki agida ke daya?meye ya konaki a hannu haka ?ya karasa maganar cikin dashashshiyar murya
bani dayabace umminace ta mutu
nayi tunanin ko sunane naje kitchen debo ruwa nayi tuntube na fada kan,garwashi na dafa da hanayena ,cikin sanyin murya take maganar ta karasa cikin kuka me ban tausayi
tundata fara maganar yake kallon ta har tasaki kukan ,shima jiyayi wani guntun hawaye ya saukomasa ,antafi da ummintaki asibiti ne ?ya
Yambayeta?Aa gatacan tanuna mai mai gefensa na dama,kanwata motsatstsiyar katifa ya hangota kwance ,dasauri ya karasa wajen cikin yanayin damuwa yace kukadaine agidan ?eh mukadaine tabashi amsa,matar dake kwance yasa hannun yadaga,ammah ba alamun numpashi atare da ita ,da sauri yajuyo meyesameta?yacemata .
tun dawowata daga islamiyyah da yamma tace cikin ta naciwo tare da kainta kuma rasha magani,
kamatamuje asibiti ba mutuwa tayiba dogon sumane,kuma kinyi wauta kamata yayi kije makotakinemiTaimako ba kizauna kina kukaba,cikin pada pada yakarasa maganar yana yunkirin daga matar dake kwance kamar gawa,da sauri ta isoshi ta kamata sukayi,hanyar fita daga dakin,tunima ta mance da ciwon dake hannun ta dan murna jinyace sumane bamutuwaba,har suka fito tana rike da kafadar ummintata shima yana rike da daya bangaren,radadin da hannunta kemata ne yasata cije lebe hawayenabin kumatunta,
saketa yace ,dama namancene da ciwon hannunki ,dagata yayi yasa abayan motar sannan yarufe yazagayo da
Sauri sauri yabude yazauna amazaunin driver,sauri daukimin phone na along with my motor 's key inside your room,hurry pls yapadamata,da sauri yake maganar sbd shima yapara tunanin matar ta mutu sbd wani i irin nauyi dayaji tayi,da sauri tajuya dan cikia umarninsa.
"allah sarki tanajin english kenan yapada aransa "
cikin sauri tashiga gidan,dakin tashiga wayan ta dauka ammah bataga key ba haske haske taparayi can ta hangoshi kan katifar da umminta ta kwanta daukatayi ta haska kan window tadau Wani dan karamin makulli ,da gudu gudu ta fito,karo sukaci a dai dai kofar gidan da sauri yaja baya itakuma ta sape goshinta,karba yayi ya shige motar,itakuma tafara kokarin rufe gidan .
"kinyarda dashi kenan dazakibishi?bakisan waye bane ammah kikabashi hadinkai yasa umminki a,motarsa kema zaki shiga"wani bangarene na zuciyarta yake kokonto akansa.ammah data tuna halin da umminta keciki sai taji zata iya binsa ko zai yanke kantane dan inba umminta to gara itama babu ita, BAYAN WUYA SAI DADI
Ammah ita tata WUYAR zai zama BAYAN WUYA SAI KUNCI inhar tarasa ummintatana wannan tunanin taji yace hee!da karfi yadafa dan ganin taki juyowa ga duhun unguwar tasu ba kyau .
Gudu yakeyi tamkar zai tashi sama,ammah gani yake kamar ba sauri yakeba,dau wayannan ki nemaminnumber ammah sam batajishiba dant ayi nisa atunanita.
sannu ahankali yarage gudun motar yafara laluben number din,ringing biyu aka daga .doctor kana ina?
MATAZ laphia bako sallama ?kuma laphia kakenemana yanxukabarni a hospital Fa,ina nan AMINU KANO HOSPITAL banje ko inaba aikin kwana ke gareni ,allah yasa laphia ?
oh!ya furzar da numfashi ba laphia doctor pls kar kayi nisa ganinan zuwa da patient kataremu zan tsaya emergency .
okay,sai ka karaso sister nace ba lpy kowa ?Aa doctor,patient din asume tske kataremu yanxu, baijira mezai ceba ya kashe wayan.
Tun kafin sukaraso doctor yafito tararsu sai dayayi jira na tsawon mintuna 7 dan tunda da yaji doctor mataz da kansa to yasan ba karamin aiki bane danko rashin lapiyar iyayensu ko matarsa da kansa yake dubasu agida,yapi tunanin ko taimakonsane ya motsa danko karpe nawane na dare yakan iya pitowa dan taimakon patient dinsa.
da wannan tunanin yaga motarsa ta haskeshi.
nurses ne sukasata kan kan wani gado mai taya sukayi ciki da ita sukuma suka take musu baya ,
MUTANE uke kanta suna kokarin ceto ranta doctor sam'u,doctor jamila sai jigo kuma jagiransu doctor MATAZ .
aiki suke tukuru,iya kwarewarsu cikin nasara suka samu numpashinta yafara harbawa, ALHAMDULILLAHI doctor
Jamila tapada,matsawa sukayi daga kusa da gadon suka koma can nesa da ita,ALHADULILAHI ALA KULLI HALIN,doctor mataz yaketa maimaitawa,shima doctor sam'u masha Allah yace.
sannan nurses suka karaso su2 , ruwa a container sukazo dashi suka bawa konne ya wanke hannuns tare da wani kyalle na goge hannun ,bayan kammala wannan .
wata nurse ce ta dubi doctor mataz tace "doctor meyesa wannan patient din take fitar da jini ta hanci sosau haka"?kinsa in MIGRAINE 《ciwon kai maitsanani wanda kesa mutum gani Da kyar》ya tsananta jini na iya fita ta hanci,yabata amsa lokacin datake kokarin rubutawa a joter dake hannunta,
i think wannan patient din,tana,bukatar karin jini ,doctor jamila ta fada,nima nayi,tunanin haka cewar doctor sam'u .
baizama obligation ba intasamu SQUARE MEAL 《abinci,mai kyau da gamsarwa 》ma zai wadatar basai ansa jini ba cewar doctor mataz,dukkan su suka amsa da to .
doctor sam'u ne yabawa nurses din umarnin sukai patient din 《I C U 》intensive care unit ,wajen da aka tanada a Hospital dan bawa marasa laphia sosai kulawa,sannan su samata ruwa,yadda ya umarcesu haka sukayi .
doctor jamila ce ta kalli doctor mataz tace doctor patient dinnan tanada matsaloli sosai, brain dinta yana fuskarta matsala,sannan na fahimci NERVOUS SYSTEM dinta yadena control din C N S and P N S ,mungode allah da HEMOSTASIS dinta yana lpy doctor mataz yafada yana maiyin,hanyar fita daga dakin.
zuwa safe zata tashin insha allah sbd tasamu long faint ne 《dogon suma doctor sam'u yafada ,suma suka Bi bayansa sukafita.
Acan falon emergency suka sameta tana rakube ta takure sbd weather sanyi ne,inda take suka,katasa,doctor jamila ce ta dafata tace come down ,patient dinki na lpy kinji ,zata tashi,zuwa saphia mamarki ce?doctor jamila ta tambayeta,kai ta dagamata alamar eh!yasunanki?takuma tambayatr,AFIFAH tafada tana kallon doctor jamila afifah kwantar fmda hankalinki,muje innunamiki inda mamarki take.
doctor kisa ayi treatment din hannunta takone a hannayen duka 2 ,doctor mataz yafadaya Mesamun guri,ya zauna .
ayyah !sannu muje afifah tadan dafa kafadar ta suka bar gurin.
doctor ina kasamu wannan smart girl din,da patient din duka ?ni daka barnan hida kacemin zakawuce,doctor sam'u ya fada.
dana tafi hanya banason bin kan titi sbd dare,sai narinka bi tacikin,unguwanni, ya kwashe duk labarin yafada masa ,sannan yace maybe baban yarinyar ya mutu dan,nafadama su kadaine agidan .
doctor sam'u ya goge gumin da ya fito mai duk da air conditioning din,dake falon,aransa yanacewa "wai Wannan wane irin mutum ne baya tsoron ya jefa rayuwar sa cikin hatsari muddin in wani zai ampanesa,yanxu haka aikin da sukayiwa matar daya kawo da kayan aikin dasuka bata da maganin da zasubata daga account dinsa zaiyi transfer zuwa account din asibitin,yana taimako da jikin sa da aljihunsa,
Gaskiya doctor kadena saka kanka a hatsari haka,bance karkayi taimakon ba ammah kadena shiga gidan mutane kai tsaye haka kuma cikin dare ,da tsautsayi ya gifta kaga da kasamu cikin matsala,ko daraba ai baka Shiga gidan mutane ba balle dare gaskiya kakiyaye my brother wannan jawabin duk,sam'u ne kewa mataz
gaskiya nigeria tanada bambanci da sauran,kasashe,doctor mataz yafada yanxu inda allah bai kainiba haka,bayin allaan nan zasu zauna har matar ta mutu ,bawanda zai kaimu su dauki ,,kuma yarinyar tana kuka yanda makota zasu iya jifa ,Hum!mutane wasu ba tausayi ammah awasu unguwannin da abu yafaru zakaga anfito cewar doctor sam'u yakuma cewa ammah dan kasaba da rayuwar england shiyasa kake ganin
Nigerian wani iri zaka saba ammah kadena shiga gidan mutane nan ba england bane.
doctor mataz yayi dry yace wai har zakacemin ba dan nigeria ba,to nida kai wayafi wani dadewa a england ?caraf doctor sam'u yace kafini dadewa sosaima,to naji nafika dadewa ammah kaima kaxauna can dai to kaga cewa ni ba dan nigerian bane bematasi ba.
umamah ce dai ta dade sosai gaskiya,dan haryanxu ita bataki mukoma canba, doctor mataz yafada yana duba agogon dake daure a hannun sa,taji dashi takoma ita kadai Mana doctor sam'u yafada yana dariya,Bari zan wuce doctor,kakula da patients dina dasafe zan dawo goma ko xuwa sha daya,doctor sam'u yace da kabari ayi asuba sai mutafi tare,umamah bana ganta agida da yamma ba kasan inta kai yamma maybe can zata kwana inbaka biya ka dauketa ba,Aa nace ta koma gida zan koma karfe goma sai kuma gashi nasa6a,nasan tanacan afusace dana koma zata fara korafi doctor mataz yafada ,wayace ta auri likita,damata auri wannan baturen da ya manne mata a england dara huta
Cewar doctor sam'u yana dariya,doctor mataz ne yamike zai fita yace gauron banza kawai yanxu mai zai hana ka kwaceta jka aurawa baturen tunda ka isa,yafice batare da ya saurareshiba.
Adaya bangaren kuwa afifah ce zaune gefen gadon da aka kwantar da umminta.
doctor jamila ce ta shigo ta kalli afifah tace kar a tasheta fa daga barcin zata samu nutsuwa data farka,kuma ga magunguna ki duba da lokacin sha yayi kije kikira nurse,sannan kina shan wannan maganin tamikamata su tare da flask na abinci da Tea da ruwa a robar suwan,kici abinci kinji akwai toilet a nan,baya inkina bukata ,nizan tafi zan fuba,marasa lpy.
mungode doctor ,afifah ta fada tana matse hawaye a idonta,bakomai kanwata tashafa kanta sannan tafice daga dakin tana tana ta wani tunani aranta "da alamun damuwa atare da yarinyar ko ina doctor yasamo yarinya me kyau hk,haka kawai taji yarinyar tana sonta kuma tabata tausayi sosai daga gani bawani karfine dasuallah sarki "da wannan tunanin doctor jamila takarasa MATERNITY WARD
(wajen da masu ciki da wanda suka haihu ake kula dasu).
doctor mataz yana isa yayiwa megadi hon,nan danan wayage masa get yashiga.key yasa ya bude falon yashiga,aiko can kasan kujera ya hangota akwance barcin ta take cikin kwanciyar hankali murmushi yayi sannan yawuce bed room yafara watsawa jikinsa ruwa sannan yafito falon,inda take kwance ya karasa yasa hannun ya shapi kumatunta yayi kissing goshinta,kamar a mafarki taji kanshin turaransa ahankali tabude idonta ido suka hada,hade rai tayi ta
Juya masa baya,oh!sorry babynah yasa hannun ya dagota dirshan yazauna a kasa sannan yadorata akan cinyarsa,tawan karmuyi haka mana habarta yadago yahada goshinsu kowannensu yana shakar nufashin dan uwansa,kara narke masa tayi tana zun6ura baki,cikin shagwaba tace sweet meyesa ka dadene nifa whl nagaji dazaman kadaicinan,daka fita jinake kamar nayita kuka gidan shuru nidaya,sweet mukoma gida mana sai,muzauna a part dinka kaga dakafita sai in tafi part dinsu momy ai yayi ko?takarasa maganar tana
Shafa sajen dake fuskarsa,dariya yayi yace wai yaushe zaki girmane umamah ?anyi miki aure fa dankizo kizauna kuma sai,mukoma inda muka baro,wato dan kullum kije kina hayewa cinyar momy tunda yanxu tahuta ko?wai kai ina ruwanka da cinyar momy danake hawane ba ita ta sabamin ba,Aa momy ta huta cinyar momy ta abbanmu ce kega takinan yanuna cinyarsa datake zaune akai,duka ta dakamasa akirjinsa sannan tace allah sweet baka da kunya yanxu momy ada abba kake dadawa hk,cikinta ya shafa yace kinci abinci Kuwa ?nasha tea tace mai,hade rai yayi yace kinganifa banaso,ace mutum bashi da abinci sai tea dan allah kinacin abinci sosai karki wahalar min da baby nafison ki haifomin katon baby mai kumatu kamar abu hurairan auty saudat,
Allah sweet ba fruit ne a fridge,nikuma innaci abinci bansha fruit ba sai inji zuciyata natashi kamar zanyi,amai,da kin duba fridge din dakina akwai,dama wasu masu cikin haka yake musu,nagode Allah ma da fruit kike sha ba wannan kasar ba ya karasa maganar yana mejan hannun
Zuwa table dan cin abinci,sai yabata ta goshi sannan shima yaci,tashi tayi tanufi dakinsa shima yabi bayanta ,fridge tabude tafara zaban fruitswanda rantake so,sai data sha ta koshi sannan ta kslleshi tace bismillah tana dariya,alhadulillah yacemata,sannan ya cire jallabiyar dake jikinsa Breeches (gajeran wandon dayawuce gwuiwa )kawai yabari ajikinsa .
mikewa tayi,inazayaki tambayeta ?wanka tacemasa ,na hanaki wanka fa dakinci abinci ,da gudun ta fada toilet tanacewa sorry sweet nadena . Tattara wajen datasha fruit yayi sannan yafada gado tare da daukan remote din dake kan wani karamin table dake gefen gadon.
tana gama wankan tacikin toilet dinsa akwai kofar dazata sadata sanata toilet din sannan tashiga ta wata kofa ta wuce dakin ta,sai data gama shafe shafenta sannan ta samu wata riga iya gwuiwa mai hannun bes tasa,dakin ta rufe sannan ta biyo ta falo takashe hasken falon sannan tayo dakinsa,akwance tasameshi yana kallon film din LIGHT AND DARKNESS na jammaje production Jikinsa tafado,Ash!wai yaushe zaki dena wannan tsalenne baby?ya tambayeta,kanta ta doran kan kirjinsa sannan tace sweet wai babynmu zaiji ciwone in ina tsallene?ehmana yabata amsa,kanta yashafa ahankali yace nayi missing dinki tawan,banayita kiranka ba baka daukaba tafada tana jan dogon hancinsa,
Kawai sai yarinyar ta fadomasa arai "Afifah ya mai maita a ransa, yana hongo kyan sura irin na yarinyar ammah tana rayuwa cikin wahala "iska yaji ra huramasa a idonsa tunanin mekakeyi sweet tacemasa Abinda yafaru yakwashe yafadamata,har da dan,kuntun hawayenta itama ,sweet kadena shiga gidan,mutane kar watarana ayima sharr,to babynah yajawota yayi yakara matseta ajikinsa kamar zai tusata cikinsa,ahankali yafara kissing din wuyanta,ta ko inah yake kaimata sumbata can yaje dai dai bakinta yahade danasa hot kisses yake kaimata,itama tana,mayar masa da martani sun dau tsawon lokaci suna tsotsar bakin junansu sannan yasa hannu yafara cire rigar dake jikinta yana shafa jikinta yana isowa kan
Bobs dinta yafara shafawa yanasqueeze dinta,sannu ahankali yasa bakinsa yafara tso……su cikin wani salo nasa na daban,nishi takeyi kasa kasa tana shafa kansa tana sumbatar goshinsa ahankali tasa hannunta tana shada ko ima ajikinsa wash……baby da……sosai suka fita hayyacinsu suna fadawa juna kallaman kauna,yana shirin isa birnin tarayya ne nace FIRRAM zomu barnan karmu ganewa idonmu abinda yafi karfinmu.
Nan muka tattara alkalaminmu da takaddumu mukayo waje sai damuka tsaya mukasharuwa a fridge din Falon dan tunda,muka fara kawomuku rahoton bamu sha ruwaba sannan mukayo waje,motar FIRRAM muka fada tajamu muka fice daga gidan danni kunsan bani da mota sai dai inkun gaji da ganina a adai daita sahu ku saimin ,SIRRIN YAMACE GROUP daku nake.
Can asibiti muka koma dancigaba da sauko muku rahoto.
AFIFAH ce zaune kan sallaya tana jero addu'oi,zuwa can data gama tsfara karanta kur'ani cikin kira'arta me dadi muryanta kasa kasa.ko agida wani lokacin bata duba wur'ani sbd tanada haddarsa tun tana
Yar shekara 12 sai dai intayi kwadayin samun ladan daukar qur'ani saita duba,haka yanxu hadda take karantawa cikin suratul baqara.
Tari taji,da sauri tajuya ta kalli in da umminta kewance kan gado,dasauri tayi wajenta kafin ta karasa har robar ruwan da akasamata a hannu tacire dafa hannun nata,ahankali tarin ya lafa ta bude ido tana yunkirin tashi zaune da sauri afifah takamata tazaunar da ita,sannu ummi afifah ta fada,daga mata kai kawai tayi RUWA!ummin tafada ahankali nanma da sauri afifah taJe wajen datayi sallah da ruwa ta dawo cikin wata robar suwan wacce doctor jamila ta kawomata.
sai data shanye sannan ayi ajiyar zuciya,Bari nakira likita sunce inkintashi inkirasu tajuya zata fita,rike hannunta tayi tace bari afifah alhadulillah jikina yamin dadi basai kin kira likita ba,duk abinda Allah yatsara mutum bazai iya canzawaba,Bazata iya jayayya da umminta ba shiyasa ta zauna agefen,gadon tayi shuru tanajin wani sanyi aranta.
Afifah!Na'am umm.
waye yakawoni asibiti ?ummi ta tambayeta
Anan afifah ta bata labarin abinda yafaru hat zuwa karshe,wanne bawan Allah ne haka afifah ?ummi nima bansashiba da farkoma tsoro yabani wai taxo wucewa yaji kukana yayi yawa kuma yaga makota bawanda yafito shikuma wucewa yazoyi,Na Allah basa karewa Allah ne yadubemu cikin tsakiyar dare ya aiko manashi,ammah daga yau karki kara irin wannan kukan afifah ko mutuwa nayi banyarda,kimin kuka msi daga sautiba duk sa kukan makine yanxu yazama mana magani yanxu ,to ummi ammah kidena zancen zaki mutu dan
Allah,ummi wani dan,guntun murmushi tayi sannan tace anyi asuba?naji anyi ikama ammah yanzu za'ayi afifah tabata amsa,afifah kamani inyi alwalah kamata tayi suka zagaya imda bandakin yake,da taimakon afifah tagama alwalah.
sai data dara rama sallar magriba da isha'i sannan tayi shada'i da wutiri,tayi sallar asuba duk azaune.
Bayan ta idar da sallarne tace yarinyata zo zauna nan tanuna mata kusa da ita,
AFIFAH !takira sunanta,na'am ummi afifah ina sonki fiye da sauran yarana.ummi kina dawasu"yaya bayanni afifah tafada, ina da yara 3kece ta4,afifah tun sanda kikayi wayo kikafara tambayata "ina babanki"lokacin da hankali yafara shigar ki sai kicemin "wai ummi mubamu da yan'uwane?"ni kuma alokacin sai narasa mezan cemiki sai namiki shuru hai ki manta,tunda kika fahimci ina shiga damuwa inkika tambayeni ina babanki da yan'uwana dana babanki sai kika dena tambayata,bawai naki fadamiki bane afifah kuma karkiyi zargin koke shegiyace shiyasa naki fadamiki inda mahaifinki dayan'uwanki suke Kina da cikakken asali kuma kina da mahaifi.
Duk sanda nayi yunkirin tuna ni wacece sai inji nakasa inna takura saina tina sai kaina sai kaina yafara ciwo wani irin ciwo mai azaba ,da hk har nacire abin araina nadena son intuna labarin meye da iyayena,yan'uwana da mijina dakuma yayana wannan yasa kikaga ban fadamiki waye babanki ba.
Amma ayanxu zan iya fadamiki wasu daga cikin tarihina,anaji acikin kwakwalwata natuna wani abu daga labarina ammah nakasa tuna wasu wanda natuna yafi wanda ban tuna
Ba yawa,matsawar danayi sai na tuna shine yasani wannan ciwon kan,danake ciki yanzu.
ummi mungode Allah dakika tuna,ko muma zamu koma rayuwar ciki yanci ummi naji dadi sosai muma yanzu zamusan matsayin mu mudena rayuwar wahala dama BAYAN WUYA SAI DADI...afifah tafada ranta cike da farinciki .
murmushin takaici ummi tayi sannan tace"Afifah ke kanki bansan sunankiba har yanzu nakasa tuna sunanki,sai yanzu nagane ashe ada tuna abune bana iyayi sai yanzu nagane meyesa nake kasa tuna abun daya faru Dani,nakasa gane meye sunana,sunan mahaifina da mahaifiyata sa sauran,yan uwana wanda yanzu hk ina ganinsu acikin idanuna,na manta sunan mijina sauran yarana "adai dai nan tafashe da kuka itama afifah kukan takeyi domin murnarta takoma ciki,zuwa can tace "afifah abinda yafimin ciwo yanzu nakasa tuna inane garinmu"ammah bari inbaki tarihin rayuwata da yan'uwana hat da mahaifinki da yadda na barsu domin inaji ajina kamar bani dawani lokaci nangaba gani gani nake daga yanxu zuwa kone lokaci mutuwa Zata iya zuwamin.sbd wani mafarki danayi acikin barcina.
MEYE LABARIN UMMI ?MEYA RABATA DA KOWA NATA DATAKE FADI?BATASAN SUNANTA BA HAR DA DIYARTA DASAURAN MAKOSANTANTA MEYA FARU DA ITA HAKA?AFIFAH TAKE KIRAN DAYAR TA DASHI AMMA TACE BATAN SUNAN DIYARTA TABA TO MEYE SUNAN AFIFAH ?TAYA AKE KIRANTA DA AFIFAH TUNDA TA MANCE SUNANTA?WAYE DOCTOR MATAZ,DOCTOR SAM'U,UMAMAH ?WANDA LABARIN YANA NUNA MANA KAMAR YAN GIDA DAYANE ?
wadannan amsoshin suna page 34 kubiyomu dan sanin amsoshinsu
taku FIRRAM .✍🏻
0 comments:
Post a Comment