Monday, 5 March 2018

TANA RAINA Page 16-20

51-52 Yah suhail yacibaga da kallon sabreen ko kyafta ido bayayi, sabreen ta lura da irin kallon da yake mata tace dashi ina zuwa, sannan ta koma ciki ta d'auki himar d'inta tasa seta fito. Palo ya koma yana jiran fitowanta, bayan ta fitone lokacin yanata zagaye palon se tace yah suhai gani. Juyowa yayi yana kara kallonta sannan yace sabreen d'azu da safe bayan nabar d'akinki naji abinda kike cewa dagaske abinda naji? Bugawa k'irjinta yayi tace me kenan yah suhail? Ya matso kusa da ita yace naji kina cewa kece yarinyar da nake nema, a'a ba haka naceba wata yarinya kuma ya suhail ni sunana sabreen, hannunta ya rik'o dukka biyu take jikinta ya fara b'ari yace sabreen "pls tell me the truth" danna dad'e ina nemanta kuma dama zuciyata tanata waswasi akanki duk lokacin dana had'a ido dake sabreen, sannan wasu lokacin ina tuna muryanki dan Allah ki gayamin gaskya sabreen. Hawayene ya fara zuba daga idon sabreen tana kallon idonsa tace NICE yah suhail, sake hannunta yayi tare da juya mata baya yace "Ohh My Gosh" sabreen meyasa, ya juyo yana kallon idanunta cike da tashin hankali yake magana meyasa kikamin haka sabreen "why" meyasa baki gayaminba tuntini, yanzu gashi aminina ya wucemin gaba why sabreen kamar zaiyi kuka. Sabreen tace kayi hakuri yah suhail, hakurifa kikace sabreen taya zanyi hakuri bayan kinsani a cikin tashin hankali, sabreen kinsan yadda nake k'aunarki a raina kuwa, kanta ta d'ago tana kallonshi ji take kamar ta rungumesa dan yadda taga hankalinsa ya tashi, sake matsowa yayi yana kallonta cike da tausayi yace sabreen baki kyauta minba yanzu shikenan ya kikeso nayi da k'aunarki sabreen? Sabreen ta juya tana kallon bayanta dan bataso hafsat ta fito ta samesu, tace yah suhai kar hafsat ta fito ta ganmu barina d'auko wayana kasamin number'nka semu k'arasa a waya pls, kansa ya kawar gefen cike da damuwa, ita kuwa d'aki ta koma ta d'auko wayanta tazo ta mik'a mishi, ya karb'a yasa mata sannan ya mik'a mata tare da rik'o hannayenta yace kafin ki tafi inason jin kalma mai dad'i daga bakinki sabreen, kallon juna sukeyi tana hawaye tace "I LOVE YOU", wani dad'i yaji a ransa baisan lokacin daya janyotaba ya rungumeta a k'irjinsa yana jin k'aunarta na ratsa jinin jikinsa, kok'arin janye jikinta takeyi amma sam ta kasa dan yadda ya k'ank'ameta yana cewa "pls let me be sabreen" na wannan lokacin kawai sansan ya tsubaci bayan wuyan yana cewa "I LOVE YOU MORE SABREEN". Kusan 3minit sannan ya saketa dan kar mum ko hafsat su fito, kanta a sunkuye dan kunya dataji, ya shafi kumatunta yace kimin flashin yanzu kinji? Kai ta d'aga batare datayi maganaba, murmushi yamata sannan ta juya da sauri ta shige d'aki sannan shima ya fafi.
Koda ta shiga d'aki setaji sabon kaunarsa yana ratsa jikinta, himar d'in ta cire ta kashe wutan d'akin ta kwanta sannan ta kirashi harya fara ringing setaji ya katse ya sake kiranta. Hello sabreen, na'am, yanzu kaka yasan maganan? A'a kaka baisan komaiba yah suhail babu wanda na gayawa se k'awata munira, suhail yace tomesa baki fad'aba? Sabreen tace yah suhail nifa mutanennan basumin komaiba, suhail yace kamar ya basumiki komaiba sabreen? Sabreen ta sauke ajiyar zuciya sannan tabawa suhail lbrn abinda yafaru acikin yanayi najin kunya. Mamakine sosai a fiskan suhail yace to ita wannan d'in wacece? Sabreen tayi karya tace nima ban santaba wlh, kan suhail ya d'aure kuma ya kasa yadda da abinda sabreen ta gayamasa. Itama sabreen tagane cewa bai gamsu da maganantaba, tace yah suhail nasan bazaka yadda amma wlh gaskya na gayamaka basumin komaiba. Suhail yace sabreen kina nufin har yanzu ke cikakkiyar budurwace? Sabreen taji nauyin maganan nasa sosai amma seta daure tace "EH" hakane yah suhail. Idanunsa ya rufe yanata juyi akan gadonsa had'e da takaicin yanzu shikenan ya rasa sabreen, taji yayi shuru baice komaibane se tace yah suhail ya naji kayi shuru? Yace bakomai sabreen ina cikin damuwane kawai bansan ya zanyi da k'aunarki a rainabane gashi kin amincewa AMININA gaskya ina cikin damuwa sabreen. Sabreen ta tausaya musu dukkansu tace yah suhail ba kana eman hafsatba? Suhail yace sabreen hafsat had'in iyayenmune bawai don ina sonta bane kekad'ai ce a raina sabreen kinsan da wani suna kamal yake kirana? Tace a'a, yace angon "TANA RAINA" saboda na saki a raina sosai kuma da wannan sunan nake kiranki kullum. Sabreen tayi murmushi tace eyyah nima "KANA RAINA" tun bayan had'uwanmu yah suhail munira ma shaidace akan hakan, dad'i sosai yaji yace to yanzu me abunyi sabreen? Tace gaskya babu wani abunyi yah suhail bazan iya juyawa yah kamal bayaba tunda harna amince mashi, suhail kamar zaiyi kuka yace kina nufin ni in hakura kenan sabreen? Cikin muryan kuka tace "EH" hakan nake nufi ka auri er'uwarka suhail ka manta dani, yace bazan iyaba sabreen bazan iyaba. Zaka iya yah suhail seda safe, yace sabreen dan Allah karki kashe wayan, amma ina ta kashe tareda swiching nashi off.
             Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
53-54 Suhail ya sake kiran wayanta amma se yaji a kashe, kwallane yaji yazo masa ido. Ya goge kwallan yanata tunani me mafita yanzu, amma sam shi kansan yasan babu wata mafita dan kuwa bazai iya cin Amanan kamal ba. Itama sabreen kodata kashe wayar kuka sosai takeyi dan tasan suhail yana cikin wani hali, kuma itama haka dan sam bata son yah kamal, koda tana sonshi kuwa to dai suhail shine a ranta. Seda tayi kuka sosai sannan, bacci barawo ya kwashesu dukkansu biyu.
Washe gari da asuba bayan su kaka sun dawo daga masallacine suhail ya sami kaka har d'akinsa ya gaya masa duk yadda sukayi da sabreen, kaka ya nuna mamakinsa a fili yace to gaskya dai na yadda da maganan sabreen dan babu yadda za'ayi maza har uku su mata fyad'de kuma ta dawo gida lafyanta lau, suhail yace hakane kaka ni yanzu mafita nake nema kasan yadda nake kaunar sabreen tun kafin insan cewa itace, dan Allah kaka ka taimakamin, kaka ya tausayawa suhail sosai yace shule babu abinda,zamu iyayi akai sedai hakuri kuma kaci gaba da addu'a, dan nariga dana baiwa kamal sabreen kuma nasan kaima bazakaso ayiwa kamal haka ba. Suhail yaji wani iri a ransa amma seya daure yace hakane kaka kamal amininane harma mun zama kaman jininmu d'ayane na hakura nayita addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agareni. Kaka yace ameen sannan sukaiyi sallama suhail ya wuce gun mum d'insa a d'aki tana karatun Qur'ani maigirma. Bayan ta idarne suka gaisa tace yana ganka haka. Kamar bakajin dad'i? Suhail yace wlh mum ina da yar damunane amma dai insha Allah komai zai daidaita kisani a addu'a, mum tace toh agun aikine kodai, suhail yace eh kidai sani a addu'a kawai. To shikenan Allah ya yaye maka insha Allah zansaka dukda dai dama inani, to mum nagode zanje ind'an kwanta, to shikenan tanata bin d'an nata da kallo harya fita. D'akinsa ya wuce ua cire jallabiyansa ya kwanta tare da d'aukan wayansa ya kirana number'n sabreen, wani dad'i yaji lokacin dayaji wayar tana ringing, da sauri ta d'auka yace hello cikinc  sassanyar murya, shima dad'a kasa da miryan nashi yayi yace hello sabreen kin tashi lfy? Lfy lau ya suhail ya kake, sabreen bana lfy ina cikin damuwa sosai wlh, tausayinshi ya kamata tace nima haka yah suhail wani sabon k'aunar kane yake shiga zuciyata tun daga jiyan, da gaske kikeyi sabreen? Da gaske nakeyi yah suhail "I LOVE YOU SO MUCH", dad'i sosai yaji mara misaltuwa yace " i love you more sabreen and i will always love you till end", murmishi tayi tace pls amma karka sake kirana dan kar wataran yah kamal ya gani ko hafsat, suhail yace insha Allah sabreen zanyi kokari inga cewa na dena kiranki amma hakan bashine zai hanani dena sonkiba, nima haka yah suhail pls ka goge number a wayarka, ok sabreen I LOVE YOU byee, tace ok byeee sannan ta kashe wayar tare dayin deleting number'nshi tana mai tausayinshi.
9:30 suhai ya farka yaje yai wanka ya shirya ya fito palo mum da hafsat suna daining suna karyawa, zama yayi hafsat ta gaishesa tasha adon safe, ya amsa yana d'an mata murmushi yace kinyi kyau, dad'i taji tare da jin kunyar mum. Suhail yace ya banga kamal yazoba har yanzu ko lfy bari dai nakirashi, bayan ya kira sun gaisane yake tambayarsa ko lfy, kamal yace wlh maigadine bayi da lfy da ciwon ciki ya tashi yau yanzu muka dawo daga asibiti bazan samu zuwaba seda rana, suhail yace subhanallah to Allah ya sauwaka nima ina zuwa yanzu ka gaisheshi, ok zaiji sekazo. Mum tace meya faru ne? Suhail ya gaya mata, tace toh Allah ya bashi lfy sukace ameen.
Da wuri sabreen tayi abincin rana kamar yadda mum tace mata ta zubawa su kamal a kula suhail yakai musu. Sun dad'e sosai sunata ta hira har 4:00pm kafin nan suhail ya koma gida, kamal kuwa suna manne a waya da sabreen yace mata zaizo bayan isha.
  Haka dai rayuwarsu taci gaba da kasancewa, kaka yaje kauye ya gayawa aminan mahaifin sabreen zancenta da kamal, sunji dad'i sosai kuma sunyi farin ciki musammanma mahaifin munira yace dama munirama an aiko kuma wai suna son auren nanda wata biyu, shine aka yanke shawaran to abari a had'asu kawai nanda wata ukun.
Kamar yadda kuka sani dai auhail da sabreen suna cikin damuwa duk sun fita hayyacinsu musamman ma suhail abun har damun mum yakeyi. Ana cikin hakanne akayiwa su suhail waya daga pakistan cewa ana da buk'atar mutum d'aya yaje a tsakaninsu, kamal yace zaije tunda dama shine da zuwa, amma sam suhail yak'i yace shi zaije kaika zauna kacigaba da shirye2 aurenka idan na dawo sekaje koda sati d'ayane sekaje kayi ka dawo.
  Haka kuwa akayi suhail ya shirya ya tafi pakistan, dan a tunaninsa idan baya ganin sabreen abin zai d'an ragu masa, amma inah seya gwammace dama baizoba gara yadinga ganinta koda bazaice mata komaiba. Duk iya k'ok'arin da suhail zaiyi domin ya cire sabreen a ransa yayi amma abin se gaba2 yakeyi domin kuwa "TANA RANSA".
Kamal kuwa se murna yakeyi ya kusa ya zama ango kullum yana tare da sabreen.
                         Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
55-56 Sabreen tana kwance suna waya da munirane taketa ganin call d'in yah kamal yana shigowa, seda sukayi sallama sannan ta kira kamal harya tsinke bai d'aukaba. Kiransa ya sake shigowa ta d'auka tace hello, kamal yace dawa kike waya haka luv? Sabreen tace da munnira ne, yace ok ya take, sabreen tace lfyanta kalau.
Kamal yace luv kamar yadda na gaya miki cewa akwai wani magana da nakeso muyi dake mai muhummanci sosai kina jina? Sabreen tace eh ina ji, kamal yace luv amatsayinki na wanda zan aura yana da kyau kisan komai tun kafin muyi aure, sabreen banaso kiji kunyata ki saurareni da kyau. Kamal ya fara da cewa sabreen na kasance ina da matsala a matsayina NAMIJI, tun lokacin da iyayenmu suke raye muke zuwa can pakistan ake dubani, likitoci sun tabbatar da cewa nan da wasu shekaru zan samu lfy yayin da nake shan magunguna, to yanzu dai acikin lokacin da suke gayamin saura 5month kenan, danaso se bayan lokacin da suka d'aukamin kafin inyi aure, toh amma se gashi yanzu aurenmu saura 2month shiyasa naga yadace in gaya miki a matsayinki na wanda zan aura. Shuru sabreen tayi gabad'aya kunya ya kamata, kamal yaci gaba da cewa sabreen banaso in cutar dake shiyasa na gayamiki tun yanzu, zaki iya hakuri dani har tsawon 3month da aurenmu batare da....katseshi tayi da cewa "EH" zan iya yah kamal bakomai, dad'i yaji sosai yace nagode sabreen "i luv u", murmushi tayi tace nizanyi bacci seda safe, yace "ok luv gud night".
Ajiyar zuciya sabreen ta sauk'e tare dayin murmushi da haka tayi bacci. Washe gari da safe bayan ta gama breakfast taje gun kaka suna hira se kaka yake cewa sabreen naso inje k'auyen mu a sayar da gidanki na gado domin a had'a miki kayan d'aki amma se kamal yacemin baya bukatan komai daga garemu dukya d'auke mana abun har kunya yake bani wlh, sabreen tace shikenan kaka kayi yadda kaga ya dace dai. Kaka ya kalli sabreen yace har yanzu kina son suhail ko? Sabreen tace har abada suhail "YANA RAINA" kaka katayani da addu'a Allah ya ciremin shi a raina, kaka yana tausayawa jikansa yace sabreen....salam sukaji ance daga waje, wslm suka amsa sannan sabreen ta mik'e ta fito dan ganin mai sallaman樂 SALMA ce a tsaye tanayiwa sabreen murmushi, kaka yace yaya dai sabreen wayene, sabreen tayi shuru tana kallon salma sega kaka ya fitoa'a salma kece sannu da zuwa, salma ta gaisheshi cikin girmamawa sannan sabreen tace muje cikin gida. Suna tfya kaka yana binsu da kallo yanajin mamakin irin damuwa da salma tayi da sabreen yana cewa dama akwai soyayyane tsakanin mutum da aljan樂? Bayan salma ta gaishe da mum ne se suka wuce d'aki, salam tace amaryan kamal kenan, sabreen dai tsoro takeji a ranta wai ita da aljanace haka kuma batayi mamakin jin haka daga bakin salmaba, tace hmm ya kike yasu mamanki? Salma tace lfyansu lau sunce ingaisheki, sabreen tayi murmushi tace ina amsawa, salma tace nasan kina jin tsoro ko, karki damu sabreen bazan tab'a cutar dakeba ki d'aukeni kamar kawarki munira, sabreen tayi karfin hali tace toh dama tace in gaisheki sosai, salma tace ina amsawa wataran zanje mu gaisa inhar kina son hakan, sabreen tace inaso kam dan munira ta dameni da zancenki sosai, salma tace to shikenan idan zanje zan gayamiki seki sanar da ita, sabreen tace to barina kawo miki ruwa, salma tace yi zamanki bana bukata. Shuru sukayi na kusan 2minit se sabreen tace salma mutane ukun nan da suka miki fyad'e shin kind'au wani matakine a kansu? Salma tayi murmushi kad'an sannan tace eh suna can suna fama da jinya gabansu ga kumbura suntum tare da azaba sosai da suke fama dashi wanda koda wasa bazasuso sake yiwa wata mace fyad'eba. Sabreen tace to amma meyasa bakiba ta wani hanyan dabanba har kika bari suka miki fyad'en? Salma tace sabreen kaddara tariga fataa domin abinda yazomin kenan a wannan lokacin inaga ta hakanne kawai zan iya taimaka miki. Har sabreen ta bud'e baki zatayi magana se salma ta mik'e tsaye tare da cewa nizan wuce sena sake zuwa kuma☺, sabreen ta mik'e ta rakata har gate tare da cewa nagode.
  Haka lokaci yaci gaba da tfy bikinsu sabreen saura 2weeks 3days kaka yacewa mum zasu koma k'auyensu don shirin biki, mum tace to su bari se zuwa jibi kafinnan suhail ya dawo, kaka yace to bakomai Allah ya dawo dashi lfy, mum tace ameeen.
                          Sad-Nas



TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
59-60 Sabreen ta sunkuyar da kanta tace bari na shiga ciki, ta juya kenan se suka had'a ido da suhail da sauri ya kawar da kansa itama sabreen haka ta wuce d'akinta. Bayan sun gama cin abincine kamal yace mum jibi zan wuce pakistan insha Allah suhail zanbar komai a hannunka pls ka kula min da sabreen bare kuma zasu koma gida itada kaka so pls kayi duk wani abu dakaga ya dace, tace bazatayi program ba, amma wanda zai auri munira k'awarta ya kirani munyi magana akan za'a had'a gabad'ayane zamuyi dinner zan baka number'nshi seku had'u. Suhail yace ok badamuwa, mum tace toh shikenan seku maidasu gida gobe donyi shirye shiryensu tunda yanzu sabreen ta koyawa hafsat girki harta kware, hafsat tace mum nima zan bisu raka sabreen, kamal yace shikenan zamuje k'anwata. Shidai suhail zuciyarsa ciwo take mishi amma seya daure sunata hira cikin farin ciki.
Washe gari su sabreen suka shirya tsab suka fito, alkhairi sosai mum tamusu dama kuma kamal ya bud'e mata account tun suna gidanshi aciki yake sa mata kud'in aikinta ita da kaka, dan yana musu kyaitan kud'in kashewa sosai shiyasa bata tab'a na account d'in.
Can k'auye kuwa munnira tayi musu girki mai kyau kuma mai dad'i ga fura da nono ta share tsakar gidansu tas dama k'asane sosai a tsakar gidan dan haka ta shareshi tas komai dai yayi. 3:10pm su sabreen suka iso k'auyensu, da sauri munna ta fito ta rungume sabreen tana murna sosai tacewa hafsat sannu da zuwa, hafsat tace yawwa sannu, sannan ta kalli su suhail tace angwaye marabanku da zuwa, sukace yawwa amare, kakane yace bisimillah ku shigo, su sabreen suka wuce ciki su kaka suna biye dasu. D'akin munna suna wuce ko ina a gyare, dukda dai su talakawane amma sam hafsat bata kyamacesuba gidan nasu ya burgeta ko ina tsab, k'auyen ya bata sha'awa sosai, munna ta kawo musu abinci da fura dukkansu sukaci tare sannan sukasha fura, sabreen tace hafsat kinga gidan namu koh, hafsat tace wlh nikam gurin ya birgeni dasu yah suhail zasu yarda su barni in kwana se gobe in koma, sabreen tace ko'in tambayesu? Hafsat tace eh ki gwada, tafawa sukayi suna murna. Bayan su suhail sunci abincine sun koshi sosai se baban munira ya kaisu gun aminan mahaifan sabreen suka gaggaisa tare dayi musu addu'oi sosai, suhail da kamal sunyi musu alkhairai dewa sosai ga kuma kyautar kud'i, sunji dad'i sosai sannan suka kira su sabreen akan hafsat ta fito su tafi. Sabreen ne ta fito lokacin suhail ne kawai ajikin mota yana tsaye, ta karasa gunshi tace yah suhail dan Allah kabar hafsat ta kwana nan zuwa gobe seta koma, kallonta yakeyi sama da k'asa yace wazai maida ita goben? Sabreen tana kallonshi har cikin ido tace yah suhail base kazo ka d'auketaba gobe, suhail ya kauda kai gefe yace sabreen bata gayawa mum ba kuma skul fa? Sabreen tace yah suhail zamu kira mum yanzu kuma hafsat bata da class gobe pls ka barta mukwana, to sabreen hafsat bata rik'e kayabafa, ya suhail inada sabon d'inki nasan zai mata pls, ok shikenanto zan dawo gobe in d'auketa, nagode yah suhail, shima murmushi yake mata mai cike da kauna yace sabreen me ma'anar (SABSU)? Sabreen zatayi magana kenan sega kamal da kaka.
       Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
    By Mmn Shureim
           (Sad-Nas)
63-64 Suhail ne a tsaye jikin mota sega sabreen ta fito tana murmushi tare da karasowa gunsa tayi hugging nashi hannayenta suna mak'ale a wuyansa suna kallon junansu cike da so da kaunan juna, kiss ya manna mata a lips nata yace shine kika shanyani ko, tace sorry kasan abinka da mai ciki se' slow tana shafar fiskarsa da hannayenta, yace sabreen koda yaushe k'ara shiga raina kikeyi wlh bansan daliliba duk randa nake tare dake se inga kamar rananne na fara kaunarki a raina, murmushi tayi wanda ya k'ara mata kyau tace nima haka "swt hrt" d'ina uban yarana kiss mai zafi ta manna mishi a kumatunsa sannan ta shige kirjinta suka k'ank'ame junansu.
Mum ce tazo tanata nocking kofan suhail, a firgice ya tashi yana kallon d'akin nasa, wani haushi yaji aransa se yace na'am mum. Mum tace lfy kuwa kaketa bacci ko breakfast bakayiba gashi har 12:20pm kace zakaje ka d'auko hafsat, suhail yace wlh mum baccinne yamin dad'i ina zuwa, murmushi mum tayi sannan ta tafi.  suhail shi kad'ai yasan meyaji a wannan mafarkin, yace mum dabakizoba k'ilama d'aki zamuje da sabreen d'ina mu farantawa juna rai, oohhh,seya koma ya kwanta tare da rufe ido yace pls mafarki kaci gaba daga inda na tsaya mezai faru daga wannan gun da muke rungume da juna? Ohh noooo mum why, dakin barini ai nad'an huta wlh, d'ankwalin sabreen ya tsunbata yace dukda dai nasan mafarkine amma naji sanyi a raina sabreen, kuma kaunarki ta dad'u a zuciyata I LOVE YOU SO MUCH SABREEN
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
65-66 Bayan yayi wankane ya shirya tsaf, bayi breakfast sannan ya wuce kauyen su sabreen ciki da tunaninta a ranshi harya isa. Wayan hafsat ya kira tace to suna zuwa, basu jimaba suka fito dukkansu sunyi wanka sunyi kyau, tunda suka fito suhail yake kallon sabreen a sace yana maganan zuciinama da abinda ya faru a mafarkina zai faru yanzuma, sabreen ne ta katseshi da cewa sannu da zuwa uah suhail, mirmushi yayi yace yawwa sabreen ya kuke sukace lfy lau itada munira, yace ya mutanen gida, sukace lfy lau, sabteen tace ya mum? Uace mum lfyanta k'alau tayi kewarki, mirmushi tayi tace nima nayi kewarta wlh. Hafsat ta gaisheshi cike da so, ya amsa yana mata murmushi yace toya kwanan garin, tace wlh dad'i yah suhail kamar in sake kwana, yace to shikenan bari in koma, dariya sukayi dukkansu sannan yace kaka fa? Sabreen tace wlh sun shiga gari amma dai inaga sun kusa dawowa, ok yace sannan sukace bisimillah ka iso, yace a'a tfy zamuyi dama nazo d'aukantane. Hafsat tace yah suhail girki na musamman fa sabreen ta maka na dambun kuskus, suhail ya kalli sabreen yace to shikenan muje, gaba sukayi ita da munira suka barsu a baya har suka shiga ciki ya gaisa da mmn munna sannan suka isar dashi zauren baba. Wani yarone yazo yace wai ana kiran munira a waje, munna tace to kaje kace ina zuwa, sannan tace hafsat abbakar ya iso zomuje, hafsat tace ok muje sannan tace yah suhail bari inyi magana da angon munira akan shirin bikin ina zuwa, ok yace ta ita, azuciyarsa kuwa dad'i yaji yace zansamu inyi magan da sabreen. Bayan sabreen ta kawo mishi abincine seta zauna tana zuba mishi abincin yanata kallonta yana tuna mafarkinsa, yah suhail bisimillah ta ajiye mashi a gabanshi, murmushi yayi yace nagode sannan ya faraci suna kallon juna, wani sabon k'aunarshi ne yake shigan sabreen seta sunkuyar da kanta k'asa, suhail yace kunyi waya da abokina? Tace eh, yace gaskya naji dad'in wannan dambun nagode sosai, murmushi tayi tace akwai wani a kula seka tafi dashi, yace a'a ina kunyan mama, dariya tayi tace wlh bakomai dama nasamaka dewa dan nasan mum ma tana so, yace to shikenan sabreen? Tace na'am batare data kalleshiba, yace menene "SABSU"? Tace zan turo maka da ma'anarsa a waya, yace noo nidai ki gayamin anan, tace to ina zuwa sannan ta koma d'aki ta d'auki wayanta ta mishi texs.
      "SABSU" yana nufin sabreen nd suhail, tunda bazan samekaba wannan suna zai zauna a raina har abada kuma dashi zan dinga kiranka a raina.
Bayan suhail ya gama karanta texs d'inne seya tsunbaci texs d'in nata tare da rufe idanunsa yana mai tausayamusu dukkansu. Da sauri ya mayar da phone d'insa aljihu danyaji shigowar hafsat gidan, gunsa ta wuce tace kayi hakuri yah suhail nabarka kai kad'ai yace bakomai ina abbakar d'in? Hafsat tace yana waje yana jiranka dan munce mishi kana cin abinci. Suhail ya mik'e yace mujeto nagama, tare suka fita yayiwa mama sallama alokacinne sabreen ta goge kwallan idonta ta fito tace yah suhail har zaka tafi, zan tafi sabreen sannan suka fito dukkansu. Bayan sun gaisane sukayi hira sosai kamar sunsan juna sannan sukayimusu sallama sabbreen taje ta d'auko musu kuskus din suka tafi suna kewar hafsat itama haka.
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
67-68 Da daddare munna da sabreen suna d'aki suna hira ce munna take cewa ayyah har yanzufa suhail yana sonki wlh kinga yadda yaketa kallonki asace kuwa, nikamma har tausayi yake bani wlh. Sabreen tace hmm toya za'ayi munna nidai har ga Allah bason yah kamal nakeyiba, kawai dai zan aureshine kodon hafsat dan tana son suhail sosai kuma kinga hafsat mutumiyar kirkice Allah ya tabbayar musu da alkhairi, munna tace ameen sannan suka kwanta ko wacce tana waya da mijinta.
Bayan sabreen sun gama waya da kamal ne seta kira yah suhail, bai d'aukaba seya sake kiranta ta d'aika hello yah suhail kun isa lfy? Yace lfy lau ya muka barku? Tace lfy lau na kira hafsat shine nace kaima bari na kiraka inji, yace eyuah tnx, yace yo seda safe, suhail yace sabreen? Tace na'am, yace sabreen inaga lokaci yayi da zamu hakura da juna, na amince zan auri hafsat kema kuma ki koyi son kamal a ranki pls tunda kinga yanzu lokacin bikin ya kusa, to yah suhail insha Allah, kuma nagode Allah yasanya alkhairi, uace ameen by... tun bai gama cewa byee d'inba sabreen ta katse wayan tana ta kuka. Munira ta juya tana cewa haba sabreen pls ki dena kukannan, sabreen cikin miryan kuka tace munna kibarni inyi kuka kefa wanda kike so zaki aura shiyasa bazaki gane me nakejiba, munna tace sabreen toki fito fili ki gayawa kamal d'in mana, sabreen tace munna da zan iya da tuni nayi hakan, amma bazan iyabane Munna zatayi magana kenan wayan sabreen ya fara k'ara, minna ce ta d'auka don ganin suhail ne yake kiranta, hello suhail munna ce, suhail yana jiyo sautin kukan sabreen yace munna sabreen d'in fa? Munna tace wlh gatanan tanata kuka babu irin rarrashin daban mataba amma taki tayi shiru, suhail yace bata wayan pls, munna tasa mata a kunne suhail cikin sanyin murya yake magana, sabreen dan Allah ki dena kuka bawai dan nadena sonki bane yasa na fad'a hakan kawai dai naga babu yanda zamuyine shiyasa na fad'a miki hakan dan abin ya fita a ranki kafin bikin kin saba, amma ki sani har abada "KINA RAINA" babu abinda zai canja ta b'angarena domin ina miki k'aunar da banayiwa kaina sabreen I LUV U pls kidena kukannan don har cikin raina nake jinshi. Sabreen ta tsagaita kukanta tace I LUV U TOO YAH SUHAIL, I LUV U SOO MUCH, suhail ya share kwallan fiskarsa yace "ok then stop craying pls SABSU" ya manna mata kiss har cikin kunnenta taji, shuru tayi tana share hawayenta seta kira sunanshi a hankali SUHAIL, yace "yes" SWEET HEART, idanunta ta rufe taji dad'i sosai dajin sunan daya kirata dashi tace pls yah suhail karkayi aure dan Allah, yace bazanyiba "SWEET HEART" nayi miki alk'awarin bazanyi aureba harse lokacin da kikace min kin fara "SON" kamal, dad'i taji sosai tace "thankyou" yace wlcum "SABSU" tokiyi bacci pls karki sakeyin kuka kinji? Naji kuma nagode byee, yace ok byee. Munira da tuntuni take kallonta cike da mamaki, sabreen ta murgud'awa munna baki sannan ta kashe wutan d'akin taja bargo tarufu. Munna tace hmmm sabon salo, tomudai namu ido .
           Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
      By Mmn Shureim
             (Sad-Nas)
69-70 Washegari da safe munira da sabreen suna karyawa se munira take cewa jiya kince Allah ya tabbatarwa hafsat da suhail alkhairi, sannan kuma naji kina cewa karyayi aure mekike nufu kenan? Sabreen tace ina ruwanki, dama ashe kunnenki nagunmu, munna tayi dariya tace mude namu eye.
Lokaci se tfy yakeyi kamal da mummynsa da kuma mijin mummynshi wanda suke kira da "UNCLE D" suna ta shirye shiryen zuwa biki, tare da abokansu na pakistan d'in. Gidan kamal da yake nigeri an sake gyarashi an canja komai na gidan d'akin sane kawai ba'a canjaba, dan bai dad'e da canjashiba, guri yayi kyau sosai abin se wanda ya gani. Mum kuwa tana ta shirye shiryen zuwan su mummyn kamal, hafsat kuwa tana can gurin su sabreen suna nasu shirin harda salma. Munira dad'i sosai taji wai yau gata ga aljana suna ta shirye shiryensu cikin kwanciyan hankali, itama sabreen ta sake jikinta anata mata gyara sosai. Su kakama dukda dai kamal tace baya bukatan suyi komai amma sunyi mata garan abinci sosai da kuma kayan sawa masu tsada. Gidansu Abbakar d'in munirama shiri sosai sukeyi abindai seni (SAD-NAS) danake d'auko muku rahoton
Shi kuwa suhail yana can yana gudanar da nashi shirye shiryen dan ganin bikin AMININSA da kuma SABSU d'inshi yayi kyau, dan shi kansa baisan adadin kud'in dayake kashewaba. Yau laraba ne su kamal suka shigo nigeria inda suhail da sauran friends nasu na nigeria sukaje d'aukosu. Hotel mai kyau suka sauk'esu da kuma UNCLE D, ita kuwa mummyn kamal tana gidansu suhail agun k'awarta mum. Bayan sunci abinci sun watsa ruwane se kamal yace to nidai zanje inga amaryata dan nayi missing d'inta, dukkansu suka kama hanya su 8 se k'auyen su sabreen.
Kwaliya sukayi sosai amma ita sabreen light make-up hafsat tayi mata sunyi kyau sosai suka fito. Kamal dad'i yaji sosai kamar yaje ya rungumota, shi kuwa gogan naku SABSU murmushi kawai yakeyi a fili kome yakeji a zuciyarsa kuma oho. K'arasowa sukayi tare da sallama, angwaye suka amsa sallamar sannan su gaggaisa sabreen tana jin kunya. D'aya daga cikin angwaye se kallon salma yakeyi, ita kuwa matsowa tayi kusada suhail tace nasan dai kaine suhail koh? Suhail yace eh nine, tace hafsat ta damemi da suhail tin d'azu to Allah ya sanya alkhairi, suhail yayi murmushi yace ameen. Salma tacewa kamal to ango nidai zan tafi amma dai zan dawo, kamal yace to mingode bari a saukeki, salma tace a'a wlh ana jirana a bakin titi, suhail yace dukda haka dai zamu kaiki bakin hanyan to kodon addu'an da kika mana, hafsat tace to shikenan sannan tacewa su sabreen sena juyo, suma hannun suka d'aga mata sannan suhail tace SADIQ shiga muje, salma ta shiga baya suka tafi suna d'agawa junhannu. Tun kafin su k'arasa suka hango wata farin PRADO tana tsaye a gefen titi. Bayan sun k'arasone se wani kyakkyawan saurayi fari tas dashi wane balarabe ya fito ya k'araso gunsu tareda yimusu sallama ya mik'awa suhail hannunsa mai sanyi kuma mai laushi suka gaisa yana mishi murmushi, sannan suka gaisa da sadiq. Salma ta Matso kusa dashi ta gabatar mishi da suhail da kuma SADIQ sannan suka tafi, su suhail ma suka tafi suna yaba saurayin.
       Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
      By Mmn Shureim
             (Sad-Nas)
71-72 Kamal dai se kallon sabreen yakeyi ya kasa ce mata komai, hafsat ce tace yah kamal yadai ai kallon yayi yawa, se'a lokacinne yace to ai na kasa d'aga idona daga kantane. Munira tace to bari mi baku guri zamu tattauna da abokan ango, kamal yace wifeynah zonan mana, gefensa ta koma ta tsaya abokinshi mai suna ALIYU yace wifey tun daga yau? Kamal yace kun samin ido fa wifey zomu zauna a mota. Motan ua bud'e mata ta shiga sannan ya rufe shima yaje ya shiga, sukuwa sunata hira abinsu. Sabreen tace sannu da dawowa uah kamal, yawwa "wifeynah" yanaga kin ramene, sabreen tace hidima mana, yace kodai kina missing nane? Mirmushi tayi tace eh harda shid'inma, dad'i yaji yace kinyi kyau fa sosai, nagode tace dashi ina mummy? Mummy tana gun mum, gobe zasu kawo kayanki, murmushi kawai batace komaiba, yace kaka fa? Tace baiyi nisaba yanzu zai dawo, ok bari yazo mu gaisa semu muce wlh agajiue nake, kallonsa tayi tace sannu, tabbas sabreen tayi missing d'in kamal sosai. Kamal yace gaskya suhail yayi k'okari sosai wlh Allah dai ya biyasa da gidan aljanna, sabreen tace ameen yah kamal zan shiga gida, meyasa kodai rowan fiskannaki kike min? A'a dai ni kawai inaso in komane☺, kallonta yakeyi cike daso yace to muje, tare suka bud'e motan suka fito daidai lokacin su suhail suka iso, tare da kaka da baban munira dan sun had'u a hanyane se suka d'aukosu. Su sabreen gida suka wuce sannan kaka ya iso dasu ciki suka gaisa aka kawo musu abinci sunci kad'an sannan sukayi sallama suka fito. Su hafsat suka fito musu da peppe chikeen da dambun kuskus wai nasu da kuma nasu mummy. Dad'i sosai kamal yaji dan dama ta tambayeshi me mummy tafi so yace mata kuskus. Sabreen ta fito tayi musu godiya da Allah kiyaye sannan suka tafi.
Washe gari ran alhamis shine ranan walima, da sassafe suhail ya kawo mata Mayan da zatasa a biki wanda shiya saya da kudinsa. Itada hafsat suka fito yaso yayi magana da sabreen ita kad'ai amma hakan baiyuba, godiya tayi sannan yace su mum zasuzo kawo kaya yanzu, dan haka nina tafi semunzo d'aukanku walima kodai akwai wani abune? Hafsat tace eh muna buk'atan d'an kud'kad'an. Dad'i suhail yaji yace jeki dash bord ki d'auko min kud'i, bayan hafsat ta tafine suhail yace SABSU nah ya kike, sabreen tace ina cikin damuwa yah suhail, suhail yace ki kwantar da hankalinki pls "KINA RAINA" har abada SABSU, sabreen zatayi magana kenan Sega hafsat, kud'in ya karb'a yace nawa kuke buk'ata? Hafsat tace 30k ma yayi, 50k suhail yabasu yace toni na tafi su kamal suna jirana, to mungode sannan ya tafi yana sauri. Bayan azahar aka kawo kaya abindai seni danagani, hidima sosai aka musu sabreen taje ta gaishesu ita dasu munira, MUMMYN kamal har cikin ranta take son sabreen dan tsaraban tama na pakistan dabanne ga kuma lodin kayan aure da suka mata. Awansu d'aya suhail da wasu abokansu suka maidasu gida sunata murna sosai a ransu suna yaba tarbiyansu sabreen.
         Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
    By Mmn Shureim
           (Sad-Nas
KUYI HAKURI FANS, PHONE NANE YAD'AN SAMU MATSALA YANA HUKING SHIYASA BANA MUKU DOGON TYPING
73-74 Da yamma amare sukayi shirin walima sunyi kyau sosai tunba sabreen dama kyakkyawace sosai bazan b'ata lokaci wajen baiyana muku kyawuntaba zaku ganta a hoto. 4:00pm angwaye sukazo d'aukansu kauye a cike da motoci se kallo jama'a sukeyi, dayake auren biyu ne. Gurin da za'ayi walimanma kawai abin kallo ne, MALAM ABDULLAHI BALALAU aka gayyata yazo, nasiha sosai yayiwa sabreen da kuma munira da al'umma baki d'aya, sannan akaci aka sha akayi ta hotuna amma sam salma bata shiga cikin hotonba. 5:40pm aka tashi sannan aka maida kowa gida, angwayene agun amare suhail yacewa salma ina angon naki baizoba kodai baki gaiyyaceshi bane? Salma tayi murmushi tace na baua son hayaniya shiyasa bazai zoba haka yakeshi, suhail yace ikon Allah to gaskya dai ya daire yazo mana dinner, salma tace sedai in aurenka ya tashi se in gaya mishi da wuri, suhail yace kina nifin dinner'n ma bazai zoba kenan? Salma tace eh amma iyayena zasuzo, suhail zaiyi magana kenan tace pls ya isa sanna ya wuce gida yanata binta da kallo樂, sabreen tace kayi hakuri yah suhail haka take bata fiye son ayita sata maganaba se dai idan ita taso, kuma itama bata son hayaniya sosai shiyasa kaga bata shiga harkan mutane hakanma dan kaine SAB... ko sabreen bata karasaba shi suhail ya fahimceta, kamal yazo gunsu yace wai surutun me kaketasa wifey nane, suhail yace sorry ango muje kar dare ya mana, kamal yace ok wifey sekin jini, murmushi tayi tace to Allah ya kiyaye hanya sukace ameen sannan suka shiga mota suka tafi.
Washe gari jumma'a tun safe sabreen taketa kuka, tunanin hakanne yasa salam tazo da wuri dan bata kwana dama. Hakuri taketa baiwa sabreen amma ina kuka kawai takeyi, hankalin salma ya tashi dan tasan sabreen iyayenta kawai ta tuno yasata kuka. Seda sabreen tayi kuka sosai sannan tayi shuru.
Bayan an dawo daga masallacine akazo kofangidansu munna aka d'aura SABREEN DA KAMAL da kuma MUNIRA DA ABBAKAR akan sadaki dubu d'ari (100k). Hawayen zuci SUHAIL yakeyi sosai, su kuwa angwayen dad'i sukeji tare dayin ALHAMDULILLAH. Kowanne ya kira matarsa a waya yana gaya mata abinda ke ranshi.
Da dare akazo aka d'auki amare sunata kuka basaso su rabu, duk dai cikin birnin aka kaisu gidajensu had'ad'd'une sosai. Kawayene kawai suka kwana da amare yaukam salma ta kwana agun sabreen dan irin kukan da sabreen takeyi. Bayan an maida jama'a gidajensu angwaye sukayiwa amaren sayayyan abun tab'awa. Tunda suke dawowa a hanya kamal ya lura da suhail kamar baya jin dad'in jikinsa, kamal yace abokina yadai? Suhail yace wlh jiri nakeji, kamal yace to tsaya bari karb'eka, suhail yace bakomai ai mun kusa, yana karasa maganar seya fara salati yana k'okarin tsaida mota dan baya ganin komai se duhu. Kafin kamal ya taimaka mishi harsun gwaru da wata mota ji kake chasss. Da sauri friends nasu da suke biye dasu a baya suka tsaya tare da fitowa a gigice suna salati suka k'araso gun motan, daga suhail har kamal babu wanda yake motsi a cikinsu
       Sad-Nas
[10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: TANARAINA
     By Mmn Shureim
            (Sad-Nas)
75-76 Cirosu akayi daga cikin motan dan motocin kam gabad'aya sun tashi a aiki, amma dai su suhil d'in basuji wani ciwo sosaiba. Hospital aka kaisu dukkansu harda 'yan d'ayan motan suma su biyune maza duk dai aka karb'esu da wuri, duk cikinsu suhail yafi jin ciwo. Doctors sun tabatar da cewa babi wata matsa zuwa gobe zasu iya tfy, amma badan suhail danshi har yanzu bai farfad'o ba. Duk wanda abin ya shafa an sanar da iyayensu, cikin d'an k'ank'anin lokaci hospital ya cika, su mum se salati sukeyi da innalillahi wa inna ilaihir raji'un!
  Bayan kamal ya bud'e idone seya tuna da abinda ya faru nan hankalinsa ya tashi da sauri ya tashi yana kira sunan SUHAIL, su mum da mummynsa ya gani akansa yace mum ina abokina a wani hali yake mummy? Mum tace kamal ka kwantar da hankalinka suhail yana halin lfy kamar dai yadda kake yana can d'aya d'akin, se yanzu ne hankalinshi ya kwanta, mummyn kamal tace sannu Allah ya tsare Allah ya baku lfy, sukace ameen, sannan tace toni bari inje gun suhail tunda mum tana nan.
Su amare kuka suna can anata ganin gida, salma ta zauna ta kafa tagumi, sabreen tace salma lfy, naga tun d'azu kinyi shurune, salma tace sabreen ki sairari abinda zan gayamiki banaso ki tada hankalinki, sabreen tace ina jinki, salma tace su suhail sun d'an had'u da tsautsayi a hanya amma suna cikin k'oshin lfy yanzu haka suna asibiti. Sabreen tace me kikace salma? Salma ta rikota tace wlh babu abinda ya samesu pls karki d'aga hankalinki barima mu kirasu kiji, nan salma ta d'auki wayan sabreen ta kira number kamal, lokacin wayan yana hannun ALIYU abokinsa, mik'awa kamal yayi yace sabreen ce take kira, mum tace an sanar dasune? Aliyu yace a'a basu saniba, kamal ya karb'i wayan yace hello sabreen, dama a handsfree salma tasa, cikin muryan kuka sabreen tace hello yah kamal ya jikin naku? Ajiyar zuciya ya sauke yace alhamdulillah ki dena kuka pls lfyanmu k'alau, yah kamal inaso inzo in ganku idan bahakaba hankalina bazai kwantaba ina yah suhail? Suhail yana nan lfy karki damu kiyi hakuri zamu dawo kinji? No ya kamal pls kasa azo a d'aukemu plss, to shikenan ga ALIYU zaizo yanzu kidena kuka pls, to yah kamal Allah ya baku lfy Allah ya kare gaba, ameen mungode. Hafsat da take tsaye akansu sabreen kuka mai karfi ta fashe dashi, salmace tayita rarrashinsu har ALIYU yazo, himar dogo har k'asa salma ta d'aukowa sabreen tasa sannan suka ja k'ofan suka fito akabar mai gadi.
Bayan sun isone hafsat tace ina d'akin ya suhail, ALIYU ya nuna musu suka shiga dukkansu mummy ce a zaune su SADIQ kuma suna tsaye, su hafsat suka k'arasa tanata kuka tana cewa yah suhail pls ka bud'e idonka sannan tace mummy ya naga bai farkabane? Mummy tace kiyi hakuri hafsat lfyanshi k'alau kawai dai yayi dogon sumane sakamakon jininsa daya hau, hafsat tace yah suhail pls ka bud'e idanunka. Sabreen tagaida mummy ita da salma sukace ya masu jikin, mummy tace jiki da sauki sukace Allah ya basu lfy, akace ameen. Aliyu yace to muje ku duba kamal, tare suka fita harda hafsat sukaje gun kamal.
Bayan sun gaisa da mum ne setace bari inje gunsu suhail. Bayan mum ta fitane kamal yace salma ga kujera zauna, sabreen keda hafsat kuzoku zauna anan, wato a kan gadon dayake. Salma ta zauna a kujeran sannan sukuma suka zauna ata gefenshi. Su ALIYU sukace bari mu duba sauran mutanen can, kamal yace ok kugaishesu sannan suka fita dukkansu.
Bayan fitansu salma da hafsat suka gaishe da kamal se hafsat tace salma muje ko yah suhail ya farfad'o, salma ta mik'e tace sabreen ina dawowa, sabreen tace to, sannan suka fita akabar MATA DA MIJI.

0 comments:

Post a Comment