BAYAN WUYA SAI……
NA
RAMLERT y salis
KAINUWA WRITERS ASSOCIATION 🤝
DA SUNAN ALLAH ……...YA ALLAH MUNA ROKONKA ABINDA ANNABI S A W YAROKRKA,MUNA NEMAN TSARINKA DAGA ABINDA ANNABI S A W YANEMI TSARINKA DA SHI.
Wannan page mallakane gareki khadija nanancy my bloody
page 34
Kuka takeyi sosai ranta namata kuna,tace ummi karkina fadin zaki tafi kibarni inazanje ummi ?wanake dashi inbakeba takarasa maganar tana share hawayen fuskarta .
Allah yana tare dake afifah tabbas BAYAN WUYA SAI DADI,dan hk koda na mutu Allah ne zai baki mafita.
Abin dana iya tunawa arayuwata kafin na hadu da wannan mantuwar shine:
Mahaifina babban dan kasuwa ne mutum ne mai tarin dukiya,yana kasuwancinsa da gaskiya da rikon amana wannan shiyasa kullum kasuwancinsa yake kara habaka,afifah Nakasa tuna koda sunan mutum daya a gidanmu sai dai dukkan su ina ganinsu a idona,Babana yana odar kaya daga kashashen waje abinda yashafi kayan mata,jakunkuna da takalma kayan mata dai sosai atampopi har da yadukan,maxa da takalma turaruka,agogo,sarkoki har dana kwal,afifah duk wani,nau'in material zaki sameshi a manya manyan shagunan babana,dukiyar da mahaifina yake da ita tafi karfin in iya lissafawa.
mahaifina su 5ne awajen iyayensu,babana shine babba sai kannansa maza3sai kanwarsa,su hudu
Maza sai autarsu mace,
babansu ma'aikacin gwanatine kakana kenan ammah na mance wane aiki yakeyi,mutumne mai rufin asiri wacce ta haifi babana ita ma'aikaciyar gwanatice.
lokacin da mahaifina ya gama karatu alokacin yafara kasuwancin,dan dama shi yakaranta .
babana yatabayin aure kafin mahaiyata,matar ta mutu a hanyarta tazuwa kasarsu dama acan suka hadu,ta haifi danta namiji,afifah banso,na mance sunan babban yayana ba wanda muka hada uba dashi domin duk cikin yayyena wanda muke uwa daya bawan
Da yanunamin so irin sa.
babana yayi aure na2bayan mutuwar daya matar data rasu,mahaifiyata ya aura.
ammah kinsan me afifah ?family meeting sukayi akan wata rigima da'akayi,dangin,matar da mahaifina ya aura wacce ta mutu danginta sun dage sai anbasu dan data haifa,shikuma babana ya dage bazai dau dansa ya kai har wata kasaba,ammah yayimusu alkhairi duk sanda kasuwancinsa yakawoshi zaizo musu dashi,ammah kiki yarda ba yadda ba'ayi da mahaifina ba ammah shima fir yaki basu.To dasukayi taron family Kakarmu tace "daga rana irin ta yau andena auren bare a zuri'arsu"wasu daga cikinsu basu yardaba ammah ta kafe bayanda suka iya da ita,domin ko cinkin yan uwanta itace babba wacce ta haifi mahaifina kenan,kuma iyayensu sun mutu ita ta zama uwa ga kanenta.ita da mijin tama yan uwane kakaninmu kenan,kuma yawanci family auren zumunci sukayi tun kafin tasa dokar.
Da mahaifina da mahaifiyata yayan wa da kanine,me bin mahaifina shine ya auri kanwar mahaifiyata hama sauran kanensa duk auren gida suka yi.mu 7 ne agurin mahaifimu yayyena 5 maza,sai ni da kaninah,babban yayanmu yan'uwansa sun matsa dole babanmu ya hakura ya bar musushi,munyi shakuwa sosai dashi saboda nikadaice mace cikinsu,lokacin da zai tafi nakusa gama primary,kuka sosai nayi dan ganin zai koma can da zama sai da'akamin wayo mukaje tare nayi kwana uku sannan nadawo akan cewa da anyi,hutu zan koma nibasan wayo akamin ba.Lokaci na tafiya komai nacanxa wa,dukiyar mahaifina sai ha6aka takeyi,kullum gidanmu cike yake da jama'a
Yake musamman ranar juma'a,bawanda zaizo acemasa babu.
Gata tako ina nake samu baga yayyenaba kadai,har iyayena da kakaninna da sauran yan uwa,hakan yasamo asaline sbd iyayena nikadaice yarsu mace,yayunama nikadaice kanwarsu mace musamman babban yayana duk da ba zaune yake akasarba ammah ina samun kulawarsa,ko da yaushe muna hira awaya,duk abinda ya shigo nayayi sai ya siya ya aikomin.
dan har kakarsa cewa tayi wai suna son abarmusuni,ammah hakan ba mai yiwuwa bane nikuma lokacin sbd Yaranta banki na tsallake dukkan yan'uwana nakoma gurin yayanaba na barmusu kasar.
yanda kikaganki hk afifah tonima lokacin danake budurwa dukkan kamaninmu daya dake,sai dai kyawuna yafi naki bayyana sbd irin hutu da kulawar danake samu,afifah ko yar shugaban kasa baxata nunamin hutu ko wani abun more rayuwa ba.
babban yayana farine sol kamarni,domin mamarshi balarabiyyace,duk inda mukaje tare sai azata shine kawai muke uwa daya uba daya dashi,kasancewar mufararene sukuma sauran duk babanmu Sukayo,shikuma babanmu bazakace masa fari sol ba ammah fatine,
family dinmu fulani ne afifah da farare sol dawanda farinsu bai fito sosai ba,da mahaifiyata nake kama.
yayyen mahaifina kowa soyake yaga yafaran amin,komai sukasamu ni,hakan yasamo asaline sbd ko wanw yaro a family babanake daukar nauyin karatunsa ko wace kasa yake son xuwa, mazan su da matansu,hk kuma duk yarinyar daza'a aurar da ita to duk kudin da mahaifinta kedashi babana baya barinsa yamata komai,shine yakeyi.
Yana taimakon "yan'uwansa sosai wasu yana sasu abakin,kasuwancinsa wasu kuma yana,nema musu aikin gwanati.
kasancewata yarsa macr tal,yasa kowa keson farantamin dan sunsan yadda yake sona.
hk muka cigaba da rayuwa cikin farinciki da yan'uwa da iyayena da babban yayana dabaya kasar,
a family mu ba'a barin mace tayi wani karatu mai zurfi akeyimata aure,wata iya secondary,wata kuma sai tafata jami'a,da miji yaxo inhar kingama secondary za'a aurar dake,ammah sai dai inshima dan'uwane wani
Lokacin ma hadaki da wani za'ayi inhar yayimiki kema kinyimasa to sai amuku aure,ammah ba'a taba yimuku dole inbakwason juna,wasu da kansu zasu kulla soyayyah ba'asanibama har sai in lokacin auren yayi su fada.
afifah family dinmu abun,burgewane,akwai akwai ma'aikata daban daban ,yan kasuwa ,malamai,dasauransu ,
Kuma sau daya a shekara ake bikin aure a family din,sai kiga an hada mutum goma ko kasa da haka,muna da yawa a family din.
Ashekarar daza'ayiwa yayuna aure akayi wani taro a family
"cewa zamu,gina family HAUSE wanda kowa zai koma ciki da zama"a lokacin nayi matukar farinciki ammah sai nake ganin kamar baxsi yiwuba sbd muna dayawa.
Wanibabban fili na gwanati babana yasiya duk da haka sai daya kara da siyan wasu filaye da gine ginan dake kusa da filin,sannan yasamu babban fili sosai.
Gudummawa kowa yafara kawowa dame karamin karfi dame babban karfi,ammah sai babana yace "shi bazai karbi kudin kowaba,zai gina gidan kuma baxai banbanta ba .
Mahaifiyarsace ta hana shi Kakata kenan,cewa "yakar6i gudummawa ga duk wanda yakawo saboda ya rage wani abun"sannan ya karba.
komai dakikasani daga waje akayoodarsa wanda za'ayi aikin gidan, daga kofofi,winduna,get,kayan bandaki,fankoki,Ac,duk dai wani abun da'ake bukata a aikin gida wanda za'asa da wanda za'asa in an gama.
Dan ban manta ba company da' akasiya agurinsu sune suka dau nauyin kawo kayan kasarnan dan kayan dayawa sosai.
Damukaje ganin gidan lokacin da'aka gama ginawa,nayi mamaki sosai afifah wane irin
Kudine hk da babana duk danasan kowa yabada nasa taimakon ammah yakashe kudi sosai,part part ne agidan kowane part da,number dinsa,kowane part akwai decoration na flower a gabansa da bayansa.
kasan gidan kuma kwaltane kwance,kofar kowane part akwai wajen ajiye motoci,akwai wani katon lambu agidan sai wajen wasan yara da wajen kiwo dan dama babana yana kiwo sosai.
Gidan yayi kyau sosai ankashe kudi ba kadan ba,
Alokacin daza'ayi bikin ina JSS one murnayi sosai domin yayuna zasuyi aure,babbanYayana shine kawai bazai zauna agidan ba ammah yar kanin babanmu zai aura,sai dai yatafi da ita duk sanda zasuzo suna da part dinsu dazasu zauna ciki,sbd yan'uwan,mahaifiyarsa baxasu yarda ya dawo gurin muba sunce"mahaifiyarsa ita dayace 'yarsu to shima shi dayane jikansu"hk abun yake dama ga wasu kasashen daga da daya sai biyu insunyi yawa uku.
Agidan mu akwai mutum 4 maza wanda za'a aurar,ni da kaninane muka rage,Gidan kanin babanmu akwai mutun 3 mata 2 namiji daya,daya kanin babanmu mutum 4 shima mata uku namiji daya,sai kanwar babanmu ita kuma 'yarta mace daya.
MATA 6 MAZA 6 haka akafara hidimar biki ta kowane 6angare,
Anfara biki cikin farinciki da annushuwa,ana gobe za'a bude family hause yayana sukazo da yan'uwansa akan cewa bayan angama biki zasu koma can suma suyi nasu bayan an kai musu amarya da yan kai amarya.
Hakama kanwar babanmu itama taxo da 'yarta wacce itace zata auri yayana wan Da nake bi,itakuma sai sai iyayenta sukoma babu ita domin mune,dangin miji.
Ranar da'aka bude family hause kowa yayi farinciki mara misaltuwa,dan kowa ka gani aranar cikin farinciki yake,an bawa kowa key din,part dinsa har da angwaye,dangin su yayana dasukazo bikin suke ta mamaki "wai wannan family dayane sukan abun ya burge su,ganin har da jikinsu shima yana da nashi part din "
Babana ne yayi wani jawabi kafin taron yatashi cewa "kowa yasa aransa agidansa yake zaune shi ba aro yabasuba Kyautane har abada" Itama kakata cewa tayi "ko bayan ranta bata yarda danta ko dan kannenta ba ko jikokinta su fita daga gidan da nufin canxa gurin zama ammah 'yayan jikokinta suna da zabi insuna son zama gidan inma basa so duk zasu iya domin wata rana yawan zai iya yin yawa "Afifah nida mahaifinkine muka fara karya wannan dokar,danmu kasar muka bari ba gidan ba.
sai datayi kuka mai isarta daga ita har afifah bamai rarrashin wani,sannan tacigaba da cewa "haka aka gama bikin kowa na murna
Bayan bikin wasu daga cikin yan'uwa wanda sukariga sukayi aure ba'auren gidaba sune suka koma gidajensu da wanda ba yan garinba da wanda ba 'yan kasarba.
Acigaba da rayuwa a family hause cikin zumunci,kullum ina part din amare musamman wacce ta auri yayana wanda nake bi,saura sati biyu hutun makaranta yakare BABANA yamin biza zuwa can inda babban yayana yake domin dama ba'aje dani bikin su nacan ba.
Nakarasa hutuna acan badan son raina na dawoba.
Akwana atashi na kammala karatuna na
Secondary,alokacin abubuwa da dama sun faru a family hause wasu sun mutu wasu sun haihu,babana shekarar tazo masada farinciki har da mahaifiyata domin sun samu jikoki har 5,baban yayana matarsa ta haihu 'yan biyu mace da namiji sauran yayuna kuma duk maza suka haifa.
alokacin samari sunmin cahh dana family dana waje wanda ba yan'uwaba ,sanin dokar family yasa bana bata lokacin kuka su.
Afifah in kina son ganin 'yargata ta karshe alokacin inkika sameni kin samu,bani dawata matsala arayuwata Babana ya tsayemin komai kaf family ba yarinyar dazata nunamin kyau,ko kudi,ko hawa mota me tsada.
motor na uku ne daya tazuwa school akwai wanda shine yake driving dina hk shine yake daukoni,daya ta yawonace nida kaina nake driving kaina,daya kuma itace nake kwasar yara ranar daba school nariga yawo dasu zuwa gidan wasanni,duk da muna da wajen wasan yara agida.
Afifah ina da yan aiki su uku suma,mekula da dakina da toilet dayimin wanki,dame girkina da kula da lokacin cin abincina domin
Ina da wasa da cin abinci,dame kula da laphia ta duk inda zani tana tare dami,ko makaranta ko unguwa saboda tasab inda zani,da namiji ne yake kula sa shige da fice na ammah babana yace baiyarda da alakata da namiji ba.
Mahaifina mutun ne mai addini sosai,mahaifiyata tana sa kirki sosai.
Koyaushe part dinmu baya rabuwa da matan manya,saboda tana kawomusu gwalagwalai,jakunkuna irin na manyan mata masu tsada da takalma,sarkane,har agogon gwal.
Matan gwana wani lokacin sukanzo har gidan Musamman intayi sabuwar oda,bata kai kayanta wani guri duk matsayin ka sai dai kazo gida kasiya ko ka aiko,inkuna dawata alakane sosai zatasa akaimaka,dan akwai sanda rasa driver na yakaiwa,matar gwana wata sarka da agogon gwal to kasancewar suna da kudi sosai yasa tace muje tare,hk mukaje tare zuwana gidan gwanati na farko afifah falon gidan yayi kyau sosai ammah babu wani abu dazai nunawa namu falon,anan muka,hadu da danta har mukayi musayan number ammah abun bai yiwuba domin da gwamna ya Tuntu6i babana dazancen babana bai boyemasa komai na dokar family muba.
Ina aji 2 a jami'a babanki ya dawo daga karatu muka dara soyayyah sosai,
wacce sai yanxu nake dana sanin yinta,munsaku a matsala munsa iyayen mu a damuwa munsa kammu anadama,munyanke farinciki kowa munyi sanadiyyar maidaku marayu munguji iyayenmu mun nuna musu munfison yayanmu akansu.
kaicona !afifah kiyafeni tabbas inkikaji karshen labarin zali tsaneni,du da gata da iyayena suka nunamin nagujesu saboda miji kuma
Saboda yarana,
mezancewa ubangiji na inna mutu bannemi gafarar iyayena da sauran yaranaba?munyi babban kuskure mun bijire maganar iyayen mu saboda son zuciyarmu akarshe munyi niyar dawowa garesu ammah Allah ya saukar mana da jarrabawa wacce tayi sanadiyyar mutuwar babban yarona dakuma ...daku...ma .. Sai ta kasa karasawa kuka kawai takeyi. Itakuma afifah tama kasa zubda hawaye a fuskarta saboda wani tunani datakeyi "wai shin ummi da babana mesukayiwa mahaifansu datake ikiratin zantsaneta inaji"?
ummi ki karasamin dan Allah waye kuma ya mutu bayan yayana?afifah ta fada tana durkusa gwuiwarta a kasa.
NIMA TAMBAYAR DAZANYIWA UMMI KENAN KUMA ME SUKAYIWA,IYAYEN SU HK?MEYE DALILIN GUJEWA IYAYENNASU?MEYESA BATA KOMA MUSUBA TO YANXU TAKE RYW CIKIN WHL BAYAN YAR GATACE GABA DA BAYA ?
MUJE ZUWA y salis (Ramlert )✍🏻
0 comments:
Post a Comment