Monday, 27 November 2017

'Ya'Ya Da Kudi Page 36-40 (THE END) LATEST HAUSA NOVEL- ISMAIL SANI


YA'YA DA KUDI Page 36-40 (THE END) 
Shirye-shirye biki akeyi ba sanya, su Hajiya Jamila.k’irjin biki, su Farhat da Queen Neena takanas suka koma gidan Hajiya Suwaiba da zama, abunda aka shirya za’ayi ran Alhamis kamu, sai Jumma’a Walima da daddare kuma dinner, washe gari asabar yini. Komai ya tsaru yanda ake so, yau ne ranar da za’a fara Kamu, da yamma ko kwaye sun shirya, har an kaisu gun jiran isowar Amarya ake, ba’a dade ba kuwa ta iso cikin wata lafiyayiyar mota, tun dana zuba ido ma Khadi kasa d’aukewa nayi, gaskiya tayi kyau, duk yan guri sai yaba kyanta suke, taro yayi taro, komai yatafi yanda akeso, sai kusan shida suka gama kamu, daga gun gidan, Hajiya Suwaiba aka sake kaita. Washe gari akayi walima shima tsaru daddare kuwa sukayi shirin dinner. Hajiya Suwaiba ta bada umurni akai Amarya gidansu daga can za’a wuce da ita Dinner har a kaita gidanta, wannan umurnin Mum ne. Masu karatu in bakwayi bamu guri, tundaga nesa na hango motoci jere suna d’eban mutane, sai da aka gama diban kowa, na hango wata maroon d’in lemo zeen ta perker, su Gwaggo da’ake leke, baki tasaki tana kalo, don tunda take bata tab’a, ganin irin motarba. Nan akace afito da Amarya Inna Yalwa ce ta rakota, ohoho sunan wani kalma waishi sorry!! Masu karatu karkuga Khadi, in har nace zan iya tsara muku kyan da tayi, wayana ba zai d’auka ba. A hankali suka isa jikin motar tashiga, ana tayar da motan taji an rik’o hannuta, a razane ta juya Umar ne yaaha kyau.
.
Koda suka isa gun dinner duk wanda ya gansu sai ya yaba, haka taro ya kare kowa cike da murna. Da safe Malam ya kira Khadi, ya mata nasiha, yan’uwan Mamanta suma nasiha suka mata, Gwaggo da k’afarta tazo tana kuka ta roki Khadi yafiya, Khadi tace” ba komai ta yafe mata. Da daddare aka d’au Amarya sai gidan Umar niko Rash nace”fatan alkairi. Gwamna gida mai ji da kyau ya bamasu Malam, yace”karsu d’au tsinke acikin nasu. Haka ayi suka koma, tsakani Beeba da Dr Abdul ko wata soyayya ne mai cike, da qauna sukeyi ma junasu, Gwaggo yanzu kamar bata gidan don Albarkacin Khadi takeci. Kwanaki sun tafi shekaru sun sud’e, koda naje gidan Khadi na hango ta da yaranta, sun girma suna gudu ko ina, Khadi yanzu ta dawo cikakoyar mace mai aji da kamala. Gwamna ya biya ma su Gwaggo da Malam aiki Hajji suka tafi.   Bayan sun dawo, su Gwaggo an dawo Hajiya, Gwaggo ne ta fito daga unguwa ta kame abayan mota, dai-dai kwanar unguwansu, ta hango an taru, wata mata sai dukan wata yarinya take, da sauri tasa mai driver ya tsaya, wani ta tambaya maike faruwa nan yasanar mata, yarinyar da ake duka yar riko ce, wai taje tala ta b’atar da naira hamsin ake dukanta. 
.
Da sauri taje ta rike matar na, tace”haba baiwar allah mai yayi zafi haka?. “Akan kd’in da baitaka kara ya karya ba?” Ko dan kinga bake kika haifetaba? “Kisani fa ‘YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU. nasiha ta mata sosai kafin ta ba ma matar 500 ta kuma ce karta daki yarinyan ta tafi. Bayan kwana biyi Gwaggo na zaune a gida, taji jiniya kafin ta mike saiga Khadi tashi da yan ‘YA’YAN TA, da gudu sukayi gun Gwaggo duna oyoyo grany, Gwaggo tace”washh yaran nan zaki karya ni, takali, Ahmad tace”ni yanzu na fasa Auren da kai ka tsufa, Hafsat”ke kuma kinyi kwaliya kinzo ki kwace min miji. “To baya sonki” Dariya sukayi gaba d’ayansu, rayuwa kenan hausawa sunyi gaskiya da kalmasu ta Mahak’urci mawadaci. Kira gareku yan’uwa mata, kunga yanda labarin nan ya kasance akan Gwaggo, kusani ‘YA’YA ko bana ka bane, kurikesu tsakani da Allah, bakasan mai tai makonka ba, bakusan wazakuci albarkacinsuba. Allah ya bamu YA’Ya na gari Ameen.
.
ALHAMDULILAH  Alhamdulilah! Dukkan yabo sun tabbata ga Allah ubangijin sammai da kassai, wanda ya bani ikon kammala wannan littafi lafiya, kuskuren danayi ya Allah ka yafe min Ameen.  - ISMAIL SANI
   
. Copied By
ISMAIL SANI 

. CALL or SMS     
  +2348038655307
.
   WHATSAPP NO:    
   +2348038655307

0 comments:

Post a Comment