'YAR JAMI'A 003 .
A B'angaren beauty kuwa sam daren ranar bacci k'aurace mata yayi don kwance take hannunta naga phone nata ta k'urawa agogon wayanta ido"tqna jiran lokaci kamar yadda ta tsara" diqq...diqq...diqq...bugun alarm kenan da yayi na nuni da 12:00a.m cikin wani matsanancin farin ciki beauty ta kai hannunta ga d'aya daga cikin sunanyen contact nata" MY KAS sunan da ke bayyane akan screen nata kenan"laluban wayan na shi ta shiga yi"har sau biyu yana shiga amma ba'a d'au ka ba"m'ikewa tai daga kwanciyan da take tare da cunkud'e fuska tana mai ci gaba da latsa wayan nata"Allah yau kam ko asuba xa tai min se na tabbatar da ka..... ba ta kai k'arshen maganan zucinta ba ta ji takkk....alamun d'aukan waya"wani gauran numfashi ta saki tare da manna wayan akunnenta" Amincin Allah ya tabbata a gareka jarumin jarumai" "Shiru" Sorry fa na hanaka bacci" "Shiru" Nasan tabbas kana ji na but ba wai maganan na ka ne abin so na a yanxu ba,abinda zan gaya maka shine abin so na da kai ka ji" "Duk da haka de Shiru" A zahirin gaskiya na yaba da kamala irin ta kwarzon dattijo kamar ka,don naji kowa yakan yabe ka,sai de ni na kasa gaskata hakan,ko meye dalili?nasan de bazan tab'a samun had'in kan ka ba,bawai dan bazan iya ba,ko banda hanyar yi,nop ko d'aya sai dan ba wannan buk'atar ce a wajena ba" . Prof.KAS abu ne k'arami a wajena amma bansan yadda kai zaka d'aukeshi ba"wato na tak'aice ma de course naka da kake yi wato 1301 nake so naga correct A1 a result d'ina" Yin hakan gareka kamar taimakon kai ne kaga ni na samu jarabawa na, kai kuma ka tsira da mutuncinka,in kuwa ka bijire wa buk'atata toh wallahi abinda zai biyo baya se yafi haka zafi da muni dan ko sai na sa an yad'a min kai a jami'a da hoton da mukai na cewa ka nemeni a office naka nak'i baka had'in kai,kasan de sharrin 'ya mace saurin karb'uwa ne dashi dan haka sai ka zab'a aciki!". Hankali kwance beauty ke maganan har ta k'arashe alamun da take gani na kamar baze tanka taba ne yasa tai k'arfin halin sai-saita dariyan da take tace"prof.nasan tunanin da kake na matarka da 'ya'yanka kai har ma da sauran jama'ar gari yadda zasu kalleka ko"?so just think about it wisely". Emmmm by the way sir d'axu baka zo lecture ba wani yaro ka turo shi wannan ya sunansa? "Shiru" Bacci ya fara d'aukana pls ka fad'a min mana" Sunansa _*SAMEER ALK'ASEEM MAJI-DAD'I* Dan Allah yarinya ki ji tsoron Allah ki fita harka ta duk da nasan ban nemeki da sharri ba wallahi ban tab'a aikata abu makamancin haka ba"ban tab'a injustice ko ba wani marks free ba se yau kike so na da hakan why?baza kije ki karatu ki ci marks d'in da kanki ba"duk yadda na kai ga wulak'anta mata masu zo min da buk'ata irin naki na kasa miki haka"toh meyasa kema baza ki fita a harka na ba pls"ko ba dan komai ba ki duba girman shekaruna da iyalina mana". Heeeeyyyyyyy ix ok sir bana son wani surutu haka"wa'azi zakai min?toh ka de ji abinda nace ni ban nemanka da sharri ba kawai de kabi dokar *'YAR JAMI'A* _So just go and sleep and i wish u a colourful night_ Tana kaiwa haka ta katse wayan abunta"tai wurgi da ita gefe". ****** Haka rayuwa ga beauty taci gaba cikin jin dad'i da kwanciyar hankali duk wani abu nata da take buk'ata na rayuwa tana samu ga mahaifinta"in kuma batun makaranta ne data buk'aci wani abu zata kira wanda abun ya shafa"dan jami'ar ma yanxu ta tsaya da zuwa sai dai lokaci-zuwa lokaci wani uzuri nata ya kaita"sosai mu'amala ta goge tsakaninta da lecturers d'in nan yadda take so haka suke mata"wanda duk yaso shiga harkar ta ko a school tuni zata sa a dakatar da mutum a karatu"shaharar beauty ta kai inda takai"dan kowa yasan wace *'yar jami'a* babba ko yaro" Duk inda ta wuce nuna ta ake"b'angaren zee-zee ma de abin ba'a cewa komi duk da takan shiga lectures amma dai suna ne don yawancin yanzu tare suke zuwa yawonsu sai can dare ko yamma lik'is sukan koma gida. Koda ummah ta tambayeta game sa canjin lokacin na dawowarta yanxu kam cewa tai an gyara musu time table ne,duk da ba wani gamsuwa tai ummah da hakan ba amma ya zatai dole ta barta a hakan!"gudun fad'an dady!" A b'angaren Sameer kuwa tun randa dady yazo mai da maganar baya son ganinshi a harabar gidansa se ya zamana kullum yana sashensa"don k'arfe 6:00a.m yake fita waje baya kuma dawowa sai 9:00p.m tunda Allah ya had'ashi da wani frnd Ameenu shike nan ya samu gidan zama!" .* Kamar kullum dai yau ma prof KAS zaune yake a faffad'an office nashi"kansa duk'e yana bitar wasu takaddu wanda da alama suna da matuk'ar anfani a gareshi yaji an bud'e k'ofa".ko da ya d'aga kai da murmushinsa ya sauke ga bak'on nasa"matashi ne ajin farko wajen iya shiga da haiba" wato Sameer kenan"k'ofan ya me da ya rufe ya k'araso ciki"cike da girmamawa ya gaishesa kafin ya nemi ixinin zama".hira suka shiga yi sosai irin na d'a da uba,inda prof ke ta zubo masa tambayoyi game da jami'ar don jin ko yana fuskantar wani k'alubale"hakan kuwa sameer yace babu don tun fara aikin bautar k'asan sameer a makarantar babu wata 'ya mace data samu damar masa magana duk da ana yawan yabawa da komai nashi amma sam yak'i bada fuska"kasancewar shi mutum ne mara son rai ni ko kad'an".daga haka prof ya d'an k'arayi ma sameer wasu 'yan nasihohin duk de akan sharrin mace"abin har yakai yana ba ma sameer mamaki yadda prof ke masa nasihan" don shi tun tashinsa mace ma bata gabansa balle har yayi tunanin biye mata"haka de yabi prof da toh kafin daga bisani yayi masa godiya da nasihan". Long sheet dake gabanshi a hankali prof yake kallonta can ya nisa ya ce wannan fa result ne na yaran can da ake k'ok'arin kafe musu yau kasan sati uku baya sukai jarabawan" D'ago kai sameer yayi yana mai bin sheet d'in da kallo sannan yace but sir ande samu gud performance nasu ko? Ehh toh gashi nan amma de..... Bud'e k'ofan da akai ne ya hana prof kasa k'arasa magananshi"hantar cikinsa ce ta bada wani irin k'ara cike da razanin halittar da ya gani gaban k'ofarsa"cikin isa da tak'ama ta k'araso har gaban tabur d'in nasa daf da kujeran da sameer ke zaune taja kujeran gefe d'aya ta zauna"kallo duk suka bita dashi musamman sameer da be tab'a tsammanin ganin wata mace a office na prof ba"musamman irin wannan matan"sam mace ba kamun kai"ga jiki kusan tsirara har kana iya hango kalar bra din jikinta don tsananin hasken kayan data sa" kai k'asa sameer yayi don baze iya jure ma ganin abu irin wannan ba" Shirun nasu ta katse cike da shauk'i beauty ke fad'in Morning sir"ka ganni se yanxu ko bacci ya d'auke ni da yawa" by d way bade wannan ne result d'in namu ba?let me see?hannu ta kai ga sheet d'in hankali kwance ta rabo shi da ita" Shiko ji yake prof kamar ya bud'e k'asa ya shige a ciki dan kunya"yanxu da wane ido zai d'aga ya kalli sameer?yanxu fa yake masa fad'a kan bin ashararan matan jami'a gashi tun ba'a je ko ina ba shi ya kamasa da irinsu". Wow good job dad'i na wallahi da mutane na saurin d'aukar darasi kaga de kowa yasan hak'k'in d'an uwansa"but second class kuma?"yamutse fuska beauty tai can kuma ta saki tana fad'in i will just manage it bari naga na k'awas d'ina" nan ta shiga duba na zee-zee" Hhhhh dariya"shegiyar gari wallahi ta haye kalli wannan gaye d'in ma da tace course na shi da wahala se gata da B2 da alamun ya bada kai kenan"? Ke wai me haka kike yi ne?cikin zafin nama da rashin jin dad'in abinda beauty take sameer ke maganar". A raunane beauty ta d'ago kai cike da mamaki ta wurga masa wani wulak'an taccen kallo tace and who are yuh? Kake min tsiwa baka bari uban gidan naka yayi?ko kuwa wani sabon iskanci ne hakan?". Be kai ga magana ba prof yayi saurin dakatar dasu" wai what's going on ne haka? Kuyi shiru mana"magana prof yake duk a kunyace"ya ma rasa me xaiyi" Kasa jurewa abin yayi sameer lura da yadda yanayin prof duk ya canja yasa shi mik'ewa tsaye a fusace ya hau dubanta yana gyad'a yatsa" Surely u dn't know who i'm" But i sameer d son of Alkhaseem cn't take all these of your nonsensity" In kuma kinyi denaying haka wait and see"bugun da yakai ga tabur d'in yayi dai-dai da juyawansa don fita".zafin naman itama de beauty ta nuna inda ta cakulo wuyansa tana me wurgi da sheet d'in waje guda tana wani zare ido kamar mayunwaciyar zakanya cike da huci ta fara fad'anta"ni kake ma shouting akai?baka san wace *'Yar jami'a*ba ko?ka rubuta ka aje wa'adin aikin ka yazo k'arshe". Sake mai kwalan riga tai ta juya a fusace da yake ba komi hannunta dama ta shigo haka tai waje abinta" Karo na farko da wata 'ya mace ta tab'a matsowa har kusa da sameer haka sai gashi abin ya kai ga cakumar riga?"kan ubancan" Yayi maganan a fili yana kallon prof da tuni idonsa ya gama cika da kwalla" dan takaici"abinda yake gudu kar wani yasani yayi masa kallon ashararan mutum yau ya tabbata" Hannu ya k'ara kaiwa ya bugi tabur d'in cikin tsiwa sameer yake fad'in ashe kuwa yarinyar nan ta taro match se na nuna mata ya ake rayuwar jami'a"bade tai ikirarin ita *'yar jami'a*bace? Be jira cewar prof ba ya juya a fusace yayi waje"ji kake garrrrraaaammm na rufewan k'ofa"! . Bata jira ji daga gareshi ba beauty cikin zafin nama ta mik'e had'e da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya,tai hanyar fita,cigaba malam umar yayi da kiran sunanta abin tin yana k'asa da voice nasa har ya k'ara raising nashi amma sam beauty tak'i sauraronshi." Cikin b'acin rai na rashin samun mafita da haka ta baro office d'in nan ta nufi hanyar barin jami'ar" gudu take sosai abin ta har ta cimma babban gate d'in kamar baza ta tsaya ba kuma kome ta tuno ai ko ta saki uban birki a bakin wajen ji kake keeeeeeeeeeee"na k'arar tsayuwar mota"cikn sauri mutanen dake bakin wajen kowa ya dawo da hankalinsa gareta don ganin ko lafiya?hankali kwance take bud'e glass na motan tare da fiddo hannu rik'e da k'aramin kati(exit) a hannunta ta mik'a ma security man d'in"tun tsayuwar motar agun duk ma'aikatan gurin sun fahimci motar wace shiyasa ma basu wani d'aga hankali da abun ba don inda sabo su kam sun saba"hannu ya mik'o had'e da amsa da haka ta maida glass nata sama ta ja motanta gaba". ****** Mutumi na kana ina ne?cewar sameer wanda yake zaune cikin mota yana tuk'i ga waya a manne a kunnensa yanayi hankalinsa a tashe kana gani kasan cike yake da damuwa"daga d'ayan b'angaren aka bashi amsa sannan yace owk toh gani nan k'arasowa ina hanya".katse wqyan nashi yayi ya ci gaba da tuk'insa,kusan minti goma kenan da yin haka sai gashi a bakin wani makeken gida"horn biyu yayi mai gadi ya lek'o gami da bud'e gate d'in fahimtar wanda ya zo da yayi",a parking Space na gidan yaje cikin jerun motocin gurin ya aje nashi gami da fitowa ya nufi cikin gidan".a falo ya tarar da mama wato mahaifiyarameenu inda cikin girmamawa ya gaisheta sannan ya nemi izinin shiga cike"cikin wannan takun nasa na isa da tak'ama yake takawa kamar wani wanda ke tsoron k'asa haka ya riski d'akin".da sallamarsa sameer ya bud'e d'akin"amsanshi ameenu yayi a nutse"amma sameer ko ta kansa bai bi ba ya nufi gado abinsa"kwanciya yayi ya juya baya had'e da rufe ido kamar wani me bacci" Ameenu Dake zaune saman 2 seater rik'e da magazine yana karantawa, cike da mamakin yanayi irin na aminin nasa dole ya ajiyeta gefe guda ya nufo gareshi" Prince lafiya? Meke damunka haka?mtsssssss......... wani dogon tsaki da sameer ya saki ne ya k'ara tabbatar masa cewa da abinda ke damunsa"hannu yakai ya d'an dafa kafad'ansa a hankali ya shiga bubbuga masa ita yana fad'in pls be lyk a man"fushi fa ba naka bane"koma waye ya b'ata maka just forget about it & let us chill like nothing do you man pls"wani wawan juyi sameer yayo nan take kuma yabi shi da kallo cike da b'acin rai kafin ya iya mosa lips na shi a hankali yace"kasan kuwa me kake cewa?kana so kace na manta da abinda ya faru yau?that is unbearable"ba ran iya hak'ura ba wallahi"nan da nan kuma yanayinsa ya canja jijiyoyin gaban kansa duk suka riga suka mik'e cikin zafin nama ya d'ago jajayen idanunsa yace"se na koya mata hankali"sena tabbatar mata cewa jami'a ba gidan iskanci bane gidan koyan karatu da ladabtarwa ne" wai ni sameer yau wata banza har zata kalleni ta fad'a min magana"by the side ita 'yar gidan uban wace take jin kanta haka? Sai a lokacin ameenu ya fahimci inda sameer ya dosa"duk ta k'are dama yasan hakan na iya faruwa'don ba yarda za'ai matashin namiji kamar sameer ace bai samu matsala da mata ba"sai gashi yau yazo masa da zancen"murmushi mara sauti ya yi kafin ya kai dubansa ga sameer ya iya cewa"calmdown prince yanxu akan wata mace kake d'aga voice naka haka?kamar ba sameer d'in dana sani a baya ba wanda kullum kake cemin mace bata gabanka yau kuma ya abin ya canja?ko de ka fad'a mata wani secret na mind d'in ka tayi rejecting ne?fad'amin naji wace lucky gal ta yi nasara akanka haka?"cike da zolaya yake maganar"mugun duka sameer ya kai masa a cinyarsa ji kake d'asss..dan maganar tai mai ciwo"stop it kaga bana cikin wasa yanzu"ko zakai min wasa karka k'ara had'ani da wannan 'yar iskar wacce bata ma san ciwon kanta ba"may be ma iskanci akai da uwarta aka haifeta shiyasa itama take haka amma kana dangantani da ita?ganin yadda sameer ya d'au zafi na ruwan bala'i yasa ameenu sassauta murya ya hau masa nasiha" Kaga de prince ba'a haka a rayuwa duk laifin da mutum yayi maka baka ai batashi haka don baka san wanne baiwa Allah ya aje a tattare da shi ba"duk da na fahimci akan mace kake wannan fad'an toh ina so ka sani ita mace k'ara min tunani gareta abu k'an k'ani na iya saka ta ga tafarkin dai-dai haka zalika abu k'arami yakan iya jefata ga halaka"saboda su mutane ne masu rauni"idan mace tai maka ba dai-dai ba rabuwa kake da ita sai kai mata addu'ar shiriya". Addu'ar shirya?shirya fa kace?lallai baka san yarinyar nan ba kenan? ai ba zata tab'a shiryuwa ba" illah kawai na samu hanyar da zan lalata mata rayuwa ta gane cewa tayi kuskure a rayuwarta data d'auki jami'a tamkar gidan b'atanci zalla"kaji de na gaya maka"yana wani gyad'a masa hannu alamun gargad'i". Toh naji but meye sunanta? Cike da harara sameer yake kallonsa" kamar shi yayi masa laifin can kuma ya saki wani dogon tsuka yace" i don't care to know that"all what i know de ana kiranta da *'yar jami'a* kaji wani banzan suna"sameer ya fad'a yana watsa hananye"shide ameenu binsa kawai yake da ido kafi ya nisa ya ce toh Allah de ya sawwak'e amma yanzu muci abinci ka huta se na rad'a maka wata sauk'ak'ak'kiyar hanya ko zaka iya binta may be da haka ka rama wanna abun da tai maka" Jin haka ba k'ara min kwantar ma sameer rai yayi ba don shi babban burinsa dama be wuci yaga ya rama abinda beauty tai masa ba musamman ya samu hanyar korarta a karatunta". Haka suka zauna gidan bashi ya koma gida ba se can bayan 10:00p.m.koda ya koma watsa ruwa kawai yayi tare a jero nafilfilinsa na dare sannan ya haye makwancinsa". . Tun fitowar beauty bata zame ko ina ba sai office d'in malam umar ko da ta isa ta tarar da dashi tare da bak'o"dole ta d'an dakata a waje"kusan minti goma da haka sai ga shi ya fito don raka bak'on nasa ai ganin beauty tsaye gaban office nasa sai kai kawo take a wajen kamar wata zautacciya"dole yayi sallama da bak'on nashi ya k'araso gaban ta cikin sauri" "Yar jami'a lafiya? . Da saurinta beauty ta juyo daga zagayen da take yi se wani ajiyan xuciya take saki tace"mu shiga ciki wannan ba maganar waje bace" Gaba ya wuce tana biye da shi a baya har suka k'ara office nashi"tsaye tai gaban kuje ran"yayi yayi ta zauna amma sam beauty tak'i" Dole shima ya taso ya dawo kusa da ita ya shiga magana cikin tattausan lafazi don ya lura tabbas yau ran mutuniyar tasa b'ace yake" Pls kyakykyawa ki d'an saki fuskan ki daga wannan cukulewan wlhi sam be dace dake ba" Wane abu kike so a makarantar nan baki samu ba? Ina ce na baki file me d'auke da komai na jami'ar nan'kuma da bakinki kince min kingama samun komi naki" Wait malam kar ka sake cewa ka bani komi"baka bani ba ni zakai ma wayo"cike da tsiwa beauty ke maganan" Wallahi a iyakar sanina na gama baki komi, amma fad'a min me kike so yanxu? Kallo me cike da raini beauty ta wurga me dole ya d'an kauda kai"kafin can ta d'ago kai tace: "Ina so ka gaya min game da wani wai shi sameer alqaseem"tell me waye shi?kuma d'an gidan uban waye a garin nan da har ze zage ni a gaban prof KAS"? Wqni gauren numfashi malam umar ya saki cike da fargaban sunan da yaji beauty ta kira nan ya ja kujerar dake gefensa ya zauna dan samun cikekken nutsuwa" A hankali ya matso da wata kujera dake gefensa kusa dashi yayi ma beauty nuni data zauna ba musu kuwa da zauna ta maido dubanta gareshi tana saurare" Wato kina ji ko 'yar jami'a bazan b'oyr miki komi ba dan nasan mun zama d'aya kuma ko wane abu zaki iya yi a makarantar nan amma bazan tab'a lamunce wa kaina baki damar shiga harkar wannan bawan Allahn ba"dan shi ba malami bane"aikin bautar k'asa ne ya kawo shi nan garin kuma yanxu yaci rabi zuwa k'arshen shekara zebar wajen nan"ki rabu da shi kawai in ma abu yayi miki kiyi hak'uri a karo na farko de pls"!! What malam umar kasan ko me kake cewa?ai gara kace min baza ka iya ba kawai na nemi wata hanyar amma ba ka tsaya min wa'azi ba"dan ko wallahi ka rubuta ka aje korarsa za'ai a jami'ar nan confirm". . Ta b'angaren beauty kuwa ranar tun komawarta gida d'aki ta nufa ta kulle kanta haka ta wuni ciki"tun abin be dami ummah ba har yakai ga ya fara don sam beauty bata fiya jimawa haka a d'aki ba ko da kuwa baza ta fito parlo ta zauna ba amma dai ta kan lek'o tym to tym sab'anin yau'se de ko da ummah taje ta tambayeta se ta nuna mata ba komi" Da misalin k'arfe 8:00p.m daddy ya shigo gida sashensa ya wuce inda ya iske ummah tsaye rik'e da garwashi na turaren wuta tana turara falon"wani a jiyar zuciya dady ya saki sakamakon wani daddad'an k'amshi daya doki hancinsa"cike da murmushi umma ta nufo shi tana me ajiye garwashin gefe guda" Rungume juna sukai na d'an tsawon lokaci wqnda hakan ya nuna tsantar kulawa da missing na junansu da sukayi"umma ce ta shiga janye jikinta a hankali tare da amsan jakan dake d'auke a hannunsa" Sannu da dawowa dear" Yawwa umman beauty"ya kula da gida da kuma kanki hope de baki wahalar min da jikin nan naki sosai ba?"daddy ya fad'i idonsa k'uru bisa nata" Haba dear kaima kasan ba yadda za'ai na wahalar maka da jikin nan naka da yawa,zaka sameshi yau fiye da kullum" Allah umman beauty??cewan dady yana washe baki. Sosai ma kuwa! se de fa wani hanzari ba gudu ba yau na kasa gane kan yarinyar can tun dawowqrta a makaranta take d'aki".what??? Amma kuma kike cemin gida lpy?yoh ba gwara komi ya hargitse ba da b'acin ran gudaliya ta"bari naje naji me ke damunta"cikin matsanancin damuwa daya riski daddy lokaci d'aya haka ya nufi sashen beauty" Knocking......yes daddy come in"beauty dake kwance can saman gado ta juya ma k'ofa baya tai maganan sanin cewa daddy ne kad'ai ke mata irin wannna knocking d'in" Bud'e k'ofan yayi had'e da kiran sunanta yana mai k'ara sowa cikin d'akin"k'aramin teddy nata dake mak'ale a jikinta ta janyo gami da wurga ma dadmdy shi kamar yadda ta saba in tana matsanancin fushi irin wannan tace pls daddy go away ni bana son ganin kowa yanxu"just go"tai maganan tana turo baki waje"be biye ta nata ba dady ya haye gadon daf da ita ya zauna tare da sak'ala hannunta cikin nashi ya juyo da fuskanta gareshi murya ciki-ciki dady ke tambayan beauty na waye ya b'ata miki rai ki gaya min ko waye shi & i promise u cewa zan dealing nashi kowaye pls my one and only one"lura da yadda daddy ya damu sosai da halin da take cike da yadda dady ke fad'in ze dealing ma damuwanta yasa ta d'an saki ran nata kad'an ta shiga magana uwa tana rad'a"dady wani lecturer ne baya son cigaba na a school d'in nan duk yabi ya dameni yau fa har ikirari yake wai se ya koreni don kawai na samu result me kyau so shine nake so dady ka saka a koreshi kafin shi ya aiwqtar da nashi akaina" Jim dady yayi a fari da jin batun da beauty ta zo mai dashi yana tunanin hanyar da zai magance damuwan nata" Beauty meye ne had'inki da wani malami a makaranta kinsan fa duk wani abu dazai janyo na samu nak'asu a har kar kasuwancina beauty bana so"bana so in ji kina rigima da wasu don duk wanda yasan cewa ke 'yata ce zai so kuyi kyakykyawar mu'amala ba mummuna ba"inda san samu na ne har ki gama karatunki ba wanda zai san ki in ba 'yan ajinku ba"suma d'in se dan ya zama dole amma yanxu ni naje nasaka a kori wani ai se a watsa a kafafan yad'a labarai wanda hakan ba karamin zubar min dq k'ima ze yi ba"pls beauty dadynki na baki hak'uri da ki bar maganar nan tunda kince kinyi nasara a jarabawarki watak'il abu kika mai ba dai-dai ba kawai ki bashi hak'uri duk randa kuka had'u kuma ki fita a harkarsa,kinsan fa bana so ummanki ta fahimci wani abu so nake ki bata mamaki duk da tana ganin bazaki iya karatun nan ba ki taimaka mu bata mamaki"ki fita da flying colours se mu had'a wani gagarumin shagali"koya kika ce beauty??fuska ba yabo ba fallasa beauty ke bin dady da kallo duk da hakan da ya fad'a sam be yi mata ba toh ya ma za'ai kamar ita ace ba wanda zai santa sai mate d'inta ashe bata cika *'yar jami'ar*ba,banda cincirun don malamai gogaggu da beauty ke harka da su"dariyan yak'e ta sakar me tare da langwab'ar da kai a jikinsa ta lafe tace ok dady na ji ba komi zan fita a har karsa amma kai ma de kasan bazan je na bashi hak'uri ba but believe me duk randa ya k'ara shiga har kata Se ka d'au fansa daddy" Dady promise me mana kayi shiru" Sanin rigima irinta beauty dole dady ya amsa mata da yes"da haka ya kamo hannunta suna ta hira abinsu duk da beauty ta gama k'udurta bin wata hanyar don ganin ta muxguna ma sameer da haka suka sakko dinning inda ummah ta gama jera kayan abinci nan suka zauna don cin dinner" Sosai beauty ke cin abincin don wata irin matsananciyar yunwa data wuni da ita nan ummah ta samesu itama tai joining d'insu"bayan sun gama ne dady ya k'ara jan hannun beauty falo inda sukai ta kallo suna hira ala dole dady naso ya ga ya kawar ma beauty da damuwarta" K'arar horn na shigowan mota suka ji dady ne yace toh ga d'an albarkan nan ya dawo" Hmmm kai da ka sanshi ba? ace yaro tun zuwanshi gidan nan ban tab'a saka shi a ido na ba"ko tunanin yazo ya gaishe ni be yi ba?cewan momy tana kalon dady"beauty ko kamar jira take nan ta soma"ai wallahi umma shiyasa ni tun farko nace ban yarda kowa yazo mana gidan nan ba don duk basu da tarbiyya dady ya nace se yazo". Hannu dady ya kai ga bakinta yayi saurin tsayar da ita a magana yana cewa kai beauty na kin manta ke kika ce min kin yarda yazo amma bakya son ganinsa a hara bar gidan nan"shine fa nai masa iyaka da cikin gida dan kar yazo ya damar mun ke". Dariya sosai kake gani d'auke saman fuskar beauty sorry dady kaga na manta,gaskiya dady na k'ara tabbatar wa kana so na fiye da tunani na me too luv you dady"peck ta kai masa a kumatu' nan suka hau dariya na jin dad'i abinsu nan-da-nan beauty ta shiga yi mai surutai kala-kala wani abun ma duk shirme kamar ba wacce ta mallaki hankalin kanta ba" Mik'ewa ummah tai don takaicin yadda suka maida ita gefe guda suka watsar suna ta hirarsu"duk abin duniya ya isheta ita ba abin tai kishi da 'yar cikinta ba'dole ta nufi sama abinta ta bar su nan falo zaune" Ba ita ta shiga d'aki ba beauty se wajen 12p.m haka watsa ruwa tare da haye wa gado"wayarta ta janyo ta shiga laluben numbers na wasu daga cikin lectures din abokan harkarta"a inda duk wanda takai ma batu na korar sameer daga aiki se a nuna mata gazawar hakan,wasu kuma su nuna mata yiyuwar hakan amma indai har zata kai musu ziyara a wajen had'uwarsu"dole take amsa musu da eh tunda bata da wani buri yanxu wanda ya wuce taga ta kori sameer daga jami'a kafin shi yayi kamar yadda ya furta mata". Yau take litinin wanda yayi dai-dai da dqwowar d'alibai daga hutun sati biyu da aka basu na gama zangon karatu na farko (wato first semester),kowa ka ganshi cikin shirinsa tsaf na komawa karatu wasu fuskoki na shek'i na samun nasarar jarabawar baya wasu kuma akasin haka" Zaune take a bakin wata theater rik'e da takadda a hannu"ta na yamutsa fuska xee-xee ta d'ago kai ta dube ta".wai beauty lapiya naga duk kin wani had'a fuska?banxan kallo me cike da jin zafin tambayar beauty ke kallonta dashi can kuma ta kai ajiyan lumfashi tana fad'in ai dama ke baxa kiga komi ba" amma fa ki kalli time table d'in nan har da statistic bayan kinsan bana son harkar calculation"ni wallahi duk naji karatun ya fita a kaina"baki xee-xee ta bud'e cike da mamaki toh da har wani karatu ma beauty ke yi a haka?a xahiri kuwa tace haba beauty ke da jami'a ke hannunki ai bake ba har ni xan so A1 ko ya kikace kawai first lecture d'in xamu shiga da haka xamu gane wa xe d'auke mu in me xafin kai ne na bar ki dashi in kuwa ruwa-ruwa ne ki watso min number d'insa" Tabbas beauty na matuk'ar jin dad'in yadda xee-xee ke yawan yabonta haka'suna cikin haka sqllama suka ji an sakar musu cikin wata siririyar murya"yi sukai uwa basu jiba haka aka k'ara rangad'a sallamar cikin kasalanci xee-xee ta d'ago kai tana kallonta"matashiyar yarinya ce kana ganinta kaga kamilar mace me cike da addini basai an gaya maka ba"don sanye take da atamfa d'inkin riga da skirt ga doguwar hijab har k'asa"sannan k'afafun nan an suturcesu da safa" Sannunku"matashiyar ta fad'a" Yawwa meke faruwa kika xo saman kanmu kikai mana inuwa kamar wata ice?xee-xee kenan tana magana tana wani taunar cingom"cikin halin ko in kula matashiyar ta saki wani k'aramin ajiyan zuciya tace eh dama naga kamar kuma class d'inmu d'aya kuma naga yawanci duk ba'a da time table shine nace bari na tambaye ku? D'agowa tai cikin sauri beauty daga jinginar da tai da kujera ta d'ago kai a karo na farko tana dubanta" Me kika ce?time me??time table?? Eyyee kaga director kai koma ince rector saboda ga sa'anninki ko?duk fad'in makarantar nan baki ga maraina wayonki cikin sanyin safiyar nan ba se mu ko?bakusan ku yak'in nema ba se an samu kuyi photo copy ki??toh ga time table d'in a hannu na xo ki karb'a?cikin fad'a-fad'a beauty ke maganan tana gyada k'afa" Jin yadda beauty ke magana yasa matashiyar k'ara san yaya murya tace kiyi hak'uri ni ba fad'a nazo yi ba"k'ok'arin juyawa ta shiga yi don barin wajen don tasan tsayuwarta kan iya haifar da wani abun" wani dogon tsaki mtsssss... xee-xee ta saki a gurin tare da k'ara kare wa matashiyar kallo ta baya"dubeta kucakar banxa ko an gaya mata nan tsangayace ko xauran wa'axi da xata xumbulo mana hijabi luuuuuu....se kuma ta katse maganar sakamakon wata muguwar dariya da taji ta kufcewa beauty"da sauri ta d'ago tana tambayar lpy de?se da tai dariya me isarta beauty sannan ta waigota tana nuna ta da hannu cike da mamaki" Dilla can kin ganki wai har kura ce xata cewa kare maye" ko kema ba hakan kike tahowa daga gida ba ki shigo mana jami'a uwa matar malam se an xo abi lungu a canja"se kuma ta k'ara tuntsurewa da dariya tana fad'in gaskiya duk ranar da na ganki cikin kayan zafin can dole na ja ki miyi selfie" Yanda take dariya abin ya matuk'ar bawa xee-xee haushi"wannan ma ai cin fuska ne"cikin fushi ta mik'e wqnda tuni beauty ta rik'o hannunta nan ta shiga bata hak'uri"zama ta koma tai fuska ba yabo ba fallasa take fad'in ok komai ya wuce yanxu ina ki kai? Yamutsa fuska beauty ta d'anyi kafin ta saki tace'gida xan wuce dama kinga abinda ya shigo dani ta nuna time table"yanxu haka kuma xan fitq a school sede hanxari ba gudu ba yanxu ma na koma gidan ummah ta hau jero min tambayoyin na dawo da wuri"kai duniya wannan wacce irin uwace"?dafe kai beauty tai cike da damuwa kafin ta nisa tace any way daddy ai nasan be fita ba tunda yanxu 9:00a.m be yiba barq nai sauri na koma na samu me karemin"xumbur beauty ta mik'e had'e da sak'ale jakanta a wuya ta juyo ta kalli xee-xee tace kin gane xan wuce se munyi waya"a haka suka rabu beauty ta shige mota ta fice a jamiar ta nufi gida!. . . Da isarta gida q haraba ta tadda motar daddy ali driver na wanke masa cike da murna ta k'ara so ciki"falo ta dosa kai tsaye tana shirin bud'e labule ta ji an bud'e cikin hanzari ta ja da baya ta tsaya"ummah ce ta fara fitowa rik'e da brief case"daddy na biye da ita"hajara lpy kika dawo gida yanxu ko kin yi mantuwa ne?cewar ummah tana dubanta fuska had'e" dama tabbas tasan haka xe faru beauty don haka tai saurin kai idonta ga daddy inda tai nare da su"gyaran murya daddy ya saki tare da kamo hannun ummah kad'an ya ja da alamun ta sauke idon ta haka daga kallon da take wurgar beauty dashi"burus ummah tai tambar bata ji shi ba inda ma ta sake jefo mata tambayan"da ke fa nake kikai min shiru ko?? Ganin yadda ummah yanayinta ya sauya ya baiwa beauty damar daurewa murya cike da sark'ewa tace emm..emm dama yau ba lecture se gobe bayan munje ne monitor ya sanar" Badan ummah ta yarda da xancen beauty ba amma dole yasa ta shareta lura da sauyawar fuskar daddy". "Beauty nah tafiya ce fa ta kamani yanxu haka,bayan fitar ki d'axu governor ya sanar dani wani taro da zashi jarmany na harkar farfad'owar tattalin arxikin kasuwanci"ya kuma nemi dana shirya muje tare yanxu haka jakata na mota xan wuce" Yeennnnnnn.....kuka beauty ta saki tuni ta shiga buga k'afa tana wani langab'ar da kai da hannu ta hau magana a shagwab'e"yanxu da bandawo ba haka dady xaka tafi ban sani ba"toh Allah nima ka tsaya na had'o kayana mu tafi tare"yunk'urawa tayi da niyyar shiga ciki dady cikin sauri har yana tuntub'e da labule ya biyo bayanta yana kiran sunanta" Ya ilahi"me xan gani haka?allahu qadirun ala man yasha'u"ita abin ma dariya ya baiwa ummah yadda dady ke biye ma beauty uwa wani rak'umi da akala ganin da gaske sun haye sama sun barta tsaye bakin k'ofa yasa ta dawowa ciki ta nemi kujera ta xauna tana fad'in kuyi ku gama kwa iske ni nan"ba inda xan biku na tadda takaici" Beauty kam bata zame ko ina ba se gaban wardrobe d'inta ta tsaya saurin rik'o hannunta dady yayi inda ta fincike da k'arfinta tana murgud'e baki tace"ni allah kar ka ce min wani abu se na bika baran zauna ni kad'ai se ummah a gida ba nasan ba fad'a ba wataran duka na zatai"cike da tashin hankali dady a karo na biyo ya k'ara kai hannunshi ga beauty ya rik'ota" Murya can k'asa uwa me shirin kuka ta shiga bata baki"_beauty na ki yi hakuri ki banni na tafi ni kad'ai kinsan fa wannan ba personal tafiya bane balle nace zani da ke kuma duka-duka fa bazan wuce 1week ba,bqtun ummah kuma tun da naji maganar tafiyar nan na ja mata kunne sosai akan kar ta takura min ke,kinji ko ki dai na damuwa indan wannan ne"da alamun yarda da maganan daddy'beauty ta gyad'a kai tace are sure daddy kai mata fad'an?yes my daughter believe me nai mata"yanxu de gaya min me kike so na baki kafin na wuce"abin ne ma ya samu ga beauty washe baki tuni ta shiga yi nan ta fara zayyano buk'atunta wanda duk basu wuce kayan sakawa ba"nan daddy ya lalo kud'i himili guda ya aje mata wanda ita kanta se da kud'in ya firgitata don bata tab'a ganin dady ya bata kud'i masu yawa haka ba"wani wawan hugging ta kaima daddy cike da jin daddy tana fad'in thank yuh my amaxing dady yanxu kam xance maka safe journey" Dariya sosai suke abinsu nan dai su kai sallama dady ya fito ya nufo falo nan ma dai jan kunne sosai ya k'ara ma ummah kafin tarakashi har mota suyi sallama cikin alhini da nuna tsantsar missing ma juna da haka sukai bankwana"ali driver ya tada mota se government house" .* Tsaye take bakin window tana lek'en dady har ya fice kafin ta maida wata nannauyar ajiyar zuciya ta maido dubanta ga d'akin"gefen gado ta taka a hankali ta zauna tare da kai hannunta ga ajiyar da dady yayi mata ta janyo su ta shiga k'irgasu"ta k'arashe lissafasu had'e da kwarma wani uban ihu na farin ciki can kuma tai saurin toshe bakinta da hannu tana sak'awa arai"_kai ashe fa dady baya nan nake sakin wannan shewar kar na jama kaina fad'a"a fili kuwa ta furta N200,000 cab lallai yau akwai shiga mall bara na kira xee-xee"nan ta mik'a hannu a haka ta xaro waya ta shiga lalubar number xee-xee"k'ara biyu wayan ta saki kafin daga bisani xee-xee ta amsa wayan da fad'in kina wuta tawan"murmushi beauty ta fara saki sai kuma ta amsata itqma da kema haka k'awas yanxu de ba lokacin hira bane ki shirya bayan sallar la'asqr xanxo har gida na d'aukeki muje shopping dan haka se ki min text na address d'in gidanku" jimm xee-xee ta fara yi a farko dan sarai ta san halin gidansu da yadda mahaifinta yake gashi da xarar anyi sallar la'asar yake dawowa gida,in yazo yaga beauty a gidansu me xe ce don tana da tabbacin da irin shigar da beauty xata xo gidan nasu"toh amma ai mama na nan kuma nasan bazata hanani zuwa ba don haka ba damuwa"nan ta amsa wa beauty da toh se na ganki"sun d'an tab'a hira ba wani sosai ba da haka sukai sallama" . _Yammacin ranar:_ 4:15p.m . Tsaye take bakin k'ofar d'aki rik'e da jakar hannu,jikinta kuwa ta zumbula wani dogon hijabi har k'asa"taji sallamar mama d'aki"wai har yanxu k'awar taki bata xo bane zainab?eh mama amma na kira ta tace min ta kusa tana hanya"toh gara dai kuyi sauri dan kina ganin lokaci yanxu gyaji sallamar mahaifinki" ya mutse fuska xee-xee tai tace wallahi mama nima abinda nake ta ji ma tsoro kenan nasan yanxu yana xuwa fitar nan ta fasu"kuma ze iya wulak'anta min k'awa ko ya koreta"saurin katseta mama tayi da inah yaushe xan bari haka ta faru ya korar miki k'awa ba ita ce wacce kike ban labari 'yar babban mutum nan ba?eh mama ita ce"toh kinga ko in zaki huld'a da 'ya'yan masu hannu da shuni a hankali mijin aurenki ma ta nan tsatson xe fito ke dai kawai ki bar min komi a hannuna bari naje na k'arasa wasu ayyuka a can d'aki na" toh xee-xee ta amsa da tai waje" Zagayen d'aki kawai take tana duban agogo kamar daga sama taji k'arar horn na mota ai cikin sauri-sauri gudu-gudu ta fito a d'akin ta nufi wajen mama ta shaida mata ta k'araso"nan mama ta nuna mata tai sauri toh su wuce dai kafin baban nata ya dawo" da saurinta ta fito inda ta iske motar beauty kafe bakin gate d'in gidan nasu nan ta nufota" . Zaune take beauty cikin mota cikin wasu arnan kaya riga da skirt sai wata k'aramar hula data sak'ale kanta dashi"idannunta kafe a gidansu xee-xee nan ta shiga xancen xuci'gaskia ba laifi gidan yayi duk da dai unguwar lunguna sunyi mata yawa ga hayaniyar jama'a amma ade xaman gidan k'aramun ma'aikacin kwamnati ba laifi yayi k'ok'ari"tana cikin tunani taji an bud'e mota an shigo se a lokacin hankalinta ya dawo jikinta ta maida dubanta ga k'ofan"me zata gani?xee-xee murk'ushe cikin k'aton hijabi har k'asa" ai beauty bata san lokacin da dariya ta kwace mata ba ta nuna ta da yatsa tana fad'in me xan gani haka xee-xee kode kema kin koma matar malam ne?"cikin wasa xee-xee ta watso mata harara tana ci gaba da k'ok'arin yaye hijabin jikinta da yake motar me duhu ce tana fad'in banda lokacin ki ni dai yanxu yi sauri mu fita a layin nan koma meye kya tsokane ni dashi"batabar dariyar ba dai haka ta kunna motar tahau tuk'i'dai-dai kwanar hawa babban titi suka ci karo da baba cikin motarsa honda 307 yana k'okarin karyo kwana" Na shiga uku"xee'xee ta fad'a tana b'oye kanta k'asa"me ya faru ne?ko kin manta na waje baya ganin na ciki?beauty ke tambayarta"se alokacin ma xee-xee ta tuna da hakan nan dai ta d'ago kai ala dole ta sha mur don kar beauty ta tsokaneta"tace ai na sani kawai de tsohon nan ne se a slow yanxu haka se kiji yace jikinsa ya basa ina cikin motar nan"na rasa me yasa sam ya kasa yarda dani"kome nawa se yasamin ido,ko shi haka akai masa da yana saurayi oho?itade dariya kawai beauty take har sukai nisa da unguwar sannan ta iya cewa dama dady ya auri mamanki se umma mu had'ata da baba suje suyi ta wa'axinsu mu kuma muna jin dad'in rayuwarmu koya kikace k'awas?dariya itama xee-xee ta saka tace ehh wallahi da mun huta da b'acin ransu duka"se de nasan baba ko ana muzuru ana shaho baxe saki mama ba kamar wanda akai wa asirin natau da ita"ke nima fa haka umma ke nanik'ewa dady na ko de su ustaxannan shigewa mutum suke? Xee-xee ta amsata da oho musu su suka san kayansu"har suka cimma shopping mall d'in nan hirar nan dai d'aya ita suke! .* Katafaren kantin country mall dai-dai nan beauty ta tsayar da motarta tare da fitowa,haka xee-xee ta biyo bayanta,ciki suka shige abinsu nan suka shiga b'angaren kaya suka jidi kaya na axo a gani designers kala-kala don yawancin kayan komai kala d'aya suka d'auka abinda ya kama jaka da takalmi kai harda jewelries abindai ba'a cewa komi ranar kud'i ya sha kayi"ma'aikatan wajen su kansu beauty bata barsu a baya ba se datai musu kyakykyawar sallama bayan sun kawo mata kaya har mota"basu suka isa gida ba sai gab da sallar magrib inda ta sauke xee-xee a k'ofar gida,nan ta janyo hijabinta cikin jaka ta xumbula tare da janyo ledar kayanta ta nai ma beauty godiya ta fita har ta cimma gate beauty ta manna mata horn ta juyo bak'ar leda ta hau nuna mata dake ajeyi a bayan mota,hakan yasata dawowa tana fad'in kinga na manta kayan da kika ce a baiwa mama ko"nan ta karb'a tana mai k'arai mata godiya ta wuce"hakanan yasa itama beauty ta tada mota ta nufi gida" Kamar yadda ta saba haka yau ma ta shiga gida mota sautin kid'a se tashi yake haka tai parkin a wajen aje motoci tare da manna horn da gudu mai gadi ya taho rik'e da buta a hannu ya xube gefen marfin motar,booth tq bud'e masa ba magana ya nufi wajen dan yasan aikinsa,da haka ta fito ta nufi cikin gida"falon shiru ba alamar motsin kowa hakan ya tabbatar mata da umma da ma'aikatan gidan kowa na wajen sallah sashenta ta nufa itama"murd'a hannun k'ofarta yayi dai-dai da fitowar ummah daga sashenta rik'e da caxbi tana laxumi"daga ina kike?tambayar data fito daga bakin ummah kenan"cikin sauri beauty ta juyo dan har ta tsorata da jin murya bayanta"tuni ta saita nutsuwarta ganin ummah tace shopping naje nayi" shopping??shopping fa kikace awannan lokacin?in har da gaske kike ina kayan da kika siyo"kafin beauty ta iya cewa wani abu baba me gadi ya hawo sama nik'i-nik'i da kaya cike bisa hannu"sanin ummah cewa dady ya d'aure wa beauty bayan rashin aiki se dai ma'aikata suyo yasa bata tanka mata akan hakanba"gaisheta baba me gadi yayi inda beauty jiki sanyaye ta shige d'akinta yabi bayanta"gefe guda ya aje mata kayan ya fice" Sallah ta fara yi duk da dai cikin sauri aka kaita ana ta d'okin bud'e kaya"tana sallamewa ko addu'a bata samu damar yi ba ta doshi kayan"a hankali ta hau fiddo kayan tana k'are musu kallo"hannu ta kai ga wata doguwar riga kalar sky blue da ratsin bak'i ajikinsa ta d'aga ta sama tana k'are mata kallo se kuma can ta nisa tace tabbas wannan rigar dake xa'ai harka gobe tunda inaga muna da statistic kamar yadda na gani a time table se de kuma long slip ce" ta nisa kamar me tunanin wani abu se kuma ta basar kawai taci gaba da duban kayanta"k'ara wayanta ya shiga yi nan ta mik'a hannu ta d'akko a jaka"xee-xee kuma toh lapiya?tambayar datai kenan sannan ta d'auka" Beauty dama mama ce tace na kira mata ke a waya"cewar xee-xee"ok toh wani abu de ko?eh godiya dama xatai miki gata ma kusa bari na bata"nan mama ta karb'i waya suka gaisa da beauty godiya ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba har ta kai ta ga fad'in ai kullum in kina son rakiya unguwa zainab tana da cikakken lokaci kixo kuje"itade beauty toh shine kad'ai amsarta har sukai sallama mama na ta shi mata albarka kafin xee-xee ta amshi wayar su ci gaba da hira"bayan ta kashe wayar ne ta shiga gyaran kayan ta jere su a wardrobe bayab ta fitarda complete kayanda xata saka gobe a shiga *jami'a* d'aukar lecture! . Zaune take bisa stool gaban madubi se shafe-shafe take da alamar fara'a ainun d'auke sama fuskarta"ta d'au lokaci tana ta kwalliya kamar me shirin xuwa wani party ko dinner"bayan ta gama ne ta nufi wajen kayan data aje saman gado ta janyo su ta saka kamar yadda ta ware su daga irin kayan data siyo a fitar su da xee-xee jiya"da kokawa da nishi doguwar rigar nan ta shige jikinta"se faman haki take kamar wacce ta sha wani aiki"rigar tsaf ta amshi jikinta sosai duk wasu sak'o da loko na jikinta ya bayyana matuk'a gashi tai mata cif-cif kamar an aunata"haka ta zura d'an kunne,tare da jaka da takalmi harda k'ara min veil duk black tunda rigar sky blue ce"ko da beauty takai kallonta ga madubi wani irin ihun jin dad'i ta saki don ita kanta tasan yau kam abin ba'a cewa komai"gefen gado ta k'arasa ta bud'e k'aramar drawer dake wajen ta ciro wata jotter me sak'ale da biro ta xura a jaka"sannan ta matsa gefe wajen ma'ajiyar tirare nan ma tai ruwansa ajikinta"kafin ta zari key na mota ta fito kunne dod'e da earpiece se kad'a kai take na jin dad'in yadda kid'in ke tsima ta" a falo suka had'e da ummah cikin sauri ta tsaida kid'an tare da gaisheta a ladabce"da fara'arta ummah ta amsa mata kafin ta nuna mata dinning table dake cike da kayan bud'e baki"fahimtar abinda ummah ke nufi beauty tai ba musu ta nufi wajen nan sukai karin kumallo" bayan ta gama tai ma ummah sallama ta fito" . Ko da beauty ta shigo jami'ar office din malam umar ta fara wucewa sai dai ina lokacin bai k'araso ba da yake safiya ce sosai dan ko 8:00a.m batai ba"dole ta hak'ura bayan ta tura masa sak'on yanemeta in yaxo da haka ta nufi venue d'in su na ranar"ta jima cikin mota zaune tana ta kallace-kallacen jama'a mai shiga dame fita se sak'a zancen zuci take"cikin waigenta ne idonta ya kai ga captain d'insu tuni ta wangale gilashin motar ta shiga kiran sunansa"meenu!meenu! Da farko ameenu bai lura da kiran da take masa ba sai da wani d'alibi da suke tafiya tare ya ce masa wai ameenu ba sunanka nake jin 'yar jami'a na kira ba da yake kowa yasan beauty yadda ya kamata" hakan ya sashi mik'a ma d'alibin takaddunsa akan ya wuce masa dasu ciki kafin shi ya k'ara so"wajen beauty ya k'arasa nan suka gaisa sai kuma ta nisa tace haba meenu ka shigo mota mi magana mana xakai tsaye a waje"da farko ya d'an yi shiru kamar baxe shiga ba sai kuma ya xagaya ya bude motar ya shiga" A nutse meenu ya d'ago kai ya dubeta yace toh ina jin ki wani abu ne?ita abin ma dariya ya bata se yayi ta wani mata magana sauri-sauri aduk sanda suka had'u besan yaga suna jimawa a hira"itama kallon nasa tayi cike da murmushi tace ba wani abu bane illah aikin da kaimin watannin baya yau ma shi za kai min"wane aiki kuma?cewar ameenu"sunan malamin da zai d'aukemu statistic nake son ji" wata ajiyar zuciya ya sauke na jin dad'i da Allah yasa ba wani abun zata sakashi ba don shi sam be son abinda zai had'ashi da ita musamman yanxu da kowa yasan wace ita a jama'iar" Saukar lumfashinsa yaxo dai-dai da bata amsa"ehh toh nima dai bansan shiba amma dai dana tambayi wani tsohon lecturer anan yace d'alibai dai na kiransa sir prince but tak'amai-mai sunansa se ya shigo lecture zai fad'a mana don haka yake yi kafin ya fara darasi"jin-jina kai beauty tayi kamar me wani naxari tana k'ara maimaita sunan a zuciyarta"sir prince"sir prince" ina kuwa na tab'a jin sunan nan a baya?ina ne kuwa?kai bazan iya tunawa ba"may be ma shima na harka ne ban sani ba" Ganin yadda ta duk'ufa da tunani ne yasa meenu ya d'an buga kujeranta yace zan iya tafiya ko?firgigit ta jiyo tana fadin yes meenu zaka iya tafiya nima ai yanxu xan shigo ka samamin seat kusa da kai bara naje na siyo orbit chewing gum a caferia"toh kawai ya amsa ta ya fice a motan ita ko ta tada mota ta nufi caferia" A wani k'aramin kanti ta siyo shi tana k'okarin kunna mota kenan ta bar wajen taji ance adawo lapiya?saurin juyawa tqi taga wanda ke mata magana"murmushi ta saki ganin sir Mutallab tsaye a gefen motan ta"wanda yake d'aya daga cikin malaman department d'insu kuma na hannun dama a wajenta dan kuwa lokaci-xuwa lokaci sukan had'u" dole ta fito suka tsaya nan fa hira ta b'arke tsakaninsu har beauty ta manta da wani abu wai shi lecture! . Kimanin minti 30 beauty na tsaye da sir mutallab suna hira can ya nisa yace au kin ga kin sha'afantar da ni da dad'ad'an kalamanki ko? gashi kinsa nayi late a lecture da zan gabatar"sai a lokacin beauty ta tuna da ashe itama fa tana da lecture dole sukai sallama a gurguje ta hau mota ta nufi venue "wayam kake ganin wajen nan ba alamar mutane kowa ya shiga ciki hakan ya tabbatar mata da an fara lecture"motar xee-xee ta hango can gefe guda, haka ga kuma wasu motoci nan sunyi jeri a gefe d'aya"tsakiyar cikinsu inda yayi dai-dai da wata mota ash colour tasha wanki nan ta aje motan nata ta d'akko jakanta ta fito" A bud'e ta samu k'ofan hakan yasa ta tura kai ciki ta shige" Juye ta riske shi ya maida kai ga allo yana ta xuba uban rubuta d'alibai na kwafa"don haka bata jira wata-wata ba ta shiga taku cikin gadara ji kake kwas-kwas takalmi na k'ara"markern dake rik'e a hannunsa sir prince ya tsayar da rubutun tare da juyowa yana kallon ikon Allah"inda tuni hankalin beauty ita ko yayi nisa a neman meenu se can ta hangoshi saman theater ga wata mace a gefensa"sauri beauty ta shiga yi don taje tai mata masifa na ta zauna mata a waje"kamar daga sama taji ance"hey lady where are u going there?ba tamabayar ce ta bata mamaki ba sai dai muryar wanda ta ji"don tabbas ko a mafarki taji wannan voice d'in xata gane shi bare a fili"juyowa tai don k'ara gaskata abinda taji"kwatsam sukai ido hud'u da prince"kusan mutuwar tsaye tayi a gun shiko me zai yi prince in ba k'ara had'e fuska ba ya k'ara jefo mata wata tambayar"tell me about your wristwatch?banbara kwai taji tambayar aiko me xatai in ba k'udurta raina masa hankali ba nan ta gyara tsayuwarta sosai ta kai dubanta ga agogon dake sak'ale a hannunta ta shiga magana cikin izzah"wow my wristwatch ix unique and fashionable"as u guys normally call it one in town"& i'm quite sure small money inside a small pocket can't afford to handle it"tana kaiwa nan ta d'ago kai cike da murmushi saman fuskarta tana dubansa"me yarinyar nan take nufi ni talaka ne kome?wato ina tambayar ta lokaci shine zata juya min da haka aiko zata ga dixgi"xancen da prince ke nanata wa kenan arai"ganin yadda aji kowa ke jiran jin me xai ce ma ta"nan ya k'ara matse fuska tamau kamar be tab'a dariya ba sai kuma ya d'an saki murmushi na gefen fuska ya shiga kad'a marker dake dauke a hannunsa yana fad'in alright class let us solve a small work here before moving to our main topic of discussion"ido kowa ya bishi dashi ana kallon ikon Allah"a inda prince ya koma gefe da rubutun shi na farko yayi wani k'aramin arithmetic yace waze iya min solving"wani d'alibi a gaban seat ya d'aga hannu yace sir let me try"prince yace ok come and try"haka d'alibin ya taso ya karb'i markern a hannunsa ya shiga solving"bai d'auki wani lokaci sosai ba sai gashi ya gama ya fitar da amsa da yake d'alibin shi ke d'aukar overall a class din"yace sir na gama"duban board d'in prince yayi a nutse yaga tabbas abinda yake so ya gani yaron ya rubuta"nan yace ko zakai min bayanin yadda akai ka samo amsar"tiryan-tiryan d'alibin yayi bayani abin yayi matuk'ar burge prince nan ya kallo class yace alright class kun gane me yayi ko?class kowa ya d'auka da yes sir"in banda wata matashiya dake gefen dama gareshi wacce ta amsa da no sir"dama abinda yayi tsammani za'a samu me fad'a kenan dan yasamu yayi nasa bayanin nan kuwa ya kallo ta cike da samun karsashi a jiki yace ok lady let me repeat it clearly"gaban allo ya koma ya shiga nunawa yana bayani daya ke quadratic equation ne sai da ya gama bayani tsaf sai yace mata ko kinsan dalilin da yasa x=0 & y=10 nan ma dai ta kara bashi ansa da no sir sai yace toh bara nai miki example da hausa yadda xaki gane sauran aji ma su k'ara fahimta sosai dan nasan akwai wanda ko an bud'e brain d'insu an zuba karatu kan bazai d'auka ba" - ISMAIL SANI
Tuesday, 26 December 2017
Home »
'Yar Jami'a Complete
» 'Yar Jami'a Part 3 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI
0 comments:
Post a Comment