'YAR JAMI'A Part 004 .
kallo ya k'ara kai wa sir prince ga sauran d'alibai dake zaune suna jiran cewarsa cikin sarrafaffiyar muryar nan tasa mai cike da kwarjini had'i da izzah haka ya fara magana" Hak'ik'a nin gaskiya ba ya cikin tsarin karatuna yin bayani da hausa don ya zama dole ne shiyasa yau zan mu ku,kun fahimce ni ko?sauran aji suka amsa da yes sir,sannan yaci gaba da magana"yana kai nuni da hannu izuwa ga allo"a duk lokacin da ku ka tashi lissafin irin wannan aiki toh ku d'auki x amatsayin mace mara kamun kai, ita kuma y amatsayin mace mai kamun kai"a yayin da x mara kamun kai ta gama zagayen ta na duniya zakuga ta tara kud'i masu d'umbin yawa (anan yayi nuni ga inda x ta samu maki100 a yanda calculation d'in ya nuna) ,har ta dunga jin cewa kamar ta fi kowa kud'i jama'ar gari kuma suyi ta bibiyarta don neman abun hannunta,har ta kai wata rana kwatsam sai a wayi gari wannan kud'in nata ya k'are a lokacin da zaton mutane bai kai ga haka ba"nan ya sauke hannunsa a inda rubutu ya nuna=0, ita kuma y mai kamun kai za kuga tana ta faman wahala a duniya( ya saita inda aka rubuta y=0) jama'a ko ta kanta basa bi don a tsammaninsu sam babu wata daraja a tattare da ita har sai an cimma gab'ar da zatai arziki alokacin ne jama'a zaka ji suna yabo gareta na k'iddige muku sai ta kai ta kawo wannan x d"in na bibiyar y don samun dacewar rayuwa"don haka jama'a wannan labari dai na san kun fahimce shi don nai muku shi dalla-dalla"bai kai ga rufe baki ba waje gaba d'aya ya d'auka da tafi ji kake raf-raf had'i da ihu kai har da shewa na jama'a,kowa na tofa albarkacin bakinsa akan wannan labari,beauty dake tsaye gaban desk k'afafunta sun kasa rik'eta ga wani matsanancin sarawa da take ji kan ta ya fara duk don wannan d'an iskan labarin da sir prince ya bayar ta san ba makawa labarin nan da ita yake"ganin tsayuwar baza tai mata ba ne yasa ta fara takawa a hankali tana dafe kai kamar wata 'yar giya ta nufo k'ofa dan barin theater d'in,tana takowa dai-dqi da inda yake tsaye nan ta d'ago fuska cikin zafin nama ta shiga k'ok'arin yin magana amma ta kasa sakamakon rad'ad'in da kanta ke mata"saurin duk'ar da kanta k'asa tayi sai ji tai kamar daga sama yana fad'in pls among u ladies someone should help her out kafin ta fad'i anan may be cough syrup ne ya fara mata aiki,ai ko kamar jira suke class suka d'orar da wani sabon ihun kafin kace me wajen ya karad'e da hayaniya,xee-xee da ke can saman theater cikin sauri tai k'arfin halin tasowa ta nufo wajenta nan ta rik'eta adaddafe har wajen mota, bud'e motar xee'xee tayi ta sanya ta ciki tana mai cewa zaki iya tuk'in ko kuwa?hannu beauty ta d'aga mata kawai da alamun ta bar ta haka ta koma ciki"ba dan taso ba haka xee'xee ta barta xuwa ciki don tasan halin beauty indai ta kafe a abu to abarta kawai" . Tunani sosai su kai ta ziyartar beauty ta sak'a wannan ta kunce wancan duniyar duk ta gama yi mata zafi,sam ta rasa me ke mata dad'i a duniyar nan ace wai yau har ita jama'a zasuyi ma ihu duk shaharar da tayi a haka zai k'are inaaa wallahi da sake hakan bazai tab'a faruwa da ni ba"duka takai wa sityarin motar tata da hannu kafin ta kunna motar cikin b'acin rai ta nufi gate ta bar makarantar!Bayan kimanin awa biyu da faruwar hakan ne sauran d'alibai suka fara tururuwar fitowa bayan da sir prince ya rufe karatunsa na ranar inda kowa ka ganshi labarin nan dai d'aya shi ake nanatawa na dizgin da akai wa 'yar jami'a da sanyin safiyar yau, shi ko prince wani dad'i ne ya lullub'e shi tun bayan fitar beauty daga theater d'in yasan ko ba komai yau burinsa ya fara cika akanta! . Horn! Take ta faman yi amma ba taga alamar mutum a wajen ba"fitowa tai ta nufo gate d'in ta bude k'aramar k'ofar ta shige ciki tabar motar a nan waje,d'akin baba mai gadi ta nufa nan ta shiga yaye labulen k'ofar!me beauty zata gani? baba ne kwance saman tabarma sai faman gurnanin bacci yake abinsa daga gani kasan baccin nasa yayi nisa"dube-dube ta soma yi can ta hango buta a kusruwar d'akin,da saurinta ta k'ara sa wajen ta janyota,ruwa ne cike cikinta haka ta nufo baba"shaaaaaa kake ji ruwa na malala saman fuskarsa"firgigit baba mai gadi yayi ya mike zaune yana nanata kalmar shahada"cilli beauty tai da butar gefe sannan ta fice a d'akin tana gungunin cewa gobe ma ka sake baccin rana mu gani"bai iya cewa komai ba baba mai gadi illah cire kayan nasa ya sauya da wasu! K'ofar falo ta murd'a a zuciye ta shiga da mamakinta sai ji tai an fincikota da k'arfi k'asa ta fad'i saman kafet ta inda ake shiga bata nan ake fita ba saukar duka take ji ta ko ina"kuka beauty ta shiga rerawa tun kana iya jin k'arar sautin kukan har ta daina"sosai ummah ta farfasa mata jiki"tana fad'in sakaryar banza da wofi,uban wa zaki kawowa raini a gidan nan? ko dan kinga ana zuba miki ido shiyasa ko?toh wallahi baki isa ba,baxaki sanadin shigata wuta ba,dan nasan alhakin tarbiyyarki na hannuna,bakya ganin kowa da gashi se ubanki ko?shi baba mai gadi sa'an ki ne?toh bari kiji daga yau har ran da uban naki zai dawo shima ya same ni duk na tanadar muku sai dai ki silar mutuwar aurena,amma tabbas ko kin k'i ko kin so sai ki kyaru"shasharar kawai"maganganun da ummah ke yi kenan tana ta haki inda su ko masu aiki ke zagaye da ita sai bata hak'uri suke"sam ummah bata bi ta kansu ba har sai da tayi dukkan don kanta ta gaji ta haye sama ta barsu anan,carko-carko sukai gaban beauty don ba damar lallashi"don sarai sunsan halin ta yanzu ta huce akansu" Kuka beauty take yi wi-wi kamar an aiko mata da mutuwa haka tai mai isarta tayi shiru dan kanta,ko da ta tsagaita da kukan sai ta mik'e don falon shiru kake ji su kan su ma'aikatan sun koma bakin aikinsu,ta nufi sama,d'akinta ta bud'e ta shige"bata zame ko ina ba sai saman gado"ta fad'a nan ta ci gaba da kukanta har bacci yayi awon gaba da ita!can cikin bacci ta ji kamar ana tashinta"k'ara gyara kwanciyarta tayi sai taji an kai mata duka a k'afa cikin sauri ta bud'e ido"nan sukai ido hud'u da ummah"ina mukullin motarki?tambayar da ummah ta fara mata dashi ke nan" murya can ciki-ciki beauty ke fad'ar yana cikin motar"bata tanka ta ba ummah daga jin haka tayi waje"beauty na nan kwance ta ji alamar bud'ewar gate tare da shigowar mota"wanda hakan ya tabbatar mata da akwai abinda ummah ta shirya da hakan!duk da ciwo ga rad'ad'i da jikinta ke mata haka ta k'ok'arta ta mik'e ta shiga bayi tayo wanka" bayan ta fito tana zaune gaban mirrow tunani ya fad'o mata na jakarta da wayoyinta da ta bari a cikin mota"haka tai sauri-sauri ta shirya ta nufi hanyar fita daga d'akin har ta isa falo kenan tunaninta ya kai ga mukullin motar"jim beauty ta yi na wasu 'yan dak'ik'a kafin tayi k'arfn halin koma wa sama ta doshi sashen ummah!k'ofar d'akin ta murd'a a hankali ta shiga da sallamarta"ummah ta amsata kai duk'e ga wata jarida dake hannunta"hajara lafiya dai ko?ummah tace"cike da tsoro beauty ta amsata eh dama umma key na motana ina son d'aukar kayana aciki? Daga jin haka ummah ta d'ago ka tana dubanta tace Key na mota kuma?da munyi dake zan dawo miki da shi ne da har zaki biyo ni d'aki?shiru beauty tai cike da mamaki ta na jin ummah inda taci gaba da magana"eyyeh tambayar ki nake?toh wai da wace tsiyar kika aje a motar in banda wayoyinki da jaka?sukansu na karb'e ran da duk kikai hankali na baki"sannan kuma kina jina ko daga rana irin ta yau kar na sake ganin kin bai wa maaikata wanki sunyi miki"tunda kema macece kamae kowa dole ki koyi wanki don gidan wani zaki"kina jina ko?ido cike da hawaye beauty ta d'ago kai tana gyadawa da zummar ehh!k'ok'arin barin wajen beauty tayi ummah ta kira sunanta ta juyo"ina zaki kuma?ai ban gama da ke ba"don na fahimci zaman kad'aici ke saki koyon wasu munanan d'abi'un dan haka wuce can ga wuri ki zauna'tai mata nuni da kujera"jiki na kyarma haka beauty ta shigo d'akin ta nufi kujerar da ummah tai mata nuna ta zauna! . Tun bayan fitowar sameer daga jami'a bai zame ko ina ba sai gidansu abokin nasa ameenu"kamar yadda ya saba"yau ma dai zaune ya tarar da ameenu rik'e da jarida yana bibiyar kanun labaran ciki"cike da farin ciki d'auke saman fuskarsa ya nufo shi"daga sallamarsa kad'ai zaka ji ka tabbatar da yanayin da yake ciki mai dad'i ne"ameenu ne ya katse shi da tambaya"gaskiya yau dai prince akwai magana bakinka ko? Murmushi sameer ya saki tare da jinjina kai da zummar haka ne kafin ya samu waje ya zauna ya maido kallonsa ga ameenu yana fad'in wato yau na ga ribar hak'uri"ribar hak'uri?na me kuma?ameenu ya tambaya,kasan fa abaya nayi niyyar bin duk wata hanya don naga na kori yarinyar nan a jami'a amma ka hanani toh yanzu maganar da nake yi maka tazo hannu don kuwa ni nake d'aukarsu statistic yau baka ga wulak'ancin da nai mata ba" Baki bud'e cike da mamaki ameenu ke kallon sameer shima dai farin cikin yake da wannan labari na abokin nashi haka sameer ua ci gaba da zayyano masa duk kan abinda ya faru a jami'ar, yinin ranar gaba d'aya anan sameer yayi ta kamar yadda ya saba yi,wanda hirarsu ta yau bata wuce akan beauty bane,bayan sun dawo daga masallaci ne sameer yayi sallama da ameenu akan zai wuce gida har ameenu na tsokanarshi ko dai wajen wata zashi haka ya fake da tafiya gida da wuri don sanin kansa ne kullum basa rabuwa sai 9 koma fiye da haka na dare"haka nan dai su kai sallama shi dai sameer bai biye ta ciwarsa ba" ya nufi gida abinsa" Kamar yadda ya sabayi kullum haka yau ma yayi, yana yin horn d'aya baba mai gadi ya fito ya bud'e masa gate,cike da girmamawa sameer ya gaishe shi kafin ya shigar da kan motarsa zuwa parking space na gidan"jakar aikinsa ya d'akko ya fito aciki ya rufe motar ya shiga waige-waigen gidan don yau ya ga sabon al'amari na rashin tashin kid'a daga sama kamar yadda ya saba ji kullum,se yaji gidan duk ya sauya masa"tambayar ko lafiya yake yi a zuciyarsa amma sanin cewa bazai samu amsar tamabayar tasa bane yasa shi sauke wata guntsuwa ajiyar zuciya tare da fad'in toh Allah yasa dai mutanen gidan yau lafiya suke da haka kuma ya nufi sashensa" Wanka ya fara yi sannan ya d'auro alwala ya fito,nafilfilinsa na dare ya shiga jerawa ba shi ya gama ba sai wajen 10 saura,yana cikin addu'o'i ne yaji wayarsa ta fara k'ara,wanda ko dama abinda yake jira kenan,da saurinsa ya k'arasa ya d'auko wayar ya kara akunne cike da shauk'i yace sweet momy nah"daga d'ayan b'angaren ma aka amsashi da my prince"wani sassanyan murmushi sameer ya saki don ba abinda ya fi so kamar ya ji momy ta kirasa da my prince,cike da kulawa suka gaisa yana ta faman nuna yadda ya ke kewar momyn tasa itama haka don kuwa akwai shak'uwa mai k'arfi a tsakaninsu"bayan sun d'auki tsawon lokaci suna hira ne momy ke tambayar sameer akan lafiyar mutanen gidan"shiru ya biyo baya hakan ya baiwa momy damar sake tambayar nasa"nan ma dai ba amsa,sameer!momy ta kira sunansa"amsata yayi muryan nan k'asa-k'asa,sai tace ko dai ba lafiya bane sameer naji ina ta tambayar ka mutanen gidan amma kayi shiru"daga jin haka sameer bai b'oye wa momy komi ba tsakaninsa da su da mutsnen gidan akan yadda daddy ya hanasa ko da lek'owa harabar gidan "sosai momyn sameer tai mamakin abin don har tana nuna masa ko dai zai samu wani masaukin kawai in nan bai masa ba"nuna mata yayi babu komai zaman nasa da ya kusa zuwa k'arshe ,don a lokacin sameer bai wuce 'yan watanni ya gama bautar k'asarsa ba"ba don ta so hakan ba amma ya zatai da ra'ayin prince dole ta hak'ura ta bishi a haka"sun tab'a hita sosai kafin yayi sallama da ita ya kashe wayar" Kayan bacci ya iya canjawa tare da gyara komai na d'akin yayi tsaf-tsaf don ya zaman to d'abi'a ta sameer kullum kafin ya kwanta sai ya gyara muhallinsa tun agida"bayan da ya gama ne ya rage wutar d'akin tare da bin lafiyar gado!" . na safe sameer tsaye yake gaban motarsa yana k'ok'arin bud'eta ya shiga ya ji kamar daga sama an kira sunansa da alamar manyance,saurin juyowa yayi cike da mamaki ya dawo da dubansa ga inda sautin kiran ke tashi,ido ya kai ga dattijuwar dake tsaye bakin k'ofar sanye cikin dogon hijabinta fari fat, tunani ya fad'o masa kan tabbas ko bai tambaya ba wannan ita ce hajiyar gidan,cikin sauri ya k'arasa har inda take ya russuna yana gaisheta kai a k'asa,sosai ummah ta ji dad'in yadda ya gaisheta'amsashi tayi kafin tai masa nuni daya mik'e tsaye"kasa mik'ewa sameer yayi se ma shiga susa k'eya da yayi yana fad'in ba damuwa hajiya nan ma yayi,murmushi ta k'ara saki wanda ke nuni da farin cikinta gareshi tace dama magana ce zamuyi amma kaje in ka dawo daga aikin sai muyi"toh kawai sameer ya amsata dashi da haka ya mik'e ya nufi mota ita kuma ummah ta shigo ciki" . Da yake daren jiya beauty na tare da ummah don a d'akin ta ma tai bacci sai ya zamana yau tashin wuri tayi,saboda tun kiran sallar farko ummah ta tasheta haka zalika bayan sun idar da sallah ta mik'a mata al'qur'ani nan beauty ta shiga karatun dole ba don taso hakan ba,har wajen shida na safe sannan ta rufe shi ta nufi gado ta kwanta"dawowar ummah cike ne ya batar damar komawa d'akin nata ta tashi beauty da tai d'ai-d'ai saman gado tana bacci"har a sakko daga gadon ba alamar motsi a leb'enta"hakan ya baiwa ummah damar kallonta cike da takaici tace ita addu'ar tashi daga baccin ni zan tofa miki ko kuwa ya akai?cikin mawuyacin yanayi beauty ta ji tambayar"ita mamaki abin ya bata yanzu ace har da wata addu'ar tashi daga bacci"amma gudun fad'an ummah hakan yasa tilas badan taso ba ta hau mutsu-mutsu da bakinta kai kace da gaske adduar take har ta bar d'akin" Ba ita ta gama shirin taba sai kusan tara na safe sai gata ta fito cikin wasu matsatstsun kaya riga da wando wacce rigar bata wuce gwiwa ba"sai wani yalelan gyale da ta rufe kanta dashi wanda dashi da babu duk d'aya ne"ko takan breakfast bata bi ba don yanzu duk abinda zau had'ata da ummah bata so don ko jakar makarantar yau wata sabuwar ta d'akko,sand'a ta shiga yi a hankali har ta sakko daga sama ta kai bakin k'ofar fita daga falo kenan ta tuna da key na motar da ke wajen ummah"dafe kai beauty tai kamar zatai kuka don takaici amma ya ta iya dole hakan zata koma"kallo ta fara kaiwa ga suturar dake jikinta tasan tabbas ta je wa ummah da wannan shigar baza su rabu ta dad'in rai ba"shiru tayi kamar me nazarin wani abu se can dabara ta fad'o mata"yes!yes ta fad'a cike da murna cikin sauri ta haye sama ta nufi sashenta" drawer d'in ta na kaya ta bud'e ta shiga lalube"tsohuwar ajiyar da tafi shekara uku a ajiye ta janyo wani dogon hijab da tun zuwan daddy dubai ya siyo mata akan tana sallah dashi ta d'akko cikin murna da wannan shawara data samo ta saka shi cike da yiwa kanta dariyar abinda tayi ta nufi wajen ummah!! . Beauty cikin nutsuwa ta tura k'ofar d'akin ummah ta shigo,zaune ta tarar da ita saman kujera hannunta rik'e da remote tana k'ok'arin sanya channel d'in MBC 4,ciki-ciki kamar mai koyon magana beauty ta shiga tambayanta key,banza tai da ita kamar ummah bata san da mutum a wajen ba har sai da beauty ta k'ara nanatawa sannan ta d'ago fuska a dak'ile ta k'are mata kallo tas,tai mamakin yadda taga shigar 'yarta ta yau amma a hakan ta cije ta b'oye narkakken farin cikin dake kwance saman zuciyarta na ganinta haka, tace gashi can saman madubi wuce ki d'auka,gefe kuma ga wayar ki can ki d'auki babbar ki anfani da ita kuma da zarar kin dawo ki maido min key d'in nan!toh kawai beauty ta iya cewa jiki na rawa ta d'akko su ta fito had'i da janyo mata k'ofa ta rufo,tana fad'in yes!yes!!cike da murna beauty ta sakko ta nufo waje!A gaban motar beauty ta cire hijab d'in ta bud'e ta wullashi ciki,kallon motar ta sake yi,sosai motar tayi kyau yadda taga an wanke ta sosai ta fita"haka ta shiga yau kam ba yabo ba fallasa gaisawarsu da baba mai gadi bayan sallamar kullum ta kud'i da tai masa"ta wuce abinta sai makaranta"! . Da yake batayi wani breakfast ba ta fito dole tana shigowa ciki ta wuce STOP & CHOP,shiru wajen yau yake tunda safiya ce sai ma'aikata da suke ta faman kai kawo suna gyaran wajen"da shigarta kowa ya yo kanta suna kwasar gaisuwa,meenu kamar yadda take kiran yaron nata na wajen haka ta kirashi bayan ta zauna ta zayyana masa abinda take buk'ata ba'a d'auki wani lokaci mai tsawo ba sai ga shi ya dawo cike da kayan abinci da na sha haka ya jere mata su gabanta beauty ta shiga ci hankali a kwance"bayan data gama ne tana k'ok'arin fita daga wajen bayan da su kai mata total na duk abincin da su kai na ranar ta biya su kud'in da zummar ayi yadda aka saba na raba wa d'alibai da sunanta"wasu mata ta gani su hud'u kana ganinsu kaga rik'ank'un mata masu zaman kansu"don lalatattun shigar dake jikinsu kad'ai ya gama fassarasu"takowa su kai suka shigo har gaban beauty sannan ko wacce ta ja kujera ta zauna"! *'Yar Jami'a*!!sunan da d'aya daga cikin matasan kenan ta kira beauty dashi wanda hakan ke nuna itace gaba da su" Ya mutse fuska beauty tayi tana kallonta kafin ta amsa mata da lafiya dai ko?ki ke kiran sunana da sanyin safiyar nan?? K'ara gyara zama sosai matashiyar tayi saman kujerar ta fuskanto beauty sosai sannan ta hau magana" A gaskiya wato kin gane kina d'aya daga cikin matan da muke yawan jin labaranki daga maza kai har da mata na jam'ar nan akan yadda kike rayuwarki cikin jin dad'i da gogewa"sai muka ga abin ya burge mu shine muka yi tattakihar cikin makarantar nan don samun damar ganinki,amma ko da muka nemeki sai aka shaida mana baki shigo ba sai dai aka nuna mana aminiyarki"ita ta shaida mana kina nan"toh agaskiya dai 'yar jami'a duk da ban san ya zaki karb'i abun ba amma mun zo miki ne da tayin wani babban rabo"wanda muke ganin zaki iya"wannan abin ba komai bane illah muna so ki shigo cikin k'ungiyarmu wanda take da reshe da yawa a sassan jahar nan,muna so ki zama cikin ta biyar agaremu,kinga taron sati da za'ai a gidan uwar d'aki sai mu gabatar dake"yanzu dai tare dani wannan ta hannun damar tawa sunanta nusaiba amma anfi kiranta da nusy,wannan kuwa ta gefen hagun sunanta shamsiyya wato shamsy kenan!sai kuma ta gefenta surayya ko kice sury daga haka sai ni mai gayya mai aiki miss lollipop wato lawiza"bata kai ga aje numfashinta ba lawiza kamar yadda ta fad'i sunanta beauty ta katse mata hanzari da hannu tana fad'in toh kin gama?caraf sury ta amshe maganar don taga kamar beauty baza tai na'am da buk'atar su ba"tace ehmm kina jiko 'yar jami'a ba wai muna nufin da ordinary men fa zaki na harka ba nooo!ba haka bane manyan Alhazawan k'asar nan ba ma jaha ba duk namu ne sai wanda kika zab'a in ma kince ba da maza zaki harka ba, suma matan akwai su kala-kala(wa'iyazubillah)sai kin zab'a kin darje,ta k'arashe maganar surry tana wani kashe wa beauty ido d'aya!kafin beauty ta samu damar yin magana har shamsy dake can gefe ta ciro wani k'aramin kati mai d'auke da suna har da lambobin waya ta aje gaban beauty"tace kar ki saurin yanke hukunci ki je ki nazari,wannan lambobin mu ne,don haka sai mun ji daga gareki,muna fatan kuma baza ki bamu kunya ba!mik'ewa sukai a tare suka fice"ido kad'ai beauty ta iya binsu dashi wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta"yanda beauty ke ta faman had'a zufa ze tabbatar maka da shigar sabon abu cikin kwakwalwarta"a sannu ta kai hannu kan katin ta d'akko shi a hankali ta shiga juyasa a hannu!toh wad'annan mutanen me suke nufi da hakan? Na fara mu'a mala da wasu mazaje a waje ko me??? Wannan itace tamabayar da take ta faman kaikawo a kan beauty! . Cike da matsananciyar damuwa d'auke saman fuskar beauty haka ta daddafa ta fito daga cikin stop & chop sallamar da take musu in zata fita yau ko ita basu samu ba"mota ta nufa ta zauna tare da d'aura kanta saman sityarin motar"muna fatan kuma bazaki bamu kunya ba?"wannan maganar ta shamsy itace take ta faman kai komo a zuciyar beauty"A zahirin gaskiya bazan so ni kai na na baku kunya ba,kuma bazan so wannan damar ta wuce ni ba ta k'ara shiga cikin wasu wayayyun mutanen"toh amma ai babu wannan tsarin a cikin file d'ina hasali ma ban tsara wannan rayuwar ta zama abin dawwama a gareni ba,sai gashi yau kwatsam kun shigo min rayuwa da wani sabon abu mara misaltuwa"yanzu meye mafita???yanda ta lula kogon tunani beauty ba kama hannun yaro,fahimtar daga k'arshe baza ta samu wata mafita bane yasanya ta dole ta hak'ura akan in ta koma gida ta yanke shawara".motar ta kunna tare da sakin sauti ta nufi lecture hall d'insu na ranar"duk da an kusa cimma k'arshe lecturen haka beauty ta banka musu ciki tsagal-tsagal ba ko kunyar suturar jikinta,kallo ta kai ga lecturern da yake tsaye rik'e da wata k'aramar takadda a hannunsa yana bayani tace morning sir,tana maganar ne a sa'ilin da duk wata gab'a ta jikinta ke motsi"tana wani kwarkwasa kamar mai shirin b'allewa"washe baki lecturern ya shiga yi da ganinta tuni ya taho yana mai laluben biro a aljihunsa yace ina kika shiga tun d'azu 'yar albarka gashi har anyi attendance?abinci naje ci! Ok toh ai ba damuwa dama shi gane karatu ai sai ciki ya k'oshi maza amshi sa sunanki daga k'asa!ba musu beauty ta k'arba ta rattaba sunanta ta mik'a masa tare da sakar masa wata kasalalliyar dariya tace"thank you sir,gaba d'aya theater tayi tsit ko wane d'alibi da d'aliba zaune suke suna kallon ikon Allah,ace duk irin zafi na malamin nan da rashin yarda a shigo masa bayan ya shigo yau shi har yake lallab'a wata"a gaskiya 'yar jami'a ta cika shu'umar kanta!cike da fara'arta ta mik'a masa takardar had'e da bironsa ta haye sama"har tayi kamar zata shige can sama sosai ta hango mace da hijabi gefenta babu kowa!da saurinta ta k'arasa wajen ta zauna"satar kallon yarinyar dake zaune gefenta tayi"ta tabbatar da farin hijabin dake sanye jikinta"leb'enta na sama ta shiga ciza da hak'oranta kafin ta janyo wayarta daga jaka ta shiga wajen aika sak'o" I need red pen!! Sak'on da ta rubuta kenan tare da lalubo lambar xee-xee ta aika mata" . Xee-xee na zaune taji alamar shigowar sak'o da kamar baza ta d'auka ba don tasan halin MTN da turo sak'o kamar ka sa su!can kuma wata zuciyar ta bata ta duba haka ta bud'e ta karanta"cikin ikon Allah kuwa tana da shi haka ta nad'e jan biro a tissue ta bayar ma ta gefenta ta mik'a wa beauty!murmushi ta saki bayan ta amsa!taci gaba da latsa waya abinta tana game yayinda ko wane d'alibi yayi nisa cikin rubutu saboda dictation yake musu"lura da shagaltuwa da su kai hakan ya baiwa beauty damar d'akko biron nan a hankali ta bude shi,nan ta shiga hura ink d'in biron a hankali yana d'iga jikin tissue d'in har ya k'are"haka ta kaikaici idon mutane ta wullar ya zama saura tissue hannunta"hannu ta zura ta baya ta dai-daici k'asan farar hijab d'in baiwar Allah nan ta shiga goga mata shi a hankali,sai da ta tabbatar da gaba d'aya k'asan hijabin ya gama b'aci da jan biro sannan ta dawo da hannunta a hankali ciki ta cukuikuya tissue d'in ta wullar k'asan seat! Karatu ake sosai ba alamar shirin tashi gashi duk ta k'agu tabar wajen dole ta d'aga hannu tace excuse me sir!"kamar jira yake daga can k'asa inda yake tsaye yana koyarwa yace yes go ahead!narkar da murya beauty tayi"duk wani kalar tausayi ya bayyana fuskarta tace"ciwon kai nane ya tashi please sir kai min izini wannan baiwar Allah ta rakani zuwa mota na tafi gida bazan iya zuwa ni kad'ai ba"cikin hard'ewar murya yake amsata da toh kuje ai ba komai Allah ya k'ara lafiya! . Badan ta so ba haka d'alibar ta kama beauty dake dafe da kai tana cuskune fuska ita ala dole mara lafiya!da taimakonta haka suka shiga sauka daga matattakalar wajen suka nufo k'asa!huuuuuuu huuu!!! Shewar maza kenan da kake ji tana tasowa daga can saman theater! Kafin kace tak gaba d'aya wajen ya cike da hayaniya"tun lecturern yana buga tebur d'in gabansa yana tsawatar musu har ya kai ga abin ya k'ufular da shi,yayi shiru ya zuba wa sarautar Allah ido,har beauty suka cimma bakin k'ofar fita gaba d'aya hankalin d'alibar bai kai akan su ake wa dariya ba,sai da suka k'araso kofa sai karaf idon lecturern nan ya kai ga hijabin jikin d'alibar yaga duk ya gama b'aci da jini wannan ne ya k'ara tabbatar dashi cewa shine abinda yasa mazan nan dariya"duk sai yaji wani iri don ganin kamilar mace abu irin wannan ya sameta a bainar jama'a!gashi d'aliban mata suna son sanar da ita amma babu hali sakamakon d'abi'ar lecturern da indai an fita toh babu dawowa ciki"dole yasa suka hak'ura,amma abin suma bai musu dad'i ba don ciwon mace na 'ya mace ne" . Cika min jiki dilla shashasha"!abinda ya fito kenan daga bakin beauty inda a lokaci guda kuma take k'ok'arin raba jikinta dana d'alibar"cikin rashin fahimta d'alibar ke kallonta don ko ba komai ai ta gode mata da taimakon da tai mata bata saka mata da zagi ba"kafin ta kai k'arshen tunanin nata taji an finciko ta da karfi har tana kai tuntub'e kan k'aramin dutsen dake gabanta,beauty ta shiga jijjiga mata dogon hijabin dake jikinta tana fad'in!ustazu uwar imani!kina gaba maza na bin ki a baya suna yabo!wai ke 'yar gidan malam me dogon carbi ko? Toh yau naga abin so a jikinki,ko an gaya miki ana ja da 'yar jami'a da zaki saka malami ya wulak'anta ni gaban aji wancan satin wai har kina ikirarin baki gane calculation d'in kan allo ba ko?toh tunda baki gane wancan ba ai nasan zaki gane wanda ke bayan hijab d'in ki ko?tana kaiwa nan beauty ta cika mata hijabin nata ta bita da wani banzan kallo!mai cike da jin dad'i"duk da har yanzu d'alibar bata gama fahimtar kalaman beauty ba amma jin ta ambaci hijabi, haka ya baya damar shiga laluben jikinta cikin sauri, gaban hijab d'in ta fara kaima kallo taga tsaf yake hakan yasa ta juya bayansa! Kasa yarda da abinda idanunta suka nuna mata tayi!jan abu ta gani gaba d'aya ya gama b'ata mata farar hijab d'inta"bata ankara ba taji kamar daga sama ana magana!hak'ik'a wannan shine sakayyar duk wanda yace zai shiga harkata"yanzu kinga sai ki koma cikin theater maza su ci gaba da miki dariya ko kuma ki nufi toilet kafin ki je can kuma mazan makaranta sun gama shan kallo"sai ki zab'i d'aya" Cike da muguwar dariya beauty ta k'arashe maganar tana watsa hannaye sama ta wuce zuwa motarta! Wasu irin zafafan hawaye ne suka fara kwaranya a fuskar d'alibar wanda ita kanta ta rasa dalilin hakan"durk'ushewa tai k'asa ta shiga rera wani sabon kuka tana tariyo abinda ya faru yanzu na yadda maza ke shewa suna ihu da ganinta haka!yanzu ina zata?tunanin daya fara kawo mata kenan,ta jima tana tunanin mafita sai kuma can dabarar kama wajen ta rike da hannu ta yadda zai b'oye jan dake wajen ya zo mata"haka kuwa akayi ta kama bayan hijab ta rik'e ra nufi bayi ta cire sannan ta nemi taimakon wata d'aliba data shiga masallaci ta d'akko mata hijab dake rataye na sallah ta saka"bayan data gama gyara jikin tane batai wata-wata ba ta fice daga jami'ar duk wani karatunta na ranar haka ta . _Luv is so sweet when u meet the right person to show it out yeeeee! Oh yeeee!_ . Wak'ar da beauty ke rerawa hankali kwance kenan cikin mota,hannu ta kai ga jakarta ta zaro wani k'aramin dairy nata,wani shafi mai cike da Manyan rubuta ta bud'e nan da nan ta kai hannunta ga wata da'ira da akai a wani k'aramin akwati da aka zana tayi tick aciki!alamun yiyuwa na cimma wani abu!bayan da ta gama ne ta kalli agogon hannunta taga har lokacin 12:00p.m ba tayi ba!Tsaki ta saki had'i da kunna motar tata, ta sureta da gudu kamar mai shirin tashi sama tai hanyar fita daga jami'ar!anan ne ta gamu da wani malami wanda ya d'auke su a zangon karatunsu na farko,wanda shima ba laifi d'an harka ne don ko ba komai ya bata marking da ta gamsu dashi"hakan yasa ya haska mata fitila itama ta haska masa na alamun dakatawa"waje ya samu gefe yayi parking itama ta samu tayi sannan ta fito tayo wajensa"da yake motar tasa itama bak'in gilashi ne haka ya bud'e mata motar ta shige ciki ta zauna!gaisawa sukayi tare da maida bayan saduwa"sun d'au lokaci mai tsawo suna hira abinsa kai kace don ita ya shigo"daga bisani ta nemi tafiya amma sam yak'i bari ta tafi,sai ma shiga bata wasu labaran yayi masu matuk'ar tasiri a zuk'ata" kwan! kwan! kwan!k'arar bugun gilas kenan suka ji daga b'angarensa,ba tare da nuna alamar damuwa ba"ya kalle ta ya sakar mata wani kasalallen murmushi itama ta watso masa sannan ya iya sauke gilas d'in motar k'asa". Baki bud'e har kana iya hakaito hasken fararen hak'oransa ya ji ance c'mon! malam bani laptop d'ina da aikin da zanyi da ita ka barni ina jira ka taho nan wajen......kalaman sameer kenan wanda bai kai ga k'arashe su ba idanunsa suka sauka ga macen dake gefen kujera zaune,wanda itama dai daga b'angaren nata shi take kallo"dimmm lokaci guda suka ji wani irin matsananciyar bugawar zuciya"kasa danne yanayin da yake ciki sameer yayi dole ya katse maganarsa ta farko ya fito da yatsa waje ya shiga nuna beauty yana fad'in"me wannan yarinyar take maka a mota kamal?d'auke da wata siririyar dariya saman fuskarsa malamin wanda aka kira da kamal ya kai duba a karo na biyu ga beauty kafin ya juyi gareshi yace wai wannan?ehhh ita!!sameer ya bashi amsa a tak'aice"ko da yake ka gane ba na buk'atar ma na sani don nasan abinda ya kori shaho daga shek'a bazai wuce yunwa ba!bani laptop d'ina na wuce"cikin fushi kake jin zafafan kalaman sameer na tashi!da yake yasan halin mutumin nasa kamal don ko suna office wani lokacin in ya d'au zafi ba mai iya masa sai in don kansa ya saki!haka ya mik'a hannu kujerar baya na motar ya janyo jakar laptop d'in ba uhmm balle um'um ya mik'a masa"karb'a sameer yayi duk da haka cikin fushi ya sunkuyo da kai cikin glass d'in yana kallonta yace wallahi i hate u to the extend level baki da hali,baki da hali banza mara kamun kai"!bai jira cewar su ba ya sa kai yayi gaba" . kamar a mafarki haka beauty ke jin kalaman sameer na dokar kunnuwanta"duk wasu k'ofofin tunaninta sun riga sun kulle ruf,k'afe ido tai ga sararin wajen da sameer ya bari tamkar mai wani nazari,can kuma sai ji tai ta saki wani irin k'aramin yak'e wanda ya fi kuka ciwo,bata jira jin wani abu daga bakin kamal ba, ta bud'e k'ofar tana shirin fita,cikin sauri kamal ya rik'o hannunta yana fad'in please dear wait ki ji wani abu"cikin zafin nama beauty tai wurgi da hannunsa gefe ta fito da sauri daga motar ta nufo tata"a fusace haka ta fad'a cikin motar kamar wacce hankali yabar jikinta haka ta finciki motar tayi waje! . Zaune yake cikin office d'insu da alama aiki yayi masa yawa yadda ya duk'ufa sosai akan laptop d'insa dake ajiye saman tebur d'in gabansa yaji an turo k'ofa,sam bai damu da sannin wanda ya shigo ba don kuwa su uku ke zaman office d'in,sallama yayi kamal yayi sannan ya shigo ciki,kujerar dake kallon ta sameer ya zauna yana d'an gyad'a k'afa,alamun daya gani daga sameer na bashi da niyyar kulasa ne yasa shi k'ara gyara zamansa yace"amma dai kaji shigowa ta ko?eh kuma na amsa maka sallama ba!sameer yayi maganar kansa na sunkuye a laptop!murmushin k'arfin hali kamal ya saki sannan yaci gaba da maganarsa"wai shin kuwa sameer ina kasan 'yar jami'a naga tun da ka ganta d'azu tare da ni duk ka sauya gashi kamar ni d'in ma fushi kake dani! Banza sameer yayi da shi tamkar bai ji me ya ce ba har na kusan minti uku sannan ya d'ago raunanan idanunsa da tuni sun gama k'ank'ancewa saboda gajiyar aiki ya sauke su saman nashi"malam aiki fa nake ka zo zaka dameni,ina ruwa na da kai da ita,tunda kai ma ka zama mai biye ma shashashan mata ai se kaje kai tayi,kar fa ka manta tare muka zo aikin bautar k'asa jami'ar nan kuma ni baka ga ina biye musu ba toh ni ma kenan dana tashi cikin hausawa,nasan illar abin ina ga kai daka tashi a birnin kudu,ya ci ace yanzu kasan me kake,basai an gaya maka ba,amma fa shawara ce bazan hanaka jin dad'inka ba sai dai ka sani yarinyar dana ganka d'azu da ita tun ran da na fara zuwa jami'ar nan na fara had'uwa da ita duk da bata gane ni a lokacin ba amma ni na ganeta saboda mummunar shigar dake sanye jikinta"don haka ina shawartarka please kaje kai dukkan abinda kake so amma ka rabu da wannan yarinyar wallahi bata da tarbiyya!cikin wani irin mawuyacin hali da yanayi sameer ke magana,kana ganinshi zaka fahimci tabbas duk kan abinda yake magana akanshi ba mai dad'i bane! Ba don kamal ya ji maganar abokin nasa ba amma ya zai yi dole ya nuna masa ya gane komai kuma zai gyara da haka suka rabu kamal ya koma tebur d'insa ya fara aiki shima sameer ya d'ora daga inda ya tsaya! **** Misalin k'arfe hud'u na yamma 4:00p.m, kenan a agogon dake sak'ale a hannun sameer"ajiyar zuciya ya saki lura da yadda lokaci ya tafi haka"kafin daga bisani ya had'a kayansa ya fito,a harabar office d'in nasu yaga an had'a jam'i ana k'ok'ari tada sallah haka ya aje kayansa gefe yabi jam'i sannan ya shigo motarsa ya fito daga jami'ar! Tafiya yake hankali kwance har ya kai ga kwanar da zata sada shi zuwa gidan aminin nasa ameenu kamar yadda ya saba wuce wa can kullum sai kuma dare ya koma gida"maganar ummah ce ta fad'o masa na cewa bayan ya tashi daga aiki zasuyi magana"dole ya juyar da kan motar tasa sanin cewa in bai je lokacin ba dare zai zamanto dare yayi nisa watak'il ma tayi bacci a sa'ilin,haka ya d'auki hanya sai gida! Horn biyu yayi baba mai gadi ya fito don ganin wane ne da mamaki sai yaga motar sameer!har ya bud'e masa gate suka gaisa ya shigo gaba d'aya baba mai gadi mamaki bai sake shi ba!tunani ya shiga yi Allah yasa dai lafiya ya dawo yau da wuri!ko da sameer yayi parking haka ya fito ya k'ara gyara zaman darkblue suit dake sanye jikinsa"sannan ya zura phones nashi a aljihu ya nufi hanyar shiga babban falo! . Assalamu alaikum!Assalamu alaikum! Sallamar da sameer yake yi kenan amma da alama babu motsin kowa a falon"ganin ya d'au lokaci tsaye ya sashi yanke shawarar ya wuce d'akinsa kawai zuwa an jima sai ya dawo"ya yunk'ura kenan zai juya yaji an bud'e k'ofar!dawo da kallonsa yayi wajen,inda hakan yayi dai-dai ga kallon ummah gareshi tace"aufff ashe kai ne? Eh ummah! Ina yini!cike da girmamawa sameer ke gaisheta!haka ummah ta amsa masa da lafiya lau!sannan tayi masa iso da ya k'ara so ciki! Cikin nutsuwa sameer ke bin bayan ummah har suka k'arasa cikin falon, kujera tai masa nuni da ya zauna! K'ara gaisawa sukai kafin ummah ta umarci akawo masa abin tab'a wa baki! Duk da ba wani iya cin komai yayi ba don sameer bai saba da cin abinci gaban mutane ba"in ba dole ba, musamman ma yau da ya kasance gaban ummah!haka ya aje juice cup d'in dake rik'e a hannunsa a centre table"ya d'ago kai yana kallonta da alamar son jin wani abu daga gareta"matsakaicin murmushi ummah ta saki sannan tayi gyaran murya tace! D'azu nace in ka dawo kazo ina nemanka"saboda a ganina yaci ace kawo yanzu nasan da wane irin mutumi muke zaune a cikin gidan nan!jinjina kai sameer yayi da nuna gamsuwa da furucin ummah!sunkuyar da kai k'asa yayi sannan ya fara motsa leb'ensa! . Ni dai sunana.......pinn pinn...k'arar wayar ummah kenan da ta fara ruri a lakacin wanda hakan ya ba sameer damar tsayawa don ta amsa wayar!hannu takai ummah ga wayar dake aje gefenta ta janyota!ta duba sunan wacce ta kira"yagana kuma?ba d'azu muka gama waya ba?ganin kiran yana daf da katsewa yasa ta tayi saurin d'aga kiran ta kara a kunne!k'ara gaisawa su kai amma duk yanayin da ta tsinceta tabbas a lamar tambaya!lafiya dai ko? Jimmm yagana tayi na wasu 'yan lokaci sannan ta nisa tace jikin malam ne ya k'ara tashi yanzu gashi babu wani babba a gida sai ni kad'ai!innalillahi wa innah ilaihirraji'un"toh yanzu yana ina?ummah tayi tambayar,gashi nan a gida na jik'a masa saiwa yasha ya d'an samu bacci!sosai jikin ummah yayi sanyi da jin rashin lafiyar mahaifinta,cikin k'arfin hali tace mata yanzu gashi baya gari kuma waya dashi sai dai cikin dare don aiki yawa yake musu,amma zan gani zuwa anjima duk yanda na yanke zan kira!toh yagana ta amsa dashi kafin nan sukayi sallama t ma kashe wayar! A sulale wayar tabi jikin ummah ta sauka kan cinyarta inda tuni ruwan hawaye ya gama cika idon ummah"damuwa tsagwaronta kake gani d'auke saman fuskarta"yanayin da ta shiga yasa sameer bin ta da kallo a hankali ya iya furta,lafiya dai ko ummah?sam hankalin ummah ya gushe a kanshi har sai da ya k'ara nanatawa,sannan ta juyo guntun hawayen dake mak'ale a fuskarta suka gangaro,a rud'e sameer ke fad'in"subhanallahi dan Allah ummah menene ke faruwa?naga daga d'aukar wayarki haka ta faru ko dai anyi rashi ne,girgiza kanta ummah tayi sannan ta share hawayen nata ta d'ago kai a dak'uke tana kallonsa,can kum tace ba'ai rashi ko d'aya ba sameer k'anwar mahaifiyata ce ta kirani akan rashin lafiyar mahaifina;yanzu haka yana can kwance jikin ya k'ara tashi kuma ba kowa a wajensa sai ita sa yake mahaifiyata ta rasu,kuma dangin namu mazan ba masu d'aukar zumunci da wani abu bane,shiyasa kaga duk na damu,in dama ace daddyn hajara na nan da da sauk'i zan iya tambayarsa gobe na shirya naje,toh baya nan ita kuma waccen shashashar yaushe zan tura ta jinya,ita da ko hankali bata cika ba,!dafe kanta unmah tayi don wani irin sarawa da taji yayi kamar zai bar jikinta hakan yasa sameer saurin fad'in ya isa haka ummah ki daina damuwa kar kema wani abun ya sameki,yanzu shi yana ina da zama?yana nan kano cikin local government d'in minjibir!minjibir?sameer ya nanata sunan wajen,a gaskiya ummah bansan wajen ba amma in bazaki damu ba ni ki wakiltani indai kinga ba wani abu sai naje ni!da sauri ummah ta d'ago kai tana kallonsa!ajiyar zuciya ya sauke yace eh ummah ni zanje in har kin amince min sai ai mun kwatance!toh sameer Kar na takura maka aikin naka fa?haba umma karki damu da wannan zan sanar kuma ko bana nan akwai masu tallafa min don haka ki kwantar da hankalinki,toh shike nan hakan yayi na gode amma kaga da waccen malalaciyar zata iya ai da kun tafi tare tunda ta san wajen ba sai ka wahala ba!yamutsa fuska sameer ya d'an yi jin an ambaci mace yace wace kuma ummah?hajara mana,kai dai Kawai Allah ya sawak'e ma wannan yarinya wallahi ban tab'a ganin mace sakara irin taba duk ubanta ya gama d'aure mata sai yadda take so ina duniya zatayi dad'i a haka?cikin fad'a-fad'a ummah ke maganar!wani dogon gauron numfashi sameer ya sauke lura da yadda ummah ke zayyana halayem yarinyar sak irin na salaha k'anwarsa,toh amma ya akai duk da jarunta da nake ganin yanzu tattare da ummah ta kasa gyara 'yarta?toh yanzu mene abunyi?ko dai na tallafa wa ummah ne tunda ga dama ta samu daddy baya nan? Sameer lafiya dai ko naji kayi shiru haka?jin ya lula wata sabuwar duniyar yana tunani yasa ummah tamabayarsa!cikin jin kunya irin nasu na maza nan ya shiga susa k'eya kamar mara gaskiya sannan yace babu komai ummah amma in babu damuwa sai mu tafi tare da ita kawai yadda nima bazan wahala ba,kuma kinga itama ai taga jikin nasa!sosai hakan yayi wa ummah dad'i nan da nan ta amsa masa da ai kuwa hakan za'ai bara ta tashi daga bacci sai na sanar mata zuwa safe sai d'au hanya"kai Allah dai yayi maka Albarka ashe kai rahama ce a gareni amma k'ememe daddy Ya hanaka shigowa ciki,ai daga yau ka zama d'an gida kuma ana tashi daga aiki ka yo gida nan ne mahallin cinka da shanka,ni na tsaya maka naga kuma wanda zai canja hakan!dariya sameer ya saki na jin dad'in kalaman ummah nan yayi mata godiya da hakan ya kuma nemi izinin wucewa sashensa,ba musu ta yarje masa har da kiran ma'aikata da'a mik'a masa abinci sashensa! - ISMAI SANI
Saturday, 30 December 2017
Home »
'Yar Jami'a Complete
» 'Yar Jami'a Part 4 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI
0 comments:
Post a Comment