Monday, 4 December 2017

'Ya 'Ya Mata Page 14 karshe Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

YAYA MATA part 14
******* KARSHE ********
.
Don haka yanzu suma suna da dan abin hannun su Bayan wata uku kuwa adda fauzy ta sintilo danta santalele kyakykyawa, ta haihu kuwa da kwana biyu momy matar ya amadu itama ta haifi danta namiji itama kyakykyawa mai kama da uban sa sakk Tunda akayi haihuwar ni da hafsy muka koma gidan adda fauzy da zama acen muke kwana, ladidi kuwa ita tazo ta zaunawa adda fauzy, ammi kuma ita kewa momy wankan jego, haka dai suka raba abun sun Suna saura kwana biyu su adda mrym, adda hamdy da adda juw suka zo, munyi murnan ganin juna sosae, haka suka rikowa da ammi da kayan arziki sukazo mata da shi, har da su lami ba'a barsu abaya ba, don kuwa kayan fitan sunan kaff adda mrym ce ta musu, lami har da kuka don dadi, sukayita godiya suna saka mana Albarka Ranar suna kuwa yaro yaci sunan mai gari wato Ibrahim ana ce mai abba, munsha shagalin suna abin mu Anyi suna da kwana biyu kuwa aka yi sunan momy ita kuma danta yaci sunan baffa wato halliru, ana cemai baba karami Sati guda su adda hamdy sukayi a gida, mazajen su sukazo suka dauke su Naci gaba da mkrnt na har lkcn zana jarabawar mu tayi, baffa shiyaban kudin da zan biya inzana jarbawar, amma ga mmkn ina kaiwa sai akace min ai na biya, ni kuma nace samm ban biya ba, exams officern mu kuwa yasake dubawa yace ai ranar da akazo aka biyawa hafsat Ibrahim maigari, to a ranar ne wani daga cikin su yabiya miki, passport kawai yanzu zaki bayar ki karbi receipt inki " jikina a sanyaye na bayar yabani receipt in, snn na fito nataho gida, ina tahowa a hanya nake tunanin babu wanda zaimin hakan in ba barr Saddiq ba, a zaure na tarar da baffa, na tsuguna nabashi kudin sa, " . yace min lafiya " nace mai naje ance min wai ya Saddiq ya biya kudin " baffa yace tooo yaron nan dai baya gajiya da hidima kwata kwata, to kuwa lalle ya dago min da wata magana ma dana sha'afa dashi Zanje in sami mai gari kawai asaka ranar auren kina gama exams innan ayi in huta, " zaro ido nayi ina kallon baffa, " baffa yace yaya dai " cikin sanyin murya nace baffa da dai an bari idan nahuta sai ayi " afusace ya dauki takalmin shi ya jefen da shi tare da cewa tashi kibani guri ja'irar yarinya " da gudu nayi cikin gida nafada gado ina dariyar farin ciki, baffa bai san maganar tamin dadi ba, kawai dai nace hakan ne kar yace bani da kunya, filo na runguma tare da lumshe ido inajin wata daddan sanyi tana ziyarar zuciya ta, karar wayata ce ta dawo dani daga nisan tunanin da nafada, a hanzarce na daga wayar tare da kashe murya nayi sallama, cikin sanyi murya ya amsa tare da cewa ya kk baby mine " lumshe ido nayi sbd jin dadin sunan da nakejin yana kirata dashi, cikin sanyin murya nace lafiya ta kalau babyluv " mirginawa yayi daga kwanciyar da yayi kasancewar ban taba kiran sa da sunan sa bama balle nakirasa da sunan soyayya Cikin jin dadi yace mai mai ta sunan da kika fada yanzu " cikin jin kunya na rufe idona, na kuma ki magana, yayi yayi ammana naki, haka dai muka karaci soyayyar mu da shi har muka gaji muka gama Wasa gske muka fara exams, bamu da lkcn komai sai na karatu, barr Saddiq kamma yace yanzu sau biyu zaina kirata a waya, daga safe sai dare, sbd wai yana son inci paper na. 
.
Muna tsaka da exams ne barr faruq yakawo sadakin hafsy, dama yace lalle lalle sai dai a fitar da mu rana daya da hafsy, farin ciki kamar zai karmu ni da hafsy, kawai sai muka ci gaba da Shirye shiryen biki kawai Gidan adda fauzy muke zuwa take gyara mu, abamu wannan mu ci abamu wnn mu sha, haka dai kullum muke fama. . Har Allah ya kaimu ranar da muka gama exams in mu Mun gama exams da sati guda aka kawo kayan lefen mu rana daya ni da hafsy, kayan cikin akwatin ma wasu iri daya ne, abin sha'awa gari duk ya dauka da zancen auren mu, tunda ake kawo kayan lefe kuwa agarin mu ba'a taba kawo irin wnn ba, zancen kuwa har garurruwan da muke makota da mu, nan kuwa kikaga yanda mutane suke tururuwan zuwa ganin kayan, har sai da baffa ya dakatar da su, Kwata kwata auren sati biyu suka saka don haka shirye shiryen biki sai abinda ya karu, su ladidi da lami kuwa su suke shiga suna fita komai yana hannun su. Mai gari shida kansa yabawa ya Saddiq da ya faruq gida acikin garin mu, wai idan munzo musami gurin sauka, ba karamin godiya ya faruq yayi ba, don ganin dattako irin na mai gari Don haka agidan suka mana jeren mu, kasancewar sunce ba sai anyi wahalar diban kaya daga nan har abuja ba, kawai a tsaya ayi shagalin biki a nan, in yaso daga baya sai mutafi Hakan kuwa akayi, gidan flat biyu ne aciki, daki ne ciki da falo da kicin sai bayan gida, sukenan, shima nasu hafsyn hakan yake Tun biki na sauran sati saiga su adda mrym, adda juw, adda hamdy, sun zo, kowa da irin nata jike jiken da take bamu, Kaiii nikam ma har nagaji wlhy da shaye shaye, daga ace yi tsarki da wnn, sha wnn, tsuguna akan wnn, kai abindai ba'acewa komai Tunda ake biki a garin mu ba'ataba yin walima ba sai akan mu, wai don za'ayi biki ayi walima kwata kwata bai dame su ba, sukan daura aure ne kawai akai amarya, . 
.
budan kai ne dai duk talaucin ku sai kunyi shi, amma abikin mu walima aka hada sosae nagani nafada kowa sai magana yake don ganin amaren kowa tasaka wata hadaddaiyar duguwar rigace, ai sai kallo yakoma kan kayan don ganin haduwar kayan, muka kira wani babban malami tun daga fofure yazo, ya wa'azance en garin mu tass, mata daddaya ne wa enda basu zo walimar ba, amma da labari ya iske su irin wa'azin da aka sha, ai kuwa kowa taji haushin rashin zuwan ta Mota har gurin walimar tazo daukan mu, cikin kasaita muka shiga, abokan su ne dasuka zo da su daga abujan, har kofar gida aka zo aka sauke ni, snn aka wuce da hafsy gida Dakin inna na nufa kasancewar tunda aka fara hidiman bikin gurin nakoma da kwana, ina shiga na ganshi zaune shida inna suna ta hiran su, Cikin sauri na juyawa zan fita " inna tace ina kuma zaki kagamin yarinya da iskanci, zonan daman ina neman kine " . banyi niyar dawowa ba ammana danaji inna tace inzo tana neman sai na dawo, ta nuna min guri bakin gadon ta tace zauna anan " na zauna kaina yana kasa " inna tace to ina zuwa " inna na fita kuwa yataso yadawo inda nake yace baby mine kinga yanda kikayi kyau kuwa, wow daman ashe kullum boye min kyaun ki kike, "Ni dai ina shiru bance komai ba "hannu yasa a kafada ta snn yajawoni jikin sa, " cikin sauri nace a'a me haka kuma, in inna ta dawo ta same mu hakan fa " yayi dariya yace baki san inna ta ban guri bane in dan zanta da ke bako " sai a lkcn na dago abinda innan ke nufi da fitan da tayi " a hanzarce na mike tare dace ana kiran sallamar magariba sai anjima " murmushi yayi snn yace gobe dai yi warhaka kin dawo tawa, sai yanda naso zanyi da ke " yi nayi kamar ban jishiba nakama haryar waje abina, snn ya mike yataso yayi waje, komawa nayi na kwanta tare da dafa kirjina don jin yanda yake dukan saba'in saba'in Iyayen barr faruq ma da sukazo a gidan mai gari aka musu masauki Washe gari Ranar asabar kuwa misalin karfe 11:00am dai dai aka daura aure na da barrister Saddiq, aka daura na hafsat da kuma barrister faruq, a kofar mai gari aka daura auren dukka. . Ina zaune dakin inna lami tashigo tana guda sosae, nan da nan wasu ma suka kama ai sai gidan ya rude da guda gaba daya, ina kwance dakin inna ni da kawaye na, na rufa kaina akan gadon sbd tsabaragen wani kunyar da ta kamani nan da nan. Shigowa sukayi suka kamoni suka saukar dani kasa aka fara min wanka da nono wato sakun lalle kenan, basu barni ba har saida suka min kaca kaca da jikina snn suka kyaleni Da daddare kuwa aka zo aka daukeni aka kaini gidana, ana shigowa dani aka shigo da hafsy aka ajiyeta a gefen ta, nima ina nawa gefen, haka aka barmu dagamu sai kawayen mune muka kwana Washe gari dasafe kuwa aka hado mana abin karyawa muka karya, snn mukayi wanka muka canja kaya, ba'ayi budan kai da wuri ba har sai bayan la'asar snn akayi, munsha ado munsha kwalliya harda alkebba muka saka, akayi budan kai, ya hadu sosae shima, sbd harda masu kalangu aka dakko, mun samu kudi kuwa sosae Ba'a tashi ba har sai shida Ana kiran magriba aka mayar da mu gida jen mu, mutane suka fara tafiya, to sai a nan ido ta raina fata Ni kadai na aka bari a dakin naci kuka na harna gaji, .

kaina yana cikin gyale na najiyo sallamar sa Shi kadai yashigo sai laidar da ke hannun sa, a hnkl ya iso inda nake zaune, cikin sanyin murya yace " baby mine lafiya na ganki kin dukun kune kanki acikin gyale, ko zafi ma bakya ji " shiru nayi bance komai ba Ya ajiye laidar da ke hannun sa snn ya zauna a gefe na, ya sa hannu ya yaye gyalen cikin hanzari " da sauri nasaka tafin hannuna na rufe fuska ta, tare da sa fuskata a cinya ta " murmushi yayi snn yace to tashi muyi sallah ko " ba musu na mike, ni nafara shiga bayan gidan nayi alwala snn shima yashiga daga baya Shi yaja mu sallahr, bayan mungama mukayi addu'o'i snn yakama kaina yayi addu'a, Jawo laidar kazan yayi ya budeta tare da juice kala kala, ya yago kazan ya mika min inci, amma me naki karba Sam, yayi yayi da ni nace mai ni banna jin yunwa, hasalima ni jikina sai bari yake a lkcn, shi inma hakura yayi da naman, yajuyo yana kallona " kamar zanyi kuka nace ni bacci nake ji " da sauri yace tashi ki shiga ciki abinki, ni kamma anan zan kwana in kin shiga ki miko min filo, " ba musu na mike tare da cewa toh Na shiga na fito mai da filon, snn nayi mai sai da safe, shikuwa harda cewa Allah yatashe mu Ina kwance bacci yafara dauka ta, kamar a mafarki sai naji ana tabani, da dai ban damu ba sai kuma naji abin gaba gaba yake karawa, ai kuwa sai naji an canza salo zahra Firgit na tashi, ae kuwa sai jin bakinsa nayi cikin nawa, . nayi nayi na kwace amma ina yayi min mummunar kamu, babu irin magiyar da banyi ba amma ina ko sauraro na baiyi ba, har sai da ya cimma kawar da budurci na, nayi kuka nayi kuka kamar zan cire raina, babu wanda ban kira ba agidan mu, ammana ina barrister yayi nisa, sai kusan asuba ya kyaleni, shida kansa ya dauken ya kaini toilet ya gasani a ruwan zafi, snn yabarni nayi wankan sallah, snn na dauro Alwala. Ina fitowa naganshi zaune kan sallaya yayi nafila, kaina akasa na nemi guri na zauna bakin gado " . a hnkl yajuyo ya kalleni tare da cewa sannu ya kikeji yanzu " bance mai komai ba idona yana kasa " tambayar yakuma min " nan ma shirun nayi " murmushi yayi snn yamike yazo yasame ni ya zauna kusa dani, jawoni yayi jikin sa tare da cewa haba baby mine fushi kike danine, pls kiyi hkr kimin magana mana " shiru na naci gaba dayi, haka yakaraci surutan sa har aka shiga sallah, yatashi yafice masallaci kasancewar akwai masallaci kusa da gidan namu agun "Yana fita namike nayi sallolina nayi addu'o'i na, har na idar na tashi nasake shiga wanka na kuma gasa jikina sosae nafito, tunda nashiga ruwan zafin kuwa naji jikina ya sake ni, naji dadin jikina sosae, naci gaba da kazar kazar ina kamar babu abinda ya wakana, ina zaune gaban madubi ina dan shafa mai ya shigo, a bakin gado ya zauna yana kallo na, ni dai bance komai ba, a hnkl yace kawarki fa tana neman ki " da sauri na jiyo tare da cewa meyasa meta " cikin tsokana yace abinda yasame ki " kunya ce takamani nan da nan na saukar da idona kasa, a hnkl na tashi na dau wata doguwar rigata nasaka, na dauki gyalena na yafa nakama hanyar fita " shan gabana yayi da sauri tare da cewa ina zaki " cikin muryar kuka nace bacewa kayi hafsy na nema na ba " yace to shine babu tambaya, ko kin mance yanzu kinzama matata " cikin sanyin murya nace to kayi hkr " daga kafada yayi tare da cewa aa kam ban yarda da wnn bada hkrn ba " . 
.
cikin shagwaba nace to me zan ma " ko kunya babu yace min kiss zaki min " rufe idona nayi da tafikan hannuna, tare da cewa bazan iya ba " yace to shikenan bazakije ba kenan " narke fuska nayi alamar kuka " yace to yimin sai ki tafi " haka dai babu yanda na iya na rufe idona na matso kusa dashi nayi mai kiss in, da sauri najuya zan gudu amma ina kamoni yayi ya rungumeni tsam ajikin sa, da kyar na kwaci kaina a hannunsa, na ruga da gudu waje, a gun nabarsa yana tsaye kamar gunki " hannu kawai nasaka naji kofar falon a bude take, da sallamata na shigo, a falon na tsaya sai da nayi sallama baki biyu sannan barr faruq yafito " tare da cewa sai yanzu ko, " dariya kawai nayi tare da gaisheshi " cikin fara'a ya amsa, snn yace kishiga tana ciki " cikin sauri na shiga, durkushe nasameta abakin gado, da sauri na dagota tare da cewa lafiya hafsy yaya dai, " a hnkl ta dago tare da cewa khairi na wahala wlhy kinga yanda naji jiki, wlhy ya faruq bai da imani kwata kwata " dariya ma taso tabani, ammana sai na daure dai nace mata to tashi in kaiki bayan gida ki kuma gasa jikin ki, ko zaki danji dadi, cikin karfin hali ta mike tare da bina, nida kaina na gasawa hafsy jiki, gsky ya faruq bai mata ta dadi ba, don kuwa yaji mata ciwo sosae bana kadan ba, ni ina ganin naji jiki ashe hafsy tafini jin jiki Shiryata nayi cikin wata riga da sikat snn na hada mata tea tasha ta kwanta, nayi mata sai anjima snn nafito A falon nasame su, ya faruq yace yaya dai khairi " nace mai ai tayi bacci, anan yayi min godiya snn ya Saddiq yasakani a agaba muka tafi Ni azatona soyayyar da mukeyi da ya Saddiq a gida itace soyayya, ammana sai yanzu nagane ashe daa shirme mukeyi ba soyayya bace, soyayyar da yake gwada min yanzu ta ninka na daa sau million's, " satin mu biyu muka dunguma sai airport acikin jimeta muka daga sai abuja, bakaramar karba muka tarar ba, hafsy da ya faruq suka wuce gidan su ya faruq gurin iyayen sa, Muma gidan su ya Saddiq muka fara sauka, kaii bazan iya misalta irin karbar da momy tamin ba, matar tana da kirki bana kadan ba, haka shima daddy kamar er su haka suka dauken, haka tayi ta nan nan da ni, sai da daddare snn muka wuce namu gidan dake palm city estate lokogoma dake area 1 Gida iya gida gashi nan ansaka mai kayan alatu kala kala, tsayawa kawai nayi nasake baki ina kallon gidan, gidan sama ne, parlourn dake kasan yasha kaya, hawa sama yafara dayaga bani da niyar haurowa ne ya dawo ya daukeni cakk mukayi sama, nan ma wata parlourn ce ha daddiya, bamu tsaya nan ba sai da muka shiga daki snn ya direni akan gado, ya hau sumbata ta tako ina, dakyar na kwace kaina nayi bayan gida na dan watsa ruwa snn na fito, shima ya shiga ya watsa, yafito ya tarar dani nasaka sleeping dress iya cinya, na kwanta ruf da ciki, murmushi kawai yayi snn yadan shafa body lotion yafeshe jikinsa da turaruka snn yazo yadaga min hnkl a inda nake kwance, kamar zanyi kuka na marairaice murya ina basa hkr amma ko saurarona baiyi ba, thanks God yau dai ban wani ji zafi sosae ba.... 
.
jin dadi kwanciyar hnkl babu irin wacce bangani a idan barrister Saddiq ba, nan da nan na dan murmure na danyi kyau da ni Yaki yabarni inje gidan hafsy wai sai nayi ciki kafin in fara fita, nayi nayi amma ina yaki, itama hafsyn dana kirata abinda tagaya min kenan, dariya kawai mukayi, mukaci gaba da zumuncin mu awaya Kamar hadin baki kuwa bayan wata biyu saiga ciki, atare muke ta lau layin mu, ammana hafsy nafini jin jiki, don ita har kwanciya tayi a asibiti, daman hafsy bata iya samun ciwo ba, to sae a sannan ne naga hafsy tun da muka zo ashe ma estate in namu suna kusa bamu da nisa kwata kwata Haka dai muka ci gaba da rainon cikin mu har lkcn haihuwa, nayi nayi da barrister akan yabarni inje gida in haihu amma ina yaki, . sai da kyar momy tazo ta dauken nakoma gidan ta, a hakan ma bai so ba, har Allah yakaimu lkc haihuwa na suntulo 'yaya na mata guda biyu kyawawa, na haihu da kwana biyu kuwa hafsy itama ta haihu ta haifi itama erta mace kyakykyawa da ita, don haka mota na musamman su barrister suka tura adamawa don masu zuwa suna, su adda maryam kuwa duk sunzo, su adda hamdy ne dai basu sami zuwa ba don kuwa suma suna nasu jegon ne agida, ahaka akazo akasha suna, suna ya hadu nagani na fada, yara sunci sunan ammi da momy, ana kiransu, kaynat da kaysa, babyn hafsy kuwa taci sunan mahaifiyar ya faruq ana kiranta da noor kowa yatafi sai san barka yake Bakaramin kyauta barrister yaban ba wai na mai babban kyauta tunda na haifa mai en biyu. Bayan wata shida Da haihuwarmu kuwa mukayi jamb, muka kuwa cii, suka saya mana form a gwagwalada bayan mun sami Admission muka fara tafiya makaranta cikin kwanciyar hnkl, . masu aiki momy ta turo mun suna tayani rainon yara, don haka agida nake barin su nake tafiya makaranta na Bayan munyi hutun semester ne lkcn su en biyu suna da wata goma, amma babu inda basa zuwa da kafar su in kagansu abin sha'awa Muka dunguma dukkan mu harda su hafsy muka nufi Adamawa Sai zuwa sannu da zuwa ake mana, kowa yana shigowa yana ganin mu, gidan mu kuwa ammi tazama hajiya, sai abinda tafada ake agidan, a nan kuwa inna da baffa suka gane cewa ashe 'YA'YA MATA ma RAHMA ne, don kuwa 'YA'YA MATA sune silan arzikin su, abinda 'YA'YA MAZA basu masu ba shine 'YA'YA MATA suka musu, don yanzu haka barrister yasa a rushe ginin kasan da ke gidan mu amana na zamani ginin bulo da bulo Haka muka Karachi hutunmu ana nan nan da ni da 'YAYA na MATA Muna komawa kuwa barrister yabiya mana aikin hajji ni da baffa da ammi da momy da daddy dukkan mu muka tafi muka bada su en biyu wa hafsy ta rike mana, Munyi aikin hajji lafiya mun kuma dawo lafiya, . sai dai fatan san barka Alhamdulillah munsami SAUYIN RAYUWA acikin rayuwar mu, watarana idan na zauna ina bawa barrister labarin irin kuntata mana da akayi agidan mu sbd mu 'YA'YA MATA ne, sai dai kawai ya kada kai yace min to ae RAYUWA KENAN Murmushi kawai nayi snn na mirgina na kwanta akan kirjinsa tare da cewa iluv u babyluv "Kiss ya kaimun tare da cewa me too baby mine Alhamdulillah!!! Ina godiya wa Allah ma daukakin sarki da ya nuna min wannan rana da Allah yasa na kawo karshen wannan littafina mai suna 'YA'YA MATA ina fatan darasin dake cikin littafin zai amfani jama'a Kuskuren da na aikata aciki kuma Allah ya yafemin, Subhanakallahumma rabbana wabi hamdika ashshadu Alla'ila ha illa anta, astaga furuka wa atubu ilaika.  - ISMAIL SANI
.
Jinjina ga marubuciyar wannan littafi baby zahra, Sai kuma ni ISMAIL SANI (ISMAIL P) Nake cewa mu huta lafiya sai mun hadu a wani sabon littafin.

0 comments:

Post a Comment