Thursday, 7 December 2017

'Yar Boko Part 1 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YAR BOKO PART 01
.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
 Neenarh zaune a school library, tana revision n lecture din d suka futo, gefanta Ummy lolo ce  ita ma ta maida hankali g calculation din gabanta, neenarh ce tace besty lokacin sallah yayi is better mufara sauke farali sannan mu cigaba d gashi, atare suka mike dan zuwa central mosque dake cikin campus danbin jam'i, zuwansu keda wuya akai kiran sallah, kafin liman y tada ikama sun idar d nafila rakaa biyu,   Wayan neenarh ce t fara ringing ,tana dubawa tace zuhra ce   tare d amsa kiran ,tace Hello? Adaya barin zuhra tace kuna inane tin dazu kunbarni sai zagaye nake cikin schl bangankuba, neenarh tace masallaci mukaje mukai sallaa,but we are on our way to d lecture hall  pls ki samar mana seat ,yanxu zamu karaso, 2:00pm suke d lecture  ka'idar malaman department din shine  in lecturer y rigaka shiga hall shikenn kayi missing lecture wannan rana, kamar kullum yauma lecture din political science deptrmt zasuyi Mai taken *INTRO TO POLITICAL SCIENCE*hango malamin sukai yana tafe a bayansu saura kiris y cimmusu aikuwa basu san lokacin d suka daga kafa d yar rige rige dan ganin sun rigashi isa ba,aikuwa suna zama shima ya shiga Hall din ,musa Abdullah auditorium katan Hall ne dake cin akalla dalibai dubu, bisa g alada duk wani dalibi n jamia yasan cewa dalibai from different department ke Haduwa guri guda dan yin lectures, su ummylolo n daga cikin dalibai da ke department of economics suke subsiding d pol Science d sociology, shigowar malamin  y Sanya aji yai tsit, saboda tin ranar d y fara shigowa y kora musu warning tare d wassafa musu sharadansa, tare d ja musu kunne subi doka a zauna lfy, dan duk student din daya fada trap dinshi zai dandana kudarshi, malam Abdulmalik shine ke daukansu course din, a hankali ya dinga musu bayani dalla dalla, inyana ma explaining concept sai kaji tankar kwakwaluwar K y bude y zubama, gashi d kawo examples d refrence, shi yasa daliban ke alfahari dashi, aladar shi guda duk lokacin d y gama, zai pointing randomly akan koma waye ya mishi tanbaya base on abin d sukai treating, in kayi nasarar amsawa y baka marks, inkuwa akasin haka zaiyi deducting 5 marks from ur continuous assessment, minti daya baya karawa akan two hours d schl t yarjemai.   A kalla arana suna yin lecture 3,kuma d intervals tsakanin ko wanne ,hakan n basu damar kara bibiyar abinda malamannasu suke koyar dasu, alakar Ummy lolo , neenerh  Xuhrah t samo asaline tin ranar d suka zo karbar admission letter, neenerh ce t fara zuwa, ganin gurin arufe yasa t nemi gefe t zauna kan benci ,saboda murna ko baccin kirki bata samu tayi ba, ummylolo ce t karaso inda taga Wata budurwa a zaune , tace hiii Sis, ta amsa d hy, t kara d cewa pls a ina ake karban admission letter? neenerh tace n wana deprtmnt din? tace economics.window din dake kallansu t nuna mata tace nan ne, nima su nake jira n Karbi tawa, jin haka yasa Ummy samun guri t zauna, jefi jefi suna dan hira, a hnkli akai t taruwa sannan aka fara basu, bayan neenerh t Karbi tata tace d Ummy barinajira ki, sai muje bank muyi payment, wannan itace silar haduwar su, yayinda zuhra kuma sun hadu a Cafe lokacin d sukaje shigar d courses din d zasuyi.   
.
  6:00pm lecturer din y futa daga hall din  neenarh, ummylolo n zuhra tafe suna hira, sannu a hnkli har suka karaso parking space n campus, motar neenarh suka nufa kirar jeep 2016 ,ummylolo zaune a gaba, Xuhra a baya, hirar abubuwan d suka wakana a schl yau suke, in suka hadu basa ji basa gani, kansu farga har anxo inda suke sauka su hau Wata motar, ita kuma t wuce gida, sallama sukai t kara gaba.   Isarta gida Gate man y bude mata kofa tare d rissinawa har kasa yana hajiya brk d dawowaa,ko daga ido batai t kalleshiba balle yasa ran zata amsa ,saidai t daga mishi hnnu,haka taita cin karo d yaran gidan amma b wanda ta amsawa sai dai insunci saa t daga musu hannu,  palo t tadda momynta d sassarfa t karasa gun ta, mom tace oyoyo daughter y lecture, Hope dai yau baki gaji kamar jiya b, cikin shagwaba tace walhi mom karatu a nyja no easy  harna fara futa a hayyacina, dama a london nai zamana n karasa karatuna, walhi mom duk ke kikasa Dady y dawo dani, mom t shafa kanta tare d cewa hba daughta zaki saba dandai baki dade kina zuwa b,at times goes on u will b Use to it, mikewa tayi t ce d Mom bari n dan watsa ruwa nayi sallar magrib.  Tayi wanka tare d Sanya English Wears, inhar tana gida kayan d take sawa kenn, dan intasa atanfa, lace ko shadda sai taji tamkar t dora dutsen dala a kanta, futowarta keda wuya t yada zango a dining, asabe t shiga kwallawa kira House maid din su, asabe, asabe, aguje asabe t tawo Dan kartayi lefi, ta durkusa har k'asa tare d cewa aunty gani, tace kawomin abinda zan wanke hannu, yau d fingers dina nake shaawar cin abinci, avin y d'aurewa asabe kai harma mom dake can nesa dasu, abinda uwar dakinnata bata tabayiba, bata d damar tanbaya  ,a hnxarce t kawo mata, tare d tsiyaya mata ruwan t wanke hannun,  umartar asabe tayi d tai serving dinta  sakwara t sa mata malmala daya d miyar ganye Wanda tasha Spice's d kaza, atake palon y gauraye d daddadan kamshi  Wanda y Sanya yawun neenarh tsinkewa, a hnkli t dinga cin abincin harta kammala  ,t wanke hannunta t koma tsakiyar Palon inda mom ke zaune tana watching wani series.neenarh ta ce mom wai yaushe Dad zai dawo ne  ? T ansa d gobe Insha Allah, wani ihu d tsalle neenarh tayi tare d cewa Wow, can't wait,nayi missing dadyna gsky, g pocket money n y Kare inason sayan takalma d viels, mom cikin bacin rai tace ina kudaden d y baki kan yayi tafiya, kina nufin Kin kashe 100k  daya baki? 
.
Neenerh tace Mom 20days fa   namayi kokari walhi nayi manejine d ita, Mom tace bari kiji in shi dadyn Naki y Saba sangartaki nibazan laminci haka b  daga yau sai yau dubu 20k zai dunga baki every month, neenerh cikin hawaye t karaso gun mom tana pleading pls mom ki rufan asiri, walhi 20k tamin kadan, kiyi hakuri bazan tanbayeshi b, zanyi manage d ragowar canjin d ke hannuna zuwa karshen wata,fada mom t yi tai mata tare d nuna mata illar sabo d kashe kudi, inba mutuwa akwai talauci, hakuri dai taita baiwa Mom saboda tasan in zancen yaje kunnen Dad shiknn y daina bata kudi  duk d irin so d kaunar d yake mata, baya Tsallake maganar matartashi, mom tai mata banxa ,sai daga karshe tace,hakan d nake miki b wai sankine banayi b, so nake n gyara miki tarbiyya Dan kwata kwata bazan laminci dabiun d kika taso dasuba.  DA sasssfe neenerh t tashi a hnxarce ganin tayi latti, t nufi toilet danyin wnka tare d alwala, ko breakfast bata tsaya yiba t shiga dakin mom, tace  mom sai n dawo, a gurguje t futo t nufi motanta t fuce, dai dai kabuga t tsaya t dauki ummylolo d zuhrah suka nufi schl.   
.
suna shiga lecture hall din lecturer haneef y shigo cikin takunsa n kasaita, duk d hayaniyar d ake lokaci daya aji yayi tsit, malamine nitsattse  ba ruwanshi d harkar yanmata.   Tunda y shigo hnklinshin n kan kyakkyawar beauty (neenarh ),jiki sanyaye yayi abinda y kawoshi y fuce  tinda y isa offc dinshi fuskar neenerh ke mishi gixo, lokaci daya zazzafar kauna d soyayyar neenerh t shiga jini d tsokar shi.    yinin ranar cikin wani mawuyacin yanayii yayi shi, bacci kuwa sai barawo.   A bangaren su neenerh kuwa byan Sun futo daga lectures xuhra ke cewa, yau n g abun almaraa? atare suka tanbayeta a ina? dariya tayi tare d shewa, tace a lecture hall, kunga yanda wannan lecturer din ke kallon ki kuwa, neenarh tace wafa  ? Atunaninta ummylolo take nufi, zuhra tace ke mna, tabe baki neenerh tayi tace Tab, iska n yawo d mai kayan kara ,a zuciyanta tace Ko a jikina, bani d lokacin kula saurayi, karatuna shine a gabana,).   A fili tace ni wallahi mmki kuke bani ku har kunada lokacin hirar samari balle harta kai g ku kula su,inkunga n kula saurayi saina kammala first degree, n gama masters d PhD, a tsorace suka zaro idanu,hba besty wanna waca iriyar maganace, a gidan aurema ai ana karatu, dariya tayi tace ai a gidanmu baa tsaida  shekarar aurena ba, haryanxu ni yarinyace a gidanmu,furucinta y daurewa kawayennata kai amma sai su ka basar, suka shiga yi mata nasiha game d muhimmancin aure g diyar musulmai, koba komai yana karawa ya mace kima d daraja a idan alumma, tare d garkuwa g fadawa hanyar d take halaka, duk d dai sun san kawar tasu nitsattsiyace amma aure shine cikar kamalar mace .   Duk maganganun d suke fada tamkar waka take jinsu, yanda suke futowa daga bakunansu, haka iska ke gaba dasu btare d sun shiga kunnuwanta b, ballantana suyi tasiri azuciyarta, haka suka karaci babatunsu amma t tafasa batace musu ba.    zuhra ce t kara d cewa ai wallahi duk zance ne inji masu magana ,danbaki sami saurayin d zai sace zuciyankiba ,amma d muma sai dai muji asama cewa Kin fada tarkon so. Dariya sukai tare d tafawa, binsu tai d ido, cikin kunar rai tayi kwafa, batasake kula suba haka suka gama lectures din yau suka nufo gida, a zuciyarta gani take Sun ci mata fuska tare d raina mata hankli, danmeyasa zasu mata dariya harda tafawa mahaukaciya suka maida t kokuma Wanda batasan Me take ba  .
.
   Ranta abace t iso gida, hawaye a fuskar t shabe shabe kamar wata kankanuwar yarinya, t nufi dakin mom t fashe d Kuka, mom cikin tashin hnklin ganin yar tata cikin halin d bata taba ganiba tace lfy daughta? kuka t kara rushewa d, mom tace Wa ya tabamin ke, sai lokacin tace su besty ne, dariya Mom tayi tace me y hadaku keda aminan naki ? A shagwabe tai mgna tsokanta suke wai wani lecturer dinmu kesona, wai sainayi aure, dariya mum tayi tace haba neenerh kema kinsan tsokanace, kinsan Dad dinkima bazai aurar dake yanxu b, batare d kincika Mai burinsa n ganin kin zamo professor b ,abinda nakeso dake kimaida hankali wajen karatu,cikin jin dadi tai dariya,tace yawwa mom Ashe kema kingane, nidai ki tayani d addua Allah yasa min albarka a karatunnawa, mom tace amin.   Mikewa tayi t nufi part dinta dan hutawa cikin tsantsar farinciki.Haka t yini cikin farinciki, bataso ayi mata zancen saurayi balle t kai g mgnar aure, wayartace tai ringing d har b zata daga b, azatonta ummylolo ce ko zuhra, amma Data duba sai taga ashe rasheeda ce, cikin farinciki t amsa call din, bayan sun gaisa take mata albishir cewa sunanan tafe zuwa yin hutu gidannasu, sun dan taba hira karshe sukai sallama,dakin mom t nufa dan sanar d ita zuwan su rashida, mom taji dadin jin haka dan hakan zai kara musu dankon zumunci d yayartata   .
.
  Neenerh anyi kwanan farinciki jin su jidda d mrym zasu kawo musu ziyara, ya'y'an ka'nwar Mom ne wadda ke aure a birnin tarayya abuja, sa'o in neenerh ne, inkagansu zakace yan ukune saboda tsabar kamar d ke tsakaninsu, jidda d marsie twince ne, duk inda zakagansu tare suke, komai nasu iri daya ne daidai d colour, ko a schl parent dinsu basu yarda a raba musu class b, jidda itace hasana  marsie husaina, dabiar su t sha banban tun suna k'anana, ita jidda tanada san hayaniya d tsokana  yayinda marsie shiru shiru ce ,Abu d yawa in jidda t yo tsokana akan marsie abin ke karewa,cox bazatace b ita t aikataba,tsawansu daya, a inda suka banbanta ita jidda tafi marsie kiba ,wani lokacin hartakai g anmata hukunci sai dai taita Kuka karshe t share hawayenta,Ak'idar  neenerh d jidda iri daya ce t burin yin zurfaffan ilimi wanda b kowana namiji yake d burin yiba, balle mace datake d takaitaccen lokaci .  Misalin karfe goma suka sauka a Aminu kano airport, driver mom taba umarni yaje y daukosu, cikin kankanin lokaci suka iso gidan  aguje suka karasa tare d rungume yayar mahaifiyar tasu, tare d risinawa suka gaisheta t amsa cikin kulawa tare d tanbayar mutanan gida, tare suka tanbayi Mom ina neenerh?  mom tace ta tafi schl amma sabida murnar zuwanku tace 12 zata dawo t debeku saikuje schl din tare t karasa lectures din.neenerh n lecture amma duk hanklinta n gida ,tunda t duba tym taga ten tayi t tabbatar d y'anuwannata sun iso a daddafe t bari malamin y futa, aikam bata tsaya bata lokaciba tayi gida, su ummylolo sai kiranta suke amma ina hnklinta yayi gida ,isarta gida, ko kulle motan bataiba t nufi ciki  tin kan t karasa t dingajin tashin muryar jidda suna hira d Mom, aikam suna ido hudu, jiddan t taho a guje suka rungume juna, marsie n zaune n kallan ikon Allah, mom KuWA cewa tai o ni Bilkisu yarannan yaushe zasu san sun girma, atare suka zube a tsakiyar carpet n palon tare d tafawa, dariya sukai baki daya, neenerh ke tanbyrsu sun iso lfy?
.
Sukace lfy. Sai alokacin t kula d marsie tace Sistr y gajiyn hnya tace lfy lu, tare suka ci abinci, sukai sallah quarter to 2:00pm suka shiga buk, straight lecture hall din suka shiga suka zauna, zuhra ce t hango shigowarsu, hakan yasa ta yafuto Ummylolo tace ganemin can neenerh dasu waye, kai amma suna mugun kama dama tanada kanne mata, kan zuhra t bata amsa Malam haneef yashigo,nan aji yayi tsit, yau ma kamar kullum sai dube dube yake tare d sanyin toxali d hasken idaniyarsa, y hangi bangaren Data saba zama, gadai friend's dinta su biyu amma b ita, hakan yasa yaji jikinsa yayi sanyi,zuciyarshi t fara harbawa d sauri d sauri, cikin dabara yafara zagayen ajin yana bayani azuwan yanason yasamu full concentration n students din ,can y hangosu zaune abaya su uku, baisan lokacin daya mutsittsike idanuwansa d hannuwanshi biyu azatanshi itace take mishi gixo,tab soyayya manya, hakan y tabbatar mishi b gixo bane su ukune masu kama daya, dandai so so ne, amma d sainace b zai iya futar d abar sannashi cikinsu ba, sai dayai dogon nazari akansu, ya ganota, t yanda y fahinta Kuwa shine , neenerh tafisu hasken fata, kuma d gani tafisu maida Hnkali Akan bayanin d yake, Dan y Kara tabbatar d zarginnasa, bayan y gama yi musu bayani sai yayi pointing at neenerh t tashi dan amsa tanbaya, with caurage t tashi tsaye tana sauraron tanbyar tashi, dayake economics yake musu y tanbayeta what are d  differences between speculative motives and precautionary motives ? cikin gwanancewa d dinbin basira tabada amsar tanbayar aikam kanta rufe baki yan aji sun dau tafi ji kake,shi kanshi t burgeshi ,take y bata 5marks bonus ,haka y tattanbayi sauran student's din har akazo kan zuhra y tanbayeta what are d differences between demand n supply, itama t bada amsa daidai gwargwado, duba agogon hannunshi yayi daidai d cikar lokaci, batare d bata lokaciba yace Class rep d assistant nashi should follow him to his office, tofa rigiji gabji,wata sabuwa injii dan caca, Kabeer wanda akafi sani d kB shine class rep  ,neenerh kuma assistant nashi.   Neenerh bataso hakanba, dan Kuwa yau a farinciki take n ganin cousin's dinta, Allah Allah take y gama, t tashi su tafi gida sai g wannan malamin zai jawo mata delay, kB ke mata mgna tazo su je, tace yayi gaba gatanan zuwa, atare suka jera neenerh, jidda, marsie, umylolo d zuhra, kallo y koma sama, kowa kallansu yake cikin mmki dama neenerh yan uku ce,isarsu kofar offc din sukace zasu jirata a waje, bataso hakanba, Da sallama suka shiga ita d KB  yayi daidai d juyawanshi yana waya, danhaka baisan su waye ba, yadai musu alamu d hannu su zauna. - ISMAIL SANI
.
KUNA TARE DA NI MUJE ZUWA?

0 comments:

Post a Comment