Monday, 4 December 2017

'Ya 'Ya Mata Page 3&4 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YA'YA MATA page 3 & 4
.
Washe gari da safe kuwa kamar yanda tafadi in batayi abin karyawar da mu ba, " yau kam har daki na bita amma sai ban ganta ba da alamu ta shiga bayan gida ne, daya daga cikin kofunan dake rufe agun na bude na juye kunun da ke ciki, da alamu kunun ya amadu ne don kuwa ba a kofin baffa bane, na mayar mata da kofin kamar akwai abu aciki nayi waje, " mukaje mukasha kunun yaji suger kuwa, mukasha muka tande baki, muka kama hanya muka tafi mkrnt " amadu ne ya shigo gidan ko sallama babu kanshi tsaye ya nufi dakin mahaifiyar shi tare da cewa mama ina abinci na, " inda kofin yake ta nuna masa tareda cewa gashin cen a kofin ka " gurin kofin ya nufa tare da daukar kofin yajita wayam, tsaki yaja tare da wurgi da kofin snn yace mama wannan wani irin iskanci ne za a ajiye min Kofi babu komai " ita kuwa uwar kamar wacce ke tsoron sa nan da nan ta mike daga inda take zaune tare da ce wa bangane babu komai aciki ba, takaraso inda kofin yake taga da gske ne, "kamar wacce aka tunkudota waje tawani yi tsalle ta duro a tsakar gidan tare da cewa yau za ayi bura uba agidan nan yaseen, wnn ma ae iskanci ne, an min sau daya anmin na biyu nayi shiru shine za a ci gaba to wlhy yau kam da sake, in banda iskanci mutum ya haifi barayi agida tun ana sace mana abinci danye yanzu andawo har dafeffen ma baza abarmu da shi ba " kamar wacce aka wurgota daga daki tace ke yaya da wa kikeyi ne naga kin tsaya kofar dakina kina ta zage zage, cewar ladidi " lami tace ohh daman kina jira ne ince da ke nakeyi, to ladidi da ke nakeyi " a fusace ladidi tace to ya isheki haka yaya wlhy idan kina wa yarana sharri a gidan nan zamu sa kafar wondo daya da ke wlhy " amadu ne wanda tun tuni yake gefe yake kallon su yace idan kun gama fadan Kimin magana a waje, kanshi tsaye ya wuce waje abun shi " kaga irin ta ai yaro ko kishin uwar sa ba yayi, cewar ladidi. 
.
Ke akan naki yaran suna kishin kine ko me, wayakai yaran ki badala a gari " ammi ce tafito tace don Allah kuyi hkr kubar fadan nan haka kudena tone tone wa 'ya'yan ku haka, wanda kuke fadan domin shi ma fa yace ya hakura da kunun, don Allah kuyi hkr haka nan " kyaleni da ita Indo saina dai dai ta mata zama a gidan nan ban taba baza mata halina ta gani bane shiyasa cewar ladidi " ammi tace yadai isa haka don Allah, jan hannun lami tayi tare da cewa yaya don Allah ki koma daki, har daki ta kaita ta ajiyeta tabata hkr, snn ta koma tabawa ladidi ma hkr, " duk da sun koma daki amma bakin su baiyi shiru ba, sai cakkawa junan su mgn suketayi daga daki, fada dai yaki ci yaki cinyewa har rana tayi anata abu daya, mai girki ma bata tashi ta dafa musu abincin rana ba " da sallamar mu muka shigo gidan, tun daga kofar gida muke jin hayaniyar lami da ladidi, mukace to anata sana a fa, nice a gaba kasancewar na kwaso yunwa, jaka kawai na ajiye snn na nufi kicin don daukar abinci, nagama kudurtawa a raina cewa ko abinci waye ne dakkowa zanyi inci, ina shiga kicin in naga wayam, ko murhun ma ba a kunna ba, babu wani alamar an hura wuta ma agun, a shar na sake daga cikin kicin in tare da fitowa tsakar gidan a fusace, yau wacce mata ce da girki da bata dafa mana abinci ba, ni fa wlhy zanyi rashin mutunci a gidan nan, daga yau ace anyi girki ban da mu sai gobe ace ba a mayi girkin ba, to wlhy zamu zuba ni da ku a gidan nan, wnn ma ai iskanci ne, me amfanin ku ba ku bane matan gidan, ko ance muku nan gidan mazajen mune da baza ayi mana girki ba har sai anjiramu mun dawo daga mkrnt kafin muyi, mutum ya dawo da yunwa snn ace wai ba ayi abinci ba, to wlhy da sake " a fusace lami tamike daga wankin da takeyi in tare da cewa to wani uban ne yasaki a mkrntn balle a damu da kin dawo daga mkrnta da yunwa mu ina ruwan mu da mkrntn ki, mkrntn banza mkrnt hofi. Ina ruwan mu da mkrntn ki, mkrntn banza mkrntn hofi..... " nace eh dayake baki san darajan mkrnt ba kam ai kya ce hakan...." Adda maryam ce tazo ta rike hannu na tana jana tare da cewa ke khairat sa'an ki ce ita da tana magana kema kina yi " ni kuwa sai cewa nake kyaleni inci mata mutunci, iskancin su kara yawa yake a gidan nan suyiwa uwar mu su mana, basu bar kowa ba " ita kuwa lami sai cewa take ubanki shine dai dai dake bari yadawo da shi zan hada ki. Da daddare muna zaune kofar dakin mu muna baran gyada kasancewar lkcn zafi ne, " baffa ne a gaba lami na biye da shi suka shigo sashin mu ko sallama babu, kaina ya nufa tare da cewa ke er banza yarinyar nan ki fita a idona in rufe, bana son iskanci fa, akan matana sa'o'in kine dazakina masu rashin kunya yanda ranki yake so to wlhy karki yarda nima insaka ki a gaba, kaga illan 'ya'ya matan kenan ai, daga zaran sun fara balaga sai suna ganin kamar kansu daya ne da iyayen su....hakanan yakaraci fadan sa lami na tayashi babu wacce tace musu ko uffan agun kowa ci gaba yayi da baran gyadan sa snn suka gama suka kwashi kuransu da burin kunyar su sukayi gaba, don ko suma sunji wani iri da sukaga babu wanda yakulasu cikin mu
** ** ** ** 
Yammacine mai matukar dadi yayinda iska yake kadawa ta ko ina, da alamu dai kamar ruwan sama ne zai sakko, a hankali na fito daga gida don zuwa aikan ammi data min zuwa gidan mai unguwa don karbar aika a gun umma wato amaryar mai unguwa,umma kawar ammina ne sosae umma yaran ta biyu ne agidan mai gari ya Umar ne babba yana mkrnt a futy dake cikin jimeta, yana ajin karshe kenan kuma shine saurayin adda Fauzy wanda ake sa ran zata aura, domin har ya kai goron tambayar sa, sai hafsy datake kawata ajin mu ma daya a boko da islamiyya kawata ce sosae duk garin an sanmu tare, yayin da uwar gidan mai gari wato asabe wacce ake kira da goggo yayar lami ce matan baffan mu, uwar su daya uban su daya, ita kuwa goggo tana da yara bakwai ne a gidan maigari mata uku maza hudu . Ina fitowa naci karo da adda maryam da uncle Aliyu suna zaune a dakalin gidan mu, da fara'ta na karasa inda suke, Uncle Aliyu copper ne daya taba zuwa yin TP daga yola, tun da yazo ya koyar da su adda maryam shikenan ya makale mata shima yanzu haka har sadakin sa yakawo, jira kawai ake suyi waec, da kuma ya Umar sukawo nasu sadakin sai asaka rana don baffa yace tare za a hadasu da adda Fauzy " cikin nutsuwa muka gaisa da shi, mukadanyi zolaye zolayen mu da shi dayake yana da son tsokana, kuma mun saba wasa dashi sosae, " snn nayi wucewata zuwa inda na nufa, banyi tafiya mai nisaba mukaci karo da hafsy itama tafito aeka zata gida, nace a'a kawata daga ina " murmushi tayi tare da kamo kafadu na snn tace na fitowa umma aikane, yanzu kuwa nake tunanin in bi gidan ku sai kuma gashi mun hadu anan, " nima murmushin nayi snn nace ni kuma gidan ku na nufa, zanjewa ammi aika " cikin annashuwa tace to ae shikenan sai muje," ibroro ne yayi saurin shan gaban mu tare da cewa yauwa khairat kamar kinsan ko ina son ganin ki wlhy " harara na daga mai snn nace banason iskanci ibroro inma kana son ganina me zai hanaka zuwa gidan mu, sai munzo layi kafin zaka kama tare mu " cikin sauri hafsy tace aishine fa neman yasa a raina mu " tsaki muka jaa a tare snn na kamo hannun ta mukayi saurin shige shi " tsayawa yayi yana kallon su yace kai khairat da hafsy akwai rigima...... A hankali muka doshi kofar gidan su hafsy, wata farar mota muka gani ajiye agun hadaddiya tagani ta fada, ga mutane nan agun" a hnkli nace hafsy kar dai mai unguwa yayi baki ne " hafsy tace da alama kam, mu dai karasa mugani.
.
'YA'YA MATA page 4

A hnkli nace hafsy kar dai mai gari yayi baki ne " hafsy tace da alama kam, mu dai karasa mugani. Sannu a hnkli muka karaso kofar mai gari, munci sa'a kuwa kafin mu iso mutanen sun shiga falon mai gari, cikin sauri muka shige cikin zauren don kar mu hadu da kowa, muna shiga mukayi kicibus da Aysha da Hauwa a cikin zauren, Aysha da Hauwa 'ya'yan goggo ne uwar gidan mai gari, suna zauna ne tare da wani matashin saurayi zai kai kimamin shekara ashirin da takwas ko da tara haka, ba fari bane kuma shi ba baki bane, chocolate colour, kyakykyawa da shi ga hancin shi har baki, wani kwan tacciyar sajece a kwance a gefen fuskar sa, ga bakin sa dan madai dai ci dashi, yana zaune a kasa sun shin fuda mai wata katuwar dadduma ga kulolin abinci nan a gaban sa, Aysha ce agefen sa ta dama yayin da Hauwa ke zaune gaban sa tana diba mai abinci a plate " dara daran idonsa farare ne ya daga su ya kalle mu da su, tare da sakar mana wata lallausar murmushi, " cikin sauri hafsy tace laaa BARRISTER SADDIQ, kaga yayan mu kuma barrister, yaushe kazo ya Saddiq " shima cikin farin cikin ganin ta yace ba yawo kika tafi ba, tun shekaran jiya nagayawa Hauwa tagaya miki ina zuwa amma kika kama hanya kika tafi yawo ko, sai na kama ki na kulleki a kotu ae " dariya mukayi duk kan mu sabanin Hauwa da Aysha da suka hada fuska kamar basa gun, " hafsy ce tace laaa wlhy ya Saddiq bata gaya min ba, ban san zakazo ba wlhy " a hnkli ya juya ya kalli Hauwa snn yace banace ki gaya mata zan zo ba " kada idon ta Hauwa tayi tare da cewa na mance, " baice mata komai ba snn ya juya yadan zolayi hafsyn suka kuma yin dariya " murmushi nayi tare da risinawa cikin sanyin murya nace mai ina wuni, "sai a lokacin ne ya ankara ashe da wata agun a hnkli shima yayi mata murmushin snn yace lafiya kalau, " hannuna hafsy tarike tare da cewa bari mu shiga ciki ya Saddiq " shiru taji yayi bai amsa ba " da sauri suka kalli inda yake kallo suka ga ashe khairat yake kallo, ita kuwa khairat idonta na kasa tana wasa da yatsun hannun ta" mai maita maganar tata tayi snn ya ankare tare da sosa keya yace to shikenan sai na shigo " to kawai hafsy tace mai snn taja hannuna muka wuce ciki. . Kai tsaye muka shige dakin umma, bata dakin don haka muka samu bakin gado muka zauna, " a hnkli nace kawata wannan waye ne haka " murmushi tayi snn tace dan yayan mai gari ne wanda suke abuja " cikin sauri nace ohhh wanda kuke zuwa hutu gurin su " ehh tace min tare da cewa ae yatafi makaranta kasar wajene ma shiyasa baya zuwa amma da zaki sanshi " nace mata Ayya yanzu yagama ne " hafsy tace ehh har yafara aiki ma, bakiji nace mai barrister ba, ai low yakaranta " kada kafada nayi snn nace to meyasa naga su Hauwa sai hararan mu suke tunda muka tsaya agun, kinsan fa ni banna daukar wannan rainin " dan dariya hafsy tayi tare da cewa karki damu kawata, wai son shi suke shine basa son ko wacce budurwa tana mishi magana, sbd sunga muna wasa da dariya da shi shine suke kishi da ni " da sauri na dafe kirji tare da cewa dukkan su kuma, to wacece zata hakura wacece bazata hakura ba " kada kafada hafsy tayi tare da cewa shifa duk baisan sunayi bama, kuma su inma suna kishi da junan su a kanshi " shiyasa kikaga ban fiya shiga harkan sa ba, kinsan bawai ina son rainin bane, balle wata yarinya taga ina mai shishshigi tadauka nima sonshi nake irin su, ni tsakanina da shi shine en uwan taka shine kawai, amma in ba haka ba babu komai, kuma kinsan mai ya daga musu hnkl " nace a'a " hafsy tace kallon da yayi miki, yanzu Zakiga sun dauki kishi da gaba sun daurawa kan su " zaro ido nayi tare da dafe kirji nace ni kuma. 

Zaro ido nayi tare da dafe kirji nace ni kuma " kai takada min alamar ehh " snn nace tabb ni kuma kinsan ba wai na iya gaba bane sai dai in suka min infito fili infada masu, toma ninawa ame daza a hada dani, na farko ni bansan shiba, hasalima yau na taba ganin shi " murmushi hafsy tayi tare da dafa kafadan ta snn tace ki kwantar da hnkli ki kawata naga har hnklin ki yatashi, inma sukayi gaba da ke ba sai kin kula su bane kafin zakisan sunayi, kuma ni ina rokon Allah ma yasa yace yana son ki inga yanda zasuyi, wlhy bakaramin dadi zanji ba " tsaki naja tare da mikewa daga gadon snn nace Allah ya sauwake ni kuma idan yace yana sona sai insoshi kenan, tabb Allah ma ya kiyaye in hada kishi da jinin lami, yanzu ma yaya muke kayawa da ita a gida balle kuma aje ga na auri wnda ersu take so ai sai abin yafi haka " mikewa hafsy tayi tare da cewa to sae me, don sunyi kishi da ke, ae sai ka kaine akeyi da kai " don Allah mubar maganar nan kar raina ya bace, muje kirakani gun umma inkarbi sako zan koma gida " murmushi hafsy tayi tare da cewa dadina dake kawata saurin fushi wlhy, . yanzu meye abin fushi anan " baki na murguda mata tare da cewa bansani ba, ni dai tashi kirakani gunta, " mikewa tayi tare da cewa to muje karki cinye ni, " a kicin muka taddata narisina na gaidata snn taban aikan tare da sakon gaisuwa snn muka juya muka nufi zauren " a gun muka kuma tadda su, fuska ta a hade snn idona a kasa nasaka kai zan wuce " cikin sauri yace a'a kanwata har kawar taki zata tafi ne " murmushi hafsy tayi tare da cewa ehh zan rakata ne, " a hnkli yace to sai anjima bakuwa, " ko uhun bance ba naci gaba da tafiyata , " kamo hannuna hafsy tayi snn tace kawata ana miki magana, " murmushin da bai kai zuci ba nayi snn nace na'am, " cikin sassanyar murya yace to baki gayamin sunan kawar taki ba " a hnkli hafsy tace sunan ta KHAIRIYYA " yace wow sunan mai dadi kuwa yayi kama da fuskarta... 

Cikin sauri Hauwa tadaga kai ta kalleshi taga shi ko ajikin shi, sai ma murmushin daya karamai kyau da kwarjini a fuskarta yaketayi, nan da nan taji wani gululun bakin ciki ya tsaya mata a rai " shi kuwa sai kallon kyakykyawar fuskar khairat yakeyi, " a fusace Hauwa ta mike tayi cikin gida, dukkan su suka bita da kallo snn hafsy taja hannuna tace masa Barrister bari inrakata tana sauri ne, " a hnkli yace to adawo lafiya kanwata, " murmushi ta masa snn suka fita, " suna fita nace kinga kin jawo min raini ko, zakisa yarinya ta raina ni a banza a wofi, ni kuwa kinsan zanci mata mutunci ne a banza babu ruwana " ajiyar zuciya hafsy tayi tare da cewa ki kwantar da hnklin ki kawata babu abinda zai faru insha Allah " hummm Allah yasa nace " snn muka cigaba da tafiyar mu, har kusa da gida tarakani snn tajuya don komawa gida
** ** ** ** 
Bayan kwana biyu da faruwar hakan ne ina kicin don daura abinci kasancewar yau ammi ke da girki, " Hauwa ce tayi sallama batare da na kalli inda take ba na amsa, itama bata kalli inda nakeba tayi gaba abinta, dakin lami ta nufa kaitsaye, " bayan kamar minti shabiyar da shiganta 15mnts sai gasunan sun fito a fusace lami ce a gaba Hauwa na biye da ita a baya. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment