Monday, 4 December 2017

'Ya 'Ya Mata Page 5&6 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YA'YA MATA page 5 & 6
.
Bayan kamar minti shabiyar da shigan ta sai ga sunan sun fito a fusace lami ce a gaba Hauwa na biye da ita abaya, kaina suka nufo, nagansu sarai amma na kau da kai nacigaba da wanke waken da nakeyi" ke matsiyaciya, kariya, macijiya wacce bata ramin kanta sai na wani, yanzu daman ashe har kwantan kin ya kai kifara bin samarikan Mutane, baza ki tsaya su ganki suce suna so ba, sai dai ke ki gansu kice kina so, to aaa hiiirrr inki da barrister Saddiq mun rigada mun daukeshi mun bawa er mu, sai kiyi hkr kinemi naki amma wannan kam yayi miki nisa " Hauwa tace ingaya miki umma kinga wani kallon da ta masa ma, har da wani cin kwalliya tazo, kuma wnn munafukarce hafsa ita tazo ta gaya mata, suka hada baki sukaje " lami tace itama hafsan zanje har gida in tadda ta saina ci mata mutunci " ladidi ce tafito ta taddasu agun snn tace yaya ke da wa kike ne tun dazu nakejin hayaniyar ku " lami tace ni da wannan er kunikan nake" ladidi tace wacce kenan " lami tace khairiyya mana" nan da nan na dago tare da cewa wace khairiyyan kike fadi " a fusace tace ke nake fadi ke khairiyya ake fadi akwai abinda zaki min ne ? " cikin gadara nace au daman dani kuke, to aeni ban saniba na dauka ciwon kune yatashi ae kukazo kuke ta haushi, to ina jinku ko za ku iya maimai tamin abinda kuka fada don kuwa banji ba, sbd ban dauka dani kuke ba shiyasa ban mai da hnkli naji bayanin naku ba, to amma tunda yanzu kunce da khairiyya kukeyi to ina jinku kowa tafadi albarkacin bakinta in kuma bata amsa dai dai da mgnr ta. . Kowa tafadi albarkacin bakinta snn kuma in bata amsa dai dai da mgnr ta, " kallon kallo sukeyi tsakanin su ukun, lami ta kalli Hauwa, . Hauwa ta kalli ladidi, abin sai basu mamaki yake don ganin irin rainin hnklin da khairat ke shirin musu, kusan mintin su biyar a hakan " cikin sanyin murya nace to tunda baku da abin fada bari in baku guri don ni ina da abinyi, bokitin wakena na dauka tare da jawo hijab ina na nufi waje don kai markaden waken, wani mahaukacin dariya ladidi ta sake tare da tafa hannu, har kasa ladidi takai don dariya, su adda mrym da suke wanki a gefe suma dariyar sukayi " nan da nan ran lami kuwa ya baci ae sai fada yakoma kan ladidi, zage zage take tayi ta ko ina, duk wanda suke gun sai dasuka karbi nasu rabon zagin, dataga abin banayi bane, taga kowa inta zageta sai ta kwashe mata da dariya sun mai da ita kamar mahaukaciya, kawai sai ta ja hannun Hauwa da ta tsaya kamar gunki tarasa abin fada, sukayi waje abin su. . Kawai sai taja hannun Hauwa data tsaya kamar gunki tarasa abin fada, sukayi waje abinsu..
** ** ** ** 
Bayan sati guda da faruwar hakanne ina zaune a cikin dakinmu ni da adda juw, sauran duk basa nan, ammi kuwa ita keda girki don haka tana cen gefen baffa "hafsy ce tayi sallama tare da shigowa ciki, " murmushi muka sakarwa juna, snn tanemi gefe na ta zauna, ta gaida adda juw, snn ta juyo ta kalleni tace kawata me kikeyi ne " girgiza kai nayi tare da cewa babu komai " ajiyan zuciya tayi snn tace zo kirakani wani gu " cikin kasala nace ina kuma, ke kam kina da son wahalar da mutum, gaki da shegen yawo " . hada fuska tayi tare da cewa in bazaki rakani ba basai kin gaya min banzan magana ba, sai anjima, ta yunkura zata mike "da sauri na jawo hannun ta tare da cewa yi hkr kawata bari in dakko hijab ina " murmushi tayi tare da cewa yi sauri to don Allah " cikin zolaya nace to kar kuma ki uzulzula min mana malama " tsaki taja snn tafice waje tare da cewa kisameni a waje " dariya nayi snn na dakko hijab ina na dan goge fuska ta da sosar powder na dau man baki na shafa snn na fito, a tsaye na tadda ta, " harara na tayi tare da cewa ohhh daman kwalliya kika tsaya yi ko, " murmushi nayi tare da cewa man baki kawai na shafa nikam karki balbaleni da masifa.
.
Murmushi nayi tare da cewa man baki kawai nashafa nikam karki balbaleni da masifa. Hannuna tajawo tare da cewa ni kam muje kina bata mana lokaci, " ban ce mata komai ba nabi bayanta " hanyar makarantar mu muka nufa, " a hnkl nace kawata wai ina zamu ne " hafsy tace wai me kike sauri ne kam ai za dai muje ko, kinsan dai ba yankan kai nakeba balle kice zan kaiki ne a yanke miki kai " cikin zolaya nace to nasani ko kin fara yanzu" kafadata ta dan buga snn muka sheke da dariya " sannu a hnkl muke tafiya har muka iso cikin harabar makarantar, kasancewar mkrntn kauye ne, ko katanga babu ajujuwa ne kawai akewaye da filin , daga nesa na hango wata farar mota, kwata kwata hnkli na baice cen zamu ba, amma ga mmk na sainaga mundoshi inda motar take, cikin nutsuwa nace hafsy suwaye acen in" hafsy tace me kike sauri ne, bakiga gun muka dosa ba " cikin tashin hnkl nace bangane ba hafsy me kike nufi " dariya tayi tare da cewa dadi na dake gajen hkur, gaki da shegen tsoron tsiya " muna cikin maganar ne har muka iso gurin da motar take, " a hnkl naga an bude kofar motar, " gaba nane yafara dukan uku uku, nan da nan zufa ya hau karyo min. . Gaba nane yafara dukan uku uku, nan da nan zufa yafara karyo min A hnkl ya sauke kafar sa akasa tare da fitowa, dayan kofar motar aka bude, a tare suka fito, " murmushi yasakar min tare da cewa ranki shi dade, " nan da nan naji raina ya baci, fuska na hada tare da kawar da kai gefe " cikin sanyin murya yace malama khairat sannu da zuwa, " shiru nayi na kada ido tare da murguda baki, na kau da kai gefe " cikin sanyin murya yace lafiya kuwa khairiyya, " cikin sauri hafsy tace hummm kasan kawar tawa sai a hnkl, tunda take a garin nan bata taba hira da kowani saurayi ba, shiyasa kagan ta haka " dariya barrister Saddiq shida barrister faruq sukayi sosae, snn daga bisani yace to shikenan naji khairat amma don Allah kidan bani minti biyu ina son zan danyi magana dake " nan ma shirun nayi " a hnkl ya dubi hafsy yace kanwata kudan bamu guri kadan " hafsy da barrister faruq ne suka ja gefe suka ci gaba da nasu hiran " a hnkl ya matso inda take snn yace khairat nidai ba wani abu bane yakawoni illa in fayyace miki abinda ke cikin raina, tun randa nafara ganin ki a gsky kika sace min zuciyata " zaro ido nayi tare da dafe kirji snn nace nasace maka zuciya kuma, a ina naganta balle in sace ta, tunda nake ni ban taba sata ba, shine yanzu zaka min sharrin sata, nan da nan idona yaciko da hawaye zanyi kuka, don tunda nake bantaba tsoron mutum ba irin barrister Saddiq, haka kawai yake min gizo a idona, tsoro yake ban bana kadan ba, " katsemin tunanina yayi da cewa, innalillahi wa inna ilaihirrahi'un, ya fadi tare da dafe kai, snn yace khairat baki fahinceni bane, ba haka kalmar ke nufi ba " fuuu naja hijab ina nabar gurin da sauri ina sharar kwalla.
.
'YA'YA MATA page 6

Ba haka kalmar ke nufu ba khairat " fuuu naja hijab ina nayi gaba " da sauri hafsy tasha gabana tare da rike hannuna, snn tace lfy kuwa khairat, meyafaru " fizge hannu na nayi tare da yin gaba " da sauri ta sake kamoni, dai dai lkcn barrister Saddiq da brr farruq suka iso gurin " . cikin tashin hnkl brr Saddiq yace don Allah kiyi hkr khairat, wlhy inda nasan in nagaya miki hakan zai bata miki rai wlhy da ban fara ba amma don Allah kiyi hkr kuma insha Allahu wnn shine na farko kuma shine na karshe, insha Allahu irin wnn maganar bazai sake fitowa daga bakina ba, kuma yanda kike zato ba hakan yake ba wlhy " a hnkl hafsy tace don Allah kiyi hkr kawata " brr farruq shima cewa yayi don Allah kiyi hkr khairiyya " shiru nayi tare da turo baki, ina kallon wani gefe " barr Saddiq ne yayi ta bani baki tare da lallashina, da kyar yasamu yashawo kaina, nadan samu nasaki fuska " tunda yaga lkc daya na rikice ne, yasa shi cewa hafsy yanzu abinda za ayi kuzo mu mayar da ku gida ko, hakan inaga zaifi " kama baki hafsy tayi tare da zaro ido, snn tace waa ai kayi tafiyar ka kawai mukam zamu koma " cikin sanyin murya yace to shikenan hafsy sai mun hadu a gida ko, " to kawai tace mai tare da jawo hannuna muka bar gurin, munyi nisa sosae kafin barr Saddiq yabar gurin, yashiga mota yajata suka tafi. Munyi nisa sosae kafin brr Saddiq yabar gun, yashiga mota yaja suka tafi Muna tafe a hanya najuya na kalli hafsy snn nace hafsy gsky baki kyauta min ba, yaza'ayi kin san niba kula saurayi nake ba amma kikama ki dakko ni kikawoni gurin shi bayan kinsan yanda en gidan ku suke, " cikin nutsuwa hafsy tace haba khairat, mutumin nan tun randa yafara ganinki ya ishe ni da zancen ki, harya koma gida fa yaga bazai iya ba yadawo, amma gsky in kika min haka baki kyauta min ba, " ajiyan zuciya na sauke tare da cewa amma nagaya miki meyafaru a gidan mu kwamanaki ko, inba dan iskancin da namusu ba kema kinsan da haryanzu ana nan anakan rikicin nan " tsaki hafsy taja snn tace to ni ina ruwa na, ni inma bana gaya miki sunzo sun sameni ba, umma tace inyi banza da su, amma dayazo min da maganar ki bashi ya hanani zuwa in gaya miki ba, kawai abinda zakiyi kije kiyi tunani akan hakan " hummm ajiyar zuciya na kuma saukewa a karo na biyu snn nace to shikenan Allah ya wuce mana gaba " amin hafsy tace, snn suka ci gaba da tafiya" cikin nutsuwa suke tafiya har suka karaso gida, a kofar gida hafsy tabar khairiyya, snn tawuce gida.
** ** ** **
Ranar lahadi ne bayan mun dawo daga mkrntr islamiyya, na kwashi wankin uniform inmu, kasancewar daman nike wanke mana, nafito dashi tsakar gida na zuba su, snn na je na debo ruwa, nafara wankin kenan saiga inna wato kakarmu mahaifiyar baffan mu. . nafara wankin kenan saiga inna wato kakarmu mahaifiyar baffan mu ta taho tare da nata wankin, tana isowa ta watsamin su, snn tajuya batareda tace min komai ba "wankina naci gaba, nima ko kula kayan banyi ba, a inda ta ajiye su agun suke, ko kallon kirki ban musu ba balle in daga su daga cakwabin ruwan da ke gurin, har nagama wankina na shanya, suna gurin nawuce daki abina Ladidi dake gurin tun tuni komai akan idonta akayi, batayi kasa agwiwa ba don zuwa tseguntawa inna abinda ke shirin faruwa " inna batayi wata wata ba ta tattaro bala'i da masifar ta tasako ladidi agaba suka nufo gefen mu " tun daga nesa naji tasaka salati snn tafara ina shegiyar yarinyar nan take, wai wnn wacce irin annabon yarinya halliru ya haifa min ne, wai ke wacce irin er iskace kam, wato uwarku ce ta ke kitsa muku munahurci ko, to wlhy baki isaba Indo, nida jikokina, naga dama ne fa kike zaune a gidan nan, kinzo kin cika mana gida da 'YA'YA MATA daman meye amfanin YA'YA MATAn in ba bautuwa ba, mu kinsan irin bautuwar da mukayi a gidan mu, shine zaki hana naki yaran bautuwa mana, to wlhy baki isaba, bari hallirun yadawo wlhy yau sai ya sakeki a gidan nan ko kuka in daga masa nono wlhy don kuwa nagaji da ganinki tun tuni a gidan nan " ammi dake cikin daki nan da nan hawaye yafara gangaro mata, hnkln mune yayi mugun tashi ganinta tana kuka " a hnkl nafito daga dakin, wani mugun kallo nafara sake mata snn nace. 
.
A hnkl nafito daga dakin, wani mugun kallo na mata snn nace " to kisa asake tan mana indai zamanki take agidan nan, wlhy da kinga tashin hnkln da baki taba ganiba arayuwar ki, wlhy inna kifita a idona in rufe, ma uwar waye kikayi mgn da kika kawo wankin naki, ko ance miki zaman ki nake ne da zaki kama kizo ki watsa min wanki kiyi gaba, ashe dai ya'ya matan suna da amfani tunda har ana iya zuwa awatsa musu wanki ace su wanke, to wlhy kar in kara ganin wannan kafarki me kamada taliyar tashigo nan gefen dasunan kinzo amiki wani abu, don kuwa watarana sai na karya kafafuwar ki ingaya miki " ihu inna tasake tare da faduwa kasa tasaka kuka tana birgima wai nazagi uwarta, "tunda nake babu wanda yataba zagin uwata sai ke to wlhy bari halliru yadawo yau duk sai ya batattare ku agidan nan wlhy bazan iya zama da kuba " adda Fauzy ce tayi karfin halin cewa to idan yadawo kice masa karya barmu da rai " adda hamdy tace wlhy kuwa " adda juw ce tafito daga bayan gida da buta a hannun ta, dai dai inda inna ke zaune sai birgima take add juw tafito tare da taka kafanta, "salati inna suka saka tare da ladidi, mmk ne ya cikasu don ganin irin rashin mutuncin da muke shirin yiwa inna, kutun tuma ashar tashiga yimana, batabar kowa ba tun daga kan mahaifiyar ammi tafara har sai da ta iso kaina, babu wacce tabari, " adda maryam ce da tun tuni take zaune take kallon mu batare da tace komai ba, sai a lkcn ta tashi ta dauki wani kara tayi kan inna dashi, " inna dake zaune tana ihu, dataga adda maryam tayiyo kanta da kara, tuni tamike har rige rigen fita suke ita da ladidi " suna fita muka sheke da dariya. . Ammi dake cikin daki tun tuni batare da tace komai ba, ta share hawayen da ke gaggarowa akan kuncin ta snn tace don Allah kurufamin asiri yanzu idan baffan ku yashigo duk laifin mani zai bayar, meyasa kuka kulata, ae da kun barta tayi tayi, tagaji tabari, wani hawayen ne yakuma zubowa daga idon ta " cikin tashin hnkl adda Mrym tace don Allah kiyi hkr ammi wlhy muma ba'a son ran mu mukayi hakan ba, mun gaji ne da cin kashin da ake akan mu, ya ishemu ne haka shiyasa kika ga har mukayi magana, ammana don Allah in abinda mukayi yabata miki rai to kiyi hkr " adda Fauzy tace to yanzu yazamuyi da baffa idan yadawo, kunsan sharrin da zata fada masa, karya da gsky duk zata gaya mai " adda hamdy tace wlhy nima shine tunani na " adda juw tace to yanzu meye abinyi " ajiyar zuciya na sauki cikin kwanciyar hnkli, snn nace musu kubar komai a hannuna, kubarni da shi " da sauri ammi tace me zakiyi khairat " cikin sanyin murya nace babu komai ammi, Allah dai yadawo dashi lfy, inan ina zaman jiran isowar sa Cikin sanyin murya nace babu komai ammi, Allah dai yadawo dashi lfy, ina nan ina zaman jiran isowar sa.
** ** ** ** 
Muna kwakkwance a daki muna ta tadi kamar babu abin da yafaru yau a gidan, tun daga nesa mukajiyo sautin baffa yanata kutun tumo a shar, har ya iso gefen mu, shine a gaba inna a baya yayin da matan sa suke goya musu baya, haka suka shigo " kuna ina don uwar ku, kurasa wanda zaku daka a gidan nan sai mahaifiyata, to wlhy bazan lamunci hakan ba, ina uwar kun take, kina ina indo, fito yau daga ke har yaran ki sai kun bar gidan nan wlhy, na sallama ku, iskancin ku ya isheni hakanan, wai kuna inane kam kuka barni ina ta ihu, Indo Indo bada ke nake bane " a hnkl na daga labule na fito tare da kama kugu, hararan su nayi dukka, tare da cewa wai lafiya kake kiran sunan mahaifiyar ya'ya mata kamar kai kasaka mata sunan, to indon batanan ammana ga madadin ta " nan da nan inna tafara gata nan nan halliru, wnn yarinya bakaramar mara kunya bace ita, kaga abinda tamin a gidan nan yau, kawai sai tasaka kuka " munafukai kuwa suka riketa sunata riritata suna bata hkr, hummm lami da ladidi kenan, kamar su in basa zagin ta a gaban idon ta," hnkln baffa ne yakara tashi, hnkl tashe yace ke don uban ki ina uwarki nace " cikin sauri nace masa gani nace maka "mmk ne yacika sa, nan da nan ya kuma cewa to idan kin shiga ciki kicewa uwarkun tatafi gida nasaketa saki daya. 

Duk da hnkl na yatashi dajin kalaman sa ammana bai sakani karfin halin cewa to shikenan kuwa itama ta huta da wnn jarabebben auren taka, ae da aure irin naka wlhy gwanda babu, kuma na maka alkawarin kai da kanka zakaje har inda take ka kuma dawowa da ita kan ya'yan ka mata, taci gaba da rainon ya'yan ka mata, har sai randa zaka gane cewa YA'YA MATA MA RAHMA NE " a fusace yace to idan tatashi tafiya kema kibita don kuwa kema na yafeki kije kawai, daman ya'ya matan sun min yawa " cikin tsiwa da rashin kunya nace wlhy babu inda zani sai dai kayi hkr, ko kuma kai ma katafi gidan ku, ammana ni nan gidan mu ne, a nan aka haifen snn kuma a nan natashi, a nan kuma nayi wayo, kuma tun tashina ake cewa nan gidan ubana ne, don haka ko yau ka mutu ina da gado mai tsoka agidan nan wlhy " . baffan shima rikicewa yayi wai ina masa fatan mutuwa don inci gado, baffa har da kuka " dakyar munafukan matan sa suka jasu sukayi waje da su, har yafita yadawo yace kar ammi takara ko minti 30 agidan sa, yasaka kai yafita A daki na tarar da inna na kuka, su adda maryam suna bata hkr, " cikin kwarin gwiwa nace ammi ki kwantar da hnkln ki, namiki alkawarin insha Allahu nan da sati daya zaki dawo kan mu, don kuwa nasan abinda kikewa kuka kenan, daman inason inji yafurta miki saki tun tuni, sbd ina shirin ai watar da wata aiki, ammana dole sai an sake ki kafin hakan zai yuyu, ammana yanzu burina yafara cika insha Allahu tun da baffa yabudi baki yace yasake ki, to komai yazo karshe insha Allahu, snn kuma duk wani hantaran mu da kyaran mu da ake agidan nan yayi kusan zuwa karshe" dukkan su suka daga ido suna kallona, mmk na yacikasu, sun dauka ko zan dan nutsu tunda naji an saki ammi, ammana sai kuma sukaji ina basu lbr sabanin hakan, " adda Mrym ce tayi karfin halin cewa kina nufin da saninki aka saki ammi " sosae ma kuwa, amsar da nabata kenan " cikin hadin baki sukace to yanzu me kike shirin yi kenan khairat, menene abinyi " murmushi na musu snn nace. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment