Monday, 4 December 2017

'Ya 'Ya Mata Page 7 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'Ya 'Ya Mata Page 7 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI
Cikin hadin baki sukace to yanzu me kike shirin yi kenan khairat, menene abin yi " murmushi nayi snn nace me kuke sauri ku kwantar da hnkln ku, nafison sai na aiwatar da abun kafin kuji ta " a jiyar zuciya adda maryam ta sauke, snn tace to shikenan khairiyya Allah yasa muji Alkhairi " amin suka amsa da shi dukkan su. " najuya na dubi ammi snn nace yanzu abinda za'ayi ammi, baza ki wuce garin ku ba tukun, kifara zuwa gidan kawu sale, kafin nan da sati guda, inyaso lkcn na aiwatar da abinda nake shiri, to kinga sai ki dawo ba tare da anyi hasarar kudin motar ba, " to kawai ammi tace min" muka hada mata dan kayan ta akaramin jakka, snn muka rakata har gidan, bamu dawo alokacin ba sai da mukayi sallar magriba. " muna shigowa gida mukayi arba da su a tsakar gida, kajine a gaban su sunaci, suna kallon mu kuwa suka sheke da dariya, lami har da hawaye, babu wacce tace musu kala, muka wuce mukayi dakin mu " adda juw ce tace wlhy yunwa nakeji ammana nasan yanzu ina tambayar abinci zasuce basuyi da mu ba " nan da nan naji zuciyata tana tafarfasa nafito cikin bacin rai, babu alamar dariya a fuskata, ina fitowa kaina tsaye nayi kicin in, hummm shinkafa da miya ma suka dafa sai kace ana wani gagarimin biki a gidan, harda lemun kwalba suka siya, sai kace ranar sallah nakai kusan minti biyar a kicin in sannan na kaftari abincin mai mugun yawa a babban tire, snn na watsa mana miya harda naman shanu aciki, nafito na wuce daki da abincin, kallona suka tsaya yi, suna mmkn irin karfin halin da nake dashi, suna cikin tunanin ne kuma sai gani na dawo, dakin ladidi na nufa. . Dakin ladidi na nufa, don kuwa nasan acen ne za a ajiye lemun kwalban nan, sbd ita ke da girki, basu gama mmkn wancen ba sukaga nashige dakin ladidi na fito da kwalaben fanta guda biyar, biyu a hammata, uku a hannu, kaina tsaye zan wuce dakin mu, ladidi ta kutun tumo wani a shar, ta dako tsalle daga inda take ta iso inda nake, harda kama kugu, ammana dataga fuskata taga babu alamar dariya a tattare dani, nan da nan naga fuskar ta ta canja, ammana sbd tsabaragen karfin hali yasata tace min "uban waye yabaki izinin shiga min daki har ki dauka min lemun kwalba, " budar baki na kuwa nace mata uban kine yabani izini, ko kuma uban kine ya sayi lemun kwalbar, ke kinsan Allah idan baki bani guri na wuce ba ko to wlhy zan fasa kwalba daya na soka miki aciki, kinsan dai ba wai inada hnkl bane ko to kibini a hnkli " nan da nan kuwa ladidi ta matsa tare da cewa ehh nasani kam, jeki, " daki na wuce abina " ina jin lami nacewa kin bani mmk wlhy ladidi yanzu yarinyar nan har zata razanaki ki matsa mata, wlhy in nice da girki wlhy baza su sha ba, sai dai suci abinci " ladidi tace ummm yaya bakisan tsautsauyi bane shiyasa, kibari ranan girkin ki sai ki kuskuri yi mata hakan inyaso sai in koma insha kallo, " wani gululun bakin ciki ne yatsawa lami a rai, karshe dai basu watse agun ba har sai da sukayi fada, baran baran aka watse a gun. . Karshe dai basu watse agun ba har sai da sukayi fada, baran baran aka watse a gun.
** ** ** ** 
Bayan kwana biyu ne da faruwar hakan, ina zaune da daddare bayan kowa na gidan ya kwanta, misalin karfe 12, nafito a hankali kicin na nufa, ina shiga na nufi inda baffa ke ajiyar wukan sa wanda yake yanka ragon sallahr Lahiyan sa dashi, na jawo wukar doguwa ce kuwa, na maidata gidan ta tare da yin wata muguwar murmushi, snn nafito a hnkl nake tafiya, sashen inna nanufa, kofar dakinta a kulle, nan dan naji gabana yafadi, raina naji yabaci nan da nan, isowa nayi dai dai kofar dakin ina tabawa kuwa najita abude, ashe tokarewa tayi da dutse, muguwar murmushi nayi snn na nakama tura kofar a hnkl nasa kai nashige, na mayar da kofar na rufe ta, tana kwance a kan katifarta na tuntun sai gwarti take zubawa, a hnkl na karasa inda take kwancen, nasaka bakin wukan nafara bubbugata da shi, a razane ta tashi, zatayi min ihu kenan, da sauri nazare wukan daga cikin gidan sa nasaka mata a wuya, snn nace kina min ihu wlhy zan yanka ki, kuma in mayar da wukan in ajiyeta a inda ake ajiyewa yanda babu wanda zai san da wata wuka aka yanka ki, kuma infi kowa yin kukan mutuwar ki, snn intaya masu bincike yin binciken wanda ya kasheki, inace dai kinsanni kinsan bawai ina da imani bane ko " a hnkl inna ta daga kanta alamar ehh tare da cewa ehh nasani, jikinta na rawa muryar tama tana rawa tace min don Allah kiyi hkr ennan karki kasheni " murmushin mugunta nayi tare da cewa a zuciyata kai inna akwai ta akwai tsoron mutuwa, bata kaunarta kwata kwata. 
.
Murmushin mugunta nayi tare da cewa a zuciyata kai inna akwai tsoron mutuwa bata kaunarta kwata kwata, gashi kuma ta kusan gan garawa, ita ko kallon tsufarta ma batayi " cikin nutsuwa nace bakya son ki mutu ko, " da sauri tace ehh wlhy ennan banason in mutu yanzu ko kadan " murmushi nayi tare da cewa to shikenan ki kwantar da hnkl ki bazan kasheki ba, amma sai kin min wani abu, in kika min in barki in kuwa ba zakiyi ba wlhy yanzun nan zan kasheki kuma infi kowa kukan mutuwar ki yaseen " cikin hanzari da son jin me zance inna tace na miki alkawari ennan ko me kike so wlhy wlhy zan miki indai bazaki kashe ni ba " a hnkl nace bazan kasheki ba indai zaki min abinda nace miki " inna tace to kuwa ina jinki ennan " a hnkl nace gobe da safen nan nakeson kisaka baffa yaje yadawo da ammin mu " tsaki inna taja tare da cewa. Tsaki inna taja tare da cewa haba ennan yanzu akan dan wannan maganar ne har zaki dauki wuka kisakamin inda kinzo kin gaya min da bakin kima da yafi, yanzu duk kinzo kin razanani inaga ma yau haka zan wuni ina guduwa, . ai kin ruda min ciki dayawa, to yanzu abinda za ayi gobe da safen nan zan sami halliru ince mai yadawo da Indo tun kan raina ya bace, ae indai Indo ce to kamar ta dawo gidan halliru ne " da farko danaji inna tayi tsaki gabana bakaramin faduwa yayi ba, ammana daga baya danaji akalar zancen nata ta canja sai naji wani farin ciki ya cika ni, ammana sai ban gwada mata ba, sai cewa nayi to ba anan abin take ba, nakara manna wuyarta da wukan, hawayene suka shiga gan garowa daga idon inna cikin rawar murya da muryar kuka tace to ennan sai me kuma, bayan nace zanyi wannan in " cikin iko da nuna kamar nice gaba da ita nace idan ta dawo, kije kice ma baffa da matan sa, zancen hantara ko kyara ya kare, wlhy idan ta dawo kuka ci gaba da hantaran mu to kuwa wlhy dawowa zanyi in kasheki kowama ya huta don kuwa kece me hada fada a gidan baffa " murya na rawa tace wlhy na daina, kuma zanyi duk abinda kika ce don Allah kiyi hkr ennan " farin cikene ya kamani, ammana sai ban gwada mata ba sai cewa ma danayi, ohon miki inma bakiyi bama nikam kasheki zanzo inyi kawai mu huta da bala'in ki a gidan nan, " to sai kuma abu na gaba " inna ta zaro ido tare da cewa ina jinki ennan " murmushi na kuma don ganin nasami kan inna da wuri haka . 
.
Murmushi na kuma don ganin nasamu kan inna da wuri haka Cikin sanyin murya nace kwantar da hnkln ki ba wani abu bane illa idan naji maganar nan abakin wani to wlhy! wlhy!! wlhy!!!, sau nawa kikaji na ranshe, " cikin sauri tace sau uku " nace to wlhy inna saina kasheki kinsan dai bawani imani ne dani ba, ki kiyayeni " cikin hanzari inna tace haba ennan sai kace bani da hnkl yaushe ake hanzarin fadan irin wnn gagarumin magana haka, ae irin su bari ake aciki " cikin razanar wa da kuma gargadi nace mata inna! " inna tace na am ennan " na kuma cewa inna!! "Inna tace na am ennan " nasake cewa inna!!! akaro na uku " inna ma ta kuma cewa na'am ennan " snn nace sau nawa na kiranki " inna tace sau uku " nace to wlhy idan kika fada sai na kasheki " inna tace nace miki bazan fada ba ennan don Allah kiyi hkr karki kasheni " na daga kafada tare da cewa indai baki fada ba menzaisa in kasheki, ammana kina fada zan biyo dare in kasheki in yaso sai in bar garin a daren " inna tace mema zai sakani in fada " nace to kuwa da kin taimakawa kanki " inna tace sosae ma kuwa" na mike na mayar da wukan cikin gidan sa snn nace to sai da safe, Allah yasa inji lbrn nan abakin wani" inna tace a'a wlhy bazakuwa kiji ba " nace tam shikenan ni kam natafi " innatace to ubangiji Allah yatashemu lafiya er albarka, Allah dai yayi miki Albarka, " nayi murmushi tare da cewa amin inna " inna tace do Allah ennan kina da maganin tsayar da gudawane ki bani insha " dariyace taso ta kwubce min ammana na daure nace ehh ina dashi ammana sai da safe zan kawo miki " cikin sauri inna tace to shikenan nakuwa gode ennan " nasaka kai nafita na mayar mata da kofar dakinta na rufe. . Nasaka kai nafita na mayar mata da kofar dakinta na rufe. Washe gari da asuba ne inna na zaune a dakin ta baffa ya shigo gaishe ta, bayan sun gaisa ne har yatashi zai tafi sai kuma tace masa " zo nan halliru, cikin nutsuwa ya juyo ya dawo ya zauna, " tace kasan me nake so da kai " yace a'a " tace to so nake ka dawo da Indo kan ya'yan ta " da sauri ya dago idon sa yakalle ta tare da cewa indon kuma yau " cikin nutsuwa tace ehh indon fa nake nufi " ganin ranta abace take maganan ne ba musu yace mata to shikenan inna karki damu yau innan zan dawo da ita" inna tace snn kuma da sharadin daga yau kar asake muzguna mata agidan nan ita da yaranta, kuma kajawa matan ka kunne idan nasake jin wani abu to lalle ka tabbartar musu da cewa zasuga bacin raina " a hnkl yace insha Allahu babu abinda zai kuma faruwa "cikin annashuwa inna tace to shikenan Allah yayi maka Albarka " amin yace snn yamike yafita tare da mmkn meyasa inna tace adawo da indo, " yana fita inna ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa Allah na gode maka da kasa baiyi min musu ba, ya yarda cikin lumana.
.
Muna zaune ne da yamma kuwa sai mukaji sallamar ammi da baffa, baffa ne a gaba inna nabin shi a baya, da gudu muka fito don tarban ta, sai dai wani abin mmk ma da muka gani shine, jakan kayan ammi ma baffa ne ya rike mata ,Wani abin mmk ma da muka gani shine jakan kayan ammi ma baffa ne yarike mata, kai wnn abu bakaramin mmk yabamu ba, jin muna ihu atsakar gida ne yasa lami da ladidi lekowa don ganewa idon su, me zasu gani inba ammi da baffa ba, mmk ne yacikasu a tsaye agun, sai kuma aka koma kallon kallo kowa da alamar tambaya abakin ta, . ana cikin haka kuwa saiga inna tashigo gefen mu itama, " tafara barka da dawowaaaa barka da dawowa sannunki sannun ki, lale lale, tana fada tana tafa hannu, "wannan abu bakaramin dagawa su lami hnkl yayi ba, harda inna aka rako ammi daki, har zama inna tayi tana tambayar ammi mutanen gida, sai in ta danyi magana sai kuma tasaci kallo na, muna hada ido kuma sai tayi saurin kawarwa, abin ma har dariya yafara bani, amma dai na cije banyi dariyar ba, " bayan inna takaraci zaman tane ta mike tare dacewa bari in barki ki huta " cikin mmkn da yagagara buya a fuskar ammi tace to inna nagode, har kofar farfajiyar mu tarakata snn ta dawo " cikin zumudin jin abinda nawa inna ammi ta dawo cikin sauri tace khairiyya me kikawa inna nagan ta haka, "dariya nayi snn nace cewa nayi saina kasheta inbatace adawo da ke ba, kunsan inna da tsoron mutuwa, " dukkan su dariya sukayi sosae kamar zasuyi yaya, muna cikin hakan ne kuma sai hafsy tayi sallama, bayan sun gaisa da kowa da kowa ne tace min kawata zoki rakani " nan da nan naji gabana yafadi. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment