Monday, 4 December 2017

'Ya 'Ya Mata Page 8 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI

'YA'YA MATA page 8 

Nan da nan naji gabana yafadi, hada fuska nayi tare da cewa ina kuma zamu " ita ma hada fuskar tayi snn tace in bazaki rakani ba kawai ki gayamin " ammi ce tace to ke khairat kitashi kuje mana " zunburo baki nayi tare da mikewa ina kananun magan ganu, jawo hijab ina nayi snn nace mata wlhy in kinsan irin na ranan zaki min ma gwanda ki kigayamin, tun kafin in je in kunyata ki agun " dariya ma abin yabawa hafsy tace to muje dai ae idon ki ya gane miki " tana gaba ina binta abaya a maimakon mufita sai kuma mukayi ban garen inna " nace mata me kuma zamuyi a nan " hafsy tace wai ni me kike sauri ne, muje mana " shiru nayi har muka isa, a dai dai kofar dakin inna ne naga takalma guda biyu masu mugun kyau na en maza, na raya a zuciya ta yau kuma inna ina tasamo baki, bangama tunanin nawa ba muka cusa kai cikin dakin, wa zan gani barrister Saddiq ne shida barrister faruq suna zaune gaban inna ga wasu laidodi nan agaban ta himili guda, sai hangame baki inna take,taga abin duniya salati na sake a zuciyata, snn nafara zaginsa cikin raina, wnn saikace maye, wani irin mayta ne wnn, wama yakawo shi gurin inna ma tukun, waye kuwa inba hafsy ba, wata zuciyar tabani amsa, to wlhy Sai naci mutunci hafsy, ban gama maganar ba na tsinkayi maganar inna tana cemin to ki zauna mana khairiyya " tsaki nayi a cikin raina snn na nemi gefe na zauna .
.
Tsaki nayi acikin raina snn na nemi gefe na zauna, fuskata a hade, babu walwala kwata kwata, inna tayi gyaran murya tace khairiyya ba wani abu bane yasa nace a kiraki ba sai don wnn yaro dan albarka yazo mani da magana mai mugun dadi da kuma alkhairi mai tarin yawa acikin ta, don haka zaki nutsu ne kuyi magana ku fahimci juna a tsakanin ku, don haka Saddiq " da sauri yace na am inna " tace kutashi kuje waje sai kuyi magana koba haka ba" cikin girmamawa yace hakane " tashi yayi yafice, ammana ni ina zaune " cikin rarrashi inna tace haba er albarka tashi mana kije yana cen yana jiranki bawani dadewa zakiyi ba " baki zun bure na tashi na fice " nesa dashi na tsaya na harde hannu, ko kallon inda yake banyi ba, " cikin nutsuwa ya matso inda nake snn yace Cikin nutsuwa ya matso inda nake snn yace haba baby K yanaga ranki a bace waya bata miki rai na ganki haka " ko kunya banji ba nace mai kai ka bata min rai " zaro ido yayi tare da cewa ni kuma " kai nadaga alamar ehh " yace me kuma na miki baby K " murguda baki nayi snn nace bana son kana zuwa guna ne " barr Saddiq yace saboda me baby K " cikin tsiwa nace sbd bana sonka " murmushi yayi snn yace kiyi hkr baby K, ita so bata shiga ran dan adam lkc daya, barin ma keda baki taba so ba, ammana don Allah kiyi hkr kibani dan wani lkc kadan insha Allahu zaki so ni " cikin tsiwa nace Allah ya sauwaka in soka, yau she zan hada kishi da su hauwa gayyan tsiya " sai a lkcn ya fahimci inda ta dosa, murmushi yayi snn yace ki kwantar da hnkln ki babu abinda ke tsakanina da su hauwa illa en uwan taka, " da sauri nace tabb wlhy a kwai, nida hauwa tazo har gida ta hadani da matar babana sukazo suka ci min mutunci wai ina son mata saurayi, kuma matar babana tace anrigada anyi baikon ku da ita, shine yanzu zaka zo ka yaudare ni kace wai kana sona " zaro ido ya kuma snn yace ni in? " 

nace ehh haka tace min " cikin tashin hnkln da fuskar sa ta Gaza nunawa yace wlhy karya ne baby khairat ni babu abinda ke tsakanina da hauwa wlhy, kawai dai sun gaya miki haka ne don karki soni ammana wlhy ba haka bane " tsayawa nayi shekeke ina kallon sa ganin yanda ya gigice lkc daya Tsayawa nayi shekeke ina kallon sa, ganin yanda ya gigice lkc daya, cigaba yayi da maganar sa" wlhy baby khairat ki yarda dani bazan miki karya ba, ki tmby kawarki ma wlhy zata gaya miki gsky, ai inda hafsy tasan cewa an mana baiko da hauwa wlhy da bazata kawo ni gurin ki bama, sbd nasan hafsy tana sonki kuma bazata so abinda zai cuce ki ba, pls baby K ki yarda da batu na don Allah, ammana zan baki lkc kije kiyi bincike kigani, inkin samu da gske ne to ki dau duk matakin da kikaga zaki iya dauka, nabaki wuka da nama, " kada kafada nayi snn nace to shikenan zanyi bincike ingani, innasamu da gske ne to kasawa ranka bazan taba son ka ba har abada " brr Saddiq yace to shikenan ni kuma na yarda " juyawa nayi na koma cikin gida abina kotakan dakin innan banyi ba, " da sallama yashiga dakin inna snn yacewa brr faruq mungama zamu iya tafiya yanzu ae " inna ce takatsemai maganar dacewa ina khairiyyan take, " cikin sanyin murya yace tashiga cikin gida, " inna tace cikin gida kuma " brr Saddiq yace ehh wai kanta ne yake dan ciwo shiyasa " inna tace to shikenan, brr Saddiq ne da brr faruq suka fito hafsy na binsu abaya, a hnkl tace ya Saddiq bari inshiga ciki gurinta, zan dan ganta ne minti biyu don Allah, " brr Saddiq yace no babu komai sai kinfito, muna jiranki, "hafsy tace too tare da shigewa cikin gida
. .
Barrister Saddiq yace no babu komai sai kin fito muna jiranki, " hafsy tace too tare da shigewa cikin gida, kai tsaye ta nufi dakin mu, hannu na taja mukayi waje " ina kokarin ce mata lafiya " sai ta rigani cewa Qawata lafiya kuwa, me kuma ya kuma faruwa " yatsina fuska nayi snn nace babu komai me kika gani, " hafsy tace naga kin shigo cikin gidane batare da kin koma dakin inna ba, me kuma yace miki yau " babu komai nace mata, kawai dai munyi magana ne akan su hauwa, " zaro ido tayi snn tace me kikace mai, " cikin sauri nace nagaya masa nayi ni bazan iya kishi da su hauwa ba, " hafsy tace ammana ae nagaya miki bason su yake ba ko " nace mata ehh shima hakan yace " hafsy tace to shine kuma zaki mai maganar " cikin gundura da tambayoyin tan nace mata ke ni karki dameni innayi niyama sai ince nafasa wlhy, kuma banga shegiyar da ta isa tasakani inso shi ba " cikin sauri hafsy tace to Allah yabaki hkr, kidaiyi tunani akan maganar, " cikin tsiwa nace idan kuma naki fa " mmk nane yacika hafsy don ganin ni rashin mutunci baya min kadan, kuma komawa inayi, dataga zamu batane a lkcn yasata cewa to sai anjima, ina jiran kifa gobe kibiyomin mu wuce mkrnt, " tsaki naja snn nayi daki abina, ita kuwa takoma tasamesu snn sukayi tafiyar su. . Wata ranar jumma'a ne bayan mundawo daga mkrntar boko, snn kuma ba na islamiyya muna zaune acikin daki ne saiga baffa yashigo dakin namu da sallama kowa yasha mmkn ganin sa, dom kuwa rabonda mugansa a dakin mu har mun manta, sai kuwa gashinan yau, bayan mun gaggaisa ne muka mike don basu guri su da ammi, don kuwa a zaton mu gunta yazo, sai kuma yace mana" kudawo dukkan ku gurinku nazo,
.
sai muka dawo muka risina kowa tana jiran taji meke tafe da shi " gyaran murya yayi snn yace maryam fauziyya juwairiyya hamdiyya da kuma ke khairiyya Abinda yasa kukaga nataraku anan ba komai bane face ina son dukkan ku ko wacce acikin ku tayi magana da saurayinta yaturo magabatan sa, don kuwa aure zan muku dukkan ku gabaki daya " cikin hanzari nadago idona na kalle shi a razane, duk duniya babu abinda natsana irin aure, don kuwa bana son damuwa, don gani nake kamar duk maza halin su daya ne da baffan mu, shiyasa kwata kwata nagagara saka wani da namiji a raina, maganar sace ta katsemin tunanina da cewa " ku maryama da fauziyya yaushene zaku fara jarabawar fita daga makarantar, " cikin sanyin murya adda mrym tace baffa nan da sati biyu ne idan Allah yakaimu, " baffa yayi ajiyar zuciya snn yace to masha Allah, daman munyi magana da maigari jiya, insha Allahu auren ku bazai wuce nan da wata guda ba, "bani ba har ita adda maryam in itama tarazana da jin batun baffan, ammana haka dai babu wacce ta isa ta musa masa, bayan yakaraci kaf bayanin sa ne, yatashi zai fita nayi saurin cewa " baffa ina da magana " badon yaso ba yakoma ya zauna, yace menene kuma " cikin sanyin murya nace baffa harda nine amaganar auren " cikin sauri yace harda ke mana, ko ke ba mace bace ba, " a hnkl nace to ni banda saurayi, banda kowa, " a fusace yace ba inna tace min jiya wani saurayinki yazo gaisheta ba, to inma baki dashi kije kinemo ni dai nagaya miki, auren ku nan da wata guda, fuuu yaja babban garen sa yafice " habawa mana biri ai yayi kama da mutum, ninasan wnn maganar bana bakin baffa bane, dama ae sai dai innan kam, don kuwa itace zata kitsa masa wnn batun, to wlhy zanje insameta saina mata rashin mutunci kuwa, da sauri na mike tsaye zan fice. - ISMAIL SANI

0 comments:

Post a Comment