'YA'YA MATA page 9
.
Da daddare misalin karfe 12 ne na taso na dauki wuka ta, farfajiyar inna na nufa, kaitsaye na nufi dakin ta, ina turawa kuwa yabude, nasaka kaina ciki, inda take kwance na nufa, da bakin wukan nadagata, tana tashi kuwa mukayi ido hudu da ita, cikin karfin hali, murya ta kasa kasa nace" mikomin wuyanki in yanka ki, wlhy yau kasheki kawai zanyi kowama ya huta, naga alamar bakya bukatar ki a raye " cikin karkarwa, murya na rawa tace min ennan don Allah kiyi hkr, me kuma na miki yau, wlhy ina son ganina a raye " cikin tsawatarwa nace au baki ma san me kikayi ba, to ubanwa yasaki kecewa baffa ya aureddamu, haka muka cemiki aure muke so kome, " innalillahi wa inna alaihirraji'un inna tace ennan kiyi hkr don Allah wlhy gobe goben nan zance masa yafasa auren kun, " cikin tsawa nace dalla rufe min baki, wato harda cewa ko da tabarmar zana ne akai mu dashi ko, su ya amadu kuma ama matan su kaya na gani nafada ko, to ta Allah bataki, najiki sarai, bakisan inada aljannun da suke gaya min duk abinda kika fada abayan idona ba, to duk abinda kike tattaunawa sunzo sun gaya min " cikin razana inna tace aljannu dai ennan, ai wlhy bansan suna jina ba ai da ban fada ba, kuma wlhy na yarda sakk fa duk abinda nafada shi kika mayar miki, to insha Allahu bazan kara maganar kuba, ennan ai aljannu ba wasa ba " inna taso taban dariya don ganin yanda ta nuna tsoronta afili, amma sai na daure naci murrr, nace cabb in kin rayu kenan, ance miki yau zan bar ki ne, ai yau sai dai gari ya waye miki a barzahu Salati inna tasaka snn tace kidubi girman Allah ki kyaleni, wlhy ko yanzu kikeson intashi halliru ince mai afasa auren nan wlhy zanje, " hummm nace snn nace mata to shikenan zan ara miki aron lkc zuwa gobe innaji wani abu sabanin haka to wlhy zan dawo in yankaki, . ki mutu kuma na kashe banza na kashe wofi, kuma infi kowa kukan mutuwarki wlhy, in kuma taya masu bincike binciken wanda ya kasheki wlhy " cikin sauri inna tace na yarda wlhy " a hnkl nace to sai kuma abu nagaba " zaro ido inna tayi snn tace wlhy iyakar abinda mukayi magana akai kenan, " nace ehh ai nasani kawai ina son ince miki ne kice masa auren adda maryam da adda Fauzy kawai za ayi, nida adda hamdy da adda juw ba yanzu ba, adda juw da adda hamdy wani shekara zasu gama makaranta, ni kuma sai nan da shekara biyu, don haka kice masa nan gaba ma auren adda juw da adda hamdy za ayi banda ni " cikin sauri inna tace to shikenan an gama ennan wlhy zangaya masa tass " murmushi nayi snn namike nace mata to sai da safe, kofar dakinta naja mata snn nayi gaba abina Baccin da inna ta gagarayi kenan tanata sakar zuci caan ma sai tayi shiru tace ummm kar aljannunta su juyo me nake fada acikin zuciyar ma.
.
Washe gari da safen kuwa baffa yashigo gaida inna, inna ta tsaresa da maganar auren, tace mai " nayi wani tunani ne inaga ayi auren maryam da fauziyya tunda sune suka kawo nasu samarikan cikin gida ammana sauran abarsu ba yanzu ba, a kyalesu su gama mkrntr tukunna " cikin hanzari baffa ya dago kai yace ko meyasa za ayi hakan inna, cikin isa da mallaka tace haka naga dama ko baza ayi bane " cikin sauri yace an gama " snn tace kuma ko wacce zaka cire kudi kamata kayan daki dai dai gwargwado " yace to shikenan inna " tace mai to Allah yayi maka Albarka " yace amin, snn yatashi yafice " ajiyar zuciya inna tasake snn tace kun daiji dai ko banyi wata magana ba, abinda tagaya min shi nafada " (hummm inna Kennan duk tabi ta tsorata ta dauka zancen aljannun da gske ne ) Cikin gida ya nufa snn ya wuce dakin mu, da sallama ya shiga, bayan ya zauna ne yadube mu yace daman zancen auren kunnan ne yakawo ni, inaga za ayi na maryam da fauziyya kawai inyaso ku sai mubari sai wata shekara don kuwa, yanzu abubuwa sun min yawa sbd auren mutane hudu ne agaba na, danliti ma jiya munje tambayar masa er gidan malam dan asabe " . ammi tace aaa lalle fa abu yayi kyau to ai shikenan ubangiji Allah ya ara mana aron rai musha biki " amin muka ce dukkan mu snn ya wuce yafita , tafawa mukayi tare da shewa da dariya snn suka dubeni sukace er uwa me kuma kikayi aka fasa auran " murmushi nayi snn nace ai kuwa babu komai, kawai dai inaga addu'ar muce ta karbu, " sun dai jini ne amma bawai don sun yarda da abinda nace ba Tuni Shirye shiryen bikin su adda maryam ya kan kama har gidan su uncle Aliyu sunkawo kayan lefe, kayan lefen adda maryam bakaramin kyau sukayi ba, tun daga kayan lefen zaka gane gidan sun suna da bajinta, lami kuwa da ladidi ina sa saka ina sa ajiye gulma da bakinciki sai cinsu suke, hassada afilin Allah suke nunawa,
.
sai yada zancen suke atsakar gida, habaice habaice kam babu ka hannun yaro, tun ammi tana damuwa har ta daina, " ranan kuwa suna zaune saiga su uncle Aliyu nan shida abokanan sa sunzo gaisuwa, daki daki suka shiga suka gaishesu suka bawa ammi turmi uku na atamfa, da kwalin indomie, kwalin taliya, macaroni, snn suka dau dubu goma suka bata, da farko taki karbar kudin, sai da suka bar mata agun sukayi tafiyar su" baffa kuwa suka bashi dubu goma da buhun shinkafa er gwamnati, lami da ladidi kuwa dubu biyar biyar, abin yabasu mmk ammana ko godiya basuyi ba, sai ma cewa da sukayi an sayar da yarinya ne, wai daman ammi tallan mu take, " dasuka je gun inna kuwa dubu goma suka bata har da turmi biyu na atamfa kar kuso kuga bakin inna ranan har kunne, fitowa tsakar gida tayi tana cewa " kai amma yau naga ranar haihuwar 'ya mace, ashe riba ce da shi " lami ce taleko snn tayi tsaki ta koma, inna tace kee ennan karki yarda kice zaki min rashin kunya, don kunga ku bakuda jari adakin ku, kun tarawa mutane gayyar ya'ya maza, babu wata ribar da zamu samu ajikin su, sai dai akaiwa iyayen wasu " ladidi ce ta leko tare da cewa kaii inna amma ke butulu ce, baki kuma tsoron Allah kwata kwata acikin ranki. . Ladidi ce ta leko tare da cewa kaii inna amma ke butulu ce, baki kuma tsoron Allah kwata kwata Anya ni tunda nake nataba ganin tsohuwa jarabebbiya irinki kuwa, "Lami ce tafito afusace tareda cewa, kifada ki kara fada bantaba ganin matsiyaciyar tsohuwa irin wnn ba, to bari kiji ingaya miki Allah bazai barki ba, sbd irin butuncin da kika masa, kince ya'ya maza yabaki, kim koma kince ya'ya mata nan ma yabaki, amma sbd butulci irin naki baki gode masa ba, nan ma kikace sun miki yawa, to wlhy ki kiyayeni don kuwa in bakiyi sa'a ba bakinki shine ajalinki " waiii kar kuso kuga inna yanda tayi tsalle tafado kasa tana birgima wai su lami sun zageta, kuma sunce sai sun kasheta "muna daki munajin duk abinda ake, tunda naji inna na ihu a tsakar gida na zame jikina nayi waje da gudu ko hijab ban dauka ba na nufi majalisar su baffa, kamar wacce a ka wurgo suka ganni agun,
.
baffa da sauri yace meyake faruwa khairiyya, cikin tashin hnkln karya nace baffa kazo su lami zasu kashe inna, " baffa yace zasu kasheta kamar yaya, " bance mai komai ba sai ma jan hannun sa danaketayi alamar yataso, kuka nasake masa mai cin rai, " da sauri abokan sa sukace to katashi kaje mana kaga ko lafiya " cikin sauri baffa yamike shine a gaba ina binshi abaya, shi yafara shiga, ni kuwa na labe a zauren, yana shiga kuwa yayi arba da inna kwance tsakar gida sai tsala ihu take, da sauri baffa yayi kanta yana tambayar lafiya " cikin sheshshekar kuka tace ladidi da lami ne suka zageni suka min tatas, snn daga bisani sukace sune ajalina Salati baffa yasake snn yadaga kai yakalli ladidi rike da kugu tana hararan sa, lami kuwa ko kallon inda suke batayi ba " yace yanzu cin mutuncin da zakumin kenan uwata mahaifita kuce kune ajalinta, ku zaga min uwa " . sai a snn nashigo nace baffa wlhy karma kaso kaji zagin harda cewa wai ko kai babu yanda ka iya da su, haka zaka gansu kuma kabar su, wai ai kai a tafin hannun su kake, juyaka suke yanda ransu ke so, kuma ko ita innar wai bata isa tafada kaji ba, sai su, " inna da ke kwance a gun cikin sauri tace ehh wlhy haka suka ce min " tsayawa kawai sukayi suna kallona don ganin irin sharrin da nake shirin kulla musu, gashi babu halin musu tunda itama innar ta goyi baya na " hawaye ne ya gangaro daga idon baffa, snn yasaka hannu ya goge tare da cewa ladidi da lami tsakanina da ku sai Allah isa kuma kowacce taje gidan su na mata sake daddaya " salati suka sake a tare snn lami tace daman ashe haka kike khairiyya, ban taba ganin babban muna fuka irin kiba tunda nake a rayuwa ta " ina daga bayan baffa na kada musu manyan idanuwana tare da murguda musu bakina, na kuma yi musu gwalo " cikin kuka ladidi tace Shegiya kawai kinyi wa kanki wlhy, mara tarbiyya kawai, "sanda baffa ya dauka tare da binsu da shi yace wlhy idan baku kwashi kayanku kunbar gidan nan ba saina muku shegen duka, da gudu suka shige daki tare da turo kofa " da sauri na nufi gurin inna ina ce mata sannu kinji inna muje in kaiki daki, da kyar inna ta mike tare da cewa" Allah dai yayi miki Albarka ennan " baffa na binmu abaya yana cewa Amin inna " . har daki muka kaita na kwantar da ita snn na koma namu dakin, ina shiga ammi tace kee khairiyya lafiyan ki kuwa, ina ruwanki da tsabgarsu dazaki saka asake su babu gaira babu dalili " ajiyar zuciya nayi snn nace kwantar da hnkln ki ammi ba dadewa zasuyi ba, bazasufi kwana uku zuwa hudu ba zasu dawo, kawai na musu hakan ne sbd ina son kudawo daya, babu yanda za'ayi ace ke kina da saki daya akanki su kuma basu dashi, ina son ne suma su taba zafin saki, su dandanata suji ko da dadi ko babu dadi, ammana ba wani dadewa zasuyiba, nida kaina zansa ke sawa adawo da su. - ISMAIL SANI
Monday, 4 December 2017
Home »
'Ya 'Ya Mata Complete
» 'Ya 'Ya Mata Page 9 Latest Hausa Novel - ISMAIL SANI
0 comments:
Post a Comment